Kanwar maza 3 Complete - Chapter 7
Kanwar maza 3 Complete Chapter 7: Kanwar maza 3 Complete Chapter 7. "Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da…
3,346 words
"Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da bibiyarki, ina son nema miki mafita ne, idan ya je ya biyo ta saman fa kamar yadda ya gaya miki?"
Iman ta ɗan yi jimmm sannan ta ce "Bakomai, Allah ya fishi, mu bar maganar nan sai wani lokacin*.
Lura da yanayin yadda iman ba ta son zancen, ya sanya Nusaiba jan bakin ta ta tsuke.
Rumaisa kuwa bayan kayan takaicin da ta turawa su usman, suna tafe a mota tana yi musu waƙe-waƙe, tayi wannan waƙar ta saki ta kama wata, gashi galibin waƙoƙin na indiya take yi, sam ba ta san ma me suke faɗa ba, kawai dai tana yi ne, kuma cikin ikon Allah daga usman har takawa ba wanda ya tanka mata har suka ƙarasa gidan rumaisa.
Usman ya kalli Adam ya ce "Mun gode ƙwarai da gaske Allah ya saka da alkhairi".
Adam ya ce "Bakomai, ni ne da godiya ai".
"Hmm ai Yakamata in ƙara ma da baka haƙuri, a kan abun da rumaisa ta yi, ka yi haƙuri dan Allah" Adam yayi Murmushin gefen baki ya ce "Kar ka damu, akwai saƙonta a mota amma, bari na buɗe booth ɗin"
Ruma buɗe motar tayi, ta ruga da gudu cikin gida tana kwaɗa sallama.
Kaya ne fal a booth ɗin Adam, da wanda ammi ta bawa rumaisa da wanda turaki ya bayar a bata.
Usman ya ɗauka ya yi wa Adam godiya suka yi sallama ya ce a gaida mama.
Ko da ya shiga gidan, rumaisan ya tarar har ta tuɓe kayanta tayi ɗai-ɗai wai ta gaji.
"Dan ubanki ni bawanki ne? Da zaki bar ni da kwaso miki kaya dan baki da kunya?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ganin irin kallon da yake yi wa rumaisa ya sanya sanin cewa akwai abun da rumaisa ta yi.
"Usman, ya aka yi ne? Kun je ɗin?"
"Eh mun je, amma ba ta sauya zani ba, ta yi iya shegen na ta da ta saba"
Mama ta kalli rumaisa ta sake kallon usman ta ce "me ta yi?"
Nan ya gaya mata iskancin da ta din ga yi, mama ta girgiza kai ta ce "Wai rumaisa me bawan Allah nan yayi miki da ki ke yi masa wannan rashin mutuncin? Duk jan kunnen da na yi miki ba ki ji ba kenan?"
"Mama na faɗa komai fa"
Usman ya ce "To amma meye na cewa sai mun fita, a matsayin sa na mijinta yafi kowa buƙatar sanin meyafaru da ita".
Mama ta ce "Meyasa baka kama mini ita ka zaneta ba".
Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ai kin san wasu lokutan sa'a ce da ita, daga zuwanmu ta dinga zuba tana yi wa dattijon shishshigi tana ce masa baba, aikuwa ya dinga biye mata, saboda sakarci har da ci masa abinci a gabansa"
Huzaifa da yake banɗaki yana jin hirarsu, yana fitowa ya ce "Sai ka ce mayya daga zuwa baƙunta ki hau cin abinci"
Aikuwa ta ce "To zigazigi wutar maƙera, mai zuwa lahira da ƙoƙon dambu waya kasa da kai gwanin na iya".
"Kin rufe mini baki ko sai na taushe shegen bakin naki"
"Wallahi mama ni ban ci abinci ba, wannan abun na kayan gara mai kamar kashin nan da suga shi kawai na ci".
A fusace mama ta ce "Ni rufe mini baki, bera kawai" haka ta koma ta tura baki tare da jin haushin yadda kowa yake caccakarta.
Adam sai da ya fara biyawa yayi sallar la'asar, yana komawa mota ya tarar da missed calls ɗin Bashir.
Bin kiran yayi, bayan bashir ya ɗaga sun gaisa ya ce masa akwai issue, su haɗu a wani wurin cin abinci bayan sallar isha'i. Adam ya amsa masa, ya yanke shawarar fara zuwa gida, kan lokacin sallar isha'i sai su haɗu da Bashir.
Ko da ya je gida, Ammi ta din ga tambayarsa yaya suka yi, da fari basarwa yayi, da ammi ta matsa ya gaya mata cewar rumaisa ba ta yi magana a gabansa ba sai da ya fita.
Ammi ta yi shiru ta ce "Wai ni anya Adam babu wani abu a tsakaninka sa yarinyar nan ƴar tsamar da ku ke ta yi yawa, ta rainaka da yawa".
Ya girgiza kai ya ce "Ni ban santa ba sai a dalilin abun nan da ya faru, dan haka ni babu komai a tsakanina da ita"
"To, amma ina kyautata zaton akwai wani abu mai muhimmanci a bakinta, tun da taƙi faɗa a gabanka".
"Haka nake tunani nima, amma zan koma wurin turaki, sai mu yi magana".
"To shikenan, Allah ya yi jagora"
Ya amsa da amin.
Kamar yadda suka shirya, suka haɗu da Bashir a wurin cin abinci, ya tambayi adam mai za a kawo masa ya ce ba ya jin yunwa. Bashir ya ce "A'a ba zai yiwu ba, sai ka ci abinci ko na koma da labarin da na zo da shi".
Da ƙyar adam ya yarda a kawo masa chips, bashir ya din ga yi masa hira, tare da gaya masa ya kusa komawa abuja wurin aiki. Adam dai bai iya tankawa ba, jira yake kawai ya ji me Bashir zai ce masa.
"Wai ni kuwa ya ake ciki da maganar binciken da ka ke yi ne, na mutanen nan mutane hukuma fa suke jira, su ji sakamakon binciken ku, gashi wa'adin da kwamitin da gwamnati ta kafa ya cika ya wuce, amma ba su ce komai ba, kaima kuma kun yi shiru.
Adam yayi ajiyar zuciya ya ce "Bashir, sawun giwa ya take na raƙumi ai, ƙasar da ba ta damu da halin da al'ummarta suke ciki ba, tayaya zan cigaba da wahalar da kaina, a hukumar tamu ma kana gani sun rabu biyu, wasu suna goyan bayanmu wasu ba sa yi, a ƙasa kuwa talakawa ne kawai suke supporting ɗinmu. Ni yanzu hankalina yafi karkata ga binciko wanda suke da hannu wurin sace matata, dan a jikina nake jin na jikina ne".
"Kenan kana nufin zaka fito ka cewa duniya sace matarka aka yi, bayan an gama jita-jitar a ƙasar waje ta zo haihuwa ta mutu?"
"Bashir dole hakan zan yi mana, ba zan bar mutuwar aisha ta tafi a banza ba, ko da haka yana nufin zubewar kimata ne a idon duniya".
Bashir ya jinjina kai, ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ya ɗan daddana sannan ya miƙawa adam.
Adam ya karɓa ya fara dubawa, shafin wata jarida mai suna ciki da gaskiya ya buɗe masa. Yana shiga ya ci karo da hotonsa, tittle ɗin labarin aka rubuta dara ta ci gida. Shahararren jami'in tsaron nan na farin kaya, mai jagorantar wata tawaga da ta zama babbar barazana ga manya ɓarayin ƙasarmu, ko kuma dai ace, shugabannin da yake yi wa sharrin sata, wato Adam Sharif Galadima. Kwanaki kaɗan bayan kamala zaman makokin mutuwar mai ɗakinsa, An bankaɗo wani babban al'amari game da shi, in da lamarin mutuwar matarsa ya sha ban-ban da abun da aka sanar game da rasuwar ta ta, ashe ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da mai ɗakinsa, har ta haihu a hannunsu, daga ƙarshe ta rasa ranta. A wata majiyar kuma, aka ce da sanya hannunsa a yin garkuwa da matar ta sa in da ya kasheta yayi tsafi da gangar jikinta, kwatsam wata yarinya ta zo da jariri a zuwan ɗan matarsa ne, duk dan a ɓatar da hankalin mutane, da tunaninsu daga kan zargin shi wannan zaƙaƙurin bawa da yake jin cewa ya fi kowa gaskiya da adalci, masu bibiyarmu ko menene ra'ayinku game da wannan labari?!
Hannun adam har rawa yake yi a lokacin da ya kammala karanta labarin, wani irin wahalallen gumi ya din ga tsatstsafo masa, ya aka yi maganar nan ta fita? Waye ya yi masa wannan yankan bayan?. Jiki na rawa ya ajiye wayar, ya miƙe tsaye, jin kansa ya fara sarawa, yana neman rasa nustuwarsa, bashir ya tashi zai yi masa magana, amma tuni adam ya sulale ya bar wurin.
Kafin ya cimmasa, ya hau motarsa yayu mata key, ya fice daga restaurant ɗin da gudu.
08081012143 [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: Paid book ne ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce "A'a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba"
Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam.
"Amma dai ammi ai ni ban taɓa ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima ƙirjinsa babu komai"
Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya ɗauke daga kan maganar.
"Ammi" ta faɗa a hankali.
"Na'am umman sabir"
Rumaisa ta washe baki ta ce "Wayyo daɗi, ammi na ji daɗi, Allah ya amsa dukkanin buƙatinki, na fili da na ɓoye ya biya miki buƙatunki na alkhairi, na ji daɗi da ki ka kirani umman sabir"
"Amin rumaisa, in dai kin ji daɗi, ina son ki din ga saka baban sabir a addu'a, Allah ya biya masa buƙatunsa".
"To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu'a ba dan halinsa ba"
"Subhanallah, meye da halin nasa?"
"Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne"
Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.
Ammi ta ce "Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane".
"To ni dai saboda ke zan yi masa addu'a kawai"
"Yauwwa rumaisa, maƙiya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba ɗan sa bane ba"
Ruma ta waro ido ta ce "Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala'i, to shi kuma yayi shiru" ta yi maganar tana ƙare masa kallo.
Sai kuma ta sake cewa "To shine yayi kuka da aka faɗi haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?".
"A'a ba kuka ya yi ba, addu'a dai zaki din ga yi masa"
Ruma ta ce "Taɓ, ammi kin san wani abu?".
Ammi ta ce "A'a".
"Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake ƙanwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ƴan unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faɗa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko.....
Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa "Bari mu tashi mu tafi".
Ammi ta girgiza masa kai, ta ce "Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir"
Ta sake gyara zama ta ce "Tun da na fuskanci ƴan unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaɗai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala'in da na gani a hannun 'yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaƙa da ita ka nemi shaida ka kaini kotu. Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na ɗauka, ai tunda na gane ƴan unguwa sun gane lagona su kai ƙarata gida mama tayi mini faɗa na fetsare, ka kai ƙarata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ƙarata aka tambayeni na yi in ce eh, zaɓi ya rage a kasheni ko a barni da rai. Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi ɗin, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai ƙara, ko kuma tun da ɗan sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faɗi yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya ɓata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai".
Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaɓa kayan ta.
Ammi ta ce "Waii, rumaisa an gaisheki, ban taɓa ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya ƴan bindiga suka iya zama da ke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba ƙarya ammi. Ni fa tun da ga kano aka ɗaukemu da ƴan bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taɓa ba sai ƴan bindiga sun yi maka izini, ni na je na ɗauki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.
Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faɗa a gabana ba, na ce idan na kuɓuta sai na faɗa suka ce kona faɗa a banza, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba ƙaƙƙautawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuɓuta ni da sabir"
Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce "Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?"
Rumaisa ta ɗaga kai ta kalli adam, sannan ta ce "Na manta sunan garin"
Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taɓo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce taƙi magana.
Ruma ta yi wa sabir kiss, ta miƙawa ammi shi ta ce "Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba".
Ammi ta ce "To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuɗin mota".
Ruma ta ce "A'a muna da kuɗi, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daɗi da zuma da nono, da kilishi na gode sosai"
Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.
Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce "Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?"
"Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita".
Ammi ta ce "No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaɗai, kar ka yi ƙoƙarin lallai sai an yadda da kai"
Ya numfasa ya ce "Ammi wannan shirmenta ne kawai na ƙuruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya ƴar ƙaramar duniyar ƙwaƙwalwarta, bari na tafi masallaci ".
Ammi ta ce "Shikenan Allah ya taimaka".
Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.
Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ƙafar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida. A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faɗa a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.
Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare. Jabir ya ce "Ka gama jan ajin ka neme ni kena?"
"Jan ajin me fa?"
"Ai ka fini sani, ka ce zamu haɗu amma na yi ta kiran wayoyinki ka ƙi ɗagawa"
Adam ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba, kaɗaici nake buƙata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa".
Jamil ya ce "Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri"
"Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaɗawa a media dan a ɓata mini suna"
Jamil ya ce "Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun ɗazu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?"
"Ba ni da isasshen lokacin da zan ɓata wurin ƙoƙarin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani ƙorafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu" yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faɗa.
Jabir ya waro ido ya ce "Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da ɓata maka suna?"
"Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da ƙoƙarin wanke kaina, za su cigaba da ƙoƙarin kaini ƙasa, idan na tsaya a kan ƙafata na cigaba da karɓar duk abun da za'a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta"
Jamil ya ce "Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye"
Adam ya ce "In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni"
Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.
Jabir ya ce "To, bari mu ga zuwa yaushe wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora"
Adam ya amsa da Amin, ya miƙe ya ce "Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna".
Jamil ma tashi yayi ya ce "bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku".
Jabir ya ce "To Allah ya bamu alkhairi"
Kamar yadda Jamil ya faɗa, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa. Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta ƙaraso, hannunsa ta ja ta ce "Mu je motarka mu yi magana" bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga. Shiru ne ya ɗan ratsa, daga bisani ya ɗan numfasa ya ce "Ina jinki"