Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 26
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 26: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 26. Ƴammatan suka fice cikin ladabi, su ma suna cewa, “Allah ya kara…
4,474 words
Ƴammatan suka fice cikin ladabi, su ma suna cewa, “Allah ya kara miki lafiya saƙonki zai isa garesu .” Na tsaya ina bin su da kallo har suka bace a ƙofar falon. Uwar Amarya ta mike tsaye, ta gyara mayafinta, ta kalle ni cikin ido. “Ranki ya daɗe, kar ki manta. A nan, kalma ɗaya tana iya ɗaga mutum, ta kuma iya rusa shi. Sarauta tana da kyau, amma tana da tsanani. Idan kika saba da dokokin gidan nan, to sai kowa ya girmameki. Amma idan kika yi kuskure, ko magana ɗaya, sai ki ji an yi shiru, amma an gama miki hukunci.” Nadaga mata kai bance komai ba.
Tunda na ji hayaniyar gaisuwa daga babban falon, na san cewa ba kowa bane wannan irin murya da ladabi, sai mata masu sarauta
Muryar Uwar Amarya ce ta fara bayyana daga nesa “Takawarku lafiya, matan yarima! Allah ya ƙara muku lafiya!”
Sai na ji wata daga cikin murya masu sanyi ta amsa da ladabi, “Amin, Uwar Amarya. Matan Yarima Abba da Matan Yarima Muttaqa suna sallama ga matar Yarima Asad. Suna gaisuwa gareta, suna kuma neman izinin shigowa.”
Na ji zuciyata ta dan buga. Ban saba da irin wannan salon gaisuwa ba. Na so in ce, “Ku shigo mana,” amma kafin na buɗe baki, Uwar Amarya ta riga ni da magana.
“Matar Yarima ta amince, ta karɓi gaisuwarku, tana muku maraba da zuwanku cikin fadarta mai albarka.” Na tsaya na zuba mata ido, jikina ya yi sanyi. Na kasa cewa komai, sai kawai na ji kamar nayi dariya ko kuka lokaci guda.
Sannan ta juya gare ni “Ranki ya daɗe, idan za ki karɓi baki a gidan sarauta, ba ke za ki fita ki musu sallama ba. Su ne zasu shigo su taddaki. Dole ki nuna sarautarki.”
Na ji kamar zuciyata ta tsaya.
Na ce cikin ɗan rawar murya, “Bangane ba, Uwar Amarya…”
Ta murmusa kadan, “Ki zauna, ranki ya daɗe. Su zasuzo su taddake, ba ke za ki tashi ba.”
Na sauke numfashi cikin nutsuwa, na ji hawaye suna son fitowa saboda kunya da rashin fahimtar wannan tsarin. Wannan gidan dai ya banbanta da komai da na saba…
Kafin in kara magana, sai wani irin ƙamshi mai daɗi ya cika falon. Na kalli ƙofar ga su sun shigo.
Su matan Yarima biyu ne, kowacce a cikin farin zani, sun sha ɗaure da mayafi .
Suna tafiya da wani isa da izzah kamar basa son su taka kasa sosai.Fuskokinsu cike da kwalliya, hannayensu na ɗauke da zobba masu kyan gaske.
Da suka ƙaraso bakin falon, sai suka tsaya cikin ladabi, suka ce da murya mai laushi “Matar Yarima, Muna taya ki murna da wannan babban matsayi.”
Na murmusa cikin jin kunya, na ce, “Sannunku fa da zuwa, ya hanya?”
Sun dan murmusa, amma kafin su amsa, sai na ji muryar Uwar Amarya ta ɗan tashi cikin ladabi “Matar Yarima tana gaisuwa sosai gareku, tana kuma maraba da zuwanku cikin fadarta mai albarka.”
Sai na ji sunce, “Allah ya raya ranki, muna godiya.”
Kamar wasan kwaikwayo, kowanne kalma tana da izini. Na ji kamar in tashi in kawo musu ruwa saboda kunya”
Sai na mike cikin gaggawa na ce, “Bari a kawo muku ruwa, don kunada gajiya.”
Kafin in fita gaba ɗaya, Uwar Amarya ta bi ni da sauri har zuwa kicin. Ta rike hannuna a hankali, “Ranki ya daɗe, ki tsaya. Wani ruwa za ki kai musu? Gidan sarauta ba haka yake ba.” Na tsaya cak, na kalle ta cikin mamaki.
“Amma su baki ne fa…” Ta girgiza kai. “A’a, ranki ya daɗe. Ba ke za ki kai ruwa ba. Wannan aikin bayi ne. Ki tsaya ki jira, su zasu kawo musu abin sha. Idan kika tashi kika fara yin hakan, suna nan za su dauka baki san matsayinki ba. Wannan sarauta ce, ba gida na talakawa ba.”
Na tsaya na rasa abin cewa.
Zuciyata ta fara yin wani irin nauyi.
Na ce cikin murya mai rauni, “Uwar Amarya, wallahi bana jin daɗin irin wannan girmamawar. Ni dai mutum ne kamar su, me yasa sai anyi haka?”
“Ranki ya daɗe. Wannan ba girmamawa bane, doka ce. Idan kika yi ƙasa da matsayin ki, sarauta zata yi miki sama da kima. Ki kiyaye.”
Na yi shiru, saboda kalmarta ta tsaya a zuciyata. Na dawo daga kicin din ina jin kamar na koyi sabon darasi darasin da bai da suna, amma ya daɗe yana tafiya cikin gidan nan.
Na koma falon, sai na tarar da matan Yarima suna zaune cikin natsuwa, suna hira da murya ƙasa kamar ana koyon karatun ladabi.
Na zauna a gefen kujera, Uwar Amarya tana tsaye a gefe kamar jami’ar tsaro .
Daya daga cikin matan yariman ta ce da murmushi “Mun ji labarinki sosai, Matar Yarima. Kowa yana maganar ki mukace bari mu zo muyu gaisuwa..”
Na murmusa cikin jin kunya, “Allah ya saka da alheri.” Sai suka sake kallon juna, ɗayan ta ce, “Za mu iya ganin Yarima insha Allah? Mun ji yana jinya.” Na ce, “Ina fatan haka, amma yanzu yana hutu.” Suna cikin magana sai Uwar Amarya ta kara cewa, “Mai martaba ne ke da ikon sanarwa. Idan lokaci ya yi, za ku gan shi.”
Sun gyada kai cikin natsuwa.
Da suka tashi suka yi sallama, s “Allah ya kare ki, Matar Yarima.” Na amsa da murmushi, amma Uwar Amarya ce ta karasa musu amsar “Mai martaba da Matar Yarima suna muku godiya.”
Da suka fita, na ja numfashi mai nauyi.
Na ce a hankali: “Uwar Amarya, wannan gidan nan... kamar coci yake, komai da tsari da ladabi.”
Ta yi dariya kadan ta ce, “Eh, ranki ya daɗe.
Na kalli ƙofar da matan suka fita, zuciyata cike da tunani.Na sunkuyar da kai cikin ladabi, na ce “Na fahimta.” “Haka ake koyon sarauta, ranki yadaɗeDaga kuskure ake koyo.
Amma kar ki sake yin magana da kalmar da zata nuna girma fiye da wadda ake nufi.
Domin a nan, koda dariya tana da iyaka.”
Na murmusa cikin girmamawa, amma zuciyata tana wani irin motsi
“To Uwar Amarya, kiyi haƙuri da ni. Zan yi ƙoƙarin koyon komai a hankali.”
Ta ce cikin murmushi
“Zan koya miki, ranki ya daɗe.
Nana hadiza
09030569336
[29/10, 7:15 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SITTIN DA TARA
Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
BiA mugun firgice na farka daga baccin da nake yi. Kukan da nake yi a mafarkin bai gama yankewa daga zuciyata ba har yanzu ina jin shi a kunne na.Na buɗe idona da sauri, jikina duk ya yi zufa, numfashina yana fita kamar wacce tayi gudu. Na kama kirjina da hannuwana biyu, na fara karanta addu’ar da ake karantawa idan an yi mugun mafarki “A’uzu billahi minash shaidanir rajim. Allahumma inni a’uzu bika min sharri ma ra’aytu.” Na maimaita sau da dama, amma har yanzu zuciyata na bugawa. Wannan mafarkin daban yake kamar gaske ne.
Na ji kamar na ga wani mutum yana ƙoƙarin kashe Yarima Asad, yana zuba abu acikin wani abu, shi kuma a ƙasa yake, yana ƙoƙarin kare kansa amma jikinsa babu ƙarfi.
Na girgiza kaina da sauri, hawaye suka cika ido. “Allah ka tsare shi,” na furta cikin muryar da ke rawa. Na zame bargon jikina, na tashi tsaye cikin sauri. Hasken dakin yana da rauni, sai kawai na miƙa hannu na danna madannin fitila a gefen gado. Fitila ta kunna, haske ya mamaye dakin gaba ɗaya. Na lumshe ido cikin tsoro saboda har yanzu ina jin kamar mafarkin yana ci gaba a zahiri.
Na nufi bandaki cikin rawar jiki, ina maimaita “La ilaha illa Allah” kamar wacce ta tsorata da wani abu da idanu ba su gani ba. Na wanke fuskata, nayi tsarki gaba ɗaya, sannan na yi alwala. Na fita zuwa dakin, na ɗauko daddumar sallah na shimfiɗa, na taɗa sallah cikin nutsuwa.
Na tsaya na ɗauki lokaci mai tsawo, zuciyata cike da fargaba, amma kalmomin sallah suna ratsa ni kamar ruwa mai sanyi. Bayan na idar, sai na zauna ina karanta Suratul Yaseen, hawaye suna zuba a hankali. Bayan na gama, sai na jingina da gadon, na ɗan lumshe ido wahalallen bacci ya kwasheni.
Sai mugun mafarkin ya dawo min kai tsaye wannan karon ma fiye da da.Na ga Yarima Asad, yana cikin duhu, yana kiran sunana cikin rauni. Na farka cikin kidima, na riƙe kirjina da sauri, ina maimaita, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah ka tsare shi!”
Na kasa zama. Na miƙe tsaye, na fara yawo cikin daki, numfashina yana fita da sauri.
“Me yake nufi wannan mafarki?”
“Shin akwai wani abu da zai faru da shi?”
“Ko dai hakan yana nufin shima mutuwa zaiyi ya barni?”
Tambayoyi ne suke yawo a zuciyataNa tsaya na ɗan jingina da bango, na ɗora hannuna a kirji, ina jin wani irin nauyi a cikina.
Zuciyata tana bugawa da sauri kamar ana tsoratar da ita.
Na juya na kalli kofar daki, sai hasken fitilar ke sake bayyana bango da labulen da iska ke motsawa a hankali. Na nufi gefen gado, na zauna, na ɗora kaina a kan gwiwata, na cigaba da ambaton Allah. “Subhanallah... Alhamdulillah... Astaghfirullah... Allah ka tsare ni, ka tsare shi.” A cikin wannan zikiri, na ji kamar zuciyata tana sanyi a hankali.
Na koma kan dadduma, na sake shinfida, na ɗaga hannuwa sama cikin nutsuwa, na ce cikin kuka “Ya Allah, idan wannan mafarki wani alamar ne, to Ka juyar da sharri zuwa alheri. Ka ba shi lafiya, ka ƙara masa ƙarfi, ka tsare shi daga makiya da asirai.
Ka bani ikon zama mata tagari gare shi.
Allah ka bani haƙuri, ka tsare zuciyata daga tsoro.” Na yi addu’a sosai har hawaye suka ƙafe, zuciyata ta samu natsuwa kadan.
Na kwanta, amma bacci bai dawo ba sai dai tunani. Na tuna duk abin da ya faru da ni tun shigowata gidan sarauta Dokoki, ladabi, iyaka a kowane abu… amma yanzu babu wani abu da yake da muhimmanci fiye da rayuwar Yarima Asad. Na lumshe ido a hankali, amma zuciyata tana magana kai tsaye.
“Allah ka kiyaye shi. Kada ka sake barin wani ya cutar da shi. Idan mafarki gaskiya ne, to ka juya shi cikin kariya.”
Ban san lokacin da bacci ya sake dauke ni ba, amma sai da na ji ana kira sallar Asuba daga masallacin cikin fadar. Na tashi, na sake yin alwala, sannan na yi sallah cikin nutsuwa da hawaye Bayan na idar, na zauna na jingina da bango, na ce da zuciyata cikin murya mai rauni “ Wato Rayuwa a gidan sarauta... ta koya min abu guda Koda kina cikin zinariya, sai addu’a ta zama suturarki.” Sai na lumshe ido, na sake kiran sunan Allah cikin zuciya.
Ina ƙoƙarin komawa bacci sai ga door bell tana ta kara. Na buɗe ido cikin kasala, na dubi agogo, sai na tuna ban je gym ɗin da aka ce Hajja ta umarta ba. Da sauri na miƙe, na shiga bandaki, na yi brush, na fito na saka kayan training ɗina.
Tun ranar farko da na shigo gidan nan, an ce duk safiya sai na tafi motsa jiki a sashena kowacce matar yarima da matan sarkin sunada daƙin motsa jiki asashen su kamar yadda uwar amarya tafada. Na tuna ranar farko da naje, yadda nasha wahala har na kasa taka ƙafata daga baya saboda yadda sukayi tsami sosai wajen motsa jiki to bayi nakeyi ba Amma cikin kwanaki uku nasama sosai har yazama banajin zafin kwata kwata.
jikina ina jin daɗinsa sosai wato haɗuwar gurin kamar wanda nake gami a tv ne kuma ina gamawa baiwaf dake sashen zata haɗamun protein shake ta bani nasha.
Na gama motsa jiki na tsawon mintuna talatin, sai na fita zuwa babban sashen. Mutanen da nake ganinsu suna tsoron gurin sai gaidani suke yi, wasu ma har tsugunnawa suke idan na wuce. Na ji kunya sosai, amma ban ce komai ba. Na shige sashenmu.
Na nufi kitchen, sai naga Uwar Amarya tana duba abinci. Na gaidata cikin ladabi, ta amsa tana murmushi. “Ranki ya daɗe, akwai wani abu da kike bukata ne?”
Na ce, “Aa, kawai dai inason nayi aiki tare da ku.” Ta girgiza kai cikin nutsuwa, ta ce
“Ranki ya daɗe, hakan bai kamata ba. Aikinmu ne mu kula da ke, ba ke ba. Ki zauna ki huta. Abinda muke bukata daga gareki shine ki bada umarni, mu aiwatar.”
Na jijjiga kai cikin kunya, na fita.
Cikin raina inata masifa. “Daga kwanciya sai kallo, babu abin da zan yi.”
Na cire kayan jikina, na kwanta saboda bacci nake ji. Amma cikin bacci ma saj da nasakeyin mafarkin na tashi cikin firgici, jikina yana rawa. Ban san daga ina ihun ya fito ba, amma zuciyata ta fara tsoro. Na tsaya a tsaye, numfashina yana fita da sauri.
Na fara addu’a, amma kalmar bata fito daidai ba saboda rawar murya. Na dafa kirjina cikin rawar jiki, na ce “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Na shiga bandaki, nayi wanka Kafin na fito, sai ga Uwar Amarya ta kawo kayan da zan saka wata alkyabba ce ja mai kyalli, tana kamshi da turaruka masu daɗin da ban taɓa sani ba. Na saka kayan, na kalli kaina a madubi, Nayi kyau sosai.
Na fito zuwa falon, Uwar Amarya ta gaisheni, ta gyara zamanta. Na zauna a dinning, ta zubamin tea mai ɗumi.
Sai na ji jikina babu kuzari, kamar na yi wahala sosai. Na sha kaɗan, sai ta kalleni cikin damuwa“Ranki ya daɗe, lafiya kuwa? Naga jikinki kamar babu ƙarfi.”
Na kalleta cikin mamaki yaya take gane canjin jikina ko da bai fito fili ba?
Cikin sanyi nace, “Ina jin kamar bana da lafiya sosai... inason ganin Yarima Asad.”
Ta jinjina kai cikin ladabi, ta ce “Allah ya taimakeki. Bayan kin gama cin abinci, Hajja ta bada izinin a kaiki wurin ta.”
Na amsa da “To,” cikin sanyi.
Ban ƙara cin komai ba, na tashi.
Bayan wasu mintuna, muka nufi sashen Hajja.
Motar da ta ɗauke ni daban take ba irin ta baya ba har nakasa gane adadin motocin gidan nan.
Da muka isa, wasu bayi suka buɗe ƙofa, suka fara gaisuwa da ladabi. Na ji kunya sosai. Saboda Allah wasun sun haife ka ko suyi jika da kai. Suka ce, “Ranki ya daɗe, barka da zuwa.” Na amsa cikin murya mai taushi.
Suka raka ni zuwa babban sashen Hajja.
A can suka ce“Tana cikin ɗaki, ta ce a shigo.”
Na tsaya da mamaki domin Uwar Amarya ta faɗa min cewa babu mai shiga wurinta sai ‘ya’yanta da matan da ta amince da su.
Zuciyata ta dinga bugawa yayin da nake taka ƙafata cikin ɗakin.
Da na shiga, sai ƙamshi ya cika hanci na.
Kamshi mai daɗi, wanda yake haɗe da turaren wuta da airfresh na. Na tsugunna har ƙasa bakin gadonta, na ce “Barka da hutawa, Allah ya ƙara miki lafiya, ranki ya daɗe.”
Ta yi murmushi, fuskar ta cike da natsuwa, amma akwai alamun damuwa. “Tashi Ramlatu,” ta ce da murya mai sanyi, amma cike da iko.“Ina fatan kinajin daɗin fadar taki?”
Na sunkuyar da kai cikin ladabi, na ce “Tabbas, ranki ya daɗe.”
Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi. “Kiyi haƙuri, Ramlatu. Kin shigo cikin gidan sarauta a lokacin da mijinki ke cikin jarabawa.
Har yanzu jikin sa ba daidai ba ne.
Jiya ma sai da muka kwana dashi muna roƙon Allah.Amma mai martaba ya hana mu fitar da shi daga asibiti. Ina roƙonki, kidinga yimasa addu’a sosai.”
Na ji hawaye sun cika idona.
Cikin rawar murya na ce“Ranki ya daɗe... dan Allah... zan iya ganinsa ne?”
Nana hadiza
09030569336
[30/10, 12:29 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Ta ɗan yi murmushi, duk da fuskar ta cike da damuwa. “Yanzu zaki tafi wurinsa, kamar yadda mai martaba ya bada izini.
Amma ba zaki kwana ba. Kullum za ki je, ki dawo. Wannan ita ce umarnin sarki.”
Na sunkuyar da kai cikin ladabi. “Nagode sosai, ranki ya daɗe. Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai.”
Ta ɗaga hannunta ta shafi kaina, ta ce cikin kulawa “Allah ya ƙarfafa ki, yarinya mai haƙuri da hankali.Rayuwar sarauta tana da wahala, amma zuciyar mace mai addu’a tana da ƙarfi.”
Na ji kamar hawaye zasu sake zuba, amma sai na riƙe su. Na ɗaga kai, na ce “Insha Allah, zan zama mai haƙuri.”
Hajja ta murmusa kadan, ta ce “Hakan nake so. Ki tafi yanzu, a kai ki wurinsa.” Ko minti uku ban yi ba, wata baiwa ta shigo da natsuwa, ta sunkuya ta ce “Allah yakara miki tsahon rai ca lafiya ya kareki, ana jiran matar yarima.”
Na ɗan gyara zamana na yi mata sallama cikin sanyi, sannan na fita. Wata mota ce a waje sabuwa, fara tas wacce ban taɓa ganin ta ba. Tana jiranmu fadawa biyu bakinta sun buɗe kofa Ba tare da wata tambaya ba,na shiga. Muna fita daga ƙofar masarauta, zuciyata ta fara sauka. Jikina ya yi sanyi, amma a gefe guda akwai wani abu da ke motsi a cikin ƙirjina tsoro. Tsoron kada shima in rasa shi, kamar yadda na rasa Bashari.
Kukan da ke makale a cikin maƙogwaro ya silale, ya fito a hankali. Na yi saurin gogewa, amma idona sun riga sun nuna damuwata.
Mun isa babban asibiti. Kafin na ce komai, bafaɗi ya buɗe ƙofa da girmamawa. Na shiga ciki da ƙafafuwa masu nauyi, ina jin yadda ake gaishe ni daga gefe-gefe, amma hankalina ba ya wajen su.
Sai ga wani dogon mutum yana wucewa ta gabana, yana waya. Muryarsa da yadda yake tafiya suka tsoratar da ni. Na kalleshi ya yi kama da wanda yake fitowa daga ɗakin yarima. Amma saboda yawan ‘yan uwansu, ban zurfafa ba. Gabana yana waduwa. Na tura ƙofar ɗakin a hankali, iska mai sanyi ta daki fuskata, ƙarar na’urar AC na rawa a kunne. Na ɗaga kai idona suka sauka kansa.
Na tsaya cak.Ya rame,Fuskarsa ta canza,Numfashina ya tsaya,Na furta cikin firgici “Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un…”
Ban san sanda na karasa kusa da shi ba. Na durƙusa a gaban gadon, na riƙe hannunsa da hannaye biyu. Jiƙinsa da mugun zafi, Na fashe da kuka ba tare dana sani ba, ba na tsoro kaɗai ba amma na wani irin baƙin ciki da ban iya fassara ba.
A hankali, na ɗaga kaina, na kalli fuskarsa.
Wannan mutumin da duniya ke ganin shi mai matsayin mai ƙarfi, mai kuɗi, ɗan sarauta ga shi yanzu yana kwance ba tare da iko ba.
A lokacin ne na ji jikina ya yi sanyi sosai, har cikin zuciyata. Na zauna a gefen gadon, ina riƙe da hannunsa. Bansan mintuna nawa nayi haka ba, amma naji muryar wani a bayana ana mun magana a hankali.
“Ranki ya daɗe, kidaina kuka dan Allah. Zai samu sauƙi sosai. Muna iya bakin ƙoƙarinmu.”
Na juyo a hankali, idona a cike da hawaye. Likita ne, sanye da farin rigarsa, fuskarsa cike da damuwa amma. Na ji muryata ta fita da rawar jiki “Doctor... tsawon wani lokaci yake haka? Meke damunsa ne? I’m scared, Doctor.”
Ya ɗan sauke numfashi, ya gyara takardar dake hannunsa sannan ya kalle ni da ido.
“Please, just pray for him. We’re trying everything we can. Zai samu lafiya, Insha Allah.”
Na gyada kai a hankali, amma zuciyata ta kasa yarda gaba ɗaya. Kalmar “pray for him” ta tsaya a kunnena kamar ana maimaitawa.
Na juyo na kalle shi, amma sai hawayen suka sake zuba. Na ce a hankali
“Allah ya sa.”
Sai wayata ta fara ringing. Na duba Momy ce. Na tsaya, kamar ba zan daga ba, amma sai na miƙe na tafi Na fita daga ɗakin cikin sauri, don kada na dame su da magana a waya. A cikin corridor ɗin asibitin, iska ta daki ni mai sanyi, sai na ji kamar jikin nawa yana rawa. Na danna wayar a kunne, na ce da muryar da take rawa “Hello Momy…”
“Auta! Ina kika shiga? Na kira sau biyu ban samu ba. Yau za a kawo gara, sai nake tunanin bari nasanar dake ko?.”
Na ce cikin rawar murya “Momy… ina asibiti.”
“Asibiti?! lafiya? Ko jiƙin nasa ne!”
Na kasa magana. Zuciyata ta kulle. Sai hawaye suka zubo cikin sauri. “Momy… shi ne... Asad. Har yanzu bai farfaɗo ba. Kullum mafarki nake yi akansa, Momy… ina tsoron mutuwa shima zai yi.”
Momy ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai muryarta ta sauya ta koma da sanyi, irin ta uwa da take son kwantar da hankali
“Auta, ki saurare ni da kyau, kinji? Addu’a zakiyi masa, ba kuka ba. Ki tsaya da ƙarfin zuciya. Allah yana tare da shi. Ki ninka addu’a, ba hawaye ba.”
Na share hawayena da bayan hannu, na amsa a hankali “To Momy… Insha Allah. Zan yi addu’a.” “Haka nake so. Allah ya albarkace ku.” Na kashe wayar, na jingina da bango. Hawayen da na so in danne suka sake fitowa.
Na yi doguwar ajiyar zuciya. Kalaman Momy suna yawo a kunne na kamar tana nan kusa da ni tana faɗi “Addu’a, ba kuka ba.”
Har nayi shirin komawa cikin ɗakin, sai na ji muryar da ɗan bayan corridor din.
“Ranki ya daɗe, jiya ma da kyar aka barka ki shiga kaga mai martaba ya hana yanzu sai ka canza gaba daya salon shigowa. Kazo da wuri kafin kowa ya iso. Kada akamak.”
Na kalle bangon bayan babu wanda nagani saboda gini amma ina jin muryoyin su cikin mamaki.“ amma ganin ban fahimci zancen ba yasanya ni komawa ciƙin dakin a hankali na tura kofar doctor na gani yana masa allura. “ Ranki yadade ki zauna dashi inada surgery for just 3 hours i will be back.” Na kaɗa masa kai kawai. A cikin ɗakin nan ina tsaye, jikina babu ƙwarin motsi. Kamar wanda aka tsayar da lokaci, zuciyata ta cika da tunani. A hankali, na tuna da littafin Nana Diso da na taɓa karantawa a cikin application ɗin Arewa Pen. A cikin littafin, na karanta yadda jarumar ta nuna soyayya da kulawa ga mijinta, duk da yana cikin asibiti, yana fama da rashin lafiya. Ta kasance kusa da shi kullum, tana masa sannu da addua, tana bashi ƙarfin guiwa. Wannan labarin ya taɓa zuciyata sosai. Yadda ta dage ta tsaya tare da mijinta, hakan ya zama darasi gare ni. Na kalli rayuwata, na tuna da wanda yake ƙaunata, wanda shima yanzu yake kwance cikin rashin lafiya.
Na ji zuciyata ta motsa. Kamar wani ƙarfi ya dawo cikin jikina. A hankali, na fara tafiya zuwa gare shi kowane mataki yana cike da niyyar nuna kulawa da soyayya kamar yadda jarumar ta yi a cikin littafin.Na ce a raina, "Idan ita ta iya nuna gaskiyar soyayya da juriya, ni ma zan iya."
Na zauna a gefen gadon Asad, numfashinsa yana fita a hankali. sai sautin injin ɗin oxygen ke rawa a kunnena kadan kadan. Na rike hannunsa cikin hannuna, na ji yadda fatar sa ta yi wani zafi kamar wuta. “Asad... ka ji ni? It’s me, Ramlah,” na furta cikin murya mai taushi, kamar ina tsoron in karya wani abu a cikin iskar da yake shaka. Babu amsa. Babu motsi. Sai numfashin injin ya ci gaba da kadawa, daidai da hawayena da ke zubaɗaya bayan ɗaya kamar ƙwayoyin ruwan sama da suka rasa inda za su tsaya. nashiga shafa hannunsa, ina kallon fuskarsa da injin oxygen ya cika. Cikin wani sanyin murya da shagwaba, ciki da hawaye nashiga nace, “My Asad… dan Allah katashi, inasonka ina jiran ka.” Hannuna ya rike nasa, na kasa fahimtar yadda bakina ya motsa ban san sanda na aza bakina gefen fuskarsa ba. A hankali na matso, na masa sumba a goshi, na kara rike hannunsa cikin ƙarfi, ina masa rada kalaman soyayya sun fara zubowa daga bakin da ke cike da tsoro da bangaskiya. “Ka ji, Asad? I love you,” na ce, murya ta dai rawa. Na yi masa magana kamar yana jin ta kamar akwai wuri a cikin duhu inda muryar kiɗa za ta isa masa. Amma a zahiri, baya cikin hankalinsa gaba ɗaya. Wannan ne ya sa zuciyata ta fi ƙarfi in ba zai iya amsawa ba, ni zan zama muryar sa, ni zan zama numfashin sa… Nafada batare da nasan maganganun danake ba. A hankali na juyo, na duba injin, na saurari beep ɗin da ke bugawa kamar mummunan kiɗa wanda ya zama sarki a wannan daki. Na sake matsowa kusa da fuskar sa, na sumbace goshin sa da ƙaramar murya, “Wake up, my love. I need you.” Sai na ji kamar duniya ta tsaya, amma babu wani motsi. Sai dai zuciyata ce ta ci gaba da magana ta yi masa alkawari… Zan kasance a bayansa, zan rika masa addu’a, zan rika masa magana har sai idanuwansa su buɗe.
Nana hadiza
09030569336
[01/11, 8:22 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Karar bude ƙofa ta daƙin ciƙin asubutin ta ƙwace min numfashi. Na miƙe da sauri daga inda nake zaune gefen gadon, hannuna na share hawayen da ke kan fuskata. Kafin na iya tantance abin da ke faruwa, sai na hango dogari biyu suna buɗe ƙofar cikin ladabi da girmamawa, sun sunkuyar da kansu suna cewq “Mai Martaba Babangida Na Uku yana shigowa.” Wani irin sanyi ya ratsa jikina. Da sauri na tsugunna a gefen kafet, zuciyata na bugawa tamkar ana danna tambarin sarauta a zuciyata. Sai ga Mai Martaba Babangida Na III, cikin doguwar shadda mai alamar iko, da rawanin sarauta da yake fari . A bayansa kuwa wasu magidanta ne suke biye dashi Yarima Aliyu babangida da Waziri Isa.manyan mutanen da ke sanya fadarsa ta yi armashi da tsari…kamar yadda uwar amarya tagayamun.
Cikin murya mai nutsuwa amma cike da izza, Mai Martaba ya ce “Ramlatu, har yanzu baki koma ba? Na zata kinje ki huta, amma ga shi kina nan kina wahala harda kuka.” Maganarsa ta cika ɗakin da iko. Na kasa ɗaga kai saboda rawar da zuciyata ke yi. Sai da na tattaro ƙarfin zuciya kafin na ce cikin murya mai rauni “Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon rai, Mai Martaba. Barka da zuwa, ranka ya daɗe.” Bai yi magana nan take ba. Ya tsaya yana kallona, sannan ya ɗan gyara murya, yana ɗan murmushi mai cike da natsuwa da hankali. Yarima Aliyu ya dan lumshe idonsa yana kallona da mamaki, yayin da Waziri isa ya ɗan gyara tsayuwarsa da girmamawa.