Kanwar maza 3 Complete - Chapter 32
Kanwar maza 3 Complete Chapter 32: Kanwar maza 3 Complete Chapter 32. Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa,…
3,360 words
Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi.
Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata ɗakinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe ɗin ta, ga su iman nan, su tayata a haɗa mata ɗakin.
Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi.
Tana ƙoƙarin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce "Bar shi, zan yi da kaina"
Kallonta suka yi gaba ɗaya,Nusaiba ta ce "Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so"
Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi".
Nusaiba ta ce "To shikenan, baba uwani ƙyale mata".
Adam ya shigo ɗakin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan.
Nusaiba ta ce "A'a ta ce a ƙyale mata, za ta yi abun ta da kanta".
"Shikenan, ku ƙyale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la'asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba".
"A'a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?".
Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce "Do as i said"
Baba uwani ta yi mamakin yadda ƙiri-ƙiri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa taƙi. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo.
Sannan ta yi mamakin yadda suka haɗu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara ɓoye mata wasu abubuwan.
Kan su ƙarasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ƙarasa gida.
Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce "Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi".
"Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru".
Iman ta ce "Ammi kin san me?"
"A'a sai kin faɗa".
"Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ƙyalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun 'yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama"
Ammi ta yi shiru ta ce "Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam da rumaisa, sai ya bawa mara ɗa kunya in sha Allah".
Nusaiba ta ce "Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wataƙila Mummy ce zata saka su, ai daɗinta maman Sabir ɗin ma ba kanwar lasa ba ce".
Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faɗa sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa'a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya.
Mummy ta kalleta ta ce "Ya aka yi?".
"Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ƙyalle, ya ce wannan tsohuwar al'ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya....
Samha ta ce "Dakata, ƙarya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ƙarya yake babu abun da ya faru" Mummy ta ce "Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace".
Ta risuna ta ce "In sha Allah uwar ɗakina".
Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window ɗakinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo.
A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ƙasan bene bata taɓa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ƴan gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta ɗan rage damuwa, da yin la'asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta.
A kwana na huɗu ya lura, tana gujewa haɗuwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai.
Bayan sallar magariba ya shiga ɗakinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru.
Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya.
Ƙasan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ƙasan benen.
Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buɗe gaban motar ya ce ta shiga.
Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar.
Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huɗu, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan.
Security light duk ta haske ko ina a gidan.
Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.
Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.
Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita"
"Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta"
Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.
Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki"
Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman".
"Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai"
"To ni kaɗai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka"
Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga ɗebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta".
Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, ɗauke da Sabir a hannunta.
Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman"
Rumaisa ta ce "Mata ina wuni"
Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa"
Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu. Adam ya ce "Kai, kwana huɗu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki ɗauke shi"
Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.
Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir.
Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haɗo mini kayansa, na tafi da shi ko?"
Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a ɗauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata".
Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faɗi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.
Ayshercool 08081012143 [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
A gigice ya tashi zaune yana tambayar rumaisa ko lafiya. Idanuwanta duk sun yo waje, sai sauke numfashi take yi, hannunta ɗaya riƙe da cikin ta, tana kuka.
"Ki yi mini bayani, menene meya same ki?".
"Cikina ciwo, zan mutu dan Allah ka taimakeni, wayyo mama" a gigice ya sauka daga kan gadon, ya kunna fitila hakse ya gauraye ɗakin.
Tana durƙushe ta riƙe cikinta, hankali tashe ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya saka jallabiya, ya ɗauki mukullin motarsa, ya tafi ɗakinta da sauri, ya ɗauko mata hijjabi, ya saka mata, ya riƙo hannunta.
Da ƙyar take iya takawa, sai yarfe hannu take yi tana kuka, suka saukko ƙasan benen.
Baba uwani na jin motsi but kamar fitar tusa ta fito, "Ranka ya daɗe lafiya? Meya samu ƴar ta wa?".
"Ba ta jin daɗi ne, zamu je asibiti".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya sameki haka?"
Rumaisa ba ta amsa mata ba, ta cigaba da kuka.
"Yallaɓai ko biyoku zan yi, ko za a buƙaci wani abu, ba ka tafi asibiti kai kaɗai ba, daga kai sai ita".
Adam ya ce "A'a baba uwani, ki yi zamanki dan Allah, ba sai mun wahalar da ke ba, zan iya kula da ita".
Ya saka rumaisa a mota, ya kunna ya fita.
A cikin motar ma, she was very restless, ta rasa in da za ta sanya kanta, ta juya nan ta juya can, sai kuka take yi.
"Ko dai wani abun ki ka ci ya ɓata miki ciki? Ko kuma abincin da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin".
"Nima ban sani ba, cikina zai haɗe da ƙafata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku".
"Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu".
Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka buɗewa rumaisa file ya shiga da ita.
Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa.
Ta ce masa "Cikina ne da ƙafafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai".
Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?"
Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?".
Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?".
"Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa.
"Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne".
Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?"
Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban taɓa yi ba"
Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar? Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?".
"Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta.
Adam ya ce "Za ayi watanni takwas".
Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a.
Yayi counseling ɗin ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba.
Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya karɓa ya ja hannunta suka fita.
Ta bashi tausayi ba kaɗan ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba.
A durƙushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata.
Sai dai ta ce Allah karta ba za a buɗe mata jiki a ganta a gaban Adam ba.
Ga ciwo na cinta, ga zunzurutun wauta, in da Allah ya taimaka, nurse ɗin da take on duty mace ce.
Ƙarshe ta tsaya ayi allurar nan, ba ta tsaya ba, dai da adam ya fita, daga waje yana jiyo kukanta, sai ka ce ƴar shekara biyar, saboda an yi mata allura.
Sai dai ana gama yi mata allurar ta hau amai, kasancewar tun rana rabonta da abinci.
Aikuwa Adam ya din ga yi mata faɗa, na rashin cin abincin da ba ta yi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya tare da ita, ƙarshe sai da suka dangana da saka mata ruwa.
Haka Adam ya zauna da ita, har asuba a asibitin, aka gama yi mata abun da za ayi mata, na ƙarin ruwa da allaurai ya ɗauke ta zuwa gida. Suna tafe a hanya ta samu barci, dama tun suna asibiti yayi sallar asuba.
Da ƙyar ya kaisu gida, saboda barccin da yake ji.
Sai da suka isa gida ya tasheta, ta fita daga motar tana takawa a hankali.
Baba uwani na jin tsayuwar motar, ta fito tana yi musu maraba, tana tambayar jikin rumaisa, Adam ya ce mata da sauƙi.
Suka nufi step ɗin bene, baba uwani ta sake cewa "Takawa ko zan zo na taimaka da wani abun ne?"
Ya ce "A'a ta warware, ciwon ciki ne dama, yanzu bacci za ta yi"
Ta ce "To shikenan babu laifi, Allah ya ƙara lafiya".
Ya amsa mata da Amin.
Sai da ya raka rumaisa har ɗakinta, sannan ya juya ya fita, sai dai yana fita ya ji kukanta ta na faɗin "Na shiga uku, zan mutu".
Da sauri ya koma yana tambayarta menene?.
Ta ɗage doguwar rigar jikinta, Jini na bin ƙafarta.
"Dan Allah ki yi wa mutane shiru da wannan koke-koken, maganin me zai yi miki?"
"Jinina ne zai ƙare, idan ya ƙare mutuwa zan yi".
"Ai gara ki mutun in huta, ki yi mini shiru ni, bari na yi wa baba uwani magana, ta zo ko da abun da zata taimaka miki da shi".
Da sauri ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka kirata, ka kirawo mini su Yaya usman a waya, dan Allah"
Kallonta yake, cike da mamakin wauta da rashin hankalinta.
"Ke wai ya ki ke so na yi ne?, shikenan ba zan huta ba saboda na aureki? Tun da ba za a kirata ba, sai ki wuce toilet ki gyara jikinki".
"Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin".
Guntun tsaki ya ja, ya wuce banɗakinta, ruwa ya haɗa mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banɗakin.
Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banɗakin, ya janyo akwatin lefenta, ya ɗauko mata pad, kasancewar lokacin da aka haɗa lefen har da ita a ciki. Ya ɗauke bedsheet ɗin daga kan gadon.
Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banɗakin, tana ta raɓe-raɓe.
Ya kalleta ya ce "ƙazamar ina ce ke? Ba ta ɓaci da jini ba ki ka kuma sakawa?".
"To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.
Ajiye mata pad ɗin yayi, ya ɗauki bedsheet ɗin ya fice.
Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad ɗin na in da ya ajiyeta.
"Ba zaki saka bane?".
"Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani"
Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba.
Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad ɗin ta ɗaure a leda, ta canza phant ta canza wata. Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata ɗakin.
Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haɗa da kayanta da ta cire suna banɗakinta.
Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice.
Ko da baba uwani ta ciro bedsheet ɗin, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya.
"Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ƴar tatsitsiyar ƴar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ƙarshenta ma na sha zagi".
Babban abun da ya yi wa rumaisa daɗi, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?"
Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daɗi, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka".
Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daɗin ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi"
"Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman".
Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karɓi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya.
Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai ɗaga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ƙaraci ringing ɗin ta, ta kaste yaƙi ɗagawa.
Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yayi sallama.
"Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma taƙi zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma"
"Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ƙorafi?".
"Mama taƙi ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya".
Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka? Meya sameki?".
"Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba".
Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ƙyaƙyace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo".
Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi"
Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?".
"Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa".
Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki".
"To ai ba wayata ba ce ba".
"Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ƙara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar ɗaukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar.
*** "Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves ɗin sa ne?".
"Ranka ya daɗe, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa".