Karfen kafa complete by fatty noor - Chapter 26
Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 26: Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 26. Ta ɗan yamutse fuska kawai ta share batun. Dakyar ta iya…
3,361 words
Ta ɗan yamutse fuska kawai ta share batun. Dakyar ta iya miƙewa ta shiga wanka ƙofa a bude saboda Ummi.
Babu komai a kicin din sai wani guntun Doya da Aliyu ya siyo. Kusan kwana uku kenan da ƙarewar abincinsu sai maneji. Dafa doyar ta yi, Allah Ya taimaka tana da sauran yaji ta ci da shi.
A daren ta yiwa Aliyu text na zuwan Ummi gidansu, bai hana ba sai fatan alheri.
*** Washegari kuwa tun safe Mudan ya kirata akan kar ta zo za'a basu sallama zuwa anjima, hakan na yi fiyemata don bata kaunar shiga asibitin a yi mata kallon matar mashayi. Abin da kunya.
Wuraren karfe sha daya na safe sai ga Amrah, ba jimawa sai ga A'isha ta zo ɗaukar Ummi. A tsaitsaye ko zama ba ta yi ba har Ramlat ta mike ta shiga dakin dauko jakar Ummi da ta haɗa kayanta.
"Ke kam Auta ko zama fa ba ki yi ba." Fadin Amrah tana kallon A'isha dake tsaye tana dan yiwa Ummin wasa. Ko ba komai yarinyar ta shiga ransu sosai. Taɓe baki ta yi.
"Wallahi Anti Amrah sauri nake, kinsan yau za'a soma bikin Yaya Hilal. Zamu je tare da Anti Bilkisu, tana can tana jirana."
Daidai sadda Ramlat ta fito, karaf maganar ya shiga kunnenta. Ji ta yi gabanta ya fadi, Hilal zai yi aure? Ko ya ya dama tasan sai ta ji wani iri. Hilal mutumin da ya yi mata so da kaunar da wani ɗa namiji bai mata makamancinsa ba. Ya mata so a sadda ya kamata ace ya fi kowa gudunta adalilin wulaƙanci da cin mutuncin da take mishi, sai dai madadin hakan cewa yake "Bana miki son da zan iya barinsa a lokaci guda."
Ta sauke ajiyar zuciya gami da share fuskarta da gyarawa gudun kada su gane. Karasowa ta yi sadda A'isha ke koɗa matar Hilal.
"Ba ki ganta ba wallahi kyakkyawa da ita ga kirki. Har waya suna yi da Hajiya."
Jakar ta miƙamata.
"Gashinan."
A'isha ta karɓa tana kallonta kadan don so take ta ƙular da ita. Amrah da bata gane ba ta yi murmushi.
"Aikuwa na yi mishi murna wallahi. Allah Ya basu zaman lafiya."
"Amin. Na wuce."
Suka yi mata fatan alheri ta fita.
Shiru ya biyo baya kafin Amrah ta dubeta.
"Wai meke samun Aliyun?"
Ta haɗiyi miyau mai daci, nan ta kwashe dukkan abinda ke faruwa ta fadamata. Salati kawai Amrah ke yi, hakan ya kara raunana zuciyar Ramlat ta fashe da kuka.
"Kinga sakamakon abinda na aikata ko? Duk abinda kika ce ya faru a kaina. Na wulakanta kaina kafin kowa ya wulakantani. Na fita zakka a cikin ƴan uwana. Amrah rayuwata ta ƙare, na kashe kaina da hannuna. Ban taɓa riskar farin ciki mai daurewa a aurena da Aliyu ba banda bakin ciki da takaici. Me zan ce ga yarana a sadda suka dubeni suka tuhumeni da zaɓamusu mahaifi irin .."
Hannun Amrah ta ji a saman bakinta, ta shiga girgiza mata kai tana fidda hawaye.
"Ya isa, ya isa don Allah Ramlat. Ki gaggauta istigfari, kin fita hayyacinki har kin soma kalaman saɓawa mahaliccinki. Kar ki manta, Allah Ya riga Ya rubuta zuwan yaranki duniya ta jikin Aliyu. Ki yi hakuri ki yi ta istigfari da nemawa mijinki shiriya. Addu'ar mace ga mijinta ba ya faɗuwa. Komai ta roƙamasa, Allah zai amsa."
Gyada kai Ramlat ta shiga yi tana sauke numfashi. Haka suka wuni da Amrah, tana cike da jin kunya ganin Amrar ce ta fita ta yi musu cefane da kudinta ta dawo suka girka dafadukan taliya suka ci.
"Kina da labarin yajin aikin da aka soma kuwa?"
Fadin Amrah, ta zaro ido.
"A'a, ki ce sun tafi?"
Taɓe baki Amrah ta yi.
"Asuu ai basu yi ba, ina ta so na fadamaki na manta. Zaman gidan ya ganmu. Karatu a ƙasarnan ya zama abinda ya zama."
Ramlat ta numfasa.
"Allah Ya kyauta."
Suka amsa da amin.
Amrah na nan Aliyu ya dawo, gaisawa kawai suka yi sannan ta wuce.
*** BAYAN SATI DAYA.
Jikin Aliyu sosai ya yi sauki don har ya ci gaba da fita kasuwa. Sabon yaron shagonsa Sama'ila, ya je ya tarar ya tafiyar da komai duk kuwa da irin ɓarnar da ya mishi na karya wasu cikin farashin kayayyakinsa. Shi a nasa tunanin ya yi dabarar da kayan zasu siyu. Kayan abinci ya soma kaiwa gidansa, duk abinda yasan za'a buƙata. Hakan da ya yi ya yiwa Ramlat dadi, ba ta fita ko'ina iyakacinta makwaftansu sai fita awo asibiti. Zaman gida sosai ya kamata musamman sanadin yajin aikin da ake wanda ba ta ga ranar kammalawa ba.
***
Ummi ta zama ƴar Hajiya, koyaushe idan Abba na gida suna tare. Wannan ne silar da yasa Munir dauke ƙafa daga gidan. Ba ya kaunar ganin yarinyar tare da su. Akwai sadda ya gaji ya yi magana
"Yanzu Hajiya ba za ku maida yarinyar nan ba?"
Ta daure fuska.
"Ai dama ina kula da kai, na lura da take-takenka Muniru. Ka fita idona, ko ba komai ai hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yarr. Duk lalacewar Ramlatu kanwarka.."
"Shikenan, shikenan Hajiya. Allah Ya huci zuciyarki. Da yardar Allah ba zan ƙara magana a kai ba." Ta yi kwafa.
"Ka ma ƙara mana Muniru. Ka ma ƙara tunda kai zuciyarka ba ta san afuwa da mantuwa ba. Mu da muka haifeta mun yi hakuri sai kai ko? To ka ci gaba."
Shi dai ya yi shiru ya lallaɓa ya bar gidan.
*** "Yaron nan da yake auren Ramlatu fa naji kamar jama'a na raɗe-raɗin yana da cutar ƙanjamau, shiyasa nace gwara na faɗa maka."
Abba ya ji gabansa ya fadi, ya tsurawa manajansa Audu ido.
"Wa ya fadamaka wannan zancen? A ina ka ji?"
Audu ya gyara zama don dama maganar na cinsa, kwana hudu kenan da ya ji daga bakin ƙaninsa Lamin wanda yake abokin kasuwancin Aliyun a kasuwa.
"Laminu ƙanina, ai kasan kasuwarsu daya. Kwanakin baya a asibiti ma ya kwanta, yanzu haka dai ya koma kasuwa kowa na takatsantsan da shi."
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ka tabbatar da wannan zancen Audu?"
Audu ya gyada kai cike da karfin gwuiwa.
"Kwarai kuwa Alhaji, wannan magana haka take."
Abba ya mike tsaye da sauri.
"Alhaji."
Abba ya daga mishi hannunsa wanda har rawa yake.
"Tafiya zan yi Audu, ka kula da komai."
Cike da ladabi Audu ya gyada kai da kara russunawa har Abban ya fita. Wani a shagon da suke kira Garzali ya ƙaraso wurinsa.
"Amma ba ka kyauta ba Maigida, sai da nace kar ka fadawa Alhaji wannan zancen amman ka ƙi."
Audu ya harareshi.
"Kai waye da za ka fadamin abinda ya dace da wanda bai dace ba Garzali? Kar ka manta a ƙasana kake, idan na ga dama sai na yi maka sanadin barin shagonnan."
Garzali ya daga hannu alamun saranda ya wuce ya na mai ba shi hakuri.
*** Shi kuwa Abba yana fita, Idi na ganinsa ya taso da sauri, wasu a gefe na gaida Abba bai ma tsaya amsawa ba.
"Muje."
Ya fadi hana kama hannun ƙofar motar, da sauri Idi ya bude da muƙulli ya budemasa ya shiga. Shima ya shiga ya ja suka wuce.
Idi na lura da yanda Abban ya yi shiru yana fidda numfashi, ya kasa hakuri ya cez
"Ranka ya dade ko asibiti zamu wuce?"
Abba ya yi murmushin takaici ya girgiza kai yana ci gaba da jin wani zafi a kirjinsa.
"Aa idi, kai ni cikin iyalina. Ba komai."
Idi ya amsa ba don ya so ba suka nufi gidan.
Abba kuwa tunanin da ya soma zuwa kansa shi ne Ramlatu ta kamu da cutar ƙanjamau.
'Shikenan ya cuci ɗiyata,ya kashemin rayuwarta. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun.'
Abba ke nanata wa a ransa. Ya zama dole ya je ya dauko ɗiyarsa.
*** "Please Zaki ka bar bibiyata. Haba! Wai dole ne na kulaka?"
Aliyu baki sake yake duban G Baba wanda ke kokarin shigewa wata haɗaɗɗiyar Jeep sabuwa dal. Koda dai dama, mahaifinsa mai kudi ne, yanzun kuma ya samu aiki ya bar yawon shashanci aure ma zai yi.
"G Baba, ni kake cewa na daina binka? Don ubanka ka manta waye ni a wurinka ko?"
Aliyu ya ƙarashe da ƴar zolaya, so yake ya samu ko rance ne yana son yin odar abayoyin mata daga Dubai.
G Baba ya kalleshi kallon raini kafin ya ja guntun tsaki.
"And so? Wai don Allah ka yi zaton ban san cutar da ke damunka bane? Kana yawo da HIV shi ne kake so na ci gaba da yawo da kai sunana ya ɓaci a hanani auren Teemah? Haba Zaki, kai kanka kana iya tunawa iyakarmu bariki, ko gidanmu ka ga na taɓa kuskuren kai dayanku? No! So please ka fita daga rayuwata ka bar bibiyata. Ni wallahi daga yau abotar tamu ma na datseta da ƙaton almakashi. Ban sanka ba, kai ma ka saka a rai ba ka sanni ba. Ka je can ka ji da lafiyarka. Mtsw."
Daga haka ya shige motarsa ya bar filin parking din na kwari. Dama kasuwar ya shigo ganin wani abokin Dad dinsa wanda zai hadomishi lefe daga Dubai. Aliyu ya bishi da kallo har ya fice. Ranar iyakar wuya ya kai, wato kowa ma kallon mai cutar ƙanjamau yake mishi shiyasa kowa ya juyamasa baya a kasuwar.
Dawowarsa kenan daga wani gidan abinci ya hango G Baba zai tsallaka ya biyo bayanshi don dama yana ta kiransa a waya bai daga ba, shi ne ya mishi wannan cin kashin.
Haka ya koma kasuwar ransa na suya, karshe ma kasa zama ya yi ya mike ya tafi gida don dama lokacin tashi ta kusa.
Ramlat na zaune tana karatun Alkur'ani bayan ta gama girki sai ganinsa ta yi, ya zube saman kujera ransa a ɓace. Ta kauda kai ta karasa aya ta yi addu'a ta maida Alkur'anin sannan ta dubeshi.
"Kowace irin damuwa gareka, don Allah ka dinga yimin sallama."
Ya gyada kai kawai, ta mishi sannu da zuwa ta shiga ciki ta kawomishi ruwa da zoɓon da ta dafa.
"Bismillah."
Ya karɓi kofin da ta miƙomishi ya ɗan sha ya ajiye. Idanunsa a kaɗe ya dubeta.
"Meyafaru?" Ta tambaya bada shiri ba.
"Kallon mai cutar Ƙanjamau ake yimin a kasuwa Baby. Kowa guduna yake. Bansan wa ya yaɗa wannan jita-jitar ba, an ɓatamin suna Baby. Shikenan. Yau har G Baba ke guduna?"
Ta sunkuyar da kai tana mai jin ciwo a ranta.
"Ka yi hakuri." Abinda ta iya cewa kenan. Ya yi ƙwafa
"Wato ga Aliyu banza shashasha ko? G Baba ya ci mutuncina ya nunamin daman can Bariki ce ta haɗamu, wato su masu wayo. Usman ma da na kira text ya yimin wai na rabu da shi, duk wanda na kira a cikinsu kauracemin yake. Ashe dama ni ke musu kaunar tsakani da Allah? Wai har G Baba ke iƙrarin na rabu da shi kar na ɓatamasa suna a fasa aura mishi budurwarsa?"
Ramlat ta dubeshi tana murmushin takaici.
"Wannan bai isheka ishara ba? Bai isheka dalilin da za ka gane rayuwa ba ka watsar da munanan halayya ba kaima? Wadanda ka rikesu ƴan uwa kuma kake jin maganarsu sama da ta kowa, su ne suka juyamaka baya. Koda ace cutar gareka na tabbata ba za ka taɓa zaton za su juyamaka baya haka ba. Idan yanzu duka wadannan jarabtar da Ubangiji ya yi maka bai sa ka shiryu ba, me zai sa ka nutsu Aliyu?"
Ya tsuramata idanu tana fidda hawaye, za ta miƙe ya riko hannunta ya maidota ta zauna. Rungumeta ya yi a jikinsa.
"Kiyi hakuri, wallahi ban kara shan komai ba tun da na dawo sha asibiti. Na ce miki ba zan ƙara ba, ki ta yimin addu'a."
"Allah Mai amsawa ne, amma kaima sai ka tsarkake zuciyarka da kyakkyawar tuba. Duk abinda zai sa ka ji kana sha'awar aikatawa sai ka ƙaurace mishi. Ka maida hankali wurin bautar Ubangijinka, sai kaga Ya taimakemu."
Ya gyada kai yana mai amsawa da toh. A karshe ya mike ya nufi daki ya kwanta, ba ta bishi ba don ita kanta tana bukatar jinyar nata zuciyar.
Wayarta ta dauki ƙara, ta mike ta dauka. Hajiya ce.
"Ramlatu, maza-maza ki zo Abbanki ba lafiya."
"Innalillahi! Hajiya meke faruwa?"
Ba amsa, a firgice kuma a rude ta nufi daki, tun kan ta isa take kiran sunan Aliyu.
Yana naɗe saman gado, shi kadai yasan kwanakinnan da bai sha abin maye ba ya yake ji. Ga damuwar abinda abokansa suka yi mishi na cinsa, ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na tursasashi akan ya je ya sha ko zai ji sanyi amma yana yiwa kansa faɗa da tunasarwa kansa har abada ya daina. Jin yanda Ramlat ke kiransa ne yasa shi miƙewa a razane ya tarbeta har tana kokarin faduwa. Hanya kawai take nunawa tana kuka.
"Baby nutsu please, fadamin meke faruwa?"
"Abba, Abba ba lafiya Aliyu. Ya ce na je, don Allah ka kaini Aliyu."
"Kiyi shiru, yanzu zamu je ki ganshi. Kiyi hakuri."
Daga haka ya fito rike da hannunta, hijabinta da ta cire ya dauka ya mayarmata. Bai yi karambanin daukarta a mashin ba gudun kar ta kifemasa a hanya. Titi suka nufa suka sami abin hawa.
*** Kusan a guje ta shiga dakin da Abba yake kwance a asibitin. Gaba daya iyalin Abban ne a dakin sai Baba Dakta wanda bai jima da shigowa asibitin ba.
Kai tsaye ta yi kan Abban.
"Abba! Abba!!"
A hankali ya bude ido lokacin da Zulaihat ta janyeta. Munir na gefe yana ji kamar ya je ya shaƙe Ramlatun. Ko ma mene ai ita ce ta ja.
Hannu Abba ya mika, ba musu Ramlatun ta saka hannunta cikin nashi tana wani irin kuka.
"Ya cuceni, ya cutar min da ke Ramlatu."
Aliyu wanda har ya murɗa kofar dakin zai shigo ya tsaya cak ya fasa. Ya juya ya koma da baya ya zauna saman kujera cike da jin kunyar kansa da kansa.
Abba ya ci gaba da magana dakyar.
"Meyasa tun farko kika dage akan sai shi? Ba ki hango abinda na hangomaki ba ko? Ba ki hango aibunsa ba Ramlatu. Yanzu shikenan ya cutar min da ke ya sanyamaki ciwon da ba'a warkewa."
Ji ta yi numfashinta ya tsaya cak, ta shiga jawoshi da ƙarfinta.
"Abb..Abba...me..kake nufi?"
Abba ya runtse idanu yana jin saukar hawaye. Ba shi kadai ba, hatta da mutanen dakin abinda suka kawo shi ne, Ramlatu ba ta san komai game da ciwon mijinnata ba.
"Abar zancen haka Alhaji Khalid, ba'a son yawan maganarnan naka. Don Allah ku ragu a dakin."
Abba ya girgiza kai.
"A'a Dakta, bana jin ciwonnan nawa na tashi ne. Ka bar ni na yi sallama da iyalina. Ni kadai nasan me nake ji."
Ya fadi gami da runtse ido sai hawaye. Hakan ya kara ruɗa mutanen dakin. A'isha kuka har da sheshsheka hakanan su Rafee'ah. Shi kuwa Munir idanunsa ne suka kaɗa sai sauke ajiyar zuciya yake.
"Abba an ce maka Aliyu nada ƙanjamau ko? Abba wallahi karya ne, ko wa ya fadamaka karya yake!"
Abinda Ramlat ta fadi kenan sakamakon tunanin da ya zo mata. Yan uwan da ma iyayen kallonta suke cike da takaici, wannan wane irin so ne da har ciwon Aliyun ma ɓoyonsa take?
"Ramlatu kinsan Aliyu na dauke da ciwo kika yi shiru? Tun yaushe?"
Hajiya da ta kasa hakuri ke wannan tambayar tana duban diyarta a kidime.
I just published "BABI NA ASHIRIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/f5qPHpmrzab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
26)
Cikin kuka ta dubi Hajiyar.
"Wallahi Hajiya ba ƙanjamau ce da shi ba. Jita-jita ce kawai. Ciwon zuciya ce ke barazanar kama shi sakamakon shaye-shaye, sai Infection da ya jawomasa gudawa shine har ya kwanta asibiti na kwana ɗaya. Abba ka tashi don Allah, Abbana kar ka mutu saboda damuwata. Abba ka yafemin. Kaicona "
Kukanta ya ƙi tsayawa, Abba ya kara damƙe hannunta.
"Rabi ki yi shiru. Ki yi shiru. Haka Allah Ya tsara wa Ramlatu. Dakta."
Ya maida dubansa ga Baba Dakta.
"Ka taimakamin a yiwa Ramlatu gwajin jini, idan har tana dauke da cutarnan don Allah a gaggauta dora ta kan magani."
"Abba, wallahi lafiya kalau. Abba dagaske nake maka, ina rantsuwa da ..."
"Kina da tabbas? Mene hujjarki?!"
Munir ya katse a zafafe. Ta dubeshi sai kuma ta kasa magana. Baba Dakta ya bada umarnin duk a fita a bar Abban. Suka fita dukkansu, likitan Abban ya shigo ya kara dubashi sannan ya fito.
"Muje Ramlatu." Fadin Baba Dakta. Ramlat ta dubeshi kamar wata wawiya, yau ita za'a yiwa test akan cutar da ko a mafarki ba ta taɓa ganinta da shi ba? Me ya jawomata wannan tozarci da wulakancin?
'Auren Aliyu.' Cewar wani ɓangare na zuciyarta. Sai a sannan kuma ta tuno tare ta zo da Aliyu, ta waiga baya wurin hakan yasa ta maida dubanta ga Baba Dakta.
"Baba Dakta wallahi wallahi..."
"Yi hakuri, yi hakuri Ramlatu. Kwantar da hankalinki, ki bari ayi din ko don samun nutsuwa da kwanciyar hankalin Abbanki. Kina so ya samu lafiya ko?"
Ta gyada kai gami da jan majina.
"Yauwa ko kefa, muje."
Ta bi bayansa bayan ta bi yan uwanta da kallo. Munir harara ya watsamata, ta kauda kai tana kuka.
Test aka yi mata na jini sannan ta dawo wurinsu ta zauna.
"Ya ake ciki? Me sakamakon ya bayar?" Fadin Hajiya tana dubanta.
Ta bude baki za ta amsa sai ta kasa, kuka ya ci ƙarfinta ga wani bakin ciki da ya tsayamata a ƙahon zuci. Auren Aliyu ya jawomata wulaƙanci, yau ita ake yiwa kallon mai cutar ƙanjamau?
'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'
Ta fadi a karo na barkatai.
"Hajiya nifa banda komai, bana dauke da kowace cuta. Hajiya don Allah ki yarda da ni. Wallahi ba ƙanjamau ne da Baban Ummi ba."
"Allah Ya tsinewa kalar so irin naki Ramlatu! Son da har za ki ɓoye cutar mijinki ki rufamasa asiri ki cuci kanki! Wallahi Hajiya ya ci ace kun fidda hannunku a lamarin yarinyarnan, wanda fa ya yi nisa ba ya jin kira! Sanadinta Abba ya fada cikin wannan halin, ai ba ita kadai ku k haifa ba! Tunda ita ba ta bi ku ba, kuma bai kamata ku damu da lamuranta ba. Ta je idan ma mutuwa za ta yi ta mutun mana idan har Abba zai rayu! Mtsww!"
"Kai kuma mene sunanka?! Me za mu kiraka da shi? Ka tsaya kana fada alhalin Abba ba lafiya? Wannan shi ne girman?!"
Zulaihat ke maganar a fusace, tun ɗazun ya kai ta wuya dannewa kawai ta yi.
"Ke! Ni kike faɗawa magana?"
"An fadamaka din! Don kawai kana babba..."
"Ya isa! Haba mana!"
Hajiya ta katsesu a tsawance, faɗan Muniru da Zulaihat sakamakonsa bai fiye kyau ba.
Muniru ya juya a zuciye ya bar wurin, Hajiya ta dubi Zulaihat.
"So ku ke ku nunan halinnaku a asibiti? Shikenan ai."
Ta ƙarashe a fusace. Rafee'ah dai banda hawaye ba abinda take yi, magana ma ta kasa saboda tunanin Abban yayinda A'isha ta kwantar da kai a cinyar Rafee'ah ta yi shiru tana kallon kowa. Ramlatu kuwa kukanta ma har ya yi yawa.
Suna nan zaune Baba Dakta ya nufosu fuskarsa dauke da murmushi. Suka zubamishi idanu.
"Alhamdulillah, koda Aliyu na dauke da wannan kwayar cutar, bai kai ga shafamaki ba Ramlatu. Komai naki lafiya kalau yake. Ki kwantar da hankalinki."
Gaba daya suka sauke ajiyar zuciya. Murnar da suke bai wuce yanzun Abban zai farfaɗo ba idan ya ji sakamakon gwajin da aka yiwa Ramlatun.
Baba Dakta ya shiga dakin ya karasa har gadon Abban yana murmushi, sai dai me? Cak murmushin ya dauke da sauri cikin rawar jiki kuma ya kai hannu bisa tsintsiyar hannun Abban. Ya kara kaiwa saman kirjinsa don bai gasƙata abinda ke faruwa ba.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Baba Dakta ya furta kafin ya dubi fuskar Abban, kamar za ka kira sunansa ya amsa ga wani dan murmushi. Hannu ya sa ya ja zanin rumfar ya rufemishi fuska.
Ya jima a tsaye yana tunanin t hanyar da zai sanarwa iyalin rasuwar Abban. A karshe dai ya daure ya fita ya fadamusu. Kowannensu ya saka salati.
Dif! Kukanta ya dauke sai kallo. Ta kalli wannan ta kalli wancan.
"Kuka ku ke yi? Abba ai bai mutu ba. Ku daina kuka."