Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 8
Kanwar maza 1&2 complete Chapter 8: Kanwar maza 1&2 complete Chapter 8. Gidan duk ya yi mata babu daɗi, sai faɗace-faɗace take da su Yasir. Suka gama suka…
4,494 words
Gidan duk ya yi mata babu daɗi, sai faɗace-faɗace take da su Yasir. Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daɗi rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi. Ɗakin 'yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya saƙaleta. Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran ɗakin. A ƙalla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba ɗaya ta daina wannan shining ɗin da take yi saboda azabar omo.
Aka jima, ya haɗa wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.
Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta duƙufa tana guga. Ya tsaya yana ƙoƙarin gane me take gogewa.
"Wai meye wannan ki ke gogewa haka?"
Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Kayan yaya Umar ne, na ga ya saƙale su a ɗaki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa".
Abdallah ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?"
"To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?"
"Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?" Ai suna cikin maganar ruma ta ƙone gaban rigar.
Dafe kai ta yi ta ce "Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ƙona masa shadda?"
Abdallah ya ce "Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa"
Hannu ruma ta ɗora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.
Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.
Cikin kuka ruma ta ce "Dan Allah mama ki bashi haƙuri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing".
"Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba".
Abu kamar wasa, har bayan la'asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.
Huzaifa ya ce "Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan taɓargaza da ki ka aikata masa"
Duk da mama a ƙule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma taƙi ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da ɓarna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.
Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka. Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce "Kukan me ki ke yi?"
Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa ɓarnar da ta aikata. Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.
"Dan Allah yaya ka yi haƙuri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba"
Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce "Lallai kin bashi mamaki kam"
Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce "Dan Allah yaya ka yi haƙuri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba"
"Zaka ɗau hukuncin da zan yi mata kenan?" Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.
Yasir ya ce "Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take"
A ɗan tsawace ya ce "Tashi ki ɗauko mini kayan na gani"
Sumi-sumi ta tashi ta je ta ɗauko kayan, ta miƙa masa. Ya karɓa ya duba, gaba ɗaya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.
"Tun da ki ke na taɓa saka ki wanki?" Ta girgiza kai.
"To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?"
"So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba"
Ya girgiza kai ya ce "Zubo mini Abinci" ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.
Ya karɓi Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce "Ci Abinci"
Fuska duk hawaye ta ce "Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Ba zan saka ki ba" yayi maganar yana ɗebo Abincin ya kai bakinta.
"To ka haƙura?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"To dan Allah ka yi haƙuri, tsautsayi ne"
"To, ci abinci" sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ƙyale ruma ba, basu taɓa kawo zai rabu da ita ba.
Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta ce "Me sunan Baba"
"Na'am"
'Dan Allah ka yi haƙuri, zan karɓi kuɗina na wurin mama sai na saya maka wata "murmushin gefen baki ya yi ya ce 'To Shikenan".
Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lallaɓa ya bi ruma ɗaki yana cewa "Ruma, wace addu'a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ƙyale ki ne? Zo ki gaya mini"
Usman ya ce "Wallahi nima na yi mamaki duk ɓarnar nan da ta yi masa ya ƙyaleta"
Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.
Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ƙi zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ɗan mai makarantar ta liƙewa, duk ajin da za shi ya yi ƙari sai ta bishi, gashi ta maƙalewa Auwal, yaya sama yaya ƙasa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.
Yanzu ma 'yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma. Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata. Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ƙarin nan aka idar. Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi 'Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faɗa a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba"
Dariya 'yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.
Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce "Malam nima zan karanta"
Ya ce "To bisimillah"
Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ƙaramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.
Ɗari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba. Da ya kammala ƙarin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haɗe rai ta ce "Malam ni ka bar ni a nan ajin"
Malam Habibu ya ce "To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata"
Suka ce to.
Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taɓa zama shiru ba.
Ruma ta shige cikin 'yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ƙasarta, amma duk tana jin me suke faɗa.
Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.
Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ƙofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ƙasa kyauta. Duk shegen son kuɗi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ƙasarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.
Ta karɓi farar ƙasarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ƙawaye, a cewarta ɗaliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ɗaliban sa'aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma 'yar abi yarima a sha kiɗa ce.
Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, "Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan faɗi me aka yi mini" jin kowa ya shareta ya ƙi kulata ya sanya ta ce "Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?"
"Da aka yi miki me?"
"Mama a gabanki 'ya'yanki suke ce mini ƙwaila, amma baki taɓa hana su ba"
Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce "To ba ƙwailar bace ba?"
Ruma ta buɗe baki ta ce "Au mama har da ke?"
Aliyu ya ce "To meye dan an ce miki ƙwaila, ai ƙwailar ce"
Ruma ta ce "Kutt, ƙwaila fa wadda ba ta da nono kenan?"
Aliyu ya ce "Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa"
Mama ta ce "ke waye ya gaya miki haka?"
"'yan ajin su Yasir ne suke faɗa, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su"
Mama ta ce "To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ƙwaila ba?"
"Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ƙulla a leda na dinga sakawa" cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ƙyaƙyata dariya yake ƙasa-ƙasa lamarin ƙanwar nan ta su sai Addu'a kawai.
Aliyu ya ce"Ke da ki ke ƙanwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau"
Ta ce "Kuma fa haka ne" ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa "Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana ɗan warin nan da ƙamashin turare "
"Fitar mini daga ɗaki dan ubanki, shashasha mara alƙibla fita ki bar mini ɗaki".
AYSHERCOOL 08081012143 [08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
*A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*
10
Ɗan tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce "Mama wai me na yi to?"
"Ban sani ba fitar mini daga ɗaki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini 'ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?" Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta. "Ba zaki fita ki bar mini ɗaki ba, sai na taso kan ki?" Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.
Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce "Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?"
Ta murguɗa baki ta ce "Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo"
"To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?"
Huzaifa ya yi caraf ya ce "Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo ɗin ta gani"
Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.
Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga ɗakin mama ya ɗau jakarta. Ruma ta ɗaga murya ta ce "Mama, ga Huzaifa nan ya ɗaukar miki jaka"
Ya ce "To munafuka"
"Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuɗi"
Huzaifa ya ce "Mama aron naira ɗari zan ɗauka"
Mama ta ce "Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka ɗaukar mini kuɗi ba bani ka ke ba"
"Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi"
Daga kitchen mama ta ce "Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo ɗakin nan?"
"Mama wallahi bai ajiye miki ba"
A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.
Ruma ta ce "Dana sani na bar shi ya ɗauka, nawa nake bin mama ba biyana take ba"
***
Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma. Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B. Malamin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi".
Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.
Ƙarshe dai ruma ce ta taimaki 'yan ajinsu, gaba ɗaya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ɗaliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.
Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu. Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.
Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya niƙi-niƙi.
"Ke wannan kayan na menene?"
Ruma ta zubewa mama kayan ta ce "Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani"
"Meyasa aka baki?"
"Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ƙi koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar"
Mama ta ce "Hmm, ai shikenan"
"Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?"
"Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa"
Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Mama wace gurguwar kuma?"
Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce "Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka" Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta ɗebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo muryar Usman ya shigo, daga banɗakin ta buɗe murya ta ce "Yaya Usyy Albishirin ka"
"Ruma ban hanaki surutu a banɗaki ba?"
Ta ce 'yi haƙuri mama"
Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumuɗi ta fito daga wankan 'Yaya usman, bari na nuna maka wani abun mamaki"
Ba ta san a ya ta fito daga banɗakin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta fito. Ta koma ta ɗauko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.
Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce "Ruma ban yarda da ke ba"
Ta ce "Saboda me?"
"Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?" Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce "To me ka ke nufi?"
"Ɗauko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi" ta miƙe ta je ta ɗauko masa takardar ta miƙa masa.
Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci. Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce "Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa da ta ƙarshen aji, ita ta yi wannan ƙoƙarin"
Ruma ta yi murmushi sannan ta ce "Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce mini daƙiƙiya ba, shi ya sa na dage na je na iya"
"Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki"
Ta taɓe baki ta ce "A'a da wahala gaskiya, ka san baƙar wahalar da na sha kan na iya wannan abun, dan a dai na ce mini daƙiƙiya daga wannan ba zan kuma ɗaukar dala ba gammo ba"
Usman ya yi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce "Haba ƘANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ɗarsawa ranki cewa akwai wani abu da zai gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da faɗi tashi, musamman ga ɗan talaka. Kar wani abu ya ƙara razana ki, ko ki yadda ke daƙiƙiya ce zaki iya komai kema" Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Dan Allah da gaske Yaya Ussy?"
Ya jinjina mata kai ya ce "Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa akwai kalar ƙalubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan ƙafafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan daƙiƙiya ya biki ba"
Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce "Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da hankali na yi karatu sosai na daina wasa"
"Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa"
"Kuma zan cigaba da ƙoƙari, in zama mai ƙarfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum"
Mama da take jin su ta ce "Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba kya fatan Allah ya shiryeki ki daina faɗace-faɗacen banzan man a matsayinki na mace, faɗa ba na 'ya mace bane"
Ruma ta ce "A'a mama, gara ki bar ni na koyi ƙarfi sosai"
"Sai kuma ki yi ai".
Usman ya kuma murmusawa ya ce "Ba irin wannan ƙarfin ake magana ba, ƙarfin zuciya da kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su razana ki, ko sau ɗaya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ƙalubale duk girmansa, ki yi gaba da gaba da shi"
Ruma ta ce "Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke faɗa, sai na ji kamar ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba"
"Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci" Ruma ta miƙe ta tafi kitchen.
Mama ta ce "Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan, me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?"
Usman ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba, ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take buƙatar ta tsaya da ƙafarta ta cimma nasara" Mama ta ce "Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu'a kullum cikin yi muku ita nake, ba ku kaɗai ba, dukkan 'ya'yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku"
"Amin mama, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama"
"Amin ya rabb"
A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka har ta fara ƙular da mutanen gidan. Dan hatta maƙwabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi ƙoƙari a makaranta an bata kyauta. Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata murna tare da sanya mata albarka, ta ƙarasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta gaya musu ai a makarantar boko tayi ƙoƙari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan alkhairi, ji take a duniya yau ta ƙure daɗi tayi abin da ba ta taɓa ba. "Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar"
Wani malami ya kalleta ya ce "A sanar da me?"
"Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ɗin su"
"To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa ɗalibai"
Ruma ta ce "A'a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki".
Malam Habibu ya yi caraf ya ce "Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu" cikin jin daɗi ruma ta ce "Yauwwa malam na gode"
Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce "Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa".
Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin maza, ta leƙa ta ce "Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba".
Malam Habibu ya ce "To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka"
Haka malam Habibu ya tashi ya ce "'yan uwa ɗalibai da malamai, a taya 'yar uwa murna, wato 'ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu'a, Allah ya ƙaro nasarori"
Daɗi kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.
Huzaifa da suka yi salla sahu ɗaya da Yasir ya ce "Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?"
"Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta".
Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida. Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta faɗa jikinta ta ce "Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?"
Dattijuwar ta washe baki ta ce "Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ƙi saboda ina ƙauye".
Mama ta ce "Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku"
Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin daɗi ta zauna.
Matar ta ɗora da cewa "Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. Ɗan uwana ya ƙallafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matuƙar ƙaunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ƙartin ne kawai suke zuwa in da nake" ta yi maganar tana fashewa da kuka.
Mama cewa take "Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda za a dinga kawota".
Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ƙyal-ƙyale da dariya ta ce "Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?"
Yaya Aliyu ya ce "Ai gara ta fara gwada miki halin"
Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce "Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?"
Ruma ta ce "Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai daɗi a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa"
Gwaggo ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah" "Gwaggo wai ina wannan 'yar ta ki, mai kamar ni ɗin nan?"
Jin ruma ta tambayi 'yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce "Au Lawisa tana nan ƙalau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo"
Ruma ta yi dariya ta ce "Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?"
"A'a zaku yi tsayi ɗaya da ita"
Ruma ta yi murmushi tana kaɗa ƙafa.
Abubakar ya ce "Ruma ɗaga mata ƙafa mana"
"A'a ƙyaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa"
Ruma ta ce "Amin, ki yi mini Addu'a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai kuɗi sosai"
Mama ta riƙe haɓa ta ce "Ruma, ƙanƙanuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai kuɗi?".
Gwaggo ta ce wa mama "Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki" ta mayar da hankali kan ruma ta ce "Amin 'yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wadaƙa".
"Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau".
Aliyu ya ce"Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?"
Gwaggo ta ce "Ƙarya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ɗaya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da 'ya ta ba daga nan ba"
"Gwaggo kin san wa nake so na aura?"
"A'a sai kin faɗa"
"Kina kallon wrestling?"
Gwaggo ta ce"A'a ni ban san shi ba"
'To ball fa?"
"Ni ina zan ga wannan shirmen"
Ruma ta ce "Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su".
Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce "Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki" ruma ta miƙe daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.
Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma taɓara ta ƙaru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata faɗa ba, gashi kullum cikin faɗa take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.
"Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan 'yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan ɗan naki mugu ne" Gaba ɗaya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.