Kenza eBookz

Kamar da wasa complete novel - Chapter 20

Kamar da wasa complete novel - Chapter 20

Kamar da wasa complete novel Chapter 20: Kamar da wasa complete novel Chapter 20. "Bilkisu kenan.... Wai bake hamood yacewa zai aiko akawo muku magani ba?…

3,293 words

"Bilkisu kenan.... Wai bake hamood yacewa zai aiko akawo muku magani ba? Last 3 days yaje hospital wurina karbar drugs dinsu wanda yakesha saboda lalurar da yake dauke da ita but unfortunately ranar babu maganin ba akawo ba kuma yace min tafiya zaiyi amma idan ankawo intaimaka inkawo masa gida zan samu matarsa sai nabata saboda itama tanada bukata u know he's my childhood friend...."

"Nidai to... Amma wallahi har yanzu ban ganeba da dai wasila na nanne may be ita yake nufi not me..."

"Wasila....?, wasila kuma? Har yanzu suna tare da wasila?"

"Likita kasanta ne...?"

"Ehhh ai itace ta jona masa HIV din... Can wurin yawon barikinsu suka hadu, dama suna tare?"

"Kana nufin ba matarsa bace?"

"Mata? Mata kuma? Tayaya wasila tazama matarsa? Sai dai ko farkarsa...."

Ai tun kafin ya karasa bilkisu take jin jiri yana daukarta abu biyune suka taru suka dagula mata lissafi awannan lokacin nafarko jin wai hamood yanada HIV na biyu kuma jin wai wasila karuwarsa ce, sama sama take jin bayanin likita amma tunda jimawa tadaina fuskantar komai maganin tasa hannu ta karba daga nan tawuce ciki jiri yana cigaba da daukarta ko sallamar da yake yimata bataji.

***

Cikin nasara admission dinsu fahad yafito kuma yasamu inda suka bashi BSC laboratory level 200 saboda result dinshi na diploma yayi masifar kyau dan da distinction yafita kuma SLT ya karanta shiyasa, shi anasa zabin ma pharmacy yaso subashi yadora amma suka bashi laboratory dole babu yadda ya iya hakan zai daure ya karanci lab din,babu bata lokaci yashirya yaje ya karbo admission letter dinshi, har makaranta ya kaiwa husnah tagani tayi congratulating dinshi, suna tare yaya Baffa yayan salim yayi masa waya wai yazo ya sameshi agida, sallama yayiwa husnah yahau Babur dinshi yatafi yana zuwa yaya baffa ke sanar dashi wai wasu turawa ne zasu karbi hayar gidansa idan har zai basu zasuyi aiki na shekara daya agarinne kuma a wannan area din suke son gidan, baba fahad yakira awaya ya sanar masa babu bata lokaci baba ya amince shima fahad baida zabin da yawuce ya amince din, cikin kwanaki biyu aka gama komai aka bawa turawa gida suka hau gyarashi,kudi mai yawan gaske suka biya aka sakawa fahad cikin account dinsa. Da wadannan kudin yadiba yaje yayi registration ya kama hayar dakin da zai zauna anan opposite din makarantar wanda ya kasance private hostel na manyan yara shi dinma a babban yaron yafito bayan yagama registration yakoma gida zaije yashiryo yadawo saboda nanda yan kwanaki za afara lectures.

*_Ummi Shatu_*👌🏻 [11/28, 08:20] Hafsat Rano: *Wannan littafin na siyarwa ne,me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*

35***Babu bata lokaci fahad ya kammala shirye shiryensa na tafiya makaranta domin shi aburinsa idan yatafi bazai dawo gidaba sai semester ta kare, duk abubuwan da zai bukata ya tanadi kudinsu domin acewarsa baya so ya debi kaya daga nan kano har zuwa kaduna wai za arainashi yafi son sai yaje can sannan yasiyi komai, anan gida dai ayiyah da mamuh sunyi masa jar miya cikin plastic da dakakken jan yaji mai daukeda tafarnuwa wai dan adan saukaka masa yayinda su anty Fauziyya suka yimasa snacks. Ana igobe zai tafi yaje gidajen yan uwansa duk yayi musu sallama shida salim bayan sallar ishah suka dawo gida bai samu ganin husnah ba a wannan dare domin ka'idar makarantarsu karfe 6 ake rufewa, shiyasa yabari sai washe gari da safe zaije ganinta before yawuce.

Lamo yayi kwance bisa katifarsa yana sake sake acikin ransa wato gaba daya rayuwar nanma jarrabawace acikinta da gaibu saboda duk yadda kakai ga shiryawa kanka rayuwa baka taba sanin abinda zai faru gobe komai iya hasashenka shidai koda wasa bai taba kawowa zai yi soyayyar aure da husnah ba asalima kallon mai dan tabin hankali yake yimata ada amma yanzu duk da bajin sonta yakeyi acikin ransa ba tana da wani muhimmanci agareshi, bilkisu dai insha Allah yamanta da ita koda kuwa hakan zaisa ya dawwama acikin bakin ciki da damuwa. Washe gari kamar yadda ya tsara bayan yagama shiryawa cikin kananan kaya bakin jeans da t shirt din polo yellow, hatta takalmin da yasaka na kamfanin polo ne da p cap, gidansu salim yaje yayiwa mamansu sallama sannan suka wuce wurin husnah tare, kasancewar weekend ne bata da class shiyasa da personal tafito tasha yellow din atamfa mai zanen kwarya, tana karasowa salim yafara tsokanarsu,

"Kaga amarya da ango.... Wato tsabar ma zuciyoyinku anko suke da juna shine harda saka kaya kala daya...."

Murmushi fahad yayi itama haka amma batace komai ba sai fahad ne ya mayar masa da martani,

"Kasan aduk lokacin da masoya suka shaku da juna to komai nasu rikidewa yake yakoma iri daya shiyasa sai ka gansu tamkar wasu yan biyu... Ni bakaga har wani kama mukeyi da ita ba.... Ko husnah ta? Ai kamarmu daya ko?"

Dariya tayi tarufe fuska tana fadin,

"A'a ya fahad wallahi kafini kyau..."

Dariya yayi yana kallon wani wuri,

"To ai kinfini haske Asma'u kuma ma dai kamar tamu daya..."

"Kana dai kawai tsokana tane fa..." Tafada cikin shagwaba,

"To kuma meye abun turo min bakin? Ko kina son inbaki goodbye kiss ne...."

Dariya tayi ta juya masa baya,

"Nidai bana so..."

"Nima bance kina so ba kawai tambayace yan matanah...."

Shidai salim ashe yajima da sulalewa yabasu wuri yana can zaune gaban wata bishiya mai dauke da benci a karkashinta,

"Ya fahad dan Allah idan katafi karka manta dani.... Karka maye gurbina da wata... Wallahi idan kayi min haka zan iya rasa raina..."

Saida ya matsa kusa da ita sannan yafara yimata magana kasa kasa cikin alamun rarrashi da tarairaya,

"Haba husnah ai ko amafarki bazan taba mantawa dake ba.... Kina da wani babban bangare acikin zuciyata, kisa aranki akoda yaushe kina cikin zuciyata kuma insha Allah bazan taba zama sanadiyyar rasa rayuwarki ba domin zan baki kulawa zan sadaukar miki da lokutana aduk lokacin da kika bukaci hakan.... Amma kin san me? Karfa nima ina tafiya kiyi min kishiya...."

Murmushi tayi kwalla tana ciko idanuwanta,

"Ya fahad only u, kasa wannan aranka nice dai nake tsoron yanmatan Jami'a kar inje ina nan wata ta kwace min kai...."

"Husnah no need to worry about that....saboda ni wallahi tsoron mata nakeyi yanzu.... Karki dauka da wasafa... Seriously tsoron mata nake ayanzu dai...."

Kallonta yayi yanda take hawaye dagaske tana gogewa,

"To menene wai na kukanne?? Idan bakya son natafi shikenan sai infasa karatun husnah indai hakan zai saki farin ciki..."

Girgiza kai tayi tana share hawaye,

"A'a ya fahad kaje, Allah yabasa sa'a.... Sai munyi waya"

Daga haka tajuya tatafi yasan wani kukan takeyi wanda bata son yagani duk kuma sai yaji wani irin tausayinta yana shigarshi, shida yazo suyi sallama amma gashi tatafi da kuka ko sallamar ma bata bari sunyi ba.

"Allah sarki husnah Allah yabani ikon faranta miki...."

"Amin" salim ya amsa wanda karasowarsa wurin kenan, dafa kafadar fahad yayi yahau bayan Babur din yana cewa,

"Rabuwar masoya tana zafi gashi ku baku sababa....."

"Dallah can... Meye hakan"

"Ahh waka ce mana nake yimuku... Allah sarki husnah..."

Buga Babur din fahad yayi suka fita sai da suka bar kofar makarantar sannan yace da salim,

"Salim wallahi husnah tausayi take bani... Ina tsoron kar zuciyarta tashiga wani hali saboda soyayyata kamar yadda tawa zuciyar ta tsinci kanta sakamakon halin da bilk....."

Sai kuma yayi shiru domin baya son tunata baya kaunar tunawa da ko sunan bilkisu arayuwarsa domin abinda yafaru tsakaninsu shine abu mafi muni da ya taba faruwa dashi wanda baya jin zai iya mantawa,

"To ai indai zaka danne zuciyarka kanuna mata soyayya ka riketa da gaskiya bazata taba shiga halin da kake tsoron shigarta ba...."

"Zan kokarta insha Allah i will try my best to makes her happy,lovely and even special... I will for eva care for her"

Dariya salim yayi,

"Ai nasan zaka iya... Lover boy"

Da hirar husnah a bakunansu sukaje gidansu fahad yayi sallama dasu ayiyah har baba ma yana nan yana jiran tafiyarsa bai fitaba sai lokacin yake jin kamar zaiyi kuka, su maryam kam kukan suke tayi kamar anyi musu mutuwa shiyasa shima saida yaji kwalla na shirin zubo masa da koke koke dai yadau kayanshi yatafi shida salim wanda zaiyi masa rakiya har inda zai hau motar Kaduna.

Bayan sallar azahar yashiga kaduna, dakinsa wanda yakama yaje ya shirya kayansa yaci snacks ya kwanta domin hutawa duk da yana son shiga kasuwa yasiyo abubuwan da yake bukata na amfainin yau da kullum da kayan abinci. Zuwa dare ya kammala komai yagyare dakinsa tsaf ya siyo duk abubuwan da yake bukata, kwanciya yayi kan katuwar katifarsa ya bararraje ya kira gida saida suka gaisa da kowa na gidan sannan yakira ya abba shima suka dan taba hira sannan yakira husnah daga karshe ita kam hira suka sha sosai domin har 10 da wani abun domin shagwabar da yasaba yaketa zuba mata,

"Ko inje infadawa baba adaura mana aure akawoki nan mu zauna.... Ni kin san bana son harkar yunwa gashi bana son yin girki da kaina...."

"Ka rinka zuwa captaria kana ci mana..."

"Yanmatanah abincin saidawa farin maggi suke sakawa nikuma bana so idan naci sai nayi amai...." Yakarashe maganar cikin shagwaba, dariya husnah tayi,

"Ya fahad kaifa dadina dakai shagwaba...."

"Kin manta ni dan auta ne? Komai ayiyah tasamu ni take baiwa fa...."

"Su Mariya fa? Basune auta ba?"

"Ke wadannan fa "yayana ne, yaran sister nane..."

"Badai 'yayanka ba,'yayan Anty dai.... Kai ai tukunnah..."

Dariya yayi ya lumshe idanuwanshi,

"To me kike ci na baka na zuba..., nima din kwana nawane muna yin aure zaki haifo yan biyu kafin shekara ta zagayo...."

"Wai wai... Lallai ya fahad, yauwa dama inaso in tambayeka wai dan Allah...."

Jin tayi shiru yasashi bude idanuwansa,

"Menene? Go on ina jinki..."

"Wai meya rabaku da matarka"

"Husnah dan Allah kar muyi wannan maganar saboda ciwona zai iya tashi kinga nasamu kwana biyun nan yasauka...."

"Shikenan ya fahad insha Allah bazan sake yimaka magana kwatankwacin irin wannan ba,Allah yakara maka lafiya..."

"Thank you husnah"

Sun jima suna hira daga bisani sukayi sallama kowa zuciyarsa fari tass saboda dadadan kalaman da suka fadawa juna.

Washe gari yafara fita lectures tun aranar yayi friends guda uku dama su ukune tun level one suke tare haidar da Bashir sai mukhtar shi dai fahad baya son hada kai da kowa a makarantar nan kamar yadda su ayiyah sukayi masa fada akan ya tsaya yayi abinda yakaishi sannan banda kula abokai barkatai domin hakan babu fa'ida acikinsa amma saboda yanda suka manne masa dole saida ya kulasu dukda yana jin tsoro domin yaga kamarsu yaran manyane shikuwa ba dan kowan kowa bane sai dai sam ko kadan su basu nuna masa hakanba domin aranar ma dakinsa suka bishi bayan sun fito daga lecture harda kokawa akan guntun snacks din dake cikin jarida a nannade wanda yarage shiyasa shima ba adauki wani lokaci mai tsawoba yasaki jikinsa dasu saboda yaga basuda wani mummunan hali basa shaye shaye basa iskanci basa komai shi dama dan shaye shaye ya tsana bazai taba iya abota dashiba.Kullum suna tare su hudunnan kamar wasu yan hudu shi mukhtar gidansu a abuja yake sukuma su bashir duk yan cikin Kaduna ne, duk lokacin da suka fito daga lecture sai dai su zauna suyita bacci adakin fahad ko kuma wani lokacin suyita buga games a wayoyinsu ko game din kati shiyasa fahad yafara kokarin nemarwa kansa mafita domin baya son zaman nan na asara shiyasa ya yanke shawarar fara zuwa shagon dinkin da yagani tsallaken gidan da yake zaune su mukhtar nata tsokanarshi suna cewa yana babban yaro amma shine zai je yana dinki? Shi dai cewa yayi ehh babu komai ai Sana'a ce saboda yasan basuda masaniyar irin kudin da yake samu ta hanyar dinkin nan shiyasa kwana biyu da baiyiba duk jinsa yake sai shankali hatta kafarshi kumbura takeyi ita kadai tana sabewa.

***

Tunda bilkisu tazauna acikin falonta bayan tafiyar Dr abrar takasa samun nutsuwa gaba daya jinta take kamar acikin mafarki, takasa zaune takasa tsaye sai kaiwa da komowa takeyi burinta kawai taga dawowar hamood cikin gidan ta zazzage masa abinda ke cikinta,

"Wannan ai cin amanane da mugunta, ni hamood zai yiwa wannan butulcin...? Ohh my God.... What a heartless..... Wannan wacce irin mugunta ce..."

Wasu hawayene ke kwaranya daga cikin idanuwanta mikewa tayi tawuce bedroom dinta tasoma hada kayanta gashi abin haushi akwatunanta ansace balle tazuba kayan aciki duk da hamood yayi mata dadin bakin wai zai siya mata wasu, haka dai taci gaba da zama amma babu hamood babu labarinsa tana ta kiran wayarshi kuma akashe har dare bai dawo gidanba sai wise ce tadawo gidan da misalin karfe 10 nadare ko kallonta bilkisu batayi ba amma itama yau kallo daya zaka yimata kagane ashirye take da ko wanne irin bala'i wanda mutum keji dashi, babu wanda ya tankawa wani wise tawuce bedroom dinta wanda ke falon kasa sam hakan bai damu bilkisu ba ayau domin yanzu ita ba ta wasila takeba ta hamood takeyi so take yazo gidan ta kare masa tanadi amma abin takaici da bacin rai bai dawo gidanba har 12 nadare har lokacin bilkisu bata runtsa ba tana jiran taga ta inda hamood zai bullo anan falon ta kwana har asubah dama tunda tazauna bata tashi sai dai idan salla zatayi.

Safiyar ranar da misalin karfe goma tana zaune tana zaman jiran tsammani domin bata son tatafi gida tasake dawowa tafiso tatafi gaba daya da takardar sakinta ko wani abu mai kamada haka, ga kayanta nan agefe wadanda ta shirya domin tafiya dasu, akan idonta wise tafito tashiga kitchen ta dafo indomie tazo takoma daki, har takosa da zaman tana shirin tafiya inyaso sayita su kare awaya taji dirin shigowar motarsa, mikewa tsaye tayi ta rike kugu tayi tsayuwar ashirye nake da duk abinda mutum yazo dashi tana jijjiga kamar ansaka mata wayar wuta masiface rubuce kan fuskarta ahaka hamood yabude kofa yashigo ya isketa.....

*_Ummi Shatu_*👌🏻 [11/28, 08:20] Hafsat Rano: 36***Tunda hamood yashigo ta dauke kai tamayar dashi gefe daya ganin haka yasashi shima hade rai yadaure fuska kamar bai taba dariya ba,

"Macuci.... Azzalumi..... Mugu to Allah ya toni asirinka....yanzu dama hamood kasan kana dauke da kwayar cutar HIV amma shine ka aureni ahaka har kake burin hada shimfida dani?"

Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yazare farin tabaran dake sanye cikin idonsa, zama yayi kan kujera ya dora daya kan daya yana watsa mata kallon dake kara tafarfasa ranta,

"To sai me dan na aureki ina dauke da HIV? Bake kika manne min kika like min akan dole sai na aureki ba? Karfa ki manta har aurenki kika kashe dan kawai in aureki in zauna dake...."

"Ya isa haka malam.... Ai duk wadannan abhbuwan dakake ikararin cewar na aikata na aikatane acikin rashin sani... Kuma ina nadamar hakan ahalin yanzu, wallahi hamood kaci amanata kuma ka zalunceni wanda bazan taba yafe maka ba har abada.... Sannan ka gaggauta sallamata domin gidan ubana zan tafi insha Allah nagama zama dakai...."

Wata shakiyiyar dariya yasaki irin wacce ke dauke da mugunta tsantsa aciki sannan yayi mata kallon uku ahu,

"U are such an idiot mai gado, sai yanzu nasan bakida tunani sam.... Hmmmm to idan ke shashasha ce ni mai hankaline... Bazan taba sakinki ba koda kuwa za amaimaita yakin duniya akaro na uku.... And lastly abinda zan fada miki shine u should mind ur tongue kisan irin maganar da zaki rinka fada min idan bahaka ba jikinki zai rinka gaya miki....."

Yana kokarin mikewa taje tasha gabansa cikeda masifa da tashin hankali,

"Wallahi hamood koda baka sakeni ta dadin rai ba to yazama wajibi ka sakeni ta dolen dole koda kuwa agaban kotu ne domin nagama zama da macuci,mayaudari, mashayi kuma mazinaci... Ko kana tsammanin har yanzu ban san irin kazamar rayuwar da kuke yi kaida waccan karuwar ba? To Allah yagama tonar asirinku dan haka kasakeni kuma kabani kudina naira dubu dari biyar wanda abbana yabani kai kuma ka lallabani ka kwace....."

Tafa hannaye wasila tashiga yi wacce fitowarta kenan daga cikin daki,

"My dear yanzu kana tsaye kanajin abinda wannan mahaukaciyar take fada maka amma shine bazaka dauki mataki ba?"

Tun kafin wise tarufe baki hamood ya dauke bilkisu da wani gigitaccen mari wanda yayi barazanar makantar da ita, zafin marin yasa bilkisu sake daga murya tana furta,

"Allah ya isana macuci azzalumi kuma wlhi sai ka bani kudina sannan dolenka ka sakeni...."

"Banza yar gidan matsiyata ni zaki yiwa sharrin na karbar miki kudinki? Uban me uban naki yake dashi da har zan karba? Saki kuma bazan yiba ko kin zaci nima irin wannan sakaran yaronne da zan sakeki aduk lokacin da kikaso? Koda zan sake ki yazama dole inmore sadakina dan haka sai kishirya daukar kwayar cutar HIV...."

Tun kafin yakarasa bilkisu ta dadimeshi tana kuka,

"Ni ba yar matsiyata bace sai dai idan kaine dan matsiyata kuma wallahi daga yau nagama zama dakai...."

Wani marin yasake bata sannan yashiga dukanta babu ji ba gani har saida takai kasa lokacin ne yafara ball da ita yana nausa mata kafa aciki, kuka bilkisu takeyi tana ihun neman dauki ganin yana kokarin kasheta yasa wise zuwa tana kokarin hanashi amma yahaukace kwata kwata bayaji bare gani,

"Nashiga uku hamood ka kusa kasheta... Kar kayi kisan kai kaga yanda takeyi fa... Kabarta haka"

Shine abinda wise keta fada amma hamood yaki saurararta ganin haka yasata sulalewa daga gidan tagudu tun kafin hamood yakashe bilkisu azo tafiya dashi ahada harda ita.

Bilkisu kam tajima da fita daga cikin hayyacinta sakamakon na jakin da hamood ya lakada mata abu na karshe da zata iya tunawa shine taji hamood ya gwarata da kujera ta fadi akan hannunta na hagu wanda take awurin wani azababben zafi ya ziyarceta, cikin azababben ciwon kai take bude idanuwanta ahankali wadanda suka kumbura suntum sakamakon uban bugun da suka sha,

Ammah ce da meenah zaune acikin dakin wanda ko ba afada mata ba tasan asibitine domin ga alamu nan sun nuna hakan, ga ruwa nan ana kara mata a hannunta na dama sannan hannun hagun ta kuma an daddaureshi dasu bandeji alamun dori,

Wasu hawayen nadama ne suka zubo daga cikin idanuwanta, ganin ta dan motsa yasa ammah da meenah azamar tasowa dukkaninsu Wanda har bakinsu na haduwa wurin yimata sannu,

"Sannu mai gado..." Inji ammah,

Kai ta dan daga cikin azabar ciwo ta rinka binsu ammah daya bayan daya da kallo kamar yau tafara ganinsu. Bata iya cewa komai ba sai ciccije baki da takeyi sakamakon ciwon da dukkanin jikinta keyi mata musamman ma hannunta na hagu,

"Sannu adda labour.... Allah yatashi kafadunki"

Dagawa meenah kai tayi tana cije baki hawaye na kwaranya daga cikin idanuwanta ahaka su maama suka shigo itada Hindu,maama na dauke da sultan ita kuma Hindu tana goye da meenal abayanta sai hudah wadda hannunta ke rike da nata, cikin zuciyarta take wani irin kuka mai tsuma rai saboda ganinsu mama da 'yayayensu yasake fama mata raunin da take fama dashi, su gasu da yaransu agidan mazajensu cikin walwala da kwanciyar hankali amma ita tanata shiga cikin runtsin rayuwa,

"Allah ka gafarta min... Allah natuba... Astagfirullah..." Shine abinda taketa fada cikin zuciyarta, jinta take ta tsani hamood ta tsani duk wani namiji mai irin halinsa ahalin yanzu,

"Allah ya isa..." Shine abinda lebanta suka furta amma babu wanda yaji, cikin tausayawa da jimami maama da hindu suka karaso gaban gadon su dinma kamar zasuyi kuka,

"Sannu Adda.... Sannu... Sai Allah yasaka miki insha Allah" inji mamaa,

"Kuma inbanda zurfin ciki irin na Adda labour bata fa taba fadar irin zaman da sukeyi ba bare tafadi cewar yana dukanta..." Hindu tafada tana kokarin zama agefen gadon,

"Ni dama tun jimawa wallahi na fuskanci akwai matsala kugafa irin ramar da tayi har iyallo ke cewa ciki ne..." Meenah itama dake tsaye kusa da amma ta tofa nata,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull