Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 30

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 30

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 30: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 30. Ya ce "To baki nayi ki ka ɗauka? Ko kema kin fara sha ne ban…

4,490 words

Ya ce "To baki nayi ki ka ɗauka? Ko kema kin fara sha ne ban sani ba? Kodayeke biri yayi kama da mutum, da ki ka iya kallona ki ka din ga jifana nan gaba ina ga swizaland zaki saka mini ina ga"

"Ni ba na shan komai, kuma ban ɗau komai ba".

"Ba ki ɗauka ba ya aka yi ki ka san a kan me nake magana?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Hankaɗata yayi, ya janyo ledar kayan shaye-shayen sa a cikin bargonta.

"Na gaya miki idan kin gaji ba zaki iya zama ba, ban ɗaure ki ba, ki ƙara gaba"

A ƙule ta ce "Ka ɗaure ni mana, zan tafi ba ka sallame ni bane, ka rubuta ka gani idan ban tafi ba. Tun da baka da tausayi idan ba mutuwa na yi ba hankalinka ba zai kwanta ba" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ya kalleta, gaba ɗaya ko faɗan ba ta iya ba, voice ɗin ta sam ba na masu faɗa bane, shagwaɓa kawai take yi.

Ya ce "Kin yanke hukunci kenan? Ai da kin gaya mini da duk ba a zo nan ba, zan rubuta na baki, dama na gaji".

"Kuma wallahi idan ka yi shaye-shaye kai da Allah"

Bai kulata ba, ya jefo mata kwalin sabuwar waya gal, ya ce "Gashi nan, akwai layi a ciki na yi rijista, idan kuma na yi wani laifin na gudu ke za a kama".

"Bana so" ta faɗa tana kwanciya, duk da ƙasan zuciyarta tayi mamakin wayar.

Ya saka hannu ya ɗauka ya ce "To kin huta" ya fice ya bar ɗakin.

Ta kwanta ta yi shiru, sai ta fara tunanin ya aka yi ya ɗaga mata ƙafa ya ƙyaleta, sai kuma ta ga rashin kyautuwar abubuwan da ta yi masa.

Bayan sallar asuba bacci ta koma, ƙarfe takwas da rabi ta farka, tana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, tayi tozali da farar takarda da biro. Gabanta ya faɗi ta ce "Na shiga uku sakin nawa ya yi?" Ba ta taɓa takardar ba, ta saukko a sukwane ta tafi ɗakinsa sai dai baya nan ya fice.

Gaba daya jikinta yayi sanyi, sai yanzu ta ƙara jinjina girman wauta da aikata.

Yau rahila har gidan su jauhar ta je, suka ƙule a ɗaka ita da Anty Zakiyya suna ta surutu da shewa.

"Zakiyya ina ga 'yar ku fa an gamu laulayi take yi"

"Kai haba dan Allah"

"Wallahi da gaske, ke 'ya mace shu'uma komai ƙanƙantarta, kin san yaron nan har gida ya zo da wuƙa ya gama ta'addancin sa tana zubar da jini, zai yi mini hauka a gida wai su Amira sun je masa gida sun yi matarsa ko me oho musu, na ga tashin hankali na ce iyee yanzu har ta samu wannan matsayin. Wallahi mamaki nake yadda ta iya zama da yaron nan"

Zakiyya ta ce "Ba ki ganta ba kamar sokuwa, kafin ki ga ta yi fushi, ko tayi zuciya da abu za a jima, ko kuma kawai tsabar ƙarfin hali ne da ƙi faɗi ba"

Rahila ta ce "Sai ta yiwu, ya ake ciki da maganar hafsa?"

"Mu na nan ana ta murginawa, ana shirin kawo kuɗin aure, na ce lallai ta ce masa a haɗo da kayan lefe, ana sallacewa ayi auren, duk da wannan matar ta nuna bakomai na san tsohuwar muguwa ce, wataƙila wani abun zata kitsa, dan haka kan tayi wani yinƙuri ayi a wuce wurin".

"Yauwwa kar ki kuskura ki sakankance ko ki yadda da ita, ni ban zaci lamarin ma zai zo da sauƙi haka ba, ku cigaba da tatsarsa kuna tarin kayan aure"

Zakiyya ta ce "Ke kin ga hidima, ai ni dai Allah ya kashe ya bani, da yanzu sai dai mu ga ana yi wa waccan yarinyar jauhar"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ga mijinta can suna fama, amma wallahi ya fara son yarinyar nan, kai amma ba ƙaramin haƙuri take yi ba bala'i Allah ya kyauta" suka cigaba da hirarrakinsu, da shirin biki.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, suka fito daga taron meeting, daga ofishin jam'iyya, sakamakon gabatowar manyan zaɓuka da za a gudanar a cikin Nigeria.

Yau bai san iya adadin meetings ɗin da ya yi attending ba, suka jero da shi da mataimakin firaministan jam'iyya na jiha, ya ɗan yi miƙa ya ce "Kai, yau na gaji over"

"Kai honorable, da an yi babban zaɓe an wuce wurin, haka ne, ka san ban yi sati da shigowa daga Abuja ba, can ma wasu tarurrukan ne, abun duk babu sauƙi, ina ta ƙoƙari in sha Allah sai na kawowa excellency yankina, ina nan a satin nan zan yi empowerment na matasa, kuɗina duk sun tafi a campaign ɗin nan"

"Kar ka damu honorable, hannun jari ka saya, da an wuce wurin sama zaka din ga kwashe ribarka, ka mayar da uwar da ribar ka ɓace ba zasu sake ganinka ba, sai bayan shekara huɗu" suka kwashe da dariya.

Suka yi sallama, kowa ya nufi motarsa, ko da ya je gida, matarsa tuni tayi bacci, yayi wanka ya nemi wuri ya kwanta, dama ba yunwa yake ji ba, sai dai bacci ya gagare shi, ya din ga juyi a kan gadon, ga gajiya ga baccin yana ji, amma ya kasa ya ɓuge da lissafe-lissafe abubuwan da yake son yi idan ya dace ya samu ya ci zaɓen nan. Ji yayi kamar kansa zai fashe, saboda stress kawai ya tashi ya ɗauki mukulli, ko direba bai nema ba ya hau motarsa ya fice.

Yamma da gari yayi, ya hau kan titin gwarzo road kasancewar dare ne, titin babu ababen hawa, ya sauke glas ɗin motar kaɗan, yana tafe a hankali yana shaƙa wani abu a hancinsa. Sai d yayi nesa da cikin gari sosai, sannan ya yi parking a gefen hanya, ya rufe glasan motar, ya cigaba da shaƙa abun nan, kusan mintuna talatin, sannan ya juyo kan motar ya nufi dawowa yana tafe iskar kan titin nan na ratsowa cikin motar, sannu a hankali har ya koma gida.

Jauhar kuwa tun da tayi tozali da takardar nan ta kasa nutsuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuma taƙi buɗe takardar, da ta leƙa ta hangota ma, sai ta yi sauri ta fito daga ɗakin, ta din ga lissafa irin halin da za ta shiga idan ta koma gida, da irin dariyar da za su yi mata.

Kuma yaƙi dawowa, har dare ba ta ganshi ba, hakan ya ƙara sanyata cikin tashin hankali, ba irin tunanin da ba ta yi ba, har ta fara tunanin ko da ya saketa, barin gidan yayi gaba ɗaya, sai dai kayansa suna nan, dan ita ta gyara ɗakin ya watso da komai ya bar mata a wurin.

Sai sha biyu saura ya dawo, idonta biyu ya dawo ba ta yi bacci ba, sai da ta tabattar ya shiga ɗakinsa, sannan ta ɗauki takardar ta bishi ɗakinsa.

Yana kwance a kan katifarsa, ya cika ɗakin da warin taba.

Yanayinsa ya nuna a buge yake, saboda fitilar ɗakinsa a kunne take, ya haye katifa ya mimmiƙe idanunsa sun yi ƙanana da ƙyar yake ɗaga su, kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da idonsa ya lumshe.

"Master sai da ka rubuta takardar nan hankalinka ya kwanta ko?"

Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ke ki ka ce na rubuta"

"Kuma sai ka rubuta ɗin ko? Saboda ina fargabar kar ka sake ni, bakomai maraici ne ya janyo mini, Allah ya gani na yi iya yi na, na yi biyayyar aure, amma kullum kallona ka ke yi wadda ta takura rayuwarka, ga takardarka nan, ban ma buɗe ba balle na san meye a ciki, kuma wallahi ban saku ba" ta dire masa takardar a jikinsa, ya ziro harshensa tare da naɗe shi ya mayar, ya gyara kwanciyar sa, har ta gama surutanta, bai kuma motsawa ba.

Kasa bacci tayi, ta ɗaura alwala ta tayar da salla, ta din ga addu'a Allah ya sa ya fasa sakinta, saboda ita a ganinta gara ƙalubalen gidan Al'amin a kan na gidansu.

Duk rintsi ba zai daketa ko ya ci mutuncin ta ba, ko yi mata sharri ba, sai dai miskilancinsa da gaya mata baƙar magana wasu lokutan da har daɗi take ji ya kulata, ciyar da su kuma da take yi mafi yawan lokuta baya damunta, sai ma yi wa Allah godiya da take yi da ko yaya ba ya hanata abun da zata sarrafa su ci, ko yaya ta kasa abun sayarwa za a saya dan ma ana yi mata mugunta.

Bayan sallar asuba tayi shiru tana tunani, ta ga sam ba ta kyauta ba, wasu abubuwan da ta yi masa, tun daga jifansa da kwanuka, har zuwa tsiwar da ta yi masa, ita tayi mamaki ma da ya ƙyaleta.

Yau ba ta iya komawa bacci ba, ta fito aikace-aikacen ta, tana yi tana leƙawa ko ta gani ko ya tashi.

Tana falo ta jiyo motsinsa, ta tashi ta shiga ɗakin da sallama.

Ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba.

Jiki a sanyaye ta durƙusa ta ce "Master ina kwana?"

"Lafiya ƙalau"

"Ka tashi lafiya, ya ciwonka?" Sai a wannan karon ya kalleta sai dai bai ce komai ba.

"Master dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi haƙuri idan ka sakenin ma, ka yi haƙuri ka mayar da ni" tayi maganar cikin rauni.

Ya lumshe idanunsa ya ce "Bani wuri zan kunna hayaƙi"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, ka yafe wa 'yar madara ɓacin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri"

"Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi"

"Dan Allah ka yi haƙuri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?"

"Eh ki kawo mini, sai fa kintafi"

"Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta roƙonka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da kuɗi ba zaka ganni ba".

"Eh na ji, kafin ki fara ɗaukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita" yayi maganar yana danƙa mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta buɗe idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata.

*Ba zan dawo da wuri ba, na bar kuɗi a kan katifata ki sai wani abun ki ci*

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce "Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?"

Hamma yayi, yayi shiru ta ce "A'uzibillah" duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu'a bai yi ba, sai tayi masa.

Ta ce "Aishikenan amma dan Allah ka yi haƙuri abubuwan da na yi maka ka yafe mini"

"To, ki bani wuri zan sha abu"

Ta ce "To bani wayar da ka bani jiya" gefen katifarsa ya nuna mata, ta tashi ta ɗaukkota a kwali.

Ta kalleshi ta ce "Yanzu dan Allah wannan ta wa ce master? To kai ina taka?" Ya nuna mata keypad ɗin sa.

"Wallahi ko a mafarki ban taɓa tunanin riƙe waya ba, yaya saifu ya taɓa bani keypad mama ta ƙwace, Allah ya saka maka da alkhairi ya saka ka a aljanna, Allah ya nuna mini ranar da zaka daina shan komai, ka zama limami saboda salihancinka, Na gode master na gode sosai da sosai" tayi maganar tana tattaɓa wayar.

"To excuse me, ina son yin caji"

"To yi mana"

Ya ce "Ki fita ki bani wuri dai, kar ki sume mini yau bani da kuɗin zuwa asibiti"

Maƙale kafaɗa tayi, ta ce "Master, wai yaushe zaka kai ni na gaida mama ne? Da wurin hajiya ma?".

"Wace maman?"

"Mamanka mana, bamu taɓa zuwa ba, na san wadda na gani a gidanku ba ita ce mamanka ba"

"In ji wa?"

Jauhar ta ce "Babu uwar da zata zauna hankalinta a kwance, alhali an yi wa ɗanta sharri an tsare shi".

"Mama ta mutu" ji tayi kamar ya soka mata mashi, ta kalleshi ta ce "Kai ma ka san pain ɗin master? Ka girma da ita ka santa?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Jiki a sanyaye ta ce "Ni ban ma santa ba, ina yawan takura ƙwaƙwalwata, dan na tunota, da rayuwar da muka yi tare, amma bana iyawa, baba ne yake da hotonta, nayi-nayi ya bani, ya hanani, idan na shiga ɗakinsa zan gyara masa, sai na ɗauki hoton in yi ta kallo ina jin daɗi, duk da ina jin kewarta, ina son in san yaya take ya halinta yake, yadda su mama suke faɗa ne ko akasin haka? Kawai saboda Baba ya saka hoton a cikin wallet ɗin sa, ya ce zai kai a wanko wani ya saka a yi enlarging ɗin sa ya bani, mama ta ɗauki hoton ta yayyaga, ta watsar wallahi ji na yi kamar ta yaga zuciyata, bana riƙo idan an yi mini laifi mantawa nake yi, ana yawan cewa bani da zuciya amma haryanzu a raina, na kasa jin cewa na yafe wa mama abun da ta yi mini. Da farko da na taso, na zata mama ce ta haife ni, daga baya na gane ba ita haife ni ba, sai na fara tunanin ko kawai faɗowa na yi ko tsinto ni aka yi, kowa yana da uwa ban da ni, wataƙila a haka aka haifeni, daga baya na yi tunanin ko kawai 'yar aiki ce ni, na zata 'yan aiki duk ba su da iyaye. Daga baya na gane baba ne babana, uwa ce bani da ita, sannu a hankali kuma na gane ina da uwa amma bata duniyar. Sai dai ba na jin daɗin irin yadda su mama ke aibata mamana, duk da ba ta raye ban san ta ba, har suna cewa mayya ce ta taɓa kama su ma, amma baba yana faɗar cewa mamana mutuniyar kirki ce, irin halina ɗaya da ita, haka yaya saifu ma yana faɗa. Mama ce mariƙiyata, na so in tashi kamar ita ce wadda ta haife ni, amma ƙiriƙiri sai ta nuna mini banbanci ba ita ta haife ni ba. Ta saka aka cire ni daga makarantar kuɗi, aka mayar da ni ta gwamnati wai ba na gane karatu ni daƙiƙiya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini. Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ƙazafin nan da suka yi mini, na fanɗarewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba. Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ɗa da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da daɗi master, wataƙila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sauƙi". Tana gaya masa raɗaɗin abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi.

Ya ce "You are missing her?" Yayi maganar yana kallonta.

Ta jinjina masa kai ta ce "So badly"

"Ki yi mata addu'a" ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka haɗu da wanda ku ke da irin matsala ɗaya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ƙyaleta.

Duk da kuka take yi, ta fara ɗaukarsa a hoto tana murmushi ta ce "Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya jiƙan mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu'ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma"

Har cikin ransa ya ji daɗin Addu'ar da take yi masa.

Ya kuma amsa da Amin.

"To mun gama ki tafi"

"To me na yi maka ka ke korata?"

Ya ce "Sigari zan sha"

Ta ɓata fuska ta ce "Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da hayaƙi, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye 'yar madara, yau dai ɗaya ayi haƙuri dan Allah a ɗaga ƙafa kar a sha da sassafen nan" kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta karɓe lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu.

"Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga leƙowa saura na ga mutum ya sha wani abu"

Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa.

Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Baba na yi waya"

Baba ya ce "Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya"

"Ka hau what's app mu yi video call"

Baba ya ce "To shikenan waliyya" Al'amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi.

"Master, nan ne wurin video call ɗin ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Tana kira baba ya ɗaga fuskarsa ta Bayyana a screen ɗin wayar.

"Baba wayata touch screen ce mai kyau".

Baba yayi dariya ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?"

"Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what's app, zan din ga kiran su kuma a waya"

"To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?"

"Master ne ya saya mini" sai kuma ta ce "Au amm maigidan ne ya sai mini"

Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki ɗaya"

"Amin baba" ta kaste wayar.

"Master " ya ɗago ya kalleta.

"Na gode sosai" ya ɗan tsuke fuska ya ce "Kin faɗa kin sake, ya isa haka"

"Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole".

Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take roƙon gwamna, sarki da kuma jami'an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ɗa da yayi, ya soke shi da wuƙa, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ƙarfi, tana neman a bi wa ɗanta hakkinsa.

Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al'amin, tamkar bai ji me aka faɗa a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ƙururus ƙurus ko a jikinsa an mari dutse.

Ayshercool 08081012143

32 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955Jiki a sanyaye jauhar ta ce "Master, dama rigima ka je ka yi, ka ji wai a nemoka"

Bai tanka mata ba, ya ɗauki kofin shayinsa, ya kai bakinsa.

"Dan Allah ka yi magana, menene abun yi yanzu? Ko zuwa zamu yi mu ba ta haƙuri" kallon Allah ya kiyaye ya yi mata.

Ta gyara zamanta ta ce "Ka san wani abu? Uwa uwa ce, kuma duk lalacewar ɗanta tana son shi, ba zata taɓa mantawa da kai ba, illata mata ɗa da ka yi, babu faɗuwa a ciki idan mun je mun bata haƙuri, idan dan ɗan wani abu mu bata. Ba yanzu ake ji ba gaba ake ji master, duk rintsi duk wuya kar ka bari wani ya ƙullaceka, sai ka manta ka cutar da mutum, amma nauyin hakkinsa yayi ta ɗawainiya da kai".

Ya shanye shayinsa tsaf, kamar a mafarki ta ji ya ce "Alhamdilillah"

Ta ce "Masha Allah, Allah ya ƙara mana wadatar zuci da rufin asiri, mu koma waccan maganar master, dan Allah ka yarda mu je mu bata haƙuri"

Ƙwanƙwasa gate ɗin gidan aka fara yi, Al'amin ya tashi ya je ya buɗe.

Ɗaya daga cikin yaran unguwar ne marasa ji, ya risuna ya ce "Allah ya ja zamaninka"

"Ya aka yi?"

"Wallahi guduma ne suka yi faɗa da dattijonsa jiya, ya kore shi daga gidan ya ce ya bar masa gida, ya sallamawa duniya shi, shi ne yau ya je ya sha wani abu, gashi can ya kulle mai unguwa a gida, da makami ya ce sai ya sara shi, an kirawo jami'an tsaro an kasa buɗe gidan"

Ya ce "Mu je in gani"

Suna zuwa gidan mai unguwa suka tarar da mutane cirko-cirko a ƙofar gidan, ga 'yan sanda su huɗu, ana ta fama a buɗe ƙofar gidan an kasa, sai kururwar mai unguwa ta cikin gidan, yana a taimake shi, a raba shi da ɗan sa kan ya kashe shi"

Al'amin ya zagaya, ya kama katanga ya dira cikin gidan, ya tarar da guduma a tsaye a ƙofar ɗakin mai unguwa, riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa, sai ƙyalli take yana dukan ƙofar ɗakin, yana maye yana sai ya kashe mai unguwa babansa.

Sauran matan gidan da yara, duk sun rufe ɗakuna suna neman ɗauki.

Al'amin ya tunkare shi, yana zuwa ya riƙe shi, ya karɓi makamin hannunsa ya kwaɗa masa mari, hakan ya sa ya ƙara gigicewa, ya danƙo rigarsa ya buɗe ƙofar ya fito da shi sai tangaɗi yake yi.

'yan sandan suka yo kansu, za su kama guduma, Amma Al'amin ya ce "Zamu zo da shi station anjima idan ya dawo hayyacinsa.

Mai unguwa da ya tsira da ƙyar ya ce "Ofusa kar ku bari ya tafi da shi, dama shi yake goya musu bayan iskanci a unguwar nan, da ɗa na bai kai haka lalacewa ba, a haɗa a Kama har da shi".

Al'amin bai kalleshi ba ya ce "Ko ya gudu ni a kama ni, ba zai gudu ba, idan ya dawo hayyacinsa zan kawo shi da kaina, mu haɗu a station zuwa ƙarfe biyar na yamma ina son a zauna da babansa"

"Shikenan, mu na jiranka"

Mai unguwa ya ce "Ofusa ya zaka yi mini haka, yaron da ya nemi rayuwata"

"Mai unguwa ka jira ya dawo hayyacinsa mu gani, Allah ya kaimu ƙarfe biyar ɗin.

Jauhar na wanke-wanke, Al'amin ya turo ƙofa, hannunsa riƙe da guduma, ta tashi tana bin sa da kallo.

"Sako hijjabinki, ki kawo mini tabarma"

Ta jinjina masa kai, ta sako hijjabi, ta kawo masa tabarma, ya kwantar da guduma, ta ƙare masa kallo ta ce "Wannan ai shi ne ya hana wani ya sare ni, lokacin da na je gida da aka tsare ka"

Al'amin ya ce "Kawo mini ruwa a bokiti da kofi"

Ta kawo masa ruwa, ya ɗiba ya dinga sheƙawa guduma a ka, ya din ga zabura kamar zai zare, ya ɗaukko gawayi a kurfotin Jauhar, ya daddaka ya kaɗa a kofi, ya matse guduma ya dinga ɗura masa a bakinsa, ya sha wani ya zubo da wani, ya gama ya hankaɗa shi ya kwanta.

"Master wai meya same shi ne? Ba shi da lafiya ne?"

"Ƙwayar da ta fi ƙarfin kansa ya sha, ya kusa halaka mahaifinsa"

Waro ido ta yi ta ce "Mahaifinsa kuma? Subhanallah lamari ya ɓaci"

Bayan mintuna arba'in, guduma ya wartsake, ya din ga kallon gidan, sai da yayi ido huɗu da Al'amin, sai ya ƙara nutsuwa.

"Ka farfaɗo?" Guduma ya sunkuyar da kai.

"Ka san me aikata ko?" Yayi shiru bai ce komai ba.

Al'amin ya yi ajiyar zuciya ya ce "Me ka sha?"

"Sigari ce"

"Da me?"

"Itakaɗai"

A fusace ya ce "Zan saka maka ƙarfe wallahi, uban me ka sha ka ke yinƙurin kashe mahaifinka?"

"Wiwi ce kawai ban sha komai..... Ba rufe baki ba, Al'amin ya riƙe maƙogwaronsa ya ce "Zaka faɗa ko sai ni na kashe ka?"

A rikice jauhar ta ce "Dan Allah Master ka ƙyale shi, kar ka kashe shi"

Cikin kakari guduma ya ce "Baƙin capsule ne"

"Waye ya baka, kuma waye yake dillancin sa a unguwar nan".

"Botorami ne"

"Botorami, yaran da suka sareni, na ƙyale shi, shi ne ya fara sayar muku da wannan muguwar ƙwayar? To wallahi sai ya bar unguwar nan. Uban me babanka yayi maka ka nemi kashe shi? Bayan sharrin ƙwaya har da iskanci, uban meyasa ba ka yi yinƙurin kashe kowa ba sai shi?".

Cikin damuwa guduma ya ce "Kora ta yayi, ya ce kar na sake zuwar masa gida"

"Ba dole ya kore ka ba, tun da abun naka babu hankali a ciki, in anjima zamu je police station, ka bashi haƙuri, idan kuma ka bari yayi maka baki, ka shirya lalacewa da taɓewa fiye da wadda ka ke ciki yanzu" ya jinjinawa Al'amin kai.

Al'amin ya ce "Ka zauna a nan kar ka fita ko ina"

Jauhar mamaki ta din ga yi, dama Al'amin ya san abun da ya dace, amma shi yake wanda bai dace ba.

Jauhar ta gama abincin rana, ta zuba ta bawa guduma, ya karɓa ya ce "Ya gode"

Al'amin ya zaunar da shi yana yi masa tambayoyi, sai dai bayanin da ya yi wa Al'amin, a kan irin rayuwar da ya tashi a kai, gaba ɗaya jikin jauhar yayi sanyi, wato wasu lokutan mutane na yin gaggawar yankewa wasu hukunci, ba tare da sanin ainihin abun da ke ɓoye ba.

"Da la'asar suka tafi police station, tun da suka je mai unguwa yake bala'i, har da cewa 'yan sanda su kama guduma su yi masa duk abun da za su yi masa shi yafi ƙarfinsa.

"Uwarsa ce ta lalata shi, sannan ta dawo mini da shi, baya sana'r komai sai shaye-shaye na tsiya da ya ɗorawa ransa, yau kuma rayuwata yake nema, to wallahi ba a haifi ɗan da zai kashe ni ba, waccan shashashar uwar ta sa ita ce silar komai, bayan ya lalace ta nannaɗo ta kawo mini shi"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull