Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 20
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 20: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 20. "Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza…
4,485 words
"Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya.
"Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki"
Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta.
Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba.
Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ɗakin da ta gano shi.
Ɗakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buɗe dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ɗakin yake yi.
Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta.
Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ɗauki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ɗan ɗebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana.
Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da 'yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi.
Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ɗaya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan.
Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata.
Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su"
Ta ɗan yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuɗin da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji.
Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa.
Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba.
Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu.
Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni".
"Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana".
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni".
Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?"
Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?"
"Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?"
Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga ɗebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi"
Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman kuɗi".
Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka"
Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan buƙatu.
Jauhar ta ji daɗin hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi.
Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai.
Ta ɗebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ɗebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta.
Tana aikinta, tana jin radiyo a mp.
Ta bawa yara kuɗi, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi.
Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo.
Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi.
Ba ya falo, ta shiga ɗaki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ɗakin da yake.
Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banɗakin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa. Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba.
'yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama.
A fusace ya ce "Meye ne?".
Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka"
Ɗan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daɗi da bai haɗu da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta.
"Ga kuɗin" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi.
"Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "Kuɗin fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ɗakin.
Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuɗin, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo.
"Kwashe kuɗin nan ki bar nan" jiki na rawa, ta ɗauka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ɗakin.
Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi.
Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba.
Maimakon ya ɗebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buɗe flask ɗin, ya juye salad ɗin a ciki, ya ɗaga flask ɗin miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma.
Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ɗaya, ɗaya kuma ta zuba masa ruwa.
Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata.
Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan.
Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba.
Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faɗuwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba.
Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ɗaya, dama taliya leda guda yake cinyewa. Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ɗin ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin.
A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet ɗina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta ɗebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ɗakinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar.
Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba.
Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke.
Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta.
Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye"
Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta leƙa.
Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al'amin ba ba.
A ɗan tsorace ta ce "Sannu"
Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?"
Ta ce "Eh meyafaru?"
"Ɗan je ki ce mata ana sallama da Boss"
Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?"
"Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?"
Jauhar ta ce "Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba"
Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?"
Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ƙofa ta rufe.
Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya ɗaga ya ce "Ya mai laya".
Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa"
"Wacece ya aka yi?"
"Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne"
Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa"
"Kai haba maza, wannan ɗin?"
"Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti"
Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta".
"Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme".
Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan.
Kamar ba zata buɗe ba, ta sake buɗewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?"
"Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani"
"Shi wa?"
Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan"
"Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba"
Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?"
Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa".
Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe.
Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su.
Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ɗaukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta ɗauka ta mayar masa ɗakinsa
Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi.
Walid ya je ya samu Al'amin, ya din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya ci a hannunsa.
"Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure 'yar yarinya ta hana aiki yau?"
Al'amin ya kalle shi ya ce "Ƙila"
Yayi tsaki ya ce "Yauwwa, na haɗa maka da mp ɗina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba"
Al'amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa ɗakin, ya tabattar ɗauka tayi ta kunna.
A ransa ya ce 'Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba'
"Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp ɗina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?".
Aminu ya miƙe ƙafa ya ce "Sai ka dawo"
Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al'amin, ba zai koma gidan nan ya ɗaukko kayan ba.
Ƙarfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye.
Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari.
Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera.
Ta durƙusa ta ce "Yaya ina kwana" waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba.
Har ta fitar da ran zai amsa ya ce "Lafiya"
Ta miƙo masa leda ta ce "Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ɗiba na dafa mana tea?" Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce "Da me zaki dafa tea ɗin?" Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce "Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ɗin taliya ce?"
"Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?"
Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji daɗin mahaukaciya da ya kira ta da ita ba.
"Dan Allah ka yi haƙuri, ban sani bane".
"Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami'an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki"
Shagwaɓe fuska ta yi zata yi kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ka bashi haƙuri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa"
Ya saka hannu ya ɗauki ledarsa ya tashi zai fita ta ce "To karin kumallon fa" ko waiwayowa bai yi ba, ya fita.
Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ɗakinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ɗaya da zai saka, ta ɗaukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wuƙa. Gabanta ya faɗi wuƙar kawai abun tsoro ce.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta ɗauka"
"Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani".
A razane ta ɗago jikinta na tsuma.
"Fita ki bar mini ɗaki, bincike ki ke yi mini ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba"
"Fita to"
Ta ce "To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka".
Ya sake tsuke fuska ya ce "Ki fita na ce"
Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin.
Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntuɓe, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton.
Ta lallaɓa ta fita ta kunna gas, ta ɗora shayi.
Buga gate ɗin gidan ake yi da ƙarfi, ba shiri ta tafi ta buɗe.
Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa.
Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce "Ina matar gidan?" Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta. "Lafiya?"
"Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini".
"Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ƙararsa muka kai"
Ta ce "Subhanallah, laifin me yayi muku?"
"Au jira zamu yi sai ya yi kan mu ɗauki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana 'yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen ɗan daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala'i. Gara aje a zauna da mai unguwa da 'yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi".
Jauhar ta ce "Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin 'yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina".
"Ke rufe mini baki kan na kwaɗe ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba"
Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke faɗa.
Da sauri ta leƙa ta ce "Ka tafi kar ka bari ya ganka"ta waiwayo ta rufe gate ɗin tana kallonsa.
"Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa".
Ayshercool 08081012143
22 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Kafin ta yi wani yinƙuri, ya janyeta daga jikin gate ɗin, sai dai kasancewar ba ƙwari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ƙasa.
Ya buɗe ƙofar ya lelleƙa, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ɓace.
Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ƙafarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda faɗuwar da ta yi.
Ƙwafa ya yi ya wuceta, ta lallaɓa ta tashi, ta shiga kitchen ta ɗora tea, ta ɗebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ƙara gyarata ta zuba ta kai masa falo.
Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci.
Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge.
Dan haka ta sayo toilet paper, take haɗo masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ƙaramin yaro.
Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige ɗakinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba.
Idan za ta gyara masa ɗaki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ɓata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ɗakin.
Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su haɗu ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ƙaurin hayaƙi gashi ba sa jin sinadaran ɗanɗano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su.
Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu daɗi, ya ajiye ya ce gida zai tafi.
Walid ya ce "Da ranar nan tsaka zaka fi gida?"
"Eh" ya amsa a taƙaice.
"Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya ɗayyiba"
Ya haɗe rai ya ce "Mai laya"
Walid ya ce "Sorry maza, na kiyayi mai zamani" ya fice ya tafi gida.
Jauhar tana ta lissafin kuɗin hannunta, sun kusa ƙarewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe.
Da 'yan dabaru take yin ɗan wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al'amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci.
Ya shiga ɗakinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara ɗakin tsaf.
Tsaki yayi ya ce "Ita dai wannan an yi 'yar wahala"
Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta ɗauke da sallama.
Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ƙamshin manjan, ya cika masa hanci.
Ta ajiye masa ya haɗa abun sa ya fara ci.
Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce "Yaya" shiru ya yi mata, yana haɗiye ɗan wakensa da hurhuɗu biyar-biyar.
Ta sake cewa "Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka".
"Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya" a ranta ta ce 'Ai na san a rina'
A zahiri kuma ta ce "Ai ba zan iya faɗar sunanka ba, ya za ayi na faɗi sunan mijina kamar mara ɗa'a" sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta.
"To me zan din ga ce maka?" Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ƙarƙashin mutum, amma ba zai kulaka ba.
"Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?" Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ƙarfin hali kawai take da take yi masa magana.
Kallonta yayi, tana murmushi dimple ɗin ta na side ɗaya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana.
Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma yaƙi ya sha kunu, yana suɗe kwanon ɗan wakensa.
Cikin hikima ta ce "Da da sauran garin ɗan waken nan, da na dafa maka wani, ko na ƙaro maka?"
"A'a" ya ajiye kwanon, cikin sauri ta miƙa masa wani tsumma mai kyau, ta ce "Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai" ya karɓa ya goge, ya koma ya kashingiɗa yana duba wayarsa mai madannai.
"Na ce, dan Allah sonake na shiga maƙwabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba"
"Sauka lafiya" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.
"Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la'asar, sai na je. Yauwwa mutumin ɗazu ya ce wai mai unguwa na nemank..... Ba ta ƙarasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa.
Bayansa ta bi da kallo, 'Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba' tayi maganar a hankali.
Huɗu da rabi, bayan ta yi la'asar, ta leƙa ɗakinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla.