Kanwar maza 3 Complete - Chapter 8
Kanwar maza 3 Complete Chapter 8: Kanwar maza 3 Complete Chapter 8. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil,…
3,352 words
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki"
Jamil ya ce "Haka ne, ina saurarenki".
"Yaya jamil game da takawa ne"
Ya dubeta ya ce "Takawa again, me kuma ya faru?".
"Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai kaɗai zaka fahimci halin da nake ciki"
"Wai ke samha ba zaki ƙyal adam ba kamar baki da zuciya? Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?"
Kamar ta fashe da kuka ta ce "Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil"
Jamil ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zan fara yi wa adam ɗin maganar na ji mai zace"
Da sauri ta ce 'A'a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen"
"To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan"
"Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?"
'dole ki yi haƙuri, lokaci ya ɗan tura kaɗan"
"To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida " ya jinjina mata kai, ita kuma ta buɗe motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.
Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta ɓangarensa yaƙi cewa kowa komai, kuma yaƙi magana da kowane ɗan jarida. A yau babu tsammani, mai girma turaki ya karɓi baƙuncin wambai da misalin ƙarfe tara na dare. Turaki yayi mamakin ganin ɗan uwan nasa a wannan lokacin, amma ya ɓoye mamakinsa, ya karɓe shi.
Wambai ya ce "Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba"
Cikin rashin fahimta, turaki ya ce "Meke nan kake nufi?"
"Maganar rasuwar ƴar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?"
Turaki yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen"
"Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba ɗaya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?"
Turaki ya girgiza kai ya ce "Na san mai ɗakina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda maƙiya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha".
"Turaki kana nufin goya masa baya wurin ɓoye laifinsa, dan me za a ce a ƙasar waje ta mutu a ɓoye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan ƙasar nan da kawo ƙarshensu, ai gashi shi zasu kawo ƙarshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da ƙarya. Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba'in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan ɗauka a kan sa ba zai yi muku daɗi ba. Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba ƴarka ba wane irin abu ne haka?"
Turaki ya ce "Da Adam da A'isha, duk tsatso ɗaya ne, kuma ƴaƴanmu ne, dukkansu.....
Bai ƙarasa ba, wambai ya ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Ba nasiha nake buƙata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake ƙoƙarin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba"
Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.
Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.
Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.
Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da ɗalibai suka din ga yi mata barka da arziki na kuɓutowa daga hannun ƴan bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda ƴan bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita ƙi ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha. Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida. Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu ɗan wake, suka kewaye suna ci suna hira.
"Ruma ina yaya Aliyu ne?"
Ruma ta kalleta ta ce "Meyasa ki ke nemansa?".
"A'a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba"
"To meye haɗinki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan daɗi kina bani"
Waro ido habiba ta yi ta ce "Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka ɓata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida".
Ruma ta kwashe da dariya, ta ce "Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma"
"Shawarar me" habiba ta yi maganar tana suɗe hannunta.
"Mutumin nan da ya ƙwace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in karɓo ɗana?"
"Wai ƙwace jaririn suka yi gaba ɗaya to saboda me?"
"Saboda wulaƙanci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya ƙwace mini shi. Habiba kin san in da kotu take? Ƙararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai ƙara kotu alƙali ya bata ɗan ta ba, to nima kotu zan kai shi".
Habiba ta ɗan yi shiru ta ce "Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu"
"Na sani, ai ba wasa zamu je ba, ƙara zamu kai".
Habiba ta ce "To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je".
Ruma ta yi murmushi ta ce"Amma na ji daɗi habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani ɗa na, bari na tafi gida" ta miƙe suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.
Idan har da wanda za'a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na ɓoye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al'umma haƙuri na ɓoye haƙiƙanin gaskiyar abun da ya faru.
Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da ƴan jarida, ya wanke adam.
Ayshercool. [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
Masifa mummy take kamar ta ari baki, duk ƙoƙarin da ta yi, amma turaki lokaci ɗaya ya watsa komai.
Takawa ma mamaki ne ya kama shi, da ganin abun da turaki ya ce, ya wanke shi ya ɗau laifin, bai jira komai ba ya tafi gidan turaki. Bayan an yi masa iso ya shiga sun gaisa da turaki, ya dubi turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai, na ga abun da ka gayawa manema labarai, amma ni yakamata na ɗau wannan laifin na magantu ba kai ba".
Turaki ya murmusa ya ce "A'a mu ɗin ne dai yakamata, wambai ya zo nan ya nemi mu sanya ka fito duniya ka bayar da haƙuri, a kan abun da ya faru, wai sunan masarauta na neman ɓaci saboda kai, hakan ya sanya ni na bayar da haƙurin, kar ka ji komai"
"Amma Allah ya taimake ka..."
Turaki ya girgiza wa adam kai ya ce "An rufe wannan babin, ina ƴa ta?"
Adam ya ce "Wace ƴar ta ka?"
Turaki yayi murmushi ya ce "Ƴa ta yarinyar da ta kawo jikana, rumaisa"
Adam ya ɗan tsuke fuska ya ce "Tana gidansu"
"Allah sarki, duk lokacin da aka ganta, ace muna gaisuwa, Allah ya ƙara mata lafiya" turaki yayi maganar yana murmushi, yana tuna lokacin da rumaisa ta zauna a gabansa tana ta zuba shirme son ranta.
Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa. Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja. Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu. 'kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka ɗauka, ta kai ka ta baro' wata zuciyar ta gargaɗe shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.
Maganar da turaki ya fito ya yi, ta ƙara yamutsa hazo, kowa da abun da yake faɗa, yayin da hakan ya ƙara tunzura wambai, turaki ya ƙara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.
Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba kaɗan ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Wata irin ƙishirwar son ganin yaron ke damunta. Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli kuɗin makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.
Ta san kuɗin hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta saɓi hanya da ƙafafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali. Tun da sanyin safiya, har rana ta ɗaga ta fara jin zafinta sosai a jikinta. Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba. Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya ɗauke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.
Sai dai da ta ƙarasa, tana zuwa ƙofar gidan, security suka tare ta.
Ta kalli wanda ya sha gabanta ta ce "Wucewa zan yi"
"Ki je ina?" Ya tambayeta.
"Ciki mana wurin ɗana, ko ba ka gane ni ba ne?".
Ya ce "Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?"
Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"
"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"
"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani ɗana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"
"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"
Wata irin zuciya ta turnuƙo rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani ɗa na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate ɗin.
Tare gate ɗin ɗaya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"
"To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga"
Gaba ɗaya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.
Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, ɗaya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"
"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta taɓa zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"
Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ƙofar gidan, sanye da ƙanan kaya, kunnensa ɗaya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ƙiba abunsa, kan ya ƙarasa gate ɗin rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta riƙe rigarsa tana kuka.
Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka karɓe mini yarona? To ka shiga ka ɗauko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"
Ɗaya daga cikin security zai yi magana, ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"
Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na ɗebo maka ƴan sanda, ko kuma tun da kai ma ɗan sanda ne, na san haɗa baki zaku yi, alƙali zam je na gaya wa, kuma ka bani ɗana ba zan sake zuwar muku gida ba"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga ɗan na ki, sakar mini rigata".
"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta ƙara riƙe masa riga, suka nufi gate ɗin.
"Ranka ya daɗe, Yallaɓai ya ce kar a sake bari ta shiga".
"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"
Ya girgiza kai, suka buɗe gate ɗin, suka shiga, sai da suka zo ƙofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.
Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.
Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.
Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.
Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"
Ta ƙarasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ƙafa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da ƙyar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ƙanan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan". Tayi maganar tana kallonsa.
Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta ɗaya, jin ta ce da ƙafa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.
Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"
"Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?".
"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.
Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi haƙuri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.
"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".
"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wulaƙanta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"
Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.
Ammi ta riƙe hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wulaƙantaki a kan sabir, sabir ɗanki ne, ki yi haƙuri zan ɗau hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"
Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar ƴar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.
"Kiyi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wulaƙanki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".
Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwaɗayi". Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ƙuruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.
Ta ce "Ai na baki haƙuri, kuma na gaya miki zan ɗau mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai" da ƙyar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata shaƙa ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.
Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.
Rai a ɓace Ammi ta ce "Ban ji daɗin abun da ka yi ba ƙwarai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?"
Cikin ladabi Adam ya ce "Tuba nake, ba na yi haka ne domin ɓata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu"
Ammi ta ɗan yi shiru ta ce "Ban ƙi ta taka ba, amma a ƙuruciya irin ta ta, da irin ƙaunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a ɗauki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wulaƙantata ko cutar da ita ba. Tana da matuƙar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wulaƙanci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba".
Ya risuna ya ce "In sha Allah"
"Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ƙafa ita kaɗai"
Ya jinjinawa ammi kai.
Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce "Ammi zan tafi".
"Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida" rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce "Ba'a jayayya da umarnin giwar galadima" Ammi ta yi mata maganar cikin gargaɗi, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.
Adam ya miƙe yayi gaba, rumaisa ta durƙusa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.
Kamar yadda ransa yake a haɗe, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.