Kenza eBookz

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 6

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 6

Kanwar maza 1&2 complete Chapter 6: Kanwar maza 1&2 complete Chapter 6. Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan…

4,430 words

Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ɓera ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nannaɗe su tayi, wasu ta ninka su biyu, a taƙaice kai ka ce bolar wani office ɗin ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ƙasa da sauran goriba duk a ciki. Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba. "Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai. Ya sanya hannu ya ɗau littafi ɗaya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi ɗaya sai ta yi duk subject ɗin da ta ga dama a ciki. A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject ɗaya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta faɗuwa shine maths.

Yayi ajiyar zuciya ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Ashe asarar kuɗin tara kawai ake a banza ko? A biya miki kuɗin makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza faɗi ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Ƙarya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ɗin da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating " Ras! Gaban ruma ya faɗi "Na shiga uku, dan Allah ka yi haƙuri, zan daina surutun in dinga karatu".

"Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da daƙiƙanci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya buɗe Alqur'ani nuna mini a surar da ku ke" Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke ɗin ba. Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ƙafa dubu. Da haka yaya umar ya ƙwaci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ɗaukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ƙafa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ƙyaleta ta kwanta ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji. Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da daƙiƙanci, sai ya sa an yi mata repeating.

********* Zaune take a kan makeken gadonta, ɗakin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai ɗakin 'yar gata ce. Ta dunƙule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka. Daga ita sai doguwar riga 'yar kanti, kanta babu ɗan kwali, kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Turo ƙofar ɗakin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ɗakin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta riƙe da tray da cup. Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ɗan girgiza kai, ta ƙarasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana faɗin "Haba Iman ɗina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ƙaddara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?" Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta. "To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi haƙuri kin ji babyna" Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.

Ta ɗakko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ƙauna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.

********** Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta. Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ƙoshi ba, ta kwaɗa garin kwaki ta zauna tana ci. Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ƙauye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta. Mama ta kalleta ta ce "Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda ɗaya ki gwada ba?"

Ɗan ɓata fuska tayi ta ce "Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla"

"Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so" Shiru ta yiwa mama tana cigaba da danƙarar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.

Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ɗan taɓuka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ƙoƙarin ta ko ba duka ba, ta ɗan iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ɗan samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.

Yau ana can ana sallar la'asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam'in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba. Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu. A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su. Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan ɗanyen aiki haka. Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala. Cikin kiɗimewa, ta ɗauki ƙatuwar buta guda ɗaya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ƙwala masa butar, daga ƙarshe ta durƙusa ta ɗibi ƙasa tana watsa masa tana kuka.

Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa, balle ya kare kansa. An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ɓata masa jiki da ruwa da ƙasa a gogaggen uniform ɗin sa, ta haɗa hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.

Da ƙyar wani malami ya ɓanɓareta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba. Malamin ya dubi ruma ya ce "Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?"

Cikin kuka ta ce "Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba". Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa. Yayin da hankalin ɗaliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta duƙunƙuna masa kamar ya faɗa taɓo.

Haƙuri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa. Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba kaɗan ba. Auwal ɗan ajin su Yasir ne, ya san ƙanwar yasir ce, sai dai sam bai taɓa shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a durƙushe a wurin ba, yayi mamakin ƙarfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.

Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, haƙuri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ƙyale ruma ba sai ya ɗau mataki a kanta.

Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal haƙuri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi haƙuri. Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ɗin ma tsoron taɓata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.

********* Gaba ɗaya ruma ba ta wani ɗokin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ƙara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama taƙi sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ƙin jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci. Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.

"Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?"

Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce "Na gaya maka bana son sunan amma ka ƙi daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji"

Huzaifa ya ce "Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ɓarar da ke ba".

"Hmm haƙuri halin abin ƙaunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba" girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ɗakin mama.

Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.

Mama ta dubi ruma ta ce "Murmushin me ki ke yi ne?"

Ruma ta ɗagowa mama takarda ta ce "Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ƙarfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ɗin nan ɗari biyu da hamsin, zamu yi mu da 'yan wata makaranta"

"Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ƙarfi ko kunya ba ki ji ba" Abdallah ya faɗa a hasale.

"To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba" tayi maganar cikin taɓara.

Mama ta ce "amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?"

Ruma ta tsuke fuska ta ce "Wato mama ke ma dai daƙiƙiyar zaki ce mini ko?"

Abdallah ya ce "To mecece idan ba daƙiƙiyar ba" gaba ɗaya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi. Babu wanda ya bata ƙwarin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.

Zaune yake a cikin chemist ɗin, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist ɗin ta ce "Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai" na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana ɗaga kai suka haɗa ido. Murmushi ta yi masa ta ce "Yaya auwal ina wuni" juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.

"Baka da lafiya ne?" Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ɗin yake zuƙewa.

A hankali ya ce "lafiya lau, ya su yasir?"

"Suna nan lafiya, ya jiki?" Da sauƙi ya bata amsa, yana tuna yadda ta damalmala masa kaya a islamiyya, da yadda yayanta ya rutsata ta bashi haƙuri amma ta ce sai dai ya mutu, ba zata bayar ba, idan suka haɗu a makaranta, sai ta tsaya ta harare shi, har da murguɗa baki, amma wai yau take gaishe shi, har da su yaya bayan ko yayan nata yasir ba ta ce masa yaya.

"Deluwa wannan hamsin ɗin taki za ta karɓuwa kuwa?" Cewar mai chemist.

"Awaisu mai chemist, duk ranar da na tashi jajjaga maka rashin mutunci, a kan kirana da deluwa, sai ka yi kuka" ta faɗa very serious.

Dariya ya yi ya ce "Ke, ai ko ban kai sa'an 'yan biyun gidanku ba, na san na girmi Aliyu, amma ni zaki saka kuka?"

"To shikenan, ka cigaba zaka gani, bani maganina na tafi"

Bayan ya bata maganin ta kalli auwal ta ce "Yaya auwal, Allah ya ƙara lafiya" tana gama maganar ya fita tana tsalle kamar kwaɗuwa. Tun da ga ranar da suka haɗu da auwal a chemist, kullum ta ganshi a makaranta sai ta gaishe shi, duk da baya sakar mata fuska idan zai amsa, amma bai sanya ta daina ba.

**** Ɗaya ga watan ramadan, bayan gari ya ɗauka an ga wata, mutane na ta shirin ɗaukar azumi, da asuba mama ta tashi kowa sahur, amma da ƙyar ruma ta tashi ta yi sahur, saboda nauyin bacci. Ranar ɗaya ga azumin ya kama asabar ce, ruma ta ce gaskiya ba zata iya zuwa islamiyya ba, tun ƙarfe goma take jin kamar zata mutu. Wajen ƙarfe sha biyu na rana, ta dinga yiwa mama kuka tana burgima wai hanjinta na gutsutstsurewa ita fa mutuwa zata yi.

Aliyu ya ce 'mama dan Allah ki ƙyake yarinyar nan, tun da ba zata yi ba ta je ta ƙarata".

"Aikuwa sai ta yi, idan ya wajaba a kan ta wa zai mata?"

"Mama ki bari ua wajaban sai ta yi, kalli fa kamar zata rasu"

Mama ta ce ruma ba zata karya azumi ba, mama tana can tana salla, ya kandamowa ruma ruwa ta sha ta karya azumi. Sai da mama tayi kamar ta zane Aliyu dan takaici, a ganinta sangartar ruma ta yi yawa.

Abu kamar wasa, ruma taƙi yin azumi, idan ma ta ɗauka ta ji wuya, sai ta karya abin ta, idan aka sha ruwa kuwa tafi uban kowa zaƙewa, daƙyar ska samu ta yi shida, shima Usman ya ce bai yarda da ingancinsu ba. idan aka ce ta je sallar asham kuwa sai ta ce ita wallahi gajiya taje yi da tsaiwa, ƙafafuwanta sai sun fara suɗewa ake ruku'u, nan ma sai bayanta ya kusa karyewa ake ɗagowa ba zata iya ba. mama kuwa ta gaji ta kamata ta zaneta da mafici.

Idan kuwa aka matsa ta je sallar asham, wataran a can cikin yara ake tsintowa mama ruma tana tsalle -tsalle ko dambe a maimakon salla, tilas mama ta hanata zuwa take titsiyeta su yi a gida.

Sai da salla ta gabato, ruma ta sake da tabattar da mama ba zata yi mata wani ɗinkin ba, ta dinga yi wa mama magiya, a kan ta yi mata wasu kayan, amma mama ta ce ba zata yi ba, lokaci ne da zata rama rashin jin da ruman take yi mata. Gaba daya ɗokin sallar ya fita daga kanta, saboda ba ta son kayan da aka sai mata, gashi sallar bana ko arzikin takalmi da jaka bata samu ba, dan haka ta ce ba zata yi ko kitson salla ba.

Mama ta bata kuɗi ta ce taje ayi mata lalle, dan ba zata yi salla haka ba. Ruma ta tafi ƙunshi tun safe, sai bayan la'asar ta dawo. Mama ta kalli lallen nan babu kyan gani, kamar ana saka shi aka ɗauraye.

Kafin mama tayi magana mai lallai ta kira mama, suka gaisa. Mai lalle ta ce "Mama, wallahi kar ki ga lallen ruma bai yi kyau ba, ana saka mata wai sai an cire ba ta so ta gaji, da na ƙi cire mata, ta cire abinta wai kashi take ji"

Mama ta ce "To shikenan, kar ki damu na gode sosai" ta kalli in da ruma ta tsaya ta ci magani kawai ta jinjina kai ba ta ce mata komai ba.

Tun magariba, ruma taga mama ta kwaɓa lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.

Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yinƙura zata tashi, ta ji motsin leda a ƙafarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ƙafarta duk leda.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama me ya sameni?"

