Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 89

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 89

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 89: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 89. "Abba dan Allah ka yi mini magana mana, ko zan samu ƙwarin…

4,376 words

"Abba dan Allah ka yi mini magana mana, ko zan samu ƙwarin gwiwar sanar maka da abin da na zo maka da shi.

"Kin gama fushin kenan?"

"Abba ka fahimce ni, ka yi mini uzuri dan Allah. Na kasa sarrafa zuciyata ne a wannan lokacin, ka yi mini uzuri ni ma 'yar uwata na rasa. Na je wurin baba mun yi magana ne, dan Allah Abba.

"Stop it please, in dai maganar mahaifinki ce ba na son jin komai menene, sannan ki je ki cigaba da kare wanda ya kashe 'yar uwakki saboda rashin kishin kai".

"Abba ba shi ya kasheta ba...

"Ba shi ya kasheta ba ke ce kenan? Azzalumin mutumin nan, bayan kashe mini 'yar uwa, yar da ta bar masa ma, ya kasa riƙeta babu abin da za ki gaya mini a kan mahaifinki na yarda Nabila, Kodayake laifina ne, da na kai masa ita, ni dama ke na kai".

Jiki a sanyaye ta ce "Abba...

"Get out Nabila, ba na son ganinki ma, fita ki bani wuri" ta haɗiye wani abu mai mugun ɗaci, ta fice daga ɗakin nasa.

Ɗakinta ta tafi, kawai ta nemi wuri ta kwanta, baba magajiya ta kawo mata abinci, amma ta ce ba zata ci ba.

Washegari da sassafe, Viper ya isa ƙofar gidan su Nabila, ya tsaya ya na kiran wayarta, Nasir ya fito da motarsa.

Bai kula shi ba ya ci gaba da kiran Nabila, ta ɗaga ya ce "Ina waje" mintuna kaɗan ta fito cikin shirinta na fita aiki.

"Ina kwana"

"Lafiya ƙalau, ba wata matsala dai ko?"

"Akwai mana, meyasa za ka tambayeni, kai ma ka san akwai muje kawai"

Wani irin azababben kishi, ya turnuƙe Nasir, ya fito daga motarsa ya tunkaro su.

"Nabila, ki na nufin kin fifita son zuciyarki a kan abin da Abba ya gaya miki?"

Nabila ta ce "Mu ƙaddara haka ne, meye naka a ciki?"

"Mutumin da ya kashe 'yar uwakki, haryanzu ki na kan bakanki na kare shi kenan?"

"Kai ma da ka samu dama, kashenin za ka yi, domin cikar naka muradin. Yaya Nasir kallonka kawai nake yi, kuɗin da aka baka domin ka kama shi, wasa da rayuwata da ake yi, ba tare da ka sanar mini ba, ko ƙoƙarin bani wata cikakkiyar kariya ba, duk fa kallonka nake yi" saroro ya yi ya na kallon Nabila.

Viper ya riƙe gefen kwalar Nasir, ya risunar da muryarsa ya ce "Kar ka manta, ni ba karabutin ɗan daba bane kawai, hatta evidence na kuɗin da aka baka, ina da shi. Dan haka ka ajiye kishi a gefe sauran mutuncin da ka ke da shi a idonta ya zube. Nabila ta wa ce, ko da kuwa ita ma zan kashetan ne"

Nasir ya kalli idon Viper, Viper ya kalle shi.

"Na fi ka gwagwarmaya da ganin wahalar rayuwa, dan haka ba wani zare ido, da wani abu makamancin haka da zaka yi mini da zai tsorata ni. Ka daina shiga harkata dan ka ganni tare da ita, idan ka ci gaba kuma abin da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba".

Tsagwaron kishi ne yake damun Nasir, kamar zuciyarsa zata tarwatse haka ya na kallonsu, suka hau mota su ka tafi.

*** Abbu ya na zaune ya na ta lissafi na shekara, nawa zai fid da zakka da sauransu. Hankalinsa ya yi zurfi sosai a tunanin.

Rahila na gefe ta na ta yi wa shahida masifar, an raba auren su, ta dawo gida su na haɗa kafaɗa. Shahida ta ce "Auren da da shi, gara babu, ni wallahi ba na dana sani".

"Ai dama ba zaki yi ba, nan gaba za ki fahimci abin da nake gaya miki"

Wayar Abbu ce ta fara ringing, sai da ta yi sau kusan uku, sannan ya ɗaga.

Jin muryar babban mutum ya sanya ya nutsu, su ka gaisa.

"Daga nan hedkwatar hukumar hisba ne, mun kamo 'yarka a cikin sabon gari, shekranjiya da daddare, kuma a binciken da aka yi, an gano ta na ɗauke da juna biyu, kuma ga cutar ƙanjamau, dan haka mu na buƙatar ka zo mu na son ganinka"

Abbu ya ce "Ba ni ne mahaifinta ba, ta baku lambar babanta ba ni ba ne ba" ya gama wayar, Rahila ta ce "Na ji ana maganar hisba, ka ce ba kai ne babanta ba"

Ya ce "Eh, 'yar ki da ki ka ce mini ta na gidanku, ita aka gano a sabon gari, da ciki da kuma ƙanjamau, dan haka na ce a nemi mahaifinta ba ni na haifate ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace, ciki da ƙanjamau kuma? Wayyo Allana"

Tashi ya yi ya fice ya bar mata falon.

*** Garden ɗin da suke haɗuwa da Nabila a da, can su ka tafi.

Ta kalle shi ta ce "Meyasa ka kawo ni nan"

"Ina jin nishaɗi idan na zo irin wurin nan, sannan wuri ne mai sanya nutsuwa, ki ɗan huta kawai" wani irin daɗi ne ya ratsa Nabila, ganin yadda ya nuna damuwarsa a kanta ƙarara, sai dai ta basar da ta tuna alƙawarin da ta ɗauka.

Hannunsa riƙe da leda su ka ƙarasa cikin garden ɗin, ta zauna ƙamshin furannin wurin na ratsata, haka kurum ta ji zuciyarta na narkewa da ƙaunar mijin 'yar uwatta ta, da take ganin kamar ba ta kyauta ba cin amana ne yin hakan.

"Vi"

"Abla"

"Abba yaƙi fahimta ta, ya kore ni, ya ce muddin ina son zaman lafiya, to sai na bar shari'arka, na rabu da mahaifina".

Viper ya gyaɗa kai ya ce "Ya ɗauki zafi da yawa ne, amma zai saukko, ba ya bari kin kwana a gidan ba?"

"Eh, jiya da na dawo ma na tarar ya na faɗan babu ruwansu da ni, ina ga so su ka yi ya kore ni ma, duk sun gaje mini kaya, har da motata"

Ya ce"Sorry"

Ta numfasa ta ce "Ka na addu'a kuwa, a kan Allah ya bamu sa'a?"

Ya ce "Eh, ina yi"

"Masha Allah, amma fa dole mu ƙara, kuma ka yi haƙuri dole za mu yi exposing wasu abubuwan da ka yi a kotu"

Ya ce "Kamar yaya? Ba dai aikina ba?"

Tayi murmushi ta ce "Ba wannan ba, rashin jin da ka yi, da alaƙarka da indabo, ka san babban kuskuren da ka yi? Biye wa Nura guduma da ɓoyewa likitoci ainihin abin da ya same shi. Da sun yi documenting hakan zai bamu ƙwarin gwiwa da cikakkiyar hujjar dalilin da ya sanya rigima tsakaninka da Indabo. Yanzu dole abin ɓoye ya fito fili, muddin lakwari ya kuma denying kashe jauhar, shaidar ɗan mama kaɗai ta yi rauni, dole duniya ta san da videon nan".

"Ki na nufin Videon Nura? No ba zai yiwu ba, cin amana kenan da karya alƙawari".

Ayshercool 08081012143

90 Ta girgiza kai ta ce "Ba ina nufin lallai sai videon ya fita ba ne ba, ka fahimce ni. Indabo sun san me muke shirin yi, ba fa za su ƙyale mu ba, bar ganin hankalinsa ya na kan ɗan sa da kuma tuhumar da ake yi masa, ya na da muƙarrabansa, ya na da iyayen gidansa da waɗanda siyasarsu ta dogara da shi, ba za su taɓa zuba ido su na kallonmu ba. Duk wani tanadi da shiri da yakamata mu yi, dole mu yi shi, ko da kuwa ya na nufin faɗar abubuwan da ka aikata. Dan ba kowa ne zai ɗauki cewar akwai wata alaƙa tsakanin ɗan daba da mutum kamar sanata ba, har ta kai ga ya kashe maka mata ba. Dole sai mun shirya da shaidu da hujjoji fa, ba da ƙanan lauyoyi zan kara ba, na sani manyan lauyoyi ne iyayena a harkar aiki, muddin aka kai ga gaɓar da sunan Indabo zai fito a cikin shari'ar nan. To fa tsuguno ba ta ƙare ba, dan haka kurum su lakwari ba za su kashe maka mata ba, kuma dole za su yi ƙoƙarin kare kansu, ko mu bamu faɗa ba, su za su iya faɗar wasu abubuwan da suke da alaƙa da ka yi daba da kuma dillancin miyagun ƙwayoyi, wanda laifi ne ga dokar ƙasa, da za na iya fuskantar tuhuma"

Viper ya yi shiru jikinsa a sanyaye ya ce "Da sauran rina a kaba kenan? haryanzu ban gama karɓar sakamon laifukana ba kenan" yayi maganar cikin damuwa ya na ɗan murza zoben hannunsa.

Cikin kulawa da matsanancin tausayin sa ta ce "In sha Allah komai zai warware, ai babu abin da ya fi ƙarfin Allah, kuma shi mu ke gaya wa. In sha Allah abubuwan da su ka faru, kaffarar laifukan ka ne, in sha Allah sai an tuhumi indabo a kan mutuwar jauhar, muddin sunan sa ya fito a kotu, to shi ma za mu yi ƙararsa ne, fatana Allah ya bamu nasara" yayi shiru ya na tunani.

"Vi" ta kira shi a hankali. Ya ɗaga kai ya kalleta amma bai yi magana ba.

"Ka ce wani abu mana"

"I have nothing to say"

"Idan ka karaya ni fa? Dan Allah ko yaya na ga alamar ƙwarin gwiwa a tare da kai mana, kar ka saka na karaya mana Please" ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Duk mai nema, dole ya sanya rai a samu ko rashi, duk wanda ya riske ni, zan karɓa da murna na gode wa Allah"

"Duk da haka, yakamata bawa ya kyautatawa Allah zato, burina ɗaya tak ya rage a duniya da nake fatan cika shi, shi ne ƙwato muku hakkinku, da kai da jauhar, ko da hakan ya na nufin ƙarshen rayuwata. Ina ta gudanar da bincike na a ɓoye, ina tattara bayanai, hatta report ɗin likitoci a kan mutuwar ta, ina processing na karɓa. Alhaji mu'azzam ya na taimaka mini sosai da sosai"

Nan da nan annurin fuskar sa ya ɗauke, rai a ɓace ya ce "Shi kuma me ya kawo shi cikin wannan maganar?"

"Komai ma mana, ka san abubuwa da yawa ban da taimakon Allah, ya sanya ya na tare da mu ya na taimaka mana, da tuni an kaimu ƙasa an ga bayanmu, bawan Allah nan ya cancanci yabo wallahi" banza ya yi mata yaƙi yi mata magana.

"Ni idan Allah ya sa aka kammala shari'ar nan, lallaɓawa zan yi na yi aure, su Baba idan za su shirya da major to, idan sun ƙi ina ɗakin mijina ina yi musu addu'a Allah ya yafe musu ya sanya su gane"

"Amma kin manta mijin 'yar uwakki ne?"

Nabila ta ce "Na sani mana, dama ba jauhar ya fara so ba? Kuma ai yanzu ba ya tare da hafsan idan ba zai mayar da ita ba ni sai na aure shi, ko na auri barrister Habib, ko ma duk wanda Allah ya sa ya samu, Allah ya zaɓa mini mafi alkhairi ya bani wanda zai kula da ni" ta na cikin maganar ya miƙe ya bar wurin. Tashi ta yi ta bishi, amma har su ka shiga mota su ka fara tafiya bai kulata ba.

"Vi ka yi haƙuri idan laifi na yi maka mana, ka wani haɗe rai ka sha kunu kamar boss" gefe ya ci gaba da kallo.

"To ni dai yanzu ba tsoronka nake ji ba duk muzuran da za ka yi mini, da dai na fi jin tsoronka" ya juyo ya yi mata wani irin kallo, take ta tsuke bakinta ta ce "Am sorry".

*** Ramma laulayi ya sakata a gaba, ba ta iya cin abinci, komai ta ci sai amai, duk da ƙasan zuciyar mahaifiyarta babu daɗi ta na tausaya mata, amma a zahiri yadda rammar ta fifita abin da take so, a kan cin zarafin da aka yi musu, ya fi komai baƙanta mata rai, da ta tuno hakan sai ta ji ranta ya ƙara ɓaci.

Alhaji mu'azzam ne ya je gidan, duba su ramma, su ka gaisa.

Ya ce "Hajiya ku yi mini uzuri fa, ayyukan ne da yawa sosai sai godiyar Allah, kwana biyu ban samu na leƙo ku ba"

Maman ramma ta ce "Wallahi babu komai Alhaji, ai muke da godiya Ubangiji Allah ya ƙara arziki ya sanya a fi haka"

Ya ce "Amin, mun yi magana da Nabila ta ce babu wata matsala, amma ya na ga rahaman kamar a cikin damuwa ne?"

"A'a babu komai, kawai dai ba ta jin daɗi ne"

"An je asibiti ne?"

"Eh lafiya lau".

Ya ce "To Alhamdilillah ai Nabila ma ta ce mini ta na hanya, ina son jin ya ake ciki, zuwa yanzu yakamata ace ai an fara shari'ar, tuni a tura shi prison" gaban ramma ya faɗi, duk yadda ta so ta takura zuciyarta ta ji ta tsani Abdul a yanzu kasawa take yi, tausayinsa ya kanannaɗe mata zuciya baki ɗaya.

Ba a jima ba sai ga Nabila ta iso, Ramma na ganin Nabila ta ji farinciki ya mamayeta, saboda itakaɗai ce take fahimtar ta, take lallaɓata ba tare da ta ƙosa ko ta hantareta ba.

Duk su ka gaggaisa, Alhaji mu'azzam ya ce "Barrister ya ake ciki ne? An ce an ɗauki statement da komai, me ake jira ba a gurfanar da shi a gaban shari'a ba?"

Nabila ta ce "Eh na je na tuntuɓa, ina ta bibiyar lamarin shi Abdul ɗin ba shi da lafiya sosai, haryanzu ya na fama, ya na kwance a asibiti ma, ya na karɓar treatment. Duk ina son na je na duba shi, dan na tabattar"

"Yakamata, ki je da kanki, kar ayi wata cuwa-cuwar ko kuma ƙarya yake yi"

"A'a ba ƙarya yake yi ba, ba shi da cikakkiyar lafiya dama" sai kuma ta yi saurin tsuke bakinta, ganin duk sun waiwayo su na kallonta, musamman mama da ta galla mata wata uwar harara.

Kankarofi ya ce "Too, ikon Allah me yake damunsa haka?"

Ta ɗan saci kallon mama, jiki a sanyaye ta ce "Ciwon ciki ne mai zafi"

Ya ce "To Allah ya bashi lafiya, ayi Shari'ar nan, a ƙwatar miki hakkinki da ke da mahaifiyarki"

Nabila ta juya harshe zuwa turanci, ta ce "Yallaɓai, ina tsoron yin shari'ar nan yarinyar nan ta bamu kunya, wallahi ta na son mijinta, daga ita har shi su na son junansu"

Waro ido ya yi ya kalli Nabila ya ce "Haba dai?"

"Ka ga abin da su ka yi a station kuwa? Ga mutuminka ya ɗauki zafi a kan lamarin nan, ka san fansa yake so ko ta halin ƙaƙa, a zuciye yake da su, nayi-nayi ya ƙi fahimta, ka san ba ta da wani tsayayye yanzu idan ba shi ba, ya kafe ya dage, dan kamar zai daketa, ga ciki kuma na rasa yadda zan ɓullowa lamarin nan"

Kankarofi ya jinjina kai ya ce "Lallai akwai ƙura, to dama ni nawa support ne, na yi supporting ɗin ku, financially na baku security, decision kuma wannan naku ne, Ubangiji Allah ya bayar da sa'a duk abin da ku ka yanke, ni dai-dai ne a wurina"

Nabila ta ce "Shikenan, hakan ma mu na matuƙar godiya, Allah ya saka da alkhairi ya sanya a fi haka"

Ya amsa da "Amin Barrister, ai aikinki ya na kyau Ubangiji ya ƙaro mana irinku a cikin al'umma, kin sake komawa wurin mahaifinki kuwa, na je masa sau ɗaya, haryanzu ina jin nauyinsa ne abin da nayi".

"Kar ka damu, ai ba mutum ne mai damuwa ba, iyaka idan ka na buƙatar ya dawo maka da matarka ne shikenan, sai na tayaka biko" ya ɗago ya kalli Nabila ya yi shiru, sai kuma ya miƙe ya tashi ya yi musu sallama.

Nabila ta ce "Rahama, ki na cin abinci kuwa duk kin rame"

Maman tayi caraf ta ce "Ina fa za ta ci, ta ɗauki soyayyar ɗa namiji ta saka a zuciyarta, ba ta tausayina ba ta kallon a masifar da ya saka mu a ciki wata da watanni ina yawon yadda za ayi na ganta, hankalina a tashe"

A marairaice ramma ta ce "Mama ya ce nemanki yayi ya rasa, shiyasa bai dawo da ni ba, saboda za a iya kashe ni, dan a kare shi kuma wallahi ni ba soyayyarsa na saka a raina ba, a kan me zan so wanda ya keta mini haddi"

"Rufe mini baki, ko na zaune ki, soyayyata ki ka saka a ranki ai ko? Tun safe yanzu sha ɗaya na safe, ba ki fito kin nemi abin karya ba, ki na kwance ki na tunani"

Nabila ta katse hirar da"ba zai yiwu ba, tashi mu je ki dafa abinci da hannunki, mu fita shan iska, kya samu ki huta ke ma"

Ta saka ramma a gaba, su ka shiga kitchen, ta ce mata ita ba ta son ko ƙamshin abinci, ita ba za ta iya cin komai ba".

Nabila ta ce "Dubiya za mu je, mijinki ya ce lallai ya na son ganinki, idan kuma ba kya so shikenan" ai babu shiri ramma ta zage, ba tare da ta san tayi hakan ba, ta yi girki, zuwa azahar su ka yi salla, Nabila ta ɗauke ta su ka fice.

Har asibitin da Abdul yake su ka je, jami'an tsaro na ƙofar wurin a tsaye.

Nabila su ka shiga tare da ramma, ƙirjinta sai dukan uku-uku yake yi.

Shi da wani su ka tarar da shi, su ka gaisa da mai jinyar wato Salim wanda abokinsa ne kuma ɗan uwa dan su na da alaƙa, Nabila ta ce "Lauya ce ni, ko za ka iya bamu wuri for some moment" ya ƙarewa Nabila kallo, ya ce "Na gane ki ai" daga haka ya tashi ya fice.

Abdul ya na kwance, ya na bacci, ya na sanye da wando 3quater da vest, fuskar nan ta yi fayau saboda ciwo.

Ramma har tsuma take yi, ta na bin sa da ido.

Nabila ta ce "Bari na je waje na jira ku" ta fice daga ɗakin ita ma.

Kamar jira take Nabila ta fita, ta ƙarasa da hanzari ta saka hannu ta riƙe hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ta ɗan jijjiga shi ta ce "Doctor, Abdul tashi ni ce" a hankali ya juyo, ya buɗe ido, da sauri ya kalli ɗakin ya kalleta ya ce "Rahama, ke ce ya aka yi ki ka zo nan?"

"Anty Nabila ce ta kawo ni"

"Wannan lauyar ta ki?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Abdul ya ce "Ai na ga kamar ta na da tausayi, ba kamar wannan mai zamanin ba mara imani"

Ramma ta ce "Yayana ne fa, shi kuma yar uwar matarsa ce, yan biyunta ce"

"Ke ma kin san ba shi da kirki, ko tausayinmu ba ya ji, am missing you sweetheart" yayi maganar yana janyota jikinsa.

Luf ta kwanta a ƙirjinsa, ta ce "Ya jikin naka?"

"Wallahi ba zan ɓoye miki ba, babu sauƙi, ni kawai a kaini kotun, idan a can prison ɗin zan mutu shikenan, idan ina da rabon na rayu, gara ayi a kai ni na fara lissafin shekarun da zan yi"

Cikin rauni ta ɗago ta kalleshi ta ce "Dan Allah ka daina cewa zaka mutun nan, idan ka tafi binka zan yi, ko bacci ba na iya yi, na rasa abin da yake yi mini daɗi"

"Dan Allah da gaske rahama? Ki na so na kenan? Wallahi ciwon nan nawa har da damuwa, hepatic tuberculosis ke damuna, TB ta kama mini hanta, ikon Allah ne kawai zai saka na rayu, saboda shaye-shayen da na yi ne na san ya haddasa mini hakan"

Ramma ta ce "Zaka rayu in sha Allah, ka daina irin wannan maganar, ka na karya mini zuciya" tayi maganar tana hawaye.

Ya tallafi fuskarta, ya ce "Rahama dan Allah kan na mutu ki ce ki na so na, ko sau ɗaya ne"

"Wai ba zaka daina zancen mutuwar nan ba, wallahi zan daina zuwa idan za ka din ga wannan maganar"

Ya ce "To na daina"

Ta goge hawayenta ta ce "Ga abinci na kawo maka, ai za ka ci ko?"

"Ba na iya cin abinci, amma tun da ke ki ka kawo, dolena na ci ai, your excellency rahama Abdul yasar"

Murmushi ta yi, ta ɗaukko flask, ta zauna a kusa da shi, ta fara ɗebowa ta na kai wa bakinsa.

Ci yake yi ya na kallonta, ba zai iya misalta abin da yake ji a kanta ba, na soyayya.

Hannu ya saka ita ma ya na bata, sai su ka so manta halin da suke ciki.

Ta gama, ta raka shi banɗaki, ya yi alwala, ya dawo ya zauna ya tayar da salla.

Duk abin nan Nabila na zaune ta na danna waya, ta yi shiru ta na kallon ƙofar ɗakin, da alama ma sun manta da ita ne a wajen, ta jinjina kai lallai mata da miji sai Allah. Ban da Abdul ya na da gata, ya za ayi ma a kawo shi wannan asibitin jinya, kamar ma ba wanda ake tsare da shi ba. Nabila na ɗaga kai ta hango babar Abdul na tahowa, tare da security ɗin ta, hannunsu da fulasai.

Abdul kuwa bayan ta gama ba shi abinci, sai ya marairaice wai dan Allah ta yi masa wanka, wai da kansa yake yi, baya bari kowa yayi masa, kuma idan yayi baya fita.

Ya lallaɓata da daɗin baki, ta saɓa hijjabinta, su ka tafi toilet.

Maman Abdul na zuwa Nabila ta tashi, ta ce "Sannu da zuwa, bari ayi musu knocking tukuna, ya na da baƙuwa ne" kallon banza ta yi wa Nabila, kawai ta buɗe ƙofar ɗakin.

Abdul ya na kwance ruf da ciki, ta yi masa wanka, ta na shafa masa man zafi a bayansa.

Tashi ta yi cikin tashin hankali, ramma ta ja da baya, ta na zazzaro ido, tare da ƙoƙarin sanya hijjabinta.

"Me zan gani haka, wannan matsiyaciyar yarinyar har asibiti me ki ke yi a nan, ke wace irin 'yar isaka ce ne?"

Abdul ya ce "Mummy ba 'yar iska ba ce, mata ta ce fa"

"Rufe mini baki ko na ɗauke ka da mari"

Nabila ta ce "Hajiya, ba ramma ce ta kawo kanta ba, shi ya nemi ya ganta ta hanyar lauyansa, su ka roƙi alfarma na kawota, amma ba 'yar iska ba ce"

"Rufe mini baki, banda munafunci, kun haɗa baki a kan lallai sun kun kassara mini iyali, kun dage sai kun kulle mini ɗa, kuma saboda iskanci kin kawota ta na yi masa karuwanci, ƴar ƙanƙanuwa da ke kin iya bariki"

"Mummy dan Allah ki daina aibata mini mata, wane irin karuwanci fisabilillahi. Ni fa ina buƙatar matata a kusa da ni"

Ta ƙarewa ramma kallo, ciki ne a jikinta ya fara tasawa.

"Me nake gani a jikinta kamar ciki ma? Amma dai ba na ka bane ko?"

Abdul cikin damuwa ya ce "Dan Allah Mummy ki daina aibata mini mata, ba dan ni ba, ina son matata, idan laifi ne na yi musu laifi, dan Allah ki daina aibata mini ita, ina jin zafi sosai" galala ta buɗe baki ta na kallon Abdul.

Nabila ta ƙarasa ta danƙo hannun Rahama, ta ce "Zo mu tafi"

Riƙeta Abdul ya yi, ya na yi mata magana ƙasa-ƙasa.

"Na gode sosai da sosai your excellency tun da aka kama ni, ina cikin baƙin ciki da damuwa, amma na yi farinciki sosai da sosai, na gode rahama. Allah ya saka da mafificin alkhairi, ki cigaba da yi mana addu'a"

Jan shi mahaifiyarsa take yi, amma ya yi ƙam da rahama, ya na yi mata magana a kunne.

Jinjina masa kai kawai take yi, idanunta na cika da hawaye.

Hankaɗe ramma ta yi ta na ce mata munafuka, Nabila ta riƙe ta, ta kalli maman Abdul ta ce "Ki bi a hankali, wannan zafafa ƙiyayyar ba naki ba ne ba, rayuwar ɗanki na hannun Allah ta na da alaƙa kuma da Rahama, duk wannan fusatat da ki ke yi akwai rabo a tsakanin su, gara ki kwantar da murya ki lallaɓata da iyayenta, dan wannan abun da yake yi a kanta, ba soyayya ce kawai ba jarrabawa ce".

"Wallahi ƙarya na bi matsiyata yan ƙauye ina roƙonsu, shi ma asiri su ka yi masa"

Nabila ta ce "Idan ke ba ki bi su ba, shi gashi ya lalace ai a kan yar ƙauyen"

"Ke ki iya bakinki ko na kifa miki mari, na saka ayi dukan tsiya"

"Barrister ce ni, tsaf hakan zai saka ke ma a yanka miki tikitin tafiya in da mijinki da ɗanki ke shirin tafiya".

Ramma kuka kawai take yi, Abdul kuwa ya kasa magana, sam bai ji haushin abin da aka yi wa mummyn ba, shi matarsa ce kawai damuwarsa.

Nabila su na tafe a hanya, ta ce "Rahama za ki iya yafe wa Abdul yasar?" Ramma ta kalli Nabila amma ta yi shiru.

"Ki na son mijinki ko?" Still shirun ta yi ta na wasa da yatsunta.

"Ki gaya mini masalaha nake son a nemo"

"Ba na son shi, kawai tausayi yake bani"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Rahama kenan, menene son menene tausayin, ki na tsoron abin da zai biyo bayan amsar da zaki bani ne kawai. Abin da ki ke so dole shi za ayi, idan ki na son mijinki, ki gaya mini a nema masa sassauci ko ma ki yafe masa, ku yi rayuwar aurenku, na san yadda zan ji da Mama da Vi"

Ramma dai ta yi shiru, ba ta iya cewa uffan ba.

Tunani ta tsunduma, yadda suka kasance tare yau tare da Abdul, "Dan Allah rahama kar ki bawa kowa zuciyarki har na fito, zuciyarki tawa ce nikaɗai"

"Ba zaka yi shiru ba, sai na saka maka sabulun nan a baki, da kyar ka ke magana sai haki ka ke yi"

Ya marairaice ya ce "Dan Allah ki bar mini zuciyarki"

"Nawa zaka saya?"

Yayi murmushi ya ce "Ai darajar zuciya, ba a iya musayarta da komai, sai zuciya 'yar uwatta"

"Ji yadda ka ke magana, kamar a film juya ko na zuba maka dundu ni"

Ya lumshe ido ya ce "Dundun ƙauna ne" murmushi ne ya suɓucewa ramma, ba tare da ta shirya ba, Nabila kawai ta kalle ta, ta girgiza kanta.

A falo su ka tarar da Viper, fuskarsa babu rahama babu annuri, tuni Ramma ta tsure, Nabila kuwa ta sha jinin jikinta.

Cikin dakewa ta ce "Vi sannu da zuwa, dama zaka biyo nan ne? Na zata tafiya kawai ka yi"

Miƙewa ya yi tsaye ya ce "Daga ina ku ke?"

"Amm...mm" ganin ta na neman ƙaryar da za ta yi masa ta kare kanta, ya sanya shi ɗago mata wayarsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull