Kenza eBookz

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 9

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 9

Kanwar maza 3 Complete Chapter 9: Kanwar maza 3 Complete Chapter 9. "Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa,…

3,367 words

"Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ƙaraso.

Ta ƙarasa tana ɗan haki ta yi murmushi ta ce "Ashe ba kai ne shi ba?"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.

"Na zata shine da na ganka ɗazu, idona ya rufe sosai da ɓacin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane"

Yayi murmushi ya ce "Kin ga jaririn naki?"

"Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. Ɗa na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ƙwace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan"

"Wace aishar?"

"Kai baka san ta ba? Kai ba ɗan nan gidan bane?".

"Eh ɗan nan gidan ne, amma bana ƙasar jiya da daddare na dawo".

"Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na kuɓuto da ƙyar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ƙwace ɗan kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?"

Mahmud ya yi murmushi ya ce "Bai kyauta miki ba gaskiya"

"To kai baka taɓa zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga ɗan nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke"

"Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni ɗan Mummy ne".

"Wacece kuma hakan?" Ta tambayeshi tana ɗan gyatsine fuska.

"Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sauƙi"

Cikin fitsara rumaisa ta ce "Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan taɓa manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga ɗana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir" tana maganar ta yi gaba tana murmushi.

Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa ɗan sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.

Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karkaɗewa motar ƙura.

Ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?".

Ta kalleshi ta ce "Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi haƙuri. Ya nuna mini karamci saboda ni ɗan adam ce bai koreni ba ɗazu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so". Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa daɗi ko kar ta yi masa bai shafeta ba.

"Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina ɗaga miki ƙafa albarkacin yaron nan da kuma ƙuruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap ɗi na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana buƙatar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za'a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana buƙatar sake ganinki a kusa da shi" yayi maganar cikin kashedi.

Cak ta tsaya ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.

Ayshercool [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

"Meyasa baka ɗau maganar mahaifiyarka da muhimmanci ba, har kake yi mini wannan barzanar a bayan idonta? Ko ba komai tana tausayina wataƙila ta san me nake ji game da sabir" ta saka idonta cikin nasa, wanda hakan ya sanya musu faɗuwar gaba a tare, cikin jarumta da ƙarfin hali ta daki motar Adam ta ce "Idan har bayan mutuwar anty aisha an yi umarnin a kashe sabir, na ɗau duk wani riski Allah ya dafa mini na kuɓutar da shi, kana tunanin bayan kuɓutarmu ne wani zai haɗa kai da ni a cutar da yaron da na ɗaukarwa babarsa alƙawarin kula da shi? Wace irin zuciya ce a jikinka?"

Ma'aikatan wurin ne suka tunkarosu, amma adam ya dakatar da su, saboda rumaisa ta faɗi wani abu mai muhimmancin gaske.

"Kai ka san abun da ya haɗani da kai ai tun farko, kuma ban janye abun da nace ba, ba zan taɓa janyewa ba kuma. Sabir idan ka ga dama ka kai shi bangon duniya, ka yi duk abun da kake ganin ya dace. Mara imani ban taɓa tsanar abu a duniya ba kamar kai, ko ƴan bindiga da na zauna a hannunsu wataran suna mutunta ni. saboda furucin da ka yi a kaina, wai a haɗa baki da ni a cutar maka da ɗa, na gode daga yau ba zan sake zuwar muku gida ba in sha Allah, in dai ni ƴat halak ce mama ce ta haifeni su yaya usman ne yayyena ba zan sake zuwa gidan nan ba" ta ɗauko maganar tiryan-tiryan ta ƙarasa da shirme, tana kuka ta juya ta nufi gate ɗin.

Jikin Adam yayi sanyi, tabbas a abubuwan da ya faɗa sun ɗan yi tsauri.

Da sauri ta fice tana kuka, ta bi hanya, dan ko za a kasheta ba zata hau motarsa ba, wata irin wutar ƙiyayyarsa ke cigaba da azalzalar zuciyarta, duk wanda zai yi yinƙurin rabata da sabir, to babban maƙiyinta ne.

Sashin Mummy ya shiga yana ɗan tunani, lokaci-lokaci kuma yana murmushi. Mummy ta kalleshi ta ce "Bani labarin wannan murmushin, dawowar nan ta yi maka daɗi kenan?".

Ya sake yin murmushi ya ce "Wata yarinya na haɗu da ita da zan shigo, na fita yanzu na kuma ganinta, gaba ɗaya zubinta da character ta abun dariya".

Mummy ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce "Ko ka fara soyayya ne?"

Ya ce "Soyayya kuma? Yarinya ce ƴar ƙarama fa, amma abubuwan da ta faɗa ya bani mamaki, wai ita ce ta dawo da jaririn nan da ake ta surutu a kai, na aisha turaki, wai ta zo ta ga ɗan ta, ya ce idan ta zo kar a sake bari ta shigo. Yarinyar mugun ƙarfin hali ne da ita, maganganunta sam ba irin na shekarunta bane, akwai shirme a maganganunta, amma akwai hikima a cikin shirmen na ta. Ba abun da ya bani mamaki kamar yadda ta iya riƙe rigata cike da ƙwarin gwiwa take tuhumata a zaton ta wancan gayen ne".

Cikin rashin fahimta Mummy ta ce "Wai kana nufin wadda ta zo da jaririn aisha a gidan nan? Ka ce yarinya ce ƙarama?".

"Eh, wannan ai sai kun fi ni sani ku da kuke cikin gidan, ni ban san komai a kan zancen ba, kawai dai na san yarinya ce dan ta yi wutar duniya, ba za ta fi shekara sha uku ba, a nawa tunanin"

"What! Kana nufin ƴar shekara sha uku ce ta zo da jaririn da ake cewa na adam ne? Amma rainin hankalin mutanen nan yayi yawa, ta yaya ƴar shekara sha uku za ta kuɓuto da jariri daga hannun'yan bindiga".

Mahmud ya ɗage kafaɗa ya ce "I don't know".

"Amma tsaya, yarinyar tana nan haryanzu ne, ina buƙatar in ganta"

"Mummy ki ganta ki yi mata me? No need dan Allah ki daina shiga sabgoginsu da bin diddigin sai kin san abun da suke ciki, shiyasa suke raina ki, ki ƙyalesu su ji da matsalar su" yayi maganar yana miƙewa. Bin sa da ido mummy ta yi, amma da ta iya cewa komai ba. Sai mamaki da sake jinjina lamarin giwa da ɗanta saboda zallar goge hadda, wai ƴar shekara goma sha uku ce ta kuɓuto da jariri.

Rumaisa kuwa tafiya kawai take yi tana kuka, dan ta ji zafin maganganun takawa matuƙa. Ta kusa titi kawai ta ji an danƙi hannunta, a fusace ta ɗaga kai, amma kan ta yi wani yinƙuri ya fara janta, a fusace ta fara kokowar ƙwace cikin tsiwa take cewa "Ka cikani me na yi maka?".

Ba zata manta fuskar sidi ba, wanda suka taɓa kamota suka kaiwa takawa. Bai saurare ta ba, ya buɗe bayan motar takawa ya jefata, ya rufe motar, Adam ya sauke glass ɗin motarsa ya jinjinawa Sidi kai, sannan ya rufe glass ɗin motar ya fara ja.

"Malam ka tsaya in sauka daga motar nan, bana son ka kaini gidan ka sauke ni bana so" banza yayi mata ya cigaba da tuƙinsa.

"Na ce maka ka sauke ni, wai kai meyasa ka ke mini haka ne? Ka sauke ni"

Ganin bashi da niyyar kulata, ya sanya ta fara kiciniyar buɗe motar, amma ta ji ƙofar motar a rufe gam.

Adam a zuciyarsa yake jinjinawa masifa da taurin kan rumaisa, da a buɗe motar take haka za ta buɗe ta ce za ta fita. Ganin ba za ta iya buɗewa ba, ta zauna ta cigaba da kuka tana ƙanan maganganu.

Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, mamaki take yi a ina ya san gidansu?.

Ko da yayi parking bai fita daga motar ba, sannan kuma bai buɗe motar ba, rumaisa ta hau kiciniyar buɗe ƙofar motar, amma ta ji a rufe.

"Ka buɗe mini in fita" ta kai masa duka dan takaici.

Danna wayarsa ya hau yi, na wani ɗan lokaci sannan ya buɗe motar ya fita. Sai dai ya kulle rumaisa a ciki, bai buɗeta ba, bubbugawa tayi ta yi, amma ya fita ya tsaya ya ƙi saurarar ta.

Aliyu ne ya fito daga cikin gida, yana ganin Adam ya faɗaɗa Murmushin sa, ya ƙaraso suka gaisa, rumaisa ba ta iya jin mai suke cewa, amma sun ɗan jima suna tattaunawa sannan ya buɗeta ta fito tana wani basarwa.

Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, sannan ya ce "Sai ki wuce ki shiga" ko a jikinta, ta yi gaba dan ita yau ko za'ayi mandaƙo da ita tun da buƙatar ta ta biya shikenan.

Wani wawan burki ta yi, da ta ga mai sunan Baba a ƙofar ɗakin mama, yana gyara botirin hannun rigarsa.

Wani irin mugun yawu ta haɗiye, ta fara takawa a hankali kamar hawainiya. Fuskarta ƙarara ta bayyanar da tsantsar tsoro da razanin da take ciki.

Aliyu ne ya yi sallama da shi da Adam, mai sunan Baba ya amsa ba tare da ya ɗago ya kallesu ba, sai ma ja da yayi da baya ya basu hanyar shiga falon mama. Bai kula Adam ba, shi ma bai kula shi ba, suka shiga ɗakin mama da sallama, da gudu rumaisa ta bi su tana waiwayen mai sunan baba.

Mama ta faɗaɗa murmushinta tana yi wa Adam barka da zuwa.

Ya ce "Tuba nake mama, tun da aka bar asibiti ban samu na zo na gaisheki ba, abubuwa ne sun yi mini yawa ƙwarai da gaske"

Mama ta ce "Babu komai, ya gida ya hajiyar take? Ya kuma mai gidana".

"Duk suna nan lafiya, ta ce a gaishe ki"

Rumaisa ta kalleshi a ranta ta ce "Kalleshi, kamar ba yanzu ya gama wulaƙanta ni ba, har da shigo mana gida ya zauna, yana washe baki dan ace masa mutumin kirki".

Mama ta ce "Rumaisa duba kitchen, ki kawo masa ruwa" sai da ruma ta ji kamar ta yi fitsari, saboda kar ta fita mai sunan baba ya kamata.

Sai da ta leƙa ta ga baya nan, sannan ta shiga kitchen da gudu, ta ɗauko pure water ɗaya, ta dawo ta tsaya a kan Adam ta miƙa masa.

Kallon da mama ta yi mata ne ya sanya ta rasa in da za ta sanya kanta, dan gaskiya a tsorace take sosai.

Da ƙyar ta sake komawa, ta zubo ruwan a wani ƙaton baho, kusan guda goma sha biyu, ta ɗauko ta zo ta dire masa.

Aliyu ya ce "Wai ke wace irin taɓaɓɓiya ce ne? Ya zai yi da wannan ruwan babu plate a kitchen ki ɗoro masa ko huɗu ne, sai ki yi wannan shirmen?"

Adam ya ce "Rabu da ita, yanzu zan tafi nima, daga gida nake Alhamdilillah a ƙoshe nake, dama ammi ce ta sanya na dawo da ita gida,kamar yadda na kira Aliyu a waya na yi masa bayani, maimakon ta je makaranta ta taho cikin gari ganin sabir, kuma ta tafi a ƙafa wanda akwai hatsari a hakan, mussaman da yanzu yakamata ace tana ƙarƙashin tsaro sosai, na kawota ne a ɗan ƙara sanya ido a kanta sosai, a kula da ita kar a sake bari ta zo, idan tana buƙatar ganinsa ayi waya za a kawo mata shi. Sannan makarantar su ma yakamata ce, sun bibiyi abun da ya sanya ba ta je ba yau, kamata ya yi ace sun kira gida"

Aliyu ya ce "Makaranta suna iya ƙoƙarin su, ita ce dai kamar ƙanwar aljanu, saboda rashin ji da kafiya, duk abun da idan ta san za ta yi ayi magana shi take yi. Kuma makarantar ta gwamanti ce, suna da ɗalibai sosai babu lallai ma su san ba ta zo ba"

Mama ta ce "Ai idan ba ta je ɗin ba suma hutunsu ne, mun gode sosai da sosai, in sha Allah za a sake kulawa, hakan ba zata sake faruwa ba".

Ran rumaisa ya ɓaci, yadda su mama ke ta ce mata fitinanniya a gabansa, salon ya sake rainata.

Babu wanda ya san da shigowarsa, sai gani suka yi yayi sama da rumaisa yayi waje da ita, tana ihu. Adam ya bi mai sunan baba da kallo, ganin yadda ya ɗaga rumaisan kamar ya ɗaga kara.

Aliyu ya ce "Madalla, dama tun da ki ka dawo baku haɗu ba, ai gara ya tuna miki yana nan".

Adam ya ce "Amma wannan ɗaukar da yayi mata, kar ƙashinta ya samu matsala, tun da ba ta gama warwarewa ba"

"Da zai samu matsala, da ba ta kawo yanzu ba da hannun a jikinta, zata yi facing displine master". Da fari ruma tana ta kiran sunan mama, tana bashi haƙuri, amma da yayi mata wata irin tsawa tuni ta nutsu ta rufe bakinta.

Ruwa ya saka ta janyo, ta cika wani ƙaramin bokiti, ya ɗora mata a ka, ya tsayar da ita a rana, ya sanya takalmansa ya fice.

Hirarsu suka cigaba, babu wanda ya sake bi ta kan rumaisa, duk da mama a cikin ranta, ta ɗan ji tausayin ruman.

Sai da suka ɗan taɓa hira, a kan abubuwan da suka din ga yawo a kansa a social media, haka nan yake yabawa da nutsuwar mama, tare da jinjina mata raino da tarbiyyar wannan zaratan mazan su bakwai itakaɗai, kuma wasunsu na karatu wasu suna sana'a a yanzu haka. Hakan ya sanya yake jin tana da wani experience na rayuwa, a ɗan haɗuwar da suka yi a asibiti, da yadda take magana yanzu, ya sanya ya fuskanci surutun rumaisa yana da nasaba da rayuwa cikin mazan nan, wanda kowa da kalar tunaninsa da kuma irin halinsa. Ga uwa uba yadda mama ke bayanin wasu abubuwan da ya shafi ƙasa, sai ka ce wata babbar mai kwalin karatu ce, amma wai kawai jin radio da bibiyar labarai ya sanya take sanin abubuwa sosai a kan lamarin ƙasa.

Adam ya yinƙura ya ce zai tafi, mama ta ce "Gashi ka zo bamu ko sauke abincin rana ba, kuma ka ce wurin aiki zaka koma, Gadanga ko ka kusa sauke shinkafar?"

Aliyu ya ce "A'a da saura, kuma ga miya ma, ko wani abun za a sayo maka?"

Adam ya ce "Kai ka ke yin girki? Ka iya girki?" Yayi maganar cikin mamaki, dan shi ko gas tsoron kunnashi yake balle girki.

Aliyu ya yi dariya ya ce "Ko in zo ammi ta ɗaukeni kuku ne? Ba abun da ban iya dafawa ba"

Dariya suka yi, Adam ya tashi ya ce "Kar ku damu, a ƙoshe nake sai anjimanku".

Mama ta ce "A'a tsaya"

Ta shiga ɗakinta ta fito da tasar turare, da kuma dabino lubiya a leda ta ce "Ga turare ka shafa, dabino kuma a bawa hajiya"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull