Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 6
Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 6: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 6. Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da…
3,300 words
Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da maimaita abinda aka ankarar da ita.
"Eh, an sanyamin rana. Ka yi hakuri."
Ya yi murmushin yaƙe. Ya dubi Usaina.
"Kaicon wanda zai yi wasa da damarsa. Akwai kuskure a jan lokaci har haka. Watakila kuma rabon Aliyu ce. Ina muku fatan alheri."
Ya dubi Ramla da fuskarsa wacce ta yi narai-narai.
"Matar mutum Ramla, matar mutum.."
Daga haka ya juya ya bar wurin. Ramla ta tsaya kamar wata mutum-mutumi. Kafaɗarta aka jijjiga.
"Ke dillah can! Mene hakan? Waye shi? Ko kin manta da sanya ranar da ke kanki? Ke Usaina waye shi?"
Duk Nafisa ke wannan kalamin daidai sadda suka ƙaraso, zantukan ƙarshe sun sauka saman kunnuwansu.
Tuni ta soma tafiya kanta a ƙasa, tana ji Usaina na basu labarin abinda ya faru suna jan tsaki da kiran kwalelansa. Can kuma ta ji suna koɗa iya ɗaukar wanka da kuma kyan da Allah Ya mishi daidai gwargwado. Ta shiga tariyowa.
Milk shadda ya sanya da aka yiwa aiki daidai da zamanin, ya dora hula brown da ratsin milk din. Dogo ne don har ya fi ta da kaɗan, yana da hasken fata. Tafiyarsa ma kadai za ta burge mutum. Yana da ɗan duhun lebba, gashin kansa a cike luf-luf wanda ya taho har gefen fuskarsa ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa. Lafuzzan Aliyu ma kadai abin burgewa ne.
Murmushi ta yi wanda ya taho tare da hawaye, ta yi azamar sharewa lokacin da Maryam ta dafa kafaɗarta. Ta kai duba gareta.
"Ina za ki?" Sai sannan ta waiga ta gansu tsaye a ƙofar gidan yayinda ita kuwa ta ɗan yi gaba. Tabbas tunanin Aliyu ba zai kasheta ba. Ta yarda matar mutum kabarinsa don haka ta haramtawa rai da gangar jikinta tunaninsa tunda har shima ya fahimci Hilal ne zaɓin Allah a rayuwarta, kamar yanda shima ya samu daidai shi.
'Allah Yasa hakan kake nufi.'
Ta furta a ƙasan ranta.
Sun wuni cur a gidan Kawu Kabiru tare da iyalinsa, tun Ramla na ƙin magana da faɗawa tunani har dai ta yi watsi da komai sai dai ta kasa yakice kalmar Ina sonki da Aliyu ya furta. Da zarar ta tuno a karon kanta sai ta saki murmushi.
Sai yamma suka bar gidan.
Haka ta ci gaba da rayuwa gidan kakanninta tare da su Jidda, duk kuwa hakan bai tafiyar da tunanin Aliyu ba. Abinda ke tsorata ta bai wuce yanda so da kaunarsa ke neman rinjayar zuciyarta ba. Har yakan maida tunanin Hilal gefe guda ya ajiye.
Sai da ya rage sauran kwanaki uku su koma makaranta sannan duk aka watse kowannensu ya koma gidansu, nan ma ji suke kamar kar a rabu.
***
"Wai ke ba za ki buɗe kofar ba? Me kenan hakan? Ba'a isa a faɗamaki ki ji ba?"
Muryar Maman twins ta bugi kunnuwanta, ta share hawayenta ta tattara hotunan ta maida mazauninsu sannan ta bude kofar fuska a haɗe. Shigowa ciki Maman Twins ta yi tana fadin
"Allah Ya shiryamana ke Ramla, bansan sadda za ki rabu da wannan bakin ran naki ba. Haba jama'a! To sai ki fito Hajiya na nemanki."
Ta miƙe ta bi bayanta zuwa falon. Hajiya sosai ta buɗe mata wuta kan ba ta son irin haka, dole ta ba Hajiyar hakuri itama Rafee'ah ta bata.
Kafin su bar gidan sai da ya kasance komai ya wuce kamar ba su yi ba.
*** Kwanci tashi asarar mai rai, cikin ikon Mai Duka bikin A'isha ya taho gadan gadan, ana saura sati ƴan Daura suka dinga cika gidan. Wasu a can Yakasai wasu kuwa anan wurin Hajiya.
Ana saura sati a sanya A'isha a lalle Ramla ta ɗauki katukan daurin aure da na wuni ta kai ofishinsu. Ranar da ta kama Asabar kuwa, takanas ta shirya yara sai gidan Muhibbat wanda daga nan zasu wuce gidan Ramla rabon kati. Mutane biyu masu muhimmanci a rayuwarta kenan. 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
08)
_*Dawowa Labari*_
A kofar gidan Amrah ɗan sahu ya ajiye Ramlat. Ta biyashi tana mai kama hannun Affan wanda duk ya ɓata kayansa da cakulet suka fara knocking. Aka bude, harararta Amrah ta yi.
"Sai yanzu ko? Yinin kenan?"
Ramlat na dariya ta juya.
"Shikenan, bari mu juya daga nan." Da sauri ta kama hannunta ta maidota baya suna dariya.
"Ni ban ce ba, yi hakuri." Suka shiga ciki suka zauna, nan take sanarmata sai da ta biya gidan Muhibbat.
"Allah Sarki Muhibbat, matarnan akwai kirki wallahi. Ba ruwanta, kinsan babu ranar da ba za ta turomin gaisuwar juma'a ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ai wannan daban take cikin mutane ma. Allah dai Ya bamu ikon yin zumuncin mu ma." Amrah ta amsa da Amin. Ramlat ta shiga waige-waige.
"Ke ina ƴata wai? Tun da kika ce min kun dawo ita nake son ganin yanda ta girma."
"Tana wurin Mama na kai mata yaye. Abinda ya ban mamaki ko ciwon nono ban yi ba."
Ramlat ta dara.
"Kika sani ko wani cikin ya shiga? Tsarabar Lagos?"
"Allah Yasa. Ai nikam ina so wallahi."
Ba ta yi mamakin kalaman Aminiyarta ba don tun bayan aurenta sai da ta shekara biyar ba ta samu ciki ba sai yanzun. Mijinta Ɗahiru ya ce ba ita babu planning sai ta yi biyu.
"Allah Ya kawo mai albarka toh. Nidai yanzu yunwa nake ji."
Miƙewa suka yi a tare zuwa kicin Amrah na fadin. "Mutuminki ɗan wake nayi niyyar yi kuwa, na haɗa komai ki dora ruwa idan ya tafasa ki yi sakin bari na yanka mahaɗin."
"To da ban zo ba fa?"
Amrah ta yi dariya.
"Ai kuma tunda kin zo din magana ta kare. Yi hakuri ki taimaka ban jin dadin jikin."
Haka ta soma sakin ɗan waken tana yi suna hira.
"Ni kuwa ina Hilal?"
Tambayar Amrah ta tunasar da ita yanda suka yi a kwanakin baya, text ya yi mata akan ta sanyamishi rana da lokaci ya zo su tattauna abu mai muhimmanci sai dai ba ta yi karambanin ba shi amsa ba, daga ranar kuma bai ƙara nemanta ba.
"Kamar ban kyauta masa ba, amma a wurina hakan ne daidai."
"Me kika yi mishi?" Jin abinda Amrah ta ce yasa ta fahimci zancen zucin ya fito fili, nan ta bata labarin yanda suka yi. Ajiye wuƙar hannunta ta yi ta juyo da mamaki ƙarara saman fuskarta tana dubanta.
"Meyasa kike yiwa kanki irin wannan gangancin?"
Cikin rashin fahimta ta ɗan dubeta.
"Wane gangancin kuma?"
Haushi da takaici ya kusan kashe Amrah anan tsaye.
"Tambaya kike Ramsy? Ko kin manta na tunamaki waye Hilal? For all abinda ya faru bai sa ya juyamaki baya ba, bai kuma sa ya bar sonki ba, don me yanzu kin samu damar gyara laifukanki kike kokarin juyamasa baya? Allah Kike son yiwa butulci?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ba ta ce komai ba ta juya ta ci gaba da sakin ɗan wake, sanin hali na idan ta ga dama ba za ta ce uffan ba yasa Amrah itama ta ci gaba da aiki sai dai ta kumbura kiris ya rage ta fashe. Dama sun saba irin haka tun yarinta.
Ita kuwa sai da ta kammala ta wanke hannu ta jira ya dahu ta kwashe ba ta ko tsaya tambayar inda filas yake ba ta dauko. Sai da za ta zuba ne Amrah ta dakatar da ita.
"Wannan na Daddy ne." Tana nufin mijinta, murmushi Ramlat ta yi don tasan ƙawarta ta shaƙa, ta fice daga kicin rike da plastic din da Amrah ta yanka kayan cin dan waken. Sai da ta soyamusu manja sannan ta fito itama. A falon suna zaune sannan ne Ramlat ta dubeta a nutse.
"Tsaya don Allah ki saurareni."
Amrah ta dakatar da zuba ɗan waken da take kokarin zubamusu bayan ta ɗibarwa Affan nashi ya ja gefe. Harararta ta yi.
"Me kuma za ki cemin bayan kin maidani wata banza don kawai ina nunamaki abinda ya dace."
Hannunta ta riko tana dubanta.
"Kiyi hakuri, wallahi duk ba haka bane. Amrah yanzu ke a tunaninki da wane ido zan kalli Hilal na ba shi dama a karo na biyu bayan ni ce ummul aba'isin duk wani abu da ya faru a baya? Ko kin manta ba da Hilal kadai zan zauna ba? Akwai matarsa kuma akwai danginsa da babu ranar da zan goge bakin fentin da na yiwa kaina a idanunsu? So kike na bar wa ƴaƴan da zan haifa da shi abin gori? Yanzun ma wadannan din da ya na ƙare? Kin fi kowa sanin abinda ya faru, kuma kin fi kowa sanina Amrah. Da ace zan iya auren Hilal, da tuni yanzun wani labarin ake banda wannan. Amma bakin alƙalami ya bushe, zan iya yin aure ga kowane mutum a doron ƙasa banda Hilal. To balle ma auren babu shi a gabana yanzu, na gwammace na zauna na kula da yarana. Hakan zai fiyemin komai dadi."
Tausayinta sosai ya kama Amrah, har ba ta san sadda hawaye ya zubomata ba, ita kanta uwar gayyar sai jin ɗuminsa ta yi saman kuncinta. Ta kuwa shiga yi ba kakkautawa.
"Na cuci rayuwata Amrah, na cutar da mutane da dama wanda har gobe ban bar dana saninsa ba. Amrah har gobe ina tunanin bakin cikina ne sanadin mutuwar Abbana duk kuwa da irin rabuwa ta salama da amincin da muka yi. Ƴan uwana ba sa fahimtana, har gobe suna min kallon mai laifi a idanunsu. Ya zan yi ne wai?"
Nan fa suka shiga kukan har Affan wanda ganin Mominsa na kuka shima ya shiga yi. Dakyar suka rarrashi kansu sakamakon ƙarar da Affan yake da kuka yana rirriƙe Ramlat. Komai da komai ya shiga dawowa kwanyarta, daga lokacin da ta saki jiki suka soma gudanar da soyayya mai karfi tsakaninta da Aliyu, daga lokacin ne komai ya faro asali wanda har gobe ta kasa goge *BAƘIN FENTIn* a zuƙatan masoyanta.
*** *BAƘIN FENTI*
_*Komai yana da sila, komai da mafarinsa. Duk abinda bawa bai ɗora kan turba mai kyau da tsari ba, mafi yawan lokuta ƙarshensa nadama ne! Koda ace a haka kaddarar ta zo masa.*_
"Wai Ramsy me kike ne? Ki fito kina ɓata lokaci."
Muryar Amrah kenan sa'ilin da ta ke kokarin shigowa dakin. Zuwa yanzu ta kai matakin da ba ta jin za ta ɓoyewa kowa a duniya sonta ga Aliyu. Wannan tasa ko bayan shigowar Amrah ba ta fasa amsa wayar a nutse ba ba ta ko damu da kallo da murmushin Amrah ba.
"Kai wannan Hilal, shi ba ya jin kudinsa ko? Daga Malaysia mutum ya kira a yi ta wayar fin sa'i biyu? To nidai don Allah ya kyalemin ke ai daya, idan ba haka ba wallahi zamu yi lattin."
Ba ta da niyyar ba ta amsa, ta fahimci ba ta gane wanda suke wayar ba, ko ma ta ce ba ta sanshi ba.
Daga dayan gefen Aliyu wanda ke zaune a falon Muhibbat yayinda ita kuwa ke kicin tana shiryamusu abincin rana ya ɗan hade fuska kamar tana kallonsa.
"Baby waye Hilal? Baby ashe ban Kai darajar da har yanzu za ki iya sanar da mutane ni din kike so ba ba wani banza ba? Watanni goma da soyayyarmu wanda ya fi karfin na wadanda suka kwashe shekaru goma suna yi shine har yanzu ban samu karɓuwa ba? Sai anjima."
Ya katse wayar gaba daya yana fitar da huci. Fitowarta kenan daga kicin, ta ji dukkan abinda yake fadi, sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ranta na ƙuna kamar koyaushe, ta haɗiye kwallar dake barazanar tona abinda ke ranta. Ganin ya ɗan kalleta ya kauda kai ya ja tsaki ya sanya ta kakalo murmushi ta nufi inda yake zaune a darare.
"Yaya na kammala girkin."
Ya yi mata kallon sakara. Ta sauke kwayar idanunta, a duniya idan da abinda ta tsana ya biyo bayan kallon wulakancin da Aliyu ke mata a lokuta da dama.
"Sai aka ce miki yunwa nake ji? Ga jaki kin ajiye? Mtsww!"
Ya ja dogon kafin ya mike tsaye ya sa kafa ya ture Centre Table a zuciye har yana kifewa, ɗan flower vase din dake kanta na ado shine ya fashe. Bai ko waiwaya ba ya sa kai ya fice daga gidan. Ta zubawa ɓarnar da ya yi mata ido, ko ba komai kudi aka sa aka siyamata. Ba abinda ta nema ta rasa na ƙawata gida wanda iyayenta basu yi mata ba, yayyunta maza kuwa ba wanda bai ba ta gudummuwarsa ba duk kuwa da irin tsanar da suka yiwa Aliyu. Kuka sosai ta shiga yi tana tattarawa, Aliyu bai damu da ita ba. Ta hakikance ba ya sonta, ba kuma ya tausayinta. Ita kullum ke kwana da tashi da bakin cikinsa, ga so da tausayinsa wanda ke sanyawa ta ɓoye aibunsa a idon danginsu har a gaban Abulle wacce koyaushe cikin sanyamusu albarka take. Burin Abulle ta ga ɗa ko ƴarsu sai dai har a sannan Allah bai ba ta ciki ba. Ba kuma ta zargin Aliyu da komai.
"Allah ga mijina, Allah Kai ke shiryawa, Allah Ka shiryamin shi. Ka karkato da hankalinsa gareni." Ta furta a fili tana mai daga hannu gami da kuka, sannan ta shafe fuskarta ta ci gaba da tsince ɓarnar da ya yi.
A gefen Ramlat hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, hawaye take tana kara dialing lambarsa sai dai amsa daya ce, a kashe. Wannan ya tashi hankalin Amrah. Ta dubeta a gigice gami da dafa kafaɗarta.
"Ke, meyafaru da Hilal din? Me yace maki? Mun shiga uku."
Ambaton Hilal da ta ƙara ya farkar da Ramlat. Ta buge hannunta a saman kafaɗarta ta hau masifa.
"Hilal Hilal! To hell with him! Haba! Sai kiramin Hilal kike, a sanadinsa kin sa Aliyu ya yi fushi da ni! Ya kashe wayarsa bansan kuma me zai aikata ba! Dole ne zuwa walimar?! Ba zan je ba! Nace ba zan je ba ko za ki kaini dole?! Wallahi zuwanki bai min rana ba! Ni ki tafi kawai ki rabu da ni!"
Yanda take rufe ido tana zuba masifa iyakar gaskiyarta shi ya fi komai ba Amrah mamaki.
"Aliyu kuma? Waye hakan? Yanzu akan wani banza Aliyu kike min masifa?"
Ai kiran Aliyu da banza shi ya kara tunzura Ramlat. Ta nuna ta da yatsa.
"Kin yi na farko ya zama na karshe Amrah don wallahi ba don ina ganin mutuncinki ba sai na gasamaki abinda zai miki zafi a rai! Aliyu ya fi karfin ki kiramin shi da banza! Kika kara kuma Allah Ya isa! Ba zan je walimar ba ki tafi ki kyaleni! Aliyu shi nake so kuma da iznin Allah shi kadai ne mijina anan duniya!"
Daga nan ta juya a fusace ta soma cire kayanta tana tsaki. Amrah ranta ya dinga suya har bata san sadda ta shiga hawaye ba.
"Akan wani Aliyu kikemin Allah Ya isa? Idan kin kara ganina a gidanku kimin abinda ya fi haka."
Daga haka ta juya ta fice. Allah Ya taimaka Hajiya na wurin Abba, A'isha kuwa kallon cartoon da take a tashar Spacetoon ya dauke hankalinta.
Ita kuwa Ramlat ko a kanta, tashin hankalinta fushin Aliyu. Ta kwanta lamo tana fitar da hawaye, text ta shiga aikamasa kashi kashi.
_*Sweet na tuba don Allah Ka yafemin. Sweet fushinka barazana ne ga lafiyata. Wallahi sweet kai kadai nake so, Kar ka manta na san da zaman Hilal din amma nake sonka."
_*Wallahi Sweet Aliy zuciyata za ta buga. Wallahi har fada muka yi da Amrah a kanka. Ka yafemin. Wallahi don ba ka yanda na ci mutuncinta ba.*_
_*Sweet Aliy har walimar ban je ba saboda kai. Na kasa samun nutsuwa. Sweet Aliy ka yafemin ka bude wayata. Na maka alkawarin fadawa kowa kai nake so. Ka ji? Kuka fa nake. Kaina ma ciwo yake*_
Haka ta yi ta rubuta malamai kashi-kashi tana aikawa sai dai duk ba ya tafiya adalilin wayarsa a kashe. Ta kuwa ci gaba da rusa kuka, dakyar ta samu ta mike ta yi alwalar la'asar ta shiga sallah. Tun tana cikin sallar ta ji wayarta na kara, sallamewa kawai ta yi ba ta ko ida ba ta nufi wayar a guje. Ganin mai kiran ya sa ta ɗagawa da sauri ba tare da ta jira ya ce ba, ta ce.
"Sweet Aliy ka yafemin don Allah, na tuba wallahi ba zan ƙara ba."
"Zan yafemaki Baby amma sai kin fito na ganki. Ina nan bayan layinku. Ba zan iya bacci ba idan ban sanyaki a ido ba."
Wani dadi ta ji a ranta,
"Yanzu zan zo Sweet, ban minti biyar."
Sallar da ba ta yi ba kenan ta bar shi a sai ta dawo, nan da nan ta shafa hoda ta sanya lip gloss, kayan zuwa walimar da ta cire su ta mayar. Ta ja mayafinta, sai da ta kama kofa za ta fice daga dakin ta ji faduwar gaba, me Amrah ta ce ga su Hajiya kafin ta fita?
'Ko me ta faɗa ita ta sani, ke dai kar ki ƙara laifi wurin Aliyu.'
Wani bangare na zuciyarta ya ba ta shawarar da nan take ta dauka. A hankali ta fito tana ɗaga labulen da ya raba dakunansu da falon, babu kowa sai A'isha da ta gaji da kallonta tana bacci. Hamdala ta yi ta fice da sauri. Tun kafin ta karasa a hangoshi tsaye gaban mashin ɗinsa. Ya haɗe cikin shadda kalar sararin samaniya, babu hula a kansa sai dai ya yi kyau kwarai a idanunta. Kirjinta har wani bugu yake tsabar so da kaunarsa. Shima ya zubamata ido yana ji kamar ya saceta su gudu.
"Ba ki kyautamin ba."
Ya furta yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Ta yi narai-narai da idanunta. "Ka yi hakuri don Allah."
"Banda wannan, na hakura ai tun kallon farko da na miki na mance dukkan damuwata. Sai dai ba ki kyautamin da kika yiwa Aminiyarmu wulakancin da kika faɗa ba."
Sai a sannan ta tuna da ta yi laifi, ta jinjina kai.
"Haushi ta bani, banza fa ta kiraka." Ta fadi cike da wauta.
Ya ji ciwon kalmar sai dai ya yi murmushi. Har a ransa ya ji haushin Amrah na kiransa da banza.
"Kiyi hakuri, a kanki komai zan dauka zan kuma shanye muddin za ki zama rabona. Idan dai kina don farin cikina ku shirya a yau ba gobe ba."
Ta shiga gyada kai.
"Zamu shirya, zan je har gidansu na ba ta hakuri amma yau ba ta nan ta tafi walimar da na fadamaka zamu je dazun. Idan muka hadu a makaranta gobe zan bata hakuri ka ji? Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy."
Ya dan lumshe idanunsa yana murmushi, murmushin da ke ƙara tafiya da imaninta.
"Ya isa, shikenan ya wuce. Allah Ya kaimu goben. Da ban ganki ba, ba zan iya bacci ba."
Wani sanyi da dadi suka lulluɓe zuciyarta. Nan da nan kuma suka shantake da hirar soyayya kamar kar su rabu. Sai dab da karfe shida suka rabu, ba ta iya tafiya ba sai da ta ga tafiyarsa sannan ta juya cike da annashuwa ta koma gida.
"Sai yanzu ku ka dawo? Kun so ku yi dare." Abinda Hajiya ta fadi kenan, sai ta ji kaunar Amrah a ranta, wato dai ba ta sanarmata rigimarsu ba.
"Eh Hajiya, ki yi hakuri."
Hajiyar ta gyada kai tana kallon yanda ƴar ke zuba uban fara'a kamar wacce aka yiwa albishir da aljannah. Gudun kada Hajiyar ta watsamata tambayar da za ta kasa amsawa game da walimar, ya sanya ta saurin shigewa daki gami da faɗawa kam gado tana murmushi, Aliyu shi ne komai nata a yanzu, ba kuma ta jin har abada za ta bar shi ko me za'a yi, kuma ko me zai faru. Tunawa ta yi da sallar la'asar, da sauri ta mike ta faɗa banɗaki ta kara dauro alwala sannan ta tayar da sallar kusan ma a sallar banda murmushi da addu'ar Allah Ya sa ta zama matar Aliyu ba abinda take.