"A ina?"

"Wannan ledar mecece?"

Mama ta ce "Ahh, ruma ai ba ke kaɗai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya kuɗi ayi miki lalle ki ka ƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta faɗa kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane huɗu ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai".

Ruma ta kalli yadda aka ƙunshe mata ƙafa har ƙwauri, ga hannayenta kuma ana batun ayi mata zanen Hausa guda huɗu a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta ɗora hannu a ka ta zunduma ihu.

DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE

AYSHERCOOL 08081012143 [03/07, 2:14 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro. Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724 Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode

*Ina miƙa saƙon godiya, ga waɗanda suka yi mana ta'aziyya na rashin uba da 'yar uwa Naima Suleiman (Nimcyluv) ta yi, muna fatan Ubangiji Allah ya jiƙansa da rahama.*

*TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*

P8

Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo ɗakin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun. Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce "Mama meya sameta ne?"

Mama ta ce "Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba"

Abdallah ya ce "Ke menene?"

Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.

"Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya"

Ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka iya ƙarfinta.

"Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?" Usman ya daka mata tsawa.

"Ba mama ce ba"

"Me maman tayi?"

"Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta faɗa kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi".

"Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?"

"Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na"

Abdallah ya ce "Allah ya ƙara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba".

Mama ta ce "Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla".

Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.

Abdallah ya ce "Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta faɗa kwatar ne?"

Cikin kuka ruma ta ce "Irin fa wanda mama take yi a ƙafarta"

Dariya ce ta ƙwacewa Abdallah, ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"

Mama ta ce "Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada kuɗi ayi mata abin arziki na zamani, amma taƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane huɗu za ayi miki".

Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta ɗoɗar hannunta da ƙafarta.

Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.

Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ƙarfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.

Kamar yadda mama ta faɗa, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ƙi tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ƙwaƙwalwarta saboda yadda matar ke jan gashin. Ko da aka gama kitson, ruma ta haɗa gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.

Ruma da ta kalli hannunta ranta yake ɓaci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.

Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ƙauna da mama tayi mata. Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ƙunshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ƙarfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da. Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga ɓacin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.

"'Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?"

Ta ɗaga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan. Shiru tayi masa tana tura baki.

"Meyasa ki ke kuka?"

Miƙewa ta yi tsaye tana faɗin 'Babu komai"

Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ina Yasir?"

Cikin ƙunƙuni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta. Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wulaƙanci.

Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya murɗe mata kunne, saboda yadda ta je ta daɗe.

Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba. Huzaifa kuwa musamman ya ƙi shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.

Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.

"Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan".

"Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?"

Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta ɗau kayan ta saka su wuce sallar idi.

Ga lalle dungulmi, ga kaya ɗinkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sarƙa koma kamar 'yar ƙauye. Huzaifa kamar ya shiɗe don dariya.

"Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ƙauye" Yasir ya yi maganar yana dariya.

"Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi".

"Na kuma jin bakin ki sai na ɓarara da ke, maza wuce mu tafi" Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.

Usman ne ya miƙo mata sabon hijjabi ya ce "Gashi nan ba dan hakinki ba". Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun ɗinkin, tun da hijjabin dogo ne.

Karɓa tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.

********

"Masha Allah, looking take away my beautiful angel" Ammi ta faɗa tana kallon Iman.

Murmushi iman tayi ta ce "Ammina, an yi salla lafiya"

"Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu'a"

Murmushi ta yi ta ce "Ba dole ba Ammina"

Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta ɗago ta ce "Wai mu Ammi baki ganmu bane?"

"Na ganku mana"

"Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin" cewar ɗaya yarinyar.

Ammi ta ce "Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ƙanwarku"

Iman tayi musu gwalo ta ce "Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina"

'Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ƙarshen ƙauna"

Ammi ta girgiza kai ta ce"Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla". Ɓata fuska Iman tayi ta ce "Ammi"

Kan ta ƙarasa maganar, Ammi ta ɗora yatsanta a kan lips ɗin ta ta ce "Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa" Ɗan gyaɗa kai Iman tayi ta ce "Shikenan Ammi, bari na shirya"

***** "Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba" Ruma ta kwaɓe fuska ta ce "Dan Allah mama ki yi haƙuri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini"

"Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?"

"A'a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta".

"Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki" Usman ya daka mata tsawa.

Jiki na rawa ta tashi, ta ɗau kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.

A hanya ta haɗu da wasu 'yan makarantar bokon su, cikin fara'a ɗayar ta ce "Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?"

Ruma ta kalleta ta ce "Ji masifa, to ba ni da su, ba a ɗinka mini ba"

"Daga tambaya sai masifa?"

"Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?" tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.

"Kutmelesi, ruma meye wannan a ƙafarki?" Gaba ɗaya suka kalli ƙafar ruma, da take sanye da silifas ɗan madina, ga ƙafa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba iya ɗaurin zani ta yi ba, zanin ya ɗage har ƙwaurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ƙafar ba.

"Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ƙafar tsohuwa"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull