Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 20
Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 20: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 20. Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin…
3,353 words
Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin sheshsheƙar ruman a cikin net ɗinta.
Mama ta kuma haskta da fitila ta ce "Ke dan ubanki fito daga cikin net ɗin nan, ki zo ki gaya mini abin da aka yi miki?"
Ruma tayi saurin goge fuskarta tayi kamar bacci take yi.
A hasale mama ta ce "Ba zaki fito ba sai na zo?" Ruma ta janyo jikinta ta fito, ta zo gaban mama ta zauna, amma ta kasa magana.
"Gaya mini menene kuma? Ko wani ne yayi miki wani abun?"
Ruma ta girgiza kai, "to kukan me ki ke yi wa mutane, ki gaya mini ko na leƙa na kira miki dodon naki"
"Kiyi haƙuri, zan gaya miki amma kar ki ce na gaya miki"
Mama ta ce "Ina jinki" nan ruma ta kwashe komai ta gaya wa mama, sannan ta ɗora da cewa "Mama Allah ya bamu kuɗi, ya horewa su Yaya ya sa kar su daina zuwa makaranta, kuma ni ba sai an canza mini makaranta ba, Allah ya bamu kuɗi su daina shan wahala, yayana ya kwana biyu bai ci abinci ba mama, wai an kore shi daga kamfani bai gaya miki ba" ta ƙarasa maganar tana kuka.
Jikin mama yayi sanyi ainun, duk wauta sa rashin tunani irin na ruma ashe ta na da hankali wasu lokutan, biri ya yi kama da mutum, Abubakar ya rame amam yaƙi gaya mata meke faruwa.
Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ruma, kin ga wannan yana ɗaya daga dalilan da yasa nake miki faɗa a kan nutsuwa, ke gaki a gida amma sai abin da ki ke so shi zaki ci, kin ga yadda suke ta wahala da ƙoƙarin faranta mana, dan Allah ki daina rashin ji kin ji, ki yi ta yi muku addu'a, nima ina yi, yanzu ki je ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu kin san zaki tahfiz". Ruma ta jima ta kwanta, sai dai bayan kwanciyarta mama ta kasa barci, sai tunanin yadda za ta ɓullowa al'amuran.
***** Kirarin da ɗaya daga cikin hadiman Ammi ke ta rangaɗawa ne, wadda suke kira da Baba uwani, ya tabattar wa da su Iman da ke zazzaune a falo, takawa zai shigo, nan suka din ga kintsawa, ban da Iman da ta rashe a jikin Ammi, suna hira. Sai dai Adam tare da Jabir suka shigo, hakan ya sanya Iman jan mayafi ta rufe kan ta. Cikin girmamawa suka gaida Ammi, Jabir ya kalli Iman ya ce "Ke ba ki san girma ya zo ba ne?, Look at you, you are now a big girl duk kin bi kin danne mana Ammi"
"To idan ba ta danne ni ba wa zata danne? Ƙyaleta 'yar auta ce ai"
Jabir ya yi wani murmushi sannan ya ce "Ammi, biyo takawa na yi, na kawo miki ƙararsa, ko ke zai ji maganar ki"
Adam ya harari Jabir, amma Jabir ya maze ya cigaba da magana.
"Ammi kin san halin ƙasarmu sarai, kin san yadda abubuwa ke gudana, duk da kasancewar sa shima wani ne, amma gaba da gabanta ta yaya zai sako Senator wakili da mutanensa a gaba, ai duk wanda ya kwana ya tashi, ya san mutane ne masu ɗaurin gindi, dan me zai tsananta?"
Ammi ta ɗan numfasa ta ce "Ban ƙi ta taka ba Jabir, amma abin nan na ga duk sabgar aikinku ce, ni ba komai nake ganewa ba, amma nima ina yawan yi masa magana a kan ya san in da zai din ga kai kansa"
"Yanzu haka Ammi, wai akwa ibom zai je, na rasa abin da zai kai shi wata akwa ibom"
Ammi ta kalli takawa, da ya kashingiɗa ya lumshe ido, kamar ba a kansa ake tattaunawa ba, ta yi murmushi ta ce "Rabu da shi Jabir, zan yi magana da shi"
"Ai gara dai Ammi" ya mayar da kallonsa kan Iman ya ce "Iman, ɗan sama mini abin sha mai sanyi mana, zan je garden in ɗan yi wani aiki"
Haushi ne ya kama Iman, ga masu aiki amma bai saka kowa aikin ba sai ita, ga Ammi a zaune balle ta ce ba zata yi ba. Haka ta tashi ta tafi kitchen dan haɗa masa wani abun.
Adam kuwa ɗakinsa ya wuce, ya je ya nemi wuri ya kwanta, dan ya ji kansa ya fara yi masa ciwo, tun wayewar garin yau.
A garden ta tarar da Jabir, tun da ta ɓullo ya kafeta da idanunsa, da hakan sai da ya ƙona mata rai, ta yi tsaki. Tana zuwa ta dire masa jug da kofi, za ta juya. "Ɗan tsaya mana" ta tsaya cak, sannan ta waiwayo ta kalle shi.
"A tunaninki haka kawai na ce ki zo ki sameni a garden, magana zamu yi".
Cikin yanayinta mai kama da shagwaɓa ta ce "Ni uncle J karatu fa zan yi, ina da exams"
Tashi yayi ya zagaya kusa da ita yana kallonta.
"Maganata ba ta da muhimmanci kenan?"
Ta ɗan ja da baya ta ce "To ina jin ka"
"Iman me na yi miki ne ki ka tsaneni, ki ke guduna kwanan nan?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Sai gani yayi kamar ta ɗan razana tana kallon wuri ɗaya.
Waiwaya ya yi domin ya ga mai take kallo, Mahmud ya gani a tsaye yana kallonta, gaba ɗaya ta ruɗe.
"Zo nan" Mahmud ya faɗa cikin isa yana kallonta.
Jabir ya ce "Kamar yaya ta zo, haka ake yi?"
"Ban saka da kai ba, kar ka ɓata mini rai"
Jiki na tsuma, Iman ta sunkuyar da kai ta nufi in da Mahmud ya ke.
"Amma Mahmud kamar ba ka ikon nuna wa iman wannan isar, tun da dai ba wani abu a tsakanin ku"
"Jabir, kafi kowa sanin waye ni, idan ba ka kiyayeni ba, za a ji kaina da kai, ba ruwana da abin da ku ka laɓe a lambu kuna yi, abin da ya dameni shi zan yi"
Waro ido Iman ta yi, jin abin da Mahmud ya faɗa, sai dai ko kusa ba ta ga fuskar da zata kare kanta ba, haka zalika ba ta da zaɓin da ya wuce ta bi umarnin Mahmud.
Ya tasata a gaba har sashin su na Mummy, da Mummy da Fuziyya da ruƙayya duk suna falon sai kuma Samha da dama tun tasowarta kusan kullum tana gidan su.
"On your knees" yayi maganar cikin tsawa. Cikin mamaki iman ta yi abin da ya ce, tana son jin laifin da ta yi.
"Ke saboda baki da mutunci, Mummy ta aika a kiraki amma ki ce ba zaki zo ba aiki ki ke yi wa Ammi, Mummy sa'arki ce?"
Cikin rashin fahimta iman ta ce "Ni kuma? Wallahi ba wanda ya zo ya kirani"
Mummy ta ce "Au iman ruƙayya ƙarya za ta yi miki kenan, ai da ka ƙyaleta, dama ta daɗe tana nuna mini ba ni na haifeta ba, dama ba wani abun ne ya sa na ce a kirata ba, dogwayen riguna ne na saya musu, nace ta zo ta karɓi nata".
"Wallahi Mummy ban haɗu da Ruƙayya ba jiya, ruƙayya a ina muka haɗu?"
Ruƙayya ta ce "Ni zaki rainawa hankali, kina falo fa kina kallo a lokacin ki ka ce mini ba zaki zo ba"
Samha ta girgiza kai ta ce "Yaya Mahmud, ta ina zaka yi tsammanin tarbiyya a wurin 'yar da ba jinin sarauta ba, 'yar karere 'yar riƙo"
Haka suka din ga jifan iman da miyagun maganganu.
Tun da ta taso, ta buɗi ido a gidan Galadima, take fuskantar ƙalubale sharri gami da makircin hajiya Jamila wato Mummy, makira ce ta gaske. Suka ƙare mata cin mutunci, Fauziyya ta watso mata dogwayen rigunan a jiki, Mahmud ya ce ta yi godiya ta ɗauka ta bar sashen. Ba yadda ta iya, ta aikata abin da ya ce ta tashi ta fita gwiwa a sanyaye.
Mummy tayi murmushi, a ranta ta ce bari mu gani, yarinyar nan zata gayawa wancan mahaukacin ne ya zo yayi hayagaga ko kuwa? Idan har ya zo yayi mana tashin hankali, zan tabattarwa da Samha akwai alaƙa a tsakanin iman da Adam, ko kuma in cigaba da amfani da wannan damar, wurin rura wutar ƙiyayya tsakanin Mahmud da shi, ina baƙantawa matar nan.
***** Mama tayi ta faɗi tashi, ta tarawa Abubakar kayan abinci na komawa makaranta, wanda sam shi bai san ma tana yi ba, tun da ya dawo yake ta buga-buga yana tara ɗan abin da zai tafi da shi, ranar da zai koma mama ta tambaye shi babu wata matsala, ya ce mata eh ai yana da komai. Mama ta yi murmushi, ta nuna masa watto bagco ta ce ya ɗauko, ya duba. Ya ɗauko ya duba, kayan abinci ne da ta tara masa.
Ya ce "Mama na gaya miki fa ina da komai, Meyasa zaki takura kan ki?"
"A'a ni ban takura kaina ba, Ubangiji Allah ya bada sa'a ya taimaka" yayi ta yiwa mama godiya, mai sunan Baba ya raka shi tasha, ya bashi dubu biyar, amma sai da suka kai ruwa rana Sannan ya karɓa.
Ruma ce ta fito daga wanka, ta tsaya a gaban mudubi daga ita sai pant, tana kallon kanta. Mama ta kalleta ta ce "Meye haka ne ki ke tsaye tsirara ki nemi kaya ki saka"
Ruma ta juyo ta kalli mama cikin damuwa ta ce "Mama kalleni"
"Na ganki meyafaru?"
"To ba abin da ki ka gani?"
"Ni banga komai ba"
"Mama wai baki ga ƙirjina kamar ya kumbura ba?"
Mama tayi murmushi ta ce "Na gani"
"Mama to ya kike dariya, ba alamomin ciwon Cancer bane?"
Mama ta ce "A'uzubil'ahi, ba wannan bane ƙirga dangi ki ka fara"
Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Wane dangin na ƙirga, ni ina zan iya ƙirga danginmu?"
"Ba wannan ake nufi ba, girma ki ka fara zaki zama budurwa, fitowa za su yi"
Ruma ta haɗe rai ta ce "Ni bana son su fito"
Mama tayi dariya ta ce 'Saboda me?"
"Da nace ina son su fito a daina ce mini ƙwaila, Yaya Aliyu ya ce gara na yi zamana a haka, ai suma basu da shi"
"To ke namiji ce, da zaki zauna a haka nan gaba da kanki zaki zo kina nema daga baya, ke da a da ki ka ce zaki sayo na sayarwa ki saka"
"To ai yanzu na fasa, gara kar ya fito, idan ya fito fa ba zan din ga yawo ba riga ba"
Mama ta ƙarewa ruma kallo, alamomin girma duk sun fara bayyana a jikinta, mama ta numfasa ta ce "Yanzun ma ai na hanaki yawo babu riga"
Ruma ta ɗau vest ɗin ta ta saka, ta ce "Mama kalli fa, kalli yadda vest ɗin fa tayi mini, to wai tsayi zai cigaba da yi? Ko kuwa?"
"Nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito, sai ki ga yadda za su yi, ki dai kula da kanki, ban da wasan banza da maza ko mace, duk wanda yayi miki wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki, idan kin zo ki gaya mini, wannan wurin ba wurin wasa bane, gaba ɗaya jikinki ma al'aura ne abin alkintawa ne".
"Ni mutum ya taɓani ma, ba sai na sumar da shi ba"
"Ni dai bana son rashin hankali, ki kula da kanki, zuwa gaba in ga mai yakamata ayi, idan rigar mama yakamata a saya, sai a sayo ki farawa sakawa".
Ruma ta ce "Taɓ, haka kurum a din ga yi mini kallon 'yar iska"
Mama zata yi magana, usman yayi sallama ya shigo, ba ta amsa sallamar ba ta ce "Yaya usy, kalleni me ka gani?"
Ya ce "A ina?"
"Au dan ubanki gaya masa zaki kin fara nono, ni yau na ga ta kaina, Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Jin abin da mama ta ce ya sanya Usman ja da baya ya bar ɗakin.
(Masu nema daga farko, ku din ga dubawa watpad ko arewabooks)
Ayshercool 08081012143 [01/08, 5:33 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
*Na Aisha Adam (Ayshercool)*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
P19
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su. *1 Supplements na gyaran jiki*
*2 Supplements na gyaran gashi*
*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*
*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki glowing skin*
*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress
*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*
*7 Supplements na masu shayarwa*
*8 Supplements na tsofaffi*
*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*
*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*
*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*
*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14Supplement na whitening/glowing skin*
*15 Supplement for Acne, dark spots remover*
Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
P 19
"Wai ke duk yadda mutum ya so ya kwaɓeki ya nuna miki rayuwa ruma ba kya ganewa, sai ka ce rainon daji, yanzu usman ɗin zaki gayawa kin fara ƙirgar dangi, abin da ake ɓoyewa a tattala?, kai wannan yarinya kune yaran ƙarshen zamani"
"To mama ai gani na yi yayana ne, kuma bana ɓoye musu komai"
"Eh ba kya ɓoye musu komai, kuma aka ce miki ciki har da tsairaicin ki ko? Ɗauki kaya ki saka ni ki fice ki bani wuri, kan na taso kanki."
Ruma ta durƙusa ta ɗau kayanta ta saka, dama mama ce za ta aiketa.
Mama ta kalleta ta ce "Ruma wai ke komai naki butsu-butsu babu kintsi, haka ake ɗaura zanin ma, dama a dama ake ɗaura zani, kalli ƙwaurinki duk a waje kamar zaki tsallaka wuta"
Kamar ruma za ta yi kuka ta ce "Mama ni ya zan yi, ni wallahi bana son zanin nan, idan ina tafiya a hanya ji nake yi, kamar na kwance shi na riƙe a hannu, harɗe mini ƙafa yake, ni nafi son wando ko doguwar riga"
"Aikuwa kin daina saka su, dole ki koyi ɗaurin zani ki na 'ya mace, matsonan na ɗaura miki"
Ruma ta ƙarasa fuskar ta a haɗe, dan har ga Allah ba ta ƙaunar zani sam.
Mama ta ɗaura mata sannan ta kalleta ta ce "Ga farar hoda can a kan mudubi, ki ɗan shafa sannan ki saka kwalli"
"Mama farar hoda kuma kamar wata 'yar tashe, ni ki bar mini fuskata a haka kawai, bana son shafa mata komai, kwallin nan ma idan na saka zazzagowa yake fuskata ta koma kamar ta boka"
Mama ta miƙe ta danƙi hannun ruma, ta ja ta zuwa gaban mudubi ta ce "Wallahi sai kin saka kwalli, ba zaki fita da ido kamar jan nama ba" ruma har da kuka mama ta gwale idonta ta saka mata kwalli, ita ruma a rayuwarta duk wani abu ma shafe-shafen kwalliya na mata, bai dameta ba ba tayi, dan basa burgeta. Ta sha zagi wurin mama kan ta tafi aiken nan.
*** Takawa kuwa lokacin da ya shiga ɗaki, kan sa ciwo yake yi masa sosai, dan bacci ma yake ji a lokacin. Kwanciyarsa babu daɗewa bacci mai nauyi ya fara ɗaukarsa, sai dai baccin bai je ko ina ba ya fara jin wannan muryar a kunnensa tamkar ana yi masa raɗa "Sarki mai koriyar alkyabba" a hankali ya buɗe idonsa, ya hau dube-dube a ɗakin, amma babu kowa. Kawai sai ya ji ba ya son kwanciyar, dan haka ya tashi da sauri ya fito daga ɗakin.
Iman kuwa sai da ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga sashen Ammi.
Ammi tana nan a in da suka bar ta a falo ba ta tashi ba, Iman ta ƙaraso cikin yaƙe ta ce "Ammi, kin ga Mummy ce ta kirani ta bani"
Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke da ki ka fita kaiwa Jabir lemo, me kuma ya kai ki sashin su? Kin san bana son zuwanki in da suke"
Iman cikin dakiya da ƙoƙarin danne hawayenta ta ce "Yaya Mahmud ne ya kirani, ya ce Mummy na nemana shi ne ta bani, bari na je na gwada" ta na gama maganar ta yi gaba, dan kar Ammi ta fahimci wani abu.
Takawa na tsaye a falon, har Iman ta yi gaba, ta ji ya janyota ya dawo da ita, ya ɗan ƙura mata ido.
"Me suka yi miki?"
"Wai ni? Babu komai fa, kaya kawai ta bani"
"Me suka yi miki?" Ya kuma maimaitawa.
Tunanin ƙaryar da zata yi masa ta hau yi, amma kan ta kai ga furta komai ya daka mata tsawa, hakan ya sanya jikinta fara rawa. Cikin razani ta gaya masa abin da ya faru.
"Wuce ki tafi" ya faɗa yana nufar ƙofar fita daga falon.
Ammi ce ta tare shi ta ce "Ban lamunta ba, kar ka kuskura ka je in da suke, da gayya suka yi, ka ƙyale su kawai"
"Ammi, ba saboda Iman kawai nake wannan abun ba, na san a duk lokacin da aka taɓata, kai tsaye ka aka yiwa, Ammi ko tausayin yarinyar nan ba sa ji?"
Ita kanta Nusaiba da ke zaune tana cin abinci, al'amuran gidan sun fara isarta, tana tausayin Iman sosai da sosai.
Ammi ta ce "Na fahimce ka takawa, amma tun da ka ga ina kawar da kai, to kai ma ka dinga haɗawa da haƙuri, ka koyi kawaici ba a komai zaka yi magana ba, kar ka kula su".
Baba Uwani da ke 'yan kaye-kaye a falon ta ce "Ayi haƙuri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi haƙuri"
Da ƙyar Adam ya haƙura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa, shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.
Nusaiba tsam ta miƙe, ta nufi ɗakin Iman, ta tarar da Iman ɗin zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.
Nusaiba ta dafata ta ce "Masoyiya"
Iman ta kalli Nusaiba ta ce "Na'am Anty Nusyna"
Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.
"Be brave iman, kiyi haƙuri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko ɓata ranki"
Iman ta yi murmushi ta ce "Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba"