Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 24
Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 24: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 24. Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma…
3,339 words
Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma shi wannan 'yar shilar ke rainawa hankali, yana yi mata magana amma ta mayar da shi ɗan iska.
Jabir ya jinjina kai ya ce "Lallai gaba da gabanta, anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace ba?" Kallon Jabir tayi ta galla masa harara, haka kawai tana ganinsa ta ji ta tsaneshi, wani mugun haushinsa ya kamata, ya fiye shishshigi.
Adam rasa abin yi ma yayi, dama wata babbace he knows how to deals with her, amma wannan ya hukunta ta ya ce ya yiwa wa?.
Ruma ta miƙe tsaye da jakarta, tana kallon wanda suka kawota, jinjina kai kawai suke, da ganin namijin ƙoƙarin da ubangidansu yayi.
Cikin ƙunƙuni ta ce "Ni a mayar da ni in da aka ɗauko ni" tayi maganar tana nufar ƙofar fita.
"Ku kamata ku ɗaure mini ita, sannan a nemo mini waye ubanta, in nuna wa babanta banbancin arziki da tsiya, shine dai-dai yi na, dan na fuskanci bayan talauci har da rashin tarbiyya a tare da ita.
Ba tare da ta waiwayo ba ta tsaya, dan ma kar ta kalleshi ya yi mata kwarjini ta ce "Shi baban nawa sai ka bishi kabari ka nuna masa ka fishi kuɗi, kuma Alhamdilillah ni dai an yi mini tarbiyya dai-dai gwargwado, kuma wallahi sai na saka yayyena sun yi maka bugun sakwara, har DPO na unguwarmu sai na gaya masa, ba sunanka Adam ba ɗan galadima ko wambai to wallahi sai na faɗa ka saceni ka kawoni cikin maza" tuni ya daskare a wurin, jikinsa ya hau tsuma, ga zafin maganganu da fitsarar Ruma, ga razani na jin muryar da take ta addabar kunnuwansa.
Cikin azama ya fizgota, ya juyo da ita gabansa, ya riƙe hijjabinta tare da rigar uniform ɗin ta. Kallon hannun takawa tayi, da ya sanya wani agogo mai kyawun gaske, amma babban abin da ya razana ruma, yadda ya riƙota ta wuya hannun ƙaton namiji a jikinta kan ƙirjinta, abin da aka ce ta ɓoye ta tattala, kar wani ya kai hannu wurin, idan ba haka ba za tayi ciki, amma hannun wani ƙato a wurin !!!
(Saura page ɗaya mu kammala book1, wanda za su sai book 2, an fara payment 500 ne, in sai an gama document 800.
0009450228 Aisha Adam Jaiz bank. Sai a turo shedar biya ta 08081012143)
Ayshercool 08081012143 ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
P22
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*
Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su. *1 Supplements na gyaran jiki*
*2 Supplements na gyaran gashi*
*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*
*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki glowing skin*
*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress
*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*
*7 Supplements na masu shayarwa*
*8 Supplements na tsofaffi*
*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*
*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*
*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*
*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14Supplement na whitening/glowing skin*
*15 Supplement for Acne, dark spots remover*
Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Wani mugun ɓacin rai ne ya kama ruma, kamar za ta yi kuka ta ce "Malam meye haka? Meyasa zaka taɓani ka cikani"
Cikin tsananin mamaki, da rashin abin yi yake sake sauraren muryar ruma "Da..d...dama kece, meyasa ki ke bibiyata mai na yi miki ne?"
"Ni yaushe na sanka ma? Ka cikani kafin na yi maka hauka da tijarar da zaka yi dana sani, ka sakar mini hijjabi"
Tsananta riƙon da yayi wa ruma ya yi, yana sake bin ta da kallo, yana jin tamkar ba shi bane ba, anya mutum ce yarinyar nan, ko kuma dai muryar ce ke cigaba da yi masa gizo.
Ganin yadda duk ya gigice kamar zai fita hayyacinsa, ya sanya Jabir ƙoƙarin cire hannun takawa daga jikin ruma.
"Takawa, dan Allah ka kula mana, yarinya ce fa ƙarama ba sa'arka ba, dan Allah ka saketa, sannan kamar yaya tana bibiyarka?" Hankaɗe ruma yayi, ya koma gefe ya zauna, yana dafe goshinsa.
Kuka ruma take wiwi, ta ɗauki jakarta.
Jabir ya kalli wanda suka kawo ruma ya ce "Sidi ku mayar da ita".
Suka tasa ruma a gaba, ta waiwayo ta kalli takawa ta ce "Wallahi ban yafe ba ku....."
"Ke wuce mu tafi, kin samu an ƙyaleki kuma kina yi wa mutane iskanci, mara tarbiyya"
Cikin dakiya ta ce "Eh bani da tarbiyyar, ku tarbiyyar ce ta saka kuka ɗauko ni ba da sanin iyayena ba ku ka kawo ni nan, cikin maza Allah sai ya saka mini"
Jabir ya ce "Kar ka kuma tankawa yarinyar nan, mayar da ita"
Jabir ya zauna a kusa da takawa ya ce "Takawa, wa me yake faruwa ne, ka san ta ne?"
Adam yayi shiru bai motsa ba, kuma bai ce komai ba, Jabir ya yi masa tambayoyi har ya gaji, amma bai amsa masa ba.
Ruma kuwa suna zuwa unguwar su, suka ajiyeta suka tafi, ta samu wani borehole ta wanke fuskarta, sannan ta tafi gida. A tsakar gida ta tarar da Yaya Aliyu, ya kalleta ya ce "daga ina ki ke?"
"Makaranta" ta bashi amsa tana ɓata rai.
"Ba jarrabawa ku ke yi ba?"
"Laifi muka yi aka saka mu punishment" ta bashi amsar tana tsoron kar ya ganota.
"Haka dai ki ka iya, kullum cikin laifi kamar ke kaɗaice ɗaliba a makarantar"
Ganin bai ganota ba, ya sanya ta shiga ɗaki, ta ajiye jakarta ta tafi gaban mudubi ta tsaya, ta ƙarewa kanta kallo, ta tuna yadda takawa ya shaƙeta hannunsa har yana taɓo ƙirjinta. Wasu hawayen ne suka shiga ziraro mata. "Wallahi sai ka gane baka da wayo, ka zunguro sama da kara, ni za a ciwa mutunci? Wallahi sai na kuma rubutawa, zaka gane ba ka da wayo, ai talauci ba hauka bane, mai kyan banza" haka ta tsaya a gaban mudubi, ta cigaba da kuka. Kamar zararriya ta ɗauko jakarta, ta ɗauko wayar ta kuma komawa kan account ɗin da Jabir ya saka hoton takawa, ta sake rubuta "Wallahi Allah ban yafe ba, sai na kai ƙararka wurin 'yan sanda, zaka san da ni kake yi" ta ajiye wayar tana fatan Allah ya sa kar idan mama ta dawo ta fuskanci wani abu.
****
Baba uwani ce ta shiga kitchen ta tarar da iman tana faten dankali.
"A'a mutuniyar ba kya gajiya da aiki, Ammin ake yiwa girki ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "A'a baba uwani, nice zan ci"
"Au yau ba za a ci abincin namu ba ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "Ba haka bane, kawai da wannan ɗin nake sha'awa bana son takura muku ne"
"A'a ai da kin faɗa ma babu wani abu, sai ayi miki, ni kuwa na ce takawa lafiya ƙalau kuwa yake?"
Cikin rashin fahimta iman ta ce "Me ki ka gani?"
"Ganinsa na yi duk wani iri"
"A'a lafiyarsa ƙalau, ina ga hakan ya na da alaƙa da yanayin aikinsa, kin san abubuwa su kan yi masa yawa"
Baba uwani ta ce "haka ne wallahi, ina tausayawa takawa yadda al'amura suke shan kansa Allah ya yi masa jagora"
Iman ta ce "Amin" a dai-dai lokacin ta juye dankalin a plate ta ɗauka ta fice.
Baba uwani ta yi tsaki ta ce "Kai wannan yarinyar kininabbiya ce ba wani abu da zaka samu daga wurinta".
Takawa fa abubuwa suka sake rikice masa, tun bayan haɗuwarsa da ruma, da ya ji muryarta da take masa yawo a kunne, yana ta tuntuntuni, mutum ce ko akasin haka, dan iya ƙwarin gwiwar ta, da rashin kunya da ayar tambaya a kanta. Yau gaba ɗaya bai koma gida ba, ya wuce gidansa ya tura wa Ammi message a kan ba zai shigo gida ba, a gidansa zai kwana. Bayan ya turawa Ammi saƙon, ya kuma komawa Instagram, ya duba comment ɗin da ruma ta yi a kansa, kawai ya ci karo da sabon saƙonta, ya tabatta kenan ita ɗin ce dai ta yi comment ɗin farko. Kiran Ammi ne ya shigo wayarsa, ya saita nutsuwarsa ya ɗaga tare da yin sallama. Ammi ta amsa sanna ta ce "Yanzu na ga saƙonka, ka sam yadda yanayin jikinka yake, amma ka ce zaka kwana a gidanka kai kaɗai, kar wani abu ya sameka fa"
"Ammi kar ki damu, babu abin da zai sameni in sha Allah, ina son gabatar da wani aiki ne"
"To shikenan, amma dai da ka ji wani abu ka kirani a waya".
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, in sha Allah sai da safe" suka yi sallama ya katse kiran.
Ya rintse ido, yana jin muryar ruma na sake amsa kuwwa a kunnuwansa, ya tuna yadda ta danganta shi da sata, take ya ji ya tsani yarinyar, kuma daga uniform ɗin jikinta zaka gane 'yar talakwa ce, amma sai ƙarfin hali da rashin mutunci, to yayi faɗa da wannan 'yar ma ya ce ya yi da wa? Wani uban tsaki ya ja, ya koma ya kwanta yana ƙwafa. Ya kuma komawa ya na duba comment ɗin ruma, amma ya tarar Jabir ya goge posting ɗin gaba ɗaya.
*** Ko da mama ta dawo, ta tarar gaba ɗaya ruma ba ta da walwala, duk tayi wani iri, mama ta tambayeta ko ba ta da lafiya, ta ce ita lafiyarta ƙalau kan ta me yake ciwo, mama kuwa ta ƙayleta, amma ta cigaba da monitoring ɗin ta. Yau ko wannan uban surutun da take kamar an jefeta a ka, babu ta yi shiru sai tunane-tunane take a ranta, a kan me za ta yi wa wannan ɗan tahalikin ta huce, gashi ita ba ta san a ina ma za ta sake ganinsa ba, balle ta gaggaya masa magana ta huce da abin da yayi mata.
Mama suna ta hira suna tsara yadda bikin saukar su Yasir zata kasance, ruma ta koma kusa sa Abdallah ta ɗan yi ƙasa da muryarta ta ce "Yaya Abdallah, dan Allah waye galadiman Kano?"
Ya dubeta ya ce "Basarake ne a Kano, ba shi ne aka ce yana Germany ba bashi da lafiya, meyasa ki ke tambaya?"
"Babu komai kawai tamabaya na yi, amma ba ya mutu ba?"
"Anya, gaskiya ban sani ba, na ji dai an ce yana Germany babu lafiya"
Ɗan shiru ta yi ta na tunani, a wurin Hauwwaliya kawai za ta samu abin da take so, dan haka ta sake gyara zama ta ce "Yaya dan Allah ranar juma'a mu je cikin gari"
"Ba zani ba, ina da abin yi ranar"
"Dan Allah, na ji mama tana waya da mamansu, an ce Hauwwaliya babu lafiya dan Allah ka kaini na ganta"
"Ke na ce miki ina da abin yi ranar"
"Ai Allah na ce, ka taimaka" ta yi maganar cikin magiya.
Abdallah ya ɗan yi tsaki ya ce "Zan yi tunani"
Ta ce "Dan Allah ka kaini"
Bai sake kulata ba, saboda baya son magiya, ruma kuwa ta ƙware a kanta.
***
Kamar wasa Samha ta kira Khalifa a waya, kamar dama jiran kiranta yaje, tana kira ya ɗaga.
"Adon gari ya kike?"
"Ba dogon surutu ba, ina son sanin deal ɗin da kake son mu yi, na gani idan zan iya"
Murmushi ya yi, tare da kashe sigarin hannunsa ya ce "Kin yi tunani kin ga ni ke da mafita dai kenan? Sai dai kin so ki makara dan na samu wanda ya kawo tayin shiga deal ɗin, ban sani ba ko ta wurnki aka samu bayani, amma duk da haka kema akwai role ɗin da zaki taka, a ina zamu haɗu?"
Cikin mamaki Samha ta ce "Amma waye haka, da har ka ke tunani ta hanyata ya ji labarin deal ɗin nan?".
"Kar ki damu da sanin waye, mu haɗu a hotel ɗin da muka haɗu last"
Ta girgiza kai ta ce "No, kar ka manta ni 'yar babban gida ce, ba zai yiwu ma din ga yawon hotel ba, ka sama mana wani wurin kawai".
"To Shikenan, zan turo miki wani address ɗin, ki huta lafiya" ta sauke wayar daga kunnenta, tana tunanin anya ba ta yi garaje ba wurin amincewa da Khalifa ba tare da ta san aikin sa za ta yi masa ba?.
***
Ranar juma'a ana tashi daga makaranta ruma ta taho gida, saboda ta tirke Abdallah ya cika mata alƙawarin kai ta cikin gari, dan tuni ta tambayi mama, mama ta barta Abdallah ya kaita, musamman da ta ji ta ce Hauwwaliya zata duba. Ƙasan zuciyarta kuwa, so take ta sake haɗuwa da takawa, ta yi rashin kunya ko ta huce abin da ya yi mata. Duk wani hoton Adam yake kan account ɗin Jabir, sai da Jabir ya sauke shi, ƙarshe ma yayi blocking ɗin ruma, bayan yayi reporting account ɗin ta an rufe mata shi.
Abdallah ya ce "Sai dai ruma ta yi haƙuri, dan wani wurin za shi, amma mama ta ce ya daure ya kaita, dan ruma a zahiri damuwa ta nuna da rashin lafiyar Hauwwaliya.
Ba dan ya so ba ya tasa ruma a gaba zuwa mandawari, Hauwwaliyarma ta samu sauƙi, bayan sun gaisa da mutanen gidan, Abdallah ya ce da yamma zai zo ya ɗau ruma.
Hauwwaliya ta yi ta murna da ganin ruma, dan rabon da su haɗu tun wancan zuwan. Bayan ruma ta ɗan jima, ta fara ƙoƙarin aiwatar da abin da ya kawota.
"Hauwwaliya, ina ne gidan Galadima ne?"
Hauwwaliya ta ce "Wai makaranta?"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Galadiman kano"
"Wanne?"
"Au biyu ne?"
Hauwwaliya ta ce "Ai akwai Galadima na yanzu, wanda ba shi da lafiya yana Germany, sannan akwai gidan Galadiman kano wanda ya rasu"
Ruma ta ce "Wanda ya mutun"
Hauwwaliya ta yi dariya ta ce "Ke ai wan baban su Janna ne, jikar turakin nan da muka je gidan su biki ta bamu kaya, kuma yayan Galadiman kano na yanzu ne duk fa 'yan uwa ne, sarautar ba a rabawa a bawa bare dole sai su"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Ni fa ba nasaba na tambayeki ba, ina ne gidan na sa"
Hauwwaliya ta ce "Shi wa?"
"Ke wai ya ina magana kina raina mini hankali, maganar wa muke ne?"
"To ke meye alaƙarki da su da ki ke tambayata?"
Ruma ta ce "Assignment aka bamu a makaranta"
"Aka ce me?" Ruma ta ɓata fuska ta ce "Hauwwaliya, ni zaki wulaƙanta?". Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce "Yi haƙuri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan sarki yake, wani ƙaton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan yake"
"To kin san 'ya'yan gidan?"
"To meye alaƙata sa su da zan san 'ya'yan gidan, suma 'ya'yan gidan duk a cikin assignment ɗin suke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "A'a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna"
Haka ruma ta din ga lallaɓa Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house ɗin su Takawa.
Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka koma gida.
Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya ɗauketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta ƙudirce a ranta ba zata haƙura ba. Sai dai gate ɗin gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata 'yar kafa da za ta bi ta shiga, ga masu gadi a zaune a ƙofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sauƙi ba.
*** Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu ne mai sauƙi ba. Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shikaɗai me mafitar da ya rage mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da alaƙar nan ta yi ba, to ita da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi ƙoƙari wurin takawa su Hajiya Jamila burki a wasu ɓangarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.
*** Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a ƙarshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta can katsina a garin Ƙanƙara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi musu, masu exam a biya musu, masu buƙatar jari duk ayi musu. Sannan still akwai filinsu da aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya. Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar ɗan abin da ya samu da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba ga son su je in da suje, ƙarshe aka yanke Aliyu zai je. Yaya Abubakar ya ce "Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da faɗan da suka din ga yi ba, wai kin fiye son 'ya'ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji faɗan da ya yi ba".
Mama ta ce "Ba ƙi nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin babu lafiya".
"Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi" Mama ta ce "To, Allah ya sa"
Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe ɗaya ta fi son sai ta tafkawa takawa ɓarna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.
*** Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ƙamshi duk ya gauraye ɗakin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.
"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples ɗin ta suka lotsa, ta ce "To idan ban kwalliya ba me zan yi?"
Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai" ɓata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana faɗin "My Chubby girl".