Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 24
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 24: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 24. Na fito falo inda su Yaya Aliya ke cin waina da miyar taushe,…
4,477 words
Na fito falo inda su Yaya Aliya ke cin waina da miyar taushe, ƙamshin daddawan da tafarnuwa suka cika gurin. Samun guri nayi na zauna naci munata hira dasu kala kala.Cousin ɗina Maimuna ta shigo tana cewa, “Auta, Momy na kiranki a babban falo.” Na ɗauki mayafina na fita. A falon Momy ke zaune tare da Yaya Usman. Na durƙusa cikin ladabi, “Ina kwana Yaya?”Ya yi murmushi, yana kallona da fara’a. “Amarya, har yanzu banga kimfara kuka ba?” Momy ta yi dariya tana cewa, “Aa , Usman kukan me zatayi da sassafe haka. Da yamma zata fara kukan ai” Na dan murmusa, na ce cikin ladabi, “Momy gani .” Sai ta kalle tace “Autata, Ashe ba’a sallami mijin naki na Nazata an sallameshi daga asibiti, ashe sai bayan sati biyu. Amma yanzu Mai Martaba ya turo mota, yace kije ki dubashi kafin a kai ki fada yau. Abbanki ya bada izini. Ki je ki ganshi, ki dawo yanzu.?” Na ce a hankali, “Momy… Maryam zata rakani?”Ta girgiza kai tana murmushi. “Aa, Ramlah. Gidan sarauta da sirri . Abbanki ma yace yawancin mutane suna zaton yana kasashen waje har yanzu. Kada ki damu, ki je ke kaɗai.” Zuciyata ta buga da karfi, amma na daure.
Na gyada kai, na ɗauki mayafina, na nufi bayan gida inda aka ajiye motar fada mai launin baki, tambarin gidan sarauta yana haske kamar azurfa a jikin kofar. Dogari ya buɗe kofar yana faɗin, “Your Highness, please.” Na shiga cikin nutsuwa, numfashina yana fita a hankali. Motar ta fara tafiya cikin natsuwa, ƙamshin turaren Oud Royal ya cike motar, yana hade da sanyin AC.
Na jingina da kujerar.
Da muka isa Royal Crest Private Hospital, an buɗe mini ƙofa cikin girmamawa.
Na bi corridor ɗin da ya sha fitilu masu haske ƙamshin turaren disinfectant yana yawo.
Har na isa kofar ɗakin da aka rubuta “VIP 1A”.
Na tsaya na ɗan daidaita mayafina, Na tsaya a bakin ƙofar ɗakin, zuciyata na bugawa kamar ana ƙoƙarin fasa ƙirjina da ƙarfi.
Ko da yake an ce min yana samun sauƙi, amma ba haka nake jin zuciyata ba. Hannuna na riƙe wayata, sai zufa ke ɓullowa a tafin hannuna duk da sanyin gurin .sannan na murɗa ƙofar cikin sanyi.
“Assalamu alaikum…”
Muryata ta fita kamar iska. Cikin ɗakin, iska mai sanyi ta buge ni, tana ɗauke da wani ƙamshi mai natsuwa ƙamshin turarensa da na ruwan asibiti suka gauraye.
Idanuwana suka sauka a kansa.
Na ɗaga kallo a hankali, idanuna suka sauka a kansa… mijina yanzu. Yana kwance cikin farin kaya, fuskarsa ta cika da annuri amma har yanzu akwai alamar rauni. Gashinsa ya kwanta bisa goshinsa, idonsa a rufe, kamar wanda yake cikin baccin da yake jin dadi.
A hankali ya motsa, idanunsa suka buɗe. Lokacin da ya gan ni, murmushi ya bayyana a fuskarsa. "Na yi tunanin baki zo ba," muryarsa ta fito da sanyi, amma tana da wani irin ƙarfi da ke girgiza zuciyata.
Na kasa magana. Sai kawai na sunkuyar da kai Na matsa a hankali, na tsaya “Yaya jiki?”
Na ce sau biyu, amma har yanzu shiru.
na ji muryarsa muryar da ta soki zuciyata daga tushe, mai sanyi, mai natsuwa amma mai nauyi “Da izinin wa kika tafi jiya?”
Na ɗan daga kai cikin sauri, idanuwamu suka haɗu sai wani irin yanayi ya ratsani. Na tsaya cak, yana kallona kai tsaye. A cikin idonsa akwai tambaya, amma akwai wani abu dabam kulawa, fushi, da soyayya a lokaci guda.
Na kasa magana. “Ni… Momy ta ce…”
Ya sauke numfashi a hankali, idanunsa basu bar nawa ba.
“To wannan shi ne ƙarshe. Kada ki sake tafiya kibarni. Idan kika zo… ki zauna kusa dani.” Zuciyata ta tsaya cak, jikina ya fara rawa. Kafin na iya cewa komai, sai muryarsa ta sake fita, wannan karon cikin taushi, amma tana da wani irin iko da zuciyata bata taɓa jin irinsa ba. “Bazakizo ba?”
“Bakyasona ko?” Ya saki murmushi.
“Ni fa mijinki ne yanzu,” ya ce
Na kasa magana.
Sai kawai ya ɗan tabe labbansa da ƙarfi kaɗan, “To ni ina sonki, Ramlah.”
Kalmarsa ta yi min wani sanyi ajiki.
Kafin in iya motsawa, sai ya miko min hannunsa hannun da yake da zafi mai laushi, yatsunsa sun motsa a hankali.
“Come to me… My Euphoria.”
Na tsaya a wurin kamar wacce aka daskarar.
Zuciyata tana bugawa, kamar zata fasa ƙirjina.
Numfashi ya kasa fita daidai.
Da kyar, na ɗaga ƙafata, na matsa kadan.
Sai na ji idonsa suna biye da ni kamar maganadisu.
Nana hadiza
09030569336
[26/10, 9:15 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SITTIN DA UKU
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
*****
Kafin inyi wani abu, hannunsa ya riko nawa a hankali. Wani irin daɗi ya shige ni, kamar jikina ya saki gaba daya Numfashinsa ya fara fita a hankali. “Ki zauna, don Allah.”
Na zauna a gefensa, zuciyata na bugawa da tsoro da kunya da wani abu da ban san sunansa ba. Yana kallona kamar wanda yake son tabbatarwa da kansa cewa gaskiya nake a gabansa. “Na gode…” ya faɗa cikin rauni.
Ya lumshe idanu, yana shafa yatsuna a gefen tafin hannuna. “Kin san na yi ta mafarki kina kallona haka?”Na kasa kallonsa, sai dai numfashi na ya fara sauri.Sai kawai ya ɗaga hannuna ya kai gefen fuskarsa.
Na kasa cewa komai, sai kawai hawaye suka zubo daga idanuna.
A cikin zuciyata, na ji kalmarsa tana maimaituwa My Euphoria…
Yana kallona da idanunsa , Numfashinsa yana fita a hankali, yana motsa labbansa da muryar da ta cika dakin da wani irin sanyi “Kinyi kyau… Ramlah.
Kingaji ko?
Kun sha biki?
To me yasa baki taɓa hira dani ba kibani labarin biƙin mana?”
Kalmar ta fita daga bakinsa cikin salo, kamar wata waka. Na kasa amsawa.
Kunya ta mamaye ni gaba ɗaya, har harshena ya makale. Zuciyata tana bugawa kamar ana busa ganga a cikinta, numfashi ya tsaya a ƙirjina.
Sai ya ɗan murmusa, yana kallona kai tsaye, muryarsa ta canza zuwa mai zurfi da tausayi “To, ki bani labari.
Ki gaya min wani abu, My Euphoria… kinji?”
Na yi shiru.
Na kasa cewa komai saboda yadda yake kallona.Idonsa ya haɗu da nawa, numfashinsa ya dinga fita cikin natsuwa.
Sai ya ɗan matsa kai a hankali, yana kallon yadda nake rike mayafina da hannuwa biyu.
“Ina kaunarki, My Euphoria,”
ya faɗa da murya mai taushi amma cike da ma’ana. Na rufe idona a hankali saboda kunya.Na ji kamar gaba ɗaya jikina ya yi sanyi.Na kasa magana kamar harshena ya makale saboda jin nauyin da ke cikin kalmar “Ina kaunarki.”A hankali ya ce
“Ki zauna kusa da ni… ina son jin kamshinki sosai.” Sai kawai na ji ya matso kusa dani.
Kamar wanda yake tsoron kar in ɓace, ya kamo hannuna cikin natsuwa, sai kuma a hankali na ga ya miƙe daga inda yake kwance, ya zauna. Numfashinsa ya ɗan sauya yana fita cikin huci, amma idanunsa basu bar fuskata ba.
Kafin in san me ke faruwa, sai na ji hannunsa ya ɗan zagayo ni daga baya, ya rungume ni da wani irin sanyi mai cike da nauyi.
Wani kalar dadi da sanyi ya ratsa jikina lokaci guda. Na tsaya cak, zuciyata tana tsalle. “Ni dai… bana so ki tafi yanzu,” ya faɗa a hankali, yana murmushi da jiki mai karkarwa
Ya jingina fuskarsa a wuyana, yana sauke numfashi cikin natsuwa. Na ji kamar lokaci ya tsaya cak babu komai sai bugun zuciyata da nashi suna haɗuwa.
Amma kafin na iya cewa komai, sai numfashinsa ya fara sauyawa.
Wani irin ƙara mai rauni ta fito daga bakinsa, jikinsa ya ɗan kakkare. Na ji hannunsa ya fara karkarwa sosai a bayana, sai jijiyoyin wuyansa suka fito fili.
Ya kama kafadata da ƙarfin da bai dace ba, numfashinsa yana fita cikin zafi.
“ Ya Allah!”
na furta da murya mai rawa.
Ya ɗaga kansa kadan, idanunsa suka fara bushewa, sai suka koma kamar wanda yake neman faduwa Cikin sauri jikinsa ya fara jijjiga gaba ɗaya,N tureni yana mai komawa kwance jiķin na girgiza sosai har yana fita hankalinsa idonsa na kafewa “Doctor! Doctor!”
na kira da ƙarfi, cikin tashin hankali.
Na Naja jikina daga gefensa cikin tsoro, zuciyata tana dukan da ban taɓa jin irinsa ba.
Na fice da gudu daga ɗakin ina kuka, ina kiran ma’aikatan asibiti. “Please! Ku zo! Jikinsa! Jikinsa yana jijjiga!”
Likitansa Dr. Khalid da nurses suka shigo cikin gaggawa, suna ɗauke da kayan gwaji da allura. Na tsaya a bakin ƙofa ina rawar jiki, hawaye na zuba ba tare da tsayawa ba.
“What happened?” Dr. Khalid ya tambaye ni da sauri.
“He was… he was fine! Ya zauna, ya tashi, sai kawai jikinsa ya fara karkarwa!”
Nurses suka zagaye gadon, suka daura oxygen, suka duba numfashinsa.
Dr. Khalid ya ba da umarni,
“BP dropping! Give me the sedative! Quick!”
Dakin ya cika da karar kayan gwaji da sautin injin da ke bada gargadi. Na rufe bakina da hannu, hawaye suna gangarowa cikin tashin hankali. “Oh Allah, ka taimake shi…”
Na ji nurse ɗaya tana cewa cikin gaggawa,
“He’s going into shock, Doctor!” “Push the medication! Now!”
Sai na ji jikinsa ya yi wani irin karkarwa na ƙarshe, sannan ya kwanta shiru.
Likita ya sauke numfashi mai nauyi, yana duba monitor. “Stable… he’s stabilizing now. He’ll be fine.”
Na tsaya ina kuka kamar yarinya, idona a kansa. Fuskarsa ta koma daidai, amma har yanzu zuciyarsa tana bugawa.
Na ɗan matsa gefe, ina kallonsa cikin hawaye. “Ya Allah… ka bashi lafiya.”
Dr. Khalid ya juyo ya kalle ni da tausayi.
“Calm down, Princess. He just needs rest. His body is weak. Please, you should rest too.”
Na gyada kai cikin rawar murya, na juya na fita daga ɗakin cikin sauri, hawaye na zuba.
Cikin hallway, iska mai sanyi ta buge ni, amma jikina har yanzu yana rawa.
Na jingina da bango, na rufe idona, zuciyata tana tambaya cikin tsoro da tausayi a hankali nakarasa zuwa motar.
Motar fada na gama tsayawa a harabar gidanmu, direban ya buɗe ƙofa da girmamawa. Ban jira ya faɗi komai ba, na fito cikin sauri idona duk ya kumbura, fuska cike da hawayen da suka bushe suka sake fitowa.
Na rufe bakina da hannu ina ƙoƙarin danne kukan da yake kara tasomun.Da na shiga gidan, hayaniyar mutane koina nayi saurin haye sama kada kowa yaganni.Na wuce kai tsaye sama, ba tare da na tsaya ba.
Sai dai kafin in karasa, Momy ta fito daga ɗakinta tana kirana da sauri “Auta! Ramlah!”
Tana ganin fuskata, sai jikinta ya yi sanyi.
Ta karaso cikin hanzari ta rungume ni “Subhanallah! Me ya faru haka, autata? Me ya same shi?” Na kasa magana, sai kuka kawai nake yi.Zuciyata ta kasa ɗaukar nauyin abin da na gani. “Momy... yau ma sai da naje jikinsa yakara jijjiga, yana wahala... na tsorata Momy…”
Na fadi haka cikin muryar kuka, hawaye suna fita. Momy ta rungume ni sosai, tana rarrashi na “Shhhh... shhhh... komai zai wuce, kin ji?
Kada ki damu, Allah zai ba shi lafiya.
Kiyi shiru, kada mutane su jiyo da hankalinsu ƙanki kinji kidaina kukan kinji.”
Ta shafa bayana tana goge min hawaye da tafin hannunta, tana sake maimaita mun kalmomin masu taushi. “Kiyi shiru, autata. Kiyi tawakkali, wannan jarrabawa ce Allah zai bashi lafiya.”
Na girgiza kai ina kuka. “Momy, to me isa sai naje ne yake shiga wannan haļin? Na je da niyyar dubashi kawai, amma sai hakan ta faru sau biyu kenan fa...”
Ta ɗan janye ni daga jikinta ta kalle ni da kulawa. “Ba ke kika jawo ba. Kaddara ce, autata. Ki daina kuka, yau fa rana ce mai albarka, aure ya riga da ya tabbata, ki tsaya ki karɓi wannan a matsayin jarrabawa daga Allah.”
Na share hawaye da bayan hannu ina jin muryarta na shiga zuciyata kamar ruwa mai sanyi. Sai lokacin na ji ƙofar falon ta buɗe, muryar Abbana ce yakaraso cikin dakin yana “Assalamu alaikum.” Momy ta amsa da sauri, ta ce da ni “Tashi, Abbanki ne.” Na goge kukan da hanzari, na daidaita mayafina, na sauko ƙasa cikin nutsuwa. Abba yana zaune a kujerar babban falo, sanye da farin babbar riga mai kyau, fuskarsa cike da natsuwa.
Na durƙusa a gabansa cikin ladabi “Abba, ina kwana.” Ya kalleni da murmushi.
“Lafiya lau, Ramlah.” Sai ya ɗan gyara zama, ya ɗora hannu kan cinyarsa, yana kallona ki sani, ɗiyata, rayuwa cike take da jarrabawa.
Kaddara ba ta neman izininmu kafin ta faru tana zuwa ne don ta gwada imaninmu.”
Na sunkuyar da kai, hawaye na cika idona. “Abba, na tsorata. Na tsorata da abin da na gani.” Ya gyada kai, cikin tausasawa.
“Na sani. Amma ki tuna da abin da na koya miki, Ramlah mace mai imani tana fuskantar jarrabawa da haƙuri, ba da kuka ba.
Ki kasance kamar uwa ga mijinki, ko da kuwa jarrabawa ta same shi a rana ta farko.”
Sai ya ja numfashi mai nauyi.
“Asad mutum ne mai girma da daraja, Mutum ne mai kirki wanda kudinsa da sarautarsu bai sanya yana wulakanta dan adam ba, Nayi rayuwa dashi sosai zan iya ce miki mutum ne mai kiyaye dokokin Allah ga tsoron Allah ko a mafarki banta tunanin zaizo ki ba dan nasan akwai tazara a tsakaninku amma da yake matar mutum kabarinsa kinga yadda Allah yatsara, kada naji kada nagani Auta ki kara hakuri dan can ma wani babin jarabawa ne Allah zai kara bude miki.amma yanzu yana bukatar addu’a da soyayya daga gare ki fiye da komai. Kar ki bari tsoro ya raba ki da abin da Allah ya rubuta miki.”
Nana hadiza
09030569336
[26/10, 9:15 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SITTIN DA HUDU
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
*****
Na share hawaye cikin jin kalmarsa tana shiga zuciyata. Ya miƙo hannu ya dafa kafadata“Ki ɗaga kai ki zama karama mace amma mai ƙarfin zuciya. Da daddare za a ɗauke ki zuwa fada, ki tafi da natsuwa, ki tafi da addu’a, akwai kudinki a hannuna sjn bada kudin da suka dora a lefe 5m sannan sadakinki 1m kwanaki mahaifin bashari yazo yakawo gadonki na bashari 2.3m sai kuma tukwuicin da kika samu da walima kimanin nawane ma kaltume?.” Hajja kaltume tace “million 5 da dubu dari uku”. Yauwa kinga kudinki yakama million 13 da dari shida to kmar yadda muka tsara za’a siyamiki rumfa dashi sai ki dinga karbar haya duk shekara. Na manta akwai wani gida da akace bashari yasiya miki kamar yadda mahaifinsa ya gayamun to shi sun bada mukullinsa zan saka asiyar sai ahaɗa duka. DanAllah ki kula sosai kibi mijinki kada naji kada na gani auta banson kawayen banza akula sosai akuma yi hakuri duk halin da kike ciki ga kaltume nan ki gayamata itace uwarki har abada. Na gyada kai cikin rawar murya. “To Abba. Insha Allahu.” Sai ya murmusa, “Allah Ya sanya albarka a wannan aure. Ki zama kamar haske a gidan su. Kada ki manta, kaddarar mutum ba ta nufin ƙarshen farin ciki sau da yawa, ita ce farkon sa.”
Ya miƙe, ya shafi kaina da hannunsa mai dumi. “Allah Ya albarkace ki, ɗiyata.”
Hawaye suka sake zubo min, amma wannan karon hawaye ne na tausayi da godiya.
Na durƙusa na rungume gwiwarsa cikin ladabi, zuciyata tana faɗin Ameen sau da dama.
Da yamma ta yi, rana ta fara sauka, Kafin lokaci ya cika, gidanmu ya cika da hayaniya da fatan alheri. Masu ɗaukar hotuna suna tayi “Amaryar ki fito lokaci yayi!”.
Na tsaya gaban madubi ina kallon kaina cikin mayafi fari sol. Momy ta matso kusa da ni, ta ɗora hannunta kan kafadata. “Ki tafi da addu’a, Ramlah. Wannan tafiya ba kamar kowace tafiya bace. Duk inda kika sa ƙafarki yau, kada ki manta da addua rayuwar gidan sarauta sai Allah kinjj.”
Na gyada kai cikin natsuwa, muryata ta kasa fita.A zuciyata ina jin kalmarta tana yawo “Ki tafi da Addua.”
A nan aka ji karar horn na motar fada. “Duk wadda taji wannan ƙara, ta san na gidan sarauta ne.”
Masu gadi suka buɗe ƙofar harabar gidan, sai motoci suka fara shigowa cikin tsari.
Babbar motar gaba black limousine mai tambari ta tsaya kai tsaye a gaban ƙofar filim gidan Dogarai a cikin fararen riga da hula mai launin royal blue suka tsaya a jere suna gaisuwa “Barka da zuwa.!”
“Allah Ya tabbatar da Alkhairi!”
Na kalli Momy, hawaye suka ciko idona.
Ta share min cikin sauri ta ce, “Ki shiga, autata. Badani zaku tafi ba kamar yadda tsarinsu yake babu wacce take rike amarya sai ta ɓangarensu zanzo idan ankwana biyu ki kula da abunda zakici karkiyi wasa da addua kinji.”
Maryam da yaya Aliya suka rikemun hannu suna nunamun motar da zasu shiga tare da sauran anties dina na daga musu kai.
Yaya billy kuma tana gefe ina ganimta tana kuka bance mata komai ba nashige mota daman momy tunsafe batazo ba wai batada lafiya tace.
Na shiga cikin motar cikin nutsuwa, zuciyata tana rawa kamar kar zafa fasa ƙirjina.Na zauna a bayan mota, na jingina da gilashin window, ina kallon fitilun gari da suka fara bayyana. Direban fada ya danna start, motar ta kama hanya cikin nutsuwa, tana biye da sauran motocin tsaro motocin dogarai, motocin jami’an Royal Security, sai wacce ke ɗauke da Uwar Amarya. Sai fitilun siren suka fara kyalli, suna nuna alamar “Masarauta babu batun tsayawa”
Dukkanin titin faɗar akwai kyau da kawatuwa sosai Bangarorin hanyoyin an shuka itatuwan royal palms masu tsayi da furanni masu haske. Daga nesa, fitilun manyan katanga masu launin zinariya suna haskawa tamkar taurari. Na zuba ido ina kallon su kowacce fitila tana da siffar zobe da alamar gidan sarauta mai rubutun “Daraja ta tabbata ga gidan Babangida.” Motar tana tafiya a hankali cikin wannan sararin da yake cike da tsaro, nutsuwa A gefe na dama, na hango dogarawa suna tsaye cikin kakkarfar layi kowanne da tambarin “Royal Guard.” Kowa yana riƙe da sanda mai launin azurfa. suna yi min salute cikin natsuwa yayin da motar ke wucewa.
Zuciyata ta kasa zama a wuri ɗaya.
Na jingina kai da gilashi, numfashina yana fita a hankali, zuciyata tana cewa “Yanzu haka ni ce amarya a wannan gidan ni ake bawa girman nan ohh Allah mai iko?” “Ni ce matar Yarima Asad, wanda ake kira Yariman da duniya ke girmamawa?” Na lumshe ido, zuciyata ta tsaya tsakanin tsoro da farin ciki.
A gefe, na hango wata alama da aka rubuta d “Fadar Babangida Gidan Da Alfahari Ya Huta.”
Da muka wuce ƙofar farko, ana busar kakaki daga nesa, karar ta cika ko’ina Na ji jikina ya yi sanyi na fahimci cewa daga wannan rana,
rayuwata ta sauya gaba ɗaya.
Motar ta ci gaba da tafiya Inata addua “Ya Allah..”
Lokacin da motar ta fara nufar ƙofar fada ta ƙarshe, hasken fitilu ya fara shigowa ta gilashi. Sai na lumshe ido, hawaye suka sauka a kuncina. Motar ta tsaya a hankali, kamar maƙogwaron lokaci ya tsaya yana sauraron wannan lokaci mai tarihi.
An isa bakin ƙofar Fadar Babangida.
Dogarawa sun tsaya a jere, kowannensu sanye da rigar royal white uniform mai ɗauke da tambarin gidan sarauta a kirji. A hannunsu akwai sanda mai sheƙin azurfa.
Suka daga sanda lokaci ɗaya, suka tsugunna suka ce cikin murya ɗaya mai ƙarfi “AURE YA DAURA, AMARYAR FADA TA ISO!”
A lokaci guda, kakaki biyu masu launin azurfa suka tashi sama, ana busawa cikin natsuwa.
Sautin ya cika “Phaaaammm! Phaaaaammm!”
Wani irin girma ya cika zuciyata, har sai da numfashina ya tsaya.
A lokacin ne mata masu bauta wa sarauniya suka fara fitowa daga cikin ƙofar. Fuskar kowacce cike da natsuwa, sanye da dogayen riguna masu launin royal blue da zaren zinariya a gefuna Na kalli yadda suke tafiya a tsari Inna Mero ce a gaba, mace mai shekaru amma mai fuskar da ke nuna iko da hikima.
A bayanta Zulaihat, mai murya mai sanyi, da kuma Gambo wacce tana tafiya ƙamshi ke biye da ita.
Inna Mero ta tsaya a gabana, ta durƙusa cikin ladabi, ta ɗaga kwalbar ruwa mai dauke da sandan azurfa a cikinta.Ruwan yana sheƙi Ta ce cikin murya mai ɗauke da girmamawa “Bismillahir Rahmanir Rahim.
Ga ruwan tsarki na gidan sarauta, alamar karɓa, albarka, da tsarkakewa daga duk wata fitina kafin shiga.”
Ta yayyafa ɗan ruwan a ƙafata, yana fita da ƙamshin rosewater da ɗan ɗanɗanon misk al-ward. Sai ta ɗora hannunta a ƙirjinta, ta ce “Da wannan ruwa, fadar Babangida ta karɓe ki da albarka. Ki shiga da natsuwa.”
Na lumshe ido a hankali, hawaye suka ciko saboda irin darajar da kalmar ta yi a zuciyata.
Lokacin da na buɗe ido, Gambo mai kamshi ta karaso da bukhoor a hannunta, tana yaye mayafina a hankali. Iskar turaren wuta ta ratsa jikina, tana gauraya ƙamshin oud, sandalwood da amber.
Zulaihat kuwa ta durƙusa a ƙasa, tana yayyafa min garin turare a ƙafa garin mai launin dusty gold wanda ke kyalli. Ta ce cikin sanyi “Da wannan turare, amarya ta shiga da albarka, ba da ƙura ba. Gidan da kika shiga zai samu nutsuwa, kamar yadda ƙamshi ke ratsa iska.”
Wani sanyi ya ratsa jikina, har sai da hawayen farin ciki suka gangaro a kuncina.Inna Mero ta miƙe, ta daga hannu sama cikin ladabi “Fadar Sarauta ta karɓe ki, Uwargidan Asad Babangida. Ki zama amarya mai nutsuwa, mai kamshi, mai albarka.”
Na sunkuyar da kai, na riƙe mayafina a ƙirji cikin ladabi. Zuciyata ta cika da fargaba da godiya lokaci guda. A hankali, dogarai suka ɗaga sandunansu sama, suka ba da hanya.
“A bude ƙofar babbar amarya zata shiga.”
An buɗe ƙofar ta ciki, hasken wasu fitilu suka cika fuskata.Iskar bukhoor ta ratsa numfashina, zuciyata ta buga da sabon irin natsuwa. Na ɗaga kafa na farko, na taka ƙafata cikin farfajiyar fadar Babangida
cikin natsuwa, da addu’a.
Ana karɓa ta cikin fadar, dogarawa suka rufe ƙofar bayan ta shige. Sai na ji sanyi mai daɗin gaske ya ratsa jikina irin sanyi mai ɗauke da ƙamshi. Iskar oud da sandalwood da ɗan amber na tashi a hankali, suna gauraya da ƙamshin furanni masu launin cream da aka zuba a cikin vase a ƙasan bango.
Ƙasa kuwa an rufe ta da Persian carpet mai launin ja da ruwan tabarau.
Wani haske na fitowa daga fitilun crystal chandelier da ke rataye a tsakiyar ɗakin, yana warware hasken da yake ƙara kyalli a jikin rigata.
Na tsaya a bakin ƙofa ina kallon abin da ke gabana cikin mamaki da natsuwa lokaci guda.
Wannan ɗaki ya fi komai da na taɓa gani a rayuwata.
Aka ce min in tsaya a gefe, saboda za a sanar da zuwana. ’Yan rakiyata suka matsa gefe, suka barni ni kaɗai a tsakiyar babbar ƙofa. Sai na ji ana busa wani irin ƙaho, murya mai ƙarfi “Sarki zai fito.” Nan da nan mutanen da ke cikin zauren suka miƙe da girmamawa, wasu suka sunkuyar da kai. Ni kuwa na ji jikina ya ɗauki rawa, zuciyata ta buga da karfi.
Nana hadiza
09030569336
[27/10, 9:48 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SITTIN DA BIYAR
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
*****
Sai na ga wani mutum ya fito dogo, bakin fata, sanye da babban riga mai kyan gaske, fuskarsa tana ɗauke da wani irin natsuwa da izza. Idanuwansa kyawawa, amma babu fara’a sosai a fuskarsa suna kama da Asad sai dai Asad zai nuna masa haske ne kawai.
Na durƙusa ƙasa da ladabi, murya ta na rawa nace “Ranka ya daɗe, Allah ya daɗa shekaru da lafiya. Na zo neman albarka daga gareka.” haka akasanar mun zan fada danda tanine haka zance masa ina wuni.
Sai ya tsaya yana kallona kamar yana nazarina, sannan cikin murya mai taushi amma cike da iko ya ce “Albarka ta tabbata gareki, Ramlah. Allah ya zaunar dake lafiya da ɗan sarki.”
Na ji kalamansa sun shige min zuciya. A lokacin ne na fahimci wannan ba kai tsaye ga mace da mijinta bane kalmar sarauta ce, wacce take ɗauke da nauyi da alfarma.
Bayan haka, wata dattijuwa tace “Ki biyo ni amarya, za ki ga matan sarki.”
Na bi ta cikin wata hanya mai tsawo, bangon gidan duk an yi musu ado da hotunan sarakuna na baya. Wani irin natsuwa mai cike da ƙasaita nake ji, amma a zuciyata akwai rawar fargaba.
Da muka shiga babban ɗaki, na ga matan sarauta zaune cikin kayan alatu, kowacce da irin nata kwalliyar, irin nata kamanni. A tsakiyarsu kuwa, wata ce ke zaune a kujera mai kyan gaske wato hajja sai Uwar Gida agefe. Da na ganta sai na saki numfashi. Tana da kwarjini, tana da kyau, amma kallonta. Na durƙusa ƙasa nace cikin ladabi“Ina wuninku.”
Ta ɗan yi shiru, tana kallona sama da ƙasa, kafin ta ɗan murmusa tace: “Kin iso lafiya Ramlah. Allah ya zaunar dake lafiya. Ki yi hakuri da rayuwar fada, ba kamar waje bane.”
Kalmarta ta ƙarshe ta yi min nauyi “fada ba kamar waje bane.” Na ji ta maimaita min kalmar da zuciyata ta kasa amsa.
A gefe kuwa, wasu matan sarki sun ɗan yi dariyar sirri, wasu kuma kallonsu ya bayyana cewa ba farin ciki suke da zuwana ba. Wasu suna ƙoƙarin murmushin dole.
Na ɗan saki murmushi kadan don kowa ya hango natsuwata, amma a raina hawaye ke zagaye. Na san daga wannan rana, rayuwata ta shiga sabon gida gidan da kalma ɗaya ta keɓe shi, Gidan Sarauta.
Tsakanin shashina da shashin sarki akwai yar tafiya dafari a mota xamuje sai sarki yabada umarnin akarasa dani akafa domin asanarwa da kowa zuwana. Maganar haduwar bangaren ɓata lokaci ne domin yafi ma sashen sarkin haduwa maryam ce tayi gudu tana gayamun gaskiya kinyi dace kinga haduwar gurin kamar ba kasar nan ba haka muka dinga kuskus har muka karasa sai zubewa akeyi ana gaishemu.
Gadone ne mai girma, wanda ya haɗu sosai fari ne sol A saman sa, an shimfiɗa farin lallausan silk duvet mai launin ruwan madara, tare da pillows masu tambarin “Royal House of Babangida.” A bayansa kuma, akwai babban mirror wall, wanda yake nuna kowanne motsi na cikin ɗakin kamar wani hoto mai rai.
Labulen royal velvet masu launin shuɗi da zinariya suna rufewa daga sama har ƙasa, suna ɗauke da ƙamshi irin na amber rose.
A gefe akwai wata ƙaramar table mai ƙarfe da gilashi, an ajiye a kanta incense burner da ke hura turaren bukhoor mai laushi.