Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 33
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 33: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 33. Tun daga nan, idan faɗa ya haɗa Adam da yara, sai ya burkice,…
3,330 words
Tun daga nan, idan faɗa ya haɗa Adam da yara, sai ya burkice, ya na gurnani, da cizo, idan kuma yayi cizo sai jini ya fita, wanda wannan jinin aljanar take sha.
Wani lokacin idan ana ziga wutar maƙerar nan, haka yake jin ta a cikin jikinsa, yayi ta ihu ya na fuzgar fatarsa, ko kuma idan mahaukacin dokin nan, yana dara, sai ya ji tamkar ƙashin sa ake takawa.
Idan kuwa shakara ta yi, lokacin shan jinin nan ya yi, ya din ga suma kenan, har ammi ta fitar da rai da shi.
Mummy ta din ga tsorata Mahmud a kan Adam, da sai da ta kawo, ba mai kallon wani, juya masa bayan da mahaifinsu ya yi, ba ƙaramin tsaye masa ya yi ba a ransa. Sai dai ya je ya saka Ammi a gaba, ya yi ta kuka, abun da ake yi musu da tare shi da Mahmud, yanzu sai dai ayi wa Mahmud shikaɗai, hakan ya sanya ya ƙara tsanar Mahmud!.
Roƙon Allah da neman magani, da Ammi ta dage a kai ne, ya sanya ya samu sassauci har ya koma makaranta.
Lokacin da za su shiga jss1, Mummy ta saka aka kai Mahmud boarding, aka raba shi da gidan baki ɗaya, dan yanzu galadima baya iya ƙetare maganarta.
A hankali aka ɗan fara sakin jiki da Adam, cousins ɗin sa suke wasa da shi, kasancewar makarantar su ma ɗaya. A gidan su jamil, gidan turaki wanda yake wa ga sharif, akwai ƴar sa ɗaya da ya ɗorawa so shi ma, bayan mahaifiyarta ta rasu, mai suna Aisha yake kiranta da fulani, sai dai a bayan idonsa, babar su jamil, ta tsani yarinyar, kamar ba ƴar sarauta ba, saboda azabtarwa daga yayyenta, da kuma uwar riƙonta.
Tun ana yi a bayan idonsa, aka dawo yi a gaban idonsa, ba ya iya cewa komai, wasu lokutan ranar juma'a sai Ammi ta aika a ɗauko mata Aisha, a kai mata ita, ta yi mata kitso, ta saka ayi mata lalle, tana son ƴa mace, laila kuma ta riga ta balaga.
Ana haka Ammi ta haifi nusaiba, ta din ga murna, ta samu ƴa mace, da wata salla suka je gombe, a nan yayan Ammi yake ce mata, ya wuce ta rigar su ade, ya ga kamar da mutane.
Nan da nan Ammi ta ɗau hanya ta tafi, sai dai ta je ta tarar da wata kyakywar bafulatanar yarinya, da ciki.
Suka gaisa da Ammi, take tambayarta, ina su Ade.
Yarinyar ta ce "Ade kakata ce, sun yi gaba, ni daga yaye aka bar ni a wurin yayan babana, to sun tashi zasu tafi can iyaka, in da tushenmu yake, ni dai ban san sunan wurin ba, to mu ma can zamu tafi, da ni da yayan babana ne, da matarsa sai maigidana, sauran ayarin da muka taso tare sun yi gaba, ni kuma na yi nauyi, shi ne aka ce mu zauna in haihu, sai mu tafi, yayan babana ya san in da suke, ina son in ga Ade, kakata".
Ammi ta ce "Allah sarki, Ade kam tana bani labarinki, ta ce mamanki ma tana wata riga tana aure ko?"
Yarinyar ta jinjina mata kai.
"To ina mijin naki da matar yayan baban naki?".
Ta ce "Sun tafi kiwo, ita kuma ta je yin itace".
Ammi ta din ga murna ta ga jikar Ade, kasancewar za su yi kwanaki a can, ya sanya kusan kullum sai ta je, har suka saba da matar yayan baban ade.
Ammi ta sha mamaki, irin yawon da fulanin nan suke da shi, sun yi sanani sun hayayyafa, sun shafe shekaru a wurin, kuma su tashi su yi wani wurin kamar wasu iskokai.
Mijin yarinyar ma, mairamu yana matuƙar girmama Ammi, su yi ta ɗaukar nusaiba suna yi mata wasa.
Ammi kar ta tafi ta bar gida, dan ƙarfin zaman na ta ma, ayi wa Adam Addu'a ne, da nema masa magani.
Bayan Ammi ta koma Kano, tana yawan yin waya, a kan aje a gano mata jikar Ade.
Sai dai aka kira Ammi, daga garin su, aka gaya mata, an kashe mijin mairamu, an kore dabbobinsu, kuma an rasa yayan babanta da matarsa.
Kasancewar ammi ba laifi, tana faɗa aji, ta saka aka kai report wurin ƴan sanda, amma ba wani labari, Mairamu ta tayar da hankalinta, a gidan su Ammi aka yi wa mijinta sutura, aka rufe shi.
Ita ba ta san kowa ba, sai mijinta da yayan babanta, in da suka baro, duka suka taso, ayari sun yi gaba sun bar su, dan su har a lokacin ba ruwansu da abun hawa, kuma ba ta san in da za aje ba, dan ta na da ƙuruciya sosai abun da ta riƙe a in da za su je kawai shi ne kan iyaka, nan ne tushensu.
Saboda tsabar damuwa, ta fara naƙudar dole, aka kwasa aka kaita asibiti, ta haifi yarinaya kyakkyawar gaske, jawur da ita.
Ammi ce ta yi mata role ɗin uwa da na uba, dan ba zata manta karamcin Ade ba.
Ta tambayeta sunan da za a sakawa ƴar amma ta ce ta saka mata duk sunan da take so.
Ammi ta ce "Ta saka mata Khadijah, sunan mahaifiyar ta, kuma ƴar ta da ta taɓa rasuwa, amma take ce mata Iman".
Ta din ga rarrashin mairamu, tana bata tabbacin, za ta yi ƙoƙari a nemo in da ƴan uwanta suke, kuma a lokacin waya sai gidan manya, balle a sameta hannun bafulatanin daji.
Haka Ammi ta din ga sintiri tsakanin kano da gombe, mahaifiyar laila da ammi ta riƙe, ta cigaba da ɗawainiya da Mairamu, dan a lokacin suma iyayen duk babu.
Sai dai har watanni uku, babu labari a kan in da ƴan uwan mairamu suke, ga ƙuriciya kuma ta yi ta fama da rashin lafiya, ƙarshe Allah ya yi mata rasuwa.
Ammi ta yi kuka sosai da sosai, ta ce sai yayarta ta bata Iman, ya ce ba zata ba, sai ta nemo iznin mijinta.
Ammi ta yi wa galadima bayani, ya ji rauswar yarinyar, kuma ya san ɗawainiyar da Ammin ke ta yi, dan haka ya ce ta ɗaukko ƴar, dan ya san soyayyar da ke tsakanin Ammi da Ade.
Ta zube har ƙasa ta din ga yi masa godiya.
Ta je ta ɗaukko Iman, a lokacin kuma ta riga ta yaye Nusaiba, ya ce ko magani za ta yi, da ruwan nono zai dawo ta shayar da iman, yayarta ta ce kar ta shayar da ita, ta na da ƴaƴa maza, ba ta san me gobe za ta yi ba. Haka ta haƙura, ta ɗaukko iman, ta zo tana bata madara.
Kowa ya ga Iman sai ya tankata, saboda tsananin kyan da take da shi, gaya jaririya, amma gashinta irin na larabawa, mai tsawo.
Nan ma mummy ta samu na yi, wai Ammi saboda jaraba, an yarda ƴar shege ta ɗaukko wai tana so, kamar ƴar jari bolan ƴaƴa, ɗan kowa ma sai ta ɗaukko ta ce za ta riƙe, da ganin kyan wannan yarinyar, an san shegiya ce.
Aikuwa aka yadda, wasu lokutan ammi har mamaki take, yadda sirrikanta ke fita.
Jamila ta hurawa galadima wuta, a kan lallai ya sa ammi ta mayar da ƴar nan, duk dan ta cusa wa Ammi baƙin ciki.
Ya kuwa je ya samu Ammi ya ce bai yarda da riƙon ƴar ba, sai da Ammi ta dangana da wurin sarki, da mai babban ɗaki a kan su saka baki.
Mai babban ɗaki ta ce "Dan Allah idan ma ƴar tsintuwar ce, ita ta na so, ƴar ta yi mata kyau Tubarkallah".
Da ƙyar galadima ya amince, bayan mai martaba ya yi masa ta tas, a kan abubuwan da yake yi.
Iman ta fara girma, ga fari ga kyau, ga uban gashin nan, kullum tana tare da laila da su nusaiba, ga Aisha idan ta zo, amma muddin ta sake suka haɗu da Mahmud, Fauziyya ko ruƙayya, to tabbas sai ta yi kuka, saboda cin zali.
Sai dai duk da haka, ƴaƴan jamila na shiga wurin Ammi, kuma ba zaka ce ba nata bane ba, sai dai suna tsoron laila, dan suka yi mata rashin hankali ubansu take ci, duk da ana yi mata gorin ba gidan ubanta ba ne ba, ta kan ce musu, Jamila ma an riƙeta ba a gidan ubanta ba, dan ita har da Mummyn ma yi take yi, duk yadda Mummy ta so ta saka Galadima ya kori laila abu bai yiwu ba.
Adam kuwa yau fari, gobe tsumma, kusan kullum cikin rashin lafiya, idan ciwon nan ya tashi kuwa, haka zai ta burgima yana ihu, yana neman abun da zai riƙe ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta.
Sashin Ammi ya zama wurin faɗi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting ɗin sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin ɗan ta ya kashe musu ƴa ƴa, amma yaran sun riga sun shaƙu da ita.
Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faɗa, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata ɗa, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faɗan da yake yi masa.
Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai.
Adam ba ya jin daɗin hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro.
Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ƙaddarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ƙauna sama da su.
Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daɗin rayuwa da su, a haka ɗan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ƙasar.
Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taɓa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam ɗin.
Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taɓa ɗaga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaɗowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faɗan sunan sa ba.
A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ƙyae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haɗu da ciwon zuciya da ƙuruciyarta.
Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faɗi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ƙarshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba.
Ɗa da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ƙauna, a baya, Mahmud ma ya ɗimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar.
Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka ɗaga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima.
Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, ɗan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karɓe ɗan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaɗaitawa ƙawarta Lubabatu, ɗan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ƙiyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murɗaɗɗen hali na mahaifin su.
Adam yana girma ciwo yana ɗan raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida.
Ya shaƙu da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ƴar ƙaramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida.
Gefe guda, Samha ta ƙallafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam.
Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ƴan uwanta ke nunawa aisha ƙiyayya, ganinta suke kamar ba ƴar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce 'yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya ɗaukkota, ko Ammi ta aika a ɗauko mata ita.
Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake muguwa kamar Mummy, saboda waɗan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da ɗaya ba, idan uwar ɗa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa riƙon ɗan sa, babu wanda zai bawa riƙon ɗan sa.
Tun Samha tana ɓoye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba.
Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ƙaninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ƙular da ita sosai da sosai.
Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta roƙe shi ya nemawa Adam auren Aisha.
Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin ɗan ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani.
Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ƙi ya mata ita gaba ɗaya.
Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ƙuduri aniyar ko da bala'i sai ta auri Adam.
Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Ayshercool. 08081012143
What's app only please Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya ɗan samu sauƙi, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ƙafar dama.
Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matuƙar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ƙaunarsa, kusan halinsa ɗaya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai ɗa'a da ladabi.
Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi wurin matayensu, tana ɓata Ammi da ƴaƴanta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu.
Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga ɓari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ƙannensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ƙyaleta ba da sharri, da haɗata da Turaki, wai ba ta ɗauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima.
Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen haƙora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.
Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank ɗin sa ya fi na Jamil.
Akwai aiki da ƙoƙari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.
Bashi da aiki bankaɗa, da tonawa mugwayen ƙasa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ƙasa ɓarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ƙi.
Ba ƙaramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ƙi bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma yaƙi sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ƙi ji. Ya koma ya bankaɗo wata tawaga, da suke yi wa kansu laƙabi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ƙungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na hayaƙi, an rubuta THE SMOKE.
Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ƙishin walili zai tsayar da ɗan sa takarar senator, shi kuma za a ɗauke shi vice president, su yi takara, da ɗan takarar da zai tsaya shugabanci ƙasa. Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.
Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haɗa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da ƴan jarida da suke da burin yi wa ƙasa aiki saboda Allah.
Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna riƙo.
Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ƙwafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.
Saurayin babbar ƴar Mummy, Surayya, Wambai ya haɗata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.
Ƙarshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.
Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ƴaƴan mai martaba, ɗaya shi ma ya liƙe Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.
Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.
Iman ba ta da wata ƙawa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar ɗakinta Aisha matar takawa.
Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taɓa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.
Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son ɗan ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.
Wambai ya yi ta faɗa ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.