Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 34
Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 34: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 34. Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce "Ai wannan ta zama tamu, ba zamu bayar da ita…
3,374 words
Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce "Ai wannan ta zama tamu, ba zamu bayar da ita ba, ta ce sai da a kashe ta a wurin nan, dan haka muma muna so, su yi haƙuri su mance da ita, ko su fansheta da 'yan mata biyar, dan ni ba dan barde ya saka mini ido a kanta ba, da tuni ta zama yarinyata, kawai su je idan ubanta da sauransa yayi wani ƙoƙarin su haifi wata, wannan kuwa ba zamu bayar ba" yayi maganar yana ƙoƙarin rungumo ruma jikinsa.
Duk da yadda take a galaibaice, amma haka ta dunƙule hannu, ta ɗirka masa duka a ciki. Sak suka yi gaba ɗaya suna kallonta, kamar wata zakanya, ta ja da baya ta dunƙule hannu "Wallahi idan ka kuma taɓani sai na yi maka duka, ni ba 'yar iska bace ba, wane irin azzalumai ne ku? Ba kwa tausayinmu? Muma fa mutane ne kamar ku, kar Allah ya sa ku sake ni, ku kasheni ka kasheni idan kai ɗan halak ne, ni a duniyar nan bana tsoron kowa sai Allah La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" cikin tsananin ƙwarin gwiwa take maganar ga jikinta yana tsuma.
Ƙare mata kallo ya yi, dudu tsayinta bai fi cikinsa ba, ko a shekaru baya tunanin tayi sha huɗu, ko maza surrender suke idan suka shigo hannu amma yarinya ƙarama ta tsaya a gabansa tana wannan maganar.
"Dan Allah ka kashe yarinyar nan mu huta, sun hana a taɓata sun ƙi bari a saketa duk ta gallabi mutane, barde yana da matsala, kalli yadda take rashin mutunci fa" ɗaya daga cikin mutanen yayi maganar yana gyara bindigarsa tare da saita ta a kan ruma.
"Kai kuma ban saka da kai ba, idan kuma na kasa da kai to ka kwashe, kuma in sha Allah ba zaku gama da duniya lafiya ba, sai kun ga abun da Allah zai yi muku".
Murmushi ƙaton nan yayi cikin ƙarfin hali, da jin kunyar dizgin da ruma ta masa ya ce "Idan ka kasheta a yanzu ai ta ci bulus, bari in gwada mata tabon da zata tafi lahira da shi, yau ko ni ko barde amma sai na nunawa yarinyar nan iyakarta, ni ki ka ce zaki daka ko?"
Ruma ta sake gyara tsayuwa ta ce "Wallahi kana taɓani sai na ware ƙwanjina, na rama kai ka san wace ruma kuwa?"
Dogo kuwa kamar soko haka ya riƙe hannu yana kallon ikon Allah.
Cikin magiya da kuka matar nan ta fara "Dan girman Allah kayi haƙuri, kar ka yi mata wani abun zafin ciwo ne"
Ruma ta ce "Ba wani zafin ciwo, a hankalina nake, wallahi ya taɓani sai na rama, bana tsoron kowa a wurin nan"
Ya shammaci ruma ya danƙonta, zai fizge hijjabinta da yayi daƙal-daƙal saboda dauɗa, ta riƙe hijjabin ta shiga kai masa duka da hannu ɗaya tana wani gurnani da ihu kamar zakanya.
Ya saka kan bindiga ya ƙwala mata a ka, ihu ta yi ta durƙushe a wurin, sai ga jini ta hancinta.
Tasowa matar nan ta yi da ƙyar ta nufo su, sai dai kan ta ƙarasa ruma ta miƙe cikin tangaɗi ta saka hannu ta dintsi ƙasa da ciyayi, ta watsa masa a jikinsa, gaba ɗaya suka taso suka yo kan su. Riƙe ruma matar ta yi ta shiga tsakiya, ta haɗa hannayenta biyu cikin magiya 🙏 Ba ta yi maganar ba ya hankaɗeta ƙasa, ta fasa ihu jin kamar a take ɗan cikinta zai faɗo, wani irin gigitaccen ciwo ya ɗaure mararta zuwa ƙafafuwanta. Hankalin ruma ya koma kan matar, ta nufeta da sauri, amma mutumin nan ya kwarfeta, ya sanya bindiga ya dinga kwaɗa mata, yana takata da ƙafarsa, ihu take amma bakinta yaƙi mutuwa "Idan ka isa azzalumi ka kasheni, kuma in sha Allah yadda Allah ya kuɓutar da Annabi yunus a cikin kifi, ya kuɓutar da Annabi Ibrahim daga cikin wuta, sai Allah ya kuɓutar da mu, haka malamin mu ya ce mana mu yarda da Allah, in sha Allah zai saka mana" ya daka ya daka ya takata, ya sanya wani itace ya maka mata a baya. Wani irin ihu ta kuma yi, bakinta da hancinta na ta zubar da jini. Tuni ta fara gani dishi-dishi, gadan gadan ya nufi ruma, ya durƙusa a kanta ya kama skirt ɗin jikinta ya fara ja.
Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Salati da salallami mutanen wurin suka fara yi, duk rashin imanin mutanen, idan suka so keta wa haddi, suna barin idon mutanen da su, amma yana nema ya keta ruma a gaban su.
Wasu kuwa gani suke ruma ita ta janyo wa kanta, tsananin ciwon da matar nan ke ji bai hanata jan jikinta zuwa in da suke ba, ta riƙe rigarsa tana kuka tana girgiza masa kai. Wani irin mari ya kwaɗa mata, da a take shatin yatsun sa suka bayyana a kan kuncinta. Ɗaya daga cikinsu ya zo ya saka hannu ya dinga jan matar a ƙasa, ya wancakalar da ita a gefe.
Ya kuma danƙar skirt ɗin ruma, amma cikin ƙarfin hali ta riƙe.
Ji yayi an fincikoshi ta baya, an kwaɗa masa mari. A gigice ya kalli wanda ya mare shi, barde ne wanda ruma ta bawa gyaɗa kuma yake kawo mata abinci wasu lokutan.
Wata irin ashar yayi masa, cikin ƙaraji ya ce "Me ka yi mata? Me na ce maka da aka kawo ta? Au har ka manta zaka karya yarjejeniyar?"
"Amma ai ka tsaya ka ji meyafaru kan kayi mini haka"
Cikin hasala barde ya ce "An maka ɗin, wallahi da ka aikata abin da ka yi niyya, da sai na yi gunduwa-gunduwa da namanka a wurin nan" cikin huci ya nufi kan ruma, jikinta duk shaidar duka.
Ya ɗagota ya girgiza ta, ta buɗe ido ta kalleshi, a hankali ta fizge hannunta daga nasa ta mirgina ta kwanta a gefe, tana kallon matar nan, da take ta sauke numfashi da ƙyar, kamar sumammiya.
Bai sake ƙoƙarin taɓa ruma ba, ya ja ƙaton nan yayi gefe da shi yana yi masa magana.
Ruma ba ta sake bi ta kansu ba, a hankali ta mirgina, ta ƙarasa in da matar nan take kwance, tana numfarfashi, ruma ta ɗora hannunta a kan na matar, a hankali ta ji matar ta riƙe hannunta, ta sake matsawa jikin matar ita ma tana mayar da numfashi ba tare da wani ya tankawa wani a tsakanin ita da ita ba.
Dagaci kuwa tun da suka yi magana da dogo, a kan zai je ya bincika masa ruma, ya kira Aliyu ya sanar masa domin hankalinsu ya ɗan kwanta, dan haka suka cigaba da dakon abin da dagacin zai ce masu, gashi Aliyu ya riga ya gaya musu yadda suka yi dagaci, dan haka mama kullum sai ta tambayi Aliyu, haryanzu dagaci bai yi magana ba?.
*** Kasancewa Adam ba a family house ya kwana ba, Kamar kullum bisa ga al'ada yana biyawa ya gaida Ammi, dan haka yau ma a cikin hanzari ya yake tafiya, ya ƙarasa sashinta. A bedroom ya tarar da ita, sai dai saɓanin kodayaushe, ya tarar da fuskarta a haɗe, hakan ya tabattar masa da akwai damuwa.
Sai dai ya bari sun gama gaisawa, sannan ya ce "Allah ya baki yawan rai, lafiya na ga fuskar ki babu walwala?"
Ammi ta ce "A'a lafiya ƙalau, wambai ne ya bani saƙon cewa idan ka tashi daga aiki, yana nemanka" sak takawa yayi, ya dubi Ammi ya ce "Wani abu ne ya faru?"
"Ni ma ban sani ba, kawai dai ya ce yana nemanka?"
"Ko laifi na yi mass?" Adam ya sake tambaya.
"Ban sani ba takawa, ka je dai ka ji ko menene"
"Shikenan" ya faɗa a taƙaice, ya tashi ya ce "Na tafi".
"Allah ya tsare" Ammi ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.
Har ya kai bakin ƙofa Ammi ta ce "Adam!" Sai da tsigar jikinsa ta tashi, dan abu ne mai wahalar gaske ta kira sunansa haka kai tsaye.
Ya tsaya ya waiwayo ya kalli Ammi.
"Idan ka je wurinsa, ko me zai ce maka ban yadda ka tofa ko ka yi ƙoƙarin kare kanka ba, ka bishi da to kawai" Ɗan shiru yayi yana nazari, akwai wata a ƙasa kenan, a zahiri kuma ya ce "To, in sha Allah".
A falo ya haɗu da Nusaiba, ta gaishe shi, bai iya amsawa ba sai jinjina mata kai kawai ya fice.
Yana tafe yana auna kashedin ammi da kiran da wambai yayi masa, saboda shi a yanzu tension ɗin da yake ciki ya ishe shi, ba sai an ƙara masa da wani ba.
Nusaiba ta shiga ɗakin Ammi, ta tarar da ita zsune a gefen gado, ta yi shiru.
"Ammi" Nusai ta yi maganar kamar tana tsoron wani abu.
Ammi ta kalleta ta ce "Na'am ya aka yi?"
"Amma dai baki gaya wa takawa yadda kuka yi da wambai ba ko, kar ya hasala?"
Ammi ta girgiza kai ta ce "Ta yaya zan gaya masa, ni babban fatana idan ya je kiran da yake masa, Allah ya sa kar yayi masa irin cin mutuncin da yayi mini, kin san halin yayan naku da zuciyar tsiya babu lallai ya jure, dan ma na taushe shi kan ya tafi"
Jiki a sanyaye Nusaiba ta ce "Ammi ni fa gaba ɗaya a maganganun da yayi, na kasa gane wane point yake son yayi magana a kai, sai kame-kame kawai yake yi yana faɗa na babu gaira babu dalili, ko dai Mummy ce ta je ta gaya masa wani abu?"
Ammi ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, kin san shi dai dama mutum ne mai zafi, a bar maganar kawai, 'yar auta ta ba ta tashi bane?"
"Eh bacci take yi, kin san exams suke shirin farawa".
Ammi ta jinjina kai, ta cigaba da jan carbinta.
**** Hatta masalattan unguwar su rumaisa, duk salla sai an yi addu'ar Allah ya bayyana rumaisa, saboda garkuwa da rumaisa abu ne da ya zo a bazata, kusan za a iya cewa ita ce yarinya ta farko da aka sace a unguwar, dan duk irin wannan abubuwan sai dai a ji su a nesa, amma yau gashi a cikin unguwa.
Kamar yadda dogo ya yi wa dagaci alƙawari, ya koma masa da maganar ruma. Tun da dagaci ya ji dogo ne ya zo yake nemansa jiki na rawa ya tashi, ya fita tare da fatan Allah ya sa a dace a samu rumaisa. Iya ma tashi tayi ta biyo bayansa, ya tsaya ya kalleta ya ce "Ke kuma ina zaki?"
Cikin rikicewa Iya ta ce "A ruɗe nake, ni dai mu je in ji me zai ce"
"Dan Allah ki koma, duk yadda muka yi da shi, idan na dawo zan sanar miki" da ƙyar ta yadda ta koma gida, amma ta ja ta tsaya a tsakar gida.
Cikin sauri ya fito ya iske dogo suka gaisa, cikin zaƙuwa ya ce "Ya ake ciki ka ganota?"
Dogo ya ce "Eh na ganota, tana rukunin su sha tara, sun ce ba zasu bayar da ita ba, ba sa buƙatar kuɗin fansarta, dan haka ku cigaba da addu'a, wannan yarinyar halinta zai iya sakawa su kasheta, halin na ta nema ya sanya suka ce ba zasu bayar da ita ba, dan haku ku cigaba da addu'a kawai." Daga haka dogo bai kuma ce masa komai ba ya yi tafiyarsa.
Dagaci kuwa ya tsaya ya dinga nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.
Jiki a sanyaye ya koma cikin gidan, iya ta tare shi tana faɗin "Ya ake ciki, me suka ce maka?"
Yayi shiru ya kasa magana. "Dan Allah ka yi magana mana, menene ya ake ciki ya ganota? Sun faɗi me za a basu?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Tana nan a raye, amma sun ce ba sa buƙatar kuɗin fansa, ita ɗin suke so, halinta ya saka suka ce ba zasu bayar da ita ba ta zama ta su"
"Wayyo Allah na shiga uku, yarinyar mutane ta salwanta a dalilinmu, na shiga uku na lalace".
"Meye haka ki ke yi kulu? Wannan ai rashin hankali ne".
"Ƙyaleni na yi rashin hankalin, har abada uwar 'yar nan ba zata mamta da ni da gwaggo ba na shiga uku, da na sani ban karɓi rumaisa ba, ban san haka zata faru ba, Allah ka shiga lamarin nan wayyo Allahna"
Haka dagaci yayi ta fama da iya tana kwarmato da ɓurari.
**** Rana ce ta take a kan su ruma, a hankali ta ja jikinta da yake mata ciwo, ta tashi zaune, jikinta babu abin da yayi saura sai tsabar ƙarfin hali da taurin kai. Da wannan ƙaton ta fara tozali yana hararata, ita ma hararar ta watsa masa, ta mayar da idonta kan matar nan, ta fara tattaɓata. A hankali matar ta buɗe ido, ta kalli ruma, tana ganin fuskar rumaisa ta yi murmushi. Ita ma ruma murmushin ta yi mata sannan ta ce "Tashi koma waccan bishiyar, nan rana ta tarar da mu".
Cikin ƙarfin hali ta ce wa ruma "Ba su yi miki komai ba ko?"
Ruma ta jinjina mata kai, da ƙyar matar ta tashi, da rarrafe suka canza wuri zuwa wata inuwa suka zauna.
"Yunwa ki ke ji ko?" Ruma tayi maganar tana kallon matar.
Ta girgiza wa ruma kai ta ce "A'a, ke nake so ma ki samu ki ci wani abu, baki da lafiya, dan Allah ki daina rigima kar su illata ki, ba zan ji daɗi ba".
Ruma ta ce "Mhmm ki daina damuwa da ni, ni na saba da kasada, sonake su kasheni na huta na gaji".
"A'a bana son a kashe ki, in sha Allah zaki fita lafiya ƙalau".
"Ban ga alamar hakan ba, gara na tunzurasu su kasheni na huta, suma su huta amma wallahi in dai suka barni a raye na din ga tayar wa da uban kowa hankali kenan".
Matar ta waro ido ta ce "Ke ba kya jin tsoro ne?"
"Taɓ, ai tsoro yayi yamma na yi gabas, ni fa ƙanwar maza ce guda bakwai, ko 'yan unguwarmu sun sanni, dan ma na daina dambe da maza, yayyena sun hanani, duk wata kasada idan na ɗauko in tafi ƙarfina su suke shigar mini, ni fa har wata 'ya na taɓa karyawa. Bindigogi ne fa kawai da su, to wallahi bana tsoron bindigar su kamar yadda nake tsoron mai sunan Baba".
"Waye haka kuma?"
Ruma ta gyara zamanta ta ce "Yayana ne, sunanshi umar, hmmm ina tsoron Allah ina tsoron sa, nifa bana jin tsoron mama kamar yadda nake tsoron sa, kin san idan nayi laifi baya tashi hukuntani, sai cikin dare ina tsaka da bacci zan ji ni a sama, in zata ko raina aka zare kin san ance idan mumini ya mutu, to sama ake yi da ransa, to sai na ji an watsoni tsakar gida, sannan nake gane ai ina duniya, hukuncin ma sunan Baba ne, idan ya haɗe rai ya tattare girarsa sai na ji kamar in zawo a tsaye".
Duk da halin da suke ciki, bai hana matar yin murmushi ba, dan ba ƙaramin dariya ruma ta bata ba. Ruma ma Murmushin ta yi ta ce "Mai sunan baba dodon marasa hankali in ji mama, idan ya sakani kama kunne a daren nan, to wallahi da asuba a zaune zan salla saboda azaba, mai sunan Baba ya iya punishment"
"Ni kuwa zan so na ga mai sunan Baban nan da ki ke tsoro fiye da bindiga".
"Kema idan ki ka ganshi sai ya baki tsoro, shi fa ba ya dariya, kullum fuskarsa a haɗe, wataran ko hararata yayi sai na kwana uku a nutse".
Dariya suka yi tare, ruma ta ce "To baki gaya mini sunanki ba, ina mijinki da 'yan gidanku?"
Matar ta yi murmushi ta ce "Suna na, sunana Aisha".
"Anty Aisha, ke a wani garin ki ke?"
"Zan gaya miki, yanzu jikina babu daɗi na bugu, yaron cikina sai juya wa yake".
Cikin damuwa ruma ta ce "Sannu, Allah ya sa su sake ki kan ki haihu, Allah ya sa ki amayo shi lafiya"
Cikin dariya ta ce "Me zan amayo?"
"Ɗan mana, ba ta baki ake yo aman jariri ba, haka mama ta ce mini, amma su fa akuyoyi to ta wurin kashin su suka haifo ɗa, daga yi wa mama tambaya ta ce idan na kuma wurinda akuya ta haihu sai ta zaneni" halin da Aisha ke ciki bai hanata yin dariya ba, ta riƙe cikinta, saboda dariyar ta ƙarfin hali ce.
"Ya naga kina dariya, ko ba ta nan ake haihuwar ba?"
"Ta nan ne mana, Allah ya sa na amayo shi lafiya".
Ruma ta ce "Amin, ina zuwa" daga haka ruma ta miƙe ta nufi mutumin nan ta je ta tsaya masa a ka, ya ɗago ya kalleta ya ce "Me kuma ki ke nema?"