Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 27
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 27: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 27. Mai Martaba ya karasa kusa da gadon inda Asad yake wanda ke kwance.…
4,447 words
Mai Martaba ya karasa kusa da gadon inda Asad yake wanda ke kwance. Ya ɗauki hannunsa cikin natsuwa yana masa addu’a da murya mai ɗauke da tausayin da damuwa irin ta iyaye. Na ji Waziri isa yana cewa cikin ladabi “Ranka ya daɗe, Allah yakara maka lafiya acigaba da yimasa addu’a.” Amma Mai Martaba ya daga kai yaƙalleshi sosai sai yace cikin iko da nutsuwa “Waziri isa. jikinsa kamar yana samun sauƙi, ko?”
Waziri ya amsa cikin ladabi “Alhamdulillah, ranka ya daɗe. Allah ya ƙara maka natsuwa da yawan rai.” A wannan lokacin zuciyata ta tsaya cak. Na ji kamar iska ta tsaya a cikin ɗakin saboda irin nutsuwar da ke ratsa duk wanda ke cikin daƙin. Bayan ɗan lokaci da addu’a da maganganu masu hikima, Mai Martaba ya miƙe tsaye. Ya juyo gareni cikin murya mai cike da umarni yace “Ramlatu, Allah ya yi miki albarka. Wambai zai isar da ke gida ki huta.” Na buɗe baki cikin gaggawa don yin magana, amma Waziri isa ya yi saurin cewa “Ranka ya daɗe, daidai ne a bar ta har zuwa dare.” Mai Martaba ya juyo da nutsuwa ya ce: “Zai yiwu ta zauna, Ramlah ta yi yarinya ai, Waziri.” Cikin kunya da girmamawa na ce “Zan iya, ranka ya daɗe.”saboda uwar amarya tace agidan sarauta maganarka ita ke kwatarka shiyasa nima nayi hanzarin yin maganar duk da kunya data lullubeni. Ya ɗan murmusa da dattako, sannan ya ce “To, babu damuwa. Zuwa dare sai a kaiki gida, a sanar da zamanta anan. A tabbatar da abinci ya iso gareta.” Na sunkuyar da kaina, na amsa da muryar dake rawa “Allah ya saka da alheri, Mai Martaba.” Sannan suka fita. Hasken fitila ya biyo bayan su, yana haskaka rawanin da ke kansa har zuwa lokacin da ƙofar ta rufe.
A take sai Dr. Khalid ya shigo cikin riga ta likita mai farin kala, yana ɗauke da takarda da na’urori. Yana kallona ya ce da ni cikin turanci “He still hasn’t shown any response beyond breathing, right?” Na amsa cikin damuwa “Yes, Doctor. But what kind of illness is this? Just days ago, he could talk.” Dr. Khalid ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce “At first, it was poison but we managed to neutralize it. Yet now... we can’t tell what exactly is happening to him. It’s as if his body is rejecting its own healing.” Na runtse idona, zuciyata na rawa. Wambak, Yarima Aliyu, ya dawo cikin ɗaki yana kallon marar lafiyan da takaici da tausayi, yana cewa cikin muryar sarauta “Wai me ya faru da shi haka, Dr. Khalid?” Likitan ya sunkuyar da kai cikin girmamawa yana masa bayani sannan shima yayi masa tambayoyi sai Dr khalid yace “Ranka ya daɗe, muna ƙoƙarin gano hakan.”
Ni kuwa, na zauna shiru. Nayi shiru Na dubi shi dake kwance babu wani mosti da yakeyi sai na numfashi naja numfashi nace “Idan ba gurin wanda ya aure ni ba zan zauna, to gurin wa zan zauna?”
*******
Cikin falon babbar fadar masarauta ɗakin da ke cike da hotunan sarakunan baya. Hajja matar mai martaba kuma uwa ga yarima Asad, ta tsaya gaban kujera mai kyan gaske tana kallon Mai Martaba Babangida Na III da idanu masu cike da damuwa. Muryarta ta kasance mai nutsuwa amma cike da ƙunshi da ɓacin rai “Ranka ya daɗe, ban ji daɗi kwata-kwata akan hukuncin da ka yanke game da Asad. Kai kafi kowa sanin cewa ɗan nan naka ba daga cikin yaranka ne da ke son komai na sarauta ba baya son komai dangane daita baya kuma jingina kansa da’ita Duk da sarauta ta haife shi, baya kaunar komai da ya shafi iko ko mulki.” Ta ɗan natsu tana kallonsa da hawaye a idanu, ta ci gaba “Fitar da shi waje, ranka ya daɗe shine zai taimaka mana sosai wajen samun lafiyarsa kana ganin kusan satuka amma ankasa gane inda matsalar take?. Kana ganin halin da yake ciki yanzu? Mutumin da yake da jirage masu zaman kansu guda biyar, da asusun da ke cike da dukiya, amma babu kwanciyar hankali.kuma ka hana asanar da yaransa saboda wata shawara da batada amfana idan ana magana akan larura wazaiyi dariya ai shi ciwo bai ki kan kowa ba. Abokanan kasuwancinsa kuma ai sungama dariya tunda an barshi aciƙin kasar a wulakance..”
Daga inda yake zaune, Mai Martaba Babangida Na III ya ɗago kansa a hankali. Idanunsa suka yi kalar tunani da girman ikon da ya gada daga sarakunan baya. Ya daɗe cikin shiru, yana tauna kalaman da hajja ta faɗa. Hasken fitila ya ɗan haska gefen fuskarsa, yana bayyana yanayin dattako da iko a tare da shi. Sai ya ce cikin murya mai nauyi, “BAZAKI FAHIMTA BA.”
Wannan kalmar ta tsaga sararin falon kamar kibau. Duk wani dogari da ke tsaye ya sunkuyar da kai, domin murya irin ta mai martaba ba kalma bace, hukunci ce.
Hajja ta ɗan ja da baya, tana jin zafin kalmar amma ta riƙe nutsuwarta. Mai Martaba ya ci gaba cikin murya mai ɗauke da zafi da tausayi lokaci guda “Asad ɗana ne.Yadda kike sonsa ina sonsa idan da zaabani zabin wanda zai gajini to tabbas shine, ɗa guda ne tamkar da goma. Ƙin sarauta wannan yasamo asali daga keni tunda tun asalinki bakyason sarauta. Na san halinsa fiye da kowa. Amma kin manta cewa ba kowace hanya bace ke kawo warkarwa. Wannan matsalar da ke damunsa ba ta jiki bace ta zuciya ce. Naso afiddashi amma abokanan hamayya…” Ya ɗan ɗaga murya “Asad ya taso cikin ni’ima, bai san wahalar rayuwa ba. Duk abin da ya nema, an tanadar masa. Amma yanzu lokaci ne na ya fahimci cewa iko da mulki suna da nauyi, ba kyauta ba. Baza’a fiddashi waje ba kamar yadda nasanar miki!!!.”
Hajja ta lumshe ido tana ɗauke kai, ta sauke ajiyar zuciya. “To, ranka ya daɗe. Tunda haka kace, Allah ya bashi lafiya. Allah yasa wannan shawarar taka ta zama alheri.”
Ta juya da ladabi, ta nufi ƙofar falon, rawar jiki na bayyana a hannunta. Dogarawa suka buɗe ƙofar da girmamawa, suka ce cikin murya ɗaya “Mai Martaba ya zauna lafiya.”
Mai Martaba bai motsa ba. Ya jingina da kujera, yana kallon fitilar da ke walƙiya. Zuciyarsa na tafarfasa da tunani wajibi ne ya kasance sarki mai adalci, amma a yau zuciyarsa tana neman zama uba mai tausayi. Ya ɗan riƙe goshinsa da hannun dama.
Sai Waziri Aliyu ya shigo cikin natsuwa, yana ɗauke da fayil ɗin bayanan likita da sakonnin ofis. Ya tsaya a gaban mai martaba yana sunkuyar da kai “Ranka ya daɗe, na karɓi rahoton daga Dr. Khalid. Jikin Yarima Asad yana buƙatar kulawa ta musamman. Amma suna cigaba da bincika akan matsalar tasa.”
Mai Martaba ya ɗan lumshe ido. Ya ce a hankali “Ka shirya masa tafiya cikin kwanaki uku. Ku tabbatar komai ya kasance a sirrance. Kada wani daga cikin ‘yan jarida ko fadawa ya san manufar tafiyar nan naga jiƙin nasa yarikice..”
Waziri yadan zafo idanu dan ba haka yaso ba daman shi yazuga mai martaba amma yaga hajja tafita ilau itace tazo tayi wani munafurcin to ko uban me tayi asad mutuwa zaiyi dan kiris yarage sauran numfashin nasa su daina aiki. Amma ciƙin girmamawa yace “To, ranka ya daɗe.” Waziri ya sunkuyar da kai cikin ladabi. Yana kissima yadda zai ruguxa tafiyar.
Nana hadiza
09030569336
[01/11, 8:22 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
*********
Na zauna a gefen gadon, idona cike da tunani, zuciyata cike da damuwa an aiko da abinci tun dazu dakyar na dan iya ci sai na bawa su Dr.khalid gaba daya still dai.har yanzu babu wani canji momy takirani akan sun kai gara an basu kayan arzuki tana kuma yimun nasiha akan nacigaba da hakuri nace mata to.
Masu aike suka shigo suka cemun ana jirana awaje daga fada Na ɗauki mayafina cikin nutsuwa,nakarasa baƙin gadonsa ta tsugunna nayi masa kiss gaban goshinsa sannan na fita. Tun kafin na ƙaraso ƙofar, sai na ga motoci guda biyu masu duhu sun tsaya, fitilarsu na haska titin asubutin.
Dogarai suka buɗe ƙofa. Wani daga cikinsu ya ce cikin murya mai natsuwa “Ranki yadaɗe ,an zo a ɗauke ki.” Na so in ce zan kwana, amma na san cewa a fada, babu wanda ke jinkirta umarni. Na shiga motar da sanyin jiki. Motar ta nufi babban titi haka mukayi hanyar masarautar. Ko da muka isa, kafin in fito daga motar. Na hango gimbiya maryam tana tsaye baƙin shashina.Tana sanye da riga mai kyan gaske, an lullube kanta da mayafi fari, hannunta ɗauke da zobba masu daraja.
Ta kalleni sama da ƙasa cikin kallo mai ɗauke da raini. “Kin dawo daga gurin mataccen, ko?” Muryarta ta cika da ƙyama da ƙasaita. Na tsaya na kalleta cikin nutsuwa, zuciyata cike da girmamawa amma ba tsoro. Na ce a hankali “Sannu da zuwa, Gimbiya.”
Babu alamar jin daɗi a fuskarta.
Ta juya tana tafiya zuwa cikin babban palour ɗina wanda ya sha ado da kamshin turare. Na bi bayanta cikin ladabi. A ciki kuwa, masu aiki sun tsaya daidai suna fadin “Sannu da zuwa.”
Na amsa da tawali’u, amma ita kuwa Gimbiya Maryam ko kallo basu isheta ba. Ta zauna kan kujerata, ta juya da ɗan murmushi mai ɗauke izza. Sai ta dubi wata daga cikin masu aikin, wato Uwar Amarya, ta ce cikin murya izzah da wulakanci “Kije, ki bar mana wuri.”
Uwar Amarya ta sunkuyar da kai, ta ce, “To, Gimbiya,” sannan ta fice da ladabi.Shiru ya ratsa dakin. Sai Gimbiya Maryam ta juyo gare ni da ido mai tsananin tsana ta ce cikin muryar wulakanci da izza “Wanene ya baki shawarar auren Asad? Bakisan ba shi da lafiya ba? Bayan wannan ciwon, bakisan yana da matsala a gabansa ba baya motsi! Kinsan yarinyata ta taba auren Asad? Abinda ya raba su kenan. Amma ke,kamar bakida wayo, kin shiga cikin wuta baki san ba.”
Zuciyata ta buga, amma na kasa cewa komai.
Kallon da take min ya nuna ba wai kawai tana faɗa ba tana gwada iko ne, tana son ganin ko zan nuna halin yar talakawa kamar yadda ta kira ni a zuciyarta. Na ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi, na ce da murya mai sanyi “Na gode, Gimbiya. Allah ya saka da alheri.”
Ta yi dariyar da bata kai zuciya ba, dariya mai ɗauke da izza. “Ba haka ake fada ba, yar talakawa. Ki koyi maganar sarakai. A fada, idan aka faɗa magana sai a ƙara da ‘da girma da mulki’. Wannan ba gidan talakawa bane masarauta ce.” Na amsa cikin rauni “Na fahimta, Gimbiya.” Ta ɗan ja numfashi, ta miƙe daga kujerarta. “Ki sani, Ramlatu, sarauta ba wasa bace. Auren Asad ba kyauta bane, hukunci ne. Amma kada ki ɗauka saboda kin samu guri a gidan sarki, to kin zama sarauniya. A fada, kowa da matsayin sa kuma yadda kika shigo gidan sarƙin nan haka zaki fita da ƙafafunki.”
Ta juya, ta ɗan tsaya a bakin ƙofa “Da fatan baki manta da darasin yau ba. Ki tuna, magana a fada kamar wuka ce ta iya yanka kai ko kare ka. Ki koyi amfani da ita.” Ta fita tana tafiya cikin izzah. Ni kuwa na tsaya a tsakiya, zuciyata ta cika da haɗuwar ji tsoro, baƙin ciki, da ƙarfin gwiwa.Wato ita zuwa tayi nan ta zugani kokuma zuwa tayi ta wulakantani nama kasa fahimtar wanda takesonyi. Na juya zuwa sashena a hankali. Sai hawaye suka zubomin a hankali. Ina gogesu nida nasa wulakancin momy menene zai bani tsoro? Dole na zama jaruma agidan nan idan bahaka ba to tabbas hawaye na sai yaƙare.
*********
Cikin dakin Alhaji Muqaddam, hayaki na turaren wuta ya gauraye ƙamshi ko ina. Belt ɗin dake hannunsa yana tsalle a iska, yana dokan jiki ba tare da tausayi ba. "Wallahi sai kin koya hankali yau!" Ya furta da murya mai cike da fushi, idanuwansa sun cika da wutar bacin rai. Ayshatu tana ƙoƙarin kare jikinta, tana jan numfashi da kyar. "don Allah... ka ji tausayina!" ta faɗa tana kuka, hawaye suna gudu kamar ruwan damina. Duk da mamakinsa da hakurin datake bashi bai hana fushin Alhaji Muqaddam bai sauka ba. Ya kara huci yana cewa"Wacece ke idan ba baiwa ba? Matata zakije ki daka? Uwargida? Ni Alhaji Muqaddam, wanda ake girmamawa? Ni kike rainawa saboda kin mareta na hukuntaki shine zakije ki daketa?"
Ya sake zabga mata belt ɗin, yana magana cikin masifa "Ni ba dan iska bane! Ni ba butulu bane! Amma ke... fasika ce! Mai cin amanar aure! Tsarkakakkiyar macce irinta duk kazantar danakeyi tana tare dani bata taɓa cin amanata ba." Karan belt ya ci gaba da sauka har sai da jikinta ya yi sanyi, numfashinta ya yi rauni. Cikin kuka da rawar murya ta ce,
"Don Allah... ka yafe min... ban yi da nufin raina ka ba..." Shiru ya ratsa ɗakin. Alhaji Muqaddam ya tsaya yana huci, sai ya cilla belt ɗin gefe, ganin tabashi hakuri abunda ayshatu bata taɓayi ba ya fice daga dakin da sauri, yana furta kalmomi da ba’a gane me yake faɗa.
Da zarar ya fita, ‘yan aikin gidan suka shigo a guje. "Hajiya! Hajiya Ayshatu! Sannu!" suka faɗa a ruɗe. Babbar cikinsu, Dije, ta durƙusa kusa da ita tana kuka. "Ku kira driver! Mu kaita asibiti!" Kafin su fita, muryar Alhaji ta dawo daga bakin ƙofa "Kada a kai ta ko’ina! Ku bata ruwan zafi da paracetamol kawai!"
Ya juya ya bar gidan gaba ɗaya. Dije ta kalli sauran ‘yan aikin, ta girgiza kai. "Subhanallah... wannan ai azaba ce, ba aure ba." Suka taimaka suka zaunar da Ayshatu, suka zuba mata ruwan zafi. Amma jikinta kamar wuta, sai zufa ke keto mata, idanunta sun kumbura. Dije ta tsaya a bakin ƙofa tana tausaya mata, ta ce cikin nutsuwa "Hajiya, ki gyara, don Allah. Alhaji mutum ne mai zuciya, ki rage fada. Ki zauna lafiya kullum cikin faɗa kuke wanda abaya bahaka kuke ba." Ayshatu ta ɗago kai cikin hawaye, ta share fuska da bayanta. "Ku fita kawai... ku bar ni."
Da suka fita, ta jingina kanta da bango, zuciyarta cike da ciwo da nadama.
"Wayyo Allah na... nashiga uku," ta ce cikin murya mai rauni.
Ta lumshe idanu tana kuka, tana tunanin kalaman Asad yakan ce, “Ayshatu, wanda yasan darajar mace, ba zai daketa ba. Idan ta kuskure, mari ma ya isa idan har kuskuren ya girmama.” Ta sake fashewa da kuka.
"Da Asad ne... da ba na cikin azaba da bana cikin masifa datuni ina kasar waje sai inda na zana," ta faɗa cikin kuka mai ƙuna.
A wannan lokacin, zuciyarta ta cika da tambayoyi Shin wannan shi ne aure? Ko kuma kaddara ce ta fuskantar rayuwar da ba ta so? Kokuma alhakin asad ne?
Ta kwanta tana kuka har barcin wahala ya ɗauke ta .
********
Cikin bacin rai da gajiyar jiki, na kwanta. Koda bacci ya ɗauke ni, bai yi min daɗi ba zuciyata cike take da damuwa da nauyin tunani.
Washegari da sassafe, na tashi daga bacci cikin natsuwa. Na shirya domin fita training kamar yadda na saba. Na sanya doguwar abaya mai launin coffee sai ɗan ƙaramin mayafi yakara min kyan fuska. To Allah dai ya san yadda wannan alkyabba ke min nauyi, amma saboda mutuncin gidan, sai na danne zuciya na, na cigaba da shiryawa.
Da na fito daga ɗaki, idona ya sauka a kan kayan garar da aka shigo da su jiya. Kayan suna shimfiɗe a ƙasan sashen sun cika gurin gaba daya duk sun cika falon.Na tsaya cak, numfashina ya dan tsaya. Na runtse idona, hawaye suka cika kamar za su zubo.
“Wayyo Abba…” na furta a hankali, zuciyata ta tsinke da rauni. Kudin Abba ne nan yqketa kashewa domin yasiyamun mutunci dadaraja awannan gidan.
Na kira shi awaya cikin rawar murya.
"Assalamu alaikum Abba," na faɗa cikin ladabi.
"Wa’alaikumus salam, yar albarka," muryarsa ta amsa da ƙauna. Muna gaisawa cikin taushin kalmomi, kafin ya fara ba ni nasiha kamar yadda kullum yake.
"Yata, ki mai da hankali da rayuwarki. Ki rike mutuncinki, ki kula da addininki, ki kuma kasance mai haƙuri da mijinki."
Na yi shiru na ɗan numfasa, kafin na ce masa cikin tausayi "Abba... don Allah, kudin da ka ce a turo min, na bar maka gaba ɗaya.Dawainiya da ni tayi yawa, bana so ka wahala saboda ni."
Nana hadiza
09030569336
[03/11, 9:47 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
*********
Sai na ji ya yi dariya mai cike da taushi.
"Kiji yarinya... ai ba wata nayiwa ba. diyata nayiwa. Karki damu da kudi, ke dai abu ɗaya nake so daga gare ki ki kaunaci Asad, ki kuma yimasa biyayya. Wannan ne alherin da nake nema daga gare ki."
Na dan murmusa, hawaye na tsiyaya cikin farin ciki da tausayi."Inshaa Allahu Abba," na ce masa a hankali.
Na kashe wayar, na juyo cikin nutsuwa. Na ɗan yi rolling, sannan na mike cikin ladabi na nufi kofa.
Da na fito, dinning ɗin gidan ya cika da kayan breakfast bread, omelette, kunun gyada, Kallo guda zaka yi ka san gidan mai kudi ne.
Da zarar suka gan ni, ‘yan aiki suka fara gaidani da ladabi "Sannu ranki ya daɗe!"
"Ina kwana ranki yadaɗe" Na amsa cikin murmushi, na dubi kowanne cikin kulawa.
Ina tafiya, sai na hango uwar amarya, tana zaune cikin natsuwa, Na matsa kusa domin in gaishe ta, amma kafin na ƙarasa, ta fara yin kirari tana cewa "Ga ‘yar gida, ga matar sarauta, ga mace mai kamun kai!"
Na durƙusa da girmamawa, na ce"ina yini?"
Ta murmusa ta ce "Ranki ya daɗe, kin shirya kenan? Kidaina durkusamun kada wani yagani dan Allah" Mamaki yakamani sai Na ce mata, "Eh, na shirya." Kawai.
Ta ce, "To, bari a sanar da Sarkin ƙofa da kuma driver, sai a shirya tafiyarki."
Kafin ta tashi daga kujerarta, ta juyo ta dubeni da idon uwa, ta ce cikin jin kai"Amma ranki ya daɗe, naga baki karya ba?"
Na dan murmusa, na ce cikin ladabi:
"A’a, uwargida, azumi nake yi."
Ta ce, "To, Allah ya karɓa, ya ba da lada da lafiya."
Na sunkuyar da kai cikin ladabi na murmusa, na juya da natsuwa. Abayata tana ta yawo da ƙamshi yayin da na fita daga falon kamar wata mataar mai kudi.
Cikin kankanin lokaci aka sanar da fitowa ta hakan yasanya nadinga jin kuka yadda naga suna bina da gaisuwa har na isa mota aka buɗemun na shiga ciki Na jingina da jikin motar na dan huta, ina kallon hasken fitilun asibitin da ke haskaka falo mai ɗauke da nurses masu zirga-zirga. Kowa cikin hanzari, kamar dai akwai wani abu mai nauyi da ya taso a wannan safiyar kokuma nace marasa lafiya sun dan cika asubutin.
Na daidaita hijab ɗina a hankali, sannan na nufi sashen nasa. A ko’ina sai ƙamshin magani da ƙarar bututun oxygen ke cika hanci. Idona ya sauka kan gadon da yake kwance, duk da ban isa kusa ba, zuciyata ta soma kaduwa. Kafin in ƙarasa, nurses biyu suka tsaya a gefen ƙofa suka gaishe ni da ladabi. Na amsa cikin nutsuwa, na murɗa ƙofar a hankali kamar wacce take tsoron tura ta gaba ɗaya.
A cikin ɗakin, haske yacikasa sai Sanyin Ac, sai kuma na hango wani mutum kusa da drawer ɗin karin ruwa. Waziri ne mutum mai dogon fuska da kallon izza. wanda nakira“mutumin da babu dariya a fuskarsa.”
“Ranki ya daɗe, kece?” Ya faɗa da murya mai kaushi, yana kallona daga sama har ƙasa.
Na rusuna cikin girmamawa, nace “Eh, ni ce. Ina kwana?” Ya murmusa kadan, yana nuna kamar bai damu ba, sai kawai yace, “Mun maimartaba yasanya inzo in duba yadda yake.”
Na gyada kai, cikin ɗan murmushi, nace “Allah ya ƙara maka lafiya da albarka.”
Ya kalli gadon da yake shiru, sannan ya ce “To, Allah ya bashi lafiya tunda kinzo bari ni naje,” kafin ya juya ya fita da takunsa mai izza.sai wata leda ta kwado daga gefen drawer din. Baima jiyo ba inaji baiji ba yafita Da zarar ya fita, na ji zuciyata ta dan yi sanyi, amma wani tunani ya tsaya min a rai. Na kalli drawer ɗin da Waziri yake tsaye akai an jera kwalaben allurai kala-kala, wasu da rubutu, wasu babu komai. Ledar data wadi na dauka shima naga allurai ne sai na mayar daita ciki. Ina tsaye gurin Sai ga Doctor ya shigo cikin ɗakin, yana rike da file. Ya gaishe ni da girmamawa, na amsa, sannan nace da shi cikin taushin murya, “Doctor, waɗannan allurai da yawa, kowacce ta menene ne?”
Ya dan kalle ni yana murmushi, “Ranki yadade kina son sanin komai ko?”
Nace, “Eh, don in dinga kula idan an kawo wani sabon abu.”
Sai ya fara ɗaya bayan ɗaya yana gaya min wacce ke taimaka numfashi, wacce ke ƙara ruwa a jiki, wacce ke rage zafi. Amma da ya zo kan wata kwalba, sai kawai ya tsaya, ya ɗaga ido ya kalle ni.
“Me yasa wannan take nan?” Ya tambaya cikin mamaki.
Nace, “ To ai aciki take daga leda ta wado yanzu shine na sanyata ciki”. Sai naga mamaki yacikasa sosai hankalinsa ya tashi Ya buɗe kwalban, yana duba garin da ke ciki, sai kawai ya zazzago kadan, ya ɗan shaka. Cikin firgici ya kalle ni, idonsa ya faɗaɗa.
“Ranki yadaɗe… wannan poison ne! Ai tayaya zai shigo cikin nan ana saka shi cikin allura yadda zqi kassara mutum a hankali.”
Jikina ya saki gaba ɗaya. Na tsaya cak, numfashi ya tsaya min na ɗan lokaci.
“Poison?” Na maimaita cikin rawar murya, “Wallahi bansan da haka ba! Duk yadda akayi, su suke narka masa a cikin ruwa ba tare da saninsa ba shiyasa kace bakwa gane aikinku…” Na rufe bakina da tafin hannu, idona suka cicciko da hawaye. Zuciyata ta buga da ƙarfi..
Shima tsayawa yayi yace “ innalillahi da matsala wallahi kuma bakiga wanda yashigo yanzu ba?. Hannuna suka dauki rawa, numfashina ya tsaya cak. Kallon kwalban kawai nake yi, kamar zan iya fahimtar wanda ya sanya shi idan na kalle shi sosai.
Doctor ya kalli kofa da sauri, ya ɗaga murya cikin mamaki da fushi.
“Halloo! Nurse Hauwa, zo nan yanzu!”
Muryarsa ta karade ɗakin gaba ɗaya. Sai ga wata nurse ta shigo da hanzari duk arikice, “Sir, lafiya?” Ya miƙa mata kwalban da hannun da ke ɗan rawa, “Ke kika kawo wannan ruwa daga pharmacy?”
Ta ɗan tsaya da mamaki, ta ce, “Eh Sir, ni ce. Pharmacist ne ya bani nayi connecting kamar kullum.” Amma kuma kamar ba wannan kwalbar bace na. Ya daka mata tsawa, “Kamar? Kina da tabbacin wannan ba a can aka rikice ba?”
Nurse Hauwa ta soma rawar jiki, “Wallahi Sir, ban san komai ba. Na karɓa daga hannun ɗaya daga cikin assistants ɗinmu kawai.”
A lokacin, zuciyata ta kasa natsuwa. Na jingina da bango, idona na tafiya kan fuskar mijina dake kwance cikin shiru, ba tare da ya san ana ta rikici akansa ba. Hawaye suka fara gangarowa a hankali. Ko shakkah babu waxiri ke aiki akan Asad shine abunda mafarki na ke nunamun sunaso su kashe shi kenan kamar yadda uwar amarya tagayamun basasonsa sai na hatuna da kalmar gimbiya maryama datace ragowar gawa.
Doctor ya kira wani abokin aikinsa, “Dr. Musa, zo nan da sauri. Muna da emergency!”
Dr. Musa ya shigo da sauri, yana rike da file, yana tambaya, “Mene ne ke faruwa?”
Sai Doctor ya mika masa kwalban, yana fadin, “An samu poison substance a cikin kayan da ake narka wa patient ɗin Yarima.”
Dr. Musa ya duba kwalban, yana girgiza kai. “Wannan ai ba accident bane, anya ba sakawa akayi ba? Ko a pharmacy ai baa barin wannan ” ya faɗa cikin takaici. Ya kalle nurse hauwa yace “ Tun yaushe kuka fara bashi wannan?”. Ranka yadade nidai ba wannan kwalbar bace ba amma kuma nakasa ganewa kusan 4days da aka farayi masa kuma naga ruwansa ma kamar ya canxa yanzu” ta nuna ledar ruwa. Cikin zafin nama Dr khalid yaje yacireshi yace tayi maza maza ta wuce lab dashi. Dr. Musa ya dan yi shiru na ɗan lokaci sannan yace, “To gaskiya sai an bincika wannan lamarin. Amma ku tabbata akwai wanda yake son cutar da shi.” Doctor ɗaya daga cikinsu ya fita da kwalban don kaiwa laboratory, saura ni da nurse ɗin da ke kuka tana faɗin, “Wallahi ban san komai ba, dan Allah ku yarda dani.”
Na kalli nurse ɗin, raina na sosuwa da tausayi amma tsoro yafi karfi.
“ ko bakisan komai ba wannan sakacin ku ne tayaya kwalbar nan zatashiga cikin kayan mara lafiya wanda kusan hadarinta.” na furta cikin muryar da ke karyewa.
Na runtse idona, na rike kirjina. Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru sai karar injin oxygen da ke yi kamar yana kirga numfashin mai kwance.
Masifar danaji anayi a nayi aciƙin asubuti gaba daya ta dauka.sosai ake faman faɗada turanci wani lokacin kuma labarci daga ni har Dr. Mun kasa cewa komai dukkanmu muna ciƙin shock.Sai ga wani kyakywan matashi ya shigo cikin sauri, yana magana da wayarsa cikin Turanci, muryarsa cike da gaggawa ransa a ɓace sosai “What do you mean the plane isn’t ready yet? I said two hours! Two! Not three! Get them to move faster!”
Nana hadiza
09030569336
[03/11, 5:02 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Ya katse kiran, yana kallon doctors ɗin da ke tsaye. “What’s going on here? Why is everyone standing like statues? An barmun mahaifi sai kace wani wulakantacce saboda wata banzar al’adar sarauta.”
Doctor ya kalli shi da girmamawa amma da damuwa, “Sir… we found something suspicious in His Highness’s IV fluids.”
Umar ya ɗan motsa kaɗan, yana kallon kwalban da ke hannun Dr. Musa. Ya kama kwalban da hannunsa guda, yana kallon sa da ido, sannan yace “You mean… poison? You have been poising my father.. saboda rashin iya aikinku da sakacinku.”
Babu wanda ya iya amsawa Sai Dr. Musa ya yi ƙasa da kai, yace, “No sir we are sorry please.” Umar ya dafa goshi, yana lumshe ido. “This is madness. Who would dare?”