Kenza eBookz

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 7

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 7

Kanwar maza 1&2 complete Chapter 7: Kanwar maza 1&2 complete Chapter 7. Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake leƙa ƙafarta. Cikin takaici, ta juya zata…

4,370 words

Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake leƙa ƙafarta. Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata zaƙaƙurar yarinya, ta biyo ruma tana ɗage mata zani. Mai jiran ƙiris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana'ar ta ta dambe. Kasancewar a ƙule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota. Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa'ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ƙara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.

"Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba" cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.

Ɗagowa ta yi cikin masifa ta ce "Wallahi ni ba annoba bace ba"

Ta duƙa ta cigaba da dambenta. ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ƙwacewa tana kai duka.

"Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki" yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.

"Dama abin da ta aiko ki kenan?" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.

"wuce mu tafi, dage uwar faɗa"

Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.

Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.

"Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?"

Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce "Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki"

Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.

Yaya Umar ne ya fito daga ɗakin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ƙamshi yake zubawa. Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.

Nufota ya yi, ita kuma ta ƙura masa ido ko ƙiftawa ba ta yi.

Ya kalleta ya ce "Na canza miki ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi kyau ne"

Murmushi ya yi, ya miƙa mata leda ya ce "Je ki ka gwada wannan" da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta karɓa ta shiga ɗaki.

Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sarƙa. Ko da ta saka ta fito ba ƙaramin kyau ta yi ba.

"Mama kin ganni, na yi kyau"

Aliyu ya ce "Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri ɗaya babu ko labari"

Cikin tsananin farin ciki ta ce "Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?"

"Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ƙwaila ce".

Cikin tsananin farin ciki, ta faɗa jikin yaya Umar tana murna "Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya"

Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce "Allah ya sa ki daina rashin ji".

"Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka haɗani da atamfa kala uku, amma kai da ƙanwarka ka yi muku kaya iri ɗaya, wato an fi son ta a kaina" mama tayi maganar cikin sigar wasa.

Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.

Mama ta shiga ɗaki, ta fito da wata ƙatuwar leda, ta miƙawa ruma ta ce "Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar naƙi nuna miki dan in hora ki"

Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata ɗinke-ɗinke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ƙalla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.

"Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne"

Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.

Bin su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce 'Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya".

"Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?"

"Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?"

"A'a yi haƙuri mama, shi ɗin ne zai ɓata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani kuɗi ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai"

Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata kuɗi tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.

******** Ba zata iya ƙayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta ɗaga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan. Ya ƙawatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai. Da haka ta ƙarasa cikin ƙaton falon da ke cikin gidan.

Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.

Ɗaya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara'a ta ce "Maraba da zuwa".

Iman ta ce "Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?".

"Tana cikin turaka, bari ayi miki iso"

Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce "Bisimillah, ta ce ki shiga"

Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma. Shigarsu ɗakin ke da wuya, gaban Iman ya faɗi, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko haɗa hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ƙauna.

Faɗaɗa murmushi Ummma tayi ta ce "Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?"

Murmushin yaƙe iman ta ƙaƙalo, ta durƙusa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.

Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.

"Hajiya Iman, manya manyan 'ya'ya a gidan Galadima, ya kike ya school?" cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.

Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce "Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?"

"Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?" Tayi maganar tana ƙarewa Iman kallo.

Umma ta ce "Eh irinsa ne"

"Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin riƙe wuta".

Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce "Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi".

"Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla".

"A'a Umma, ai na girma da barka da salla" iman tayi maganar tana miƙewa .

"Ƙaniyarki, tsaya ki karɓa mana" girgiza kai iman tayi, ta fice daga ɗakin da sauri.

Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an riƙe mata jaka. Ta waiwayo tana kallon wadda ta riƙeta.

"Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da kuɗi baki rasa komai ba, amma yakamata ki karɓa tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?"

Cikin rauni Iman ta ce "Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?"

Cikin ko in kula Soafy ta ce "Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?" Ta fizgi jakar iman, ta saka mata kuɗin, ta saƙala mata jakar a kafaɗarta ta koma ciki.

Gwiwa a saɓule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ƙureta da idanuwansa.

Ƙoƙarin ratsewa take ta wuce, amma ya ce "Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?"

Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Anyway, kin yi kyau sosai a outfit ɗin nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?".

"Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana" daga haka ta wuce ta bar shi a wurin a tsaye.

**********

Zuwa yamma mama ta saka ruma a gaba sai sa ta cire shaddar nan, dan idan ta bar ruma da ita sai shaddar ta fita daga hayyacinta.

Kwanukan da aka ɓata, Yasir ya tattara yana wankewa, mama ta ce "Ke, shiga ɗakinsu ki dudduba mini idan da kwanukana, cokula ko kofi, duk ki fito mini da su, dan na san hali, sai a kai mini kwano ɗaki a ƙi fito da shi" Ruma ta tashi ta nufi ɗakin samarin nan, ba tare da ko sallama ba. Usman ne a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar. Buɗe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haɗe rai ya ce "Zo nan" ba musu ta ƙarasa in da yake.

"Me ki ka ji?"

Ta ce "A ina?"

"Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?"

"Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce....." Sai kuma ta yi shiru.

"Ba zaki faɗa ba sai na taka ki?"

Ta tura baki sannan ta ce "Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata".

"Sai kuma me?"

"Shikenan na ji wallahi "

"To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faɗa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ƙanwar abokina ce ba wata ba"

"To ai ni dama ban ce zan faɗa ba, mama ce ta aikoni" daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faɗin mama "Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siɗe miki kofi tas, har ɓera ya fara ci. Kin ga plate ɗin ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce".

Yasir ya ce "To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?"

Mama ta ce"Ai ba ƙarya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa ɗakin ku, sai na bi na tsinto abina, ƙazaman banza kawai"

Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce "Ina ruma"

Ta ce "Gani"

"Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci ".

Murmushi ta yi ta ce"A'a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena"

Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce "Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma".

Ta fito daga ɗakin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce "Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuɗi" tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

"Ya makaranta ya rikici2?"

Ta ce "Makaranta lafiya ƙalau, amma ni bana rikici" suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko ɗan cewa ba zata karɓa ɗin nan ba tayi ba, zuruf ta miƙa hannu ta karɓe tana godiya. Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

Ta duba a cikin kuɗin da aka bata, akwai ɗari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce "Ɗan uwanmu ɗan canza mini wannan, ba zata karɓu ba" buɗe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

Aikuwa ya karɓa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

"Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki"

Mama ta ce "To madalla"

"Mama gashi ki ajiye mini, ki ɗora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karɓar kuɗina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuɗina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuɗin da nake bin ki ba"

Cikin gatse mama ta ce "To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuɗin da ki ke bina, na biyaki"

"Dan Allah mama da gaske ki ke?"

"Eh mana" murna ta dinga yi tana cewa 'Ai mama kuɗin da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuɗin nan, unguwar da muke zuwa a bani kuɗi ai da yawa"

Yasir ya ce "Ba zaki taɓa hankali ba".

Aliyu ne ya shigo rai a ɓace yana hararar ruma. Kawar da kanta tayi gefe taƙi kallonsa.

"Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuɗi ta karɓe, wai har da cewa wai wata ba zata karɓu ba, da yake ke ki ka basu ajiya"

"Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa"

"Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai"

A ranta ta ce "Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karɓa".

Bayan sallar isha'i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira. Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce "Mama kin san me?"

Mama ta ce "A'a".

Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faɗa.

Ayshercool 08081012243

(INCLUDE ME IN YOUR PRAYERS PLEASE 🙏) [05/07, 5:40 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

P9

Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce "Mama kin san me yaya Usman ya yi?"

Mama ta ce "A a sai kin faɗa"

Usman ya ce"Haka muka yi da ke ruma?"

"Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru".

Kamar ya yi kuka ya ce"Amma haka muka yi da ke?"

Mama ta ce "Gaya mini ina jin ki"

Ruma ta kalli Usman ta ce "Sai dai ka yi haƙuri fa, amma wallahi sai na faɗa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba"

Ba dan ya san idan ya yinƙura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta ɗaga maganar nan akwai damuwa, zai sha faɗa da mita. Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaɗai ɗin ta ji, dan kawai ɗaga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

Ta gyara zamanta sannan ta ce "Ɗazu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ƙuli, na ganshi a ƙofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya, shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haɗu suna ci, kuma kin hana hakan"

Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

Mama ta ce "To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya ɗau abinci ya fita da shi sun ci tare"

"To mama sai aka ce ya je ya zauna a ƙofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa".

Mama ta ce "To shikenan, za a yi masa faɗa".

"To mama kiyi masa faɗan mana yanzu"

A fusace ya ce "Ke wai ni sa'an ki ne?"

Umar ya ce "Maganinku kenan da ku ke wasa da ita"

Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce "Mama, kin san wani abu?"

"Ke na gaji da wannan shirmen naki fa" mama ta faɗa cikin ƙosawa.

"Mama ba shirme zan ba, ɗazu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta".

"To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?"

Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce "Mama so nake a bata kaya ɗaya a cikin kayana" gaba ɗaya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

Huzaifa ya ce "Kina da hankali kuwa?"

"Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya"

"Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba ɗin" Aliyu ya faɗa yana zaro ido.

Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce "Allah ya kaimu gobe, sai ki zaɓi wanda zaki batan"

Murmushi ruma ta yi ta ce "Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki ɗan zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba".

Yasir ya ce "Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya"

"Ka daina zagar mini babar ƙawa dan Allah"

Mama ta ce "Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta" Ta miƙe ta shige ɗaki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce "Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saɓawa shari'a ba ku ƙyaleta"

Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daɗi.

Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da ɗaya daga cikin kayanta, ta zauna ta ɗaukarwa Habiba set ɗaya na atamfa har da ribbon da abin hannu. Mama bata hanata ba, ta ƙulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban. Har zata ɗauka ta fita, ta tsaya ta ce "Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan 'yan ajinmu mu yi wasa".

Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace"

Ta ɗan marairaice ta ce "Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce".

"Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?"

Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce"Yanzu ƙarfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daɗi ba".

Cikin murna ta ce "Mama da wuri zan dawo in sha Allah " ta yi waje ta na murmushi.

Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba. Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama. Sani ne ya leƙo yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce "Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?"

Hararsa ta yi ta ce "To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ƙara kumbura maka fuska"

Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banɗaki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce"Ke me ki ka zo yi mini a gida?"

"Gurin Habiba na zo"

"Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?"

Habiba ce ta fito daga ɗaki, hannunta riƙe da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce "Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo "

Ruma ta ce "Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ƙi kulani"

Habiba ta ce "Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?"

"Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?"

Mamaki ya cika babar su Habiba, ta riƙe haɓa ta ce "Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?"

Habiba ta girgiza kai ta ce "Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daɗe ma bamu haɗu ba".

Ruma ta miƙowa Habiba leda ta ce "Kawo miki na yi, ki zo ki karɓa ki gani" Babu musu ta ƙarasa ta karɓi ledar, taga ɗinkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ƙullin nama.

Habiba ta ce "Ruma wannan na waye?"

"Naki ne, in gaya miki, kayan salla na kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sarƙa, shine na ce bari na kawo miki ɗaya, ki saka mu je yawon salla".

Babar su Habiba ta ce "Ba ta so ba zata karɓa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana buƙata? Ita ma tana da kayan salla"

Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce "Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka".

Ruma ta ce "Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faɗa, dan Allah ki bari ta saka"

Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ƙyaleta. Habiba ta shiga ɗaki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka ɗinka su suka yi mata kyau. Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

Abin ka da ƙuruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daɗe ba a haɗu ba. Daga haka suka fita nasu yawo.

Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ƙawayensu, wasu a haɗu a rabu da su ƙalau, wasu kuma a ƙare da faɗa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuɗin guziri.

Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi. Da gudu ta ƙarasa in da yake tsaye ta ce "Yaya ussy, me ka ke yi a nan?"

"Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki" abin da ya faɗa ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce "Dan Allah ina zaka?".

"Zamu ɗan fita chilling ne"

"Meye chilling kuma?"

Ya haɗe rai ya ce "Cewa na yi fa ki tafi gida ko?"

"Dan Allah ka yi haƙuri, zan bika dan Allah"

"Ke wai ni sa'an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?"

Ta sake marairaice wa ta ce "Dan Allah Yaya"

Riƙe rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ƙin tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

Yayi ƙasa da murya ya ce "To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi"

"Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi"

"Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space" yayi maganar a ƙule.

"Sai na zauna a cinyarka" duk yadda ya so ya yakice ruma, taƙi ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faɗa zare idonsa ba zai hanata faɗar abin da ta yi niyya ba.

Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaɗai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

Abokansa sai dariya suke masa, suna "Ka ga Ƙanwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so" ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

Wurin shaƙatawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ƙoshi ta kalli Usman ta ce "Yaya ussy, a samo leda a ɗaure mini sauran na tafi da shi gida"

"Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba" ba dan ya ji daɗin fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

Ko da suka je gida, mama a kiɗime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce "A ina ka ganota?"

"Nima a hanya na ganta bayan la'asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita".

"Ku ka je ina?"

"Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma'il ne"

"Kuma ita kaɗai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki" Abdallah ya ce "Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata". Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ƙwaci ruma da ƙyar a hannun mama.

Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun ɗinko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla. Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull