Kanwar maza 3 Complete - Chapter 6
Kanwar maza 3 Complete Chapter 6: Kanwar maza 3 Complete Chapter 6. Adam kuwa gaba ɗaya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar…
3,340 words
Adam kuwa gaba ɗaya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar saƙon ko jabir ya zo, a bashi haƙuri ba zai iya ganin kowa ba. Ya kulle kansa a ɗaki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da saƙonni daga ƴan jarida, mutane sai comments suke kala-kala. Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba ɗaya ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da ƙudurinsa na son kawo ƙarshen yi wa ƙasa da harkar tsaro ɓarna. Ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar bincikar waɗanda suka yi garkuwa da matarsa.
Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya buɗe ɗakinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake faruwa ba, saboda kar ya sake ɗaga mata hankali.
Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta mata rai sama da haka. Yau da rumaisa ta je makaranta, ƙin zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba ɗaya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba ƙaunar makarantar take yi ba.
Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika maƙil da hadimai, da jami'an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan. Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi. Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki.
Ƙafa da ƙafa ya zo ya yi wa Adam ta'aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru.
Mai martaba ya numfasa ya ce "Turaki yayi mana bayanin komai yadda al'amarin ya faru, sai dai bai kamata a ɓoyewa duniya gaskiyar abun da ya faru ba, maƙiya za su iya amfani da wannan damar, wurin cutar da kai, kamar yadda zancen ya fasu har wata gidan jarida suka wallafa, kuma ba zai wuce saboda ƙoƙarin da ake yi wa ƙasa ba, ya sanya miyagu ke ta ƙoƙarin bayyana laifinka, amma ayi haƙuri a daure, a cigaba da abun da ake yi kar a fasa Allah zai shiga lamarin"
Adam ya risuna ya ce "In sha Allah, muna fatan mai martaba ya cigaba da sanya mu a addu'a".
"Addu'a kullum cikin yi muku ake, kuma ko dan albarkacin mu babu wani abu da wani zai iya yi ya cutar da ku a kan gaskiya a ƙasar nan, a cigaba da ƙoƙari. Ita kuma 'yar mu Allah ya jiƙanta ya raya mini wannan kyakykyawan jikan nawa" yayi maganar yana shafa kan Sabir da yake hannunsa.
Mummy ta risuna tana "Allah ya taimaki mai martaba, mun gode da wannan karamci, Ubangiji Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"
"An gaisheki amaryar Galadima, , ƴar malam kin ƙi halin malam, mai martaba ya amsa kuma yana godiya" wani irin takaici ne ya kama mummy, jin yadda hadimin mai martaba ya amsa mata.
Aka karɓi jaririn aka miƙawa ammi, shamaki ya dubi ammi ya ce "Mai martaba ya bawa jariri gidaje guda biyu, ya bashi dawakai guda uku, sannan mai martaba ya yi umarnin a gina masallaci sadaka ga mahaifiyarsa. Sannan idan ya shekara uku a duniya mai martaba ya ce a kai shi umara"
Nan dogarai suka ɗauka da "Godiya yake mai martaba, godiya yake Allah ya baka yawan nasara. Mai bayarwa da dama hagu ba ta sani ba"
Takawa ma risinawa yayi, suna yi wa mai martaba godiya. Dogaransa suka kare shi ya tashi tsaye, har zai fita ya hangi iman a gefe a zaune.
Ya ce "Ahhh giwa, wannan buzuwar ƴar ta ki tana nan dama, ko da yake an ce mini bafullatana ce? ta daina zuwar mana, Allah ya jiƙan mai babban ɗaki, lokacin da muka kai mata ziyara a Saudiyya kan ta rasu, take tambayar ina wannan buzuwar ƴar ta giwar Galadima, a lokacin bamu sani ba ko kuna tare ko kin mayar da ita, mai babban ɗaki tana sonta"
Ammi ta yi murmushi ta ce "A'a muna tare mai martaba, ai tun da kuka saka baki a kan maganar nan, muke tare da ita"
"Allah sarki, baki fuskanci wani abu ba binta, wataƙila albarkacin yarinyar nan ne Allah ya kawo muku yaron nan cikin aminci, Ubangiji Allah ya yi jagora, Allah ya raya mana su baki ɗaya"
Ammi ta amsa da amin mai martaba.
Ba ƙaramin ƙulewa Mummy ta yi ba, yadda mai martaba ya mayar da hankali a kan yaran ammi, har da agola, amma ita ko kanta bai bi ba.
Mai martaba na tafiya, mummy ta fice fuuuuu ta bar sashin ita da su Fauziyya.
Bayan fitar su Ammi ta ce "Iman, mun yi laifi fa daina zuwa gidan mai martaba da ki ka yi, balle ki je gaishe shi, kin ga har ya magantu, Allah sarki mai babban ɗaki, lokacin kina ƙarama rigingimun da aka yi ta yi a kan ki, cewa ta yi sai na bata ke, na din ga kuka, ita tsaya mini a kan riƙonki".
Iman ta ce "Ammi tsoron zuwa gidan nake, fulanin yola ta hana ni zuwa, saboda yarima Hashim, kin san ai abun da aka yi mini su da Mummy" Ammi ta ce "Na ji, kar ki yi kuka, jikina na bani mijinki mutum ne na gani na faɗa, karki damu autata"
Kunya ce ta kama Iman, Nusaiba ta ce "To ni fa, ko ita kaɗai ake yi wa Addu'a"
"Ke dai nusaiba baki da girma sai na jikinki, kishi ki ke iman ɗin?"
"To shikenan ma, ni na yi zuciya" Nusaiba ta tashi za ta fita, iman ta tashi ta bita da gudu tana yi mata dariya.
Ammi ta mayar da hankali a kan adam, da fuskarsa sam babu walwala, ta dube shi a tsanake ta ce "Mai martaba yake magana a kai ne, na ji yana cewa an yi amfani da gaskiyar abun da ya faru ana sukarka, meyafaru?"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Wata gidan jarida ne suka yi posting a social media, cewar aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, ko kuma ni na kasheta na yi tsafi da gangar jikinta tun da ba aga gawarta ba ma"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, adam waye ya aikata wannan abun? Waye ya fitar da wannan zancen har da sharri haka?"
"Nima ban sani ba, ɗazu na ɗauko wayata a mota, kira daban-daban da saƙonni daga ƴan jaridu, suna buƙatar wai na ce wani abu a kan lamarin na kashe wayar ma gaba ɗaya".
Ammi ta dafe kai, ta rasa me ma za ta ce ko ta yi? Abubuwa kullum sake rikicewa suke yi.
Da la'asar yasir ba dan yana so ba, ya saka rumaisa a gaba zai kaita cikin gari, suna tafe yana mita, sai da suka je titi, sannan rumaisa ta ce "Dan Allah Yasir taimakona zaka yi"
"Taimakon me?"
"Dan Allah gidan su sabir zaka rakani na je na ganshi" wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Ba zani ba, yaushe ki ka je ki ka ganshi? Ba zani ba ba nan muka yi da mama ba".
Riƙe hannunsa ruma ta yi ta fara kuka "Dan Allah yasir, wallahi na kasa bacci jiya, ba zamu daɗe ba dan girman Allah" ganin tana kuka ya sanya jikinsa yin sanyi.
"Kin yarda zaki wanke mini uniform, ki ɗaukar mini jakata zuwa islamiyyar"
Da sauri ta ce "Eh wallahi na yarda"
"Shikenan mu je, saura idan buƙatar ki ta biya, ki yi mini rashin kunya".
"Ai ba ma zan yi ba"
Ya tarar musu abun hawa, suka hau suka tafi.
Suna tafe yasir yana danna waya, can ya ce "Kaii"
Ruma ta ce "Menene?"
"Wani labari na gani, ke dama baban sabir ɗin nan shi ne Adam Sharif Galadima?"
"Wai wannan mai tona asirin mutanen, ba wani nan ba shi ne ba"
"Dan ubanki ƙarya zan yi miki?"
Rumaisa ta ce "Taɓ, ba shi bane ba, shi wannan yana abun arziki ne?"
Yasir ya ce "Ke ba wannan ba, wani labari aka wallafa wai, ya sayar da matarsa yayi tsafi da gangar jikinta, kuma jaririn da aka ce nasa ne, ƙarya ne rainawa mutane hankali ake"
Wani takaici ne ya turnuƙe rumaisa ta ce "In ji uban wa?"
'oho, wani gidan jarida ne suka wallafa"
Rumaisa ta ce "To rubuta musu ka ce ƙarya suke yi, wannan yaron nice nan na zo da shi"
Yasir ya ajiye wayar ya ce "A'a ba ruwana"
Rumaisa ta ce "Zan yi waya katsina a kawo mini wayata ni na rubuta, wannan ai sharri ne"
"Ke dalla rufewa mutane baki, zaki saka na ƙi rakakin wallahi"
Ta riƙe bakinta ta ce "Na daina in sha Allah"
Da haka suka ƙarasa gidan su Adam, rumaisa har da ɗan tsalle za su je ta ga Sabir.
Sai dai rumaisa ta yi ta mamakin ganin layin duk kashin dawakai, duk da abun mamaki bane, amma yanayin wurin ya nuna an yi wani sha'ani a wurin.
Yanzu babu wanda yake yi wa rumaisa shamaki da shiga sashen ammi, sai dai ta jira ta ce wurin ammi suka zo, ak shiga da su sashen Ammi.
Ko da ammi ta ga rumaisa sai da mamaki ya kama ta, shekaranjiya rumaisan ta zo, yau ma kuma gata. Ammi ta ɓoye mamakinta, ta yi musu maraba, a nutse Yasir yake gaida Ammi, rumaisa kuwa ko gaisawar ba ayi ba, ta koma kusa da ammi ta ɗau Sabir.
Shi kansa takawa kallon rumaisan take, wannan nacin na ta ya fara yawa.
"Rumaisa ya mamanki"
"Tana lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana jujjuya sabir da yake bacci, wai sai ya tashi ya ganta.
Hakan kuwa aka yi sai da sabir ya buɗe ido yana miƙa, wasa rumaisa ta yi masa, ya geɓare baki ya fara murmushi.
"Laaa kun ga, yayi mini dariya, Yasir kalli yana yi mini dariya, ya gane ni, sabir ummanka ce rumaisa ka gane ni ko?"
Ammi ta ce "Ikon Allah, ko bacci bai fiye dariya ba, lallai ya ganeki, ke ya fara yi wa dariya".
"Kaii dama kewarsa ce ke damuna, na yi ta mafarkinsa, na cewa mama a rakani mandawari na duba ƴar uwarmu Hauwwaliya, na cewa yasir dan Allah ya rakoni na ga sabir ɗina"
Ammi kallonta take tana murmushi, tana jin daɗin yadda sabir ke yi wa rumaisa murmushi.
"Rumaisa baku gaisa da baban sabir ba" ruma ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ni ma bai kulani ba, yauwwa ammi wai da gaske shi yake shayar da shi?"
"Shi wa?" Rumaisa ta nuna Adam ta ce "Haka ya ce mini, wai idan aka bani sabir bani da abun da zan shayar da shi, na ce masa ana bashi madara, wai ba a bashi madara shine yake bashi abun da ake bawa jarirai wai ni idan an bani sabir me zan bashi?"
Ayshercool. [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
A razane ta waiwaya tana kallon in da aka yi mata tsawar, wasu dogarai ne su biyu suka shigo suna baza riga, shigowar ta su yayi dai-dai da lokacin da rumaisa ke gatsali da sunan takawa.
"Hattara dai yarinya, hattara 'yar talakawa, ba a furta wannan sunan hakan babu girmamawa"
Ɗayan ya juya ya kalli Adam ya ce "gaba salamun baya salamun, takawarka lafiya magajin saraki, basarake ɗan basarake jikan basarake, mai babban suna, takawa magajin takawa, motsawarka lafiya ɗan gidan giwar galadima jikar fulanin gombe, ayi mana izinin bata horon yadda ake girmama wannan suna".
Adam ya girgiza kai, tare da ɗaga musu hannu, ɗan risuna masa suka yi, sannan suka nufi sashin turaki, dan neman iznin shiga wurinsa.
Rumaisa ta ce "Yau na ga masifa, to naga annabawa ma ana faɗar sunansu, sai sunan wani mutum gama gari ace ba za'a faɗa ba, taɓ kun haɗu da wahala, wai wani ƴar talakawa sai ka ce su masu kuɗi ne".
Usman ya ce "Dan Allah maiyasa ba ka saka sun ɗagata sun zaneta da bulala ba? Wataƙila a samu hankali ya shigeta".
"Yaya usy ai ni yanzu na wuce duka yasin, sai dukan ruwa bari na je na gaya wa baba mai rawani ka ce ba zaka zo ba" ta wuce ta koma wurin turakar turaki.
Dogaran nan ta tarar a tsaye, suna jiran iso, amma ta zo ta saka kai zata shige.
"Ke! Ke hattara dai, tsaya a nan ina zaki ba ayi miki iso ba?" Ai ba ta ko tsaya ba, ta daka tsalle ta shige da gudu, ta tsaya tana jiran ko zasu biyota.
"Wallahi tura ta kai bango, abubuwan da ka ke aikatawa sun isa haka, kai ko kunya ma ba ka ji? Ka mayar da 'ya'yanka ba komai ba, sai guda ɗaya shiyasa Allah ya kasheta a wulaƙance, saboda zaluntar 'ya'yanka da kake yi, kuma idan ba ka yi wasa ba, kuma ba ka nemi afuwar yaranka ba, kaima a yadda ta mutu haka za ka mutu. Ka binne wa mutane gaskiya, kun haɗa kai da giwa da ɗanta sai rainawa mutane hankali ku ke yi, tayaya za ace wannan yar yarinyar ce ta dawo da jariri, ta yaya aka tabattar ɗan aisha ne, wataƙila ma wani abun suka ƙulla, ya haihu da wata aka kashe aisha aka kawo yaron a matsayin nata, ba abun da ba zai iya faruwa ba, tun da dai 'yar ka ce ba tawa ba, matsalar ku ce"
Turus rumaisa ta yi tana bin Hajiya saudat da ido, ta gama zubarta, ta nufo hanyar fita, cikin tsawa ta cewa rumaisa "Ke kuma ban hanya ko na yi gaba da ke" maimakon rumaisa ta matsa, sai ta tsaya tana ƙarewa ƙwayar idon mama kallo, ba tare da tsoro ko shakka ba.
Babu tsammani, rumaisa ta ji an ja ta gefe, an bar hanyar da mama zata wuce. Hajiya sauda ta yi wa adam wani mugun kallo, ta fice. Rumaisa ta ƙwace hannunta, ta ƙarasa gaban turaki ta ce "Baba, mai ya sa ka tsaya matar nan take maka masifa, kai ba sarki bane ba? Ai ba a ɗagawa sarki murya in ji mama, haka ta ce mini kan mu zo nan"
Turaki ya ce "Yarinyar kirki, sarki a waje yake sarki, amma wani sarkin a gida bawa ya fishi power, kar ki damu zaki gane me nake nufi " ya kalli Adam ya ce "Takawa, Biliyaminu nan sun kawo saƙon 'ya ta, ba sai sun ganni ba, na ta ne a kai mini ita har gida, Allah ya yi miki albarka".
Rumaisa ta ce "To baba dan Allah ka saka baki ya bani ɗana sabir, kaga na gaya maka anty aisha ta bar mini shi wallahi, amma ya ƙwace mini shi, kar na kai shi kotu ne a ga kamar ban kyauta ba, kuma ina ganin girmanku kai da mamansa, amma da wallahi nima kotu zan kai shi wurin alƙali, wata a unguwarmu ta taɓa bawa mama labari wai a kotu an ƙwato mata ɗan ta daga wurin mijinta an bata"
Turaki ya girgiza kai tare da murmushi ya ce "Subhanallah, ba za ayi haka ba, ai mu yanzu mun zama 'yan uwa, za a duba lamarin in sha Allah, saƙonki yana mota Allah ya tsare".
Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce "To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi Allah ya sa ka zama sarki, ka zama shugaban ƙasa baba" Sunkuyar da kai turaki yayi, yana rife fuskarsa da rawani, dan sha'anin na rumaisa ba ya ƙarewa.
"Wuce mu tafi ina da wurin zuwa" Adam yayi maganar a kausashe.
"Ai ko ba ka ce ba zan tafi, ba sai ka kaɗani kamar wata akuya ba" ta yi maganar tana ficewa waje.
Tun da ta fito usman ke cigaba da aika mata harara ko ta ina, amma ta yi kamar ba ta gani ba, haka suka fita suka hau motar takawa.
Suna tafe a hanya, babu wanda ya kula rumaisa a cikinsu, usman ya ce wa Adam "Ina ga idan muka ƙarasa titi ka ajiyemu, sai mu samu abun hawa mu ƙarasa gida".
Adam ya girgiza kai ya ce "A'a zan kai ku gida, akwai kaya ma, ba zai yiwu in ajiyeku a hanya ba" daga haka suka ɗan shiga taɓa hira suka cigaba da tafiya.
Tafiyar su takawa babu daɗewa, Samha ta dawo, har ta shiga ɗakinta ta canza kaya ta fito, ba ta ga gilmawar mama ba, dan haka ta bita ɗaki. Ta iske mama na ta ƙananun maganu, da mita.
"Mama, wai baki san na dawo ba? Ke da waye ki ke ta mita haka ne?".
"Ba dole na yi mita ba, ubanku na nema ta ƙarfin tuwo ya mayar da ni mahaukaciya".
"Ohh mama, kullum cikin case da Alhaji, yakamata ku daina zuwa yanzu".
"Ke dalla rufe mini baki, mai za a fasa? Ai yanzu aka fara ma ba ayi komai ba, na rasa abun da yake shiryawa da shi da adam, sai ɓoye-ɓoye suke yi, da rainin hankali wata shu'umar 'ya ya kawo masa, wai ita ta dawo ɗan wurin aisha daga hannun 'yan bindiga" Cikin rashin fahimta samha ta ce "Yan bindiga kuma, wasu 'yan bindigar kenan kuma? Ba a can in da take karatun aka ce ta haihu ba? To meya kawo ƴan bindiga ban gane ba".
Hajiya Sauda ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ke, adam wani abun yake shiryawa, aisha ba wani a ƙasar da taje karatu da ta mutu, a hannun'yan bindiga, da suka yi garkuwa da ita, ta haihu ta mutu a wulaƙance ko gawarta ba wanda ya gani, waya sani ko shi ya cinyeta ko ya kashe ta yayi tsafi da gangar jikinta".
Cikin rashin fahimta samha ta ce "Mama kin yi wa kwanyata dabaibayi da zantukkanki, na gaza fuskantar ko da guda daga ciki, ki yi mini bayani gwari-gwari. Ƴan bindiga ne suka bi ta can suka sace ko kuwa?".
Nam mama ta fayyacewa samha komai, duk da gargaɗin da turaki yayi mata a kan hakan.
Salati samha ta yi, tare da tafa hannuwa cike da tsananin mamakin sarƙaƙiya da ruɗanin lamarin, a fili ta ce "Oho musu, ko ma dai yaya ne, a wannan karon nasan babu abun da zai hanani mallakar takawa".
Sheƙeƙe mama ta kalleta ta ce "Wai ke samha wace irin mara zuciya ce ne?, Au ke yanzu duk abun da ya faru da ke a baya, da irin cin kashin da yayi miki baki haƙura da batunsa ba?"
"Dan Allah mama karki ce komai, wallahi ina son sa haryanzu kuma abun da ya faru, ya riga ya wuce, dan Allah kiyi haƙuri ki bani goyon baya a wannan karon na auri adam dan Allah"
"Kin ga tashi ki je, ina da abun yi yanzu".
Samha ta haɗa hannayenta biyu cikin magiya ta ce "Please mama".
"Na ji, amma jeki yanzu, ki bari na yi tunanina" Samha ta tashi ta bar ɗakin mama, tana ta nazari da zancen zuci a kan abun da maman ta gaya mata.
Nusaiba ce ke ta bawa iman labarin rumaisa, da abun da ya faru ɗazu da suka zo, zasu je gidan turaki. Iman ta ce "Allah sarki, na ji ina son ta tun ban ganta ba, ai mu duk mai son waninmu muna son shi".
Nusaiba ta ce "Ke kin ganta, wallahi yarinya ce sosai, dan ba ta kaimu ba ma ko kaɗan, na yi mamakin yadda ta iya tsira da sabir".
Iman ta ce "Ai babu mamaki a cikin lamarin Ubangiji, babu abun da bau iya ba".
"Gaskiya ne, amma wai ya maganar uncle J ne, kun kuma magana da shi?"
Haushi ne ya kama iman ta ce "Dan Allah ki rabu da ni da wani uncle J"