Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 29

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 29

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 29: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 29. A cikin motar da ke biye da ambulance, naji Umar ya ce cikin…

4,434 words

A cikin motar da ke biye da ambulance, naji Umar ya ce cikin turanci “We’ll check into the suite for now. I want Dr. Henderson to report directly to me every hour. And ensure the consulate is involved paperwork must be clean.” sannan muka yi hanya zuwa hotel. Daga waje, The Inner Harbor Presidential Suites na bayyane da fitilu masu walƙiya, masu tsari kamar gidajen manyan masu iko. An bamu tsari na musammansecurity clearance, private elevator get-in to our floor, da kuma a suite ɗin akwai kitchenette, office table, da bedroom. Na zauna kusa da taga, na kalli Baltimore waterfront yayin da ruwa ke haskaka. A wannan lokacin, na fahimci cewa komai yana tafiya cikin tsari likitoci sun fara aikin su cikin ƙwarewa, asibiti ya shiga cikakken yanayi, kuma mu a hotel muna da tsaro da duk wani abu da za mu bukata.

Tun daga lokacin da ƙafafuna suka taka cikin katafaren The Inner Harbor Presidential Suites, sai na ji wani irin sanyi ya ratsa jikina. Ginin ya fi tunanina girma da tsari. Fitilun chandelier da ke rataye daga sama suna walƙiya kamar taurari da suka sauka ƙasa.

Ƙamshi mai sanyi yana fita daga diffuser ɗin da ke gefen kofa ƙamshi mai launin oud, rose, da amber.

Gaba ɗaya wurin ya cika da natsuwa, amma natsuwar nan ce irin ta masu kuɗi, wadda ke da nauyi da alatu. Reception floor ɗin ya cika da kujerun fata masu launin baki, bango kuwa an kawata shi da hotunan manyan gine-ginen Amurka da kasashen larabawa.

A zuciyata, sai na ji kamar bana a cikin duniyar da na sani. Wannan ba gidanmu bane wannan wata duniya ce daban, mai launin kuɗi, iko..

An bamu tarba da kyau sosai. Masu aikin hotel ɗin sun durƙusa suna faɗin“Welcome to The Presidential Suites, Your Highness.”

Na kalli Hajja wadda take tafiya cikin natsuwa, da Abba wanda ke gaba da mu, yana magana da wani babban bako mai sanye da three-piece suit da ake kira Wambai shine yayansu gaba daya ashe har yakarasu kuma ansanar da mai martaba ma yana tafe.

Mun gaisa da ladabi. ya kalleni da murmushi mai nauyi, yana faɗin “Ku huta yanzu. Komai zai dai-daita. Umar ya shirya komai.”

Hajja ta amsa da ladabi, “Insha Allah sannu da kokari ashe har ka iso muma mun jira a asubuti ne.”

Sai Nawal ta ce wa umar “Papa, can we share a room together? Me and Small Mom.”

Hajja ta dubeta da murmushi, “To shikenan, sai ku rabu kamar haka ni da Amina a ɗaya, ke da Ramlah a ɗaya.”

An kai mu zuwa bene na goma sha huɗu, inda suite ɗinmu yake. Lif din da muka hau yana da gilashi mai bayyana fitilu yana juyawa a hankali. Da muka fito, ban iya boye mamakina ba. Ɗakin ya yi kyau fiye da yadda zan iya faɗa.

Living area ɗin cike da kayan Versace Home, sofa mai launin fari, labule masu walƙiya, madubi masu kyau, da carpet mai launin ivory cream. A gefe akwai kitchenette mai walƙiya kamar wajen shiryen talabijin.Na tsaya ina kallon komai kamar wacce ta fito daga ƙauye.

Sai Nawal ta juyo tana kallona, ta ga yadda hawaye ke zuba a idona. “Small Mom, why are you crying?” Na share kukan da sauri, amma sai ya ƙwace min.

Nace cikin muryar da ke rawa, “Sis, I’m scared sosai… Wallahi ina jin tsoro. Bana so wani abu ya same shi.”

Nawal ta matso da sauri, ta riƙe hannuna da taushi, tana kallona da tausayi. “Don’t be scared, Small Mom. Allah zai bashi lafiya. I wish we could just find who did this.”Na kalli idonta, na ga gaskiya a cikinsu. Amma ban ce komai ba domin ni dai na san wanda ya yi.

Waziri ne.Amma sai na kama bakina, na bar zuciya ta faɗi cikin shiru: “Sai lokacin da gaskiya zata bayyana da kanta.”

Bayan mun yi wannan tattaunawar mai taushi, Nawal ta shiga bandaki ta yi wanka. Bayan ta fito, ta sa riga mai launin ruwan shudi, tana busar gashinta da tawul. Sai na ji ta ɗauki waya tana magana da Papa cikin turanci “Papa, we don’t come with anything fa. Even Small Mom didn’t bring clothes. We need to buy something. Okay, we’ll go to the mall.”

Ta kashe wayar tana murmushi, sannan ta ce da ni cikin farin ciki “Small Mom, let’s go! Suna kasa suna jiranmu.”

Na kalli kaina a madubi, na ga nagaji sosaii, amma ban so in tsaya suga kamar banda ɗa’a Na ɗan gyara abayar da nake sanye da ita, na ɗauki bag ɗina, muka fita tare da ita.

Mall ɗin da muka je The Gallery Mall, Baltimore wani abu ne daban. Fitilun da ke kan rufin mall ɗin suna kyalli, ƙamshin perfume, kayan sawa, da sautukan kiɗan turanci suna gaurayewa cikin gurin.

Mutane kowa cikin salo da kyan jiki suke tafiya mata cikin dogayen riguna na designers, maza cikin suits, wasu kuma cikin luxury casuals.

Na ji kamar bana cikin jama’a ni dai Ramlah ce yau ina tafiya da ‘ya’yan Yarima a cikin mall ɗin Amurka. Na ga Nawal da Amina suna tafiya suna duba boutique ɗaya bayan ɗaya, sai ɗauka suke, su ce, “We’ll take this. And that one too.” Su masu kuɗi kenan ba sa tambayar farashi. Farashi ba su bane ke duba kuɗi, kuɗi ke duba su. Na tsaya a gefe ina kallon kaya riguna masu wasu abaya masu buɗewa, wasu kuma designer dresses masu tsadar gaske. Amma babu rigar da zan iya sakawa ta rufe jikina yadda ya kamata.

Amina ta juyo, ta kalle ni, tana faɗin da murya mai sauti “Small Mom, lafiya baki siya ba?”

Na ɗan murmusa, nace cikin sanyi, “Ai ban ga kayan da zan iya sakawa ba. Dukkansu sai yan kantii.”

Nawal ta tsaya, ta ɗan yi tunani, sannan ta ɗan matsa kusa da ni. Ta ɗauki wata doguwar abaya mai ɗan buɗewa amma da inner mai kyau a ciki, ta miƙa min tana murmushi “This one will suit you, Small Mom. Look simple but classy. You’ll look perfect.”

Na karɓa cikin ladabi, na ce“Na gode, Nawal.”

Ta murmusa sosai, “You’re welcome. You deserve to look like who you are family.”

Kalmarta ta ƙarshe ta tsaya a kunne na family.

Na kasa motsawa na ɗan lokaci. Idona ya kaɗa saboda kalmar nan ta motsa wani abu a zuciyata. Na ɗan murmusa, zuciyata ta faɗa cikin sanyi. Amina ta ɗauki kaya da yawa, Nawal ma ta zabi wasu. Ni kuma, na tsaya da wannan guda ɗaya abaya aikuwa suka shiga nemarmun suna ɗibarmun kala kala sukaje bangaren cream suma sannan takalmi komai dai haka muka siyo.

JBayan awanni biyu da muka shafe a cikin mall, muka dawo The Inner Harbor Presidential Suites da jakunkuna masu ɗauke da kayan sawa. Nawal da Amina suna dariya, suna magana kamar ‘yan uwa da suka dade ba su hadu ba. Ni kuma, duk ina murmushi, zuciyata tana tunanin asibiti ko likitoci sun samu mafita.

A lokacin da muka shigo cikin sashenmu, hasken dakin ya yi sanyi, ƙamshin turaren jasmine yana yawo cikin iska. Na ajiye kayan a gefe, sai na zauna a bakin gado, na lumshe ido.

Nawal ta juyo ta kalle ni, ta murmusa, ta ce“Small Mom, you look tired. Ki huta kinji?”

Na ɗan murmusa, “Eh, zan dan huta.”

Nawal ta tsaya gaban madubi tana night routine ɗinta tana shafa cream, tana gyara gashi, tana fesa turare mai sanyi Ina kallonta daga inda nake kwance, amma saboda yadda kaina ke ciwo, ban iya ce mata komai ba.

Sai na rufe idona cikin sanyi, na ji sanyin iska daga air conditioner yana busa fuskata.

Haka barci ya ɗauke ni cikin tunani.

A tsakiyar dare na tashi. Dakin ya yi duhu, hasken farin wata yana shiga daga taga yana bugun bango. Na ji numfashin Nawal yana daidaituwa tana barci cikin nutsuwa.

Na zauna, na ɗan sha ruwa, sannan na nufi bandaki.

Bayan na fito, na shimfiɗa sajada a gefen daki, na yi sallah da addu’o’ina cikin natsuwa.

“Ya Allah,” na faɗa cikin murya mai rauni, “ka ƙara masa lafiya. Ka bayyana gaskiya. Ka bani ƙarfin zuciya a cikin wannan kaddara.”

Na gama, na zauna na jingina da bango. Idona ya cika da hawaye, amma zuciyata ta yi sanyi sanyi irin wanda addu’a ke kawowa.

Da safe, hasken rana ya shiga dakin Na ji ƙarar ɗan tsuntsu a wajen taga, yana yi kamar yana murna da sabuwar rana.

Na yi wanka, na saka rigar da muka siya jiya abaya mai launin cream gold. Nawal ta fito daga bandaki sanye da riga mai launin mint green, tana murmushi.“Good morning, Small Mom.” Na amsa, “Good morning.”

Mun shirya gaba ɗaya, muka sauka zuwa breakfast hall. Wurin ya cika da ƙamshi

A kan tebur, aka kawo mana abincin safe fresh orange juice, croissants, honey butter, scrambled eggs, da green tea.

Na zauna kusa da taga, Hajja da Amina suka shigo cikin nutsuwa. Hajja ta ce

“Ku ci abinci, yara. Allah ya sa mu ji alheri yau.”

Muna cikin hakan ne sai wayar Nawal ta fara ringing. Ta duba ta murmusa, “Umar ne.”

Ta ɗaga cikin farin ciki, ta kunna loudspeaker.

Muryarsa ta fito daga wayar mai ɗan kauri amma da sanyi “Good morning everyone.”

Hajja ta amsa, “Lafiya lau, Umar. Yaya asibitin?”

Shiru na dan lokaci, sannan muryarsa ta dawo “He’s awake, Grandma. Dad has regained consciousness. We talked this morning. He recognized me.”

Sai a lokacin na ji zuciyata ta tsaya cak, sannan ta buga da ƙarfi.

Na dafa kirji, hawaye suka cika idona. Nawal ta fashe da dariya tana murna, “Alhamdulillah!”

Amina ta ɗaga hannaye tana faɗin, “Ya Allah, mun gode!”

Hajja ta share hawaye da sauri, tana murmushi, “Allah ya ƙara masa lafiya. Alhamdulillah.”

Ni kuwa ban iya magana ba sai murmushi kawai. Na ce a hankali “Allah ya ƙara masa lafiya da ƙarfin jiki.”

Umar ya ci gaba da magana daga wayar:

“The doctors said he’s still weak, but he’s responding well. Dr. Henderson said it’s a miracle. In the next 3days, you’ll be allowed to see him.”

Sai Nawal ta ce cikin farin ciki, “Did he ask of us?”

Umar ya murmusa daga can “Of course he did. He asked of Grandma, Abba, and you two. And yes” (ya ɗan tsaya) “he mentioned Small Mom too.”

Na ɗago kai, idona ya haɗu da na Hajja.

Ta yi murmushi mai zurfi, ta ce “Kin ji kuwa, Ramlah? Har ya tambaye ki. Allah yakara masa lafiya..”

Na sunkuyar da kai da kunya, zuciyata tana tafarfasa. Ba don wani abu ba, sai saboda kalmar “ya tambaye ki.”

Wani abu mai sanyi ya ratsa jikina, kamar wani sirri da Allah kaɗai ya sani.

Umar ya ci gaba “Grandma, make sure everyone rests today. I’ll send the escort to bring you here. We’ll have limited access, so only family will enter the ICU.”

Hajja ta ce, “To, Allah ya taimaka. Ka kula da kanka ma, Umar.” “Don’t worry, Grandma. I’m fine. Just tired.” Ta ce, “Ka ci abinci?” “I will, Grandma. I promise.”

Wayar ta katse da murmushi daga kowa.

Hajja ta kalleni tana cewa “Ramlah, kin ga yanzu kin fara walwala. Jiya koda magana sai da ƙyar kike yi.”

Nawal ta ce da wasa, “Hajja kiga Small Mom fa, tana dariya yanzu!”

Na yi murmushi, na ɗan boye fuskata da gyale. “Eh, yanzu na samu nutsuwa.”

Sai dai wani abu ya ja hankalina yadda Nawal da Amina suke da sauƙin hali.

Ba su da takama kamar yadda nayi tunani. Hatta Mai Martaba, lokacin da muka gaisa da shi jiya, bai da girman kai. Suma haka suke kuma su ko abun sarauta basayi kwatakwata sun maida hajja kamar kawarsu

Na kalli su ina mamaki a zuciyata.

“Wannan ita ce sarauta? Sarauta mai natsuwa da soyayya, ba ta tsoro da bugun kirji ba?”

Sai na kalli Hajja, tana murmushi cikin shiru, tana shaƙar green tea.Na ɗaga kofin shayi a hankali, na sha kadan.

Nana hadiza

09030569336

[05/11, 8:33 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Washegari da sassafe, hasken Baltimore ya ratsa cikin gilashin ɗakunanmu, yana gauraya da sanyi mai ɗan taushi daga iska.

Wani irin kwanciyar hankali ne ya lullube ko’ina, wanda ke ɗauke da kamshin lavender daga turarukan da aka ajiye a cikin diffuser ɗin ɗaki.

Kowannen mu ya tashi da nutsuwa Hajja tana dakin tana sallah, Amina tana kiran yaranta ta video call, Na fito daga bandaki bayan na yi wanka, na zauna ina azkar a hankali. Zuciyata cike da natsuwa, amma har yanzu akwai ƙanƙanin fargaba. Sai kawai ƙofar ɗakin ta buɗe, Nawal ta shigo tana ɗauke da turare a hannu, mai kamshin gaske kamar ma dai siya tayi sai kuma ta kalleni tace “Small Mom,” ta faɗa cikin murmushi, “kinga Papa har yanzu bai kira ba. Muje ki rakani mall ɗin can, yanzu zamu dawo please.” Na ɗago ina kallonta, daidai lokacin da Hajja ta fito daga daƙinsu tana kallonmu da murmushi. Ta ce cikin muryar dattijuwar da ke da hikima, “Ke Nawal, baki jin tausayin jikinki ko? Bakya ganin cikin nan naki ya fara girma ne yawo yawo ko haris yaɓataki da son fita.?”

Nawal ta murmusa, tana wasa da mayafinta “To ai Grandma, cikin nawa fa baifi six months ba. I’m fine wallahi kuma kinsan ni banason zama guri daya ko.” Amina, wacce ke zaune a gefe tana tauna apple, ta ce “By the way, Haris yace zai zo gobe.” Nawal ta ɗaga gira cikin murna, “Really? You didn’t tell me earlier!” Sai ta ɗan ɓata fuska da wasa, tana murmushi “Haba Sis, you should’ve told me. At least I’d have prepared. Look at me, I’m not even looking good.” Na ɗago na kalleta da mamaki, a raina na ce “Su masu kudi ma suna da wannan irin korafi?” Sai na ji Nawal ta ce cikin wasa, “No, I must go to the spa today. My hair needs treatment. After that, we’ll just pass by the mall, okay?” Na murmusa kadan, “To.” Hajja ta yi dariya tana girgiza kai, “Ke Nawal, kin koya mata yawon nan naki. Ku daiyi a hankali. Kuyi addu’a kafin ku fita.” Nawal ta yi rolling da mayafinta, ta ce tana dariya, “Grandma, we’ll be fine. Wallahi we’ll be back soon.” Na biyo ta muka fita daga hotel ɗin, direban ya buɗe mana ƙofa.

Motar black Cadillac Escalade ce, mai sheki da kyan gaske. Spa ɗin da muka je AURA WELLNESS & BEAUTY LOUNGE wuri ne da yake kamar aljanna yayi kyau bantaɓa ganin gurin gyaran jiki mai kyansa ba. A ƙofar shiga, aka shimfiɗa carpet mai launin shuɗi, bango cike da hotuna kala kala, ga muma kamshi mai dadi da ya gauraya da sanyin ac.

Ma’aikata mata ne masu sanye da farin uniform da sunayensu a ƙirji. “Welcome, Mrs. Nawal. Welcome, Ma’am,” suka faɗa cikin ladabi. Nawal ta dubi manager, ta ce da Turanci cikin kwarewa “We’ll have full body treatment for two, please. Something relaxing, organic oils only.” Manager ta gyada kai cikin girmamawa, “Yes, ma’am. Right this way.” Aka kai mu wani sashe mai cike da sanyi da haske. Aka gyara mana gashi, aka wanke jiki da milk bath, aka yi massage mai taushi.

A lokacin da aka wanke kaina, Nawal ta tsaya tana kallona cikin madubi, ta dafa kafadata tana murmushi “Wow, Small Mom! I didn’t know you have such long hair. It’s beautiful, wallahi.” Na murmusa a hankali, “Thank you.

.” Ta ɗan murmusa, “You’re natural, and I like that.” Bayan an gama, muka ci light snack a lounge ɗin fruits platter da detox drink.

Sai muka nufi babban mall ɗin Baltimore.

Mall ɗin ya cika da mutane da hasken fitilo masu kyan gaske shaguna masu ɗauke da sunayen Louis Vuitton, Gucci, Dior, da Prada.

Muna tafiya, idona na sauka kan wasu phones masu kyau a shagon Apple Premium Store. Na tambayi Nawal cikin natsuwa, “Sis, me zaki yi da waya? Naga kusan uku a hannunki.” Ta yi dariya mai sauti, tana kallona cikin wasa. “You know, one for business, one for social, and one personal. Help me pick which color suits me most.” wato in kukaga nawal tayi hausa to tabbas subutar bakinta tayi daga ita har Amina da umar basa hausa idan sukayi hausar ma sai kayi tunanin ba su iya baniba.Na kalli display shelf, na nuna wata black iPhone 17 Pro Max mai launin baki a gefe. Na ce, “Wannan tafi kyau.” Ta murmusa, “You have good eyes, Small Mom.” “Okay, I’ll take that one. And one for you too.”

Na juyo da sauri, “Ni kuma?” “Of course. Yours is too local. You need a new one. You’re part of us now.” Na yi shiru, zuciyata ta buga. Ban iya ce mata komai ba. Sai kawai na murmusa kadan, “Na gode sosai.”

Ta ce da manager ɗin, “Add one more black, please. Same specs.” Manager ya ce, “Sure ma’am. That’ll be one thousand dollars each.” “It’s okay. Here’s the card.” Ta biya a nan take.

Na kalli fuskar Nawal da mamaki.

Duniyar dai masu kudi daban ce. Abin da zai sa talaka ya yi shekara yana tanadi, su sukan biya a minti guda kamar wasa.

Mun dawo gida, jiki duk gajiya amma zuciyata A suite ɗin, Umar na jiranmu cikin sutturar formal black suit. Yana kallon tablet a hannunsa, yana magana da Dr. Henderson a waya. “Okay, we’ll be there in an hour. Keep the room ready.” Ya ɗago idanunsa ya dubi mu, ya murmusa kadan “Perfect timing. You’re back. Dad’s ready to see you now.”

Amina ta ce da murna, “Alhamdulillah!”

Ni kuwa na kasa magana, sai murmushj da nayi Nawal ta miƙo min jaka, “Small Mom, ga wayarki. Plug it in before we go. You can set it up later.” Na ce mata okay. Na yi shiru, sai zuciyata ta cika da godiya da jin kunya lokaci guda. Na ce cikin sanyi, “Na gode sosai, Nawal.” Ta ce da murmushi, “Don’t thank me. You’re family.” Na ji wannan kalmar family ta sake shigar da wani sanyi a zuciyata.

.”

Bayan haka, na shiga bathroom na yi wanka, na fito cikin doguwar skirt da riga mai launin toka. Na saka jacket a sama kamar yadda naga matan Baltimore ke sakawa, saboda sanyi da iska. Nawal ta kalle ni ta murmusa, “Now you look like a queen.” Na yi dariya kadan..”

Lokacin da muka fito daga suite, convoy uku suna jiranmu a harabar hotel ɗin Motar Umar, black Mercedes Maybach, Motar security, da kuma Motar mu, Cadillac SUV mai sheƙi.

Jami’an tsaro na Amurka Na a tsaye suna bada girmamawa, suna buɗe ƙofofi cikin ladabi. Kamar yadda Hajja ta saba, ta fara shiga. Ni da Nawal muka biye da ita, Amina a baya.

Yayin da motar ke tafiya cikin titunan Baltimore, zuciyata tana rawa Nawal ta riƙe hannuna, tana faɗin cikin sanyi “Small Mom, I can’t wait to see him smile again.”

Na zauna a cikin motar na ɗan ɗaga gyale, zuciyata na tsalle kamar ta ƙaramin yaro. Wani ɓangare na zuciyata na son in hanzarta zuwa gare shi, wani kuma na tsoron abin da zai faru idan idonmu ya sake haɗuwa.

“Small Mom,” Nawal ta faɗa tana dariya, “don’t pretend. I can see it on your face you miss him.” Ta riƙe hannuna tana jan ni daga motar cikin wasa. Na murmusa kadan, “Ke dai Nawal kin cika wasa.” amina tafaɗa mata “Yes” ta ce tana dariya mai sanyi.

Na murmusa, Nace “ Allah ya ba shi cikakkiyar lafiya.”

A lokacin da muka isa ƙofar Johns Hopkins Hospital VIP Wing, an rufe hanya gaba ɗaya.

Motocin sun tsaya a tsari, jami’an tsaro suna buɗe ƙofa cikin ladabi.

Asibitin ya yi tsit. Har bangon gilashi yanata haskawa. A ƙofar shiga, Dr. Henderson yana jiranmu da wasu nurses biyu, yana murmushi cikin ladabi. “Good morning, Your Highnesses. The Prince is much better today. He’s been asking for you.” Hajja ta ce da farin ciki, “Alhamdulillah. Allah ya ƙara masa lafiya.” An bi mu zuwa ICU recovery suite, wani sashen musamman da aka gyara daga ICU zuwa dakin hutu mai tsada. Bangon dakin farin gilashi ne, kujeru masu kalar fari, furen white lily a gefe, da ƙamshin hospital-grade rose scent.

Mun shiga cikin ginin cikin natsuwa. Tsaro ya tsaya a bakin kofa, nurses suna gaishe da Hajja da ladabi Yana zaune a kan gadon, ya ɗaga kai lokacin da muka shiga.

Murmushi ya bayyana a fuskarsa murmushin da ya haɗa farin ciki, gajiya, da wani irin nutsuwa da sai wanda ya tsira daga ciwo yake da shi.

Na tsaya a gefe, zuciyata tana rawa.

Na ji kamar in nufi gare shi in rungume shi saboda farin cikin ganin sa cikin koshin lafiya.

Amma ganin su Hajja da sauran mutane, sai na yi ƙoƙarin ɓoye wannan jin dadi, na sunkuyar da kai cikin ladabi.

Nawal da Amina suka karasa cikin sauri suka rungume shi, suna dariya kamar yara. “Dad!” Nawal ta faɗa cikin farin ciki. Sai ya girgiza kai yana dariya, yana kallon cikinta, “Nawal, slow down. Look at you that baby is growing fast.”

Amina ta yi dariya. Hajja ta zauna kusa da shi tana murmushi, tana faɗin, “Alhamdulillah, kai lafiya tasamu.” Sai suka shiga tattaunawa, Hajja tana bashi labarin gida, yana amsawa cikin nutsuwa. Na zauna a gefe, ina kallonsu, zuciyata tana tafasa da jin daɗi da kunya lokaci guda.

Umar ya shigo daga waje, sanye da formal suit, yana duba agogo. “Dad, we need to keep it short. The doctor said no stress.”

Sai Asad ya ɗan murmusa, “Always the doctor’s soldier.” “It’s my job,” Umar ya ce yana murmushi.

Nawal ta ce da wasa, “Dad, please, don’t let Small Mom go back to that palace alone o. She’ll suffer!” Sai ta yi dariya tana kallo na.

“They’re too strict there. No fun, no peace.”

Nana hadiza

09030569336

[06/11, 9:35 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SABA'IN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Hajja ta yi saurin kallonta, “Lallai Nawal, kina magana agabana ko?” “Sorry Grandma,” Nawal ta ce tana dariya, tana turo baki. “But it’s true o. Take her to Dubai, Dad. Gidan Mai Martaba wahala ne fa.” Dariya ta kama Asad, har sai da ya ɗan rike kirji saboda murmushi. “Nawal, you never change.” Yafaɗa yana murmushi. Nima dai cikin raina naga gaskiyarta dan komai na gidan sarauta daban ne da zahiri. Ta “I’m just honest, Dad.” Ya ɗan kalleta cikin taushi, “Honesty with noise.”

Sai suka yi dariya gaba ɗaya.

Na zauna a gefe. Sai na ji Umar yace “Time’s up. Let’s go, everyone. Dad needs to rest.”

Na tashi daga inda nake zaune, ina shirin fita, lokacin ne Asad ya juyo ya kira ni da murya mai sanyi “Ramlah.” Na tsaya, zuciyata ta tsaya cak. Na ce cikin nutsuwa, “Naam, ranka ya daɗe.” Ya ɗan murmusa, “Zo nan.” Na matsa a hankali, zuciyata na bugawa.

Ya nuna kujerar da ke kusa da gadon. “Zauna a nan, you are not going with them ai.”

Nawal ta yi dariya, “Wai Small Mom kunyar Daddy kike ji? Kalli yadda kika tsaya kamar yarinya.” Na harareta da wasa, “Sisi kiyita tsokanata ko?.” Sai Asad ya murmusa, “Leave her, Nawal. I just want to see her smile.” Cikin sanyi na zauna kusa da shi, nesa kadan. Sai ya juyo da fuska, idanunsa suna kallona cikin natsuwa, “Alhamdulillah. Na ga murmushinki a zahiri yau.”Na kasa kallonsa kai tsaye, sai kawai na ce cikin sanyi, “Allah ya ƙara maka lafiya.” Ya jinjina kai.

Na ɗaga kai, idanuna suka haɗu da nasa.

Idanun sa suna cike da wani irin natsuwa Na kasa cewa komai. Sai dai zuciyata ta faɗa cikin nutsuwa mai nauyi irin ta soyayyar da bata buƙatar kalma.

Hajja ta kalle mu ta murmusa da fahimta, sannan ta ɗaga murya,

“Umar, mu tafi. Zamu dawo da safe.”

Suka fara fita ɗaya bayan ɗaya, sai Nawal ta tsaya kusa da ni ta radawa cikin kunnena “Please Small Mom, take good care of him for me.” Na yi murmushi kadan, “Kin san ba zan iya ba.” Ta ce da dariya, “Oh, you will.”

Sai ta juya ta rungumi mahaifinta da kyau.

“Dad, Allah yakara maka lafiya.”

Ya rike hannunta, yana kallonta da natsuwa,

“Ameen. Allah ya miki albarka ma, Nawal.”

Na tsaya ina kallonsu, cikin zuciyata na ce

“Sunada shakuwa sosai da junansu.” Da suka fita, dakin ya yi shiru.Sai ƙarar machine da ke duba numfashin sa kawai ke tashi.

Ya juya gare ni da murmushi mai taushi,

“Kin ga? Sun tafi. Shine zaki bisu ko? Ni na zauna nida wa? Kinsan hakurin da nayi kuwa.” Ya kalli ƙofar na ƙarshe da ta rufe, sannan ya sauke numfashi a hankali, yana murmushi mai natsuwa. “They are my happiness,” ya furta cikin murya mai taushi, yana kallona da ido.

“Bazaki taɓa samun matsala dasu ba, Ramlah. They’re all I have… they’re all I ever wanted.” Na kalle shi da murmushi mai rauni, zuciyata tana rawa, kalamansa suna shiga zuciyata kamar sautin zuma. “Gaskiya ne,” na ce da sanyi. “Sunada kirki, kamar ‘yar uwarsy haka suka daukeni.” Sai ya murmusa, “And you… you talk with them nikuma sai kina mun shiru ko..” Na sunkuyar da kai cikin kunya, “Ba haka bane… kawai ina jin kunya ne .”

A lokacin ne Dr. Henderson ya shigo cikin natsuwa, ya ɗauki tray ɗin magunguna, yana faɗin cikin ladabi“Your Highness, it’s time for your medication.”

Ya zuba masa ruwa, ya ɗauki ƙaramar allura, sannan ya duba ƙafarsa, ya yi masa injection a hankali. Sai ya dubeni da murmushi mai ladabi “He’ll feel sleepy in about thirty minutes. Don’t worry, ma’am.” Na gyada kai, “Thank you, doctor.” Ya fita cikin nutsuwa, yana rufe ƙofar da ta ɗan yi ƙara kadan.

Sai dakin ya sake yin shiru. Na ji muryarsa cikin sanyi, “Ramlah…” Na ɗago kai, “Naam?”

Ya ɗan ƙara lumshe ido kadan, yana kallona daga ƙarƙashin gashin idanunsa, “Please, go and lock the door.” Na tsaya na ɗan yi mamaki, “Door ɗin?” Ya murmusa da rauni, “Eh… ban son gab dinnan ko da minti guda.”

Zuciyata ta buga. Na tsaya na ɗan dafe rigata sannan na matsa a hankali na nufi ƙofar.

Kowane motsina yana jin kamar ana iya jin sa takun ƙafata, ƙaramin motsin zoben hannuna, ƙaramin ƙarar lock lokacin da na juyo maƙulli.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull