Kenza eBookz

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 31

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 31

Kanwar maza 3 Complete Chapter 31: Kanwar maza 3 Complete Chapter 31. Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar ɗakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu…

3,373 words

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar ɗakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"

Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina". Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen ɗin, ta ɗebi indomie, da abubuwan da take buƙata.

"Indomie zaki ci? Ko in turo barira ta dafa miki".

"A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs.

Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce.

Ko da rumaisa ta je kitchen ɗin ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke.

"Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata.

Da gudu ta fito falon, ta ɗane jikin Aliyu tana murna.

Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba.

Murmushi yayi ya riƙeta da hannu ɗaya ya ce "Ya kike?"

Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka ƙi zuwa"

"To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma".

Ta share hawayen ta ce "na daina"

Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki"

"Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba".

Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a ƙasa su waye?".

Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan".

"Saboda me, ke baki iya bane?".

"To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nikaɗai ba".

"Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?"

Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba".

Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ".

Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau baƙina da yawa"

Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba.

Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau " ya amsa yana kawar da kansa.

Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska.

Rumaisa ta karɓi Sabir tana murna.

Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin.

"Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa".

"A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an haɗa masa kayansa tukuna".

Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi.

Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku daɗe ba fa".

"Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi "

Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir ɗin".

Ta yi maganar tana tashi.

"Meyasa zamu tafi dan kin zo? Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care"

Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata kuɗi, suka fice.

Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan.

Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta haƙura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta ɗebo wasu daga kayan abinci daga kitchen ɗin ƙasa zuwa na sama.

Iman ta din ga mamakin yadda rumaisa ta iya girki.

Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane girkin wahala ce, na daina".

Iman har bayan la'asar tana nan, baba uwani na yi tana hawa benen, wai ko suna buƙatar wani abun.

Direba har ya zo ɗaukar iman, takawa bai dawo ba, haka ita ma iman ta tafi, gidan yayi mata shiru da yawa.

Sai yanzu take jin haushin tafiyar su mai sunan baba, ko a waya basu kira mata mama ba.

Baba uwani ta shigo falon da sallama da kayan abinci, ta ce "Uwar ɗakina, ga abincin mai gida, da naki na dare".

Rumaisa ta ce "A'a ai mun yi girki da iman, mun rage masa".

"To wannan ɗin a koma da shi kenan?"

Rumaisa ta ce "Eh, abincin ma a daina kawowa kawai".

"Amma saboda me?".

Ruma ta ce "Saboda na daina wahalar da ku, na iya girkin nima"

'Amma ai giwa ba ta ce mana haka ba".

Ruma ta ce "Da gaske nake na iya, kar ki damu"

Baba uwani ta fara jin haushin, rashin yaddar da rumaisa take nuna wa yadda taƙi sakin jikinta da ita.

Rumaisa ba ta damu da sanin dawowa ko fitar Adam ba, idan ba wani abu take buƙata ba, dan haka har ta yi bacci ba ta san ya dawo ko be dawo ba.

A cikin bacci yake jin kuka sama-sama, ya buɗe idonsa ya ji ana taɓa shi ana kuka.

Ya tashi sosai ya ce "Waye wannan?"

Ƴar siriryar muryarta ya ji tana cewa "Ka tashi zan mutu, dan Allah ka tashi!"

A burkice ya tashi, ya kunna fitilar wayarsa ya haskata, rumaisa ce a tsaye riƙe da hannunsa, tana kuka.

Ayshercool 08081012143 [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce "Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu".

"Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na ɗauko ki ba".

"Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba".

Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta riƙe hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji. Ya sake kallonta ya ce "You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini ɗaki, wancan ɗakunan zaki ɗauki ɗaya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can" ya ƙarasa maganar yana sakar mata baki.

"Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki"

"Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ƙarata" ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom ɗin.

Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banɗaki. Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka.

Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa.

Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ƙyam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauke shi.

Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa, ta duƙunƙune a cikin alkyabbar ta hau bacci.

Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin ɗaukar ta. Haka ma ƴan mazan nan, Aliyu cewa yake "Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ƙarama wallahi".

Usman ya ce "To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?"

"A'a addu'a kawai nake yi"

Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faɗa da ya haɗa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faɗa ba, haka suka kai har wurin ƙarfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure.

Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam. Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matuƙar tafasa da wani irin masifaffen kishi. Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba.

Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banɗaki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a ɗaki. Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faɗi, dan ya ɗauka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich ɗin ɗakin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke wai a nan ki ka kwana?" Yayi maganar yana taɓa ta.

Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi.

"Tashi, ki je ki yi salla" nan ma bata tashi ba.

Toilet ya shiga ya ɗebo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska.

A rikice ta tashi tana faɗin "Huzaifa meye haka wai?".

"Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini ɗaki ki tafi ga naki can ba"

Maimakon ta yi magana, sai ta haɗe rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba.

Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya riƙe hannunta ya yi waje da ita, ɗaya bedroom ɗin ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta.

Kallon ɗakin ta yi, wasu furnitures ɗin ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai.

Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma ɗakin da aka fara kai ta, wato ɗakin da Adam ya ce nasa ne, ta buɗe drower ya ɗau hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguɗa baki take ita kaɗai tana harare-harare.

Ta koma ɗakinta, ta yi salla, ta idar ko addu'a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli ɗakin sai ƙamshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba.

"Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su ɗauki ɗakin ƙasa, ko shi baban sabir ya koma ƙasa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu" ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta.

Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet ɗin. Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi.

Shiru ta ɗan yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce "In sha Allah sai na fita na koma gida".

"Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan, baƙi sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ƙasa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba".

Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce "To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba".

Mamaki ne ya kama shi, baƙar magana rumaisa ta gaya masa.

Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce "Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je" "To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?"

"Wuce mu je na ce" ya faɗa a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa ɗakinsa.

Ya nuna mata banɗaki ya ce "Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ƙasa suna jiranki".

Sai da ta gama kalle-kallenta a banɗaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a jiƙe, alamar yayi amfani da shi.

"Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba"

Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito.

Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buɗe wardrobe ya ɗauko, kaya ya tsaya ta gama shafa man.

Ya kalleta ya ce "Ga kaya nan ki canza".

Ta karɓa ta ce "To a gabanka zan canza kayan?".

"Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?"

Zare masa ido ta yi, ya ce "Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani"

Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta.

Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito.

Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta.

Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace ɗin yayi mata kyau sosai. Ba wani iya ɗauri ta yi ba, dan haka kawai ta ɗora ɗankwalin a kanta.

Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi.

Iman ta ce "Amaryar takawa, ina kwana"

Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta.

Ya kalli iman ya ce "Ta yi a haka?"

"Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a ɗan yi kwalliya sama-sama".

Rumaisa ta ce "Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a ɗaɗɗaure kamar ba ta wa ba".

Iman ta ce "Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya".

Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu.

Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daɗi, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta ɗaura mata ɗankwali.

Adam ya ce "Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi" Iman ta jinjina kai ta fita.

Ya kalli rumaisa ya ce "Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba".

"Kidnapping ɗina zaka yi kenan?" Ta yi maganar tana kallon sa.

"Eh" ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun da aka faɗa tana da amsar bayarwa..

Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta.

Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen.

Iman ta shigo ta ce "Yaya ku fito".

Ya ce "To, muna zuwa"

Ya sake kallon rumaisa ya ce "Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself"

Ta yi ƙuri da ido tana kallonsa. "Am talking to you" yayi maganar a ɗan kausashe.

"To" ta amsa a hankali.

Miƙa hannu yayi zai riƙo nata, ta janye a ɗan razane.

Ta girgiza kai ta ce "Ka daina taɓani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka riƙe mini hannu".

Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ikon Allah, to mu je" da ƙyar ta yadda suka jera, suka fita.

Suna fita aka din ga rafsa guɗa, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura.

Suka ƙarasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu'a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ƙuri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar.

Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta miƙawa adam hannu ta ce "Ban ga ka fito da ƙyalle ba, dan mu tabattar da me ka aura".

Ya ce "Haba jakadiya, wannan al'adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?" Yayi maganar yana kallon rumaisa.

Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?.

"To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka buƙaci gani, kar mu je saura aka kawo mana".

Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi.

Sai da ƙirjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce "Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan"

Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga ɗakin, na kwana a ƙasa, meye wani abun alfahari.

Ƴan uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce "Dama ɗaki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida".

Da sauri rumaisa ta ce "Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama".

Adam ya ce "Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a ɗan tayata zama"

Gwaggo ta ce "A'a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga saƙonki nan babarki tana gaishe ki"

Tashi rumaisa ke ƙoƙarin yi, amma ya riƙeta, ya hanata tashi.

"Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?" Ta yi maganar tana kuka.

Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo.

Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya"

Ta ce "Babu komai, Allah ya sanya alkhairi"

Ya ji daɗin tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba.

Ɗago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faɗin "Is ok, yi haƙuri kukan ya isa haka"

Ƙoƙarin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ƙyaleshi.

Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koɗa yadda gida yayi kyau.

Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce "Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taɓa zaton zaka auri ƙaramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ƙaramar yarinyar ce ta kuɓuta da Sabir, daga hannun 'yan bindiga"

"Ai babu mamaki a ikon Allah, ƙanƙantarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saɓawa shari'a ba".

Ta kalli rumaisa ta ce "Sannu ƴar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan ɗauka"

Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama.

Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara.

Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faɗe-faɗen maganganun su, da yada habaici.

Da azahar ɗin kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull