Karfen kafa complete by fatty noor - Chapter 25
Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 25: Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 25. Ta cure wuri guda gami da saka kanta cikin cinyoyinta tana…
3,365 words
Ta cure wuri guda gami da saka kanta cikin cinyoyinta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, idanunsa suka kaɗa suka yi ja, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi, a gefe guda kalaman Ramlatun suna mishi zagaye cikin ƙwaƙwalwa da zuciyarsa. Ummi kuka take yi ganin yanda uwarta ke kuka, Ramlat ta kasa ɗago kai balle ta karɓe ta. Cak ya mike ya fita kafin ya dawo ya yi zaman dirshan a gabanta, har sannan kansa ciwo yake kamar ya kife a wurin.
"Kiyi hakuri Baby, kiyi hakuri."
Ɗago kai ta yi tana kallonsa da ɗan murmushi. Majina ta ja.
"Um um Aliyu, ai kamata ya yi muyi yanda muka saba, ka kamani ka jibga, ka kamani ka zagi iyayen da suka kawoni duniya. Iyayen da na bijirewa umarninsu a kanka, na guji zaɓinsu duk domin na faranta maka. Idan yau ka zagesu waye ya bada ƙofar? Gani kake ni na baka ƙofar ka yi musu duk abinda ka so, ka fadi dukkan wasu bakaken kalamai a kansu. Toh Aliyu naji ni ce, amma na dauka idan so da kauna na gaskiya ne, karen gidanmu ma sai ka girmamashi balle kuma wadanda suka yi silar zuwana duniya? Na gaji, Aliyu na gaji. Aliyu idan kana sona dagaske, kana kaunar Allah da ManzonKa s..a.w, kana kuma kaunar iyayenka ka sauwakemin na je na yiwa iyayena biyayya. Ka sakeni na je nayi auren da martaba da darajata za ta..."
"Ramlatu!" Gaba daya suka kai duba ga bakin ƙofar, Baba Dakta ne a bayansa Amrah da Umma. Ya ƙaraso ciki da sallama suka amsa. Aliyu ya mike ya gaidashi, Amrah sakin baki ta yi tana duban hawayen da Aliyu ke fitarwa. Baba Dakta ya amsa gami da yi mishi sannu da jiki. Daga nan ya gaida Umman Amrah cikin girmamawa. Itama ta amsa ta mishi sannu.
Bayan sun zauna ya dubi Ramlat.
"Kina cikin hayyacinki kuwa? Mijinki kike cewa ya sakeki? Kinsan zunubin da kika kwasa sanadin wannan furucin? Kar na ƙara ji, duk tsanani yana tare da sauki musamman idan bawa ya miƙa lamarinsa ga Allah. Kar fa ki manta kina dauke da juna biyu, wannan damuwar sai kin daina sakawa ranki. Kinji ko?"
Ta gyada kai tana share hawaye wasu na zubowa. Amrah mai saurin kuka har ta soma tayata. Baba Dakta ya mike suka fita tare da Aliyu. A waje ya yi mishi dukkan nasiha ya kuma kara da cewar ya riƙe amanar ƴarsu da suka damƙamishi. Aliyu ya yi godiya don ko ba komai ya taimaka masa daga daurin dabaibayin da Ramlatu ta yi mishi, yasan ba don shi ba haka zasu yi ta ja in ja akan ita sai ya saketa.
*** Ranar da aka sallami Aliyu ya dawo gidan, tuni dama Ramlat ta rigashi dawowa. Sosai kuma likita ya gargadeshi akan shaye-shaye da illolinta.
Kwanakin da suka biyo baya suna faruwa ne sama-sama ga mutanen gidan. Duk kokarinsa na shawo ka Ramlat abin ya ci tura, ya kasance ba ya fita yawon dare, idan ya shigo gida da yamma shikenan sai dai ko masallaci da yanzun ya soma zuwa sallah. A baya zuwan bai dameshi ba, ya gwammace ya yi sallarsa a daki. Ta yi faɗan har ta gaji ta bari.
Wataranar Asabar ta tashi tana son ziyartar yayyunta, gidan Munir ne ba ta jin za ta iya takawa tunda ya nuna ba zai iya yafemata ba. Ta tabbatar idan ta je duk abinda ya yi mata ita ta kai kanta.
Tun safe ta lura ba shi da niyyar fita, wuraren karfe goma ta cimmasa a daki. Kwance yake yana juyi, kwanakinnan tana lura da shi a fisge. Yana cikin damuwa, girki ma idan ta yi bai fiye ci ba. Ga yawan shan Panadol da ya shiga yi kusan kullum ciwon kai.
Kallonta yake tun shigowarta dakin sai kuma ya ja guntun tsaki ya kauda kai.
"Ina kwana." Bai amsa ba, bai kuma kalleta ba. Ta haɗiye ta kara gaidashi.
"Ba zan amsa ba! Ki rabu da ni idan ma mutuwar ce na mutu Baby! Ya ku ke so mutum ya yi? Me kuke so ya zama?! Ance Aliyu dan iska ne kuma mashayi! Yanzun kuma da Allah Ya taimaka ya soma kokarin gyara rayuwarsa, nan ma bai burge ba! Kin juyamin baya ba kya shigowa inda nake sai dai ki yi girki ki dankwafarmin ki shige daki saboda mayunwaci ne ni! Ke haka Allah Ya ce ki yimin? Haka Ya ce ki yiwa Mijinki?!"
Ya na kaiwa nan ya mike zaune gami da jan tsaki kafin ya riƙe kansa da bai bar sarawa ba.
Ta yi mishi ƙurr da idanu tana kallonsa kafin ta nisa.
"Ka saka a ranka ba don mu kawai za ka gyara ba, saboda karan kanka da kuma Ubangijinka. Ba mu da wuta ba mu da aljanna. Nayi kuskure, ka yi hakuri."
Ganin ta sauko yasa shima ya sauko ya lallaɓa don dama neman shirin yake, ya gaji da zaman gabar. Sai da ya biya bukatarsa kafin ya bata umarnin ta shirya da kansa ma zai sauketa gidan Zulaihat din. Wannan ya kara tabbatarmata dagaske Aliyun ya soma kimtsuwa.
Ta shirya cikin wata atamfarta da ta ware cikin sabbin da za ta dinga fita unguwa, ta shirya Ummi cikin riga da wando ƴan kanti ɗaya daga cikin kayan da Abba ya siyamata. Ta yiwa gashinta ado da ribbons kala-kala ya yi mata kyau.
Duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki. Har kofar gidan Zulaihat ya kai ta, suka yi da shi za ta je gidan Rafee'ah a can zai isketa ya ɗauketa. Hakan ya sa ya bata ɗari uku ya riƙe dari biyunsa, a cewarsa ita kenan a aljihun, dari biyar.
*** Kallonta Zulaihat take har Ramlat ta gaji ta yi magana.
"Wai Maman Khalifa lafiya?"
"Kin rame ne, kuma kamar dai kina da ciki."
Ta kauda kai a kunyace ta dai daure ta amsa da eh.
"Ciki dai Ramlat? Yanzu ba ki ji shawararmu kin yi family planning ba?"
Zulaihat ta furta don takaici bai sa ta iya ja bakin ta yi shiru ba. Ramlat ta kasa magana ta yi shiru kawai sai hawaye.
"Tab, Allah Ya kyauta to. Ya raba lafiya."
Nan ma kasa maganar ta yi.
Ganin kamar Ramlat din batun cikin na tada hankalinta yasa Zulaihat ta barshi suka shiga hirar bikin da ya taso na su Naja'atu da su Maryam jikokin Hajja. Su biyar cif za'a aurar nan da wata biyu.
"Ki dai samu ya yi maki koda anko ne koda bai bada ma gudunmuwa ba, ke sai ki duba idan kina da hali ki yi. Sannan don Allah ki dinga cin abinci sosai ko za ki ɗan maido jikinki kar a yi ta yawo da ke a cikin taro."
Ta gyada kai.
Sai wuraren karfe hudu ta nufi gidan Rafee'ah. Ita kanta ta yi mamakin ganin Ramlat da ciki sai dai banda Allah Ya raba lafiya ba abinda ta ce don ba ta son shiga sabgarta da Aliyu.
Aliyu bai zo daukarta ba sai wuraren takwas na dare. Sun gaisa da Rafee'ah da mijinta sannan suka bar gidan.
*** BAYAN WATA DAYA..
Tsumma ne a ƙasan ƙafarta tana goge inda mai ruwa ya ɓatamata a falon tana tsaki. Sati biyu kenan da dawowarsu sabuwar unguwa kuma sabon gidan da ko ruwan famfo babu sai dai a siya.
Aliyu ya fadamata ƙudurinsa na siyar da gidan don ya samu na jari, ba tare da ta san inda zasu koma ba ta amince. A cewar ta da ta zo ta ga yanda ginin yake da ba ta amince ba sannan ga dukkan alamu idan damina ta zo dakunan zasu yi warin ruma da kuma alamun danshi a jikin bangon. Ciki da falo ne a gidan sai fyallen daki guda daya, sai kicin hade da store. Ba daki daya a tsakar gida.
Babban damuwarta bai wuce ganewar da ta yi yanzun Aliyu tuban muzuru ya yi, ta kamashi ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba yana shan sigari a ɓoye. Ta yi kukan ta yi faɗan amma a banza, wannan ta sa ta zubamasa ido ta maida hankali ga kaiwa Allah kukanta.
Shigowarsa falon ne ya bata damar dauke tsummar ta amsa sallamarsa a ciki.
"Baby wani wari kamar na gardi nake ji."
A kufule ta amsa.
"Mai ruwan da ka turo ne."
Ya ja tsaki.
"Kai rashin ruwan nan ya soma damuna. Ga cacar kashe kudi. Mtsw."
A ranta ta ce kai ka sani, ta shige kicin abinta.
*** "Biki ko na dangina fa bana anko ke kin sani. Yanzu ma da muke ta kai, wa ke ta kaya?"
Wannan na daga cikin dalilin da ba ta son tambayarsa wata bukata. Kusan ma yana daga abinda Abbansu ya gargadesu, tambayar miji wata buƙata kar ya kawo maka raini. Wani abin ne ba za ka iya shiru ba.
"Aliyu ban taɓa neman ka yimin wata sutura ba sai yanzun, abu ne na fita kunya. Cikin dangi da yan uwana zan shiga. Don Allah ka taimaka dai ka yimin."
Ya ɗan yi shiru yana wani cin magani, can kuma ya ce.
"Shikenan kiyi addu'a a samu kudi. Sannan batun sutura har yau ai kina morar suturorin da na miki, ko ba komai na kashe sama da miliyan daya a lefenki."
"Ba sai ka gorantamin ba."
Ta fadi ranta a ɓace. Bai ce uffan ba don yanzun bai fiye bari su yi dogon sa'insa ba, a cewarsa juna biyu ne da ita. Hakanan yana kokarin ganin ya kiyaye kai hannu jikinta da sunan bugu.
Ta shige daki a fusace ta kyaleshi anan tare da ƴarsa.
*** Allah Ya taimaketa dai ta samu ya kawomata atamfar ankon amma ba kudin ɗinki. Hakanan ta yi godiya ta ƙuƙuta ta bada ɗinkin, zuwa yanzu takan leƙa makwafta saboda halin rayuwa da son kiyaye shari'ah. Ta ciko ba laifi sai dai ga duk wanda ya ganta da ciki sai ya tanka. Har ta gaji ta fice daga cikin masu auren ta koma bangaren Amaren cikin ƴan mata ta zauna.
Kallon kowaccensu take cike da burgewa. Amrah ta saje a cikinsu ta ci ado har ta gaji sai hira da shewa ake. Ta tuno da nata ƴanmatancin, kauda kai ta yi gami da mirza idanunta gudun saukar ruwan hawayen da ya tahomata. Ita da ƴan uwanta amma a karan kanta kunyar kanta take ji na abubuwan da suka afku wanda har abada tarihinta ba zai goge a zuƙatansu ba. Ko ba komai ta bar baya da ƙura.
Amrah na hankalce da ita hakan yasa ta miƙewa ta karɓi Ummi a hannunta ta zauna ta shiga jan ta da hira har ta saki jiki.
*** Aka kammala biki lafiya aka kai yan matan dakunansu, ba ta samu zuwa kai su ba don ta gaji da habaice-habaicen da wasu a dangi ke mata game da aurenta. Zamanta ta yi a gida abinta.
Kamar koyaushe bayan kammala girkin dare ta yiwa ɗiyarta wanka ta shafe jikinta da hoda yanda za ta ji sauƙin zafin da ake a gari, ga ba wuta a unguwa don sai a fi sati biyu ma ko wata babu kyallinta kamar yanda ta soma shaidawa kuma ta ji daga bakin makwafciyarta. Shigowar Aliyu gidan ya bata mamaki, koda dai yanzun bai kaiwa dare sosai a waje, amma ta yi mamakin ganinsa wuraren bakwai da mintuna. Zama ya yi gefen gadonta yana dan yamutse-yamutsen fuska.
"Lafiya?" Ta nemi ba'asi.
Dan guntun tsaki ya ja yana mai ɗan sosa kirjinsa.
"Kamar dai banda lafiyar Baby, zuciyata sai ta dinga tashi ga gudawa da nake tun safe haka nake zaryar banɗaki a kasuwa."
"Allah Ya sauwake, Ya baka lafiya. Ya kamata ko chemist ka leka."
Ya jinjina kai yana mai sa hannu ya dauki Ummi dake faman mikomasa hannu tana ɓangala dariya.
*** ABU KAMARI just published "BABI NA ASHIRIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ZRLvPBGxyab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Rahmanir Raheem.
25)
Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba. Cutar amai da gudawa ta yiwa Aliyu kamun kazar kurkuku. Chemist ya je aka haɗa mishi magunguna.
Koyaushe yana gida, hankalin Ramlat ya tashi.
Abu ya wuce kwanaki ya koma sati, Aliyu ya bi ya ƙara ramewa ya yi duhu. Abin ya zamewa Ramlat goma da ashirin, ga ciki ga raino kuma ga kula da miji. Ganin abin ya ci tura ta tursasa mishi da taimakon Baban Nusaiba makwafcinsu, aka kaishi asibiti da motar Baban Nusaibar. Ta bar Ummi a makwafta.
"Madam, ba ka ji bane?"
Ta ɗan dawo hayyacinta ta kara duban inyamurin Likitan.
"Ka dauka ka je ka biya a yi."
Gyada kai kawai ta yi ta mike ta fito zuciyarta cike da tunani ga faduwar gaba. Tsoronta kar ta je Aliyu wani cutar ya shafo mai rikitarwa. Likita ya tabbatar gudawarsa bai da alaƙa da abinda yake tunani ke damun Aliyun, wannan ta sa har scanning sai da ya ce a yi.
"Ya ake ciki Maman Ummi?" Fadin Baban Nusaiba. Ta dubeshi idanunta duk sun faɗa sun yi ciki, ita kanta ta rame sai ƙaton ciki wanda sai ka rantse ya kai watanni takwas.
"Ba komai, bari na karasa na biya."
Ya gyada kai gami da amsawa da toh. Allah Ya taimaka ta taho da Atmcard dinta, ganin kudin hannunta ba zai isa bane ya sa ta fita ta zaro kuɗin. Komai ta biya aka yiwa Aliyu duk abinda ya dace. A nan ne Baban Nusaiba ya yi mata sallama kan zai koma. Godiya sosai ta yi mishi har ya fita sannan ta maido dubanta ga Aliyu wanda ya samu bacci.
Hawaye ta ji sun zubomata sakamakon tunanin da ya yi mata tsinke. Yanzu idan ya mutu me zai koma ya cewa UbangijinSa da Ya ba shi aron rai da kuma lafiya a rayuwa ya kasa tsayuwa ya kyautata rayuwarsa kuma ya godewa wannan ni'ima? Ba wannan ba ma, wace cuta ce da Aliyu? Idan wannan tambayar ta faɗomata a rai, numfashinta har tsayuwa yake cak tsabar firgici.
Tana wannan tunanin ta soma hamma kafin itama ta soma gyangyaɗi saman kujera don ɗakin ba su kaɗai bane, akwai majinyata har uku a bayansu.
Ƙarar wayarta ce ta katsemata baccin, ta yi firgigit ta ɗauka. Amrah ce. Miƙewa ta yi ta fita daga waje.
"Na ji shiru ba ki shigo makaranta ba, kuma nayi niyyar zuwa gidannaki ban san kwatance ba."
Ta haɗiyi miyau mai zafi.
"Muna asibiti, an kwantar da Baban Ummi bai da lafiya."
"Ya Rabb, meke damunsa?"
Ta gano rudewar da Amrah ta yi, ta kuma fahimci dalilin. Hakan ya ƙaramata rashin nutsuwa da tsoro.
"Wallahi ban dai sani ba Amrah, an mishi test."
"Toh Allah Ya sauwaƙe, Ya ba shi lafiya. Zan shigo ko zuwa gobe ne tunda yanzu kam na kama hanyar gida akwai tazara."
Nan suka yi sallama ta mata godiya.
Ganin dacewar ta kira ta sanar a gidan su Aliyu yasa ta dannawa Malam kira. Bayan sun gaisa ta fadamishi Aliyu ba lafiya suna Akth. Nan da nan ya ce gashinan zuwa suka yi sallama.
*** Bayan awanni biyu, tana zaune gefen Aliyu wanda ke shan kunun gyaɗa da Abulle ta kawomishi sai dai hankalinta ba ya tare da su, yana ga Malam da ƙanin Aliyu, Mudan. Suna wurin likita kai sakamakon Aliyun. Kirjinta dukan tara-tara yake yi. Fargaba kan ba'a magana.
"Ya kamata ki je gida ki huta."
Ta kalli Aliyu mai wannan batun cikin karfin hali. Girgiza kai ta yi.
"Um um."
"Nima abinda zan ce kenan, ki tafi gida tunda shi Mudan ne zai kwana, gobe kya shigo. Ai da gajiya, ke dai sannu Allah Ya saukeki lafiya."
Fadin Abulle cike da kulawa, kaunar Ramlatu sosai ke ratsata, tana lura da yanda take ba Zakinnata kulawa.
Shigowar Malam ne ya sanya hankalinsu komawa garesu, fuskar Malam ba za ka iya tantance yanayinta ba.
"Kun dawo? Me likitan ya ce?" Abulle ta nemi sani. Malam ya samu wuri ya zauna.
"Babu komai, sai dai likita ya tabbatar ciwon zuciya na barazanar kama yaron, ya kuma ce lallai ya bar shan duk abinda zai gusar da hankalinsa ko ya shaƙi iska marar dadi, idan kuwa ya ƙi komai ma zai iya faruwa. Shi gudawar sanadin me ma..?"
Ya maida akalar tambayar ga Mudan don shi ya mance ma tsabar damuwa.
Mudan ya dora.
"Bacterial infection ne wanda shan sigari ya haddasa masa, shi ya kawomasa gudawa. Amma ya ce in Sha Allah wannan mai sauki ne. Ya dai ce dole ya kula ya bar shaye-shaye saboda cutar dake masa barazana."
Salati kawai Abulle ke yi ta shiga yiwa Aliyu faɗan ya taimaka mata ya bari, tun tana yi har ta shiga kuka. Aliyu idanunsa suka kaɗa, ya kasa kallon kowa musamman ganin jama'ar ɗakin sun zubamusu idanu gami da baza kunne.
Cak ta mike tsaye.
"Zan wuce gida."
Abinda ta ce kenan. Suka dubeta.
"Toh Ramlatu, ki je da Mudan ya taho da kayan shi Alin. Ba sai kin yo girki ba, daga can gida sai a kawo. Allah Ya baki lafiya kema. Sai hakuri kin ji?"
Malam ke wannan jawabin cikin nutsuwa. Ta gyada kai, har lokacin danne hawayenta take yi, ba ta ko kara kallon Aliyun ba suka fice tare da Mudan. A hanya ma ba ta ce uffan ba duk kuwa da irin korafin da Mudan ke yi akan Aliyun da takaicin abin, suna isa ta haɗamasa abinda za'a buƙata, tare suka fito. Ita ta nufi makwafta ta dauko Ummi shi kuma ya miƙa titi.
Sai da ta zauna a falon tana duban Ummi dake wasanta, ta kara kai duba ga cikinta, kafin wasu zafafan hawaye su soma wanke mata fuska.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ita ce kalmar da ta shiga ambata tana kara nanata wa.
Daga wannan sai wannan, komai na zuwarmata a daki-daki. Rayuwa kenan, kalar rayuwar da ta ke hangowa zasu yi da Aliyu a baya, ba irinta ta samu ba. Ta shanye dukkanin komai ta hakura, yanzu kuma ga wata sabuwa. Kukan ta shiga yi sosai, wayarta ta dauki ƙara ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin ɗauka ba tare da ta duba ko waye ba.
"Assalamu alaikum."
Ta fadi cikin muryar kuka.
"Waalaikumussalam. Ramlatu? Meke faruwa ne? Kukan me kike?"
Ta yi firgigit ta dawo nutsuwa da hayyacinta, ABBA ne. Da sauri ta saita kanta ta shiga ƴar dariyar yaƙe.
"Lah Abba ina wuni? Ba kuka nake ba, mura ce ta ke neman yimin kamu."
Shiru ya dan biyo baya can kuma Abba ya yi magana
"Kin tabbata Ramlatu?"
Ta gyada kai tana jin sabon kuka na tahomata.
"Eh Abba."
"Shikenan. Ya karatu? Ina fatan dai komai lafiya? Kar ki ga ina ta tambaya, mafarkinki nayi cikin wani irin yanayi shiyasa na damu."
So da kaunar Abbannata ya kara mamayeta. Ta shiga murmushi har cikin zuciyarta.
"Abba lafiyata kalau. Abba na gode na gode. Abba ka yafemin don Allah. Na yi maku laifuka masu tarin yawa, na so kaina.."
"Zancennan ba ya wucewa ne Ramlatu? Ban hanaki tayarwa ba? Sau nawa za'a ce maki ya wuce?"
"To na daina. Ya jikinka?"
Ya yi murmushi mai sauti.
"Jiki da sauki Ramlatu, ba abinda ke damuna yanzun."
Ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, dadi ya rufeta.
"Allah Ya karamaka lafiya Abbana."
Ya amsa da amin, ya tambayi Ummi. Nan ta hadashi da ita tana mishi jagwalgwalon hausarta ya yi ta dariya. A karshe Ramlat ta maida wayar kunne.
"Wai ita ƴar nan ba za'a bani aronta ba?"
Ta kasa gaskata kunnuwanta, ba ta taɓa zaton Abban zai nemi Ummin a gidansa ba. Da wani irin farin ciki da ya mantar da ita bakin cikin Aliyu ta amsa.
"Abba ko yau ka aiko a daukarmaka ita."
Dariya Abba ya yi.
"Yanzu yamma ta yi Ramlatu, gobe zan turo Autar Hajiya ta daukarmin ita amma ki nemi iznin mahaifinta."
Sai sannan ta tuna Aliyu, ta ji kamar ta fadawa Abban rashin lafiyarsa amma ta ɓoye gudun kar Abban ya shiga damuwa.
Suka yi sallama, shigowar saƙo ya sa ta dauka. Aliyu ne. Ta bude ta shiga karantawa.
_*"Na cuci kaina Baby, na cutar da mu. Kaicon rayuwar da na zaɓarwa kaina. Ki yi hakuri ki yafemin. Ki tayani addu'a, da yardar Allah zan daina. Na daina din ma Baby. Abin ne ya ke zamemin kamar karamin hauka idan ban yi. Ciwon kai da damuwa su tararmin."*_