Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 28
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 28: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 28. Na ji kamar zuciyata zata fashe saboda irin yanayin da nake ciki.…
4,386 words
Na ji kamar zuciyata zata fashe saboda irin yanayin da nake ciki. Na tsaya a gefe, amma idona ya tsaya gare shi. Yanayinsa ya cika da fushi da tsoro lokaci ɗaya.Sai ya ce cikin fushi “I want full security around my father. No one goes in or out without my permission. Am I clear?”Dr. Musa ya amsa, “Yes, sir.”
Sai Umar ya juyo gare ni, idonsa suka tsaya da nawa. “Am sorry small mom.” mamaki nayi inda yasanni dan ni inbanda naji ance sir umar ban tabbatar da ɗansa ne. Na yi shiru, zuciyata na ta bugawa. Ban san yadda zan fada masa ba, amma sai maganar ta fito da kanta “ Ina wuni..” sai yayi sauri yace “Am sorry i don’t greet you Good afternoon.” Sai ya juyo da gaggawa yafita sai naga yadawo da mata biyu suka shigo kowacce na kuka aciƙinsu.
Umar ya tsaya shiru na ɗan lokaci, yana kallon gadon mahaifinsa. Fuskar Yarima Asad cike da sanyi, numfashinsa na hawa da sauka da taimakon injin. “Father,” ya faɗa a hankali, “I swear, whoever did this will regret it.”
Na kallisa da idon tausayi. Duk da iko da ke tattare da shi, ina ganin wani rauni a cikinsa rauni na ɗa da yake tsoron rasa mahaifi.
Sai Hajja ta shigo a hankali, tana faɗin, “Umar, me yake faruwa ne haka? Saboda rigimar ku shiyasa mai martaba yace kada asanar daku ai sai fada su nawal sukeyi haba danAllah.”
Ya kalli Hajja, yana ɗan sauke numfashi “Grandma… they found poison in his medication.”
Hajja ta dafe kirji, tana girgiza kai. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… wannan gida namu wani iri ne tayaya bayan akwai tsaro ana din?.”
Umar ya matso kusa da ita yana rike hannunta “We’ll find whoever did it, Grandma. I promise.”
Na tsaya gefe, zuciyata tana bugawa. A wannan lokacin na tabbatar, da yaransa turawa ne dan ko hausa basayi kwata kwata hana dayan mai ciki naji tanayi amma turanci ne zallah na turawa abakinsu.
Ina kallo yanayiwa hajja bayanin yadda sukayi da mai martaba da kuma gayamata komai yasanya yazama ready yanzu zamu tafi USA Inaji hajja tana cemasa why not india yace mata no USA Yafi kwararrun likitoci a duniya.
Sai Umar ya juya gare ni, yana faɗin cikin murya mai dan zafi “Small Mom, you’re coming with us to USA tonight. I want you close.” Na ɗan firgita, amma sai na gyaɗa kai. “To ranka ya daɗe.” Ya ce,”Good. Go pack your things. We leave in one hour.”
Sai ya fita da gaggawa yana magana da wayarsa “Make sure the jet is ready. No excuses this time.”
Kalmar nan ta tsaya a kunne na kamar sanyi. “I need someone I can trust.”
Ni, Ramlah ‘yar talaka daga cikin gari na zama wacce ɗan sarauta ke cewa ya yarda da ita. Amma cikin zuciyata, na san wannan tafiya Nima sai nagi jindadin a tafi dani.
Yaransa suna gefe, suna kuka har yanzu. Wacce naji hajja tacewa Aminatu ta kamo hannunsa “papa, please make sure you gind the best doctor.!”
Umar ya ɗan juyo ya ce“He won’t die. Sai kwanansa yaƙare so just pray for him.”
Sai ya juya ya fita da sauri, yana kiran wani a waya. “Get the car ready. We’re moving now.”
A lokacin da ya fita, Hajja ta kama hannuna, tana cewa da ƙasa “Ki taya mu addu’a, Ramlah. Wannan bala’i ba ƙarami bane. Na san akwai wanda ke ƙoƙarin ganin ya mutu saboda kawai abun duniya kuma in sun kwantar da hankalinsu ai zai mutu ko lokaci nayi.” Na ce cikin murya mai sanyi
“Allah zai bayyana gaskiya, Hajja. Kaddarar ba ta wuce ikonsa.” Na ji hawayen da ta share yana fita da dumin soyayya. Soyayyar uwa da ɗa amma yau naga ta ɗa da mahaifi gaba daya umar baya cikin nutsuwarsa karshe ma yace wani abokinsa ke gayamasa ashe ba gidan sarautar ba.
Na kalli gadon Yarima na ƙarshe kafin su fita da shi. Jikinsa ya kwanta, amma hannunsa ya motsa kaɗan kamar yana son ya faɗi wani abu. Sai kawai na ɗan matsa kusa na riƙe hannunsa.” Sai kawai na ji muryar Umar daga ƙofar “ let’s go. It’s time.” Na juyo, na dubi fuskarshi, sai na ga yanayinsa ya cika da damuwa. Idanunsa sun cika da wani abu da ba zan iya fassara ba ko fushi ne, ko tsoro, ko ciwon zuciya kokuma damuwa?.
A hankali na isa cikin sashina, zuciyata har yanzu tana duka. Har yanzu muryar Umar tana yawo a kunne na yadda ya faɗi da murya mai cike da iko “ you’re coming with us.” Da gaske, kalmar nan ta zauna a zuciyata kamar wani abu mai nauyi. Amma ban da lokaci na tunani yanzu, dole in shirya tafiyar nan da ke jiranmu Yanzu.
Ina shigowa cikin sashen nawa, na ji ana yi min sannu da zuwa daga ‘yan aiki. Kowane ɗaya yana durƙusawa da ladabi, suna faɗin “Sannu da zuwa ranki ya daɗe.”
Na kalli Uwar Amarya, wacce ita ce babbar mai kula da sashen. Fuskarta cike da nutsuwa, Na ce mata da murya mai taushi, “Zamu yi tafiya da shi yanzu, Hajja tace in debo wayoyinsa, sai dai bansan inda suke ba.”
Murmushi tayi, ta ɗan ɗaga gira, sannan ta nuna min wata ƙofa da hannunta tana faɗin “Akwai ƙofa can bayan labule, ki danna key ɗin sau uku, zata buɗe. A cikin dakinsa suke.”
Nayi yadda tace. Na matso kusa da ƙofar, na danna maɓallin sau uku kamar yadda ta umarta, sai na ji ƙarar click ɗin buɗewa.
Na shiga… Wani irin kamshi ne ya bugi hancina. Kamshi mai launin sarauta haɗaɗɗun turaruka, ƙamshin oud da vanilla, sai sanyi mai laushi da yake fitowa daga air condition. Na tsaya na zuba ido. Wani sashe ne da ya ginu cikin tsari kujeru masu launin ruwan kasa, carpet mai kauri kamar auduga, bango mai hotunan tarihi na gidan sarauta.
Na ji kamar ‘yar kauye a cikin kasaitacciyar duniya.
Na fara dubawa ɗaya bayan ɗaya kan teburi, kan shelf, kusa da kujera. Amma ban ga wayoyin ba. Na ɗaga labule, na leƙa cikin drawer, har na duba ƙarƙashin kujera har yanzu babu.
Na kalli bene, na ga akwai matakala da ke hawa sama. Na hau cikin natsuwa, amma duk dakunan da na samu suna kulle. Na ƙoƙarta, amma babu wanda ya buɗe.
Na dawo ƙasa a hankali, numfashina ya ɗan yi nauyi. Na koma wajen Uwar Amarya nace
“Ban samu komai ba, na duba har sama.”
Ta yi murmushi mai cike da sanin ya kamata, tace “Kar ki damu, Hajja ta ce zasu ɗauka. Kiyi shirin ki kawai.” Na ce, “To.”
Na nufi dakina, zuciyata na cike da tunani. Ban san me zan ɗauka ba, ban ma san inda zan fara ba. Na tsaya na kalli kayan jaka, akwatuna, kayan alfarma. Na ce a raina, “Wallahi rayuwa da masu kudi akwai wahala. Komai nasu cikin tsari, har wahalar su tana da alatu.”
Na shiga bandaki na yi wanka da sabulun rose scent mai ƙamshi. Bayan na fito, na zaɓi doguwar abaya ta Morocco, wacce ta sha stones masu walƙiya. Na ɗauki ɗaya daga cikin bag dina na lefe, wanda na ji su Momy suna faɗin tsadarsa a lokacin bikinq. Na saka wasu abubuwa da zan bukata turare, ‘yar hijabi, da gyale. Ganin lokacin magariba yana gabatowa agogon bango ya nuna 5:30pm sai na ce da Uwar Amarya “Ki bani cucumber drink da ɗan cake, nasan kafin mu isa Airport sallar magariba zata riske mu.”
Ta amsa cikin ladabi, “To, ranki ya daɗe.”
Na koma cikin bandaki, nayi brush, sannan na fesa manyan turaruka masu tsada da ke kan madubina. Na danna ɗan kadan a wuyana da hannuna, har cikin ɗakina ƙamshi ya cika.
Nana hadiza
09030569336
[04/11, 10:47 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA BIYAR
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Na kalli kaina cikin madubi. Idona ya ɗan kumbura saboda kuka da damuwa, amma har yanzu na yi kyau. Na murmusa a hankali, “Ko da kuwa zuciyata cike take da tsoro, dole in tsaya da kyan fasali dan naga kowacce taci kwalliya ba kamar mu ba idan ana damuwa baka samun Nutsuwar shigar kirki.”
A lokacin wata baiwa ta turo ƙofa da hankali, tana ɗan rusunawa da ladabi “Ranki yadade, ana jiranki a babban sashen Hajja.” Na ce mata, “To.” Na kalli Uwar Amarya, wacce ke tsaye tana tattara abubuwa a gefe. Na yi mata sallama. Kafin in fita, sai ta juyo, ta ce “Ranki ya daɗe, ina son in baki shawara guda ɗaya. Nuna soyayyarki gare shi ita ce zata kara siye zuciyar su Hajja da yaransa. Kulawarki kuma zata sanya su ƙara kaunarki.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, ta ɗan matsa kusa da ni, tana faɗin cikin muryar da take kama da sirri “Ki yi ƙoƙarin nuna babu kamarsa duk duniya. Ki nuna soyayya sosai, cikin salo da ladabi. Kuma kafin kiyi magana, ki taunata sosai. Kalma ɗaya da ta fito daga bakin mace mai nutsuwa, tana da ikon rusar zuciya fiye da makami.”
Na tsaya ina kallonta, kalamanta suna shiga zuciyata kamar ruwa. Sai na yi murmushi cikin ladabi nace “Na gode, Uwar Amarya. Zan kiyaye.”
Ta yi murmushi, ta ɗan dafa kafadata “Allah ya taimakeki, Ramlah. Ki tuna, fadar sarauta ba wurin wasa bace amma mace mai natsuwa tana iya zama sarki a cikin shiru.”
Na yi mata godiya, sannan na fita cikin nutsuwa. Iskar waje ta buso fuskata, ƙamshin turaren sassaka na gidan ya haɗu da iska mai sanyi. Rana ta soma faɗuwa, gefen sararin sama yana canzawa zuwa ja mai ɗan duhu.
A hankali na taka hanya zuwa babban sashen Hajja, inda Abba yake jiranmu.
Muna isa filin jirgin sama na Royal Terminal, rana ta riga ta faɗi, sararin sama ya cika da hasken fitilu. Wani iska mai ɗan sanyi ke busowa daga arewa, tana ɗauke da ƙamshin mai da kankara daga injinan jirage.
Ni, Ramlah, na fito daga motar cikin nutsuwa, sanye da doguwar abaya ta Morocco mai sheƙi, da gyale mai launin toka da ruwan kasa. A gefe ɗaya Hajja ke tafiya, tana daure da ɗan mayafi na silk mai launin royal blue, fuskarta cike da natsuwa da daraja. A gefe guda kuma akwai Abba ɗan’uwan Asad, wanda ake kira da yarima abba, mutum ne mai hankali shima mai cikakken hali irin na masu iko siriri.sanye da farin agbada da hula mai launin ja.
Jirgin da zai tafi da mu Royal Falcon X, private jet ɗin Yarima Asad ya tsaya a can bakin filin jirgi, yana sheƙi kamar gwal a ƙarƙashin hasken fitilun dare. Jikin jirgin ya ɗauki tambarin “House of Emirate Royal Air Fleet”. An rubuta sunan Yarima a jikin gefen jirgin da zinare mai launin champagne gold
“His Highness, Prince Asad Ibn babangida”
Hankalina ya tsaya a kan wannan rubutu na ƴan daƙiƙu. An shimfiɗa jan tabarma daga ƙofar jirgin har zuwa inda muka tsaya. Mutanen fadar sarauta da jami’an tsaro suna tsaye a gefe, kowanne cikin uniform ɗin da ke ɗauke da tambarin gidan Asad zaki mai ƙaho biyu da tutar a baya.
Umar ya fito daga cikin wata motar Range Rover Vogue, sanye da farar suit da rigar ciki mai launin navy blue. Yana tafiya cikin natsuwa, amma kowanne mataki nasa yana ɗauke da iko da kwarjini. “Everything ready?” ya tambayi wani cikin turanci, yana duba agogo a hannunsa. “Yes sir, all clear. The pilot’s waiting.”
Na tsaya a gefe, ina kallo. Gaba ɗaya filin jirgin ya bayyana kamar wani movie set fitilu, motoci masu sheƙi, masu tsaro da ke magana ta walkie-talkie, da ƙamshin mai da iska ke baza wa.
Hajja ta kama hannuna tana cewa cikin murya mai laushi, “Ramlah, kiyi hakuri da wahala. Wannan tafiya dole ce shiyasa naso abarki agida umar yace ai dolensa ce ke tunda matarsa ce ke da ke za’atafi.”
Na murmusa da ɗan ƙarfin hali, “ Hajja Hankalina bazai kwanta ba nima idan baa je dani ba bazan taba samun nutsuwa ba Insha Allah Allah zai bashi lafiya.”
Abba kuwa yana tsaye yana magana da wani babban jami’in tsaro, yana faɗin, “Ka tabbatar an saka ‘double check’ a kan bag ɗin equipment ɗin likitoci. Bana son a sake irin abin da ya faru.”
Jami’in ya gyaɗa kai, “Yes sir, everything has been re-scanned.”
Cikin mintuna kaɗan, aka buɗe ƙofar jirgin. Matattakalar jirgin ta sauka, hasken cikin jirgin yana walƙiya. Na kalli Hajja ta yi addu’a a hankali kafin ta hau. Na bi bayanta da nutsuwa, zuciyata na tsalle-tsalle to ban taɓa hawa private jate na.
Da muka shiga cikin jirgin, na tsaya na zuba ido abin mamaki!
Jirgin ya fi gidajen mutane da yawa kyau. Kujeru ne masu launin cream white leather, aka ɗora musu gold-plated armrests. A tsakiyar jirgin akwai ƙaramar living room mai teburin gilashi da tulin fure a tsakiyarta.
Hasken cikin jirgin ya kasance mai sanyi, kamar rana da take faɗuwa a bakin teku.
Sai na ji Umar yana magana da ɗan dariya da pilot, yana cewa“Make sure we land straight at Johns Hopkins, Baltimore. We don’t have time for stopovers.”
Pilot ɗin ya amsa da ladabi, “Yes Your Highness, direct flight thirteen hours.”
Na zauna kusa da taga. Na kalli hasken fitilun filin jirgi a waje, suna walƙiya. Umar ya zauna a gaban Hajja, yana ɗan matsar da agogon hannunsa. Ya dubeta cikin ladabi, “Grandma, are you comfortable?” Ta murmusa, ta ce da Hausa mai natsuwa, “Alhamdulillah, Umar. Ni dai addu’a nake, Allah ya tsare mu.” “We’ll be fine,” Umar ya amsa da murya mai taushi. “Dad will make it. Inshaa Allahu.”
Na lura da yadda Umar ke ɗan lumshe ido duk lokacin da aka ambaci mahaifinsa. Idanunsa suna cike da damuwa, amma yana ɓoyewa da murmushi na ƙarfin hali.
Wani ɗan lokaci ya kalli ni, sai ya ce “ Small mom, you’ve been quiet all day.” Na ɗan lumshe ido nace cikin ladabi, “Na gaji ne kadan, ranka ya daɗe.”
Ya ɗan murmusa a hankali, yana kallona kai tsaye murmushin da ya ɗan girgiza min zuciya. “Try to rest, okay? It’s a long flight.”
a gyaɗa kai, na dubi taga. Jirgin ya fara motsi a hankali. A waje, na ga fitilun filin jirgi suna raguwa a hankali, sannan na ji joar mai ƙarfi daga injin.
A hankali jirgin ya ɗaga sama, duniya ta fara yin ƙanƙanta a ƙasa gidaje, hasken tituna, da filin jirgi duk sun koma kamar ƙura.
Hajja ta lumshe ido tana karatun Ayatul Kursiyyu. Abba ya jingina da kujera, yana rike da tasbaha. Umar yana kallon taga, hannunsa ya riƙe kofi na black coffee, yana tunani.
Na kalli sararin sama farin gajimare ne kawai ke gudu, hasken wata yana haskawa a gefe.
Sai na ji Umar ya ce da murya mai laushi, yana kallon ƙasa ta taga “You see that? That’s the city … small from here, right? But that’s where all our destinies started.”
Na dubi inda yake kallo, sannan nace cikin nutsuwa, “Eh, kuma daga nan ne komai zai sake farawa.”
Ya juyo, yana kallona da mamaki, sai ya murmusa“You’re right.” Sai na lumshe ido.
Lokacin da jirgin Royal Falcon X ya shiga tsakiyar sararin duniya, dare ya gama lullube komai. Hasken cikin jirgin yana ta sheƙi cikin sanyi, ƙamshin turarukan Chanel No. 5 da Tom Ford Oud Wood suna gaurayuwa da iska mai ɗan ɗumi daga air conditioner.
Na jingina da kujera, idona na lumshe, amma zuciyata ba ta iya samun nutsuwa ba. Tunanin komai na jiya ya cika kaina asibiti, foda, Waziri, da kuma muryar Umar da take sake yawo a cikin kunnuwana“You’re coming with us.” Sai na ji wata murya mai laushi a gefe “Small Mom, are you awake?”
Na buɗe ido a hankali. A gabana suna tsaye Mata guda biyuNawal da Amina. Duka cikin shigar mata masu kuɗi ne, abaya designers na Dior da Elie Saab, gashinsu a lulluɓe da hijabi mai launin ja.
Nawal ce ta fara magana, tana kallona da murmushi mai cike da ladabi “We’re sorry, Small Mom. Jiya hankalinmu atashe yake, that’s why bamu gaisa ba.”
Amina, wacce take gefenta, ta gyaɗa kai, idonta cike da nadama. “We were so scared, wallahi. Yanzu muka dan natsu.”
Na kalle su na ɗan murmusa, zuciyata na raguwa daga tashin hankali. “Ba komai, Allah ya bashi lafiya.” Dukansu suka ce a lokaci guda, “Ameen.”
A nan ne Nawal ta zauna kusa dani. Tana da sanyi a muryarta, amma idan ta yi magana zaka ji a cikinta akwai asalin sarauta. Tace cikin nutsuwa “Yau kam sai mu zama friends, Small Mom. Jiya gaskiya I thought you didn’t like us.”
Nana hadiza
09030569336
[04/11, 10:47 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Na murmusa kadan, na ce cikin ladabi, “ Kawai dai yau abubuwa sun ruɗe kowa.”
Amina ta yi dariya kadan, “Wallahi gaskiya ne. Nawal da kuka ta wunj jiya.”
Muka yi dariya a hankali. Hira ta fara gudana kamar yadda na dade ban ji irin ta ba ba ta matsin lamba, ba ta ƙiyayya, ba ta fushi.
Nawal ta ɗan juya tana kallo ta taga, ta ce “You know, I always thought you’re too quiet. But now I see, you’re just… peaceful.”
Na yi murmushi mai sanyi, “Ai kuwa shiru ya fi magana a wasu lokuta.”
Ta yi dariya, “That’s deep, Small Mom. You sound very calm.”.
Har Hajja ta juyo daga inda take zaune, ta ce cikin muryarta mai nutsuwa “Allah yayi muku albarka, ku bar ta ta huta yanzu. Tayi aiki da yawa jiya.”
Nawal ta miƙe cikin girmamawa, ta ce da murmushi, “Yes Hajja.”
Sai ta juyo gare ni, ta ce cikin ladabi “Small Mom, we’ll talk more when we land, okay?”
Na amsa da murmushi, “Insha Allah.”
A wannan lokaci ne aka kawo mana abinci.
Wani ɗan saurayi ne cikin uniform ɗin Royal Air Service, sanye da farin riga mai ɗauke da tambari . Ya zo da tray mai ɗauke da abinci iri-iri steak with mushroom sauce, jollof rice with grilled chicken, da kuma fresh salad da aka yi da ƙamshin lemon zest. A gefe kuma akwai fresh juice na pomegranate da cucumber smoothie.
Na kalli yadda aka shirya teburin cikin jirgin komai tsaf, faranti masu kyau cokula. Abin kamar a cikin fadar wani sarki na Turai.
Hajja ta ɗan murmusa, ta ce da ni, “Ramlah, ki ci abinci. Karki zauna da yunwa a hanya. Tafiya ce mai nisa.”
Na amsa da ladabi, “To, Hajja.”
Sai na fara ɗan ɗibar abinci a hankali. Duk da damuwar da ke cikin zuciyata, ban iya hana kaina jin daɗin yadda komai yake da tsari. Haka su masu kuɗi ke rayuwa komai nasu cikin salo da alatu, amma zuciya na iya zama cike da ƙunci kamar ta talaka.
Da na ɗan ɗiba kadan, sai na kalli taga. A waje, sararin sama ya fara samun haske hasken safe yana bayyana a can bayan gajimare. Na ji muryar Umar daga nesa yana magana da ɗan turanci “Once we land, the ambulance team should be ready. I want the doctors to take him straight to Johns Hopkins emergency wing. No delays.”
Ya juyo ya dubi mu, sannan ya ce da Hajja “Grandma, we’ll be in the States in about six hours. You should get some rest.”
Ta gyada kai, “To, Umar. Allah ya sauke mu lafiya.”
Ya ce da girmamawa “Ameen.”
Na kalli yadda yake tsaye tsantsar iko da natsuwa, amma idan ka lura sosai, zaka ga wani nauyi yana kansa.
Sai Nawal ta leƙo daga gefen baya, ta ce da dariya “Small Mom, when we get to America, I’ll take you shopping. You must have American coffee with me!”
Na yi dariya a hankali Nace Mata “Thank u.”
Sai ta ce, “It’s a promise!”
Na murmusa, na kalli Hajja. Ta yi murmushi kadan tana faɗin “Allah ya haɗa zukatanku..”
Na amsa cikin sanyi, “Ameen, Hajja.”
A lokacin, jirgin ya fara sauka a hankali, ƙarar injinsa na raguwa. A nesa, hasken birnin ya fara bayyana kamar taurari a ƙasa. Zuciyata ta cika da mamaki wannan duniya ta masu kudi, jirgi na sarauta, birnin Amurka amma ni ‘yar talaka, ina cikinsu.
Jirgin ya sauka cikin natsuwa. A waje, birnin Baltimore ya bayyana kamar wani haske mai tarin yawa hasken tituna, motoci, da tsakar dare wanda ke rufe ganuwar manyan gine-gine. A fagen jirgin, mai jirgin pilot ya bada godiya sannan jami'an fadar suka fara shirya kayan.
Bayan mintuna kaɗan, an buɗe ƙofofin Royal Falcon X. Jirgin ya miƙe numfashi kamar mutum da ya yi sallama kafin fita. Masu gadin filin jirgi da jami’an tsaro na asibiti sun tsaya suna maraba. An yi tanadin ambulance biyu, masu ɗaukar kayan ICU, da wata ƙungiya ta medical escort wacce ke tare da portable ventilator, defibrillator, da medication kit duk an rubuta sunayen kayan da launin medical-grade.
Umar ya tashi, ya yi rarrabuwar kulawa cikin sauri, wanda ya nuna cewa shi mutum ne da ya saba da irin waɗannan tafiyoyi. Ya janyo hankalin pilot, ya dinga magana cikin turanci “Make sure the ambulance is ready to receive him directly. No delays. Johns Hopkins emergency, straight to ICU.”
Pilot ɗin ya amsa, “Yes, Your Highness. They’ve cleared the tarmac. Ambulances are on standby.”
An taimaka wajen ɗaga Yarima Asad zuwa stretcher da safe, an ɗaure shi cikin hankali, an haɗa masa IV line da wasu na'urori masu kima. Kayan likitoci sun kasance cikin isothermal cases, an san inda kowanne abu yake epinephrine, activated charcoal, IV antibiotics, da antidotes idan har poison ne.
A wajen ɗakin saukar jirgi, likitoci na asibitin Johns Hopkins sun zo da sannu. Suna sanye da scrubs masu tsafta, suna da ID badge da sunan asibiti. Kowa yana da tsari dai-dai kayan da za su tafi da mu, sama da su masu tsaro, da kuma jami'an fadar da ke magana da consulate liaison don tabbatar da takardu.
Umar ya kalli wanda ke jagorantar tawagar likitocin, ya faɗa cikin sauri “He is Prince Asad Ibn babangida. We need the emergency team ready full resuscitation on arrival. No media, no delay.”
Chief of Emergency ya gyaɗa kai, “Understood, Your Highness. We’ll move him directly to the resuscitation bay, then to ICU after stabilization.”
An sa shi cikin ambulance cikin hanzari. A gefen mota, ni da Hajja da Abba sadu Nawal muka hau follow car domin a bi daidai. A lokacin, zuciyata na rawa saboda ganin yadda ake jan abu a hankali, na ji Umar yana kira cikin turanci a waya “Get me Dr. Henderson. I want a toxicology specialist on standby. Prepare ICU bed, check the labs and blood bank. Move fast!” Sai ya katse, yace da mu cikin murya “We’ll meet them at the hospital. Stay close.”
Hospital ɗin Johns Hopkins ya karɓe mu kamar yadda ake yi wa manyan marasa lafiya. Sun shirya resuscitation bay tare da cardiac monitor, portable ventilator, da complete IV setup. Sun fara duba vital signs BP, pulse, SpO2, respiratory rate. An yi ECG cikin sauri. Yanayin dakin ya ɗan sanyaya zuciya haske mai tsabta, fararen labulaye, da motsin likitoci masu kwarewa.
Chief of Emergency Dr. Henderson ya bayyana cikin gaggawa, ya duba Asad cikin ƙwarewa, yana umarni “Start with airway, breathing, circulation. Give 100% oxygen, establish two large-bore IVs, draw blood for toxicology, full blood count, electrolytes, LFTs, renal profile. Start activated charcoal if within window.”
A cikin wannan lokacin, Dr. Musa, wanda ya bi mu daga can, ya yi magana da Dr. Henderson da turanci “We discovered a suspicious substance in his IV bag possible poisoning. We need a full toxicology panel and immediate gastric decontamination if indicated.” Dr. Henderson ya amsa cikin nutsuwa: “We’ll proceed. We have the antidotes and supportive care. Stay available for transfer to ICU once stabilized.”
A hankali, asibitin ya yi abubuwa nurses sun hada IV fluids, na’urar infusion pump ta fara aiki, ana shigar da drug name (antidote) a hannu. Ana auna urine output, ana saka catheter inda ya cancanta. Sun fara allunan activated charcoal in case oral ingestion ne, amma idan IV ne, za a yi enhanced elimination protocols da haemodialysis idan ya wajaba. Wannan tsarin yana nuna matuƙar kwarewa da shirin rigakafi na asibiti mai daraja. A cikin waɗannan abubuwan ne na ji Umar jiƙinsa yayi sanyj har yana share hawaye su nawal daman duk kuka sukeyi nikam nakasa kukan sai zuciyata dake zafi sai naji umar yace “Keep me posted. I want hourly updates. No one leaves the room without my say-so.”
Hajja ta rike hannunsa, tana matso kusa da gadon mahaifin, tana addu’a cikin sauti. Abba ya tsaya kusa da ni, yana kallon yadda likitoci ke aiki da ƙwarewa. Bayan an stabilise shi rage arrhythmia, kara oxygenation, da tabbatar da cewa BP ya koma daidai an tafi ICU. A nan ne za a ci gaba da rigakafin gaggawa continuous monitoring, IV drips, testing for specific toxins (heavy metals, organophosphates, or pharmaceutical overdose). Lab ɗin asibiti ya fara aiki da ƙarfi toxicology screen, blood cultures, da sauran gwaje-gwaje. Kowane sakamako zai iya zama muhimmin hujja a binciken tsakanin asibiti da gidan sarauta.
Nana hadiza
09030569336
[05/11, 8:33 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Bayan an tabbatar da cewa Yarima an mika shi ga ICU, an shirya ragamar sauran mu musamman Hajja da ni dasu nawal domin a kai mu hotel ɗin da aka tanada. Wannan hotel ɗin ba na kowanne ba ne an yi mata tanadi a yanayin five-star suite, domin tsaro da kuma damar samun nasu wurin hutawa kafin a fara shiri na dogon gwaji. An kira hotel ɗin The Inner Harbor Presidential Suites wani wuri mai kyan gani, yana kan bakin ruwan Baltimore, ana samun tsaro na musamman, private entrance, da concierge service wanda ke sarrafa duk abin da fadar zata buƙata.