Kenza eBookz

Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 35

Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 35

Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 35: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 35. "Abinci, yunwa muke ji"

3,358 words

"Abinci, yunwa muke ji"

Ɗagowa yayi yana ƙarewa ruma kallo, ita ma ƙyar ta ƙure shi da nata idanuwan.

Wata leda ya ɗauka ya wurga mata ya ce "Gashi nan shegiya mayya, mayuwanciya" ta durƙusa ta ɗauka ta ce "Koma me zaka ce na ji, na dai fi ƙarfin ka, ba yadda zaka yi da ni".

Tun mutanen wurin suna namakin ruma, har sun saba da halinta, kome zata yi sai dai ta ci duka, amma ban da haka ba wanda ya isa yayi mata wani abu.

Ta koma wurin Aisha ta zauna ta ce "Anty Aisha, tashi mu ci abinci" tayi maganar tana buɗe ledar.

Buredi ne a ciki da pure water.

"Matsiyata kullum daga gurasa sai buredi".

Aisha ta ce "Ruma dan Allah ki din ga shiru, kin ga baki da lafiya, kar su sake dukanki".

"Wai meyasa ki ka damu da ni haka ne? Dan Allah ki daina damuwa idan ba haka ba sai na koma baki haushi, haka nake, in dai ba gajiya zasu yi su kasheni ba, suna tare da wahala" ruma ta ƙarasa maganar tana miƙawa Aisha buredin a baki.

Murmushi ta yi ta karɓa, ba dan buredin na yi mata daɗi ba, sai dan rashin mafita.

****

Kwanaki kusan talatin kenan da sace ruma, babu wata tartibiyar magana a kan in da take ko yadda za a sameta, ga mama sai ciwo take a tsaye, ko ta sha maganin hawan jini, jinin baya sauka, ga ulcer ta yi mata mummunan kamu saboda rashin cin abinci.

Yanzu haka suna zaune duk sun kewayeta, amma babu iya cewa komai, sai ma ita ce cikin ƙarfin hali take musu faɗa, a kan rashin cin abinci.

Usman ya dubi Aliyu ya ce "Dan Allah ka sake kiran mijin iya, ka ce masa haryanzu muna jira bai ce mana komai ba, an samu an yi maganar da su kuwa?.

Usman bai yi musu ba, ya kira mijin iya, Abdallah ya ce "Ka saka mana a hansfree mu ji".

Aliyu ya saka wayar a hansfree, suka gaisa da mijin gwaggo sannan ya ɗora da cewa "Baba haryanzu ba ka ce mana komai ba, an gano a in da taken, ko kuma sun faɗi abin da za a basu?"

"Aliyu zancen ne babu daɗin ji, shi ya sanya na yi muku shiru".

"Sun kasheta ne?" Abdallah yayi maganar a kiɗime.

"A'a, ba kasheta suka yi ba, wanda muka tura ɗin ya dawo ya sanar da ni cewa sun ce ba sa buƙatar komai ba zasu bayar da ita ba, halinta ya sanya za su riƙeta ko kuma a fansheta da 'yan mata biyar, duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi abu ya faskara, sai dai mu cigaba da addu'a kawai".

Gaba ɗaya aka rasa mai magana, sai mama da take ta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba taurin kan take yi musu ba, Allah ka kuɓutar mini da yarinyar nan ka tsare mini ita" tayi maganar tana kuka

Abdallah ne ya rungume mama yana rarrashinta, yana goge mata hawaye.

*** Mintuna kusan talatin da takawa ya sanya aka yi masa iso wurin wambai, amma shiru bai fito ba gashi ya fara ƙoasawa da zaman, dan haka ya tashi da nufin ya tafi, dan akwai tarin ayyukan da suke gabansa ya yanke ya taho.

"Na sallameka ne zaka tafi, ko nima halin rashin ɗa'ar zaka gwada mini?" Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli wambai da ya shigo falon, sanye da jallabiya ba tare da naɗi ba.

"A'a ranka ya daɗe, na zaci ba zaka samu fitowa ba, na baro ayyuka da yawa na taho"

"Saboda ayyukan ka sun fi kirana muhimmanci ko, ashe abubuwan da ake gaya mini akan ka gaskiya ne ko Adamu?" Cikin mamaki Adam ya ke kallon wambai.

"Zaka nemi wuri ka zauna, ko kuma jera kafaɗa zamu yi sannan mu yi magana?" Adam yayi ajiyar zuciya, ya samu wuri ya zauna a ƙasa yana tunanin laifin me yayi wa wambai haka har yake kiran sunansa haka.

"Dukkanin abin da ka ke yi ya sameni, kuma ka bani mamaki ka bani kunya, turbar da ka ɗauko ba ita ce turabar da mahaifinka ya ɗoraka a kai ba, dan haka ka shiga hankalinka idan ma uwarka ke zigaka kanka yake rawa gara ma tun wuri ka nutsu ka shiga hankalinka, kuma wallahi idan ba ka yi wasa ba, sarautar da kake jiran ba zata dawo gidanku ba, idan ma ta dawo ɗin sai dai a bawa ɗan uwaka tunda kai dai ba ka san abin da yake maka ciwo ba" maganar Ammi ce ta sanya shi yin shiru, gaba ɗaya ya rasa a kan me Wambai yake yi masa faɗa tare da ci masa zarafi, shi ce masa yayi yana jiran a bashi sarauta ne?.

Nan da nan jijiyoyin kan Adam suka ɗaga, saboda tsananin ɓacin rai, haka tsohon nan ya saka Adam a gaba ya zage shi tsaf ba tare da wata tartibiyar hujja ba.

Sai da yayi mai isarsa sannan ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, yana shiga sashen Ammi ya tara da su Fauziyya da Samha a falon Ammi.

Wucewa yayi ciki yana ta huci, Ammi da take zaune tare da su a falon ba ta tashi ba, ta basar da shi. Cike da gulma Fauziyya ta ce "Ammi meya sami takawa ne?"

Ammi da tun daga shigowar su Fauziyya shashenta ta san akwai wani abu a ƙasa, dan rabonta da su anfi wata guda, kawai ta basar ne.

Ammi ta ce "Babu komai, ina ga aiki ne yayi masa yawa kawai".

"Kin ga yadda idonsa yayi ja kuwa? Kamar ba shi da lafiya fa".

Iman ce daga kitchen ta wuce ɗakinta, dan sam a ta san abin da zai sanyata shiga shirgin su Fauziyya, tana zuwa ta tarar da takawa a tsaye a ɗakinta, tamkar zai fashe, ya watsarwa mata da kayan kan mudubinta, sai karkarwa yake.

Yana jin motsin iman, ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta.

Girgiza masa kai ta shiga yi, amma ta kasa gaba ta kasa baya.

"Zo nan ya faɗa a kausashe".

"Dan Allah ka yi haƙuri, ba ni na ɓata maka rai ba" tayi maganar cikin rauni.

"A hayyacina nake iman, hannunki kawai zan riƙe".

Cikin rawar murya ta ce "Amma ba zaka yi mini komai ba?"

"Na rasa abin da zan riƙe, kaina zai tarwatse ne, help me just your hands" cikin tsoro ta nufe shi, ta ƙarasa nesa kaɗan da shi ya kama hannunta ya riƙe tamkar zai ɓallata.

Ihu ta ƙwala jin yadda ya murɗa mata hannu, haƙoransa sai karkarwa suke yi.

Sama-sama suka jiyo ihun iman, suka tashi suka nufi ɗakin Iman.

Takawa suka tarar ya banƙare hannun Iman, hannu ɗaya kuma ya shaƙeta, rigar jikinta ta ɗage sai kokowa take da numfashi tana kakari.!!

AYSHERCOOL.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

Gaba ɗaya tsaya wa suka yi suna kallon su, Ammi ce kawai ta iya ƙarasawa tana ƙoƙarin ƙwace Iman "Me ka ke yi haka ne takawa, iman ce fa"

A hankali ya saki wuyan iman yana ƙare mata kallo, jikinta duk yayi ja saboda azabar wahalar da ta sha.

"Kalli fa ka gani, iman ce fa takawa"

Kamar wanda ya warke daga ciwon hauka, haka ya din ga bin Iman da kallo, kamar zai fashe da kuka ya ce "Iman yi haƙuri, ban san ke ba ce, hannunki kawai na ce zan riƙe, na ga kin koma wata mata zaki caka mini wani abu, yi haƙuri iman, Ammi ban san iman ba ce ki bata haƙuri"

Nusaiba ce ta kalli su Fauziyya da suka yi tsaye suna kallon abun da yake faruwa, ta ce "Anty Samha ba wani abu, zaku iya tafiya".

Samha ta ce "Ba zamu tafin ba, a kan ki muke ko yayanki ne ke kaɗai".

Ammi ta ɗago iman tana yi mata sannu, iman ta jinjina mata kai.

Ammi ta ce "Ina maganinsa yake? shegiyar gardama irin ta sa ɗauko in shafa masa" A hankali iman ta yinƙura, ta je ta saka mukulli, ta buɗe wata drower, ta ɗauko wata jarka cike da wani mai.

Ƙurii Fauziyya ta yi, tana kallon in da iman ta ɗauko maganin.

Adam yayi zuruu da ido yana bin su da kallo, can ya sauke idonsa a kan su samha, cikin tsawa ya ce "Get out" sai da suka razana, kan su yi wani yinƙuri ya sake daka musu wata tsawar, cikin rige-rige suka yi waje da gudu.

Ammi cikin damuwa ta ce "Takawa, meye ya ɓata maka rai haka ne?"

Kamar mai shirin zaucewa ya hau surutai, "Ni na ce ina son sarautarsu ne? Su barni in ji da abin da ya dameni mana, me na yi masa? Idan ya kuma takura mini zan kashe shi, zan shanye jininsa gara ma ki gargaɗe shi ya fita a hanyata".

Cikin tsawa Ammi ta ce "Adam! Kar na sake jin ka furta wannan maganar, wan ubanka ne fa, ban hanaka zancen shan jinin nan ba, sai ka ce maye?"

Nusaiba ta ce "Ammi ba a hankalinsa yake faɗar shan jinin nan ba, ki yi masa a hankali". iman shammace shi, ta shafa masa maganin a fuska, a take ya yi atishawa, sai kuma a hankali ya sulale ya kwanta a ƙasa ya hau bacci.

Hawaye Ammi ta shiga zubarwa, iman da Nusaiba suka yo kanta gaba ɗaya "Haba Ammi, idan ki ka yi kuka mu kuma mu yi yaya, dan Allah ammi ki daina ki yi masa addu'a" Iman tayi maganar hawaye na cika idanunta.

"Iman, ciwon da nake tunanin ya rabu da shi, yana neman ya dawo daga rai ya ɓaci sai ya hau maganganu, ya fita hayyacinsa, ina zan saka kaina, saboda tsabar neman magani na fara tsoron kar in faɗa hannun mushirikai na rasa imanina, sanadin ciwon nan har jita-jita aka din ga yaɗawa wai maye ne fa, da wanne zan ji?".

Nusaiba ta ce "Dan Allah ammi ki daina damuwa, Addu'arki fa ba ta tafiya a banza, zai warke in sha Allah "Astagfirullah, Allah ya yaye maka Adam, duk wani hope ɗina a kanka yake, ban ce wani ne ya yi maka bs, Allah ne ya ɗora maka, ina fatan ya yaye maka"

Suna tsaka da maganar ya fara surutai "Sidi, ku je ku dubo mini yarinyar nan, na gaji a kan me zata din ga zuwar mini a bacci ko in din ga jin kukan ta a kunnena, anya mutum ce? ku je ku duba mini ni bani da lokaci" kamar sun je cinema haka suka zuba masa ido, can kuma ya toshe kunne yana faɗin "Ki daina yi mini kuka, bana son kuka, meye alaƙata da ke ne?"

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin ammi da su Nusaiba.

A hankali nusaiba ta ce "Yaya maganar wa ka ke yi ne?"

Tun da Nusaiba ta yi magana bai sake cewa komai ba, yayi shiru bacci yayi awon gaba da shi.

*** Idan da sabo ruma ta saba, dan haka yanzu baccinta take cike da mafarkan su Mama da yayyenta, sai dai babban abin da yake addabarta bai wuce ganin mutumin nan da ta tsana a cikin mafarkinta ba, wanda hakan ba ƙaramin haushi yake bata.

Yanzu ma mafarki take yi, tana zaune tana kuka a cikin dajin nan, takawa ya ɓullo sanye da wasu baƙaƙen kaya, ya ratso mutanen da suke wurin, ba wanda yake iya ganinsa sai ita, ya zo ya tsaya a kanta, ya miƙa mata hannu ya ce "Taso mu tafi"

Ta waiwaya tana dubawa ko akwai wanda yake ganin sa, "ba zaki taso mu tafi ba kin tsaya kina kalle-kalle?"

Cikin tsiwa ta ce "Eh ba za'a taso ba ɗin ni na gayyace ka?" Tayi maganar a fili, tana buɗe ido, tsaki tayi tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta ta ce "Aikin banza, ko me yake kawo shi mafarki na oho, idan na kuma ganinka a baccina, sai na yi maka rashin mutunci, dan wallahi sai na rama abin da ka yi mini"

"Ke da waye ne baby rumaisa"ta ji muryar anty aisha.

Ruma ta sake buɗe ido ta ce "Ba kowa".

"Haba dai ba kowa, tun ɗazu ki ke surutu fa kina masifa a cikin bacci, har wancan yake cewa zai taka ƙafarki ki tashi,"

Duk da duhu ne, Ruma ta zare ido ta ce "Haba dai, me nake cewa?"

Aisha ta ce "Ina ta fama da kaina ban riƙe ba, amma dai faɗa ki ke da wani a bacci"

Ruma tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani mara kirki ne yake zuwar mini, taimako ɗaya Allah zai yi masa, shine na mutu a wurin nan, amma muddin na fita ko ni ko shi, sai ya gane bashi da wayo"

Anty Aisha ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka?".

"Baki san rashin mutuncin da yayi mini ba, nonona ya taɓa mini, kuma mama ta ce duk wanda ya taɓa nan wurin na zama 'yar iska cikin shege ne zai fito mini"

"Ya salam, ke ya aka yi ya kai hannunsa nan wurin?"

"Sa wa yayi aka ɗaukoni, wai zai yi mini warning, ya shaƙo hijjabina ya taɓa wurin, ni kuwa na din ga bin diddigi sai da na gano gidansu, na je na rubuta masa wasiƙar rashin mutunci na ce a bashi"

"Kai ruma lallai jan wuya ke ce, irin wannan ƙarfin hali haka?"

"Rabu da shi, ai wallahi ya bari na fita daga wurin nan zai gane kurensa, Anty Aisha wai ke a wani gari kike?"

"Zan gaya miki ruma, na san zuwa yanzu labari ya samu mijina da dangina abin da ya faru da ni, sai dai ban ga alamar kuɗin fansa suke so ba,. Tun da sun ƙi yin waya su faɗi abin da za s bayar idan.... Ba ta ƙarasa maganar ba ta riƙe ƙugunta ta ce "Washhh"

A ɗan rikice ruma ta ce "Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki miƙe ƙafar to".

"A'a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki".

Ruma ta ce "A'a ai ba zan iya komawa ba kwanta".

A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ƙafafuwan rumaisa, Ruma ta ce "Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya" Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.

"Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daɗi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing ɗin gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ƙaddara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki".

Tayi murmushi ta ce "Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani"

"Ɗaga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba" ruma ta faɗa rai a ɓace.

"Haba ruma, ni ɗin ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada". Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce "Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba"

Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ƙila a haɗa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taɓata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.

Ɗayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce "yau kun yi faɗa da uwar taki ne?"

"To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana'ar banza".

"Ni ki ke cewa sa ido sana'ar banza, dan kin ga ana ƙyaleki?"

"Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu'a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?"

"Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya".

Ruma ta ƙarasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ƙasa da muryarta ta ce"Ka san meya haɗani da anty aisha muka yi faɗa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi"

"To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull