Kenza eBookz

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 5

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 5

Kanwar maza 3 Complete Chapter 5: Kanwar maza 3 Complete Chapter 5. Turaki ya yi mata ƙuri da ido, tsananin kwarjininsa ya sanyata sunkuyar da kai, ta ji…

3,345 words

Turaki ya yi mata ƙuri da ido, tsananin kwarjininsa ya sanyata sunkuyar da kai, ta ji kamar jikinta zai hau rawa, saboda kwarjininsa, sun fi mintuna biyar bai ce komai ba.

Adam ya kuma yi mata nuni da ta sauke facemask ɗin ta, amma taƙi sai da usman ya kalleta, sannan ta cire.

Turaki ya cigaba da kallonta sannan ya ce "Iko, sai Allah yanzu wannan ƙaramar yarinyar ce ta ceto yaron wurin fulani"

"Eh Allah ya baka nasara, ita ta zo da shi"

Ruma a ranta ta ce "Taɓ, wanna wace irin wahala ce, da ban cire facemask ɗin ba, kenan haka zamu yi ta zama ba zai yi magana ba?'.

Turaki ya ce "Bamu labari, ya aka yi aka haɗu da fulani, har aka zo mana da jaririnta?"

Rumaisa ta ɗan waiwaya ta ce "Wace fulani kuma?"

"Aisha" Adam ya bata amsa.

Sai ta yi turus, ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Usman ya ce "Ki yi magana mana"

Ta yi shiru ta shiga wasa da ƙasan rigarta.

Turaki ya ƙura mata ido ya ce "Ke muke sauraro yarinyar kirki" ɗaga idonta ta yi tana kallon adam, da ya murtuke fuska saboda ƙuluwa da ya fara yi, da iskancin da rumaisa ke yi.

"Ko su bamu wuri ne?" Turaki yayi maganar yana nuna su adam.

Ta jinjina masa kai alamar eh, ya ce "To babu laifi, takawa a bamu wuri, kar a damu a bamu wuri mu tattauna".

Takawa bai taɓa zaton iskancin rumaisa ya kai haka ba, ƙin yarda da shi ta yi masa bayanin abun da ya faru, ya sanya yayi zaton a gaban turaki za ta yi bayani, amma mirsisi taƙi magana sai sai ya fita. Ganin yadda adam ya harzuƙa, ya sanya turaki yi masa alama da ya kwantar da hankalinsa. Sai dai ba iya adam ɗin ne ya ƙulu ba, har usman ya ƙule da abun da rumaisan ta yi.

Haka suka tashi suka bar falon.

Turaki ya mayar da kallonsa ga rumaisa ya ce "Matso kusa da ni nan ki yi mini bayani"

Rumaisa ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta hango hoton aisha a bayansa, ta ƙurawa hoton ido, da har sai da turaki ya waiwaya ya kalli hoton.

Ya ɗauko hoton a hannunsa, ya shafa shi ya ce "Kin ganta nan, a cikin 'ya'ya na kusan goma sha rayayyu da wanda suka rasu, babu wadda nake jin daɗinta nake zartar da hukunci komai ɗacinsa ta karɓa sai Aisha. Na tafka babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba, Allahn da ya bani ya fi ni son ta, ban so ta mutu a wulaƙance haka ba, sai dai ba zan zargi sirikina ba, ɗana ne shima, kuma ba zai cutara da aisha ba"

Rumaisa da hawaye ya fara zubo mata ta ce "Tabbas anty aisha tana da kirki, kowa cewa yake yi bana jin magana, amma ita ta fara cewa rashin ji na yana burgeta. A makaranta bana gan karatu, amma ta ce mini mai kaifin basira ce ni, ta yi ta kula da ni a hannun 'yan bindiga kan ta rasu, amma mijinta ne ba shi da kirki ko kaɗan, shiyasa naƙi magana a gabansa".

Turaki ya yi murmushi ya ce "Tabbas takawa yana da zafin rai, amma mutumin kirki ne sosai".

"Na san a ƙule yake da ni, yanzu ba dan kai ba tsaf sai ya zaneni a wurin nan, ita rayuwa idan mutum yana son ya ci ribar abu ba haƙuri ake a bishi a sannu ba? Idan haka zai din ga yi komai ya tunkara sai ya faɗi. Kuma dai naga ɗan sanda ne shi, mai ya hana ya kai mana agaji lokacin muna hannun 'yan bindigar, da bakinsu fa suka ce jami'an tsaro ne suke basu gudunmawa, to yanzu kuma dan Allah me zai yi bayan mai faruwa ta faru".

Zuba mata ido kawai turaki yayi, yadda take zaro magana, tana arranging ɗin ta, tamakar tana karantowa, kuma ba zaka taɓa cewa yarinya ce mai kamar shekarunta take faɗa ba.

Ya gyara zamansa ya ce "Haka ne, kema kin yi magana mai kyau, amma yanzu dai ina jin ki".

"Baba"

Ya ce "Na'am yarinyar kirki"

"Amanatun amana, zan gaya maka komai, gani ake ni Yarinya ce amma ina da wayona, ta ƙarfin tsiya fa ya ƙwace mini ɗa, ko tausayina ba ya ji alhalin anty aisha ta ce ta bar mini shi halak malak. Zan gaya maka komai, amma shi ba zan gaya masa ba, kuma wallahi na san abubuwan da shi bai sani ba".

Duk girman turaki, ruma ta iya kallonsa ta ce masa amanatun amana, tare da yi masa kashedin, kar ya gaya wa kowa abun da za ta gaya masa.

Ƙwarin gwiwar ta, da rashin tsoronta a ƙananun shekarunta ne ya fi bashi mamaki, kuma tsara zancenta da kaifin basirarta ya burge shi.

Ya ce "Kar ki damu, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai ke sai Allah".

Nan rumaisa ta gyara zama ta fara yi masa bayanin abubuwan da suka faru, duk a hirarta ta ya fuskanci ba komai ta gaya masa ba, amma a hakan ta yi ƙoƙarin yi masa duk wasu bayanai da yakamata ya sani, sai dai kan ta kammala, hawaye ya wanke mata fuska, sai gogewa take da hijjabinta. Shi kansa turaki kasa jurewa yayi, cikin dabara ya goge hawayen da yake shirin zubo masa, yana jin labarin wai-wai a kafafen watsa labarai, bai taɓa zaton masifa da tashin hankalin ya kai haka ba, kuma ta bakin rumaisa ne idan aka fara haɗawa da 'ya'yan masu faɗa a ji ana sacewa wataƙila a mayar da hankali a kan maganin abun, kuma abun kunya ne ga jami'an tsaro, ace an sace matar jami'in tsaro kuma an kasa ceto ta har ta rasa ranta. Uwa uba azabar da rumaisa ta sha kan ta fito da jaririn, shi kansa ya isa abun tausayi duba da ƙananan shekarunta, gashi sai nanatawa take ita fa aisha ta bar mata ɗa, amma adam ya ƙwace mata.

Ya duba gefen sa, ya ɗauko wani handkerchief mai matuƙar kyau da taushi, sai ƙamshi yake yi, ya miƙawa rumaisa ya ce "karɓi nan ki goge hawayenki, kukan ya isa haka".

Karɓa ta yi, amma ta kasa gogewar, saboda kukan da ya ci ƙarfinta.

Usman kuwa ba ƙaramar mita yayi ba, a kan abun da rumaisa ta yi, tun da suka fito yake mita. "Ban taɓa ganin yarinya mai azababben taurin kai, na tashin hankali kamar rumaisa ba, gaba ɗaya yarinya kamar wata majanuniya, ita duk wata hanya ta masalaha ba ta santa ba, idan ta akasin masalahar ma aka biyo mata ta fi misbehaving, ba a gane gabanta da bayanta kamar ɗan wake". Adam kam azabar takaici, bai bari ya iya tankawa ba, gani yake gaba ɗaya yarinyar ta gama raina masa hankali.

A nutse turaki ya din ga rarrashin rumaisa, yana yi mata nasiha, har sai da ya sanya ta ɗan yi murmushi ta ce "Baba ka iya magana a nutse wallahi, ni yadda kake magana ma daɗi yake yi mini"

Abun da ta faɗa ɗin sai da shi ma ya sanya shi murmushi, ta kai handkerchief ɗin da ya bata fuskarta, Ta lumshe idonta ta ce "Wayyo ƙamshi, baba ban taɓa jin turare mai daɗin wannan ba, kamar na suma dan daɗi".

Jan rawaninsa yayi ya rufe fuskarsa, dan dariya rumaisa take neman ta saka shi.

Hadimai ne suka yi sallama, suka shigo masa da kwanukan abinci a kuloli da kuma akushi, aka zo aka jere su a gabansa.

Rumaisa ta dinga kallon fulasai na alfarma.

Turaki ya ce "Ga abinci nan, buɗe a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki ci".

"A'a na ƙoshi, mama ta hanani cin abinci a waje".

"To ai nan gidanku ne, ki ci duk abun da ki ke so".

Ta nuna masa akushi ta ce "Wannan menene?".

Ya ɗauko akushin ya ajiye a gabanta ya ce "Sunansa akushi".

"Akushi da rufi, sai sarki, kenan kai ma sarki ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, ni ba sarki bane ba".

"To dama ba duk masu rawani ba sunansu sarki ba"

Turaki ya murmusa ya ce "A'a ba kowane mai rawani ne sarki ba, kowa akwai sunan muƙaminsa"

Ruma ta din ga kallon akushin nan, ta saka hannu ta buɗe, ta ga dubulan fal a ciki" tayi iya ƙoƙarinta wurin tuna sunan sa amma ta kasa ta ce "Mmm ya ma, abun da ake kaiwa idan an yi aure mai sugan nan sunan shi kenan".

Ya kuma miƙo mata wani akushin, ya ce "Gashi nan, duk duba ki ci wanda ki ke so".

Ta bubbuɗe kulolin nan, wata irin miya ta alfarma, ta sha naman kaza yanka manya manya. Ta ce "Mama ta yi mini kashedi a kan banda rashin ji, kuma idan na yi wani rashin ji, yaya usman ya gaya mata zaneni za su yi".

Turaki da bai ji ya gaji da surutun rumaisa ba, kuma bai jin zai gajin ya ce "Ki ci ba zan gaya masa ba, ba zata sani ba".

"Hmm ba ka san halin mama ba, yaya usman sai ya gane, amma dai bari na ci wannan".

Ta saka hannu ta ɗau dubulan, ta fara ci, dama rumaisa gata mayyar suga, tana ci tana lashe baki.

Kallon rumaisa kawai yake yana murmushi, yarinya ce ƙarama, ita a yanzu babu abun da yake damunta, sai dai ta yi ciye-ciyenta ta faɗi abun da take ji a ƙwaƙwalwarta shi ne dai-dai, sai dai yanayin yarinyar ya nuna ba za ta yi ƙarya ko ha'inci ba, kuma tana da ɗan karen wayo.

Hajiya Sauda ce ta shigo, sai dai ta yi turus, ganin yarinya zaune a gaban turaki tana cin abinci a kwanonsa, duk da ta bawa ƙofa baya, ba ta iya sanin kowacece ba.

"Mai girma turaki wannan kuma wacece? Meyasa take cin abinci a kwaonka, kwanon da ko 'ya'yan cikinka ba su da wannan damar".

Ɗan turus rumaisa ta yi, amma ba ta waiwayo ba, ta kuma miƙa hannu, ta ɗauko alkaki, tana taunawa tana jin zaƙin sugan har cikin kunnuwanta.

Turaki ya ɗaga kai ya kalli mama ya ce "Baƙuwata ce?".

"Baƙuwarka kuma kamar yaya kenan?"

Ya kalli rumaisa ya ce "Yarinyar kirki, je ki ki kirawo mini takawa"

Rumaisa ta miƙe ta ce "To baba". Sai a lokacin ta juyo suka yi ido huɗu da mama.

Rumaisa ta wani lumshe ido, ta ce "Ina wuni". Kallon banza ta yi wa rumaisa, ta ji gaba ɗaya yarinyar ba ta yi mata ba, idonta kawai zaka kalla ka gane tattacciyar mara kunya ce. Rashin amsawar ta ta bai ɗaɗa ruma da ƙasa ba ta fita falon.

Usman na ganinta ya harareta, sai dai bai tsinke da lamarin rumaisa ba sai da ya ga tana lashe hannu tare da gutsurar wani abu a hannunta.

"Kar dai yarinyar nan ciye-ciye ta je ta zauna ta na yi? Ya tambayi kansa.

"Wai ka zo in ji baba mai rawani" ta yi maganar tana kallon adam ba tare da ta kama sunansa ba.

Bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da danna wayarsa.

"Magana nake maka, ana kiranka"

Still bai amsa mata.

"Takalmawa ake ce maka ko me?, sunanka dai Adamu ba wani Adam ba to ka zo in ji baba mai farin rawani"

Wata irin tsawa aka bugawa rumaisa, wadda sai da ta tsorata, ta kusa faɗuwa!

AYSHERCOOL[12/12, 7:33 PM] rahama Jos: *Paid book ne ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa cimmasa. Ko da Adam ya ƙarasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ƙofar suka buɗe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi.

A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha'i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta. Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ruƙayya.

Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce "Barka da warhaka giwar mata".

"Barkanki dai, kuna lafiya?"

"Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"

Ammi ta amsa da "Alhamdilillah"

"To Allah ya jiƙanta da rahama"

"Amin ya rabb"

Mummy ta gyara zamanta ta ce "To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu ɗaya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi"

Ammi ta ɗan dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da maganganu ba, ta basar ta ce "Bari a kawo shi ki ganshi" tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba.

Iman ce ta ɗauko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta karɓe shi, tana wani irin murmushi ta ce "Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa"

Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.

"To wane sunan aka saka masa?"

"Mahmud, ana kiransa sabir".

Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce "Mahmud kuma? Sunan Mahmud ya ci kenan?"

Ammi ta ce "Eh, sunansa ya mayar masa"

Mummy za ta yi magana, Adam ya faɗo ɗakin kamar wanda ya ƙwato a hannun miyagu.

Tun a falon ya fara ɓalle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi, ƙafafuwansa kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba.

A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu, tana tambayar ko lafiya.

Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi.

A gigice ammi ta ce "Iman, ɗauko maganinsa maza"

Da hanzari iman ta fita ta bar ɗakin, ammi Cikin damuwa ta ce "Takawa meyafaru ne? Meyake damunka?" Bai amsa mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi.

Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta buɗe ta tsiyayo, ta fara ƙoƙarin shafa masa, amma ya juya kansa ya ce "Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lulluɓeni" duk yadda ammi ta so shafa masa ƙin yarda ya yi, sai lulluɓe shi da aka yi.

Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce "Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?"

"Ina iya ƙoƙarina, Allah ne bai kawo ƙarshen abun ba"

"To kina zaune Allah za kawo ƙarshen lamarin, shi meye wannan ɗin da ake shafa masa?" Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa "Magani ne"

"Miƙo mini na gani" ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta ɗauka ta miƙa mata, ta karɓi jarkar ta din ga jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce "Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai buƙatar ki miƙe tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa" kamar dai ɗazu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba.

Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya ɓace masa, ya haƙura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam ɗin, kuma ya kira shi bai ɗaga wayarsa ba.

*** Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki. Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai ƙamshin gaske. Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu. Ruma ta din ga yashe baki tana murna.

Mama ta ce "Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa ɗan su rashin mutunci"

Ruma a ranta ta ce "Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na tabattar masa da abun da na gaya masa ai" mama ta yi ta mita, amma ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai ma tunanin gobe in Allah ya kaimu za ta koma makaranta abun da ba ta so.

Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa. Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin ƙishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi. Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata ɗan ta. Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya ƙulla a ƙwace sabir a hanata shi.

Cikin ikon Allah, takawa ya farfaɗo gaba ɗaya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin.

Ya ɓoye yaƙi gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.

Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya cikin uniform ɗin ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta.

A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun ƴan bindiga ya zame mata darasi. Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing ɗin abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu.

"Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, taɓ wallahi ba..." Gum ta rufe bakinta ba ta ƙarasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya.

A ranta ta ce 'Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma daƙiƙanci ne ya saka aka yi mata repeating"

Da aka fita break, ƴan ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo.

Sam ta ƙi shiga sabgar kowa, ta ɗau littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta. Har aka tashi ba ta san me aka yi ba.

Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?

Rai a ɓace ruma ta ce "saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma" ganin rumaisa za ta ɓata rai, ya sanya ta shareta.

Can rumaisa ta kuma cewa "Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba ƙafarta"

Mama ta ce "Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya kaimu"

"Dan Allah mama in je yau"

"Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba"

"To ki yi haƙuri, Allah ya kaimu goben".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull