Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 31
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 31: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 31. Al'amin ya ce "Ina mamakin yadda aka bawa mutum irinka…
4,476 words
Al'amin ya ce "Ina mamakin yadda aka bawa mutum irinka jagorancin al'umma alhalin ba ka iya jagorantar gidanka ba. Kai da ka haife shi, baka iya bashi tarbiyya ba hukuma ce za ta tarbiyantar maka da shi? Ka san ba zaka iya kula da shi ba meyasa ka haife shi? Da ka saki majaifiyarsa ka maye masa gurbinta? Sakinta ka yi ka bar mata shi, ba ka san cin sa da shan sa ba, balle iliminsa da lafiyarsa, baka nuna masa sana'a ba, baka bashi jari ba, ita ba cikakken ƙarfi ba itakaɗai tayaya zata iya yi maka rainon ɗa? Ka san jikinka yana buƙatar ka auri mata barkatai, ka yi jima'i ayi ta haifa maka 'ya'ya amma ba ka tunanin inganta rayuwarsu, ko buƙatar ka kawai ita ce buƙata?"
"Kaga Al'amin ya isa hak.... Al'amin ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya cigaba da magana.
"Babu in da za shi, tun da ka haife shi, dole ka kula da shi, ka yi masa role ɗin uwa tun da ka saki uwarsa a lokacin da ya fi buƙatar ku rayu tare, idan ba haka ba ko ba shi ba, a cikin wannan tulin 'ya'yan zaka samu mai halaka ka.
Ya mayar da idonsa kan Guduma ya ce "Kai kuma ya muka yi da kai?"
Guduma ya durƙusa ya ce "Baba dan Allah dan Annabi ka yafe mini, ka yi haƙuri ba zan sake ba in sha Allah, dan Allah ka janye korar da ka yi mini daga gidanka, nayi kuskure ka yi haƙuri "
Sai dai mai unguwa yayi tsit, dan kuwa Al'amin ya gama kwaikwaye shi a gaban mutane, yayi mamakin maganganun da suka fito daga bakin Al'amin ɗin.
"Officer, zan kawo yaron da yake sayar da wannan capsule ɗin, a riƙe shi a matsa shi, ya faɗi ina yake samota" ya sake kallon guduma ya ce "Ka shelanta, cikin unguwar nan, duk wanda na kama da sayar da irin wannan nau'in kayan, sai na lahira ya fi shi jin daɗi"
Ya jinjinawa Al'amin kai.
"Yanzu dai ina nema masa afuwa, yayi nadama in sha Allah ba zai sake ba".
"Idan ya sake fa, ni fa gaskiya rayuwata tana cikin hatsari"
"Ayi rubutu, duk abun da ya yi zan ɗauki laifin"
Ba mai unguwa ba, har Guduma Nura sai da ya kalli Al'amin.
Aka yi sulhu da rubuce-rubuce, suka fito, guduma ya risuna yana yi wa Al'amin godiya.
"Manta, mu je ka rakani asibiti, kan waccan uwar mitar ta sakani a gaba"
Guduma ya ce "Antynmu ayi mata godiya, abinci yayi daɗi na gode master" bai ce komai ba, suka tafi asibiti.
Ko da suka je emergency, Al'amin har gaban gadon yaron da ya karya ya je, ya tarar da shi a kwance, ana saka masa ruwa. Yana ganin Al'amin ya rikice, ya yinƙura zai ɗago, Viper ya mayar da shi, ya kalle shi ya ce "Na ji babarka na kururuwa na nakasta ka, a ɗaukar mata mataki, kai ba ka gaya mata babu mai iya ɗaukar mata mataki ba? Yanzu ka dawo hayyacinka ka tuna abun da ka yi ko? Ba ka sanni ba ko? Saboda ka sha ta gaya maka ƙarya, ni ka tunkara zaka sara ko? Wai ba kai ne ɗan mama ba, da aka rufe kwanaki madaki ya saka ka kashe wani yaro a dabarku ba? Ya shiga ya fita an sake ka, yanzu kuma da ka nakasa ya kasa taimakon ka ko?". Ya sunkuyar da kai ya yi shiru.
"Za a zo a biya kuɗin maganinka, nan gaba ka sake zuwa ka tari gaban tirela, ta kanka zan bi"
Ya kalli guduma ya ce "Tashi mu ware"
Ya tashi suka tafi, kamar wa da ƙani, suka bar mai unguwa da kunya.
Bayan fitar su Al'amin, jauhar ta kaiwa telar da take yi wa aiki kaya, ta rage mata wani abu a cikin kuɗin, amma ba ta bata duka ba.
Ta tarar da yaran matan layin, suna ta bajekolin magungunan mata, ana ta shewa.
"Jauhara ba za ki sayi abun arziki ba, ga kaya nan sai wanda ki ke so, kuɗi kuɗi iya kuɗinki iya shagalinki"
Kawai tayi murmushi ta basar da su.
Wasila ta ce "Wai sai an yi magana sai ki wani din ga mazewa kamar baki san komai ba? Ke an daina irin wannan abun kamar a zamanin da, idan baki zanzare kin fitsare ƙafafuwanki ba,bar ganin mijinki a haka ba ruwansa da kowa, wallahi sai ki ga ya fara 'yan leƙe-leƙe, ki zo ki ɗauki gyara hajiyata, ita mace sai d gyara, wannan kyan fuskar ta ki ba shi kawai yake so ba"
Jauhar ta ce "Hmm Anty wasila kenan"
"Ba wani anty wasila, malama ki rage maƙo dan Allah, kin iya neman kuɗi sai aukin saka turaren wuta a gida, da goge goge, amma ba zaki sai kayan gyara ba, ina ta tallata miki kayan maman neehal ɗin nan, baki ga kyan su ba, amma sai ki yi burus".
Suwaiba tela ta ce "Wai wasila ki ƙyaleta mana, ki ka sani ko tana abun ta, idan tana yi gaya miki zata yi?"
"Ba wani, ni fa jauhar ƙanwata ce, ƙanwa na ɗauketa, kunyarta tayi yawa Allah ya sa ba haka ki ke yi masa ba, babu yadda za ayi ki je ki ganta da shirt da wando, sai uban hijjabi da dogwayen riguna kamar zata yi ɗawafi. Ki tsuke ki ci zamaninki tun da ƙuruciyarki, ni ga wani tsumi nan na baki, na maman neehal ne, tested and trusted, ki gwada zaki bani labari. (0706 677 4630 ga lambar da zaku samu maman neehal, domin samun kayanta)
Kamar sokuwa haka Jauhar ta karɓa, kasancewar ta san ba wani amfani da zai yi mata.
A gurguje ta kammala abun da za ta yi a gidan, ta fito saboda irin manyan karatun da ta ji suna yi, da suka fi ƙarfin kanta.
Ta koma gida, ta din ga kallon robar abun da anty wasila ta bata, na wurin Anty lubabatu ma suna nan, ko kallonsu ma ba ta yi.
Aka fara kiraye-kirayen sallar magariba, tana salla, ƙarar wani babur ya cika mata kunne, bayan ta idar tana cikin lazumi, ta ji ana kokowar shigowa da abu, ta tashi ta fito tsakar gida, ta tarar da Al'amin yana shigowa da wani tsohon babur jincheng, hannunsa riƙe da salansar babur ɗin.
"Master, wannan kuma fa?"
"Jaki ne" ya bata amsa.
"Wai sai ka yi ta gaya mini baƙar magana, wai ko shi ne ya cika layin nan da ƙara?"
"Eh"
"To meyasa ka cire masa salansa? Ka ji ƙarar kuwa ba daɗi, kamar ya shekara ba a kunna ba".
Ya jingine salansar, duk ya ɓata jikinsa da baƙin mai, ya ce "Na fi son sa a haka"
"To wai a ina ka samo babur?"
"Sata na fara" yayi maganar zai shigar mata falo.
Ta ce "Allah ya baka haƙuri, amma tsaya na kai maka ruwa banɗakin tsakar gida ka yi wanka, idan ba haka ba zaka ɓata carfet ɗin da baƙin mai"..
"Naɗe abun ki na wuce, ba zan yi wanka a tsakar gida ba"
Ta shagwaɓe ta ce "Ba fa a tsakar gida ba, toilet ɗin tsakar gida".
"Ƙoƙarin shiga falon yake, tayi sauri ta ɗaukko tsumma, ta durƙusa ta ce "Bari na goge maka, kar ka ɓata mini carfet" ta gogge masa, sannan ya shiga.
Warin sigarin da yake yi ya sanya ta bin sa da ruwan zafi, ta matsa masa toothpaste a kan brush, ta ajiye masa.
Allah ya taimake ta, babu musu yayi wanka yayi brush, ya fito yana goge jikinsa, ya buɗe wardrobe ta shigo da sauri ta ce "Saura ka watso mini kaya ƙasa, na sake gyarawa, nuna mini wanne zaka saka na ɗaukko maka?"
Ya nuna mata, ta ciro masa su, kafin ya karɓa ta miƙo masa kwalbar turare ta ce "Ka shafa turaren, sai ka saka"
Haɗin da take amfani da shi ne, ta daka alumun, da farin muski na gari, da kanumfari, ta dafa su suka tsumu ta ta ce, ta zuba madarar turare a ciki.
Ya karɓa ya shafa, ya miƙa mata, ta karɓa ta ce "Ai naka ne, na bar maka"
Ya karɓa zai ajiye, ta ce "Baka ce ka gode ba" sai ya miƙo mata abun ta, da ya ce ya gode gara ya dawo mata da abun ta.
Tayi dariya ta ce "Hukuma sai da rarrashi, na janye ba sai an yi godiyar ba"
Ya ajiye, ya fara ƙoƙarin saka kayan, ta fita ta bashi wuri, shi kansa ya ji daɗin jikinsa sosai da sosai, ga ƙamshin yayi masa daɗi sosai da sosai.
Ya fita ya kame a falo, ƙamshin turare sai ɗibarsa yake yi.
Akwai English wears a cikin kayanta, sai dai ba ta taɓa gwada sakawa ba, dan kunya ma take ji, domin kuwa sai kwanan nan ta daina yawo da hijjabi a cikin gidan.
Da ƙyar ta iya fitowa da doguwar rigar atamfa, da ta ɗan kamata cif jikinta, ta zo ta zauna a falon, ta ce "Master ya ku ka yi a police station kuwa?"
"Labari zan baki ko yaya?"
Ta ce "Eh mana"
"Kunna radiyonki, ki ji labarai idan shi ki ke son ji".
Cikin shagwaɓa ta ce "Ni naka nake so"
Ya ce "To ni ban san me zan ce ba"
Ta ce "Ai shikenan"
"Yauwwa, na ce ba ka ga azumi saura 'yan kwanaki, yakamata ace ko sugar da lemo mu saya mu je mu gaida su Abba"
"Sai kin dawo" ya faɗa yana shan kunu.
"Master meyasa?"
"Kawai".
"Na san akwai dalili, amma koma menene ka yi haƙuri, ba a fushi da iyaye, kai fa ka gama yi wa wani nasiha ɗazu, meyasa ba zaka yi amfani da ita a kanka ba?"
Juya mata baya ya yi, irin idan kin gama kya yi shiru.
Zuciyarta cike da fargaba, ta taka ta je kusa da shi ta zauna ta ce "Masu sunanka manyan mutane ne, dattawa, ba sa haka, dan Allah kar ka saka mu shiga fushin Allah, iyaye ba abun watsarwa bane ba, ranar da babu su da kuɗi ba zamu gansu ba, mun rasa iyaye mata, mazan sai mu nemi albarkar su"
Ya ɗaga hannunsa ya ɗora a kan kunnensa, ta kalli dogwayen yatsunsa, faratansa sun yi tsayi.
"Gobe in Allah ya kaimu friday ce, a yanke farce, sumar nan ma tayi yawa yakamata a rage ta, ayi maka gyaran fuska kafi kyau idan aka aka rageta"
Juyowa yayi gaba ɗaya, ya ƙureta da idonsa.
Sai jikinta yayi sanyi, tsigar jikinta ta tashi yarrr.
"Kin fa dame ni" yayi maganar a hankali, amma muryar da yayi amfani da ita, har cikin zuciyarta.
"To me nayi maka na takura?" Shiru yayi bai yi mata magana ba, ya cigaba da ƙare mata kallo.
"Baka saka mini lambarka a wayata ba"
Ya miƙa mata hannu, ta bashi wayarta, ya saka mata lambarsa, ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga yi maka flashing, kamar sau arba'in a rana"
"Iya arba'in?"
"Eh, ko yayi kaɗan?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
"To ɗan yi mini downloading ɗin game"
Ya ce "Sai kin gama jarrabawa tukuna"
"Ai mun kusa in Sha Allah" ya lumshe idonsa ya ce "Allah ya bada sa'a"
"Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum master, 'yar madara na godiya"
Ta sake cewa "Dama wainar fulawa zan yi mana mu sha da tea, bari na ɗora"
Ta fita tsakar gida, ta hura kurfoti, ya biyo ta gaban kaskon ya zauna, sai dai kallon da yake yi mata duk ta takura.
"Master, kamar fa akwai ɓera a gidan nan, dan Allah ka sayo maganin ɓera"
Ya ce "Shi ma tsoron nasa ki ke ji kenan?"
Tayi murmushi ta ce "Eh, amma ba sosai ba"
"Ya haɗa nasa shayin, tana soya waina yana cinyewa"
"Master ban gane ba, idan ka cinye ni fa?"
"Sai ki soya wata"
"Ko kuma ka soya mini ba, ƙullin fa bashi da yawa, ka ƙoshi gaskiya" ta janye plate ɗin.
Ta gama ta haɗa nata tea ɗin, ta fara ci.
Ya zuba mata ido, cin abincin ma yanga take yi masa.
Yana zaune yana kallonta, ta gama ta haɗa wanke-wanke ta yi.
Ta gama komai, zata shiga ɗaki ta ce "Na gama taso mu tafi, kar sauro ya saka maka zazzaɓi".
"Dama na ce miki ke nake jira ne?"
Jauhar ta ce "Eh dole ka ce haka, tun da na cika maka cikinka, aishikenan sai da safe, dan Allah kar ka sha komai ka ji master".
Yayi mata shiru, ta ce "Master, magana nake fa, na san kana ji na, dan Allah kar ka sha komai ka ji Mai zamani"
Ɗagowa yayi ya kalleta, tayi masa murmushi, tasowa ya yi, ya biyo bayanta. Tsayawa tayi ta ga me zai yi mata.
Yana zuwa ya riƙe kunnenta ya ce "Me ki ka ce?"
"Master na ce"
"In kuma jin kin faɗi wannan sunan, zamu gauraya da ni da ke" sai dai duk wannan abun fuskarsa ba fara'a.
Cikin shagwaɓa ta ce "Kunnena zai cire fa" ya tura ƙeyarta, har ƙofar ɗakinta, ta ce "Kar in sake ganinki sai gobe in Allah ya kaimu".
"To na ji, amma dai kar ka sha komai dan Allah" wucewa yayi ɗakinsa, ta ƙarasa gaban gadonta tana murmushi.
Ta yi wanka, ta shirya ta shafa turarukan ta, ta nemi wuri ta kwanta. Sai murmushi take yi, tana jin daɗin cigaban da ake samu a kan zaman su.
Ta kalli pillown da take rungume da shi, ta shafi pillown a hankali, tana tuna hirarrakin da aka yi ɗazu da su Anty wasila.
Tabbas abun da take ji game da aure ya sha banban da abun da ta tarar, to ko ba haka abun yake ba? Sai kuma ta tuna har a littatafan addini ta karanta.
Hakan yana nufin Al'amin ba shi da lafiya ne? Ko kuma ita ɗin ce ba ta gabansa, sai dai ya ci, yayi shaye-shayensa ya je yawonsa, ko kallon kirki ba ta ishe shi ba.
Tunani take yi ko dai tana da wani naƙasu ne, da ya sanya ba ta gabansa, ko da wasa bai taɓa ko makamancin yi mata wani abu ba.
Ta yi juyi ta kalli gadon, yanzu idan Al'amin ba shi da lafiya ne, ko bashi da ra'ayin hakan, haka za su cigaba da rayuwa kenan, ita ba kowa ne da ita balle su tattauna, ko da wasa kuma ta san ba zata tunkare shi da wannan maganar ba, ko ta kai masa kanta, wannan ma ba mai yiwuwa bane ba.
Wataƙila wani babin ne na ƙaddarata. Ta faɗa a zuciyarta, a lokacin da bacci yake ƙoƙarin awon gaba da shi.
Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, wani matashin saurayi ne, yana ta kai komo a tsakanin wasu gidaje can wajen gari, da alama wani abu yake jira.
Wani mutum ne ya zo a keke, ya tsaya ya kalle shi ya ce "Nan ce sabuwar mahaɗarmu?"
Mutumin ya amsa da "Eh, kuma ka yi taka tsantsan, kar a gane, kar kuma ka yadda da kowa"
"To shikenan, yanzu zan je na rarrabawa gayu kayan, ga wannan balance ɗin jiya ne" yayi maganar yana miƙa masa kuɗi, mutumin ya karɓa, shi kuma ya tafi.
Sai dai ya nufi in da yake son tafiya, ya ji an danƙi jijiyar wuyans, a take ya sulale sumamme.
Suka ɗauke shi suka tafi da shi, Walid ya kira Al'amin ya ce "Maganarka haka take mai dogon zamani, mun kama yaron nan, ka san yaron madaki ne ya rarraba musu ita, idan ban yi kuskure ba madaki yana cikin manyan dilolin capsule ɗin nan.
"Ku shigo da shi cikin unguwa, ku ɗaure shi, ɗauri na gasken gaske ku bar shi, zan yi magana da 'yan sanda"
"To shikenan, amma ka din ga yi kana ankarewa da hankakin nan ka san ba mutunci suka cika ba"
"Ina ankare, sai da safe"
Har ƙarfe tara na safiya, Al'amin ya je yayi sabgoginsa ya dawo, jauhar bacci take yi.
Ya tsaya a ƙofar ɗakinta, yana ƙwanƙwasawa, a hankali ta yi juyi, ya ɗaga labulen ya ce "Ba a san gari ya waye ba ne? Yunwa nake ji"
"Afuwan gani nan" tayi maganar cikin muryar bacci.
Da kayan jikinta ta fito falo, gashinta duk a hargitse ta ce "Yi haƙuri, baccin nawa ne yayi nauyi".
Ta tarar ya sayo gasara, ya sayo awara ɗanya.
Mamaki ta din ga yi, a ina ya san ana sayarwa, amma tafi yadda aikawa yayi a sayo masa.
Ta shiga ɗakinsa gyarawa, ta buɗe wardrobe ɗin sa, kayan da ya cire jiya ta tattara zata wanke, ya kwasa ya mayar da su cikin wardrobe ɗin, kayan dai da ba ta so, sai da watso su, ya ɗauki abun da zai ɗauka duk ya cukurkuɗa su ya mayar cikin wardrobe ɗin.
Yana ganin ta tsaya tana kallon wardrobe ɗin, yayi waje dan ya san mita za ta yi.
Ta kuwa biyo shi falon "Master, yanzu duk gugar da nayi ka wargazata, ka haɗa mini wankakkun kaya da marasa wanki, har da jiƙaƙu duk ka gwamutsa mini su a ciki" tayi maganar kamar tayi kuka.
"Ke fa ki ka ce, na daina zubar miki da kaya ko ina a cikin ɗakin"
"Kuma master kaya kala ɗaya da zaka saka, sai ka hargitse ilahirin wardrobe ɗin? Zan samo maka bagco, ka din ga zuba marasa kyau a ciki, dan Allah ka daina hargitsawa" yayi mata shiru, ta gama mitarta ta gama, tana komawa gyarawa ya dafe kai, ta gama mitar kuma ta gyara.
Sai da ya tabattar ta fita daga falon, tana aiki a kitchen ya ɗaga wayarsa yayi kira.
"Kuna aikin da na saka ku?"
"Eh muna yi"
"Kar ku kuskura ku bari wani ya kwance shi, idan ba jami'an tsaro ne suka zo ba"
Ya gama karyawa, yana son ya tashi ya fice, ta tistiye shi da zancen yanke farce, haka ya koma ya zauna, ta saka reza ta yanke masa farce tsaf, tana yi tana yi masa surutu.
Baya son ta gane ya yi wata tsiyar a waje, kar ta zauna ta yi ta masa kuka.
Ta yi masa gugar kayan da zai saka, wai ya tafi masallacin juma'a, shi rabonsa da zuwa sallar juma'a har ya manta, yayi wanka ta bashi goggagun kaya, ta shafa masa turare ta ce "Ka dawo da wuri dan Allah, ina gama abinci ka ci da zafinsa, ka yi mana addu'a idan ka je"
Ya gurgura babur ɗin sa da ya cire wa salansa, ya fice ya cika layin da ƙara.
Daji ne sosai babu gida a gaba, babu a baya, daga shi sai direbansa suke tafiya sai P.A, har suka ƙaraso wurin wani dutse, suka sauka da shi da P.A, suka tattaka har gaban bukkar.
Cikin bukkar tamkar fadar mahaukaci, duk an yi mata ado ƙahunhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, har da wasu sassa na ƙashin ɗan Adam.
Gefe ga wani mutum na tsurut, kamar an fato shi, jikinsa ko riga babu, daga shi sai wani ɗan warki ɗaure a ƙugunsa.
Suka nemi wuri suka zauna, ya kalli indabo ya ce "Aikin farko yayi, wa'adin da muka ɗiba maka yau ya cika, aljanu sun sha jini a ƙasar da suka buƙata. Saura mahaɗin aiki na biyu, za a samo matashiyar yarinya, matar aure shekara sha biyar zuwa sha takwas, zaka kasance da ita, tsawon kwanaki uku, a ketowar alfijir ɗin kowace rana, zaka fara aikin a larabar tsakiyar wata, shi ne sa'ar aikin! An ɗeba maka wa'adin kwanaki Arba'in ba biyar"
Ayshercool 08081012143
33 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955
Jinjina kai indabo yayi, ya ce "Za ayi ba zai gagara ba, zamu dawo idan an kammala aikin, kuma wa'adin da aka ɗibar mana ya cika".
"Shikenan, nasara tana tare da kai, ba yaƙini muke da shi ba, tabbaci nake bakaz duk da akwai ƙalubale a gaba, sai da ba za su gagara ayi maganin ƙalubalen ba, amma a gaba kaɗan ɗin akwai dutse, da zaka yi karo da shi, na buga na duba, duk babu hanyar maganin dutsen nan, sai dai ayi ragas, ko ka kar dutsen ko ya kar ka"
P.A ya ce "Kuma babu yadda za ayi da dutsen? Ko wata mafitar?"
"A yanzu dai babu,
Suka tashi suka fito, suna tafe a hanya Indabo ya ce "P.A"
"Na'am honorable"
"Bokan nan kullum cikin faɗin ayyuka masu hatsarin gaske yake, ina tsoron tonuwar asirina, kar mu je in sake janyo wa kaina jagwal kana kallon yadda yarinyar nan Naja'atu ta zame mini alaƙaƙai"
"Mu bi komai a sannu sir, zamu yi nasara kuma samo yarinya ba zai gagara ba, ko cikin ƙauyukan nan aka bincika za a samu, ko kuma Naja'atu ta samo a irin mutanen da ke hulɗa da su" yayi ajiyar zuciya ya ce "Ba zan so ce a samo ta ɓangaren ta ba, amma kai na ɗora maka ragamar samowar"
"Za a bincika in sha Allah sir"
"Yayi, ina jiranka, ka ga idan lokaci ya ƙure, aikin da muka yi ya koma baya"
"Haka ne, da yardar Allah ka ci kujerar nan ka gama, mu je injiniyoyin suna can gida suna jiranka, aje ayi lissafi"
"Ok to, Aminu haryanzu ya ƙi zuwa ko?"
"Wallahi yaƙi, Allah da wani wanda zai iya yi mana irin kasadar da yake ɗauka, da mun canza shi, ɗan rainin hankali ne, ko fushi yake saboda wannan karon ba ka fito da shi ba?"
"Da fushi yake yi, ba zai ɗauki wayata ba, kuma ina son aiki da shi, ba ya jin kasada komai zafinta kuma ba shi da mgana ko kisan kai zaka yi a gaban sa, sai ya ga dama zai ɗaga kai, balle ka ji zancen a waje. Sannan babban abun shi ne, bokan nan ya ce nasarata tana tattare da wanda yake zubar mini da jini, na riƙe shi sosai, shiyas nake shanye iskancin sa".
P. A ya ce "haka ne ya na da amana, ba shi da magana sam, amma shi ya san da hakan ne?".
"Haba dai, hauka nake yi na bari ya sani, ba abun da ya sani, kawai aiki yake yi mini"
Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, manyan injiniyoyi ne zaune a falon indabo, suna ta lissafin ginin plazarsa. Ga wanda zai tattauna da su a kan harkar yaƙin neman zaɓensa, suma su na jiransa.
Al'amin yana cikin falon, ana ta lissafi, shikuwa yana hakimce yana kallon tv.
Sai da aka gama lissafi, za ayi total ɗin kuɗi, Al'amin ya kalli shugaban engeneers ɗin ya ce "Kayi plusing da kuɗin siminti buhu shida, da tiles carton biyar"
Ya ce "Na menene?"
"Ina ruwanka, ka saka kawai".
Injiniya ya kalli Indabo, Indabo ya ce "Kuɗi ka ke buƙata ne na baka?"
"Gyaran gidana zan yi nima"
Indabo ya ce "Engeneer a rubuta, a bashi"
Al'amin ya sake cewa "Akwai yarana mutum biyar, da nake son a saka mini su a cikin aikin ginin nan, su yi su ma a sallame su"
P.A ya ce "An gama mai dogon zamani"
"Zamu zo tare da su, ni ne cikon na shida, da ni za ayi aikin a biyani"
P.A ya sake cewa "Ba ka da matsala"
Aka gama aka sallami injiniyoyi, 'yan jami'iyya suka shigo, duk yana zaune, aka gama meeting.
Duk sai da suka gama, sannan Indabo ya mayar da hankalinsa da Al'amin ya ce "Mai zamani" ya ɗaga ido ya kalli indabo.
"Akwai tafiya da zan yi ƙaddamar da takarata, a yammacin garin nan, ina buƙatar tawagar ka kai da mutanen ka, saboda ban san ya zata kaya a wurin ba, 'yan sandan nan gaibu ne wasu lokutan".
"Yaushe ne?"
"Nan da kwana goma"
"Cikin azumi kenan?"
Indabo ya ce "Eh"
"Allah ya kaimu, baka da matsala"
P.A ya ce "Allah ya ƙara maka nisan zango mahadi mai dogon zamani. Ina matarka kuwa?"
Da sauri ya kalli P.A ya ce "Kamar ya ina matata, meye haɗinka da ita?"
"A'a babu komai, lokacin da kana tsare ne, ta zo ita da Walid, ko da yadda za ayi ka fito, lokacin honorable baya nan" Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.
Wata ƙatuwar mage ce ta shigo, da matasan 'ya'yanta, fara tas kana ganinta ka san 'yar waje ce.
Al'amin ya tashi ya nufi in da take, ya saka hannu ya ɗauki guda ɗaya ya ce wa P.A "Wannan mace ne ko namiji?"
"Namiji ne"
"Zan tafi da shi"
P.A ya ve "Ka san kuɗin abun nan kuwa? Ya kai dubu ɗari shida fa, wannan ƙaramin".
"Da gold aka yi shi ne?" Yayi maganar yana nuna ɗan muzurun da yake ta ihu saboda ya ji matsa.
Indabo ya ce "A'a ɗan Germany ne"
"Tun da ba daga aljanna ya zo ba shikenan, kai kawo leda na saka shi" yayi maganar yana kallon mai goge-goge.
"P.A ya ce wace irin leda kamar zaka ɗauki masara, kwando dai za a baka.
Yayi ƙerere, aka kawo masa kwando, ya saka muzurun ƙato da shi fari, jikinsa cunkushe da gashi mai kyau.
Ya kalli Indabo ya ce "Zan tafi"
Indabo ya yi murmushi ya ce "Ga abun kuɗi nan ka ɗauka a hannunka, ai ba sai an sallameka ba"
"Za a sallame ni ko in tafi?"
"P.A sallame shi"
P.A ya buɗe jaka, ya ɗebo kuɗi ya miƙawa Viper.
Al'amin yayi masa wani mugun kallo, indabo ya ce "Ƙara masa"
"Ya ƙara ɗebowa, ya ƙara masa"
Ya karɓa ya ce "Na karya wani yaro, yana emergency, babar yaron tayi maganar a kamani, a bi wa ɗanta hakkinsa, yana can a emergency asibitin tsakiyar gari, a kashe wutar, ko ta ƙone yiwuwar aikinka, hankakin nan suka yi ram da ni, ba zan yi aikinka ba" daga haka ya fice daga falon.
P.A ya ce "Kai, honorable Mai zamani yana hawa kanmu da yawa wallahi, wai sai abun da yake so za a din ga yi yayi ta yi wa mutane tunƙaho?"
Indabo yayi murmushi ya ce "Rabu da shi lokaci ne, bari a ci zaɓen, ai ka ga mutumin can ya ce akwai nasarar mu a tattare da shi, yanzu abun da za ayi, ka koma ka yi waya, ka saka a haɗa wata tawagar ta 'yan daba, da zasu far mana a wurin taron, yadda za a samu a zubar da jinin shi ma a can. Sannan ka tara mana 'yan media, idan hakan ta faru a ce abokan adawa ne suka yo hayar 'yan daba suka far mana".
"An gama honorable, yanzu kuwa zan je na tara su na sanar musu tun yanzu"
"Yauwwa, idan ka gama da su, a hanzarta ko aike ka yi wurin wanda ya karya ɗin, a rufe bakin babarsa"
"Ok sir"