Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 101

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 101

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 101: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 101. Nasir yana jinjina tsabar taƙama da jin kan Viper, shi ba…

4,499 words

Nasir yana jinjina tsabar taƙama da jin kan Viper, shi ba kowan kowa ba, sai a yanzu ya gane in da yake tunanin sanin Abbu, kamarsa ɗaya da Viper, sai ya lura irin tafiya ɗaya yake yi da mahaifinsa, sai dai shi harkar daba ce ta ƙarawa tasa tafiyar taƙama.

Major na jin sallamar baƙi a falonsa, ya miƙe cikin farinciki yana yi musu maraba, sai dai yayi tururs da ya gansu tare da Bashir.

Fuska babu walwala ya ƙarasa karɓar su.

Alhaji mu'azzam ya yi gyaran murya ya ce "Duk da baƙin naka, wasu sanannu ne, wasu kuma baka sansu ba, wannan shi ne mahaifin Al'amin Viper, wanda ya auri 'yar uwar Nabila, wannan kuma Al'amin, wannan kuma baban su Nabila, kamar yadda ka sani. Mun zo ne a tare da shi, mu sake baka haƙuri a kan abin da ya faru, dan Allah kayi haƙuri ya wuce, ko dan samun nutsuwar ita yarinyar".

Major ya kalli Alhaji mu'azzam ya ce "Ka kuwa san abin da yayi mini? Har duniya ta naɗe ba zan manta ba. Babu ƙoƙarin da ban yi ba na yafe masa na manta, amma na kasa, mussaman idan ina tuna yadda yarinyar nan ta mutu da sunansa a bakinta, duk tsananin kunyar bafulatana, amma ba ta son laifinsa, sosai take nuna son mijinta, amma ta wulaƙanta mini yar uwa ya tozarta ta, ya barota a dajin Allah ba ta san kowa ba sai shi. Na bashi yarinya amma ya aurawa ɗan daba ya kasheta" Alhaji mu'azzam ya ce "Ashsha! A bar tuna baya major, shi fa yaron nan da ka ke magana a kai, ga shi a zaune a gabanka, ga mahaifinsa ba zai ji daɗin ka din ga jifansa da irin wannan maganganun ba. Ni nan ni na fara neman auren Jauhar, Allah bai yi ba ta auri Aminu, amma zan iya ce maka, a duniya jauhar ma da ƙaunar mijinta ta bar duniya, saboda yar uwatta da na aura, kan yi zancenta da rayuwar gidanta. Kawai sharrin yan siyasa ne da rashin ji da yayi tsautsayi ya faru, idan zan gaya maka gwagwarmaya da wahalar da ya shiga bayan mutuwarta, to a matsayinka na uba, sai ka zubar da hawaye. Nabila dai ita ce da ta shiga rayuwarsa ta taimake shi, Al'amin ba ƙashin yarwa bane ba, amma ka yi binciken ka kaima, kar laifin mahaifinsu ya shafe shi dan Allah"

Abbu yayi gyaran murya ya ce "Ranka ya daɗe, ita duniyar guda nawa take, duk da Alhaji Bashir yayi mini bayanin komai, bai ishe mu darasi da mamaki, ace duk da ka nesanta yaran biyu, da juna Nabila ta afka rayuwar Al'amin ba tare da ta san waye shi ba? A duniya ina gaya maka idan mutum bai yi dacen mace ba, sai addu'a kawai. Ka ganni nan, da sanya hannayena bibbiyu, a lalacewar ɗa na, bayan mutuwar mahaifiyarsa na auri ƙawarta, ina saka ran ta kula mini da 'ya'ya, amma a ƙarshe saboda makirci irin na ɗiya mace, sai da ya zama tsakanina da Al'amin babu jituwa, kamar maƙiyina, dan Allah a bar tuna abin da ya wuce"

Bashir ya ce "Maitama na san duk abin da zan gaya maka, ba yadda zaka yi da ni ba, amma a irin yadda na auri Chubaɗo na fara rayuwa da ita, ka san ban aureta dan na cutar da ita ba, ƙaddara da makircin mata, ya sanya abin da ya faru ya faru, tun da ko da na aureta ka san ba mutumin banza ne ni ba. Na haɗu da sharrin mata ne da suka yi mini sihiri a kan mairamu, a gaban Nabila suka din ga faɗar abin da ya faru, amma dan Allah ka yi haƙuri, ka yafe mini"

"Ba wani sihiri, dama mutum ya tara mata ya zauna ba addu'a, ba neman tsari, ba dole kowane abu ma mata su yi wa mutum ya kama shi ba"

Abbu ya ce "A dai yi haƙuri, ya wuce dan Allah"

"To yanzu me ku ke so?"

Baba ya ce "Ina son ka bani Nabila ne, haryanzu ina kewar Jauhar, dan Allah ka bani 'ya ta"

Wani mugun kallo ya yi wa Bashir, ya ce amma dai ba ka san me ka ke cewa ba ko? Nima da na rasa 'yar uwata haƙuri nayi na faullawa Allah. Kai Alhaji mu'azzam yaya muka yi da kai, ba cewa ka yi da ta kammala shari'a zaka dawo mini da 'ya ta ba? Kawai sai ku zo mini da wani zancen daban, Nabila tun da Allah ya haɗaku, duk lokacin da take so, ta je ka ganta, amma wallahi ba zan bayar ba".

"Maitama kar mu yi haka da kai, ka bani 'ya ta ka tausaya mini mana"

"Ita ma ka kaita su yi mata asirin kenan? Ba zai yiwu ba wallahi, kuma kai Alhaji mu'azzam, kai mun yi da kai zaku dawo mini da 'ya ta ai".

Alhaji mu'azzam ya ce "Haryanzu da sauran issue ne, amma za ta dawo, tun da ai haryanzu tana zuwa nan ɗin"

Abbu ya ce "Amma dai muna fatan ka yafe masa, a manta da abin da ya faru a baya?"

"Ya wuce, mantawa kuma wannan ba lallai ba, 'ya kuma a ƙyale mini 'ya ta, Allah ya sa mu dace"

Alhaji mu'azzam ya ce "Hakan ma Allah ya saka da alkhairi, kuma tun da ka ce duk lokacin da take so taje taga mahaifinta, Allah ya saka da alkhairi ya huci zuciyarka"

Major ya numfasa ya ce "Amin"

Baba ya tashi ya ƙarasa ya miƙa wa Major hannu, ya ce "Ina ƙara neman afuwarku da ahalinku, a kan abin da nayi muku, ku yi haƙuri ku yafe mini"

Major kamar ya maze, ya haƙura ya miƙa masa hannu suka gaisa, Abbu ya din ga Alhamdilillah, Allah ya ƙara muku fahimta.

Viper kuwa dama tun da suka fara hayaniya, ya fice ya koma ƙofar gida.

Major ya ce "Bari na kira muku mutanen gidan ku gaisa, da mariƙiyar Nabilan"

Ya tashi ya sauka falo, ya ce "Magajiya, ki zo ga mahaifin Nabila ne ya zo, kai Nasir ina babarku, ku zo ga mahaifin Nabila da mijin 'yar uwatta ku gaggaisa"

Jikin Nasir yayi mugun sanyi, wani irin kishi da fargabar dalilin zuwan Viper da mahaifinsa ya tsaye masa.

Aka gabatarwa da Baba kowa, ya din ga yi musu godiya da fatan alkhairi.

Bayan tafiyar su, sannan Nabila ta dawo, ake gaya mata su Baba sun zo, ta ji babu daɗi rashin tarar da su, sai dai ta yi wa Abba godiya, jin cewar ya yafe wa mahaifinta, kuma ta san duk jajircewar Viper ce.

Ta samu Abba, ta din ga yi masa godiya, da nuna masa farincikinta, a kan yafewa mahaifinta da yayi.

Abba ya ce "Eh na yafe masa, amma ban yadda da maganar ki koma gidansa ki zauna ba, ban yadda da wannan ba".

Nabila ta ce "Nima dama ba zan koma can ba, amma na gode sosai da sosai da ka yafe masa".

Da daddare bayan ta yi sallar isha'i, ta kira Viper, yana ganin kiranta ya ɗaga, ta ce "Hello Vi"

"Mmm"

"Ashe kun zo gidanmu bana nan, baka gaya mini zaku zo ba, da na dawo da wuri, naga shiryawar Baba da Abbana" yayi shiru bai ce koma ba.

"Na san wannan duk ƙoƙarin ka ne, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, Allah ya jiƙan 'yar madara da jaririnta, ya baka abin da ka ke nema duniya da lahira na gode, na gode"

"Godiyar ta isa haka, nima na gode"

"Ba ta isa ba Vi, ban san me ma zance maka, da zai tabattar da irin godiyar da nake son yi maka ba, na gode sosai da sosai"

"Nima na gode sosai "

"Tom sai da safe"

"Nabila"

"Na'am"

"Haryanzu kina nan a kan bakanki ha zaki aure ni ba?"

"Dan Allah mu daina wannan maganar Vi, a wuce ta dan Allah, ni na riga na gaya maka matsayata, mu yi haƙuri da wannan maganar"

Ya ce "Ok, babu laifi" ya katse kiran wayar.

*****

Walid ya warke sarai, hannu ya miƙe, sai dai da Viper ya yi masa zancen Abbu zai ɗauke shi, a kasuwa a nuna masa harkar kasuwanci, sannan ya bashi jari, a fara maganar aurensa da Shahida.

Walid ya kasa magana yayi shiru yana kallon Viper.

Viper ya ce "Menene kuma? Ko ba wannan sana'ar ka ke so ba? Idan da wani abun da ka ke so ka faɗa, sai a san abin yi"

Walid ya ce "Anya gatan nan bai yi mini yawa ba Mai zamani? A bani jari kuma a bani auren 'ya?"

"Ware, ka cancanci fiye da haka mai laya, yanzu yakamata mu je ko wurin ƙannen mahaifinka ne, saboda su nema maka auren Shahida, ni kuma zan je Lagos ne aiki"

"Lagos kuma mai zamani, babu kai babu ɗan mama"

Al'amin ya numfasa ya ce "Tafiyata can na cigaba da aiki, ya fi alkhairin zamana a nan. Dama na yi zaton ko Nabila zata aure ni ne, amma ta ce ba ta so na, dan haka zan yi tafiyata kawai, na yi aikina na fi samun kwanciyar hankali da manta wasu abubuwan" "Viper, daga kai har Nabila kuna son junanku, kawai dai rashin fahimta ne. Kaga Jauhar a sadaka ka auret, baka san duk wata wahala da ake sha, wurin neman aure ba. Yanzu ne zaka yi fafutuka da gasken gaske, idan ba haka ba ka bari ta auri wani babu lallai ka iya jurewa"

"In biye mata tayi ta wulaƙanta ni?"

"Ba wulaƙantaka take yi ba, kai ka fara watsar da tayinta a farko, ka din ga nuna mata da farko, an ce mata ba sa mantuwa, amma ka yi haƙuri ka nemi aurenta, Abbu ya nema maka Aurenta" Viper dai yayi shiru bai ce komai ba.

*****

Major ne ya kira Nabila, ta same shi a ɗakinsa, ya ce "Yauwwa babanki ya turo mini baban yaron nan da ya auri 'yar uwakki, wai yana son ya aure ki, zasu kawo kuɗin aure, na ce sai na yi magana da ke, kina ganin kin yarda da nutsuwarsa a yanzu zaki iya aurensa?"

Nabila ta yi shiru. "Magana fa nake yi miki Arfa"

"Gaskiya Abba ni ba zan iya aurensa ba"

"Saboda me?"

Ta girgiza kai ta ce "Ni dai kawai a bar maganar nan, ka ba su haƙuri"

"To uban meyasa ki ka gayyato shi rayuwarki, so ki ke ace ni na zigaki ko?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Tashi ki je, Allah ya shiryeki" ta tashi sumi-sumi, ta tafi sai dai kuma haka kurum ta din ga jin tausayin Viper.

Sumayya ta kira take labarta mata abin da ya faru, Sumayya tayi shiru, ta ma rasa me za ta ce mata.

"Sumy ya ki ka yi shiru?"

"Nabila me zan ce miki, abin da ki ka yi zalunci ne, ya za ayi ya sakankance, yana sonki zai aureki, amma ki ce ba kya son sa?"

"Point of correction, nake son sa dai, amma ba yake so na ba"

Ƙarshe sai da suka kusa yin faɗa, suka rabu tsiya-tsiya a wayar.

Sumayya da kanta ta kira Abbu, suka gaisa ta fara bashi haƙuri, a kan abin da Nabila tayi.

"Bakomai kar ki damu Sumayya, ai macece idan ma tayi haka ba tayi laifi ba, na san halin kayana sarai"

"Abbu Nabila na ganin Ba ya sonta ne, kawai dai zai aureta saboda tana kama da jauhar ne"

Abbu ya ce "Na fahimceki, ita ma kuma haka, yanzu dai zan ba su lokaci, shi kansa ya zuciya yanzu haka yana hanyar Abuja, can aka kai shi ba Lagos ba kuma, ya ce auren ma ya haƙura, amma ta nan ɓangarenki, dan Allah ki ɗan lallaɓata, ni idan ta kama ma sai na zo da kaina, ba zan so ya tafi yaje ya zauna haka babu auren ba"

Jiki a sanyaye Sumayya ta ce "To shikenan Abbu, in sha Allah"

Ta sake kiran Nabila, tana gaya mata yadda suka yi da Abbu. Nabila ta kada baki ta ce "Dan Allah Sumayya ki ba wa Abbu haƙuri, ba wai ina ƙyamar ɗan sa bane ba, amma ina yi masa fatan alkhairi a duk in da yake, Allah ya bashi mace madadin Jauhar".

Ayshercool 08081012143

102 A ƙule Sumayya ta ce "Kina ganin hakan da ki ka yi shi ne dai-dai? A gidan uban wa ki ke tunanin zai samo madadin matarsa? Ke kin san baki isa ki ƙi aurensa ya bari ki zauna lafiya ba"

Nabila ta ce "Lafiya ƙalau zan zauna in sha Allah, kar ki damu da ni Sumy, Allah ya nuna mini aurenki"

"Nabila kar ki mayar da abin nan wasa, ya ki ke tunanin mahaifinsa zai ji, kin yi rejecting ɗin ɗan sa?"

Sumayya, wai kina ina lokacin da na din ga gwagwarmaya, ina nuna wa mutumin nan so yana wahalar da ni?"

"Ramawa ki ke kenan?"

"Da zan rama abin da Vi yayi mini, ko kallonsa ba zan iya yi ba, kawai dai ba zan aure shi bane"

"Munafuka, kina wani kiransa Vi, kina wulaƙanta musu ɗa, nan ki ka roƙi Allah ya baki kowane irin miji ne, mutum ya nuna yana sonki, amma kina wahalar da shi, zaman gidanku da wannan cin mutuncin ne da ake yi miki bai ishe ki ba, ki ƙarata"

Nabila ta ce "Bakomai, na ji na yadda"

**** Alhaji mu'azzam ne a ƙofar gidan su Hafsa, ya fi mintuna ashirin yana surutu, amma Hafsa ta yi masa banza ta ƙi kula shi.

"Hafsa" ta ɗago ta kalleshi.

Ya ce "Meyasa ba zaki yafe mini ki koma ɗakinki ba?"

"Meyasa zan koma in da ba a buƙatata? Gara na barka waɗanda kake ƙauna".

Ya ce "Na san ban kyauta ba, amma ki yi haƙuri, zan gyara kuskurena" murguɗa baki tayi, ta sake juya masa baya.

Murmushi ya yi a ransa ya ce "Komawar ki gidana ita kaɗaice mafita a garemu baki ɗaya" a zahiri kuma ya ce "Shikenan sai da safe"

Ba ta kula shi ba, kawai ta shige cikin gida ta bar shi a wurin.

Yayi murmushi ya furta mace kenan, duk yadda ake ganin girmansa da mutuncinsa a ƙasa, yana ta bin yarinya ƙarama tana wana shi.

**** Viper ne a tsaye a banɗaki, ya sakarwa kansa ruwa, a hankali ya kammala wankan ya fito, jikinsa duk babu ƙwari. Ya shafa mai, yayi shirin kwanciya bacci, gaba ɗaya abin da Nabila tayi sai cin zuciyarsa yake yi.

Yana jera kayansa a cikin wardrobe, yana tuna tarbiyyar Jauhar ce, da ta hana shi watsar da kaya ko ina, duk yadda ya ga dama, da har ta koya masa rashin son baza kaya ko ina.

Ɗan ƙaramin hotonsu ne shi da ita ya faɗo, ya durƙusa ya ɗauka ya zauna a gefen gado yana kallo. Kamaninta sun ɓaci da ita da Nabila.

Ya kalli jikinsa, ya tuna yadda komai dare idan ya gama yawonsa ya dawo, sai ta haɗa masa ruwa mai zafi yayi wanka, tun ba ya so bar ya zo ya saba, ta shafe shi da mai sannan ya kwanta bacci. Gashi ba ta taɓa gajiya da duk wata rigimar sa, sai dai idan yayi mata laifi, to fa ba ruwan wanka, balle shafa mai da tausa, hirar ma ba zata yi masa ba. Kayan shafe-shafen gyaran fatarta kuwa, wataran haka take zaunar da shi, shi ma ta shafa masa wai yayi kyau.

Ya ɗan saki murmushi ya ci gaba da kallon hoton, ya ce "Kin bar ni da tabo mai tsananin zafi a cikin zuciyata, sai wahala nake yi, ga twin sister ɗinki ta ce ba ta so na, ke kaɗai ki ke so na babyn robana" yayi maganar kamar taɓaɓɓe.

Ya nemi wuri ya kwanta, rayuwarsu ta baya na dawo masa, Addo'in kwanciya bacci, ita take yi masa idan bai yi ba, yawan yi masa ya sanya ya haddace su tsaf a kansa.

Ya tuna ranar da tana cikin yi masa addu'a, ta idar ta tofa masa, ta shafa sumarsa ta ce "Mai zamani, yaushe zamu je aski ne?"

Ba shiri ya buɗe ido ya ce "What me ki ka ce?" Ta hau dariya ta ce "Viper"

"Viper ko?" Yayi maganar yana matsa kumatunta.

Cikin shagwaɓa ta ce "Sorry yaya master"

"In sake jin ki faɗi wannan sunayen, ni da ke ne, matso to rarrashe ni na yi bacci, ki sake yi mini wata addu'ar"

"Naƙi ɗin, tun da ka ci zalina, ka san dai ka fi ni ƙarfi, amma ka matse mini kumatu"

Ya ce "Eyya, to ni zo na rarrasheki ki yi baccin "

"A'a ba na son wannan rarrashin, mun yi faɗa, yau ina farkon gado, ina ƙarshe"

Yayi dariya yana gyara kwanciyar sa, ya ce "Da shegen son jikinki, ina nan zaki mirgino ki same ni ne"

Ta riga shi yin bacci, aka kawo wuta unexpected, ya ashe ƙwan ɗakin a kunne yake, ya tattara nutsuwar sa, da hankalinsa a kanta, bacci take yi sosai, da alama baccin gajiya ne, dan har alarm ɗin ta ya buga na lokacin sallar dare, ba ta sani ba.

Ya tashi ya je ya sha ruwa, ya kashe fitilar ya kwanta, ya rungumeta a jikinsa, yana jin wani irin abu game da ita, na mamaye kowane sashe na zuciyarsa.

Cikin magagin bacci ta ce "Master"

Ya ce "Mmmm"

"Ya Allah ka shirya mini shi, Allah ka yaye masa wannan shaye-shayen, Allah kar saka ya dawo gareka yana aikata ɓarna, Allah ka bashi halal, ka bashi juriya da jarrabawar rayuwa. Allah ina son mijina a haka, Allah ka sanya yana da rabon shiriya" a cikin bacci take ganin kamar tayi salla, take ta jerin wannan addu'oin a fili.

A hankali ya dawo daga tunanin da yake yi, ya kalli hoton ya ce "Wannan ce juriyar da ki ke roƙa mini, juriyar rashin ki 'yar madara" ya ajjye hoton ya canza kwanciyarsa, yana jin yadda zuciyarsa take yi masa zafi.

Bacci ne ya kwashe shi, sai dai yau a maimakon Jauhar, da Nabila yayi mafarki, cikin yanayi na ma'aurata, ko da ya farka ya makara sallar asuba, tsaki ya yi ya tashi, tare da furta jarababbiya, ko meya kawo ta baccina"

Ta ƙarfin tsiya yake son sanya wa kansa jin haushin Nabila, amma abu ya gagara, wata irin kewarta ce ma take damunsa, gaba ɗaya tunanin mafarkin da yayi, yaƙi barin kansa.

Wato nutsuwa da kwanciyar hankali ba abin da ba ya sanyawa, a lokacin da yake cikin ha'ulai'in tashin hankali, ko kusa baya wani tunani, balle ya kwanta ya yi wani mafarki, ba ma haka ba, baccin ma ba iya yin sa yake yi ba, balle yayi wani mafarki. Yanzu kuwa hankalinsa a kwance yake a cikin nutsuwa, ya shirya ya auri Nabila da zarar komai ya daidaita, saboda ya san yana buƙatar hakan, amma lokaci ɗaya ta hau dokin naƙi, wai ba ta son sa.

Ɓangaren Nabila ma, yanzu zaman gidan major bai fiye yi mata daɗi ba, duk sun ƙara tsangwamar ta, yanzu ta fi zama a barrack, ta fi jin daɗin zaman wurin madam, sai dai kuma da an kwana biyu sai ta ji gida take son komawa.

Tana zaune ta idar da sallar asuba, ta yi azkar, ta kifa kanta tana ƙarasa azkar ɗin, bacci ya kwasheta, dan kuwa yanzu bacci rabi da rabi take yin sa, saboda tunanin halin da Viper yake ciki, tana ta addu'a da fatan Allah ya sa kar ya koma halinsa na da.

Kawai tayi mafarkin farkon haɗuwarsu da Viper, a lokacin da yake Vipern sa, tamkar mahaukaci, ya soka mata wuƙa a ciki. Ihu ta kurma ta tashi tsaye tana dafe cikinta.

Baba magajiya ce ta shigo ɗakin a razane, Abba yana daga saman benensa ya jiyo ihunta, sun saba da irin wannan ihun na Nabila wasu lokutan, amma kwana biyu tayi lafiya.

A sukwane ya saukko shi ma, ya shiga ɗakin nata, ya tarar baba magajiya ta riƙeta, sai kuka take tana riƙe cikinta, tana dubawa ko zata ga jini.

"Menene kuma?"

"Viper ne ya caka mini wuƙa, a kai ni Asibiti"

"Wane Viper kuma, kalli dai a ina ki ke?" A hankali take ƙarewa ɗakin kallo, ta kalli jikinta ta ga lafiya ƙalau.

"A garin shegen kwashe-kwashen ki, kin kwaso abin da zai hanaki bacci, bayan kwaso masu farautar rayuwarki, kin yi azkar ma kuwa?" Ta jinjina masa kai, ta nuna masa wayarta da sautin karatun Alqur'ani yake tashi ƙasa-ƙasa.

"Nemi wuri ki kwanta ki huta" ta ƙarasa kan gadon, tana ajiyar zuciya.

A ranta ta ce "Vi fushi ka ke da ni har haka?" ta lumshe idanunta, ƙirjinta na ci gaba da bugawa cike da matsanancin tsoro.

Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana ta gama shirinta, ta fice zuwa wurin aiki.

Tana zuwa ta tarar da Walid tare da Liti suna jiranta.

Cikin mamaki ko gaisawa ba su yi ba, ta ce "Allah ya sa lafiya na ganku, ba wani abin ne ya same shi ba ko?"

Walid ya ce "Kwantar da hankalinki, babu abin da ya same shi, yana nan ƙalau"

Ta ce "To Alhamdilillah" ta jagorance su zuwa cikin ofishinta, bayan sun gaisa Walid ya ce "Na san zaki yi mamakin zuwanmu, duk da ba abin mamaki bane ba, amma dole ki ganmu. Nabila dan Allah me Viper yayi haka ki ke wahalar mana da ɗan uwa, kin san komai zai iya faruwa ƙin auren nan nasa da ki ka yi, idan ba ke ɗin ba wacece zai je ya aura su zauna lafiya?"

"Ni ɗin ma babu lallai mu zauna lafiya" ta bashi amsa.

"Amma meyasa ki ka ce haka?"

Nabila ta ce "Halin Viper ai sai dai Jauhar ɗin, kuma ma duk ba wannan ba, gani nake cik amana ne kamar ban kyauta ba, ace na auri mijin Jauhar, dan Allah ku yi haƙuri, ku bashi haƙuri, na san a fusace yake da ni, tun da nayi mafarkinsa yana caka mini wuƙa"

Walid ya ce "A'uzibillah lallai kam ya tabatta Mai zamani yana fushi da ke, amma dan Allah ki yi tunani, ki taimaki rayuwar ɗan uwanmu"

"Oga Walid ina jin kunyarka, dan Allah mu bar wannan maganar"

Walid ya ce "To shikenan, amma dai dan Allah ki yi tunani a kai"

Nabila ta yi murmushi ta ce "To Oga walid in sha Allah za ayi"

Ɓangaren Viper kuwa, abu kamar wasa, ya damu da rashin Nabila sosai da sosai, wasu lokutan sai ya shiga what's app ɗin sa, yana sauraren Voice message ɗin ta. Gashi ba yau ba gobe cikin mafarkinta yake, abin har ya fara bashi tsoro, domin kuwa abin ya fara yawa. Tabbas yana buƙatar sake yin wani auren, dama Nabilan ce ya saka rai, kuma gashi ta ce ita ba zata aure shi ba.

**** Kwanci tashi asarar mai rai, Abdul ya cika wa'adin da aka ɗebar masa, na zaman gidan yari, tun safe mahaifiyarsa ta haɗa motoci ta tafi ɗaukar sa. Ɓangaren ramma ma ji take yi kamar salla, saboda a lissafinta yau ne fitowar Abdul, sai dai Nabila ba ta ce masa komai ba. A ɓangaren sa ma Abdul ɗin, murna yake yi na fitowarsa, ko ba komai ya fuskanci ƙalubale na gaba, na samun damar ci gaba da rayuwa da matarsa, kuma gashi ya fito dag da lokacin cikar EDD ɗin ta.

Ramma ta kasa zaune ta kasa tsaye, mama ta fara bacci, ta ɗauki wayarta, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, ta kira lambar Abdul. Cikin sa'a kawai ta ji muryarsa.

"Doctor"

"Babyna da wayar wa ki ka kirani?"

"Shi ne ka fito ko ka neme ni, ina ta zullumi da lissafin yaushe zaka dawo?"

"To ta ina zan neme ki, ba waya a hannunki yanzu, ni kuma tun da na dawo Mummy ta kafa ta tsare, ba zata bari na fita ba, amma kina raina wallahi, EDD ɗinmu ya kusa cika ko?"

Ta ce "Eh, duk na gaji wallahi, cikin yayi mini nauyi, na ƙagu na haihu na huta"

"Dan Allah kar ki saka damuwar sai kin haihu abin ya dame ki kin ji sweetheart?"

"To doctor, ka huta lafiya"

"Ina batun hutu, na so da na dawo a gidana zan zauna, in ci abincin da ki ka dafa, mu kasance tare cike da so da ƙaunar juna, na yi missing ɗinki da yawa fa, yanzu dai ga abinci ga komai, amma duk ba wannan nake buƙata ba, ke nake buƙata a kusa da ni"

"Kaga sai anjima, ba zaka yi wannan zancen da ni ba"

"Au haka ma zaki ce, shikenan anyway in sha Allah a satin nan duk yadda ake ciki, zan zo na ganki"

Suka yi sallama cike da kewar juna.

Abdul ya saka ranar da zai zo ganin rahama, sai dai ta rasa yadda za ta sanar wa mama, gani take kamar ba zata yadda ba.

Dan haka ta kira Nabila ta gaya mata, Abdul yana so ya zo ya ganta, ko zata gaya wa mama, ita tana jin tsoron ta gaya mata, Nabila ta ce ba damuwa.

Ta kira mama a waya, suka gaisa Nabila ta ce "Mama, mijin rahama zai zo ya ganta, zai ga kayan sayayyar da na yi mata, da kuma yanayin jikinta, ina fatan ban yi laifi ba, na bashi adress na ce ya zo nan gida"

Mama ta ce "Mhmm ba ki yi laifi ba, ba wani abu"

"Yauwwa mama na gode sosai, a ci gaba da haƙuri dai dan Allah"

Ta ce "Ba komai"

Ramma da ciki ya sanya, wataran idan tayi wanka, ko mai ba ta shafawa, amma mama na kallonta, har da su fesa turare, da saka kwalli da shafa man leɓe mai kala, ita dai ba ta tanka mata ba ta rabu da ita.

Yaro ne ya shigo, ya ce "Wai Abdul ya zo yana waje"

Ramma ta ce masa "To ana zuwa" ta saci kallon mama, taga tayi banza da ita, ƙarshe ma ta tashi ta bar falon.

Hakan ya bata damar tashi tana jan ƙafa da kyar, ta fita harabar gidan.

Yana tsaye cikin yadi ash, kansa babu hula, ya goya hannunsa a bayansa yana kallon gidan, yana jinjina wa Alhaji mu'azzam, ya taimaki su ramma, mussaman da ya tuna gidansu na ƙauye da ko ƙofa babu.

"Me ka ke kallo ne?" Ya juyo ya kalleta.

Duk ta kumbura ta cika, ga uban ciki tana ja da kyar, hangowa yayi kamata yayi ace tana makaranta, ko idan cikin ne, ace a gidanta na aure take, gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi.

Ya kalleta ya ce "Sannu uwar biyu"

Ta harare shi ta ce "Wane irin biyu kuma? Ɗayan ma ya aka ƙare, sannu da zuwa. Lallai prison ta karɓe ka, ka ƙara haske sosai ka yi kyau"

"Hmm ina daɗi a prsion, ke dai ayi sha'ani kawai"

Ramma ta yi masa jagora, suka ƙarasa cikin sitting room ɗin da yake harabar gidan.

Ta shiga cikin gida, ta ɗaukko masa abincinta, da ruwa da lemo ta kawo masa ta ajiye.

Tana ta ƙoƙarin yadda za ta juya ta zauna, kawai ya zaunar da ita a cinyarsa.

Riƙe cikinta tayi ta ce "Wayyo Allana, kai ba ka ga halin da nake ciki ba, da na bige ciki fa?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull