Kenza eBookz

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 32

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 32

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 32: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 32. Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya…

3,374 words

Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban ɗaki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa. Hakan ya ja mata baƙin jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "Ƴa ta bintu".

Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.

Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.

Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. Saɓanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance ɗan wannan ɗaki da wancan. Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haɗa Sharif da Bintu faɗa, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.

Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita. A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.

Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban ɗaki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.

Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taɓa ko ɓari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ƴan uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.

Ana haka mai babban ɗaki ta rasu, wanda hakan ba ƙaramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.

Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ƙaƙƙautawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ƙuruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna. Aikuwa ta ƙwafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ƙiyayya.

Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.

Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi ɓari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba. Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani.

Sai a karo na huɗu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ƙarshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ƙular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin ɗauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.

Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi ɗa namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗorata a kan yaron nan. Watanninsa shida, yayi zazzaɓin wuni ɗaya ya rasu.

Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ƙyar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake ɓari, sannan ta samu ciki ya zauna. Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faɗar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.

Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.

Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya ɓulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.

A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata ƴar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.

Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ƙaruwa, amma yana jin tausayin Bintu.

Ƙannen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faɗa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da haƙuri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faɗan ta rage faɗa.

Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.

Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matuƙar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu ɗaya da galadima.

Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama, tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.

A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ƙalubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba ɗaya ya canza mata.

Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama biƙi ba ta al'ada sai dai ta ga ciki.

Ayshercool. 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ƙuduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita kuma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai.

Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taɓa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki.

Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu.

Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ƙarami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba.

Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karɓar mata ɗan ta, amma ya ce ta yi haƙuri, da ita da Jamila duk ɗaya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taɓa haihuwa ba.

Rashin ɗan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ƙarshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame.

Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta.

Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.

Laila ce ke satar jiki, ta ɗaukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta shaƙu da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan ɗaukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.

A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ƴar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar ɗan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.

Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin ɗan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.

Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.

Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.

Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da feleƙe, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata haƙuri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.

Ammi ba ta taɓa tanka masa ba, dan a lokacin ta miƙa wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da riƙon abun ta, gefe tana zuwa makaranta.

Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka za a tsallake ƴaƴan bintu na ta su yi sarauta.

Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ƙunci tana baƙin ciki, kwanan ƴar uku ita ma ta mutu.

Nan ta din ga yaɗa cewar, Bintu ce take bawa bokaye ƴaƴanta su cinye, shi ne wannan karon ta haɗa da tata ƴar, tun da dama ƴar gidan malaman tsubbu ce.

Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ƙaunar ɗan sa takawa ba, sannan ya na ɗaukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai ɗau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata ɗan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba. Iyayen ammi suka yi ta bata haƙuri, da nuna mata dama aure, sai an yi haƙuri ibada ne, ta yi haƙuri da ɗan nan Allah ya bata wani.

A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karɓi abun sa, al'umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naɗa sarki a 'yaƴan sa, sai aka naɗa ƙanin sa. Hakan ba ƙaramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taɓu. Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naɗa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban ɗaki kan ta rasu, shi yana ɗan ƙarami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar ɗan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban ɗaki da marigayi, dan haka shi duk ɗaya ne a wurinsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ƴa macen, bayan sun gana ɓata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba.

Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba. Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huɗu da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su ɗaya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haɗu kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka.

Baba Uwani ta yi ta bata haƙuri, ta ɗauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faɗa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuɗi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ƙoƙarin ta wurin kyautatawa baba uwani.

Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ƙanwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiɗen da yake yana cewa "Maraba da kai babana, abun ƙaunata kuma magajina, galadima ɗan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai"

Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam ɗin dariya, wani dunƙulallen baƙin ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran ɗan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu. Tun daga nan ta fara turawa Mahmud aƙidar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba.

Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.', za su koma mahaifarsu.

Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta shaƙu da Ade da ƴan rigar, kamar danginta.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still ƴa ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so.

A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban ɗaki ta wancan lokacin da ta riƙe shi, ita ma ba ita ta haife shi ba.

A wannan karon, shi ma Sharif ƙarara yake nuna son Adam, saboda soyayyar da yake yi wa mahaifinsa, da yadda mahaifin nasa, ya nuna masa ƙauna.

Jamila kuma ta yi alwashin rusa soyayyar nan, da cigaba da baƙantawa giwa, domin rama abun da ta yi mata, na fara auren Galadima.

Duk yadda ta so raba Mahmud da Adam, ba ta yi nasara yadda take so ba, duk da Mahmud ya fara yadda da abun da take gaya masa, sai dai duk yadda take korar Adam idan ya zo wurin Mahmud ya kasa zuciya.

Tuni Mutanen masarautar, wasu sun fara ɗauka, tare da kiran Adam magajin galadima, har da masu ce masa galadima ƙarami, ko kuma magajin takawa, idan ƴan kan zagi suka yi masa wannan washin, haka galadima zai ta yi musu kyauta.

Hajiya Lubabatu ta samo musu wani hatsabibin boka, malam na kan dutse, suka je wurin sa a kan suna son a nakasta Adam, yadda ba zai moru ba, kuma a saka gaba da ƙiyayya tsakaninsa da Mahmud, yadda wuta da ruwa ba zasu jitu ba, haka suma sannan a saka wa galadima tsanar Adam.

Bokan ya ce "Sai an kai masa Adam, saboda ya san aikin da zai yi a kan sa, sannan a taho masa da jinin Mahmud a sirinji.

Ta koma gida, ta saka galadima a gaba, wai tana son ta je garinsu, za ta tafi da Adam, galadima ya ce bai yarda ba, ta haɗa baki da malaman makarantarsu Adam, ta je ta ɗauke shi a makaranta, aka shaƙa masa wani abu ya suma, suka tafi da shi wurin boka, tare da jinin Mahmud.

Bokan ya zuƙi jinin Adam, ya haɗa da na Mahmud, ya zuba wani abu a ciki, jinin ya rabu biyu ɗaya ya yi baƙi, ɗaya ya yi ja, ya mayar da jinin jikin Adam, ya bata sauran jinin, ya ce ta yi girki da shi, ta bawa Mahmud da galadima su ci, ya raba su.

Ta ce ai ba iya nan take so ba, so take a haɗa shi da ciwon, da zai nakasa, nakasa ta har abada, da ba zai yi sarauta ba.

Nan ya yi wani ƙulumboto, ya saka wani abu, ya huda wuyansa, ya zuƙi jinin Adam, ta wuya, ya zuba a wani abu, ya ce "Ramin da na yi a wuyansa, ta nan aljanar za ta din ga shan jininsa duk shekara, sai dai babu wanda zai iya hudat, Sannan zan yi wani abu da sauran jininsa, duk shekara za a din ga samun mahaukacin doki, ayi masa, zan haɗa laya da sunansa, wadda za a kai maƙerar da ta shekara goma, a binne, sannan zan saka wannan aljanar, ta zuba masa jinin mahaukaciyar kura a jikinsa, an nakasta shi, nakasa ta fili da zahiri, iya rayuwarsa wannan aljana za ta cigaba da kula da komai, tun da an bata jininsa, sai dai loka-lokaci, za ta din ga buƙatar wani abun" ya wassafa musu abun da za su bayar, suka bayar sannan suka tafi gida.

Ammi ta kaiwa Adam, yana bacci, wai biyo ta yi ta hanyar makarantar su, ta ga an tashi shi ne ta ɗaukko shi yayi bacci a mota. Ammi ba ta kawo komai ba, ta karɓe shi, ta yi mata godiya, sai dai tun ammi ta na saka ran adam ya tashi, har tsoro ya kamata. Sai dai bayan ya tashi ba baki, sai dai kallo.

Hankalin Ammi ya tashi, ta gaya wa galadima, hankalinsa ya tashi suka tafi asibiti aka ce lafiyarsa ƙalau, ya ce idan zuwa washegari, bai yi magana ba, za a kai shi babban Asibiti, ko ƙasar waje ne a akai shi, sai da daga haka washegarin, tunanin galadima ya sauya, ya ce wai ta ƙyaleshi shakiyanci ne.

Abu kamar wasa, sai da Adam ya yi wata tara, ba magana, ga wani irin bacci, mara kan gado, ammi ta dage addu'a, ta kai shi gidansu wurin mahaifinta aka dage da roƙon Allah, sannan ya dawo yake magana.

Gaba ɗaya galadima ko a jikinsa, ya daina nan-nan da shi, sai dai abun ka da ɗa da uba, soyayyar ba ta dishe duka ba, wataran idan ya gan shi ya na jin daɗi.

A lokacin Mummy ta haifi Fauziyya, mutane ana ta shigowa, Ammi da laila da adam, sun je ganin jaririya, Adam na ganin Mahmud, ya nufi wurin sa yana kiran sunansa.

Sai dai Mahmud ya hankaɗe Adam, sai da ya faɗi ƙasa, ai yana tasowa, sai idanunsa suka koma kamar na mahaukaciyar kura, yana wani irin gurnani, ya shaƙe Mahmud. Ammi hankalinta ya tashi, duk wanda ya je raba su, sai Adam ya cije shi, kowa ya yaƙushe shi, sai jini ya fita.

Da ƙyar Ammi ta riƙe shi ta na yi masa addu'a, ta ja shi ta tafi da shi sashinta, tana kuka ita da laila, tana tunanin menene ya samu adam?.

Sai dai haka ya wuni yana wannan gurnanin, kamar kare.

Mummy kuwa bala'i ta din ga yi, wai za a kashe mata ɗa, dama adam ɗin maye ne, ya tsotsa a wurin uwarsa, ko kuma a garin yawon bin bokaye, ɗan ta ya haukace. Magana ta din ga yawo a fada, galadima ya je har sashin Ammi, ya din ga yi mata faɗa, wai ita ta sangarta Adam, har yake yinƙurin kashe ɗan uwansa.

Halin da ya tarar da Adam ɗin sam bai dame shi ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull