Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 25
Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 25: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 25. *** Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja…
3,365 words
*** Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.
Gaba ɗaya Instagram sun yi banning account ɗin ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram ɗin sam.
Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.
Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.
Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.
A ƙofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ƙofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.
Gadan-gadan ta nufi shiga, wani ɗan sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"
Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"
"Waye wanin?".
"Sunanshi Adamu"
Wado ido suka yi gaba ɗaya suna kallon ruma "Ke! Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?
"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki faɗi wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"
"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"
"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".
"To a wurin wa zan nemi iznin?"
Ɗaya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da baki fil-fil kamar robot"
Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta ƙyar a cikin nasa.
Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya jiƙawa yarinyar nan jikinta.
Ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta taɓe baki a hankali ta ce "An yi asara"
"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"
"Ni dai ba a kanku nake ba, ku ƙyaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu naɗi.
Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba Sabuwa, kin dawo?"
"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"
Suka amsa mata da Alhamdilillah.
Ruma ce ta taso da sauri tana faɗin "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya aka yi?"
"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"
Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"
"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.
"Ke 'ya ta ai ba a faɗar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi"
Ruma ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"
Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"
"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "
Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".
"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"
"Zo mu baki sigari " ɗayan ya faɗa cikin iya shege.
"Sai dai uwar sigari" ta faɗa a hankali.
Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.
Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a ɓangaren Mummy, kuma tana ɗaya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan. Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar ɗakinta takardar su fara dubawa ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a ɗan tofinta, ta cigaba da ayyukanta.
Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da faɗa, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin saƙonta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da saƙonta. Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana ƙare mata zagi.
Wajen ƙarfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu. A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.
Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.
Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta miƙe tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.
Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani saƙona" babu musu ta fito da takarda ta miƙa masa. Ya juya ya fice.
Fauziyya ta ce "Sabuwa, takardar mecece?"
"Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ƙofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma"
"To meye a ciki?"
"Ai kin san ba iya karatu na yi ba"
"Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless" Sabuwa ta tashi cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.
Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.
Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar ta faɗo. Ya buɗe takardar wasu 'yan ƙananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter's.
*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ƙanne mata shi ya sa ka yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka saka aka ɗauko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba taɓa mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka shaƙoni hannunka yana taɓa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taɓa shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faɗa an saci kuɗin talakawa an je karatu ƙasar waje. Mu zuba mu gani daga maƙiyiyarka RUMAISA MAHMUD ƘANƘARA ƊORAYI TUNGA ƘANWAR MAZA Kazo ka kasheni*
Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ƙirjinta ranar da aka kai masa ita.
Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ƙuruciya.
"Zan ƙure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita wasiƙar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ƙular da shi irin wai ya taɓa mata nono, duk da bai riƙe cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.
Mama ta haɗawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ƙarshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taɓa nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.
Uniform ɗin ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ɗoɗar Abdallah ne ya goge mata su, sai ƙamshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye. Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ƙazantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buɗe idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?
A hankali ya sauke glass ɗin motar, suka yi ido huɗu da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba ɗaya.
Buɗe motar ya yi ya fito yana ƙare mata kallo.
"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga saƙonki, abin da ki ka ce na taɓa ɗin ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai".
"Wai kai ɗan iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango. Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke taƙama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".
Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.
"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar har da dukan ƙirjinta.
Girgiza kai ya yi, ya buɗe motarsa ya shiga, ta durƙusa ta ɗebi taɓon wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taɓon wurin ya tafi.
(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALAƘARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FAƊA? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ƊAN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BUƘATAR BOOK2 YA TUNTUƁENI TA LAMBAR WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*
Ayshercool Whats app only, ban da kira Please 🙏 0808101214
[8/22, 11:40 PM] Maman Aslam: *Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haɗa mini document ɗin littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haɗa mini document ɗin littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!* *Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
*AYSHERCOOL*
Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce "To me ka gani da ba ka yarda da shi ɗin ba?"
Cikin sanyin jiki Yasir ya ce "Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba"
Tsaki Huzaifa ya yi ya ce "Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka ɗaga mata hankali" Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shikaɗai ya san abin da yake ji a jikinsa.
Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta taɓa tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa'a a wurin taga take, dan haka take ta leƙe tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar taƙi ci taƙi cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke faɗa a wayar.
Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.
Ruma ta ɗauko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga ɗaukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai ɗagawa take tana hoto, har da hoton hanya ɗauka take, ta hau yin videon cikin motar tana ɗaukar mutane.
Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.
"Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta ɗoɗar a lailaye?" Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. Ɗaya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.
"Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke haziƙa mazaruƙs, kar na sake jin bakinki ko na make ki" Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.
"Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki"
Kamar zata yi kuka ta ce "To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi"
Riƙe kunnenta Aliyu ya yi ya ce "Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?"
"Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji"
"Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba" haka ruma tayi shiru tana ƙoƙarin goge hawaye.
Sai da suka zo wani ƙaramin ƙauye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.
Aliyu ne ya fara fusata ya ce "Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?"
Direban ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, wani saƙo za su karɓa mu wuce, yanzun nan ba daɗewa zamu yi ba in sha Allah"
Aliyu ya ce "Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai"
Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ƙorafi a kan abin da aka yi. Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.
Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin a babura, mutanen suka sauka, suka karɓo wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. Ɗaya daga cikin su ya dubi ruma cikin gurɓatacciyar hausar sa ya ce "Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.
Ya bata wata baƙar leda, ta karɓa ta ce "Na gode" Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta karɓe.
Gasashshiyar kaza ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce "Laa yaya kaza ce"
Ya harareta ya ce "Mayya, tun da baki taɓa cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya"
Ta ɓata fuska ta ce "To in mayar masa, in ce ka hanani ci?" Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.
Da ta ci ta ƙoshi ta ɗaure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.
**** Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel ɗin da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta faɗuwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala. Da yamma ya shirya ya ce bari ya ɗan fita ya je wurin abokansa, ko ya ɗan rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita. Sai dai yana fita harabar hotel ɗin, ya ji kansa ya wani sara, yayi ƙoƙarin basarwa ya fita, amma ya kasa ƙafarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya faɗi, a hankali ya juya ya koma ɗakin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.
*** Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta riƙe kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba. Ta din ga matse ƙafa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar. "Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana" cewar ɗaya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.
Aliyu ya ce "A'a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi" ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.
Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka ɗaura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.
Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce "Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya buƙata mana".
"Ɗan uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ƙyaleta ƙarya ma take ba wani kashi da zata yi"
Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su. Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ƙarewa dajin kallo tana ɗaukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.
"Ɗan uwanmu ku ba kwa sallar ne?" Ruma tayi maganar tana zama ɗan nesa kaɗan da ɗaya daga cikin mutanen.
Ya kalleta ya ce "Sai mun je gida zamu yi"
"To wai Meyasa kuke ta sawa ana tsayawa a hanya ne? Duk ku ka ja muka daɗe fa"
Ya ce "Saƙo muka karɓa a wurin 'yan uwanmu"
Ruma ta jinjina kai ta ce "Sune suka baku kaza ku bani na ci?"
Ya waiwaya ya kalli wanda ya bawa ruma kazar ya ce "Tun da ki ka cewa yayanki yunwa ki ke ji, yayi wa 'yan uwanmu waya, ya ce su sayo kazar, dama zamu karɓi saƙo a wurinsu, shine ya karɓo miki ya baki"
Ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, kuna da kirki, to ku baku da gida, 'yan uwan na ku a daji suke ba gida ba?Na ga daga daji suka fito kuma babu gida a cikin daji ai"
"Eh, bamu da gida a daji muke rayuwarmu".
Cikin mamaki ta ce "Kai sai ka ce wasu kuraye, ku wane yarene to?"