Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 25

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 25

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 25: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 25. Sai na ji wani irin natsuwa mai zurfi ya lullube ni. Na taka cikin…

4,400 words

Sai na ji wani irin natsuwa mai zurfi ya lullube ni. Na taka cikin ɗakin a hankali, takalmina yana ƙaramar ƙara “ Ranki yadade ,” wata murya mai nutsuwa ta kira ni daga baya.Na juyo a hankali. Wata dattijuwa ce mai kyau sanye da riga mai launin dark blue da zaren zinariya a gefenta. Fuskarta kyakkyawa ce mai ɗauke da natsuwa Uwar Amarya Hajiya Zulaiha sunanta kenan.

Ta ƙaraso kusa da ni cikin natsuwa, tana murmushi. A hannunta akwai wani ƙaramin kwali mai launin zinariya da rubutu a kai“Alƙalamin Amarya.”

“Ranki yadaɗe,” ta faɗa cikin nutsuwa, “a gidan sarauta akwai al’ada duk amarya ana mata alƙalamin amarya. Wannan rigar tana nuna cewa daga yau kin zama Uwargida ta Sarauta, matar Yarima Asad Babangida wanda yake ƙarƙashin kariyar ikon fada.”

Ta buɗe kwalin a hankali. Ta ɗaga rigar ta ɗaura min a kafaɗa, tana murmushi cikin tausayi da natsuwa. “Ki sanya wannan rigar da zuciya ɗaya, ki sani, daga yau baki daga cikin al’ada ta yau da kullum ba. Kin shiga gidan da ake kallo a duniya.”

Na riƙe rigar a kirjina, idona cike da hawaye Na kasa cewa komai. Ina kallo su matar uncle hamza suka tafi kowa sai santin gidan uake sj yaya aliya suka raɗamun gobe zasu dawo.

Uwar Amarya tacemun“Ki sani, gidan sarauta kamar tafkin ruwa ne yana da nutsuwa, amma yana da zurfi. Ki kasance kamar ruwa mai natsuwa, mai sanyi, amma kada ki bari kowa ya gane zurfinki. Ki zauna da kowa da ladabi, amma ki lura da kowa da idon basira”

“To Hajiya, na gode,” na faɗa cikin murya mai rawa. Sai ta juya ta fita a hankali, ta bar ni cikin wannan ɗaki mai kyan gaske tabbas abbna yayi kokari babu abunda zan saka masa dashi sai adduoi. Maganar haduwar gurin baayi .Na zauna a bakin gadon, na zuba ido cikin mudubi Zuciyata na bugawa a hankali, numfashina yana fita “Ya Allah, ka bani ƙarfin zuciya da natsuwa. ”

******?

*******????

Cikin ɗakin mai cike da ƙamshin turaren black orchid, fitilar golden lamp tana kunne tana haskaka fuskokin Ayshatu dake video call da Fatima da take zaune a jikin gado mai duwatsu a gefuna. A cikin kunnuwan wayar Ayshatu, muryar fatima tana fita tana ba ta shawara amma zuciyarta taƙi karɓa.

Ayshatu ta kalleta da fuska mai cike da mamaki da gajiya ta ce “Fatima ki saurarine mana wannan wane magana kikeyi kamar yaya nayi hakuri da Muqaddam tunda ya aureni?”

Fatima ta ja numfashi, ta kalleta kai tsaye.

“To Ayshatu, me kikeso nagayamiki sama da gaskiya? Tun lokacin da kike bin Muqaddam nace kada ki sake ki rabu da Asad.

Babu yadda banyi dake ba.

Gashi yanzu kullum cikin kuka kike, babu abin da kike yi sai kiran sunan Asad.”

Ayshatu ta juya kanta gefe, idanunta cike da hawaye “Ke kuma kinsan indai ba sakin ki Muqaddam yayi ba, wallahi Allah ba zakj taba samun Asad ba. Banda ma abunki, ki godewa Allah mana, tunda har ya aureki.

Ni da ma zan samu daga cikin ƴan barikin nawa su aure ni, da sun taimaka min.”

Ayshatu ta goge hawayenta da yatsa, tana dariyar takaici. “Fatima, rayuwar Asad da ta Muqaddam akwai tazara mai nisa.

Wallahi nazata Muqaddam mai kudi ne, sai dana aureshi naga ashe yaron Asad ne!

Ko Yaron shagonansa! Wallahi sun fi sa kudi Aysha…Mansion nake da shi a Paris da Dubai yanzu babu su. Ashe da sunan yaransa Asad ya bani ɗaya na Nawal, ɗaya na Meena.

Yanzu haka, asarar da nayi dakyar Muqaddam ya bani 10 million, shima sai da na lallabashi.

Jiya ma, Nawal ta bani 5 million inaso in haɗa in bude shago. Kinga yarinyar da ya aura?

Wallahi kwana nayi ina kuka jiya kawai, kawata ta dora hotonta, ance Diamond Mai Martaba ya bata fa! Kuma ance masa ba yar kowa bace marainiya ce, Fatima!”

Fatima ta dafe kai da takaici. “Ayshatu! Ji kike fa kamar kin san kinada wayo ko? Fatima Ko malamai zaki bi yanzu dan ki samu Asad ya dawo? Ayshatu ta juyo da ɗan tsaki, tana girgiza kai. “Ke Fatima, bakida wata magana ce da ta huce ‘hakuri’.

Ke kullum sai ki ce inyi hakuri!

Ni wallahi zan san me zanyi zan dawo cikin rayuwar Asad ko taya!”

Fatima ta mike, ta gyara mayafinta. “To ai shikenan, gaki ga duniyar. Amma ki sani, wanda yake tafiya da zuciyarsa ba ya ganin hanyar gaskiya. Sai dai idan Allah ya nuna masa.” Atake ta kashe wayarta..

Dakin ya koma shiru sai sautin numfashin Ayshatu da AC. Ta zuba ido cikin madubi tana kallon fuskarta, sai ta fashe da kuka cikin raɗa. “Asad… ka manta dani… ka auri wata…”

Kafin ta shanye hawayen, sai kawai ta ji ƙarar kwankwaso kofa, ƙofar ta buɗe da ƙarfi, an hankado ta da karfi

Muqaddam ne ya shigo fuskarsa a ɗaure, idanunsa sun kaɗa..kana kallonsa kagansa cikin tsananin ɓacin rai. Ayshatu ce ta dallah masa harara sannan tace “Muqaddam! Yaya zaka shigomun guri ba Sallama kai fa kamar ba musulmi ba..”

Kafin ta ƙarasa magana, sai kawai ya wuce gabanta, kif! mari ya rufe mata fuska. A razane ta dafe kumatunta, idanunta suka ciko da hawaye. “Ni? Ka mara ni?”

Amma bai amsa ba.Ya sake matso wa, kif! ya kara mata wani marin da sai da ta ga taurari.

Numfashinta ya tsaya, zuciyarta na bugu da sauri. Yana huci kamar zaki da aka ɓata masa farauta. Ya nuna ta da yatsa yana faɗin “Ke! A wacece da zaki marar mun Uwargidana bayan marin ma har da cin mutunci?

Wannan iskancin naki ya isa wallahi.

Su basu shiga harkarki ba, amma ke kije ki ci mutuncin Uwargidana sa’arki ce kokuma kinada matsayinta agurina kokuma angayamiki kinfita ne? To bari in gayamiki, iskancinki ya tsaya a kaina.”

Ayshatu ta dafe kumatunta, tana rawar murya. “Muqaddam, ka mara ni saboda wata yar kauye da baka alfahari da ita sai yawon bariki

To naji, Allah ya isa! Ka sake ni! Ka sake ni kawai!”

Nana hadiza

09030569336

[28/10, 8:41 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN DA SHIDA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

*****

Cikin sauri ya shakota da ƙarfi, yana kallon cikin idonta. Muryarsa ta canza “Ke bari ki ji ki kuma sani… Ni cikakken dan iska ne, kuma wallahi bazan sake ki ba! Idan kina ganin wasa nakeyi, mu zuba!”

Ta shiga ƙoƙarin ƙwacewa tana huci, amma ya ƙara riƙe hannunta da ƙarfi, yana ƙara matsawa. “Kin ga wannan gida?

Har abada, ke da Asad babu ke babu shi tsakaninku idan ma dan shi kike cewa na sakike wallahi bazan yiba kuma kikara daga hannu kan matana narantse da Allah sai nayimiki hukuncin da sai kinyi kuka da kanki.

Kuma shi As’ad din dakike takama akansa wallahi bazai taɓa waiwayarki ba.”

Ya tura ta da ƙarfi ta faɗi kan kujera, ya juya da fushi yana huci, ya fita daga ɗakin da ƙarar takalminsa ya bugo kofar, labulen da ke gefen dakin ya motsa.

Ayshatu ta durƙusa, tana rike fuskarta da hannu biyu. Da wuyanta inda ya shaketa tana jan numfashi sosai Hawaye ke sauka, abunda baa taba yimata ba asad ko ihu bai mata baya zaginta kullum cikin faranta mata yanzu kuwa daga kunya, raɗaɗi, da bakin ciki.

“Ni Ayshatu... matar Asad... na zama haka?ni namiji ke tozartawa akan macce ina gidan asad yayi aure sama da sau 6 amma kowacce tazo sai tabini take samun lafiya. Nice yau wani ke duka? Har yana shakeni? Innalilahi” Ta fashe da kuka mai ƙarfi, numfashinta na rawa. A ƙasan zuciyarta, ta san wannan kukan ba na nadama bane kawai

amma farkon shan hukuncin ƙaddara da ta tsani jinta tun farko. “ Wallahi sai na komawa Asad koda zan tafi tumbur ne kai nakeso kai nake kauna Asad babangida farin cikina.”

**********

A cikin ɗakin VIP Room 1A na Royal Crest Hospital, shiru ya mamaye sararin dakin.

Sai ƙarar na’urorin monitoring machine ne kawai ke bugawa cikin natsuwa beep… beep… beep… Fitilun farare na asibitin suna haska jikin Yarima Asad wanda yake kwance, fuskar sa ciƙin rauni.

Cikin awanni biyu da suka wuce, jikin nasa ya kara sake rikicewa. Maganin bacci da Dr. Khalid ya sa masa bai yi tasiri ba. Sai zuciyarsa ke bugawa da sauri, numfashinsa yana ɗagawa kamar wanda ke neman numfashin.. “Ramlah…”

“Don’t cry… please…” Muryarsa ta fito da sanyi, kamar yana magana cikin mafarki.

Dr. Khalid da ke tsaye a gefe ya tsaya cak, yana kallon monitor ɗin zuciyarsa “Strange,” ya furta a hankali. “ Yakamata ranki yadade Ramlah ta dawo kusa dashi ta kula dashi duk da asubutin nan baa jinya but yana bukatar ta He’s reacting emotionally… not physically.”

A gefe,Mamy wacce takasance babbar yaya ga Asad tana zaune bankalinsu duk atashe Hajja ta zauna, hannunta a kirji, idanunta cike da hawaye. Mamy ce ta miƙe Tace cikin muryar da ta cika da damuwa “ hajja lafiya lou ko jiya? Amma yanzu jikinsa… yakara rikicewa.” Dr. Nahla , wacce ke taimaka wa Dr. Khalid, ta matsa kusa. “Zuciyarsa tana yin irregular rhythm, Your Highness. Maganin ya kamata ya kwantar da shi, amma kamar wani abu ke motsa masa jiki daga ciki mun rasa gane komai .” Hajja ta dafa hannun ɗanta da ke gefe Abba, wanda shi ne ɗan uwan Asad, ya kalli likitan da firgici a fuskarsa “Doctor, idan haka ne, yakamata mu fitar da shi daga nan. Mu kai shi abroad.”

Amma kafin Dr. Khalid ya amsa, ƙofar ta buɗe Hakimi wambai da waziri da mai martaba abayan su suka shigo Mai Martaba Babangida III. Sanye yake da farar Agbada royal da rawani mai launin azurfa, fuskar sa cike da damuwa karara. Ya tsaya bakin gadon ɗan nasa, ya kalli Asad na numfashi cikin wahala. Cikin natsuwa ya juyo ga likitocin.

“What happened? Bayan kacemum zaayi sallama tun shekaran jiya yaya jiƙin nasa yanzu.”

Dr. Khalid ya duƙa cikin ladabi. “Ranka yadade, ba gubar ce ba yanzu don jiyama sunyi gwaji munga babu amma yau da safe sai muka samu jikim yakara rikcewa kuma binciken mu ya nuna gubar na nan ajiƙinsa shine muka kara yimasa abunda zai fitar da’ita ga numfashinsa dake barazana.”

Wambai ne yace “ Abba ashirya flight yanzu.” Hajja ta saukar da numfashinta tana godiya. Idanun Sarki suka motsa yana kallon wambai. “ Da izinin wa? Me asubutin nan suka gaza?” Hajja ta ɗago kai cikin mamaki, ta haɗa idanu da mijinta. Sai da ya ja numfashi mai nauyi kafin yace da ƙarfi “Ku, kwantar da hankalinku. Lafiya ta Allah ce mu basu dama idan suka gaza nan da 5days sai a fitar dashi.

A barshi anan, kar kowa ya kuskura ya motsa shi ko ya fitar dashi daga asibitin nan.” “Amma Mai Martaba,” Hajja ta ce, muryarta na rawa.

“Bangane ba. To zaa barshi da wannan larura ne? Ka gani da idonka jikinsa na rikicewa…”

Wambai ya kalli mahaifinsa da girmamawa, amma ya kasa ɓoye damuwarsa. “hajja tana da gaskiya. Gubar nan ta fara fitowa da ciwo, yanzu zuciyarsa ce ke wahala. Ai mu shirya flight yanzu mu kai shi waje, ko Dubai ko London, kafin lokaci ya kure.”

Sai Sarki ya juya ya dafa kafaɗar ɗansa da damuwa Ya ce da murya mai cike da iko da ƙwazo “Na ce aa!

A barshi anan.” Kallon mamaki suka yi masa gaba ɗaya Dr. Khalid, Abba, har Hajja.

Ya ci gaba da magana cikin nutsuwa. “Ba inda za a kai shi. Na san abinda nake faɗi.

Abokim hamayyarsa zasu samu dama akansa amma yanzu fa? Babu wanda yasani.”

Ya juya, ya fita a hankali tare da Waziri a bayansa, yana barin dakin cikin natsuwa amma zuciyarsa cike da ɗumbin damuwa.

Hajja ta tsaya tana kallon ƙofar da aka rufe, tana furta “Ya Allah… kabashi lafiya.”

*********

Gimbiya Maryam tana tsaye tana kallon windon upper balcony. Fuskarta ta yi kaca-kaca da kishi da haushi. Da bakin cikin rashin samun nasararta kwatakwata

Ta kalli Waziri da ke tsaye a bayanta, tana magana cikin ƙasa-ƙasa “Waziri, kagani kuwa? Wannan yarinyar tana samun kulawa sosai. Ko da Asad yana asibiti, duk wanda ya shigo fada yanzu sai ya nemi ganin Ramlah yau kwananta Biyar agidan nan amma kaga yadda sarki ke kula da’ita.”

Waziri ya murmusa cikin mugunta, yana gyara babbar rigarsa. “Ki kwantar da hankalinki, Gimbiya. Asad ba zai taɓa warkewa ba ina tabbatar miki sai dai kiji labarin mutuwarsa.”

Gimbiya Maryam ta ɗago da mamakWaziri, me kake nufi?”Ya ƙaraso kusa da ita cikin natsuwa “Yanzu dai komai yana tafiya yadda muke so. Dazu da asuba na sake je wa asibitin, na saka masa ƙarin sinadarin gubar cikin ruwan da suke bashi. Kinsan har yanzu yana cikin wani hali baisan ma wa yake kansa ba kwana biyu yayi a Icu mai martaba yace a fiddashi abarshi a dakinsa.Babu wanda ya gane saboda na shigar da shi cikin kayan detox injection.”

Idanunta suka buɗe cikin mamaki da farin ciki. “Kana nufin yanzu…” “Eh,” Waziri ya katse ta yana dariya mai sanyi. “A kwanaki biyu zuwa uku, jikinsa zai sake tsanani. Na kuma zuga Mai Martaba cewa kada a kai shi waje saboda abokan hamayya zasuyi dariya.

Ya yarda. Da maganata.”

Maryam ta yi dariya mai sanyi, tana ɗaga hannunta ta dafe ƙirjinta. “Kai Waziri… wannan labarin naka daɗinsa kamar zuma yake. Na ji daɗi, sosai da sosai.”

Sai ta juya cikin natsuwa, ta bar falon, ƙamshin turaren mulki na binta.

A bayanta, Waziri yana murmushi cikin mugunta yana jin daɗin yadda makircinsa ke tafiya cikin santsi kamar ruwa mai sanyi.

****

Ranar ta biyo juna kamar yadda rana ke bin wata. Duk da ni a gidan sarauta nake, rayuwa ta ba ta da sauƙi. Kowace rana akwai sabuwar magana, sabuwar fassara, sabuwar sirri da ake ƙoƙarin ɓoye shi a bayan murmushi.

Da sassafe na tashi bayan na idar da sallah, sai na zauna a gefen gadona ina tunanin yadda rayuwa ta juya cikin lokaci kaɗan. Na tuna lokacin da nake a gida, ina cin tuwo da hannuna, ina dariya da Momy a kicin, babu mai umarni sai ni da zuciyata.

Yanzu kuma? Har motsin ƙafata sai an tambaya.

Ina cikin wannan tunanin ne aka kwankwasa ƙofa.

“Ranki ya daɗe,” muryar Uwar Amarya ce mai taushi, da nutsuwa, “Shigo, Uwar Amarya,” na ce ina gyara zaman hijabina.

Ta shigo da tray a hannunta akwai madara, zuma, da nono. Ta durƙusa ta ce, “Hajja ta aiko, ta ce kin sha wannan bayan kintashi.”

Na karɓa da godiya,

Rayuwa a cikin gidan sarauta ba kamar yadda mutane ke zato take ba. Kowa na tunanin da zarar kika shiga gidan sarki, to komai zai zama jin daɗi, kwalliya da alfahari. Amma gaskiyar magana, wata sarkakkiya ce, mai wahalar fassara. Tun da na shigo gidan nan yau kusan kwana shida kenan, amma ban taka ƙofar waje ba. Komai sai da izini, komai sai da yardar mai martaba ko kuma Hajja.

Kulawa kuwa? Ana kulawa da ni sosai, fiye da yadda zan iya tunani. Ba ni da abin yi sai bacci da kallo. Har takalmina da nake sawa sai Uwar Amarya ta ce ita za ta cire min. Na rasa yadda zan ji, kunya ce ta mamaye ni. Na kan ce mata, “Dan Allah, Uwar Amarya, ki bar ni in cire kaina. Ni ina ganin wannan girman ya yi yawa.”

Sai ta murmusa ta ce, “Ranki ya daɗe, ni da kaina zan cire miki. Ai wannan al’ada ce a gidan sarauta.”

Nana hadiza

09030569336

[28/10, 8:41 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

*****

Na kasa cewa komai, amma zuciyata ta cika da mamaki.

Kwana biyu kenan zuciyata ke cikin damuwa. Gidansa Nake amma shi yana kwance a asibiti. Ban san halin da yake ciki ba, ban kuma san yadda jikinsa yake ba. Sauran matan sarki kuwa suna nan kowanne a shashinsa. Kusan kullum uwar amarya sai tacemun Hajja yanzu tana asibiti tare da shi.

Sai ‘yar uwarsa Firdausi, wacce nake kira Gimbiya Fiddy, ke yawan shigowa wajena. Kyakkyawa ce sosai, yar gayu, kullum cikin gayu.. Ita ce ke sanyaya min rai da hira. Haka na ke wuni hira da ita, ina yawan kiran Momy, da Yaya Aliya, da kuma Abbana a waya domin gaisawa.

Da rana ina zaune a falona ina kallon shirye-shirye a talabijin, sai ga Uwar Amarya ta shigo. Ta ce, “Ranki ya daɗe, sannu da hutawa.” Ta zauna a kasa kusa da ni. Na kalli kujerar gabana na ce, “Dan Allah, ki dinga zama kan kujera fa, ba nason naganki a sama kina uwata koma nace kakara ki zaune kasa haka.”

Sai ta yi murmushi ta ce, “Ranki ya daɗe, wacece ni? Bar ni nan. Kujera ai na masu daraja ce.”

Kafin mu gama magana, sai ga wasu ‘yan mata sun shigo. Sun kawo flask ɗin shayi, fruits da snacks. Sun durƙusa, suka ajiye a centre table. Sunyi gaisuwa cikin ladabi. Kunya ta lullube ni, zuciyata ta yi nauyi.

Uwar Amarya ta zuba komai a faranti ta miko min tana karayi min kirari kamar yadda ake a gidan sarauta. Kuka ne kawai ban yi ba. Na ji kamar ina zaune a wani wuri da ba ni ba ce ba.

Na ɗan numfasa nace, “Uwar Amarya, tun da na shigo gidan nan ban ga Hajja ba. Me yasa?”

Ta ce, “Ranki ya daɗe, ai sai da izini ake zuwa wurinta. Idan tana son ganinki, za ta aiko.”

Na daure nace, “To, amma shi fa? Kin ji labarinsa?”

Sai ta jinjina kai ta ce, “Eh, amma kin san irin wannan magana fa ba a yarda da tana yawo a gidan sarauta na . Amma jiya, ina cikin girki, na ji Gimbiya Firdausi tana gaya wa yarinyarta Nawal cewa jikinsa bai da sauƙi. Nasan suna hanyar zuwa .”

Na ce da ita cikin murya mai rauni, “Dan Allah, inason in ganshi. Ko na dan tsaya kusa dashi ne bansan halin da yake ciki ba duk na damu..”

Sai ta ce, “Ranki ya daɗe, sai da izinin mai martaba . Ai ba wanda ke fita ko shiga wurin shi sai da umarni.”

Na lumshe ido nace, “Allah ya ba shi lafiya.” Amma zuciyata ta cika da tunani. A zahiri, ana kulawa da ni kamar sarauniya, amma a zuciya, ina jin ni tamkar ajiye ni aka yi.

Uwar Amarya ta kalle ni ta ce, “Kin san komai a gidan nan sai da izini fa. Bama shi mai gidan naki da bayason mulki ko kadan.Ai ba mai son rigimar sarauta bane. Yana son zaman lafiya sosai.shi mai martaba ne ya tsananta akan lallai lallai, sai ya dawo kusa da shi.”

Na ce, “To amma shi mijina baya son sarauta gaba ɗaya kenan?”

Ta ce, “Babu abin da ya tsana irin sarauta. Bai son abubuwan dake tattare da ita rashin sirri, dogon al’ada, da girman kai. Amma kin san sarauta ba a tserewa idan jinin ka ne.”

Na yi shiru. Na ji kamar wani abu mai nauyi ya sauka a zuciyata. A waje, ana ganin kamar rayuwar gidan sarauta cike take da jin dadi, amma a gaskiya tana da nauyin da ba kowa zai iya ɗauka ba.

Asad shi ne ɗa na huɗu a gidan mai martaba, ɗan da kowa ke gani kamar sanyi a cikin rana. Yana da kyau, nutsuwa, da halin kirki. Ba ya magana da yawa, amma idan ya yi magana, sai kowa ya saurara. Yayunsa mata biyu da maza biyu ne suka rigaye shi, amma shi kadai ya fi shahara saboda natsuwarsa da arzikin da Allah ya bashi.

A gidan mai martaba, kowa ya san cewa Asad ya bambanta. Ba ya shiga harkar mulki sosai, bai son fitowa fili, amma kowane ɗan siyasa, attajiri, da mai kudi na neman taimakonsa. Allah yabashi arzukj sosai . Hajja, mahaifiyar sa, mace ce mai hali nagari, amma asalin ta ba jinin sarauta bace. Mahaifinta tsohon dan kasuwane a kasar waje ne wanda ke da suna wajen hada hadan kasuwanci Lokacin da mai martaba ya hadu da ita a wani tafiya zuwa can kasarsu, soyayya ta shiga tsakaninsu kamar me. Duk wani ƙa’ida ta fadar sarauta ta tsaya cik, saboda sarki ya nace sai ya aureta.

Shi ne dalilin da yasa wasu daga cikin manyan gidan suka tsaneta musamman Waziri da Gimbiya Maryam.

Suna ganin ba ta dace da sarauta ba, amma sarki ya tsaya akan kalmar sa “Wanda Allah ya nufa da daraja, ba asali ke hana shi ba.”

Hajja ta rayu cikin tawali’u da nutsuwa. Bata taɓa amfani da matsayin ta don girman kai ba. Ta fi son zaman lafiya da alheri ga kowa.

Mutane suna fadin, “Asad irin halin mahaifiyarsa ya gado.”

Aliya ita ce farin cikin farko a rayuwar Asad.

‘Yar siririya ce, mai hankali da natsuwa, bata son hayaniya. Soyayyarsu ta kasance ta biyayyar iyaye don mahaifinta shima dan sarauta ne . Sai dai bayan haihuwar ɗansu Umar, kaddara ta raba su. Aliya ta rasu a lokacin haihuwa. Asad ya rikice sosai.

Rashin Aliya ya bar masa rauni.Sai ya tafi Dubai tare da ɗansa, inda ya sayi gida ya bar mahaifiyar Aliya ta kula da shi.

Ayshatu ita ce ɗiyar baiwar da take aiki a gidan mai martaba, ‘yar kyakkyawa mai takama da isa gashi batada kirki ko daya ga wulakanci sosai Asad bai taba tsammanin zai so ta ba. Amma soyayya ba ta tambayi matsayin mutum. A hankali, sai ya fara lura da yadda take da kulawa, yadda take taimaka masa da kuma irin soyayyar datake masa.

Kowa ya ji daɗi da jin cewa ɗan mai martaba ya auri ‘yar baiwa saboda kauna, ba don matsayin ta ba.

Sun haifi yara biyu Nawal da Amina.

Yara masu hankali, masu tarbiya . Nawal lawyer ce, Amina kuma ta shiga harkar kasuwanci.vTun suna ƙanana, Asad ya tura su Dubai wajen Umar, ɗan sa na farko, domin su girma tare. Kowa cewa yake idan ka gan su uku Umar, Nawal da Amina sai ka rantse ɗaya uwa ce ta haife su daga karshe ma sai adinga tunanin ko mahaifinsu ne.

Amma daga baya, soyayyar Asad da Ayshatu ta fara dusashewa. Ba saboda rikici ba, sai dai saboda sirrin da babu wanda ya sani.

Wasu na cewa Hajja bata so wannan auren, wasu kuma suna cewa Asad ne ya fara nisanta da ita saboda wani abu da ya faru tsakanin su wanda bai taɓa faɗawa kowa ba wasu sunce bashida da lafiya ne.

Numfashi naja nace “ Tana ina yanzu?”

Ayshatu ta bar gidan sarauta. Ta sake aure wasu sunce ma abokinsa ta aura.Kalmar da ta fito daga bakin Uwar Amarya ta tsaya a kunnena har bayan ta gama magana.

“Ki ninka addu’arki, ranki ya daɗe…” ta faɗa cikin nutsuwa, amma muryarta tana da nauyi.

Na tsaya ina kallonta, zuciyata tana bugawa.

Ta gyara zamanta a ƙasa, ta ɗaga ido cikin ladabi ta ce, “Na san da yawa a cikin gidan nan basa farin ciki da auren nan. Amma ki kwantar da hankalinki. Sarauta tana da nata ƙa’idoji. A nan, ki yi magana kadan, ki yi addu’a da yawa. Gidan nan, kowa na da ido, amma ba kowa ne ke da zuciya ba.”

Na lumshe ido na dan murmusa cikin damuwa.

“Na gode Uwar Amarya. Amma wallahi bana jin daɗi. Na shigo gidan nan Gashi shi yana asibiti, ban san halin da yake ciki ba. Kuma yaran sa ma, har yanzu ban gansu ba.”

Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi.

“To gaskiya, ranki ya daɗe, yaran ba su zo ba saboda ba su samu damar zuwa ba. Idan an hana a sanar dasu, Amma ni na tabbata idan sun ji labari. zasu zo insha Allah.”

Na ɗaga kai cikin tausayi, na ce da karfin hali, “Allah yasa.”

Kafin mu kai ƙarshe a maganar, sai ga ƙarar takun ƙafafu yammata biyu ne suka shigo da sallama , sanye da uniform mai fari da ruwan dorawa, fuskokinsu cikin murmushi na girmamawa. Duk suka durƙusa sukace cikin ladabi “Ranki ya daɗe, Matan Yarima Abba da Yarima Muttaqa suna neman izinin ganawa dake. Sun zo su gaisheki.”

Na kalle su cikin natsuwa, zuciyata ta yi wani irin bugu. Ban san me yasa kalmar “Matan Yarima” ta cika min kai da nauyi ba. Na ce cikin sanyi “To ai babu matsala. Ku ce su shigo mana.”

Amma kafin kalmomi su fito daga bakina gaba ɗaya, sai Uwar Amarya ta yi saurin magana “Aa, ranki ya daɗe. Ba haka ake cewa ba.”

Nana hadiza

09030569336

[29/10, 7:13 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN DA TAKWAS

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Na tsaya cak, ina kallonta.

Ta dan matsa kusa da ni, muryarta ta sauya zuwa irin da ladabi amma mai cike da umarni.

“Ki ce musu ‘Tana gaisuwa sosai gare su, kuma tana maraba da zuwansu cikin gidanta mai albarka.’”

Na kasa cewa komai, sai dai na zuba mata ido cikin mamaki. Ta ɗan murmusa kamar wacce ta san tunanina, ta ce “A gidan nan, magana tana da matsayi. Ba komai ake cewa kai tsaye ba. Duk wata magana tana da hanyar da ake furtawa. Ki koya hakan, ranki ya daɗe.”

Na sauke numfashi cikin sanyi.

Zuciyata ta cika da mamaki da girmamawa lokaci ɗaya. “To Uwar Amarya, ashe har gaisuwa ma akwai dokarta?” Ta yi dariya kadan, ta ce, “Eh mana. A gidan mai martaba, komai yana da doka. Gaisuwa ma tana da iyaka. Zaki fahimta a hankali.” Na jinjina kai, amma zuciyata tana magana da kanta Wannan rayuwar sarauta, kamar rayuwa ce ta cikin madubi komai yana da nuni.Ƴammatan suka tsaya suna jira a ƙasa, ba tare da sun ɗago kai ba. Sai na ce cikin murya mai laushi kamar yadda aka koya min, “Tana gaisuwa sosai gare su, kuma tana maraba da zuwansu cikin gidanta mai albarka.” Uwar Amarya ta murmusa cikin jin daɗi, ta ce, “Haka ake magana. Allah ya ƙara miki basira.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull