Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 102
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 102: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 102. "Haba dai, na san abin da nake yi ai, na fiki son cikin nan…
4,450 words
"Haba dai, na san abin da nake yi ai, na fiki son cikin nan fa" ya ɗaga rigar jikinta, cikin nan yayi girma sosai da sosai. Cikin matsanancin shauƙi da ɗokin son ganin abin da zata haifa, ya ce "Sannu your excellency, Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, na gode Allah da na fito kafin haihuwar ki, ni zan karɓi haihuwar nan, na rigaki ganin babyn"
"Taɓ, a'a gaskiya, ba zaka karɓa ba, ni wallahi tsoro ma nake ji"
Abdul ya ce "Ba wani tsoro, ki kwantar da hankalinki, ai na san ke mai yawan ibada ce, mu yi ta addu'a Allah ya sauƙaƙa miki. Yaushe zamu je sayayyar kayan baby ne?"
"Ka manta mun sayo ni da Anty Nabila, Alhaji mu'azzam ma ya sayo wasu ya kawo"
Abdul ya ce "To Allah ya saka da alkhairi, Anty Jidda sun haɗa kai da Mummy, suna ta yi mini faɗa, saboda ke wai ba ni da zuciya, ni kuwa in dai a kanki ne, ba zan yi zuciya ba duk tsanani, ni dai a bar mini ke, mu yi rayuwar aurenmu cikin kwanciyar hankali".
Ramma ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya numfasa ya ce "Zuba mana abincin mu ci tare, ina fatan dai ke ki ka dafa?"
Ta jinjina masa kai, tare suka ci abincin, sai dai sai da ya so ya wuce gona da iri, ramma ta ankarar da shi a in da yake.
Ya ce "Rakani mu je na gaida mama"
Sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta shiga gaba ya biyota a baya, aka yi sa'a maman tana falo a zaune.
Abdul ya shiga da sallama, ya durƙusa har ƙasa yana gaisheta, ta kawar da kanta gefe sannan ta amsa masa.
Daga haka ya miƙe ya ce "Na tafi to, sai anjima"
Mama ta ce "To ka gaida gida"
Da suka fito Ramma tayi zaton zai nuna ya ji babu daɗi, yadda ta amsa masa, amma bai nuna mata ba, sayayyar da ya yi mata ya bata, yayi mata sallama ya tafi.
Ramma ta kasa gane kan mama, haushinta take ji ko kuma yaya, gaba ɗaya ta ɗauke mata. Abdul yana son kiran waya yayi magana da ramma, amma ta ce kar ya kira wayar mama ce, shi kansa shakkar ramman yake ji.
Kotu ta bayar da umarnin a kamo Naja'atu Bunkure, tun da taƙi gurfana ta kare kanta bisa ga tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Viper ya dira a garin Kano, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, a can gidansu da suke zaune yaje ya sauka, ya tarar daga Walid har liti duk ba sa nan, yayi wanka ya huta, sannan ya shirya ya tafi cikin gari.
Ya tarar Abbu baya nan, kawai Rahila ta fito ta ce "Sannu munafi mara mutunci" ya tsaya yana kallonta.
"Eh, na ce sannu munafuki, saboda algungumi ne kai, baka tsoron Allah, shi ne ka haɗa kai da babanka, zaka aura wa Shahida ɗan iska kamar ka, to baka isa ba, Shahida gidan tsohon mijinta zata koma"
Viper kamar ya tanka mata, amma sai ya rabu da ita ya fita.
Yana nan a ƙofar gidan daf da magariba, sai ga Abbu ya dawo, tare da Walid, Walid ne yake jan motar, Abbu yana gaba suna hira.
Walid ya din ga yi wa Viper horn,ya taso ya nufo su, Abbu ya ce "Ya aka yi ka dawo kuma? Ni na yi ɗa dama baka dawo yanzu ba"
Viper ya yi murmushi ya ce "Ai ba daɗewa zan yi ba, yanzu ma idan aka ce na koma tsaf zan tafi"
Abbu suka fito daga motar, Walid ya ba wa Abbu mukullin ya ce "To Abbu sai Allah ya kaimu gobe"
Abbu ya ce "A'a, kira wo mini Abdallah a waya, ya ƙaraso shi ma ku ci abinci tukuna"
Suka yi alwala, suka je suka yi sallar magariba suka dawo, suka yi shimfiɗa a ƙofar gida suka zauna, har ƙarfe tara na dare suna tare, wajen tara da rabi, Viper ya ce su tafi zai taho.
Abbu ya din ga bawa labari jin daɗin zamansa da Walid, saboda biyayyarsa da riƙon amana, kuma ya ga sun fuskanci juna da shi da Shahida, dan haka baya son a wani ɓata lokaci, saboda Rahila na ƙoƙarin ɓata lamarin. Haka suka cigaba da tattauanawa, a kan yadda shirin bikin zai tafi.
Liti kuwa Alhaji ya ce sai ya koma makaranta ko per time ne, sannan kuma zai kai shi kasuwa.
Liti ya ce "Amma dai da daddare idan na dawo, an je rumfar shayi"
"Wai rumfar shayin nan, ba cewa aka yi kayan shaye-shaye kuke sayarwa a ciki ba?"
"Wallahi mun daina sayarwa, harkar shayi da indomie da sauransu ake yi a wurin, kuma wannan rumfa tana da tarihi domin tunawa da marigayiyya Jauhar matar Viper, ba zan bari rumfar nan ta mutu ba. Kuma a yanzu haka wallahi yaranmu sun kai biyar da suke cin abinci a wurin, ni kula nake yi da ita, akwai amana ai, duk in da na je da daddare sai na je rumfar nan"
Alhaji ya ce "To, Allah ya tallafa"
Ya amsa da Amin.
*** Kwana na biyu kenan ramma ramam tana ta zubar da ruwa, ta rasa yadda za ta yi, gashi mama yanzu ba wani sakar mata fuska take yi ba, dan haka ba ta gaya mata ba, ba ta zata hakan wata matsala ba ce, dan haka ta ja bakinta tayi shiru.
Sai da Nabila ta bushi iska, ta je gidan, take gaya mata, Ba ƙaramin ƙuluwa Nabila tayi da abin da mama take yi ba, ta karɓi lambar Abdul, ba tare da ta saurari mama ba, ta kira shi ta sanar masa, a sukwane ya ce gashi nan.
"Ina zaka je kana zauna kana cin abinci kuma?"
"Mummy asibitina zani, aikin gaggawa ne ya taso"
"Yaushe ka dawo har ka koma aikin da zaka ce mini wani aikin gaggawa? Da da kake tsare waye yake aikin?"
"Ki yi haƙuri na je na ji menene" ya ajiye cokalin ya yi gaba. Ya kira lambar Nabila ya ce ta ɗaukko ramma su haɗu a asibitinsa kawai.
Nabila ta fito falo ta ce "Mama zan tafi da ramma asibitin royal, can asibitin mijinta, ba ta da lafiya ya ce lallai a kaita shi ma ya tafi, kwana biyu tana zubar da ruwa"
Sai kuma ta tashi a kiɗime, ta ce "Ramma naƙuda ki ka fara baki gaya mini ba?"
Ramma tayi shiru, ta ce "Ai akwai tofinta, da kayan haihuwa da na haɗa, ko da su za a tafi, ko haihuwar ce?"
Nabila ta ce "A'a bari muje kawai, tun da ba ciwo take ji ba, idan haihuwar ce sai muyi waya ki taho"
"A'a ba haka za ayi ba, mu tafi kawai bari na ɗaukko mayafina" tana shiga ɗaki, sai ma ta rasa wa zata kira, kawai ta kira Viper tana gaya masa.
Ya ce "Ai yau da daddare nake son zuwa da ni da Abbu ku gaisa, amma gani nan zan biyoku asibitin"
Ko da suka je asibitin, a harabar wurin suka tarar da Abdul, yana ta kaiwa da komowa, suna isowa, ya nufe su, Nabila ta kamo hannun ramma, ta fito daga cikin motar, tana takawa da kyar, duk da ta saka pad, amma ruwan da take zubarwa duk ya ɓata mata jiki.
Wheel chair ya ɗaukko da gudu, ya ajiye suka ɗora ramma a kai, ya tura ta cikin asibitin.
Tuni ya kira doctor Muktar, wanda abokinsa ne, kuma shi ya yi wa ramma awo.
Bayan fitar Abdul, doctor Muktar ya yi wa ramma scanic, ya kalleta ya ce "Yaushe rabon da cikin yayi motsi?"
Ta ɗan shiru ta ce "Tun jiya da safe"
Abdul ya dawo ya ce "Muktar, yaya ake ciki ne?"
Ya gyaɗa kai ya ce "Low amniotic fluid, a shirya OR kawai, ayi mata EMCS"
Ya ce "Ya subhanallah, amma ya babyn" ya faɗa a rikice.
Muktar ya ce "Meye haka? Wato saboda wannan taka ce shi ne zaka wani ruɗe? Dan Allah ka nutsu mana, normal in sha Allah, ka shirya ka yi assiting ɗina, sai a ciro babyn, ka kira anesthetic ɗin"
"Abdul meya same ni?" Tayi maganar kamar zata yi kuka.
Ya ƙarasa ya riƙe hannunta, ya ce "Ki kwantar da hankalinki, tun yaushe ki ke zubar da ruwan nan?"
"Ni na manta, ka gaya mini Meya same ni?"
"Ruwan da babynmu yake ciki ne yayi masa kaɗan, saboda rashin sanarwa da wuri da ba ki yi ba, duk ruwan ya zube, yanzu tiyata zamu yi miki a ciro shi"
Ramma ta fashe da kuka ta ce "Yanka ni za ayi kenan, wayyo Allah tsoro nake ji"
Ya ce "Ki yi haƙuri, babu wani abu in sha Allah"
Ya kalli muktar ya ce "Doctor Muktar, ko zaka yi wa mamanta bayani, suna falon office ɗina" ya jinjina kai ya fita.
Doctor Muktar yana zuwa, ya tarar da Nabila da mama, ya ce "Matar master, sannu fa"
"Matar master ai ta rasu"
Ya ce "Ai ni duk abu daga nake gani, amma ya aka yi ta gama awo successfully, matsala ta taso ku kasa faɗa sai da ta zama worse? Kwana kusan biyu tana zubar da ruwa fa"
Nabila ta ce "Wallahi ba ta faɗa bane ba doctor "
Ya ce "Aishikenan, yanzu tiyata zamu yi mata ta gaggawa, amma babu wani abu in sha Allah" maman ramma ta dafe ƙirji ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu ina ramman take?"
"Ki kwantar da hankalinki, yanzu kafin a shiga da ita, zaku ganta in sha Allah, ke Nabila taho muje ko da abin da zaki yi mata". Suna barin wurin sai ga Viper, ya tarar da mama na matsar ƙwalla.
Ya ce "Lafiya ya ake ciki?" Nan ta gaya masa abin da suka ce, a rikice ya nufi cikin asibitin, ba ya ƙaunar duk wani abu, da zai shafi mai ciki.
Ba tare da ya yi knocking ba, ya shiga ɗakin, har Abdul ya sanya wa ramma rigar tiyata, ya rungumeta yana ta rarrashinta tana kuka, wai tsoro take ji. Tsit suka yi suka zuba masa ido, ramma na ƙoƙarin barin jikin Abdul.
Nabila ce suka shigo tare da doctor Muktar, ya bata consent form, da za a saka hannu ayi wa ramma aiki.
Doctor Muktar ya ce "Allah ya taimaki master, kwana biyu " ya miƙa wa Viper hannu suka gaisa.
Al'amin ya ce "Ina ganinka gabana ya faɗi doctor Muktar, a wancan karon matata a wannan karon ƙanwata, ya ake ciki menene matsalar?"
"Ahh ba wata damuwa, in sha Allah, aiki zamu yi mata, ruwan da yaron yake ciki ne yayi masa kaɗan"
Ya jinjina kai ya ce "Allah ya raba su lafiya"
Ya kalli ramma da fuskarta ta jiƙe da hawaye ya dafa kanta ya ce "Rahama" karon farko da ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi.
"Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki kin ji? In sha Allah babu wani abu, za ayi miki aiki lafiya a gama lafiya, ki yi ta addu'a, ki daina wannan kukan, kar jininki ya hau"
Ta ce "Yaya tsoro nake ji, yankani za ayi"
"Ai ba zaki ji zafi ba in sha Allah"
Nabila ta maze kamar ba ta ga Viper ba, kamar yadda shi ma ya maze.
Ta ce "Ga consent form da aka ce a cike, wa zan bawa ne?"
Ta miƙa wa Abdul, ya saka hannu zai karɓa, Viper ya karɓe form ɗin ya na tsareta da idanunsa, ya ciro biro a gaban rigarsa ya saka hannu. Abdul kawai ya zuba wa sarautar Allah ido.
Ya ajiye form ɗin bayan ya saka hannu, ya miƙa wa ramma hannunsa, ta saukko daga kan gadon, ya kalli doctor Muktar ya ce "Ina ne ɗakin tiyatar?" Ya jagorance su, su na tafe yana tuna 'yar madara, su na zuwa bakin ƙofar mama ta ƙaraso.
Ta ce "Ramma, Allah ya fito da ke lafiya, Allah ya sa ayi a sa'a"
Abdul ya ƙaraso, Viper ya kalle shi, ya miƙa masa hannun rahama, Abdul ya kama hannunta, suka shiga cikin tiyata, tana yi tana waiwayowa tana kallonsu.
Ayshercool 08081012143
104 Abdul ya shiga da ramma cikin ɗakin, ya taimaka mata ta kwanta a kan gadon tiyatar, ya shiga ya canza kayansa zuwa na tiyata, sai rarraba Idanu take yi, cikin matsanancin tsoro. Aka shirya ta tsaf, Abdul ya ce a kuma scanic, Doctor Muktar ya ce no need. Duk wani examination da zai yi wa ramma, sai Muktar ya hana shi, ya ce masa ya riga ya yi.
Aka duba Vitals ɗin ramma, komai normal sai palpitations, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, suka din ga rarrashinta, suna kwantar mata da hankali.
Aka yi mata abin da yakamata, aka kwantar da ita, aka ce ta ɗaga ƙafafuwan ta, ta ce ba zata iya ba, suka rufe yadda zata ga me suke yi, ta miƙa hannu ta riƙo na Abdul.
Doctor Muktar ya ce "Anya ba korarka zamu yi ba, malam ka nutsu ka mayar da hankalinka mana"
Ramma ba ta san me ake yi ba, ta ji kamar ana yi mata shocking dai, kuma ana jijjigata. Gashi sai surutu suke yi mata, suna mata hira mai ma'ana da mara ma'ana.
Ta ce "Doctor Abdul"
"Yes my dear"
"Ban taɓa ganinka a cikin kayan tiyata ba, sai yau da Allah ya yi kai zaka yanka ni"
Ya ce "To ya ki ka ga, sun yi mini kyau?"
Ta ce "Sosai ma, duk sun fi yi maka kyau".
Muktar ya ce "Ban da son kai fa, tsakani da Allah na fishi kyau"
Ramma ta ce "Anya kuwa? Doctor ashe doctor Muktar ne ya yi wa Anty Jauhar matar Yaya Aminu awon ciki, kuma shi ya tabattar da rasuwarta"
Abdul ya ce "Haba dai?"
"Wallahi tambaye shi ka ji"
Muktar ya ce "Baka ga yana ta lallaɓa rahama ba, gayen nan na tausaya masa, ko yanzu kafin mu shigo, naga damuwa a tare da shi, ana gobe za a kashe ta, na gaya masa ya tanadi kuɗi, idan inducing bai yi ba, yayi failing C.S ne, gayen nan ya ce ko nawa ne, zai nemo su, na daɗe ban ga zunzurutun so da ƙauna ba sai a wurin su, kuma kalli ikon Allah ga 'yar uwatta nan da take kawo Madam awo, kamar su ɗaya sak"
Shiru Abdul yayi, bayan da Muktar ya ciro jaririn cikin rahama, jibgegen yaro, fari ƙal alama ya daɗe ma da mutuwa, fatarsa ta fara macerating, sai dai kyakykyawan gaske ne, ga gashi cunkus a kansa, har goshinsa zuwa girarsa gashi ne.
Abdul ya kalli doctor Muktar, amma ya girgiza masa kai, yayi masa alamar yayi shiru.
Ramma ta ci gaba da magana, doctor Muktar yana bata labarin Viper da Jauhar.
Ta ce "Wai haryanzu ba a ciro ɗan ba?"
"Babyn naki ne, ƙato to, amma yanzu za a ciro shi in sha Allah"
Ta ce "Allah ya fito mini da shi lafiya, na bi na ɗaga hankalina, ashe CS ɗin ba abin tashin hankali bane ma"
Maman ramma na can waje, tana jera salloli tana addu'a, Allah ya sa a fito mata 'yar ta da lafiya.
Viper kuwa kamar ya haɗiye Nabila, sai satar kallonta yake yi, duk da ta basar da shi, amma zuciyarta azalzalarta take yi, ta kula shi, ta yi kewarsa sosai amma ta maze, ta kira Sumayya ta gaya mata suna Asibiti wurin ramma.
Ramma ta ji shiru-shiru, ba a ce mata ga ɗa ba, ta ce "Nifa ban ji yayi kuka ba, idan kun ciro shi, ku nuna mini shi mana"
Muktar ya ce "Ai sai mun gama, an kai ki ɗakin hutawa sannan zaki ganshi"
Ta ce "Ka haɗa kai da abokinka sai ya rigani ganinsa, shikenan ai"
"Wai dama kina magana haka? Kullum idan aka kawo ki awo, kanki a ƙasa kina ɓuya"
Tayi murmushi ta ce "Idan na yi shiru, zai shiga damuwa ne, shiyasa nake magana"
Muktar ya girgiza wa Abdul kai, saboda yadda ya karaya jikinsa yayi sanyi, ya ƙallafa ransa da ɗora buri a kan abin da ramma za ta haifa, daga fitowarsa ya sai sa da rago, saboda ya ce ko me za ayi, ko a faɗa sai dai ayi, amma babban shagalin bikin suna zai yi.
Ya nananɗo jaririn a zani, ya fita daga cikin tiyatar jikinsa a sanyaye.
Gaba ɗaya suka nufo shi, suna jera masa tambayoyi.
Maman ramma ta ce "Yaya ina rahaman? Mutuwa tayi?" Ya girgiza musu kai alamar a'a.
Viper ya ce "Kayi magana mana menene?" Yayi maganar yana ƙoƙarin karɓar jaririn.
Ya karɓe shi, ya buɗe shi, ya ga bashi da rai.
Take jikin Viper ya sanyi ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Yaron ba shi da rai, kamar ma ya kwana biyu da rasuwa, amma mama da wa yaron nan yake yi miki kama" yayi maganar yana nuna mata fuskar jaririn.
Ta ce "Kaii, kamar Nura ce ai wannan, wallahi kamar su ɗaya sak, bani shi na gani, ina ma yana da rai, wayyo Allana" ta karɓi jaririn tana kallonsa, hanci har baka ƙato mai kyau, amma babu rai.
Abdul ya koma ya jingina da jikin bango yana kallonsu kawai, jikinsa gaba ɗaya ya yi sanyi, yama kasa komawa ɗakin tiyatar.
Sai da Nurse ta fito ta ce masa, ana nemansa, sannan ya shiga, ya tarar an gama ɗinketa, har an sakata bacci, aka fito da ita daga tiyatar, suka nufeta, suka tarar bacci take yi, dan yadda aka fito da ita kamar matacciya.
Aka kaita post-op room, aka kwantar da ita.
Doctor Muktar ya kalle su ya ce "Haƙiƙanin gaskiya, tun da ku ka zo na yi mata scanic, naga yaron ya mutu, bana son ɗaga muku hankali ne, ta ƙara karaya kafin ayi aikin, rashin sanar da batun zubar ruwan nan ne, da wuri ya ƙara ta'azarra lamarin. Amma Alhamdilillah ita tana nan ƙalau, mun tura lab ayi post-op pcv, mu gani idan jinin jikinta ya isheta normal ne, idan kuma akwai buƙatar a ƙara shikenan, amma dan Allah a rarrashe ta, a bata baki"
Mama da su Nabila suka yi ta yi masa godiya.
Viper ya ce "Yakamata ka zo mu je a binne shi ko"
Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah a jira ta farka, ta ganshi, idan aka rufe shi ba ta ganshi ba, za ta ji babu daɗi"
Viper ya jinjina kai, mama ta miƙa wa Viper yaron, ta tafi gaban gadon ramma da take ta bacci, tana kallonta tana shafa kanta cike da tausayawa.
Viper ya riƙe yaron sosai, ya zuba masa ido, ya tuna shi ko gawar masa ɗan ma bai gani ba, kamar dai Abdul ɗin nan haka ya din ga zumuɗi a kan haihuwar da yake saka ran ayi masa, amma a ƙarshe duka biyun ya rasa su.
Shirun da ya yi yana kallon jaririn, Nabila ta san me yake tunawa, saboda yadda ya tattara nutsuwar sa kacokan a kansa, yana ta sauke numfashi.
Nabila ta miƙa wa Viper hannu, ta ce "Ba ni shi nima na ganshi"
Mugun kallon da ya yi mata sai da ta ja da baya, ya koma gefe ya zauna, rungume da gawar yaron.
Alhaji mu'azzam ba ya gari, ya aiko yaronsa da yake yi wa su ramma hidima, idan da wani abu da ake buƙata.
Nabila idan idonta dai-dai yake gane mata, har da harara Viper yake ta aika mata.
Abdul kuwa sai da ya zubar da hawaye, a cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar yaronsa, gashi dai babu rai ya zo, amma sosai yake jin son sa a ransa.
Mummy ce ta addabe shi da kiran waya, ya gaji ya ɗaga ta ce "Kana ina ne?"
"Ina Asibiti Mummy"
"Na ji muryarka ƙasa-ƙasa wani iri, menene?"
"Rahama na yi wa C.S, ta haihu ɗan babu rai".
"To kuma shi ne me? Ba zaka raba kanka da harkar mutanen banza nan marasa mutunci da suka ɗaureka ba ko? Ka dawo gida babanka yana hanya zai shigo Kano, yana son ganinka, tun da kai ba ka ga dacewar ka je in da yake ba"
"Mummy, ɗa na fa na rasa, an yanka 'yar mutane, haryanzu ba ta farfaɗo ba, kawai na kama hanya na tafi na bar su, anya na yi musu adalci kuwa?"
A fusace ta ce "Ni ka ke gaya wa haka Abdul?"
"Ki yi haƙuri, ba wai rashin kunya bane ba, ko gaya miki magana ne ba, amma duk fa abin da ya samu rahama ni ne sila, zuwa anjima in sha Allah zan dawo, ina jiran ta farfaɗo ne"
Ya katse wayar, yana mamakin son kai irin na iyayensa.
Ramma ta farfaɗo daga baccin da take yi, suna ta jera mata sannu, kafin ta amsa ta kalli Nabila ta ce "Anty Nabila ina jaririn ne?"
Nabila ta ce "Bari a kirawo Abdul ɗin"
Aka kirawo Abdul, ya shigo cikin kulawa yana yi mata sannu.
Ta ce "Ina babyn?"
Ya zauna a gefen gadon ya ce "Ki na ji rahama, ki yi haƙuri da duk abin da Allah ya hukunta mana, babyn bai zo da rai ba, da alama ya ma kwana biyu da mutuwa a cikinki, sai mu yi haƙuri"
"Wayyo Allana, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu duk wannan wahalar da na sha amma ya mutu"
Mama ta ce "Ke ramma, ba musulma ba ce ke? Ba za ki yi tawakalli ba?"
"Mama na sha wahala fa, amma ya mutu" ta yi maganar tana kuka.
"To dan ubanki sai ki dawo da shi, ke da ki ka samu kanki lafiya ƙalau ba zaki gode wa Allah ba?"
Ramma ta kasa jurewa ta fashe da kuka, Abdul ya yi shiru ya ma rasa me zai ce mata, shi kansa kukan yake son yayi, saboda ya saka rai sosai da sosai.
"Rahama" Viper ya kira sunanta.
"Na'am" ta faɗa tana ɗaga kanta ta kalleshi.
Ya ƙarasa gaban gadonta ya ce "Ba a jayayya da ikon Allah kin ji ko? Mamanki da ta rasa Nura haƙuri tayi, nima na rasa ɗa na da matata da tsohon cikin da na ƙallafa rai a kansa, amma ko ganinsa ban yi ba, na rasata na rasa ɗan, dan haka ki yi haƙuri ki yi masa addu'a"
Ya nuna mata jaririn nata, ta kai hannu ta taɓa fuskarsa ta ce "Shikenan, Allah ya jiƙansa ya sa ya huta"
Abdul ya ce "Amin, ki yi haƙuri kin ji madam, Allah ya kawo mai amfani, ki kwantar da hankalinki, dan a samu ki warke da wuri" ta jinjina masa kai.
Viper ya saka yaron a kwali, ya ce wa Abdul, "Mu je a binne shi ko?"
Abdul ya jinjina kai, har magariba Nabila na tare da su rahama, ana ta rarrashinta, daga baya tayi musu sallama ta tafi gida.
Sai da Viper ya tabattar da su mama basa buƙatar komai, sannan ya tafi.
Muktar ya daɗe yana ba wa Abdul labarin Viper da matarsa, da yadda aka liƙa masa kashe matar ta sa, har yake gaya masa yaje kotu ya bayar da shaida a kan shari'ar, tare da nanata Naja'atu Bunkure ba ta da imani.
Abdul ya yi shiru yana tunani, tabbas duk abin da Viper yayi, tirsasa masa aka yi, an cutar da shi da yawa, dole ya tsane shi.
Jikinsa a sanyaye ya koma gida, yana hasko cewa shi ɗansa kawai ya rasa, duk ya damu ya shiga cikin tashin hankali, amma shi Viper da matar da ɗan ya rasa, kuma aka ɗaure shi aka tauye masa hakkinsa. Da haka ya ƙarasa gida.
Yana zuwa gidan ya shiga falon Mummy, suna tare da Indabo, yana cin abincin dare.
Ko zama bai yi ba, ta hau shi da faɗa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, tana kiransa mara zuciya da bai san ciwon kansa ba.
Cikin takaici da mutuwar jiki, ya ce "Mummy ɗa na fa na rasa, haihuwa aka yi mini ɗan ya koma, kuma ɗa na halal ɗan sunna. Mummy idan iyayen rahama sun saka an rufe ni, meye na ɗa na a ciki? Yadda ki ke jin so da ƙaunarmu, haka nake ji a raina, ɗa na ne ya zo babu rai, amma baki tausaya mini ba, baki jajanta mini ba sai faɗa ki ke yi mini ya zan yi ne?"
Indabo ya ce "Abdul" Abdul ya kalle shi ya ce "Zo nan" Abdul ya ƙarasa gaban digning ɗin ya ce "Gani"
"Zauna mu yi magana" Abdul ya ja kujera ya zauna yana sauraren indabo.
"Yanzu Abdul duk abin da ka haddasa, duk bai dameka ba ko? Ka wulaƙantar mini da kuɗi, a kan shashashar 'yar ƙauye, ka yi asarar takarar da nake ta fafutukar na tsayar da kai, dan na san ina tsayar da kai, za ayi caa a tona asirinka, a sake ɓata mana suna, yanzu ni na riga na san na yi asarar takarata duk saboda wawancinka, kuma still baka yi regreting ba, kana faɗar maganganu kana cikin hayyacinka kuwa Abdul? Tun wuri tun da ta haihu, shikenan ina son lallai ka rabu da yarinyar nan, ka fita harkarta, ka zo ayi settling maganarka da yar party chairman haryanzu muna da sauran chances, a next tenure za a iya baka minista, ni kuma in san abin yi. Dan haka lallai ka saketa tun da dama ba wanda ya san ka aureta"
Ya kalli mahaufinsa cikin matsanancin takaici ya ce "Daddy, yadda Jafar yake Mexico a tsare, ranka yake maka zafi saboda an tsare maka 'ya, haka maman rahama take ji, koma fiye a duk lokacin da ta tuna na keta wa 'yar ta haddi. Ba dan na zaɓi rahama a kan ku iyayena ba, amma sai da rahama ta shigo rayuwata, na fuskanci gaba ɗaya rayuwata jarrabawa ce, kasancewarku iyayena, babu wanda ya tsawatar mini da shaye-shaye, ko sauran laifuffukan da nake aikatawa ba, kuna kallon hakan a abu ne da zan daina a gaba, rayuwar cikin turawa ya sanya na zama haka. Ban ƙara tabattar da zamanku iyayena jarrabawa ce ba, dai da na nuna maka videon mummunan aikin da ka aikata, amma hakan bai wani dame ka ba, kuma bai girgiza Mummy ba, saboda duniyar ce kawai a gabanku, ni kuwa tuni rahama ta ankarar da ni fifikon Lahirata a kan duniya saboda ita ce dahir. Na miƙa lamurana ga Allah, la'akari da Annabin Allah ma, Annabi Ibrahim alaihi salam, Allah ya jarrabe shi a kan mahaifinsa, haka an jarabci Annabi nuhu da ɗansa, kowane bawa da irin ƙaddararsa, wallahi ku ka ci gaba da matsa mini, zan bar gidan nan, zan je na ci gaba da rayuwata kawai"
Indabo ya kwantar da murya ya ce "Haba Abdul, duk wannan abubuwan da kaga ina aikatawa, duk dan mu yi surviving ne, na inganta rayuwarku, kuma abin da ka gani abu ne da ya riga ya wuce, na daina aikatawa, kowane ɗan Adam akwai irin laifin da yake yi wa Allah, kuma Allah mai rahama ne da jin ƙai"