Kenza eBookz

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 9

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 9

Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 9: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 9. Ai kuwa ta ci sa'a don tana kammala girka shinkafa da miya, suka…

3,372 words

Ai kuwa ta ci sa'a don tana kammala girka shinkafa da miya, suka ci. Ba ta ko biyewa mitar Anti Bilkin ba na ta karar mata da kudin kira kuma ta hadata faɗa da miji, ta tattara ana la'asar ta yi gaggawar barin gidan cike da kwarin gwuiwa ta doshi gidansu don kuwa tana ji daga zuciya da gangar jikinta, yanzun tana da abin faɗa, tana kuma da abin kare kanta. Ta gaji da ɓuyar.

*** "Gida zan tafi da ita, ba zan bari ta koma gidansa a wannan halin ba. Ba kuma zan bari kakarku ta ci gaba da juyamin yarana ba son ranta. Dole wannan karon a yiwa abin tufka."

Fadin Mama tana huci cike da takaicin halin da Muhibbat ke ciki. Duk wannan karfin ikon tana yi ne bayan tafiyar Abule gida don a farko Abule ta kasa ta tsare cewa kafarta kafar Muhibbat din, ita za ta kula da ita, acewarta ta ga jiya kuma ta ga yau, don haka sai dai ta koyar da wankan jego. Dakyar su Justice suka lallaɓata ta bar asibitin.

Ta zubawa mahaifiyarta idanu tana mai jin hawaye na sauka bisa kuncinta. Sosai ta goyi bayan hakan, ta ji ta kuma gani za ta koma gidan iyayenta. Komawar da za ta zama na har abada. Wannan na nufin alaƙarta da Aliyu ta ƙare. Lumshe ido ta yi bayan ta share hawaye ta yi shiru kamar mai bacci tana ci gaba da sauraron yanda yayyunta maza da kuma Mamar suke fadin albarkacin bakinsu. Don babu wanda bai taɓa ganin cin kashin da Aliyu ke mata ba, musamman mazan da suka fi kowa sanin har gobe bai bar shaye-shaye ba.

Ta tuno yanda komai ya faru har ya yi sanadin faduwarta da kuma suma.

_Tana zaune a falo ta zubawa talabijin ido sai dai rabin hankalin ya tafi ga tunani, cikin wannan halin ta ji bugun ƙofa kamar za'a ɓalla. Da hanzari ta mike ta fito tsakar gidan, shakka babu bugun ne. Wannan yasa ta tuna bai fita da mashin dinsa ba, asalima mashin din kwana biyu ta bar ganinsa, ta kuma ji yana waya yana kiran siyarwa zai yi ya siya wani._ _Hijab ta zura gami da daukar mukullin gidan jiki na rawa ta nufi kofar a ranta tana mamakin abinda ya hanashi daukar nasa mukullan. Kai tsaye ta bude gami da kaucewa ganin mutum ya shigo a hargitse kuma yana tangaɗi. Ji ta yi cikinta ya yi wani irin juyawa, tabbas yana sha, amman duk ranar da ya yi niyyar sha zai umarceta da fita daga dakinsa ya kulle, takan sa kunne ta ji yana tamɓelansa har bacci ya kwashe shi. Kusan rabin mayen a kiran sunan Ramlat ko kuma Baby zai ƙare sai kuwa zage-zage._ _"Ki rufe ƙofar kin tsaya kina kallona kamar farin wata."_

_Ya yi furucin da muryar ƴan maye. Jiki na rawa ta rufe suka koma ciki tana ambaton Allah a'a zuciya. Abinda kawai take tunani bai wuce na kasancewar mashayi uban ɗan cikinta ba, ta shafi cikin da tun da ya murda bai saki ba tana kuka sosai. A haka ta iskeshi ta zube a saman dinning table yana bude kulolin abinci gami da watsar da murafan a tsakar falon. Ba don plastic bane da ya fasamata._

_"Ke, ban hanaki yimin tuwo a gidannan ba?"_

_Ta share hawaye, ya za ta yi? Abinda ke cikinta shi yake da muradi, ta kasa cin komai tun safe. Ganin kuma sun jima ba su ci bane ya sanya ta girkawa._

_"Ka yi hakuri."_

_Miƙewa ya yi ya ƙaraso inda ta ke, ba zato ta ji ya ɗauketa da mari, abinda tun da take za ta iya cewa ba'a taɓa marinta ba da girmanta. Wannan ta sanya ta yin baya a gigice, ba kuma zato ta bugu da bangon dake gefen 3 steps na hawa dinning din wanda ya yi sanadin gocewarta ta fadi akan cikin da ko fitowa bai yi ba. Ba shiri ta saki wani mugun ƙara gami da ambaton Allah, a hankali ta daina motsi. Shi kuwa ya nuna ta da yatsa._

_Tsabar raini ya shiga tsakaninmu shi ne za ki kwanta bacci ina magana? To don uwar ubanki ki yi ta baccin mana! Aikin banza!"_

***

Ta ƙara runtse ido, tabbas ta ji wannan kalamin can tsakar kanta kuma kamar a mafarki, koda ta farka a gadon asibiti ta ganta Abulle a gefanta tana sharar hawaye da surutan kada Allah Ya sa ta mutu ba ta ga yaran Aliyu da Muhibbat din ba. Ta kudurta wannan buri na Abulle ba zai samu ba da yardar Allah, ta hakura da Aliyu koda sonsa zai zama ajalinta. Ta ba shi damar auren wacce duk yake so. Ita kam karatunta da yace ba ya so shi za ta koma yanzun. Bangaren iyaye sun dauka a karon kanta ta ce ba za ta koma makaranta ba, ita da Aliyun ne kaɗai suka san sirrin rashin komawarta. Duk don ya kuntata mata ya ce ba za ta koma ba.

Tana ji yayyunnata suka fita a dakin sakamakon sallamar su Amarya da sauran mutanen gidan.

*** Aliyu na tsaye a farfajiyar asibitin, shigowarsa kenan. Ko kallonsa ba su yi ba, shi kuwa ya bisu da banzan kallo da harara, yana tafe yana tunanin me ya yi mata? Daki-daki ya tuno dukkan yanda aka yi.

_Yana tangaɗi ya kife saman kujera bacci ya yi awon gaba da shi bayan ya yi magaginsa ya gama. Bai farka ba sai da sanyin asuba ya ratso falon. Cikin mamaki ya tashi gami da dafe kansa dake ɗan sarawa. A hankali ya shiga tariyo abinda ya faru daki-daki, shi dai ya san sun siya kayan maye da abokansa. Anan motar abokinnasa suka sha banda G Baba wanda ke tuƙi yana musu dariyar rashin hakurinsu na ƙarasawa gida. Duk cikinsu shi ɗaya ne ya yi aure banda su da ke kokarin hada takardun Degree. Bai manta sadda suka kawo shi gida ba suka yi gaba, bai kuma yi kasa a gwuiwa ba wajen budurin da suka yi da Muhibbat. Da hanzari ya mike ya nufi hanyar ɗakinta, ba ta nan, banɗaki ma haka. Ya fito da niyyar nufar nashi dakin ya hango mutum kwance a hanyar wurin dinning table. Jiki na rawa ya karasa, ba karamin kaduwa ya yi na ganin jini ba. Kai tsaye ya kira family doctor din su Muhibbat din da ma jama'ar gidan. Ba ɓata lokaci ya mishi bayanin halin da take ciki, sanin tana da ciki ya sanya shi bada umarnin kawo ta asibiti. A gigice ya fita da zummar kwankwasawa makwafcinsa, ya ci sa'a ya fito don zuwa Masallaci. Lurwan ya dubeshi._

_"Lafiya kuwa Aliyu? Meyafaru?"_

_"Muhibbat ba lafiya, taimaka ka kaimu asibiti nan kusa ne don Allah."_

_Ba tare da ɓata lokaci ba suka je asibitin aka karɓeta suka wuce masallacin asibitin suka yi sallah, likita ya tabbatar da fitar cikinta._

"Sai kuma shikenan a dinga yi min kallon mai laifi? Mtsw"

Ya ƙarashe da tsaki don shi dai yasan da ace a hayyacinsa ne ba zai yi wannan gangancin ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta bayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan.

*** Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arzikin kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta.

"Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.

"Banda Hilal, akwai wani da kike kulawa ne?"

Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana.

"Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yaushe ku ke tare?"

Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare.

"Sunansa Aliyu."

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

09)

Tun shigarta ajin ta hango Amrah ta sauya wurin zama daga kujera mafi kusa da ita zuwa can ɓarin hagunta, ba ta yi mamaki ba don dama duk sadda saɓani ya haɗasu sai an gane a ajin ko don sauya wurin zama. Ba ta yi gigin zuwa inda take ba ganin malaminsu ya taho. Sai dai kusan rabin hankalinta yana gareta, a yanzun ta gane kurenta sosai, Amrah yar uwa kuma Aminiya tun suna yara bai kamata ace ta yi mata hakan ba. Yanzun ta fi koyaushe bukarta kasancewarta abokiyar shawarar da suke haƙowa su binne ba tare da kowa ya ji ba. Sai dai a ranta tana da yaƙinin muddin ba za ta bata goyon baya game da sheƙar da ta sauya ba, komai ma ya biyo baya ba matsalarata bace. At her age, Babu wani ko wata da za ta bari ya tauyemata ƴancinta. Test har biyu suka yi, da na Economics da Commerce, bai bata wuya sosai ba, ko ba komai tana da basira daidai gwargwado sannan ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin karatu bisa shawara sanyin idaniyarta.

Ana tashi break ajin duk an fita sai ita sai kuma Amrah da ta maida hankali ga kwafar note. Wurinta ta nufa kai tsaye, ko ba ta ɗago ba ta san ita ce, takaici ya kamata. Nan da nan kalaman da ta jefata da su suka dawomata, wasu hawaye ta ji sun soma wanke mata fuska.

"Ko ba amintaka tsakaninmu Ramlat, zan ci darajar kaunar da nake miki kamar ƴar uwata ta ciki ɗaya. Akan namiji kika zageni kika wulakantani tamkar ba ki sanni ba. To ni kuwa me za ki cemin? Tsayuwarki ba ta da amfani don yanzun babu komai tsakanina da ke face gaisuwar musulunci, shima gaisuwar idan naga za ki wulakantani ba lallai ba tilas."

Tana maganar tana jijjiga biro tana fidda hawaye, itama kanta uwar gayyar hawayen take. Damuwa biyu suka tarar mata, ga na bakin cikin dawowar Hilal da kuma gaggawar bari a sanyamusu ranar aure da ta yi, ga kuma na zafin abinda ta aikata ga Aminiyarta wanda har sai da Aliyu ya ankarar da ita kuskurenta. Hannunta ta kama wanda dole Amrah ta tsayar da rubutun don dama tuni ta daina fahimtar abinda take kwafa sakamakon hawayen da ke maida idanunta gani dusu-dusu. Littafin kuwa duk ya soma jiƙewa.

"Ki yafemin don Allah don Manzon Allah s.a.w, nayi kuskure ba zan ƙara ba. Na fahimci laifina. Idan na kara ki dauki dukkan matakan da kika yi niyya."

Jin chanjawar muryarta da kuma kukan ya karya zuciyar Amrah, basu soma ƙawance don wani can ya rabasu ba. Sun saba su yi fadansu kuma su shirya ba tare da sun bari wani third party ya shigo tsakaninsu ba.

Dakyar ta yarda suka shirya karshe kuma suka hau hira har da dariya tamkar ba su ba.

"Waye Aliyu?" Tambayar da Amrah ta jefomata kenan. Sai da gabanta ya fadi tsabar so da kaunar mai sunan. Ta lumshe idanu ta bude tana murmushi gami da duban agogon tsintsiyar hannunta.

"Saura 3mins a dawo class, ki bari idan an tashi i promise to tell you everything about him."

Murmushi ta yi.

"Shikenan."

Ana tashi kuwa suka ci sa'a ba'a zo ɗaukar kowannensu ba, don haka suka samu wuri can ƙasan bishiya saman kujera suka zauna. Babu abinda ta ɓoyemata dangane da Aliyu da karfin dangantakarsu a yanzu. Cikin hawaye ta kara da fadin.

"Wallahi wallahi kin ji rantsuwa ta ƴar musulmi, ban taɓa son wani yanda nake son Aliyu ba, ciki kuwa har Hilal! Ba zan iya auren Hilal ba, ba kuma zan yarda a auramin wanin Aliyu ba ko waye shi."

Baki sake Amrah ke dubanta. Ko a jiyan da suka yi wannan rikicin, ta san cewa ko wane Aliyu, Ramlat ta yi nisa a begensa.

'Ko asiri ya mata?'

Girgiza kai Ramlat ta yi gami da dariya mai ciwo.

"Kinsan Allah ba wani asiri, wannan son tsaftatacce ne."

Amsar yasa ta fahimtar zancen zucinta ne ya fito muraran.

"Wallahi gani nake kamar wata Ramlatun ce zaune anan ba Ramsy Ramlat da na sani ba. Kwanakin nan dama na lura da yanda walwalarki ta sauya, na lura sauyi a yawancin abubuwanki ta yanda hatta da wayarki kina kaffa-kaffa kar a taɓamaki. Ashe wata tsiyar kike shirin tafkawa!"

Nan da nan Ramlat ta ɗan sauya fuska.

"Ki bar kiran tsiya akan abinda bawa ba shi da iko a kansa, ko daga labarin da na ba ki na haɗuwarmu da Aliyu, ke kanki kin san haɗin Allah ne ba yin kanmu ba. Wallahi na guji Aliyu kamar gudun rai da ajali amma kuma ya zan yi tunda Allah Ya ƙaddara akwai ɓoyayyen lamari tsakaninmu?"

Miƙewa Amrah ta yi a fusace.

"Na gaji da jin wannan tatsuniyar! Na gaji da jin wanin Hilal a bakinki Ramsy! Me ya shiga kwakwalwarki wai? Ramsy Hilal fa? Mutumin da kika so a ganin farko, ban taɓa zaton irin wannan son mai shiga a yaɗuwar farko yana shafewa ba. Shawarar da zan ba ki shi ne ki nemi zaɓin Allah, kar ki biyewa zuciya ki yi saki na dafe, kar kuma ki biyewa sharrinta ki ƙare a zaɓen tumun dare! Ki sani babu hannun Amrah a cikin shafin Aliyu, har gobe ina sonki da Hilal kuma ina hango maki kyakkyawar rayuwa da mutum kamili irinsa da yardar Allah. Ban san Aliyu ba ban kuma taɓa ganinsa ba, sai dai ina miki rantsuwa bai kwantamin ba. Allah Ya ganar da ke Ramsy. Kin ban mamaki."

Daga haka ta juya tana shirin barin wurin ta ji amon muryar ƙawarta wanda ko cikin bacci ta tashi ba zai ɓacemata ba.

"Hilal dai! Ke ki aureshi mana muga ƙarshen so!"

Ta yi maganar cike da tsawa da nuna jin zafi ta ƙarara, anan Amrah ta gane irin nisan da Ramsy ta yi a lamarin Aliyu. Ta juyo a sanyaye, kuka ta yi zaman yi mai nuni da ranta na suya, tana tare da damuwa. Tausayi ta ba ta sai dai ba ta jin za ta taɓa ba ta goyon baya ta bar nagartaccen mutum mai alƙawari irin Hilal akan wani wanda ba su san halayyarsa ba. Ta koma ta zauna gefenta, sai da ta bari ta yi mai isarta sannan ta soma magana a tausashe.

"Kiyi hakuri Ramsy, ki yi hakuri da dukkan kalamaina."

"Me za ki cemin tunda kin kasa fahimtana, idan kika kasance ta farkon juyawa lamarina baya, ya kike son na yi?"

Ɗan murmushi Amrah ta yi, tausayin Ramlat da kuma Hilal na cin ranta. Shakka babu an mishi kwacenta lamarin zai ba da wuya.

"Kiyi hakuri, na yi kuskure. Shawara kika buƙata ko?"

Ta gyaɗa kai kamar wata ƴar goye.

"Addu'a, ki yi addu'a sosai na neman zaɓin Allah. Ki hakura ki tausasa zuciyarki kar ki biyewa son ranki. Ramlat ga duk namijin da zai kiraki a lokutan da yake tare da matarsa ta sunnah har a ranki ki ji maƙurar so yake maki ina tabbatar maki kin yi babban kuskure. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Wannan cin fuska ne, ina roƙonki ki bar shiga hakkin wata saboda zai iya zuwa kanki ki ji haushi. Ba karfin sonki bane ya sanya, ki lura."

Ta ci gaba da ba ta shawarar mika lamura ga Allah da kuma ci gaba da ɓoye batun Aliyu a gida, Ramlat ta dauki shawararta tunda ko ba komai akwai sauran lokaci na kammala karatun da kuma auren. A ranta ta kudurta ganar da Hilal a sannu-sannu yanda zai fahimci ta sauya sheƙa ta kuma bar ra'ayin aurensa. Batun rabuwa da Aliyu bai taso ba!

"Amrah Abdullahi! Bala yana magana!'

Suka juya ga mai maganar, Zuhra Ishaq ce ƴar ajinsu wacce suka fi kira da Big Mama saboda ƙibarta, tun tana jin haushi har ya zamemata jiki. Tsaki Amrah ta ja tana mai miƙewa da daukar jaka lokaci guda tana aikamata daƙuwa jin ta raina direban gidansu wanda a haife ma zai haife su. Tare suka tako da Ramlat tana ƙara ba ta shawara.

"Nagode, zan yi aiki da shi. Ki tayani da addu'a dai." Murmushi Amrah ta yi ta bita da toh, sai dai kuma ta san kafiyar Ramlat, fatanta kar ta jawo abinda zai hargitsa lamura.

Tun da yammacin ranar da suka yi waya ya sanarmata zai shigo bayan Isha'i su gaisa take cika take batsewa, duk wanda ya kalleta ya san ba ta cikin walwala.

"Ke kuma meke damunki wai?"

Fadin Zulaihat da ta wuni a gidan.

"Bar ta Uwani, ta yi kuncin ta gama, yanda kika ganta tun sadda ta ji labarin dawowar yaronnan take cika da batsewa. Ban san kuma me hakan ke nufi ba. Ina fatan kar ta ba ku kunya."

Hajiya ke maganar ranta a ɓace don dama tun ɗazun ƙuncin da Ramlat ke yi da tsakin da take bugawa akai-akai ke cin ranta, magana ce kawai ba ta yi ba. Maganar Hajiyar yasa Zulaihat kallonta dakyau, ga mamaki ma hawaye ta shiga sharewa.

"Meke faruwa ne Ramlat? Kun yi faɗa ne?"

Ta girgiza kai, takaicinta yasa Hajiya sungumar Khalifa yaron Zulaihat na farko suka bar falon. Zulaihat ta dawo gefenta ta zauna.

"Fadamin damuwarki. Ko Hilal din ne ba ki yi murna da zuwansa ba?"

Duk kwarin gwuiwar da take tunanin tana da shi sai ta ji ta kasa kataɓus, ta kasa fadawa Zulaihat abinda ke ranta game da Hilal.

"Ko kin daina sonsa?"

Ta dubeta da sauri ganin ta harbo jirginta. Girgiza kai Zulaihat ta soma tana murmushi gami da yi mata kallon yarinya karama don duka a sannan ba ta fi sha biyar ba.

"Kar ki soma don Allah Ramlat, ina mai tabbatar maki ba wanda zai goyamaki baya. Kar ki sake ki ɓullowa da wanin Hilal matsayin saurayinki. Take-takenki kenan wanda ba zan so ya janyomaki wani tambari kuma abin yayatawa ba a dangi. Ture ma batun dangin da kuma mu, ba ki kyauta ba, za kuma ki amsa sunan mayaudariya. Ina so ki binne kuma ki ci gaba da haɗiye abinda ke ranki, ki tattara wajen miƙa wa Ubangijinki. Shi zai zaɓamaki abinda ya fi alheri. Kar ki yarda kuma kar ki yi gangancin bada kofar da za'a ƙara fahimtar inda kika dosa. Allah Ya kyauta don kuwa akwai matsala."

Daga haka ta mike ta bi bayan Hajiyar zuwa ɗaki, itama ganin ba amfanin zamanta sai ta koma ɗakinta, kuka ta yi son ranta sannan ta fito. Ta ga alamar babu wanda zai fahimceta, zuwa yanzu za ta kwantar da hankalinta har ta kammala Sakandire, a wannan lokacin ne za ta san abin yi.

Da wannan shawarar ta ɗan saki ranta ta sauya, koda Hilal ya zo hakanan ta danne komai ta hau gyara jikinta babu ko kwalliya. Tana jin muryarsa yana gaisawa da su Hajiya, can kuma ta ji an murda kofar ɗakin an shigo. A'isha ta gani.

"Yaya, Hajiyata ta ce ki je waje ga Yaya Hilal."

Ta gyada kai tana hararar A'ishar cike da bakin ciki. Mayafin abayar da ta sanya kawai ta ja ta rufe kanta, a falon ta tarar da Hajiya don tuni Zulaihat ta tafi.

"Hajiya zan je."

Ga mamakinta fuskarta a sake ta amsa.

"Toh wuce mana. Kar ki kai dare dai."

Ta amsa da toh tana satar kallon ledojin da ke kusa da kafar Hajiyar wanda ba tantama shi ya kawo.

Yana tsaye jikin motar ƙirar Honda wacce ta yi daidai da zamanin. Bayansa take hangowa, cikar kamala da ingarman jiki irin na maza ƴan kwalisa kuma abin muradin kowace mace, Hilal ya kai. Tana tafe kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana karantarsa, zuwa lokacin ya juyo shima ya zubamata idanunsa. Kallon da take mishi da ace a sannan akwai sauran cikakken nutsuwa tattare da shi, zai fahimci ba kallo ne mai nuni da kewa ba, kallo ne na ƙurillah, na ƙeƙe da ƙeƙe. Kallo ne na son gano abinda ya fi Aliyunta da shi wanda har ake zubamata gargadin ɓoye sittin zuciyarta. Shakka babu ya sauya, fatarsa ta kara murjewa, farinsa kuma ya kara fitowa. A gefe guda ya kara kyan da zai burge ƴanmata banda ita.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull