Kenza eBookz

Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 19

Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 19

Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 19: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 19. Jabir ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

3,367 words

Jabir ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

***

Bil haƙƙi mai sunan Baba ya nunawa ruma aure zai yi mata, ya je ya a sayo sabuwar katifa ta 'yan makaranta, ya ce wa mama gata nan a ajiye ta ruma ce, ya sayo kwano da kofin silba mai murfi da sabuwar buta, shi ma ya ce na ta ne. Hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta, cikin dare mama ta na bacci ta ga ruma tana shimfiɗa sallaya tana kuka.

Mama ta ce "Ke lafiyarki kuwa?"

"Sallar dare zan yi, na roƙi Allah a kan mai sunan Baba, tun da kin ƙi ki hana shi, an rasa wanda zai hana shi yi mini aure".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ke fa ki ka ce kin ji kin gani, ki yi addu'a kawai Allah ya baki zaman lafiya da ke da wanda zai aura mikin"

Zaman dirshan ruma tayi, ta ɗora hannu a ka tana kuka, mama ta rufe fuska tana yi mata dariya ba tare da ta sani ba.

Ruma ta daɗe a sujjada tana addu'a, sannan ta koma ta kwanta.

A islamiyya kuwa, malamin ajin da take ne, ya lura yana ƙari tana kuka, dan yanzu a ɗan samu cigaba, ta daina guje-gujen aji, a babban aji da ajin su Yasir take zama, kuma yanzu tana iya karatu ba kamar da ba.

Sai da ya kammala ƙarin Alqur'ani, sannan ya kira ruma yana tambayarta me ya sa take kuka? Ba ta gaya masa ba, ta ce mai babu komai, ƙarshe sai ƙyaleta yayi.

Ranar juma'a kuwa da farar safiya da kuka ta tashi, dan yau ne kwanakin da mai sunan baba ya ɗibar mata suka cika, ba tare da ta samu wanda za ta kawo ba, a matsayin wanda take so, to ita wa ma take da shi.

Mama sai fama take da ita ta shirya ta tafi makaranta, amma ta rungume uniform ɗin tana kuka. Umar ya fito fuska a haɗe ya daka mata tsawa, cikin tsuma ta hau saka kayan ba tare da ta yi ko wanka ba.

"Ki fice ki tafi makaranta, idan kin je can sai ki yi musu kukan, shi ne ki ka gayawa ɗan uwa wai zan yi miki aure ko? To shi ma bai isa ya hanani abin da na yi niyya ba, ai ke ki ka nuna ki na son auren, wuce ki bawa mutane wuri"

Kamar korarriya, ta ɗau jakarta ta tafi makaranta.

Bayan fitarta, mama ta kalleshi ta ce "Babana, a sassauta mata ta horu haka, kwanaki uku kenan ba ta ko cin abinci, ayi mata afuwa babana"

"Ƙyaleni da ita, horata kawai nake, amma yau zan ƙyaleta in sha Allah"

Ƙin shiga makarantar ta yi, ta tsaya a waje tana kuka, mai gadi ne ya ganta, ya ja ta ya kaita ofishin Headmaster, ya sanar masa da a waje ya ganota ta tsaya ta na kuka.

Headmaster ya ce "Ai ni rigimar yarinyar nan nake tsoro, ke me aka yi miki?"

"Yayana ne ya ce zai yi mini aure yau"

Waro ido ya yi ya ce "Aure kuma? Waye zai kwasa? Ke bana son wasa"

"Wallahi haka ya ce"

Headmaster ya kalli ruma, sai ya kawo ko rashin hanklin ruman ne ya motsa, dan haka ya ce "To shikenan, ki yi haƙuri ki tafi aji, zan kira gidan na ku mu yi magana da su" yayi ta lallaɓa ruma ya kaita aji.

Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba, sai da ta dawo gida ta tarar mama tayi tuwon shinkafa da miyar taushe, da wainar masa wai azo a kai maƙwabta ace na auren ruma ne, mai sunan Baba ya ci farar shadda ya fito tsakar gida ya ce "Mama, idan an idar da sallar juma'a za a ɗaura mata aure, sai ayi mata addu'a"

"Na shiga uku, mama wai da gaske ne? Mama ku yi mini rai ban isa aure ba wallahi"

Wani mugun kallo ya yi mata, ta shige ɗaki da gudu tana kuka, ya fice ya bar gidan. Dariya Huzaifa ya din ga yi mata yana "Ruma, Allah ya sanya alkhairi zan kawo miki goron ɗaurin aurenki har gida ki tauna, dan mijin naki ma tsoho ne, malam labaran ladan ne"

Ruma sam ba ta shiri da malam labaran ladan, saboda ya taɓa tsula mata carbi, wataran yana kiran salla, ta taɓa tsayawa a ƙofar masallaci tana kiransa da ƙarfi, wai saboda muryarta ta fito a sufika, ya idar ya kamata ya zane ta da carbi, gashi tsoho sosai.

Mama ta shiga ɗaki ta tarar da ruma sai rizgar kuka take.

"Haba amarya, ya da kuka kuma kamar ba amarya ba?"

"Dan Allah mama ki bani kuɗin mota na gudu"

Mama ta kwashe dariya ta ce "Dama ruma akwai abin da zai baki tsoro haka?" Rungume mama tayi cikin kuka ta ke faɗin "Dan Allah mama kar ayi mini aure, wallahi na daina rashin ji, ina sonki sosai, bana son na rabu da ku, mama zaki yadda a aura mini wanda ya dakeni dan Allah mama ki hana shi aurar da ni"

Rungumeta mama ta yi tana murmushi, tausayin ruma ne ya kamata, dan har ramar dole ta yi, saboda damuwa. Mama ta zubo mata abinci, ta zaunar da ita ta bata, amma ruma taƙi ci.

Mai sunan Baba suka yi sallama, duk suka shigo a tare daga sallar juma'a, duk sun sha kwalliya.

Aliyu ya ce "Amarya kin sha kuka, to Allah ya sanya alkhairi" ta rirriƙe mama tana girgiza kai tana zubar da hawaye.

Mama ta kalli mai sunan Baba ta ce "Tuba muke babana, Allah ya bada haƙuri duk ta rame, ayi haƙuri"

Yasir ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"

Mama ta yi masa daƙuwa tana harararsa.

Umar ya ƙarasa gaban ruma da ta takure a jikin mama, tana share hawaye.

"Kalleni" yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta ɗago a hankali ta kalleshi, idanunta sun yi jawur.

"Daga rana mai kamar irin ta yau, idan na sake jin ki aikata wani abu na rashin mutunci, ko wannan shegen surutun naki, to ki tabattar aure babu fashi, kin ji na gaya miki?" Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume mama.

Mama ta ce "To madalla godiya muke, Allah ya rayaki, ya kaimu auren ki na gaske, da miji na gari ko?"

"Ni ba zan aure ba, bana so da ma da wasa nake, kuma ba zan auren ba"

Mama ta ce "Tashi ki yi godiya, tun da dai ya janye maganarsa"

"Na gode" tayi maganar tana ɓoye fuskarta.

Tashi yayi ya bar ɗakin ba tare da ya ce mata komai ba, ta din ga sauke ajiyar zuciya ta ce "Amma an shiga hakkina, Allah zai sakawa marainiya"

Yana tsaye a bakin ƙofa, karaf maganarta a kunnensa.

(BOOK 1 FREE NE, BOOK 2 PAID, BOOK1 YA KUSA KAMMALA IN SHA ALLAH, GODIYA TA MUSAMMAN GA MASU BIBIYAR LITTAFIN ƘANWAR MAZA)

Ayshercool 08081012143 [29/07, 7:26 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

P 18

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000* *Royal jelly 30 pieces 2200* *Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000* *Vitamin C-100, 2700* *Vitamin E big 3000* *Pesona 2300* *Dara 2300* *Cantik ayu 2300* *GLUTA white 2700* *Khusus ibu 3800* *Sugar wanita 3500* *Majakani 3 in 1 3200* *Eve Care 3700* *Juliet eve 11,500* *Phyton buster 18,000* *Phyton collegen 18,000* *Glute sparkling 18,000* *7 days ginger oil for hair 1,200* *Papaya oil for breast 1,200* *Garlic oil for hips 1200* *Vitamin C serum 1,500* *Vitamin E serum 1,500* *Busty blend 2800* *Gluta prime 2800* *Collegen+C 3800* *Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

Sarai ya ji abin da ruma ta ce, amma ya share kawai ya tafi, dan idan ka biye mata babu abin da zai hana ta saka maka hawan jini.

Sai a lokacin ta samu zarafin dirarwa wainar da mama ta yi, ta fara ci ta na ajiyar zuciya, dan a kwanaki ukun nan Allah kaɗai ya san tsananin damuwar da ta shiga.

Yasir ya ce "Na so auren nan aka yi miki, mu ga ta tsiya, kowa ma ya huta da halinki"

"Ta Allah ba taka ba, bakinka ya sari ɗanyen kashi, na asuba mai tururi"

Mama ta ce "Meye haka, ki na cin abinci kina zancen ƙazanta"

"To mama ba sune suke tsokanata ba"

"Ina ruwanki da su, wato har kin samu kanki za ki ɗora daga in da ki ka tsaya ko?".

Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai na shiryu ba zan ƙara ba"

"Kima cigaba, wallahi kin san idan ya zuciya da halinki, zai aikata abun da ya ce"

Sallamar Abubakar da suka ji ne, ya sanya ruma yin wani zillo, ta daka tsalle ta yi waje, maƙalƙale shi tayi tana murmushi tana faɗin "Oyoyo yaya"

"Amarya ba kya laifi, kar dai har an ɗaura auren ban samu ɗaurin auren ba?"

Ta ɓata fuska ta ce "Yaya har da kai ko?"

"A'a, nima fa kirana aka yi a waya, aka ce mini yau ɗaurin aure"

Waiwaya ta yi, ta kalli mai sunan Baba da ya shimfiɗa tabarma ya baje litattafai yana dubawa, ta kalli Abubakar, ta kai bakinta kunnensa ta ce "Wallahi hussaininka ya ɗau hakkina, ba dan yayana bane ba ko? Hmmm"

Ya kalli mai sunan Baba ya yi murmushi ya ce "Kai, a wani dalilin ya sa ka ɗaga mana hankali haka fisabilillahi?" Ko ɗagowa bai yi ba, balle ya kallesu. Ruma ta kama hannunsa suka shiga ɗakin mama.

Mama ta ce "Ta barka ka ƙaraso in ganka kenan? Na ga ta je ta tsareka da zance, kamar ba yanzu ta gama kuka da neman taimako ba"

Abubakar ya yi murmushi, ya zauna ya ce "Sannu da gida Hajiya mama, uwar 'yan maza da 'yar budurwa, na sameku lafiya?"

Mama ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, amma ba ka da lafiya ne?"

Ya ɗan kalli jikinsa sannan ya ce "Me ki ka gani?"

"To ai ganinka nayi wuri-wuri duk ka rame Saddiƙu"

Ya shafi sumar kansa da taru sosai ya ce "Mama wannan karatun namu, ai ba sauƙi ne da shi ba, pressure ce kawai, ruma zubo mini abinci" miƙewa ruma ta yi, ta fita ta kawo masa kulolin abincin ta dire masa, ta zauna ta saka shi a gaba, tana ta zuba masa surutu, mama kuwa kallon yadda yake zira abincin nan yake babu ji babu gani, kai da ganin yadda yake cin abincin ka san akwai yunwa a tare da shi, ba dai ta ce komai ba suka cigaba da hira.

Da la'asar shi da mai sunan Baba suka tafi masallaci, bayan sun dawo kuma suka zauna a tsakar gida suna hira. Ruma so take ta zauna da Yaya Abubakar, ta yi masa hira sosai dan ya fi kowa tsayawa ya saurareta, amma ta ga hankalinsa yana kan ɗan uwansa. Ganin ta zauna daga nesa tana ta kallonsu, ya sanya yaya Abubakar cewa "Ruma, ɗauko comb ki zo mu yi tsifa, na ga kitson kanki ya tsufa" ta jinjina masa kai, ta shiga ɗaki ta ɗauko comb da kibiya ta kawo masa, ta zauna a kusa da shi, tana yi tana kallon fuskar Umar, dan kar ya hantareta ko ya koreta. Yaya Abubakar ya karɓi kayan tsifar, ya kwantar da kanta a kan cinyarsa, ya fara tsfefe mata kai. Rai a haɗe mai sunan Baba ya ce "Amma dai ka san bana son ƙazanta ko?"

"Ƙazantar me kuma?"

"Dan me zaka zo kusa da ni kana aikin gashi, ko ƙyanƙyami ba ka ji"

Abubakar ya yi murmushi ya ce "Kayi karatunka ka ƙyalemu mu yi tsifar mu" a hankali ruma ta fara lumshe ido, bacci yana ɗibarta, cikin gyangyaɗinta ta ji Abubakar yana cewa mai sunan Baba "Ka ga ƙoshin nan da na yi cikina har wani ciwo yake yi"

Mai sunan Baba ya kalle shi ya ce "Kamar yaya, da ba ka ƙoshi ne?"

"Wallahi Akhi rabona da Abinci kusan kwana biyu yau, a ƙafa fa na taho tasha, na samu mota na taho gida shi ma daga tasha na ninko, Allah ya haɗani da wani ɗan unguwar nan ya goyoni a babur"

Cikin mamaki Umar ya ce "Garin yaya?"

"Wallahi kamfanin 'yan chinan da muke yiwa aiki ne suka koremu, suka kawo mutanensu. Ni kuma na ga ban aiko da komai gidan nan ba, ta yaya zan bugo na faɗi matsala, na sayar da wayata na sai ƙarama ina ta fama, gashi mun kusa exam, shiyasa ban zo gida ba, shekaranjiya garrin kwaki na ci ko jiƙawa ban yi ba, na wahala a semester nan wallahi"

Umar yayi tsaki ya ce "Akhi kana da matsala, amma ko baka gaya wa mama ba, ni mai ya hana ka gaya mini, sai ka je ka kashe kan ka da yunwa, idan ba abinci ta yaya karatu zai yiwu?"

"Kai ba fa ban gaya maka ne dan ka yi mini masifa ba, ko nima ƙaninka ne?. Na tafi na barku kuma kuna ta fama da yadda zaku yi, ni ban muku ba, kuma na ɗoro muku matsala, gashi na yiwa yarinyar nan alƙawarin sabuwar jakar makaranta ban samu saya mata ba, har kunyarta nake ji wallahi".

Mai sunan Baba ya numfasa ya ce "Dole mu din ga gaya wa juna matsalolinmu, watarana sai labari, ni kaina abubuwan sai a hankali, na saya wa yarinyar nan sabuwar katifa kusan dubu talatin, ta ta ta lalace, da so nake na sauya mata makaranta, makarantar gwamnatin nan ba ta iya komai, an ce mini registration dubu Arba'in, duk term kuma dubu Ashirin da biyar, gashi muma an yi mana ƙarin kuɗin makaranta, ga komai ya yi tsada, rayuwar ƙasar nan sai dai Allah ya sassauta mana, ina jin su Huzaifa ma suna zancen zasu yi sauka, suma kusan dubu sittin ake nema su biyu, ga garin a tsaye yake cak, sai dai Allah ya iya mana kawai, ita kanta mama ba ƙaramin ƙoƙari take ba, yakamata ace zuwa yanzu ta fara hutawa, ta sha wahala domin mu rayu mu zama mutane".

Abubakar ya ce "Haka ne, amma komai lokaci ne, daga cikin godiyar da nake yiwa Allah shi ne kasancewar dukkaninmu Allah sa babu wani wanda yake fita ya ɗauko mata magana a waje, ko ba komai hankalinta a kwance yake "

"Sai wannan abar" mai sunan Baba yayi maganar yana nuna ruma, da tayi pretending kamar bacci take.

"Ba wani ɗaukar magana, guda nawa take"

"Kai ba zaka gane ba, da ta je ta karya 'yar mutane a makaranta, sai da aka kusa korarta, har wurin 'yan sanda aka kaita"

Abubakar ya waro ido ya ce "Autar"

"Hmm kai ba ka nan, ba ka san wainar da ake toyawa ba kawai, wannan yarinyar ba ta da kai sam, kullum cikin nemo magana take ana ta abin da za a ci"

"To a daina faɗa, gara ayi ta mata addu'a "

Mai sunan Baba ya ce "Ai Addu'ar ce kamar ba ta kamata, duk gidan nan babu mai ibada kamar mama, kuma babu wanda zai yi mata addu'a ta karɓu sama da wadda take mata, amma haryanzu shiru, kullum rashin jin ta gaba yake yi, ni tausayi take bani wasu lokutan, tana da zaɓe-zaɓen abinci, and we can't provide what she wants, kuma ba ta san babu ba, sai ta zauna tana kuka, wai an bata kunu ba suga, ko ba za ta ci tuwo ba, could you imagine?"

Abubakar yayi murmushi ya ce"Allah dai ya yassare mana, in sha Allah za su huta, ita da mama"

Ruma da ta yi bakamm ta na jin su, wani irin tausayinsu ne ya kama ta, wato duk wannan zare idon da hantarar da mai sunan Baba yake yi mata, yana son ta har yana tausayinta haka.

Tana wannan tunane-tunanen har baccin gaske ya yi awon gaba da ita, sai magariba ta tashi, Yaya Abubakar ya tsefe mata kai tas ya taje, dama ya saba yi mata tsifa idan har yana gari.

Duk in da suka gilma sai tayi ta kallonsu cike da jin tausayinsu, tabbas tun da ta buɗi ido a duniya, yayyen nan na ta maza kowa ƙoƙarinsa ya ga ya kawo abin da za a rufa kai asiri, haka mama kullum cikin faɗi tashi take. Ta zubo abincin dare ta zauna tana kallon yadda kowa ke ta walwala kamar ba su da wata damuwa, ta zubawa su Mai sunan Baba ido, da suka zuba Abinci kwano ɗaya, tausayin Abubakar ya kamata, da tuna yadda yake gaya wa ɗan uwansa ya kwan biyu bai ci abinci ba, kuma ya sha garri ba ruwa balle suga, kuma ba wanda ya gayawa. Ta kalli Abincin gabanta, Usman ya sayo kifi ya ɗora mata a kan abinci, kifin da shi bai ci ba, bai kuma bawa kowa ba sai ita, gefe ga ƙullin lemon fata da Aliyu ya shigo da shi, shi ma bai sha ba ita ya bawa. A hankali ta ture abincin, ta shiga ɗaki ta zauna tayi shiru, sai kuka wani irin ƙauna da tausayin yayyen nata ya kamata.

Babu tsammani ta ga mama ta hasketa da fitila.

"Kukan me ki ke yi a duhu haka, ga abincin ki ba ki ci ba?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "Ba kuka nake ba"

"To me ki ke yi idan ba kuka ba, ƙarya nake kenan?"

"A'a mama ni fa ba kuka nake yi ba"

"To meya hana ki cin abinci ki ka dawo ɗaki ki na kuka?"

Ta girgiza kai ta ce "ba komai"

"Wai ba ance miki batun auren nan wasa bane ba, shi ne ki ka cigaba da takura kanki, ba zaki tashi ki je ki ci abincin ba?"

"Ba magana ake yi miki ba, ko sai na zo kan ki?" Ta jiyo muryar Yaya Umar daga tsakar gida. Jiki na rawa ta taso ta fito.

Cikin haɗe rai ya ce "zauna ki cinye abincin nan, sai wani ciwon ya kama ki ki cazawa mutane"

Ƙoƙarin kai abincin bakinta take, amma ta kasa kuka ya kuma ƙwace mata.

Aliyu ne ya dubeta ya ce "Ko Abincin ne ba kya so, ki ke yiwa mutane kuka? Me zaki ci?"

"A'a zan ci"

"To kukan me ki ke yi?"

"Ku ƙyaleni dan Allah, na ƙoshi ne" tayi maganar tana share hawaye.

Abubakar ya ce "Ikon Allah, taso dawo nan kusa da ni, zo ki saka hannu mu ci namu abincin tare" ba ta son ɓata masa rai, dan haka ta tashi ta je kusa da shi ta zauna, ya dinga ɗebo abincin yana bata a baki tana karɓa yana rarrashinta ba tare da sanin dalilin kukan nata ba, sai dai ba rarrashin da yake yi mata ne ya sanya ta yi shiru ba, hararar da mai sunan Baba ya jefeta da ita ne, ta sanyata haɗiye kukan da take yi.

Haka ya dinga lallaɓa ruma, da kansa ya gyara mata wurin da zata kwanta, ya saka mata net, har da yi mata addu'a, hakan ya ƙara sanya tsananin tausayinsa a ranta. Sai da ya tabattar ta ɗan nutsu, sannan ya tashi ya fita, Mai sunan baba kuwa sai tsaki yake yi, yana hararar Abubakar, ya san da ya yi wani yinƙuri na yiwa ruma tsawa, zasu yi faɗa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull