Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 21
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 21: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 21. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta,…
4,484 words
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta taɓa tsammanin yana kai goshinsa ƙasa ba.
Ta zauna a bakin ƙofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la'asar ya haɗa a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla.
"Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu'a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba" dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita.
Matasan 'yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na 'yan makaranta.
"Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi 'ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?"
Rahila ta ce "Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ƙarata, ya ƙara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf"
Shahida ta ce 'Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?"
Amira ta ce "Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close".
Shahida ta yi murmushi ta ce "Ina ne gidan nasa ne?"
"Yana can gidansa na ɗorayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lallaɓa ya dawo mana nan ya je can su ƙarke".
"Ahh haba umma, sai mu yanke alaƙa da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?"
Amira ta ce "Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki"
"Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?"
Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce "Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke alaƙa da shi?"
"Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?"
Ta tashi ta ce "Ai ba babanmu ɗaya ba, Yaya Al'amin kuma babanmu ɗaya, kowane ina son sa"
Rahila ta ce "La ila ha illalahu Shahida "
Amira ta ce "Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne"
Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al'amin.
*** Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen maƙwabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makarɗe.
A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ɗinki, har ta karɓa tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana'oin hannu suna matuƙar burgeta.
Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata.
Matar ta ce 'To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai"
Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ɓarke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ɗinki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata.
Ganin hadari ya fara haɗowa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya buɗe ƙofa ya fice.
Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ɗauki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ɗauke kayarsa, ta ce "Da sauƙi, tun da ba ka yi mini faɗa ba".
Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ƙara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ƙarfin iskar da ruwan.
Ta takure wuri guda, tana ta addu'a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na karɓar addu'a, mafi yawan addu'arta a kan Al'amin ne, da take masa fatan shiriya.
Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya jiƙe ɗakin, ta buɗe ƙofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta banɗkuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi.
Haka ta samo kwano, ta din ga ɗibar ruwan tana zubarwa, ta naɗe carfet ɗin ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfiɗa a ƙasa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan.
Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba.
Ana sallar isha'i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo.
A ransa ya ce "Iyayenki ne suka ja miki" tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya karɓi kwanon, ya haɗe mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ƙaramar wayarsa, ya ƙarasa kwashe ruwan. Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana buƙatar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka.
Ya ɗaɗɗaga labulayen, saboda ɗakin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata.
Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ƙanƙame jikinta take yi, ƙarnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta.
Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ɗin macaroni, kasancewar falon a jiƙe yake, da danshi, da sauran Lipton ɗin jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ƙofar ɗakinsa, bai amsa ba dama labulen a ɗage yake ta shiga.
Ta ajiye masa ta ce "Ina kwana?" Ba ta jira ya amsa ba, ta haɗa masa tea, ta tashi ta fita.
Aka jima ta dawo, ta shiga banɗakinsa ta wanke, ta ɗauki bokiti ta dawo, ta haɗo ruwan zafi na wanka, ta kai masa banɗakin ta ce "Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai ɗumi ne" idan ta ce mastern nan, sai ya ɗaga kai ya kalleta.
Ta ce "Yauwwa, master zan kafa ƙusa a toilet ɗin ka, idan ka gama wanka, ka dinga saƙale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ƙare da wuri"
Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ɗakin kamar ƙaramin yaro.
Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ƙamshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa daɗi.
Yana zaune ta gyare ɗakin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ƙarasa, ya kunna sigari a ɗakin. Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin ɗakin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin.
Ta maze ta ce masa "Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura"
A hasale ya ce "Ke, fita ki bar mini ɗaki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min ɗaki, ba zan wankan ba"
Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa riƙe da waya yana cewa "Kar ku raga musu, gani nan zuwa" ta miƙe tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana.
A haka yana ƙaurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri.
Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu'a Allah ya sa ba wani rashin jin zai je yayi ba.
Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi.
Yana fita ya tarar da 'yan uwan Alhaji mu'azzam da suka kawo kuɗi.
Suka gaggaisa, ƙanin mahaifin Alhaji mu'azzam ya ce "Gamu mun dawo, ɗanka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da haƙuri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ƙarasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can".
Gaban Baba ya faɗi jikinsa a sanyaye ya ce "Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da kuɗin aurenku".
Suka yi turus gaba ɗaya suka ce "Wace irin matsala ce haka?"
"Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku haƙuri, a bashi haƙuri dan Allah. Zan kawo muku kuɗin aurenku"
"Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu'azzam ɗin yayi?".
Baba ya ce "Ko ɗaya, ka san matar mutum kabarinsa, mu'azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi haƙuri"
Suka ce "To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi".
Suka amsa da "Amin"
Baba ya ce "Ku bani account number, na mayar muku da kuɗin auren"
Ɗaya daga cikin su ya ce "A'a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya"
Ya amsa da "Amin".
Bayan la'asar yara duk suna islamiyya, babu 'yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa.
A ƙofar gida suka haɗu da maman su halimatu a waje da wata maƙwabciyar su, suka gaisa ta ce "Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu".
"Wallahi Amarya, ba ƙi muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru".
Ranta bai yi mata daɗi ba ta ce "Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu" tayi gaba zuciyarta babu daɗi, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu.
Har dare ba ta sake ganin Al'amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al'amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba.
Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba.
Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba.
Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin yaƙe ta ce "Maman halimatu, sannu da zuwa shigo"
"A'a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?" Gaban Jauhar ya faɗi ta ce "Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?"
"A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi ɗin dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba".
Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce "Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba taɓa shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma".
Tayi ƙasa da murya ta ce "Yana anti daba can aka kai shi".
"Menene anti daba kuma? Ina ne?".
"Can in da ake kai 'yan daba, ki shirya ki je ki duba shi".
Ta ce "To na gode" bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata.
Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta faɗa, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta ɗora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata.
Su kansu yanayin jami'an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta taɓa zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce "Dan Allah wani nake nema"
"Wa kenan?" Wani ya tambayeta.
"Al'amin sunansa"
Ɗan sandan ya ce "Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama".
Ta ce "Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini"
Na kusa da shi ya ce "Ko viper take nufi?"
Ta ce "Eh shi, mai dogon zamani"
"Ya aka yi me zaki yi masa?"
"Wurinsa na zo, maƙwabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba".
"Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ɗin ba? Wacece ɗin sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban taɓa ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba"
Ta ce "Mijina ne"
Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ƙarama da ita.
"Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama'a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ƙarshe aka fito da shi aka ce aure yayi" waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi.
Ɗaya daga cikin su ya ce "Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka 'yar mutane fara sintiri saboda shi".
Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, 'yan sandan suna yi mata tambayoyi.
Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ƙaraso gaban kantar ya kalleta ya ce "Me ya fito da ke?"
"Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba"
Ya sake kallonta ya ce "To ware ki koma"
Jauhar ta ce "To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?"
Al'amin ya ce "Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware" haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara.
Ta ɗora leda ɗuake da flask ɗin Abinci ta ce "Gashi abinci ne na kawo maka" sai da ya ɗan yi shiru yana kallonta.
Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu.
"Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci"
Bai saurari ɗan sandan ba, ya ɗauki abincinsa ya koma gefe.
Ya buɗe, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa "Ka fara wanke hannunka"
Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin.
"Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?"
"Mmm" ya amsa yana cigaba da cin abincin.
"To yaushe zasu sake ka, kar ka yi rashin lafiya, saboda cizon sauro" shi dai yayi shiru yana cin abun sa.
Ya gama ci ta bashi ruwa, ya karɓa ya zuƙe, ta ƙara masa wani ya shanye.
Ta ce "Officer, to zaku sake shi? Bai yi komai ba"
"Ke, da wiwi muka kama shi da ƙwayoyi, sai kuma ki ce bai yi komai ba? NDLEA zamu kai shi".
Jauhar ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba in sha Allah, Master ka basu haƙuri su ƙyaleka mu tafi" miƙewa yayi tsaye, ya nufi hanyar komawa cikin ceil.
"Officer to, idan na sayo maganin sauro da ashana, zaku bar shi ya kunna?"
Gaba ɗaya sai ta basu tausayi, ya ce "Sayo"
Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya ya waiwayo ya bi bayanta da kallo.
"Viper, wai dan Allah ka bamu labari, wurin wani bokan ka kai 'yar mutane da iyayenta, suka aura maka 'yar su?"
Shi dai ya ƙarasa ya koma cikin ceil, yayi zamansa, ba a jima ba, sai gata da maganin sauro, da ashana.
Suka karɓa a nan kan kanta, suka ce ta tafi.
"Dan Allah ku bari na sake ganinsa"
"Ke wuce ki bar nan, da ki ka samu ma aka bari ki ganshi?"
Ba ta karaya ba ta sske cewa "To ana bashi abinci? Ko ina kawo masa na dare ma"
"Au uban wa ki ka ajiye da zai bashi abinci a nan? Ware ki tafi"
Jiki a sanyaye ta ce "To, zan tafi ga wannan dan Allah officer ko buredi ku bashi" ta ajiye musu ɗari biyar sannan ta ce "Dan Allah kuma ku yi haƙuri, kar ku kai shi NDLEA, dan girman Allah in sha Allah zai daina, ba zai ƙara ba ma dan Allah"
"Ki je ki kawo dubu hamsin, sai mu sakar miki shi"
Tayi shiru, har ga Allah ba ta da ita, ba ta da dalilinta amma ta ce "To zan kawo, amma dan Allah kar ku kai shi, zan kawo muku in sha Allah"
Ta fito daga wurin, tana tunanin ina zata nufa ta samo dubu hamsin a sake shi.
Ayshercool 08081012143
23 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Tun da ta hau adaidaita sahu, tunani take yi, yaya za ta yi ta samu dubu hamsin ta kai, a sako shi. Ta san muddin aka kai shi NDLEA case ɗin tsayi zai yi, ba zata musa an ganshi da kayan maye ba, tun da yana sha.
Ta koma gida tayi salla, amma abun duniya ya isheta, ta kasa ko cin abinci, tausayinsa duk ya cika mata zuciya, jikinsa yayi ruɗu-ruɗu da cizon sauro, gashi almu sun nuna ba abinci ake ba shi ba.
Baba kuwa abun duniya ya dame shi, yadda ya ji kunya a idon iyayen Alhaji mu'azzam, ace sun kawo kuɗi sun gama magana, amma ya aurar da ita ga wani, ko gaya musu bai yi ba, ya rasa me yake yi masa daɗi, har sai da zakiyya ta fahimta ta ce "Baban su Saifu, wai lafiya kuwa? Tun da ka yi baƙi jiya, gaba ɗaya ka rasa nutsuwar ka"
Ya sauke numfashi ya ce "'yan uwan Alhaji mu'azzam ne, suka zo suna bayar da haƙuri a kan jin su shiru da aka yi. Wai za ayi mata visa ayi auren a tura ta can"
Waro ido tayi ta ce "Sai kuma ka ce musu me?".
"Na aurar da ita" yayi maganar a sanyaye yana sake jinjina wautar da ya yi.
"Ba a haka fa, sai ka ce musu Allah ne ya ƙaddara a hakan, amma akwai yayyenta, ko hafsa ba sai a maye gurbinta da ita ba, hafsa ba ta fi jauhar komai ba ma? Ai bai kamata a bari ya tafi haka ya tsallake gidan nan ba".
"Zakiyya, kun saka na yi abun da yake damuna, na cuci 'ya ta ba gaira babu dalili, na aurar da ita ga mutumin da ba na kirki ba, na rasa yadda aka yi, lamarin nan ya faru, kunyar haɗuwa da jauhar ma nake yi, na kasa komawa gidanta, zuciyata zafi take yi mini"
Zakiyya ta ce "Jauhar fa an gama babinta, sai a fuskanci 'yan uwanta, bai kamata a bari mutumin nan ya tafi haka ba"
"Zakiyya, dan Allah ki bari na samu nutsuwa, ni ban san ma meyake damuna ba, dan Allah ki bari na ji da abun da yake damuna"
Ta kwantar da murya ta ce "Babu wani abu fa da yake damunka, kai ne ka ke neman ɗorawa kanka matsala, amma komai mai sauƙi ne, idan ya dawo ba sai a lallaɓa shi a bashi Hafsa ba ya aura".
Baba ya ce "Na ji, amma dai yanzu ki ƙyaleni" ya ɗauki hularsa ya saka ya fita.
A tsakar gida ya tarar da su surayya, aiki duk ya kacame musu, aiki ba aiki, wanda da jauhar na nan, ita kaɗai take yi suna mimmiƙe kamar kifi a fridge.
Suna ta yi masa a dawo lafiya, ya dawo da baya ya tsaya, ya kalle su ya ce "Surayya, kun je gidan ƙanwarku kuwa kun ganota?" Duk suka yi shiru, suka kasa amsa masa.
"Yakamata ku je ku ga in da aka kaita, ita ma ta ji daɗ".
Mama ta fito daga kitchen ta ce "A'a fa, ka san dai yadda mijinta yake, ba zuwa gidanta ne ba za ayi ba, kar mutum ya je ya illata shi". Yayi shiru bai ce komai ba.
Jauhar kuwa kasa nutsuwa tayi, har sallar nafila tayi mussaman tana fatan Allah ya sa kar a kai Al'amin NDLEA.
Duk yadda ta kai ga tunani, ta rasa mafita, bacci ya gagareta, a gidanma ya ta ƙare da sauro, ina ga shi da yake can, ta yi ta fatan Allah ya sa su saya masa buredin nan su bashi, sai kuma ta tuna ba ta bayar da kuɗin da za a saya masa ruwa ba, gaba ɗaya ta shiga damuwa, haka har garin Allah ya waye.
Ta ji ƙarar babur ɗin malam lawan alamar ya fita, tana ta tunanin ko shiga za ta yi gidan, ta yi wa maman halimatu magana, ko akwai taimakon da za ta iya yi mata.
Tana cikin tunanin, maman halimatu ta shigo, suka gaisa jauhar ta ce "Yanzu nake tunanin zuwa gidan wurinki".
Maman halimatu ta ce "Yaya kin same shi ɗin?"
"Eh yana can, sun ce na kai dubu hamsin a bayar da belinsa, amma wallahi bani da ita"
"To yanzu ya za ayi?"
Jauhar ta ce "Wallahi ban sani ba, shi nake ta tunani"
"To ki kira gidanku mana ki faɗa" ta girgiza kai ta ce "A'a, daga yin auren sai na fara kai musu complain, a'a gara na rufa masa asiri na samu ya fito"
"Aikuwa Jauhar sai ki yi tunanin in da zaki samo kuɗi".
Tayi saurin cewa "Dan Allah ko akwai wanda zaki haɗa ni da shi, ya sai carfet ɗina?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh akwai wata dillaliya, kusa da titi gidanta yake"
Cikin ɗoki jauhar ta ce "Mu je ki rakani maman halima".
"Shikenan, amma Jauhar kina me ki ka auri mutumin nan, gashi daga aurenku kin fara wahala, da kyanki da ƙuruciyarki, kin auri wanda zai wahalar da ke".
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Maman halimatu ku daina aibata shi dan Allah, ku din ga yi mana addu'a"
"To Allah ya kyauta"
Jauhar ta saka hijjabi, suka tafi gidan dillaliya, sai dai bata nan, aka kirata a waya, ta ce sai yamma zata dawo, zata biya gidan maman halimatu, su je gidan Jauhar ɗin.
Wunin ranar jauhar kamar ta yi hauka, saboda dillaliya ba ta zo ba, sai tunanin halin da yake ciki take yi.
Sai wajen ƙarfe biyar sannan ta zo, ta ga carfet ta ce zata saya dubu goma.
Maman halimatu ta ce "Haba sahura, wane irin dubu goma, bai fi sati biyu ba ca carfet ɗin sabonsa dubu kusan sittin ne fa".
"To ku ɗauka ku mayar kasuwar mana, tun da an shimfiɗa ai ya zama taoho".
Jauhar ta ce "Bakomai na yadda" ba ta da burin da ya wuce ta ga Al'amin ya fito.
Sahura ta ce 'Saboda kin ban tausayi, na saya dubu sha biyu, bari na baki kuɗin.
Maman halimatu ta ce "Wallahi sahura shiyasa da yawanku ba kwa arziki dillali, duk cuwa-cuwar ta ku, a tsiyace ku ke mutuwa"
Sahura ta ce "Oho miki dai"
Ganin ta fito da kuɗi da yawa, ya sanya jauhar shiga kitchen ɗin ta, ta ɗauko blender da set na tukwanenta masu kyau, ta cewa dillaliya su ma ta saya.
Maman halimatu ta ce "Jauhar, idan 'yan gidanku suka gane kin sayar da kayanki fa?"
Sahura ta ce "Wallahi uwar su halimatu ke 'yar baƙin ciki ce, ke kika saya mata?".
Jauhar kamar ta yi kuka ta ce "To ya zan yi maman halimatu, bana son zamansa a wurin nan, sauro ma kawai ya ishe shi"
Sahura ta ce "Allah sarki yarinya, Allah ya mayar da alkhairi, idan an tashi sayar da wasu ma ki kira ni" Da ƙyar ta bawa Jauhar dubu ashirin da huɗu gaba ɗaya. Wanda a ƙalla sun kai kayan dubu ɗari da wani abu.
Ƙoƙarin nemo wani abun take, maman halimatu ta hanata, ta ce ta bari gobe ta je station ɗin, ta basu haƙuri ta ce musu abun da take da shi kenan.
Jauhar ta ce "Ki na ganin za su karɓa kuwa?"
"Za su karɓa mana, ai kin yi ƙoƙari" kamar ta janyo wayewar gari, ta din ga addu'a Allah ya sa su karɓa su sake shi.
Da wuri ta gama komai, wurin ƙarfe goma da rabi ta fita, shi ma maman halimatu ce ta hanata fita da wuri, ta ce mata ba da wuri suke zuwa ba.
Suna ganin Jauhar suka ce "Madam ya aka yi ne? Kin sake dawowa ganinsa ne?"
Ta ciro kuɗin ta ce "Gashi dan Allah yallaɓai ku sake shi, sukaɗai na samo dan Allah ku yi haƙuri"
Ya zuba mata ido ya ce "Shekarar ki nawa ne?"
Ta ce "Na kusa shiga sha bakwai, dan Allah ku yi haƙuri"
"To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, karɓi kuɗinki, ba zamu sake shi a kan wannan ɗan kuɗin ba, kotu ma zamu kai shi"
Kawai ta saka kuka, "Dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison"
Ɗaya daga 'yan sandan ya ce mata "Yi haƙuri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi"
Kasa daina kukan tayi, hannunta riƙe da kuɗin, wani ɗan sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al'amin da wani mutum.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a ɗaure babu walwala.