Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 44
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 44: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 44. Ya share hawayena da yatsunsa.Ya rad’a da murya mai laushi “Lafiya…
2,025 words
Ya share hawayena da yatsunsa.Ya rad’a da murya mai laushi “Lafiya ta ce. Abinmu biyu ne. Kaddararmu ce, ba taki kadai ba.”
Na jingina a kirjinsa ina jin bugun zuciyarsa mai nauyi, mai sa ni jin cewa rayuwa ba duka ta kare ba.Ya dora harshensa a gefen kunnena yana ce min“Ramlah… my love… my peace… ki tsaya ki rike ni.
Ni da ke ne har karshe.”A wannan daren, Asad ya nuna min irin ƙaunar da ban taba tsammani ba.Ba soyayya ta jiki ba.
Ya riƙe hannuna har na yi bacci.
Ya rike ni kamar abin duniya.Ya ce a hankali, kafin in rufe ido“Ki sani idan ba ma haihuwa ba, to ba laifin ki bane.
Kaddararmu ce mu biyu.”
Na yi bacci a kirjinsa ina kuka, amma wannan karon ba zan iya cewa hawaye ne na ciwo kadai ba.
Suna ɗanɗanon jin cewa ina da wani da ya tsaya a gefena, ko da duniya gaba ɗaya ta juya.
Ranar da Yaya Billy ta zo masarauta, har da yaranta guda huɗu, gida ya cika da ihu da dariyar yara. Na fito palon Hajja ina murmushi, ina rungumar kowane yaro ɗaya bayan ɗaya.
“Assalamu alaikum,” na faɗa ina sumbatar kakan, ɗan ƙarami mai shekara biyu.
Suka kurma dariya suna cewa, “Aunty Ramlah! Aunty Ramlah!”
Na ji wani abu ya tsinke a zuciyata ba ciwo ba, ba bakin ciki ba, sai dai kuma wata tambaya da na saba jefawa raina kowace rana “Shin ni fa nawa zai kira ni Mama?”
Na dan murje kaina domin kada hawaye su bayyana a idanuwana.
Yaya Billy ta shigo daga baya tana kallona da murmushin manya, riga ce a jikinta mai tsada, kamar sabuwar amarya.
“Ah-ah, Ramlah!” ta faɗa tana dariya, “Kin ga yadda nake koma kamar balarabiyar mace ko?.”
Sai ta matsa kusa dani, ta ɗora hannunta kan cikinta ta ce cikin dariyar da ba a boye kanta ba“Wai ni fa har yanzu jikina na sanin zafin haihuwa… amma ke… ba ma ke san zafin ciyo ba ko?”
Palon ya yi shiru kafin ta ƙarasa da wani murmushi “Ke fa ba kya sanin wahalan da mace ke sha wajen kawo yaro duniya.
Amma ai lokaci na Allah ne…”
Na yi murmushi.Murmushin da ya fara a lebena amma bai kai cikin zuciya ba.
JNa karye a ciki, amma ban nuna ba.
Firdausi da ke gefe ta ɗan kalle ni, ta kauda kai kamar bata son tashin hankali.
Na ce cikin sauƙin murya
“Allah ya raya mana su Yaya Billy. Allah ya saka muku alkhairi.”
Ta yi dariya irin wadda ba a gane ko dariya ce ta tausayin kai ko ta raini ba.
****
Ban manta ranar da na zauna cikin bandaki ina kuka ba.Na rike marata ina jin kamar zuciyata ta tarwatse.Shekaru goma… goma cif… amma babu labari.IVF sau 3.Hormones.
Fertility injections.HSG.Scan kala-kala.
Magungunan da suka sa jikina ya kumbura ya yi zafi.
Duk likitoci guda goma sha uku duk sun ce ina lafiya… amma Allah bai rubuta ba.
Lokacin da Hajja ta yi min zafi, lokacin da wasu matan masarauta suka yi gori, lokacin da na ji Billy ta ce min
“Ai ke baki san zafin haihuwa ba.”
Na kai hannuna cikin hijab dina na lumshe ido na ce“Ya Allah… ka bani abin da yafi yaro.”
Wata rana cikin dare, Asad ya rike hannuna yana share min hawaye yace “Ramlah, kaddarar mu ce. Ba taki kadai ba. Idan Allah bai ba mu ba, mu godemasa.
A daren, bayan na gama sallah ta Tahajjud, na zauna a kan darduma na ji kamar wani ƙwaƙwalwar tunani ta sauka a zuciya:
****
Na kira Asad.
Muryata na rawa.
“Ranka ya dade… ina so na buɗe gidauniya.”
Ya yi shiru na mintina biyu.
Sai ya ce cikin nutsuwa mai sanyi“Ramlah, wannan shine mafi girman buri da kika taba furtawa.Zan baki duk abin da kike bukata.”
Bai jira gobe ba. Ya tura mini kudidon farawa.Ya kira Alh. Bashir (Chief Auditor).Ya kira Barr. Isyaku (Legal).Ya kira Architect Farouq.Ya ce “Wannan aikin matata ne. Na fashe da kuka.
Aikin da nayi wanda ya canza rayuka Na fara tallafawa mata marasa karfi su yi IVF
Mata 36 sun samu ciki a shekara ta farko. Mata 11 sun haihu twins. Mata 5 suka dawo su ka sumbaci kafata suna kuka.
Na kafa shirin “Matar Jiya Uwar Gobe” don kula da matan da mazajensu suka barsu saboda rashin haihuwa.
Na gidan Counseling na soyayya don darasi duk masarauta suna girmamawa.
Na dawo sarautar mata.
Na zama uwa ga jariran da muka dauki nauyin haihuwa.
Kowane yaro da aka haifa ta IVF, matar ta rubuta sunana akan takarda:
“Ramlah wacce ta ceci zuciyata.”
Ina zaune a ofis dina, yara hamsin suna dawainiya a playground, ina kallonsu daga window na kuma jin zuciyata na cika“Toh, ga ‘ya’yana…
Daren da Asad ya zo min da wani littafi a hannu Ya zauna ya ɗago kaina daga kansa yace “Kin ga wannan?”Na karanta an rubuta RAMLAH THE WOMAN WHO GAVE BIRTH WITHOUT A WOMB (Mace wadda ta bada haihuwa ba tare da ta haihu ba.)Na fashe da kuka ina dariya.Ya rungume ni sosai, yana shafa bayana, yana rad’a cikin kunnenshi “Even without a child…you became a mother to nations.”
Na rufe ido na ce“Alhamdulillah Ya Allah… Ka bani abin da ya fi cikin haihuwa.”Shekaru goma sha kenan cif babu ciki, babu bacci mai nutsuwa, babu zuga mai ƙarewa.
Goma sha da Asad yake rike hannuna yana daura murmushi,amma na fi kowa sanin cewa shi ma zuciyarsa tana sha’awar jin “Daddy”.
Goma sha da kowanne gwaji ya ce “Lafiyarki kalau.”Amma kuma cikinka shiru.
Asad ya ce “Ki saurara Ramlah… ki karanta wannan.” Ya ce“Duk wacce bata haihu ba Allah yana so ya ɗaga ta. Saboda jarabarta tana da ladan da mata masu ciki basu da shi.”
Na runtse ido da sabon kuka.Ya janyo ni ya rungume kuma yace“Ki tuna da wannan ‘Ba haihuwa ba ce jarabarki yadda kika jure ne darajarki.’Kuma Allah yana ce
‘Ni na fi sanin abinda ya dace da bayina.’”
Sai ya ce “Ki tuna Maryam ta samu jarabawa, Hajar ta samu jarabawa.Babu wacce Allah ya ƙi kuma babu wacce aka ƙi saboda bata haihu ba.”Kalmar ta buga zuciyata sosai.
Ya saka hannunsa ya tallafe kumatuna ya kamo fuskata.
*****
Shekaru sun ja…
ranakun farin ciki da na kuka sun shige, amma soyayyarmu bata taba tsufa ba.
Ni ce, Ramlah, yanzu ina da shekaru.
Mijina, Asad, yana da shekaru
Yana da mukami mai girma a duniya:
Yarima, Bilioniyan da ya fi kusan kowa farin jini a ƙasarsa mutum na biyu mafi arziki.
Amma a wurina?
Shi fa mijina ne kawai. Wanda ya ɗauke ni da ciwo, ya goyata da hawaye, ya lallashe ni da soyayya, ya kare ni daga duniya.
yau muna Paris.A kan gadonmu mai launin milk-white wanda ya cika da pillows masu sanyi da kamshin jasmine. Ina kwance a gefensa, hannuna cikin nasa.Yana cikin white knitted sweater, jikinsa yana a hankali amma yana dumi dumin da na saba tun ina yarinya.
Ya juyo gare ni a hankali, yana lumshe ido kamar yana jin wani kiɗan zuciya daga jikina.
“My Ramlah…”
Muryarsa dadi, mai sanyi, mai nauyin shekaru da soyayya.Na yi murmushi cikin kukan farin ciki.“Na’am… Asad-na.” Ya matse hannuna da rauni, amma yana ƙarfi sosai a zuciya.“Na rayu saboda ke.”Ya furta kamar yana buɗe littafin zuciyarsa.“Ko da ba mu samu yara ba… kin cike min dunia. Kin zamo mata, uwa, aboki, addu’a, natsuwa…”
Na rufe ido hawaye suna zubowa.
“Aa Asad, kaine da soyayya. Kai ka mayar da ni mace fiye da duk wata mace.”
Ya yi murmushi.
Idanunsa sun cika da hawaye masu sheƙi kamar gilashi.“Ramlah… kina so ki ji wani abu?”Na ce, “Na’am.” Sai ya matso da kansa da ƙyar, ya manna goshinsa da nawa.
“Da ace zan dawo duniya… sai na roki Allah Ya bani ke sau dari. Ko ba tare da haihuwa ba.”
Na ji wani irin kuka ya taso daga zuciyata.
Kuka mai daɗi, mai tsarki, irin wanda mace mai nutsuwa takan yi idan soyayya ta gama mallake mata rai.
“Asad… ka zabi ni? Har yanzu?”
Ya lumshe idanu yana murmushi.
“Har ƙarshe. Har bayan mutuwa.
Ni da ke… ba mu dogara da jini ba. Mun dogara da zuciya.” Sai na yi masa hugging a hankali sosai, jikinsa mai rauni amma dumi kamar bargo.Bayan mun gama, ya ce cikin sanyi“Ramlah… ki tuna ayar nan, ita ce rayuwarmu ta gina:” ‘Allah yana halitta yaro wanda Yake so, Yana barin wanda Yake so ba haihuwa…’(Ash-Shuraa 42:49–50)Na ce masa “Ayar da ta bani kwanciyar hankali fiye da maganin duniya.” Ya lumshe ido yana cewa “Ramlah… ki san wannan: Na ƙaunace ki fiye da dukkan mata masu haihuwa dubu.”
Na kissa kansa a kirjinsa.Na ce masa cikin kukan farin ciki “Ni kuma na ƙaunace ka fiye da dukkan mazan duniya.” Hasken Eiffel Tower ya cika dakin. Sanyi ya shigo amma muna dumi cikin juna. Asad ya yi bacci.
Na rike hannunsa sosai kamar ina rike da rayuwata. Sai na furta a hankali, hawaye suna zubo min “Ya Allah… ka amshi soyayyar mu a matsayin ibada.”Na rufe ido.Dakin ya yi shiru.
Zuciyar Asad tana bugawa a hankali.Na ji kamar duniya ta tsaya.Kamar lokaci bai gudu.
Kamar komai ya gama zama lafiya.
Kaddara ta kasance.
Ba haihuwa ce ta gina mu ba.
Soyayya, hakuri da zuciya ce.
KARSHEN LITTAFIN ƘADDARAR RAMLAH
A hankali na runtse idona bayan na ga karshen littafina…
Sai na narke kamar gishiri a ruwa.
Ban san ko a lokacin da nake rubuta shi ba… amma yau da na dawo karantawa, sai na ji wani irin nauyi ya tashi daga zuciyata.
Nayi murmushi, nayi kuka, na yi shiru… sai kuma na yi hamdala.
Sannan na shiga nazari kamar haka. Duk abin da mutum ya aikata, sai ya gane darajarsa a karshe.Rayuwa tana zagaye kamar juyawar kwarya a ruwa.
Abin da aka aikata daga sharri, komai sirrinsa, zai dawo.Abin da aka aikata na alheri, komai ƙarancinsa, zai tsiro.
Ramlah ta samu albarka saboda girmamawa, ladabi, halayya. Shi yasa ko da ba ta haihu ba, Allah ya ba ta duniya albarka ta hanyar zaman lafiya, daraja, arziki, karɓuwa.
Yarda da ƙaddarar Allah ita ce mafita mafi ƙarfi
Ba haihuwa?
Ba aure?
Rashin lafiya?
Rashin kuɗi?
Shan tozarci?
Duka kaddara ce.Kuma Allah ba ya jarrabar bawa sai domin ya ɗaga darajarsa.
Na tuna ayar Allah “Kuma idan kuka yi hakuri, to hakuri shi ne mafi alheri ga masu hakuri.”
(Surat An-Nahl 16:126–127) Da kuma “Wadanda suka yi hakuri kuma suka dogara ga Ubangijinsu kawai.”
(Ankabut 29:59)
Hakuri abu ne mai zafi, amma a ƙarshe ya zama zuma.
Ya kai ‘yar uwa, ki bari aure ya gyare ki, ba ya hallaka ki.
Ki zama mace ta alkhairi
• Haƙuri
• Zaman lafiya
• Biyayya
• Tsabta
• Zuci mai sauƙi
• Tsoron Allah
• Addu’a
Daga cikin mafi girman darasin littafin shine wannan
“Naƙasa ba rauni ba ne.
Ba haihuwa ba kaddara ce, ba hukunci ba.”
Mutane da yawa sun yi gorin haihuwa… amma a ƙarshe su ka gane cewa Allah yana baiwa kowa kashensa.
Wasu yara suke da su, ba su da nutsuwa.
Wasu ba su haihuwa amma suna da zaman lafiya.
Wasu suna da komai amma basu da farin ciki.
Allah yana ba kowa daidai da abin da zai iya ɗauka.
A nan nake kawo ƙarshen littafina mai suna
ƘADDARAR RAMLAH
(Wacce soyayyarta ta tsaya bisa ƙaddara, ba haihuwa ba)
Lokaci: 11:55 PM
Rana: …
Wata: 16/11/ 2025
Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin zuciya mai daɗi da soyayya mai tsarki.
Tsira da Aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW).
Abin da muka rubuta ba daidai ba Allah Ya yafe mana.
Abin da muka rubuta daidai Allah Ya saka da alheri.
Ku ɗauki darasi daga wannan rayuwa
Ku riƙi aure
Ku riƙi hakuri
Ku rungumi ƙaddara
Ku daina mugunta
Ku zauna da zuciya mai tsabta
Allah ya albarkaci rayuwar ku duk.
Allah ya biya bukatunku na alheri.
Allah ya kare ku daga sharrin juna.
+234 903 056 9336
Allah Ya saka da alkhairi. Na gode da ƙaunarku, da addu’o’inku, da yadda kuke bibiyar littattafanmu. Ku cigaba da kasancewa damu akwai sabbin littattafai masu ƙarfi suna zuwa nan ba da jimawa ba in shaa Allah.
NAN DISO (Mutan Madina)
“Ina muku soyayya ta musamman.”