Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 22

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 22

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 22: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 22. Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a…

4,485 words

Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci"

"Wannan fa me aka yi mata take kuka?"

"Sir, matar Viper ce" ya kalleta ya ce "Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?".

"Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta.

Ya kalli 'yan sandan ya ce "Waye ya ce ta kawo dubu hamsin"

"Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka"

Nan ya hau yi musu faɗa, suka din ga bayar da haƙuri, Al'amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru.

Walid ya ce "Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana"

A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa "Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?" Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata.

"Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?" Tsaki ya yi yayi gaba.

Walid ya ce "Yi haƙuri mu je, rabu da shi ya ƙarata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi" suka tari a daidaita sahu suka tafi gida.

Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid.

"Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah"

Ya tsaya ya ƙarewa ƙofar gidan malam lawan kallo, yayi ƙwafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba.

Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi.

Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ƙusar rataye soso a banɗakin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito.

Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ƙara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida.

"Ke!" Ta ɗago ta kalleshi.

"Meye sunanki ne?"

"Jauhar"

Ya kalleta ya ce "Me? Angela?"

Murmushi ta yi ta ce "Angela kamar wata mage, sunana Jauhar"

Guntun tsaki ya yi ya ce "A saka muku normal suna, sai dai a saka ƙaƙale-ƙaƙale da iyayi, ni ba zan iya ba"

"To ka kirani da fatimata fatima zahra" wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ƙaunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi.

Ya maze ya ƙarewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ɗin ta sannna ya ce "Zo nan"

Ta fito ta ce "Gani"

"Wa ki ka sayar wa carfet ɗinki da kwanukanki?"

Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani?

Ya ƙare mata kallo ya ce "Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan kuɗin da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ƙarya kuma jikinki ya gaya miki"

Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai.

Bai ce mata komai ba, ya fita.

Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta.

Ta tashi ta ce "Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai.... Haɗiye maganar tayi, da ya sako ƙafarsa cikin isa tsakar gidan.

Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet ɗin, a shimfiɗe a falonta.

Ya ce "Liti, ku naɗo mini carfet ɗin nan"

Ta waro ido ta ce "Malam lafiya?" Walid ya zaro wuƙa ya ce "Ki ka kuma magana, sai kin ɗaware daga sararin nan yanzun nan" daga ita har sauran matan, suka hau tsuma.

Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka naɗo carfet.

Viper ya ce "Dubu sha biyu ki ka saya ko?" Ta jinjina masa kai.

Ya ce "Ɗaukko mini sauran kayan da ki ka karɓa a wurinta" jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su.

Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce "Ɓarauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta kuɗinta".

Liti ya zaro kuɗi zai bata, Al'amin ya ce "Wait, ta riga ta shimfiɗa a ɗakinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet ɗin ku kai mini gida.

Haka kuwa aka yi, suka cilla mata kuɗi, suka kwashe kaya suka tafi.

Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana ɗebe mata kewa.

Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce "Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ɓata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani"

Baki buɗe ta ce "Master, karɓowa ka yi, kuɗinta suna wurina fa, Allah zai kaman..."

"Na ba ta kuɗinta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ɓaci".

A hankali ta ce "Na shiga uku".

*** Matasa ne a ƙalla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa.

Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba ɗaya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa.

"Kai gayu akwai matsala wallahi" gaba ɗaya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa.

Ya ce "Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?"

Ɗaya daga cikin su ya miƙe ya ce "Ƙarya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa".

"Nustu, ni ma ban sani ba sai ɗazu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan".

Ɗayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce "Guduma gaskiya kar dagus ɗin ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?".

"Guys mafita ɗaya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani ɗaya ko?"

"Me ka ke nufi?"

Guduma ya ce "Dole ɗaya ya bi ɗaya"

"To waye zai bi wani?"

"Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi'a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai sa a din ga jin tsoranmu"

Wani matashi ya ce "Ƙarya ne wallahi, babu wanda ya isa ya zo unguwarmu mu yi masa mubayi'a ba a isa ba".

"Kai Kwano, bari na yi maka wani lissafi, duk sarkin da ya zo garinka ba da ziyara ba, ya shafe awanni arba'in da takwas, a irin harƙallarmu, to ɗayan biyu, ko dai ɗaya ya bi ɗaya, ko kuma a yaƙi juna, a kama sarki ɗaya da mutanensa a matsayin ganimar yaƙi, mu rayu a matsayin bayinsa, harƙalar da Mai zamani yake yi, ta ci uban tamu, ba sa'anmu bane ba, mu yi abun da ya dace, idan kuma mu ka bari rigima ta ɓalle, wallahi a unguwar tamu, zamu rayu kamar bayi ne amma ku yi tunani".

Can Al'amin kuwa yana zaune a station, ga mai unguwar da yake da sauran mutanen unguwa.

Yana zaune yana kallonsu, suna ta ɓaɓatun gaskiya ya tashi ya bar musu unguwa, saboda bad record ɗin da suka samu, a kansa daga in da ya baro, kuma nan ma ya zo yana yi musu shaye-shaye kar ya ɓata musu yaran unguwa.

Suka yi suka gama, yayi shiru kamar mai zancen zuci, suka yi suka gama, D.P.O ya ce "Malam Aminu, ka ji abun da mutanen unguwar da ka tare suka ce, me za ka ce?" Sai da ya ja wasu seconds, sannan ya ɗaga kai, ya kalle su da jajayen idanunsa masu matuƙar kwarjini, duk suka yi shiru, suna sauraren sa, ya ce "Haryanzu ban ji an ce ga abun da na yi ba ai. Ba zan ce komai yanzu ba, gobe in Allah ya kaimu, mu haɗu a nan ƙarfe huɗu na yamma, zan faɗi abun da na yanke".

D.P.O ya ce "Ina fatan ba wata ɓarnar zaka yi ba?"

"Ba na sara sai an zo ramina" daga haka bai kuma cewa komai ba, ya tashi ya fice, ba tare da ya jira iznin hakan ba.

D.P.O ya ce "Abun da nake so da ku shi ne, ku bi yaron nan a sannu a samu maslaha, kar ku yi wani abu da zai tunzura shi, ya fara yi muku fitina a unguwa, ku bari mu bi a hankali mu sasanta, ɗan ƙasa ne yana da damar zama a in da yake so, ku bi a hankali ayi musu sulhu".

Shi kuwa yana fita, ya kira wayar liti, bugu biyu ya ɗaga. "Liti, nan da mintuna arba'in zuwa awa ɗaya, ina son ka tattara mini, duk wasu yara marasa ji a arear unguwar nan da nake da kewayenta, duk wanda ya yi gardama, ayi masa ɗaurin igiya da swizaland gaba da baya, a layin gidana nake son su taru".

Liti ya amsa da "An gama shugaba"

Sahura kuwa, sai da ta je har gidan maman halimatu ta ƙare mata cin mutunci, a kan yadda Al'amin ya je har gida, ya ƙare mata tanadi, a kan ta sai kayan matarsa, maman halimatu ta din ga ba ta haƙuri, ta ce su shiga gidansa su yi magana da jauhar ɗin, amma ta ce ai ba mahaukaciya ba ce ita, da zata shigar masa gida ya ritsata ya kashe.

Jauhar tana ta aikin stone, ta ji ana wata irin busa a unguwar, kamar da ƙaho ake yin busar, irin bushe-bushen da aka din ga yi, ranar ɗaurin aurenta, dan haka gabanta ya faɗi ta shiga cikin tsoro.

Sannu a hankali, hayaniya ta fara cika layin nasu, da surutan matasa, ɗaki ta gudu ta rufe ƙofar falo, dan tunani ta fara yi, ko yaran madaki ne, gashi ba waya ce da ita ba, balle ta kira Al'amin

Kafin ya ƙarasa layin gidan, liti ya kira shi a waya, ya sanar masa sun fara taruwa matasan, dan haka bai bi ta cikin ba ya bi ta baya.

Jifff! Ta ji dirar abu a tsakar gida, ta katanga ya diro gidan, ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon, amma a rufe ya jijjiga ya jijjiga amma ya ji a rufe. Ya shiga bugun ƙofar kamar yaƙi, ƙulewa tayi a ɗaki, ta hau addu'a, tare da tunanin ta ta ta ƙare, yaran madaki sun zo neman Al'amin, ko sun zo sassarata.

"Ke malama ki zo ki buɗe mini ƙofa" sai da ta ji muryarsa, sannan ta fito ta buɗe, ta kalle shi, ta leƙa tsakar gida ta ce "Ai ban san kai ba ne, biyoka aka yi ne?" Wani irin kallo ya yi mata, ya ce "Matsa ki bani wuri" ta matsa ta bi bayansa tana surutu "Master ka daina dirowa ta katanga dan Allah, gaba ɗaya na tsorata wallahi, na zata madaki ne, suka zo nemanka na ji sai busa ake yi ga warin kayan shaye-shaye...... Haɗiye maganar tayi, da ya waiwayo yana yi mata kallon warning.

Ta ce "Yi haƙuri, ka ga abokanka sun dawo da carfet ɗin, wai wanke shi suka yi, amma dai yakamata na je na bawa dillaliyar nan haƙuri, ai ka ga an shiga hakkinta, har gida ta zo tayi wa maman halimatu masifar abun da ka yi" ɗakinsa ya shiga, ya kulle ƙofar ya saka sakata ya bar ta a bakin ƙofa.

Sai abun ya bata dariya, kafin awa ɗaya matasan nan sun kusa cika layin nan, sai hayaniya suke yi.

Malam lawan kuwa, a waya matarsa ta kira shi, ta ce kar ya kuskura ya dawo yanzu, 'yan daba sun cika layin nan.

Jauhar na ɗakinta, tana aikinta, ta ji yana buɗe gate, a razane ta fito saboda yanayin bushe-bushen da ake yi, ya tabattar mata da akwai matsala.

Yana fita wurin yayi tsit, kamar ba su ne suke hayaniya ba da.

"Sai da kai sarki, ƙaramin dodo magajin babban, ko ma in ce ka ɗara shi. Mu na yi maka maraba da zuwa wannan unguwar, mun fito ƙwanmu da kwarkwata domin yi maka mubayi'a". Cewar guduma yana geɓare baki, yanayin yadda yake maganar kawai a buge yake.

Viper ya goya hannunsa a bayansa, ya ce "Manyanku sun kai ƙarata a kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ni da ku zan yi wannan yarjejeniya. Abu goma a cire bakwai a tara da ɗaya zan gaya muku, a bi iyaye, ayi caji kaɗan saboda lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa, a kiyayi taɓa kayan wani. Babu zubar jini a tsakanin ku, ko duk wani wanda yake unguwar nan, abu na ƙarshe mafi muhimmanci da fari salin alin na so zama a unguwar nan, wataƙila na ɗan lokaci na baku wuri, amma tun da abun ya zo da haka, sarki biyu ba zai yi sarauta a zamani ɗaya ba. Ko dai mutum ya yi mubayi'a ko ya bar unguwar nan. Kar kuma a kuskura a matsi ramina idan ba haka ba, zan yi ɓarna. Mu haɗu da shugabannin dabar Unguwar nan da kewayenta gobe a station ɗin unguwar nan, domin yarjejeniyar zaman lafiya. Kuna iya samfewa"

Su ka din ga yi masa kirari, yana jin kansa yana sake fashewa.

Bayan sun watse, maman halimatu ta shigo, tana ba ta labarin abun da sahura ta zo ta yi mata.

Jauhar ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri maman halimatu, dan Allah ki bata haƙuri, ba yadda zan yi, na so mayar mata ma da kayan, ya ce idan na sake sayar da wani abu, zai ɓata mini rai. Wallahi yana ankare da komai, ko cokali na sayar zai gane, ni har tsoro yake bani, bari na baki dubu goma a kuɗin, ki kai mata ta ƙara ki bata haƙuri dan Allah"

Maman halimatu ta ce "To shikenan, Allah ya kyauta" ta bata dubu goma ta kaiwa dillaliya, ita kuma ta bata kyautar dubu biyu, sauran kuɗin kuma ta ɗan yi musu cefane dan kuwa shi babu ruwansa.

Washegari tun ƙarfe biyu, su mai unguwa suka koma police station, suna jaddada dole a kori Al'amin, dan jiya kafin su je gida ya rigasu zuwa, ya tara musu dandazon 'yan daba a unguwa.

Al'amin bai je ba, sai ƙarfe huɗu tare da rakiyar su walid, da kuma matasan yara 'yan shaye-shaye da sun kai ashirin da wani abu.

D.P.O ya ce "Lafiya, waɗanan fa?"

Al'amin ya kalli mai unguwa, ya nuna masa guduma ya ce "Ka san wannan? Ko ba ka bani amsa ba ɗanka ne, meyasa ba ka kore shi daga unguwarka ba? Ko dan shi ɗanka ne?. A wannan ba wannan matasan wakilai ne da suke jagorantar wasu yaran a ƙarƙashin su, wanda duk a cikin unguwarka suke, kana nufin a sati biyu da zuwana duk ni na lalata su? Har na tare a unguwar nan, ba su san waye ni ba, sai jiya da na saka a tara mini su. Dama can kuna da lallatun yara, harƙallata nake, ba na lalata ɗan kowa, duk ɗan wanda ya lalace, dama lalataccen ne. Ina sake maimaitawa ba na harbi sai an matsi ramina ko in da nake. Ga mafita zan bayar, wadda ba zan ƙara ko rage wani abu daga abun da zan faɗa ba. Mafita biyar ce ba uku, ko dai a haɗa a kore ni, da ni da yaran nan, ko kuma ku yi wa gidana kuɗi ninki uku, yadda zai isheni na sai wanda ya fishi, na bar muku unguwa, idan ba haka ba....... Ba na ƙarasa magana sai dai na aikata.

Duk sai suka yi ɗif D.P.O ya ce "Mai unguwa mai ku ka yanke?"

Shiru suka yi ba su ce komai ba, D.P.O ya ce "Tashi ka ja zugarka ka tafi, babu wani abu in sha Allah".

Ya miƙe ya ce "Galibi yaran nan secondary school drop out ne, wasunsu idan son zuciya ne ya kai su wannan halin, wasun su laifinku ne, ko dai ku nutsu ku gyara rayuwar matasan yaran nan, ko kuma su cigaba da lalacewa kuna rusa al'ummarku da hannunku" yana gama maganar suka fice da shi da su.

D.P.O. ya ce "Yaron nan fa ya san abun da yake yi, jiya kuna barin wurin nan, daga can unguwar su, Aka kira ni aka ce a gargaɗe ku, babu ruwanku da shi, yaron 'yan siyasa ne, dan Allah ku lallaɓa ku zauna lafiya da shi.

Bayan sun bar station ɗin, wani irin ɓacin rai ya din ga cizon zuciyarsa, a duk lokacin da aka samu matasa ire-iren sa, al'umma ba su da wani burin da ya wuce, yin watsi da shi, da nesanta kansu da ire-iren su, bayan su ne ƙashin bayar lalacewar ta su.

Yau abun na sa ya fi na kullum, domin kuwa a buge ya dawowa jauhar, wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, ya wuce ɗakinsa, ba ta kula shi ba ta koma gefe ta zuba masa ido.

Washegari da safe shiru bai fito ba, ta leƙa ɗakinsa, ta tarar da shi a kwance yana bacci, gefensa ga kwalin ashana da na taba, ga kwalabe.

Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, a hankali ta fara magana "Sun san da haka suka aura mini kai, Allah na roƙi ka bani mafita ka zaɓa mini shi, Allah ka kawo mini mafita, Allah ka shirya mini shi, Allah shiriya taka ce, Ni da shi duk bayinka ne, Allah bai gagari ikonka ba, Allah ka shirya min mijina. Allah ka sa ya daina abun da yake yi, Allah kar ka sa ya mutu yana saɓa maka" ta yi maganar tana kuka.

A hankali ya yi juyi, satchets ɗin ƙwayoyi, suka zubo daga aljihun gaban rigarsa, ta saka hannu ta kwashe su, da kwalaben, ta hau caje ɗakinsa, duk wani nau'i na abun da ba ta yarda da shi ba, sai da kwashe daga ɗakin.

A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa, ita kuma ta fice daga ɗakin.

Da ƙyar ya iya tashi, dama bayan sallar asuba, ya sake yin shaye-shayen.

A yunwace, ba tare da ko wanke baki yayi ba, ya hau cin abinci, saboda kayan shaye-shayen sun rarake masa ciki, ji yaya ko tsayuwa ba zai iya yi a kan ƙafafuwansa ba, sai da ya gama ci ya dawo dai-dai.

Ya shiga banɗaki, ya wanke bakinsa ya fito falo, ko ɗaga jauhar ba ta yi ba, balle ta kalleshi.

Ya je gabanta ya miƙa mata hannu.

Ta ɗago ta kalleshi. "Bani abun da ki ka caje mini ɗaki ki ka ɗauka" gabanta ne ya faɗi, mutumin da yake bacci ya aka yi ya san ta ɗauka?.

"Bani mana"

"Na zuba a shara an zubar!"

(Yau juma'a mu yawaita salati, ga shugaba Sallallahu alaihi Wasallam)

Ayshercool 08081012143

24

🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Duk da cikin matsanancin tsoro da tashin hankali ta bashi amsar, amma ta tattaro jarumtarta ta dake, ta ƙi kallonsa.

"Ai ɗago kai zaki yi ki kalle ni, ki bani amsar da ki ka faɗa yanzu"

Ta yi shiru, tana jiran yayi mata duk abun da zai yi mata.

Ya ce "Dama ba ni na kawo ki gidan nan ba, kuma ba ni na ce a kawo ki ba, idan kin gaji ki tafi dama kin isheni, kuma idan ki ka kuma zuwa kaina ki ka tsaya ki na kuka, sai na ɓarar da ke".

Gabanta ya faɗi, a buge ta tarar da shi yana bacci, ya aka yi ya san duk abun da ya faru, sai dai kalmarsa ta ƙarshe da ya ce a kawota ba, ta yi mata ciwo.

Ta zata zai yi mata tijara, da ta ce ta zubar, sai kuma ta ga ya tashi ya nufi hanyar fita, kawai ta fara kukan da ba ta san na menene ba ma.

Waiwayowa ya yi yana kallon ikon Allah, da ta samu bai casata ba, da ta ɗebe masa kaya,ta ce ta watsar kuma ya san ƙarya take yi ba ta zubar ba, shi ne saboda samun wuri har da ɓare baki tana kuka.

Sosai yarintarta ta fito, yadda ta tura baki tana kuka, tamkar irin 'ya'yan madarar nan shagwaɓaɓɓu.

Kawai ya girgiza kai ya fice, kafin ta fusata shi.

Rahila da Zakiyya kuwa sai shewa suke yi, tare da farincikin yadda shawarar da suka yanke ta yi amfani.

Zakiyya ta ce "Ni fa na zata yadda yake ɗin nan, ana kaita ya korota tun da ba son auren yake yi ba, amma dama na san ko zai daketa ya cinye abu ne mai wahala ta faɗa ko tayi yaji, juriya ce da ita kamar dutse shegiya".

Rahila ta ce "Shi ɗin me? A duniya akwai namijin da zai ce ba ya son mace ne, ke ban da abun makirci wannan yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa, wa zai ce ba ya so, dan ma ƙarama ce, gashi ai sati biyu kenan sun yi luf daga shi har ita".

"Wallahi na zata ba zai saurareta ba, ƙila ma ya korota, a yadda ki ke bani labarin yadda ya zama, da kuma rashin jin da yake yi".

"Ba fa mahaukaci ba ne, idan ta iya zama da yaron nan, ba lallai ki ji kansu, ai duk wannan bala'in da nake yi da tashin hankali a kansa, wasu lokutan shi da 'yar uwassa yana yi mata abu, ke har magana shahida take gaya mini a kansa"

Cikin mamaki zakiyya ta ce "Kai haba dai?"

"Wallafa Allah, ba suna school aka yi auren ba, sai da na kusa dukan yarinyar nan, ƙiri-ƙiri wasu lokutan take nuna in daina takurawa ɗan uwanta, aikuwa ubanta nake ci".

"Gaskiya kar ki zauna a kanta, ita ana neman mafita tana shirme? Ni kam yanzu menene abun yi ne? Ƴan uwan Alhajin nan fa sun zo, wai ayi aure ayi visa ta bi shi china"

Rahila ta ce "Aikuwa sai dai a lahira idan ana zuwa".

"Aikuwa, wai yanzu ya fasa dawowa nan da watan ɗayan ba, ina nan dai ina ta lallaɓa uban, a kan ya haɗa shi da hafsa".

"Ai ba iya lallaɓa shi ba, malamai zamu cigaba da yi, in sha Allah sai abub nan ya tabatta, ita waccan ai an gama da babinta".

Zakiyya ta ce "Haka ne kam, to Ubangiji Allah ya amince, ni dai ko nawa ne zan kashe, idan ta aure shi na san zan mayar da kuɗina".

"Kar ki damu ai ba zama, za ayi duk mai yiwuwa, hafsa zata auri mutumin nan".

***

"Ku yanzu a ganinku ya dace mu na ji mu na gani, baƙo ya zo unguwarmu ya saka mu yi masa mubayi'a? Baƙo ne fa, mu kuma a nan aka haife mu muka girma, muka kafa sabgar nan, kuma ace sai dai mu bi shi, ba dai ya bi mu ba?"

"Wallahi nima dai haka na gani, abun yayi mini ciwo, guduma ya fi kowa bani haushi shege, ai wallahi sai dai a rabu biyu, ayi ta zubar da jini, har sai ya yarda ya bi mu, ba wani shege da zai shigo arearmu ya buɗe mana ido, mu zagaya mu ji ta bakin sauran, mu ji su waye suka bi, kuma suwaye za su yi tawaye".

Ɗaya matashin, ya hurar da hayaƙin wiwi ya ce "Mu tabattar da suwaye a tare da mu tukuna, zamu yi masa sara na warning, idan ma ta kama, mu kawar da shi da ga sararin nan, ba wani ɗa da zamu yi wa biyayya, tun da muka yi wa iyayenmu ma tawaye".

Suka cigaba da tattaunawa a kan yadda za su ɓullowa lamarin, su yi maganin Al'amin.

***** Kamar masu kasa gyaɗa, haka suka kewaye farantin wiwi, suna naɗawa a takarda. Suka mayar da wata ƙwaya garri, suka haɗata a cikin wiwin, ita ma suka ɗaura ta daban.

Matasa ne suka din ga shigowa da ɗai ɗai, suna karɓa, suna zube balance, suna karɓar kaya.

Liti ya shigo cikin ɗakin da Al'amin yake, da robar abinci, ya zauna ya ce "Taso ga abinci"

Ya tashi zaune ya kalli miyar kan abincin, sai ya ji ƙyanƙyamin abincin, miyar sam ba ta ji mai ba, ga ta ba ta soyu ba, ba irin wadda waccan taɓararriyar yarinyar take bashi ba.

Guntun tsaki ya ja, Walid ya ce "Lafiya?".

"Na ƙoshi"

"Meyasa?"

Ya girgiza kai ya ce "Bakomai".

"Ka ce mini kawai, abincin amarya zaka je ka ci, wai mu ko sau ɗaya ba zaka kawo mana abincin na ta mu ci ba? Sai dai ka yi ta ci kai kaɗai?".

Kai tsaye ya ce "Ba zan kawo ba"

"To ka ƙarata, ku ci ku kaɗai, dama ni naga kamar haushina ma take ji, ban san me nayi mata ba".

Ya tashi yana fatan Allah ya sa ya je ya tarar ta yi abinci. Sai kuma ya tuna kukan da tayi kan ya fito, ƙila ma ba ta yi girkin ba.

Sai dai kafin ya ƙarasa gidan, aka tsuge da ruwan sama, dan haka ruwa yayi masa duka, yayi ta sauri ya ƙarasa gida, ya san ƙarshenta ruwa yau ma ya shigar mata falo.

Sai dai yau aka yi sa'a, ruwan bai shiga da yawa ba, sai dai tsakar gidan ya cika da ruwa.

Tana ɗakinta tana salla, ya fara cire kayan da suka jiƙe, ta shigo da sallama, sai dai cikin matsanancin hanzari, tayi wani irin burki, ta juya.

Shi mamakin ta yake yi, sam ba ta da zuciya ba ta fushi.

Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Ina da ruwan zafi a flask, na kawo maka ka yi wanka, sai ka ci abinci kar ka yi mura saboda ruwan da ya dake ka?".

"Kawo" sumi-sumi kamar mara gaskiya.

Ihunta ya jiyo a tsakar gida, bai san ya aka yi ba, sai ganinsa yayi a tsakar gida, cikin hanzari yana zaton wani abun ne ya sameta, tayi jifa da flask ɗin a gefe, Allah ya sa na silver ne tana ihu, ta maƙale a jikin bango.

"Ke menene? Meyafaru?"

"Kwaɗo ne, zai riƙe mini ƙafa"

Ji yayi kamar ya ƙarasa, ya kwaɗeta, wai kwaɗo take yi wa wannan ihun.

"Zaki rufe mini baki ki zo ki wuce, ko sai na zo na tumurmusa ki?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull