Kenza eBookz

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 5

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 5

Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 5: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 5. "Aa please, za ki yimin illa babba fa. So kike ina tafe ina tuna…

3,375 words

"Aa please, za ki yimin illa babba fa. So kike ina tafe ina tuna kuka maimakon murmushinki? Kar muyi haka da ke. Kinji? Idan kin yi kuka ni kuma na yi me?"

Ganin duk yana neman hargitsewa sai ya ba ta tausayi. Ya shiga rarrashi.

"Ki kwantar da hankalinki kinji? Da kaina zan siyamaki waya na aikomaki don ba zan jure rashin jinki ba. Ramla ba don karatu dole ne ba kuma ina sonmu da shi wallahi Hilal zai iya ajiye karatun ya aureki daga baya ki ƙarasa naki a gidana. To ba zai yiwu ba, komai bisa tsari ya fi. Ki yi hakuri kin ji?"

Ta share fuskar tana murmushi. Kukanta biyu ya haɗarmata, kirjinta bugu yake bana wasa ba, tana ganin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari da zai fi ƙarfinta, jikinta na bata akwai babbar matsala sai dai wani ɓangare na zuciyarta na ƙarfafarta akan kar ta ba shaiɗan damar wasa da hankalinta. Yanda Hilal ya dage rarrashi ma duk sai ya bata tausayi dole ta nuna mishi ta sauko, suka rabu kamar kar su rabun. Tuni ya yi sallama da su Hajiya da Abba, wannan tasa kawai wucewa ya yi. Hotunanta kala-kala na takarda ta ba shi har yana fadin zai sa a mishi enlargement dinsu ya kafa a ɗakin kwanansa na makaranta. Dariya kawai ta yi. Daf da zai bar gidan ya dakata gami da fiddo wani ɗan akwatin ƙarami na zobe, kai tsaye ya miƙamata yana murmushi.

"Karɓi mana."

Ta sa hannu ta karɓa tana kallo.

"Duk da ba zancen alƙawari yanzu, saboda inada yaƙinin irin kaunar da muke yiwa juna, ina da tabbas a kanki Ramlata. Ki sanya a hannunki, ya kasance har bayan dawowata shi zan tarar a hannunki. Wannan kaɗai zai sa ni farin ciki. Ina miki fatan alheri."

Daga nan ya fice a gaggauce don da alama ya soma karyamata zuciya.

"Azurfa mai kyau." Shi ne abinda Rafee'ah ke kira yayinda ita kuwa ta mike ta bar falon zuwa ɗaki. Kuka ta ci sosai na abu biyu da ta rasa da wanda za ta ji. Sai da ta yi mai isarta ta share fuska, ta ɗau alwashin rabuwa da tunaninsa balle ya kai ta da mafarki. Ta ƙara gaskata mafarkan Aliyu duk kissimawar shaidan ce, shi ke mata yawo da hankali a mafarkanta.

"Daga rana irin ta yau babu ni ba tuna dukkan wani abu da ya shafeka Aliyu, har abada. Allah ina neman tsarinKa daga sharrin shaidan da kuma na zuciya da saƙe-saƙenta."

Sai dai kuma wasu lamuran sun fi gaban yanda dukkan bawa ke ɗaukarsu. Duk a rashin sanin cewar yanzu aka fara!

*** Ƙarar ababen hawa ya cika kunnuwanta, dole ta saita kanta ga ci gaba da tuƙi cikin nutsuwa da kwarewa, a hankali ta sa bayan hannunta ta share fuska. Daidai wani boutique ta yi parking ta fito. Kai tsaye ta shiga, tunda Ummi da Ansar suka ƙwallafa rai akan halartar Children's Day. Ta shiga ciki kai tsaye ta nufi ɓangaren kayan yara. Tun kan ta ƙarasa ta hango bayan mutumin riƙe da waya a hannunsa yana video call bai ko damu da tsilli-tsillin mutanen dake shagon ba wadanda wasu ke kallonsu suna dariya wasu kuwa su yi gaba.

"Wannan kina so?"

Ya ɗaga wani takalmin, yarinyar ta turo baki kamar mai shirin kuka ta girgiza kai da mirza idanu. Ya sauke ajiyar zuciya.

