Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 60
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 60: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 60. Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir. Sosai…
3,355 words
Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir. Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ƙwarin gwiwa. A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi. Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce "A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke ɗin. Amma ina ga kamar yadda madam ta faɗa, ka yi ƙoƙarin gano wanda suka yi maka maƙarƙashiya, amma hukunta su sai Allah".
Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba.
Adam kansa abun ya ɗaure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ƙalau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba.
Gashi bai bai gama da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a buƙaci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin.
Sai dai cikin ƙudura ta Ubangiji mai kyauta da ƙari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, yaƙi kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba.
Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ƙular da ita, ta fara zaginta.
Mama ta ce "Ba zaki rufe mini baki ba?"
"Mama baki san me nake ji ba ne"
Mama ta ce "Dan ubanki ƴaƴa biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba".
Ammi ta ce "Maman rumaisa ki yi haƙuri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daɗi"
Aka naɗo jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa ɗaya sak da Adam.
Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce "Mimi, baby ya buɗe ido" yayi maganar cikin yarinta.
"Boy babynmu ya mutu"
Ammi ce ta karɓi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura.
Ƙarfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho, ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ƙarasa asibitin jikinsa duk a sanyaye.
Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa.
Ya durƙusa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?.
Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ƙarasa.
Ammi ta miƙa masa jaririn, ya karɓe shi ya buɗe zanin, kamar mai bacci, kamar sa ɗaya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne.
Ya miƙawa ammi shi, ya ce "Allah ya sa mai ceto ne" suka amsa da amin.
Mama tuni ta tashi ta bar ɗakin, ya ƙarasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta.
Kawai ta fashe da kuka ta ce "Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi"
Ya rungumota jikinsa ya ce "Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daɗi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi haƙuri ki daina kuka"
Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai.
"Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani" rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai.
Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune.
Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taɓrar da ruma take ba ta damunta.
Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman "Ina mai sunan baban?"
"Ƙarfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi"
Ammi ta ce "To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake ɓallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba.
Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda ɗinkin da aka yi mata.
Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a ɗaukko mai kula da ita. Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba. Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti.
Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!.
Ayshercool. 08081012143.
*WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK*
Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can.
Mai sunan baba ya ce "Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba"
"Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba"
Ba tare da wani ɓata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba.
*** Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda biƙi, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru. Tana zaune a ɗakinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu.
Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai buƙatar ta gyara jikinta sosai.
Rumaisa ta ce "To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir".
Laila ta ce "Yaya bacci yake yi bai tashi ba"
Ruma ta ce "Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?"
"Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daɗin zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daɗin da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna"
Ruma ta ce "Sai wani yabon sa ki ke yi"
"Dole in yabe shi mana, dole a sarawa mama, yaranta gaba ɗaya masu tarbiyya ne da nutsuwa, ke ce kawai mara ji"
Ruma ta ce "To nima papa yana yabona, yana sona a haka"
"Ai shi dama ba zai ga rashin jin da ki ke ba. Yauwwa mimi ya hatsaniyar gidan kuwa ta lafa?"
"Ina fa lafawa, suna can suna cigaba da tashin hankalin su, ni ina nan ina fama da kaina, da mutuwar ɗa na, mummy sun watse da Hajiya Lubabatu, ashe Jabir lalata suke shi da ruƙayya, abun duk babu daɗi mahmud dai ya rufe shi"
Laila ta ce "Lamarin gidan nan sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa mu dace kawai mimi, bari na bari ki huta"
"To anty laila na gode sosai"
Tana gama wayar, Gwaggo ta shigo da kunun kanwa, ta ce ruma ta sha.
Ruma ta ce ita wallahi ta gaji da wannan kunun kanwar, gudawa yake sakata.
"To idan baki sha ba nonon ya zube ki huta ai, gyara ki nake son yi, na bayar da dawa ma a niƙota in sheƙa miki tuwo, ga yajin daddawar ki nan"
"Gaskiya gwaggo ba zan ci tuwon dawa ba, in haihu ki bani wani tuwon dawa taɓ. Kunu kuma ina da sauran sabayata, yaushe zan ta shan kunun kanwa cikina yana ciwo".
"Kya ji da shi dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya"
Haka rumaisa suke faɗa da gwaggo, komai sai ruma tayi raki.
Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa taƙi yadda ayi, ta maƙale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi.
Takawa ya shiga ɗakin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce 'Mimi meyasa ki ke da gardama ne?"
"Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar ɗa na, ko na ruwan zafi?"
"Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je" yayi maganar yana miƙa mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa.
Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaɗan.
A banɗakinsa ya haɗa ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai.
Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya ɗauki magungunan ta ya bata ta sha.
Ya kalleshi ta ce "Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?"
Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata.
Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ƙasar.
Ya ce "Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah"
Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaɓi.
Gaba ɗay tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa ɗan, amma akwai wani pain ɗin na daban.
Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi haƙuri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace.
(0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haɗin maman Khadija na sabaya 0703 777 7442)
Da safe har wurin ƙarfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita.
Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faɗa "Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ƙwari ba, dama gashi kin ƙi bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ƙarata".
"Ni fa gwaggo ke ba kya lallaɓa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ranƙwashi na ki ka yi"
"An ƙi a lallaɓa ki, ku ƙara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baɗala ba" haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta.
Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raɗaɗi da ɗacin abun da iyalinsa suka aikata. Wanda ya ɗora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haɗi, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so.
A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus.
Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta roƙi a saka baki a bayar da belin jamil, kowa yaƙi.
Samha ba ta taɓa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba.
Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan buƙatar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa'anin yin ba ne ba!.
*** Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ƙanin nata sam bashi da ɓaci.
Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin.
Babu ɓata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan.
Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce "Adamu ne?"
Umar ya ce "Kin gane shi? Kin san Ammi?"
Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Na san Bintu, bintu ƴar ɗakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ƙaunar ji"
Mahmud ya ce "Kin tuna jikar ki mairamu?"
Ade ta fashe da kuka, ta ce "Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ƴan fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ƙaryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ƴan uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro ɗan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan".
Mahmud ya ce "Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?"
Ade ta ce "Waye kuma ima?"
Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin.
Jiki na rawa ta ce "Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta riƙe ƴar mairamu?"
Mahmud ya ce "Ƙwarai kuwa wannan mijinta ne ma?"
Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka.
Ta ce "Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba ɗaya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari" nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da haƙuri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su.
Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daɗi da malam umar ya zamana mijin jikarta.
Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.
Nan da nan riga ta ɗauka, an samu ƴar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.
Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ƴar mairamu.
Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman. Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta ɗaya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?"
Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman ɗin da amm...
Ade ta ce "Wane mutum, da ƙafar nan tawa ko a ƙafa zan taka na je kano, na ga Bintu"
Alhaji Aminu ya ce "Da wace ƙafar? Ƙafa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba ɗaya "
Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haɗa kai da ƴan bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.
Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce "Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala"
Dariya yayi ya ce "Ai shikenan"
Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce "Yau ba zaki bishi ba?"
"Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri"
Gwaggo ta ɗora hannu a ka ta ce "Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faɗa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan"
Ruma ta ce "Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faɗa mini, dan sai ya bi ba'asi"
Ta samu ɗan kwali ta kwaɗawa ruma a baya ta ce "Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina".
** Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce "Su shirya, su haɗu a wuri guda, suna tafe da manyan baƙi zuwa kano shi da mai sunan baba.
Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma yaƙi gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen.
Ammi ta ce "Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai"
Mahmud ya ce "Baƙi ne masu muhimmanci, har mimi muna buƙatar ta a wurin" Ammi ta din ga mamakin wane irin baƙi ne kuwa haka?".
Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ƙarasowar ta su, aji wani irin baƙi ne, ya ce idan sun iso a kira shi.
Ammi ta sanya aka yi ta ɗorawa da saukewa, duk da bata san wane irin baƙi ba ne, amma akwai buƙatar ayi girki.
Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye baƙin, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba.
Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce "Hero suwaye baƙin?"
Ruma ta gwale baki ta ce "Su hero manya"
Takawa ya ce "Umar kun bar mu a duhu kai da ƙaninka, ku muke ta jira"
Yayi murmushi ya ce "Yanzu za su shigo" ya kalli iman ya ce "My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga baƙin nan fa" yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu. Kunya ce ta kamata ta ce "To me zan baka?"
"Saniya zaki sai mini" gaba ɗaya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce "Mai sunan baba kun sauka? Ina baƙin?"
Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya riƙo ade, sai ƙannenta guda biyu.
Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce "Ade" da ƙarfi.
Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta ɗago ta kalli Ammi ta ce "Bintuna"