Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 29
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 29: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 29. Ya mayar da wayarsa aljihunsa ya ce "Shikenan, maganar da…
4,462 words
Ya mayar da wayarsa aljihunsa ya ce "Shikenan, maganar da nayi miki, ki yi tunani a kai, a ɓangarena ni ina ganin hakan shi ne mafita kawai, amma ki yi tunani abun da ki ka yanke, ki sanar da ni".
Dummm ƙirjinta ya buga, kenan haryanzu yana kan bakansa? Ba ta ce masa uffan ba, ya fice.
Rasa abun yi tayi, duk da ba ta da tsarki, tayi alwala ta zauna ta kalli gabas, tayi ta addu'a a kan lamarin rayuwarta.
Can wurin su Walid ya tafi, in da suke zama su yi shaye-shaye, su naɗa wiwi.
Walid ya kalli Al'amin ya ce "Maza lafiya kuwa? Yanayinka ya nuna kamar akwai damuwa".
Banza ya yi wa walid, dan haka shi ma ya share shi, ya cigaba da aikin gabansa.
Sai kuma can ya ce "Mai laya"
"Na kiyayi mai zamani, ya aka yi?"
"Dama yara matasa suna hawan jini ne, ba sai tsofaffi ba?"
Ya ce "Eh to, na ji an ce akwai wanda ake haifar su da shi ma, amma hawan jini a matasa, maybe damuwa ce ko gado".
Ya jinjina kai.
Liti ya ce "Maza ko kai hawan jinin ke damu? Kana da 'yar madara, ai ba zaka yi hawan jini ba"
Tsuke fuska ya yi, jin liti ya kira jauhar da 'yar madara.
Gidansu Al'amin, Abbu ya shirya zai fita ya kalli rahila ya ce "Yakamta idan an janye yajin aikin nan, ku je ku duba matar yaron nan"
Rahila ta ce "Taɓ haka kurum, su dai yaran su je ni in je ya illata ni a banza? Su dai su je"
Abbu ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ce "Amira, ga kuɗi nan ku hau mota, ga dubu biyar ku saya mata fruit ku kai mata, na ji an ce zuwa jibi in Allah ya kaimu, za a janye yajin aikin, sai ku je ku duba jikin nata, kafin na samu na je nima"
Ta amsa da to Abbu. Sai dai bayan fitarsa Amira ta ce "Na samu na saka data, dan ba za ta ci 5k ɗin nan ba".
Shahida ta ce "Wallahi kuwa da sai na gaya masa, ai ba haka ake yi ba" haka suka cigaba da faɗan su na sakonni.
Jikinta ya ɗan yi sauƙi, sai dai ba ta daina ciwon kai ba, ga damuwar abun da Al'amin ya sake nanata mata, kenan yana nan a kan bakansa na rabuwa da ita.
Kusan kwanaki biyu, ba ta bari su zauna wuri ɗaya, saboda kar ya sake tayar mata da maganar.
Ya gama karyawa, yana kallonta tana ta shirin dutsenta, karyawar ma ba ta yi ba, kamar yayi magana kawai ya shareta, ya tashi ya fita.
Su halimatu suka shigo, suka tayata aikace-aikace, sannan suka koma gidansu.
Tana falo tana karatunta tana shirin dutse, aka yi sallama a tsakar gida.
Ta amsa tare da bayar da izinin a shigo, 'yan mata ne da zasu girme mata su biyu, suka shigo falon.
Jauhar ta faɗaɗa fara'arta tayi musu maraba.
Suka gaisa da ɗayar, ɗayar kuwa sai hura hanci take yi.
Shahida ta ce "Kin gane mu kuwa?"
Jauhar ta ce "Na gane wannan ranar da na je gidan, mun haɗu da ita ai, ƙannensa ne ko?"
Shahida tayi murmushi ta ce "Kin canka"
"Sannunku da zuwa, baku taɓa zuwar mana ko sau ɗaya ba"
Shahida ta ce "Ai da yake ba ma zama a gari saboda school, shekaranjiya ya je gida ya ce baki da lafiya, Abbu ya ce lallai mu zo duba ki kafin ya zo shi ma. Ya jikin?"
"Jiki Alhamdilillah na warware"
"To Allah ya ƙara afuwa, ko mu ce Allah ya raba lafiya, ya kawo mana baby lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi.
Buɗe baki Jauhar tayi ta tashi da sauri ta ce "Bari na kawo muku ruwa"
Ta kawo musu ruwa, lokacin ta hura gawayi, ta ɗora girki.
"Wancan ba tea flask ɗin mu bane?" Amira tayi maganar tana nuna flask ɗin.
Jauhar ta ce "Ina ga naku ne, shi ne ya zo da shi, ina ta so nayi masa maganar na waye, yanayin jikina ya hana, amma tun da Allah ya kawo ku shikenan".
Suka cigaba da hira da shahida, yayin da Amira ke ta harare-harare itakaɗai.
Shahida ta ce "Yaya muka ji da abun da ya faru da yaya na rufe shi da aka yi, Ubangiji Allah ya tsare gaba" Jauhar ta ce "Amin ya Allah, sharri ne ma aka yi masa, amma duk da haka a tayamu da addu'a dan Allah, duk zai daina wataran sai labari. Ina mama?"
"Haka ne, ana nan ana yi, mama tana nan ƙalau, tana gaishe ki"
Shahida ta sake cewa "Nikam wai dan Allah ya aka yi kuka haɗu da yaya ku ka yi aure, har ya taka ya je gida, sha biyu fa ta wuce, ya ce na yi masa girki matarsa ce ba lafiya na ce wace 'yar baiwa ce haka? Kin san a rayuwarsa ta duniya mata ba sa gabansa mu kanmu yadda ki ka san dodo haka yake a wurinmu". Jauhar za ta yi magana, Amira ta ce "Kin jiki da wata magana shahida, a ina kuwa za su haɗu?, Tallarta fa aka kawo masa ba ta ji, ta fanɗare a gida an rasa yadda za ayi da ita, aka haɗa su, aka jogana masa, da yake shi ma ba sanin ciwon kansa yayi ba, ko ke baki san zancen ba? Kin zauna kina ta zuba ni ina da wurin zuwa" ta ƙarasa maganar tana tashi tsaye ta ɗauki jakarta tayi waje.
Gaba ɗaya jauhar ta yi sak, jikinta yayi shock, yayi wani irin sanyi da mamakin maganganun Amira.
Cikin dirircewa shahida ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ƙarya take yi, ina zuwa" ta lallaɓa ta ɗauki takalmanta cikin tsananin jin kunya ta bi bayan Amira.
Biri yayi kama da mutum, duba da yadda aka yi auren cikin gaggawa ko wata guda ba a rufa ba, ashe abun da aka gaya musu kenan a kanta?
A take ta ji ciwon kanta ya tsananta, ta fara tunanin wace irin muguwar ƙiyayya ce tsakaninta da 'yan gidansu har haka.
Gidan su jauhar, Hafsa ta shigo daga zance, ta zauna a tsakar gida, Yaya saifu ya shigo, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?"
"Zance" ta bashi amsa kai tsaye.
"Wurin wa?" Tayi shiru tana kallonsa.
Ya ce "Wallahi kun yi asara, yanzu dama Saboda hafsa ta auri mutumin nan, da yake son jauhar shiyasa ku ka aurar da ita ga mutumin banza, wallahi ba ku kyautawa kanku ba, kuma da ikon Allah sai Allah ya saka mata".
Mama ta ce "Saifu maganar me ka ke yi ne ban fahimta ba?" Ji yayi kamar ya gayawa mama baƙar magana, sa'arta ɗaya mahaifiyarsa ce, babu yadda zai yi da ita, kawai ya fice.
Mama ta ce "Zakiyya, da gaske mutumin nan ne yake zuwa wurin Hafsa?"
Ta haɗa rai ta ce "Ni ma ban san zancen ba sai yanzu"
Mama ta ce "To meye abun ɓoyewa ban da abunki, ai abun farinciki ne a gare mu baki ɗaya. Dama ai jauhar ɗin ce ba ma son ya aura, wallahi nayi murna haƙanmu t cimma ruwa".
Sai kuma ta ɗan saki ranta ta ce "Wallahi ina ta son na gaya miki, abubuwa ne sun sha mini kai, kuma ba gama daidaitawa suka yi ba"
"Ai bakomai, Allah ya tabattar mana da alkhairi" suka gama maganar ta shiga ɗakinta, ta jinjina kai ta ce "Hmm zakiyya kenan, baki da wayo da ni ki ke zancen, duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, zaki gane kuskurenki".
Yau tun la'asar ya dawo, kwana biyu ba ya yin dare, saboda rashin lafiyarta sai dai fa ba zai ce mata sannu ba.
Ya kasa gane kan yanayinta, ta zuba masa abinci, ta koma gefe ta yi shiru.
Ya gama ya tashi ya tafi ɗaki, zai ɗan kwanta ya huta, kasa jurewa ta yi ta tashi ta bi bayansa.
Ta ssme shi, yana ta watso kayan wardrobe ɗin sa da ta gyara da ƙyar.
"Master"
"Yeah" ya amsa ba tare da ya kalleta ba.
"Ƙanneka sun zo ɗazu baka nan"
"Ok" kawai ya ce, amma ƙasan zuciyarsa mamaki yake yi, tun da ƙannensa ta ce, da ƙanwa ta ce ya san shahida ce kawai.
"Dan Allah abu nake son tambayarka, na san kai ba ma'abocin ƙarya bane ba, na san ba zaka fara a wannan karon ba" bai amsa ba, dama ba tayi tsammanin hakan ba, ta ce "Da gaske tallata aka kawo maka, wai ba na ji na fanɗarewa iyayena shi ne aka aura maka ni?"
Ya ɗaga rigar hannunsa yana kallo kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Eh, haka na ji"
Cikin rauni ta ce "Kuma ka yarda?"
"Kusan haka, dan na san ba yadda za ayi a aureni haka kurum babu dalili, a abun da bai wuce sati biyu ba"
Yayi maganar yana ajiye rigar, ya ɗauki wata, sautin da tayi na ƙwacewar kuka ne, ya sanya shi ɗagowa a tsorace yana kallonta.
Cikin kuka ta ce "Wallahi ni ba lalatacciya ba ce, ban fanɗarewa iyayena ba, dama kallon da ka ke yi mini kenan, kallon da 'yan uwanka da sauran mutane suke yi mini kenan" da ƙyar maganarta take fita, saboda numfashinta da ya fara sama.
Ya ƙaraso gabanta ya ce "Wai ke ba kya gajiya da kuka ne? Komai kuka?"
Hannunta take fifitawa kusa da hancinta, alamar numfashi yana bata wahala, da sauri ya ɗauketa ya fita da ita tsakar gida, ta lumshe idonta hawaye na bin gefen fuskarta, sai dai ƙirjinta sai ɗagawa yake yi yana sauka, alamar numfashin da ƙyar take yi.
"Ko mu koma asibiti? dama sati ɗaya suka bamu mu koma" Ta girgiza masa kai.
"Ba zaki daina kukan ba?" Maimakon ta daina, sai ma wata sheshsheƙa da ta zo mata, ga numfashinta yayi nauyi.
Ya ciro wayarsa a aljihun wandonsa, ya kira liti.
"Maza ya ne?"
Viper ya ce "Kana ina?".
"Na shiga area raba kaya".
"Samo adaidaita sahu, ka zo gidana zan mayar da 'yar madara asibiti"
"An gama mazaje"
Zai ajiye wayar, ta fara vibrating, ya ɗaga bai yi magana ba.
"Honorable ya dawo, akwai taron gaggawa da zai yi, yana son ganinka"
"Na ji"
"Dan Allah kar ka ɓata lokaci sosai, ka san zaɓe yana ƙara gabatowa"
Ras jauhar ta gane muryar waye, muryar P.A ce, a take ta jinjina rashin kunya irin na ɗan siyasa.
"Dan Allah kar ka je, idan ka tafi mutuwa zan yi"
"Allah ya jiƙanki"
A sanyaye ta ce "Amin, amma dan Allah ko na mutu kar ka je ba na son ka din ga zuwa wurin 'yan siyasa"
"Ki yi mini shiru, idan ba haka ba zan tashi na bar ki"
"Yi haƙuri" ta faɗa tana haki.
A hankali take iya takawa, saboda numfashinta, ya sakata a napep ɗin da liti ya zo da ita, sannan ya shiga, liti ya zauna a gefe suka tafi Asibiti.
File ɗin ta aka kai wa likita, shi da ita suka shiga, liti kuma yana can waje.
Likita ya ce "Ka ƙi yadda ayi mata gwajin ciki, gashi tana ta fama da an duba dai"
Ya ce "To duba"
Jauhar ta ce "Ni bani da komai".
"Shikenan, ki na da athma ne dama, wannan hakin da ki ke yi?" Ta jinjina masa kai ta ce "A'a allergy ne, shi ma kuma tun ina yarinya ne"
Al'amin ya kalleta, likitan ya sake cewa "Akwai magani da ki ke sha ne? Ai kusan duk abu ɗaya ne, allergy ɗin da athma"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ai na daɗe ba na shan magani, addu'a nayi ta yi, ya daina tashi, tun ina ƙarama sosai ban kum jin alamun sa ba"
Likitan yayi murmushi ya ce "Masha Allah, ka ga 'yar baiwa, to a din ga sakamu a addu'ar mu ma, amma dai yanzu zan rubuta miki magani, sai ki kiyayi hayaƙi, ko kin shaƙi wani abun ne?"
Ta ce "A'a kuka na yi kawai na ji na kasa numfashi sosai"
Likitan ya jinjina kai, ya ce "Bari na duba bp naki na gani".
Shi dai gogan bai ce komai ba, likitan ya duba bp ɗin ta sannan ya ce "Zahra kina shan magungunan da na baki kuwa?"
"Ta jinjina kai alamar eh".
"A iyayenki akwai mai hawan jini?"
Ta ce "A'a"
Ya kalli Al'amin ya kalli jauhar ya ce "Akwai abun da yake damunki ko?" Tayi yaƙe ta girgiza kai.
"Zahra, ita rayuwar duniya haƙuri ake yi. Malam ka zauna da matarka ku tattauna idan a cikin aurenku matsalar take, a magance ta, idan ba haka ba, hawan jinin nan zai iya taɓa mata zuciya, idan wani abu ka ke yi mata da ba ta jin daɗin sa, ku tattauna dan Allah ku fahimci juna, amma tayi ƙanƙanta da wannan ciwon"
"Zahra" likita ya kuma kiran sunanta, kamar yadda ya gani a jikin file.
"Idan kun je gida, ki zauna da mijinki, idan damuwa ce da ke, ki gaya masa, ki cire koma menene a ranki, mijinki da kuma al'umma baki ɗaya muna buƙatar ki a raye" kawai ta sunkuyar da kai sai kuka.
Al'amin ya ce "Rubuta mana magungunan kawai mu tafi"
Ya rubuta maganin, ya bawa Al'amin yana kallon jauhar cikin tausayawa.
Al'amin ya kalleta ya ce "Mu tafi? Ko yau ma goyakin zan yi?"
A hankali ta tashi tsaye, ya ce "Kin daina hakin?"
Ta ce "Ya ragu"
Ya saka hannunsa ya riƙe nata, suna tafe a hankali har suka fito wajen asibitin in da pharmacy yake, ya saya mata maganin suka hau napep ɗin da ya kawo su zuwa gida.
Shi dai bai iya rarrashi ba, bai ma san ta ina zai fara ba, amma gaba ɗaya yanayin da jauhar take ciki, bai yi masa daɗi ba, ya san fiye da rabin damuwar ta shi ne sila, ya ce su rabu kuma ta cigaba da kuka.
Tana kwance a kan kujera, tayi lamo, shi kuma yana zaune a ƙasa, yana kaɗa ƙafa.
"Master"
"Mmm"
"Kana ta ɗawainiyar asibiti da ni, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara arziki"
"Amin"
Ta sake cewa "Master"
Ya ɗago yana kallonta. "Dan Allah da gaske kallon mara ji wadda ta fanɗarewa iyayenta ka ke yi mini?"
"Haka aka ce mini ai"
Ta ce "Aishikenan, shiyasa ka ke so ka sake ni?".
Ya ce "A'a kina takura mini ne kawai, kin isheni yanzu ina zaman zamana ba zan fita ba, sai dai na zauna kula da ke"
Ta ce "To ka yi haƙuri, dan Allah kar ka fita yanzu, ji nake kamar kana fita zan mutu" idan tayi zancen mutuwar nan, gabansa faɗuwa yake yi, amma ya maze ya ce "To zan hanaki mutuwa ne?".
"A'a, amma dan Allah ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, dan Allah ka gaya wa 'yan gidanku, aje ayi bincike ma a kaina, wallahi ba mutuniyar banza ce ni ba" ɗago ido yayi yana kallonta, kenan zuwansu ne suka gaya mata wannan maganar, yayi shiru ya cigaba da latsa wayarsa.
"Master"
" 'yar madara" ya amsa bai kalleta ba.
Likita ya ce "Ka daina yi mini abun da na so, ka tambaye ni abun da nake so ka daina yi mini"
Ya ce "Tom" ɗan murmushi ta yi, yau tayi sa'a ana amsa mata ma.
"Yaushe zaka sake nin?"
Ya yinƙura ya tashi ya ce "Na fasa yanzu, sai an kwana biyu, idan aka yi yanzu ina ga warewa zaki yi".
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ya shiga ɗakinsa.
Cikin ikon Allah, washegari ta tashi jikinta da sauƙi, sai dai damuwar cewar ita fanɗararriya ce, ta kasa barinta.
A tsakar gida ya taso, ya tarar da ita, tana aiki.
"Ina kwana"
"Kin warke ne?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a, bayan ba ka zauna mun yi maganar da likita ya ce ba"
"Akwai abinci ne?"
Ta ce "Eh shinkafa na dafa amma akwai sauran buredi in dafa tea"
Ya ce "Zubo mini, ke ki sha tea ɗin"
Ta zubo abincin ta kawo masa, ya kalleta fuskarta duk ta faɗa.
"Amma yau ba zaka fita ba ko? Ka zauna ka kula da ni"
Murmushi ya yi da gefen bakinsa, ta sake cewa "Idan ka gama cin abincin zan gaya maka abubuwan da nake son ka daina yi mini, ko sannu baka yi mini bama".
Tayi ta zuba, amma yayi gum.
Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya ce "Ina sane zan zo yanzu"
Ta haɗe rai ta ce "Amma ba fita zaka yi ba ko?"
Ya ce "Fita zan yi"
"Ni dan Allah ka zauna ka kula da ni" shagwaɓa da rikici kawai take yi masa tsakanin jiya da yau, kamar yau an cire mata tsoron sa.
Ta tashi ta ɗauki kwanukanta, ta tafi kitchen cike da takaici. Ko ba zai kulata ba, tana son ganinsa a gida.
Sosai ta ji ranta ya yi mugun ɓaci fitar da zai yi, ɗan tattalin da aka yi mata jiya zuwa yau yayi mata daɗi, duk da ana yi ana haɗe mata rai.
Tana cikin ƙunƙuni, ya fito da sauri hannunsa da wayarsa a kunnensa, hannunsa ɗaya da makamin da yake kira da iraƙi.
Ya ce "Gani nan, ka duba bayan nan, russiata da sweazland suna nan, ka ɗaukar mini su, kar ku bari su motsa, gani nan zuwa" hannunsa ɗaya yana soke makaminsa iraƙi a cikin ƙugunsa.
Ya ce "Fitar gaggawa ta kama ni, idan nayi dare ban dawo ba, ki rufe ƙofa, duk wanda ya buga kar ki buɗe, idan na dawo na hauro"
Banza tayi masa, ta cigaba da yanka albasarta.
"Ke ba magana nake yi miki ba?" Shiru ta sake yi masa.
Ƙoƙarin leƙawa yake yi, ya ga ko lafiya.
Kawai ya ga ta jefo masa murfin tukunya, a zatonsa ko ba ta san me tayi ba, kawai ya ga ta sake jefo masa rariya. Saroro ya tsaya cikin mamaki, ta cigaba da zaro kwanuka tana jefa masa tana kuka, bai ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka haɗa ido ta jefo masa ludayin hannunta a ƙirji.
Ayshercool 08081012143
31 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955
Tunani ya fara yi, ko tana da aljanu ne.
Ganin idan ya ƙyaleta, fashe-fashe za ta yi, ya sanya shi takawa ya riƙo hannunta, amma sai ƙoƙarin fizgewa take yi.
Kasancewar ba ta yi masa wahalar ɗauka, ya sanya ya danƙota kamar kazar cikin akurki, aikuwa ta cigaba da fizge-fizge da ƙoƙarin ƙwacewa, falo ya shiga da ita, ya tattara hannayenta ya riƙe, hakan ya sanya ta kasa cigaba da ƙoƙarin ƙwacewar.
"Meye haka ki ke yi? Kanki ɗaya kuwa?"
Kallonta yake yi, har ta fara kuka, shi bai ma san me yayi mata ta aikata hakan ba.
"Me nayi miki ki ke jifana?"
Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Meye ma baka yi mini ba, ni bani da wani amfani a wurinka, bani da ikon roƙon alfarmarka, komai ma yi mini ka ke yi, ko yayi mini daɗi ko akasin haka, ba ka tausaya mini dama ka tsane ni, so kake yi na mutu ka huta".
"To yanzu kuma me nayi miki?"
"Wuƙa fa ka ɗauka zaka fita, idan aka yi maka wani abun ko ka yi wani laifin nikaɗai nake fama, sai su yaya walid da suke taimaka mini, amma kai gaba ɗaya baka tausayina, ba ka tausayin maraicina saboda da ma ba so na ka ke yi ba. Kodayeke ba laifinka bane, tun da sama ta ka aka aura maka ni, bayan an gama ɓata ni a wurinka. Ko hira ba ka yi da ni, in tayi maka magana kayi mini shiru, idan aka ga na mutu kai ne, sai ma na rubuta na bar wasiyya, idan na mutu kai ka ƙarasa ni da takaici"
Yayi shiru ta din ga yi, tana faɗa tana kuka, sai da ta gama tsaf, sannan ya miƙe ya ce "Ki kula da abun da na gaya miki, kar ki fita kar ki bar gida a buɗe, idan na yi dare ki kwanta zan hauro".
Ta ɗaga idanunta da suka yi ja ta ce "Sai ka fita ko?"
"Ai na ce idan ba zaki iya ba, ki koma gidanku ko ban gaya miki ba?" Tayi shiru ranta na yi mata wani irin zafi, ya fita ya kwashe kwanukan da ta watso waje ya fice.
Unguwar su ya nufa, faɗa ya haɗa ɗan unguwarsu, da ɗan unguwar su madaki, yaron ya kwaso 'yan daba yaran madaki, sun shiga unguwar su Al'amin su na ta faɗace-faɗace.
Yana zuwa chamber su, ya ɗaukko wuƙaƙensa, ya fita, sai dai da ya je, yaran suka din ga darewa, saboda wanda suka taɓa karo da shi, sun san irin ƙarfin da Allah ya yi masa.
Wani yaron madaki ne, da yake ji da tashen balaga da rashin mutunci, ya sha gaban Al'amin yayi yana zage-zage yana ƙoƙarin saran Al'amin.
Ya jefar da wuƙarsa, ya nufi yaron, wanda suka san Al'amin suka din ga ce masa ya gudu, kar ya bari ya kama shi, amma kasancewar ya yi wa wiwinsa haɗin kauri da wata ƙwaya da suke yi wa laƙabi da 'yar fara, ya sanya yake jin kansa a sama, ko barikin sojoji zai iya shiga yayi rashin mutunci.
Duk iya ƙoƙarin sa ya kasa saran Al'amin, saboda yadda yake da zafin nama, wurin kare saran, wanda idan ba professional athlete ne ba, babu lallai ya iya.
Ya shammaci yaron, ya soka masa iraƙi a cinyarsa, a take ya kurma wani uban ihu, liti ne ya karyo kwanar, riƙe da nasa makamin yana ɗigar da jini, "Mai zamani yi haƙuri, kar ka karya yaron nan" sai dai bai rufe bakinsa ba, ya ga Al'amin ya fito da dogon harshensa, ya lashi laɓɓansa na ƙasa da su, idan har yayi haka sai aiwatar da muguntar da yayi niyya, kan liti yayi wani yinƙuri ya karya ƙafar yaron ya watsar da shi yana kururuwa.
"Mai zamani, yanzu zaka sake janyo mana faɗa, madaki zai ce sai ya ɗauki fansa, da baka karya shi ba"
Ya ɗago jajayen idanunsa a slow, yayi wa liti wani irin kallo ya ce "Ya zo ya ɗauki fansar a kaina, idan ya isa" ya wulwula iraƙinsa, ya cafe ya yi gaba.
Kai tsaye gidan su ya tafi, da wannan wuƙar tana ɗigar da jinin da ya soki yaron nan.
Yana shiga ya wuce falo, sai ganinsa suka yi a tsaye a kansu da makami tsirarsa.
Salati suka fara yi da kururuwa, ya kalle su ɗaya bayan ɗaya, "Me ya kai ku gidana?" Yayi maganar yana kallon shahida.
Cikin tashin hankali ta ce "Abbu ne ya ce Mu je mu duba matarka".
"Shi ya ce ku je ku gaya mata cewar kangarewa ce ta sanya aka yi aurena da ita? Ku je ku ci zarafinta?" Cikin tashin hankali shahida ta ce "Ba ni na faɗa ba Amira ce wallahi".
Rahila kuwa hankalinta ya dugunzuma, ta ce "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka yi haƙuri, dan Allah kar ka yi musu wani abu"
Ai kamar ta tunzura shi, ya saka wuƙa a wuyan Amira, "Ya zama na farko ya zama na ƙarshe, ayi duk cin kashin da za ayi a kaina, ban da 'yar mutane da ki ka haɗa kai ku ka cutar, idan aka kuma zan yi ɓarna, wallahi sai na saka wa mutum ƙarfe"
Shahida ce ta iya cewa "In sha Allah ba za a sake ba" yayi ƙwafa ya fita.
"Amira kin ga abun da ki ka ja mana ko? Da ya illatamu, da kin cuce mu"
Amira kam kasa magana tayi, sai dafe ƙirji tana hakin tsoro.
Al'amin wuni yayi ranar, yana partrol da yaransa a unguwar, saboda kar yaran madaki su zo su afkawa wanda bai ji ba bai gani ba.
Cikin ikon Allah, har dare yaran madakin ba su sake shiga unguwar su Al'amin ba, duk da sun yi artabu sosai da wasu, dan sai da aka yi masa rauni a cikinsa, ya kama hanyar tafiya gida.
Jauhar na falo tana karatun exam, duk da sun kusa kammala jarrabawa.
Ta katangar ya diro kamar ɓarawo,s an samu cigaba, yanzu idan ya ga dama ya kan yi salama. Sallamarsa kawai ta amsa, ba ta sake kula shi ba, ya wuce ɗakinsa, mintuna goma amma ba ta biyo shi ba, ya fito ya ce "A kawo mini ruwan zafi zan yi wanka"
Ta tashi ba ta ce komai ba, ta ɗaukki flask, aurensa da ita ta saba masa da wanka da ruwan ɗumi, saɓanin da da har a kuddudufi wankansa yake yi ya ƙara gaba. Yanzu kuwa kusan kullum, da an kawo wuta, take dafa ruwan a heater, ta saka a flask.
Ta zo ta haɗa masa ruwan, sai dai ta ga kamar yana ɓoye wani abu.
Kawai ta leƙa ta ga me yake ɓoyewa, yanka ne a gefen cikinsa, ya saka rigarsa yana ƙara goge jinin kasancewar ba mai zurfi bane ba.
"Ka gani ko? Sai da ka je aka yanko ka ko? Abun da nake ta gudu, sai da ka zubar da jini ko, ba za kai daina zuwa wurin da za a cutar da kai ba ko master? Kodayake ma ni abun yake damu, kai ko a jikinka".
"Na ce ya dame ki ne? Ba jikina bane?" Idan ba gizo idonsa yayi masa ba, hararsa ta yi ta fice.
Shi mamaki ma take bashi, tun da ta yi rashin lafiyar nan, take rigima kuma kamar ta rage tsoron sa.
Ya shiga ya yi wanka, ya fito ya tarar da ita da ɗan ƙaramin kwanon abinci, sai kuma kayan dressing, tun na lokacin da aka yi masa wancan raunin.
Bai kulata ba, ya ja kwanon abincinsa ya cinye, awara ce da miya, ya sha ruwa.
Ita ma ba ta kula shin ba, ta saka auduga da spirit tana goge, kan ciwon, tana gogewa tsigar jikinta na tashi, kamar jikinta take gogewa, shi kuwa kamar dutse latsa wayarsa ma yake yi.
Haushi ya isheta, ta kalleshi ta ce "Wai ba zafi ne?"
"Eh babu, idan ma dirzawa ki ke da ƙarfi, dan na ji zafi, ba na ji" ta tashi ta fice fuuu, tana yi masa fatan shiriya a ranta. Kusan awa ɗaya da rabi, ya shigo mata ɗaki, ta yi sauri ta tashi zaune, saboda ta san tsiyar da ta aikata masa.
Ya kunna fitila ya hau yi mata bincike a ɗaki.
"Me ka ke nema?"
Ya tashi ya nufo ta, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani kayana da ki ka sace mini yanzu"
"Ni ba na sata"