"Tee ya zan miki uhm? Duk wanda na ɗaga bai miki ba? So kike Mominki ta yi mana dariya ko?"

Matar shagon ta ƙara ɗauko mishi wasu tana dariya kaɗan-kaɗan. Ramla kallon yarinyar kawai take tana tasbihi ga Ubangijin da Ya ƙageta.

"Daddy ga wata Mami can a baya, ni ta zaɓamin. Dada ta cemin ba ka iya zaɓe ba."

Cewar yarinyar har tana riƙe haɓa da turo baki, jin abinda yarinyar ta faɗi yasa ta saurin juyawa ta ɗora hannu saman shelf din da ya fi kusa da ita kamar hankalinta bai kansu. Tana jin dariyar yarinyar, shi kuwa uban koda ya juyo sai ya ji kunya kaɗan cikin yaren fillanci ya yiwa yarinyar sallama ya katse kiran. "Ki ji fa, idan matar aure ce kuma fa?"

Ya yi maganar yana duban Matar dake aikin ciro mishi takalma, ta dubi Ramla da ke sauraron su kadan kadan. Ta yi dariya.

"Wannan Customer ɗinmu ce Oga,na san Madam ba ta da aure."

Ya kara duban Ramla kafin ya mike da nufin aiwatar da abinda ɗiyar ta nema, a sannan ita kuwa Ramla har ta ɗauki wata doguwar riga mai hula wanda ta tabbatar zai yiwa ɗiyarta.

"Assalamu alaikum."

Ta dubeshi, zaro idanu waje ta yi. Ganinsa anan ya yi masifar ba ta mamaki da kuma tsoro. To ina Hajiyar? Yaushe ya sauya kaya daga voyel maroon zuwa shadda ruwan toka? Ta kasa magana, shi kuwa bai maida hankali wurin kula da hakan ba ya shiga neman alfarmar ta zaɓamasa takalmin da zai yiwa ɗiyarsa. Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata.

"Hello."

Ya ƙara faɗi gami da ɗan rankwafar da kai. Ta ɗan yi firgigit sai ta basar cike da dakiya.

"Ba damuwa."

Suka ƙarasa wurin takalmin, ta shiga dubawa bayan ta tambayi size dinta. Jefi-jefi za ta kalleshi da tsantsar mamaki, sai dai duk abinta ba za ta taɓa yin shishshigin tambayar ko shi ƴan biyu bane. Wani takalmi ja ta ɗauki mai adon fulawa, tana murmushi ta miƙa masa.

"Wow, gaskiya Madam kin iya zaɓe." Fadin ma'aikaciyar wurin.

"Allah Yasa ya burgeta." Ramla ta fadi da murmushin da ya fi kama da yaƙe don har yanzu kirjinta bai bar bugu ba tsabar kamannin da ta gani ƙarara na wannan mutumin da mijin Hajiya.

Shi kuwa Alhassan banda murmushi ba abinda yake dokawa, iyakar burgewa takalmin ya mishi har cewa ya ke.

"Idan Tee ba ta so takalminnan ba to ba bulala za ta sha." Suka yi mishi dariya.

"In Sha Allah za ta so."

Daga fadin haka ta mike yana mata godiya, ta koma ga kayan maza hannunta rike da rigar da ta daukarwa Ummu. Sai da a kammala ta nufi wurin biya. Duk yanda ta nuna ba ta so hakan bai sa Alhassan fasa biyamata kuɗin kayayyakinta ba. A karshe godiya kawai ta yi, kusan tare suka fito kowa ya nufi motarsa suna kara yiwa juna godiya. Kallonsa take har ya bude mota zai shiga, hatta da tafiyarsu ɗaya ce, a yanzu ta yarda su ɗin ƴan biyu ne babu ko tantama. Har za ta tayar da mota ta ji maganarsa a gefenta.

"Mami, yi hakuri ki sanyamin number dinki, I promise you ina komawa garinmu zan kira na ba ki albishir takalmi ya burge ɗiyarki. Kuma itama ina son ta miki godiya ko?"

Ta yi jim kamar ta ce a'a, ya kuwa narkar da fuska. Sai ta yi murmushi ta karɓi wayar ta shigar da lambarta. Ya karɓa ya yi godiya suka yi sallama.

A hanya tunanin biyun masu kama kawai take yi wanda bambancin su fara'a da akasinsa. Banda wannan kamar ta yi yawa. Haka har ta isa gida tana zancen zuci.

***

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem

06)

*** Tun fakawarsa a gaban ƙaton ƙyauren na gidan Muhammad Modibbo ya ji ɓacin rai ya lullluɓe dukkan wata walwalarsa. Ya kalli gidan, abubuwa da dama suka shiga dawowa kwanyar Alhassan Aminu.

_"Tunda ubanku ya bijirewa umarninmu ya auri bare ai ko sata aka ce kun yi zan yarda. Har abada zuri'armu ba za ta karɓi Uwarku ba balle ku da ku ke yaranta."_

Ya runtse idanu tuna kalaman babban wan mahaifinnasu da ya yi. Ba don Dada ba ba zai taɓa shiga gidan ba. Sai dai matsayi da girmanta ya zarta hakan.

"Sai yau ku ka tuna da ni?" Dattijon mai shekaru sittin da ɗoriya ke wannan kalaman cikin harshen fulatanci sadda ya dubi Alhassan dake zaune a gabansa ya sunne kai. Murmushin yaƙe ya yi.

"Ba haka bane, ayyuka ne suka yi min yawa. Ayi hakuri."

Ya maida da harshen fillanci don Modibbo Hausar ba kasafai take fita ba.

"Ka koma, duk radda ka yi ritaya wurin aiki sai ka dawo a ci gaba da zumuntar." Daga haka Modibbo ya mike ya shiga ɗakinsa. Idanun Alhassan suka kaɗa, dama yasan a rina! Bai ma tsammaci zai yarda su gaisa ɗin ba. Ya mike gami da zaro hankicif a share goshinsa. Duba ya kai ga ƙaton enlargement din na yaran Mamman Gidado dake manne a falon, yaransa goma sha biyar cif har mahaifinsu wanda ke bi ma Modibbon. Ajiyar zuciya ya saki ya fice daga falon da sauri. Sashin matan gidan ya wuce, su biyu ne kuma duk daga zuri'a guda sai dai ɗaya ɗiyar wa, ɗaya kuma ɗiyar ƙani. Ɗakin Uwargida Hajja Fatuma ya soma shiga. Kadahan-kadahan ta amsa mishi, wurin yaranta ne ya samu tarba sosai, bai yi mamaki ba don dama basu da matsala tsakaninsu su cousins.

A ɗakin Hajja Amarya kadai ya samu shimfidar fuska, dama can ita ke mutunta su da ɗan uwansa da mahaifiyarsu. Anan ya shantake har girki ya kwasa suna dariya karshe ya mata sallama ta bada turarukan wuta a kaiwa Dada sai na matarsa.

Yara yasa suka shiga da kayan lemuka da ya yo tsaraba, bai ko kara shiga ba ya ja motarsa. Washegari kuwa sammako ya yi ya bar garin Kano.

*** *ADAMAWA*

Tana tsaye jikin madubin ɗakinta tana kokarin gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta. Doguwar riga kalar ruwan madara ta sanya wanda aka yiwa aikin paint work. Sauri-sauri take don tasan mijinnata na dab da shigowa gidan dalilin waya da suka yi ya sanarmata ya shigo gari. Sai dai saurinta ya kusan haifar da nawa sakamakon hon dinsa da ta ji a bakin gate. Ba ta san sadda ta turo baki ba don ita kam a duniya ba abu mai wuya wurinta irin ɗaura ƙaramin ɗankwali. Ta yi jifa da shi gefe ta koma wardrobe ta dauko karamin mayafin da ya dace da kayan ta fita. A falon suka ci karo, ya sakarmata murmushi gami da ajiye ledar saman kujera ya buɗemata dukkan hannuwansa, aikuwa da sassarfa ta ƙarasa ta shige, ya maida hannuwan ruf.

"Sannu da zuwa Abu Fatima." Ta fadi tana mai ɗagowa daga jikinsa. Ya ja karan hancinta.

"Kema sannunki. Kin yi kyau sosai."

Ta yi godiya, daga nan suka faɗa ɗaki, ta taimaka ya yi wanka ya rama sallolinsa kafin su fito falon. Miƙar da ƙafafunsa ya yi saman kujera haɗi da kiran wash.

Ta ɗaga ƙafafuwan ta zauna sannan ta ɗora saman cinyarta. Cike da tausasawa ta dubeshi.

"Sannu Abu Fatima, ka kwaso gajiya."

Ya lumshe ido da murmushi.

"Bari kawai Ummina, na sha tafiya ba kaɗan ba amman Alhamdulillah tunda na cimma nasarar abinda ya kaini. Zuba abincin."

Ya fadi yana mai miƙewa zaune bayan ya sauke ƙafafunsa. Yana cin abinci yana mata hirar diramarsa da Fatima. Banda dariya ba abinda ta yi.

"Ci gaba da biyewa yarinyarnan dai, watarana sai ta ba ka kunya. Hum, naga kokarin ma Matar da ta biyewa shirmenku."

Harara ya watsamata.

"Shikenan, kin ja wa kanki na fasa ba ki taki tsarabar."

Ta kama kunne tana murmushi.

"Na tuba. A yimin afuwa."

Ya yi murmushi kawai. *Kausar* kenan, matarsa kuma ƴar uwarsa. Sun gina rayuwa ta fahimta, so da kuma kaunar juna. Ɗiyarsu guda a duniya Fatima, tun daga kanta Allah bai ƙara ba su haihuwa ba.

Sai washegari ya je gidan Dada, bayan sun gaisa ya isar da sakon gaisuwar Modibbo da jama'ar gidansa gareta, ta ji ba don ta yarda ba. Ya ba ta tsarabar da Hajja Amarya ta ba shi. Murmushi ta yi.

"Wannan kam na yarda." Shima murmushin ya yi bai ce uffan ba.

"Daddy takalmina." Fadin Fatima tana kara mannewa jikinsa gami da turo baki. Ya na dariya ya janyo leda, ya bude kwalin ya soma kokarin sanyamata a ƙafa.

"Wowww! Daddy ya yi kyau sosai."

Dariya ta basu shi da Dada.

"Sai ki zo ki yiwa Mamin Boutique godiya."

Ta mike tana tsalle ganin yanda takalmin ya yi kyau a kafarta kamar wata balarabiya.

Ƙarshe ta rungume wuyan Uban tana magiyar a kiramata Mamin Boutique. Ba musu ya fiddo waya ya danna kira.

*** KANO

Misalin ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar, dawowarta kenan daga wurin aiki ta miƙe ƙafa a falon cikin yayyunnata mata wadanda a ƴan kwanakin suke shigowa dalilin bikin A'isha da ya taho gadan-gadan. Rafee'ah ke riƙe da takarda da biro tana lissafin kayayyakin da ya rage a siyo a kasuwa yayinda Zulaihat ke nunamusu wasu hotunan sabbin warmers ƴan Dubai a waya.

"Kai Maman twins, sun yi kyau sosai wallahi."

Fadin Ramla tana ƙara sanyo kai ta gefe ita da A'isha.

"Kyau ai ba ɗaya ba Ramla. Nidai idan ma ba za'a siya wa Auta ba ina so zan siya."

Fadin Rafee'ah tana ƙara kallon hotunan cikin santi.

"Kai Sis. Aa nidai ina so wallahi." Fadin A'isha, ganin Hajiya ta kalleta sai ta ji kunya ta ruga ɗaki. Dariya suka yi gaba ɗayansu. Daidai sadda ta ji ƙarar wayarta, ta koma mazauninta ta ɗauka. Ganin baƙuwar lamba ne ya sanya ta yi mata ƙuri, sai dai tuna ko akan abinda ya shafi wurin aikinta ne ya sanya ta ɗagawa da sallama.

"Waalaikumussalam wa rahmatullah Mamin Boutique."

Ta ɗan yi shiru sanadin abu biyu, jin muryar namiji da kuma jin sunan da ya ambata.

"Sunana Alhassan Aminu, wanda ku ka hadu a Afrah Boutique dake kan..."

"Ayya sai yanzu na gane. Fatan kana lafiya?"

Ta katseshi da sauri ganin yanda ƴan uwan suka raba hankalinsu, wani a abinda suke wani kuwa a kallonta ana ƴar dariya ƙasa-ƙasa.

Suka ƙara gaisawa sannan ya miƙa wayar ga Fatima.

"Assalamu alaikum Mamin Boutique. Ina kwana."

Yanda yarinyar ta yi sai da ta murmusa don kuwa ta burgeta. Ta amsa mata, nan yarinyar ta shiga zubamata hirar takalmi ya yi kyau Maminta ba za ta yi mata dariya ba. Ita dai Ramla ta biyemata, karshe Abbannata ya karɓi wayar.

"Idan kika biyemata sai ku cinyemin kuɗin wayar ai."

Suka yi dariya kusan a tare, ya ƙara yi mata godiya ta bada saƙon gaisuwa ga mutan gidan daga bisani suka yi sallama.

"Mene?" Ta furta tana mai duban Maman twins da Rafee'ah.

"Kin fimu sani ai, har kin samu wani majnun ɗin ba labari ko?"

Ta saki baki kawai ta kasa magana.

"Bar ta. Ni kai da naga ana shirin kasamin in law."

Hajiya ta dubi Maman twins.

"Wa kenan?"

"Baba Bashir yayan Baban twins mana, wanda matarsa ta rasu. To ai shi ne ya ga Ramlar kwanaki can ya nunan ana so. Maganar kenan da nake son nayi da ita amma ƴar albarkar ba ta kirani ba, ba ta zo gidannawa ba."

Ramla ta ja guntun tsaki.

"Don Allah ku bar wannan maganar, shi fa da kuke ganin mun yi waya, takalmi ne na tayashi zaɓar ƴarsa shi ne dalilin da ya kira suka yimin godiya don takalmin ya burge ƴar. Maman twins shi kuma Bashir ai kin ba shi lambata, sau ɗaya ya taɓa kirana kuma na ɗaga mun gaisa na ba shi hakuri. Mai kuma zan daga kiransa ya kara cemin?"

Daga haka ta kwashi tarkacenta ranta na zafi ta kama hanyar barin falon.

"Ai fa, wannan zafin rai da taurin kan ba zasu taɓa bari ki yi gaba ba Ramla. Ki dai bi sannu tunda yanzu ke mai ba wa wasu labari ce. Kinga dai makomarki."

Ba ta san sadda ta juyo gaba dayanta ba tana duban Rafee'ah wacce ta fusata. Ba dai ta ce komai ba ganin Hajiya na tsawatarwa ta juya ta wuce ciki, sai dai kafin ma ta kai ga shiga dakin tuni ta soma fidda hawaye. Tana ƙarasawa ta rufe gam da muƙulli ta faɗa saman gado. Ta yiwa kanta illa, tun ran gini tun ran zane, tana kyautata zaton dalilin ne yasa abu kadan ta aikata sai cibi ya zamo mata ƙari. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar jallabiya mai ɗankwali. Idanunta ya kai ga ɗan akwatin mai kalar golden da ke ajiye saman mirror dinta. Ƙarasawa ta yi ta buɗe, wani envelope ta fiddo ta zauna gefen gado ta buɗe. Hotunan ta ciro tana ƙaremishi kallo. Wani lokaci ta tuno wanda har abada ba zai gushe daga kwakwalwarta ba.

*** *MATAR MUTUM*

Tun tafiyar Hilal ta ƙara jin kewa ta cika zuciyarta. A bangare guda ga tunanin Aliyu da ya zamemata abin yi safe da rana. Wannan ta sanya suna kammala zana jarrabawarsu ta zango na biyu a makaranta, (2nd term), ta tattara Abba ya kaita Yakasai ta yi hutun a can ko ta sami nutsuwa.

Ta ci sa'a kuwa jikokin gidan wadanda suka kasance sa'anninta duk suna nan suma. Aikuwa suna ganinta suka ruƙunƙumeta da murna.

"Oh yarannan shikenan kuma za ku hana bakinmu ya huta da bari-bari kamar wasu ƴan shekara hudu. Ai ko su A'isha sun fi ku hankali." Cewar Talatu ƴar kawun Abba wacce ta dawo nan da zama daga Daura.

"Bar su su yi son ransu Talatu idan ba so kike yanzu Hajja ta maidaki Daura ba." Fadin Abba yana dariya. Hajja dake taunar goro tana tayashi.

"A'a to, rabu da su. Wataran sai labari duk suna gidajen aurensu."

Maganar Hajja ta ba su Ramla kunya, duk suka mike su ka yi ɗaki har suna bangazar juna.

"Magulmata." Fadin Hajja cikin dariya. Abba ya shantake har da cin kwaɗon zogale kafin daga bisani ya yi musu sallama.

Washegari da misalin karfe uku na yammaci ƴanmatan su biyar, Usaina, Maryam, Jidda, Nafisa sai Ramla. Suka shirya suka fita zuwa gidan babban ɗan Hajja Zulai, Kawu Kabiru don ziyara.

Tun kafin su fita titi Ramla ke mitar ita kam ba wacce za ta dauka saman cinyarta sai dai su yi abin hawa biyu.

"Kai Mrs Hilal, don ɓarnar kuɗin mota?" Fadin Jidda tana auna abinda zasu kashe daga Yakasai zuwa Zoo road.

"Aa fa, da gaskiyar ƙawalli, ba zan yarda nima na ɗora kowaccenku a cinya ba, ke kuma Jidda idan har za ki iya hawa bayan kujera shikenan."Faɗin Usaina.

Ta ƙasashe suna dariya don ita kanta ta faɗa ne, a ƙiba kam duk Jidda ta fi su.

"Allah Ya kiyaye." Cewar Jidda.

Aikuwa dai sai rabawa suka yi, kusan a tare suka samu abin hawa, Ramla da Usaina su biyu kacal a adaidaita sai Jidda, Maryam da Nafisa wuri guda.

Sai da suka kusa Zoo road ya samu fasinja. Sallama ya yi ya shigo, kusan da sauri ta dubeshi. Shi ne, shima yana zama ya kai duba gareta. Duk da yanda ta yi saurin kauda kwayar idanunta gefen Usaina wannan bai hanashi ganeta ba. Ta ƙara matsawa jikin Usainar ganin yanda jikinsu ke ɗan gogar juna. Murmushi ya yi ya matsa ta yanda ya san za ta fi sakewa.

Bai ce uffan ba banda murmushin da yake faman dokawa, abin mamakin shima Zoo road ya nufa. A hankali ta kai duba gareshi ta cikin karamin gilashin ɗan sahu. Kwayar idanunsu ya sarƙe da juna ta yi azamar janyewa. Ba ta ƙara gangancin kallonsa ba, mutumin da take kwana da tashi da tunaninsa. Kirjinta bai bar bugu ba, ba ta fahimtar zantukan da Usaina ke yi.

"Sauka mana." Ta ji muryar Usaina karo na biyu, sai sannan ta dawo nutsuwarta ta dubi gefenta, tsaye ta hangoshi a waje yana sallamar mai adaidaita. Ta kauda ido ta fito, Usaina na bayanta.

"Ɗauka har da nasu." Ya furta ga ɗan sahun.

Nan suka ce a'a, ya rantse shi zai biya, Ramla na shirin jan musu ta ji Usaina ta ɗan bugi kafaɗarta alamar ta yi shiru. Godiya suka yi mishi, hango su Jidda sun tsaya ya sanya Usaina nufarsu.

"Ramlat."

Ta tsaya cak gami da juyowa ta dubeshi, ba ta yi mamakin jin ya ambaci sunanta ba don Usaina ta kira sunan ya fi a ƙirga cikin adaidaita. Ya ɗan matso kaɗan.

"Karo na biyu Allah Ya yi haɗuwarmu. Tun sadda na sanyaki a idanuna har yau bani da sauran sukuni. Wallahi ina sonki!"

Ya furta fuskarsa na nuna alamar gajiyawa da kuma gaskiyar abinda ke ransa.

Ta matse yatsun hannunta jin yanda kirjinta ke bugu, ta ɗan kuramasa idanunta da suka cicciko da kwalla. Shima kallonnata yake da nashi mayun idanun wadanda tuni sun dulmiya cikin tafkin kauna da shauki.

"Ayya ka yi hakuri Malam, wallahi an sakamata rana. Nan da shekaru uku ba kaɗan bikinta."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull