Kenza eBookz

Karuwar gida Complete - Chapter 10

Karuwar gida Complete - Chapter 10

Karuwar gida Complete Chapter 10: Karuwar gida Complete Chapter 10. Ko minti goma ba'a yi ba sai Hajiya Babba da ƙaton tarmus na ruwan bagaruwa😹,Daddy da…

2,061 words

Ko minti goma ba'a yi ba sai Hajiya Babba da ƙaton tarmus na ruwan bagaruwa😹,Daddy da ke falo sunne kai yayi bayan ya buɗe mata ƙofa "ta na ina ita Mimin?"ƙofa ya nuna mata ta shiga a zaune ta tarar da Mimi ta na rera kuka sai buɗe ƙafafu ta ke. "Yau ni na ga sakalci mi zan gani?buɗe ƙafafu kike sanyi ac ya shige kika saka mu uku?"Hajiya Babba ta faɗa kuka na ƙara fashewa da shi ina ƙoƙarin tashi,tarmus ɗin ta kai toilet sannan ta zo ta ja ni. Wani uban ihu na runtuma lokacin da Hajiya Babba ta cika ƙaramin towel da ruwan bagaruwa masu masifar zafi ta danna min,"woyyo Daddy mutuwa zan yi "na faɗa cikin kuka amman sam Hajiya Babba ba ta sarara min tun ina jin zafi har na fara jin daɗin gashin na sassauta kuka na. Wannan karon kuwa tsaf na taka da ƙafafuna duk da ina jin zogi kaɗan sai na rinƙa ware ƙafafu "haka za ki rinƙa gasa jikin ki kullum kar ki ƙara tsarki da ruwan sanyi sai na ɗumi ai ki godewa Allah ma da bai sa kin ƙaru ba"Ni dai ban ce komi ba na bi lafiyar gado na kwanta. Daddy ya shigo sai sunne kai ya ke,Hajiya Babba kuwa kawar da kai tayi gefe kamar ba ta san da shigowar sa. Miƙar da ni yayi zaune ya ban tea haɗi da magani,ina gama sha na koma na kwanta sai barci.

Daddy ya mayar da Hajiya Babba sannan ya biyo da abincin da Lami ta girka domin breakfast,har yanzu Mimi barci ta ke.Bakin bed ya zauna ya na kallonta a zuci kuwa tausayinta ya ke yadda tayi jarumtar ɗaukar nauyin sa.

***

Cikin ikon Allah Fauziya ta fara samu sauƙi sakamakon ɗaukar nauyin kula da ita da Alhaji Waleed ya ɗauka,a ɓangaren soyayyar su da Nabee kuwa sai neman Allah shirya su dan kusan kullum su na tare ta na biya mashi buƙata ta baki gefe ɗaya kuma ta na bin wasu Mazan suna soyayyar shan minti amman banda sex dan tayi alƙawali budurcinta mijinta za ta baiwa kyautar sa. Nasir da Fadila kuwa tun ranar da aka zana sunan yaro aka ɗaura masu aure,yanzu haka shirye-shiryen tarewar ta ake. Nasir ya so kama mata haya sai dai Iyani tace a'a doli gida ɗaya za su zauna,babu yadda ya iya doli ya gyara ɗakinsa aka saka Fadila wacce Anna ta ƙi yiwa kayan ɗaki kawai dan ta gulala mata. Zaman Fadila zaman takura ne sam Iyani ba ta barinta wali,duk jarabar Nasir sai da ya haƙura da keɓewar rana saboda da zarar ya shigo gidan Iyani ta fara masifa kenan ta na cewa Fadila ta mallake mata Ɗa.

Ƙirjinsa ta shafa wanda furfura ta gama cika sa tace "Alhajin Allah dagaske wai ka mallaka min wannan gidan?"Alhaji Tanimu ya shafi ƙaton cikinsa yace "sosai kuwa babyna ai tunda na ga kin sha sperm ɗina ba tare da ƙyanƙamina ba na san dagaske kike sona kuma za ki aure ni"murmurshin yaudara Nabee tayi ta faɗa jikin Alhaji Tanimu ta na godiya a zuci kuwa dariyar sa ta ke.

Nabee na dawowa gida ba tare da wani ɓata lokaci ba ta shaidawa Iyani wani Alhaji yayi mata kyautar gida,cike da murna suka fara shirin komawa. Alhaji Waleed tuni Nabee ta sallame shi ta koma da Alhaji Tanimu kawai ta na tatsar sa kuɗi,tuni kuwa suka koma sabon gida Nasir sam hankalin sa bai kwanta ba hakan yasa ya yiwa Iyani zancen. Cikin masifa tace "au baƙin ciki da hassadar ƴar uwar ka kake ban sani ba?to ka na iya jan matar ka ku bar gidan "ta na gama faɗar haka ta bar shi nan tsugunne.

*** "Da zafi"na furta a shagwaɓe ina mai ɗora hannuwana bisa gadon bayansa, murmurshi ya sakar min yace "daure dai ba zan yi da zafi ba"na lumshe ido ina jin ya na shigata a hankali a tare mu ka sauke numfashi lokacin da ya gama samun daidaito,har ya gama bidirin shi ban buɗe ido ba dan har yanzu kunyar kasancewa na ke da shi gwara shi tunda dama kunyar maza ba irin sosai ɗin nan ba ce. Wanka mu ka shiga a kunyace yayi min mu ka fito mu ka shirya mu ka koma falo mu na kallo, Daddy kuwa ya zaƙe sai soyayya ya ke nuna min ni ma na manne mashi. Cikin wata biyu na murje nayi kyau haka ma Daddy sosai shaƙuwa ta da soyayya suka ƙara shigar mu,babu ranar banza da ba za mu kasance ba tun ina raki har ya kai jikina ya saba dan wani lokaci ni na ke fara neman sa.

***Bayan 1year

Sosai ake gudanar da bikin auren Ameera da Abu Maleek wanda Daddy ya bada aurenta,Dr Ibrah ma ya halarta bayan ya nemi gafarar Daddy Mami ma haka sosai kuma tayi nadamar abinda ta yi,cikin jikinta kuwa ta haifo sa amman ba da rai ba daga nan aka ɗaura masu aure Ita da Dr Ibrah bayan tofin Allah tsine da ta samu daga danginta.

Ana shirye-shiryen kan amarya na dafe ƙaton cikina wanda ya shiga wata na goma sha ɗaya,azaba na fara ji ta ko ina wanda ya saka ni sakin ƴar ƙara wacce ban shirya ba. Da sauri Hajiya Babba ta matso ta na tambayata,kasa yin magana nayi saboda azaba da sauri aka kirawo Daddy. Hankali tashe ya shigo tuni uwaye mata uwanda ba su kai ga shiga motocin kan amarya ba suka kewaye ni,wani irin nishi ni ke goshina na fitar da zufa kan kace wani abu naƙuda ta zo gadan-gadan. Dr Ma'aruf ya aka kira dan kuwa ba za'a kai ka zuwa asibiti ba haihuwar za ta zo tunda tuni kan ɗa ya sawo kai,cikin azaba na fara kiran sunan Daddy wanda tuni ya fice hayyacin sa duk da manganar da Hajiya Babba ke mashi na ya fita waje amman ya ƙiya. Cikin ikon Allah na haifo triples duk gan mata,wani irin kuka Daddy ya fashe da shi ya duƙa yayi sujidah shukur kafin ya fara ɗaukar yaran.

Gyara min jiki Hajiya Babba tayi aka gyara gun da na ɓata aka saka turaren wuta, asibiti mu ka wuce aka duba lafiyar mu da ta babies sannan aka sa min ƙarin ruwa. Momy,Hajiya Babba, Daddy da kuma Abba sai aka rasa wanda ya fi son yaran kowa sai bajinta ya ke nunawa. Washegari aka sallame mu,direct gidana aka kai ni Hajiya Babba ta min wanka dan ita ba ta ɗauke ni a sarakuwa ba matsayin jika ta ke ɗaukata. Sai bayan ta gama min ta yiwa ƴan uku sai kuka suke,ni kuwa na ɓata rai kar a toye min yara😹 Daddy ma da ya shigo sai da ya saka hannunsa cikin ruwan dan jin zafin su ƴan barka uwanda suka kasance duk dangi sai dariya suke.

Ranar suna aka saka masu *UMMU SALMA,UMMU HABIBA DA UMMU KULTHUM* sosai na samu Gift daga ɓangarori daban-daban. Lokacin da Mami ta zo kasa ɗagowa nayi na kalleta dan kunya na aure mijinta har da haihuwa,Gift ta bani ta na murmurshin da duk wanda ya gani ya san na ƙarfin hali ne.

Bayan arba'in Tuni yarana sun yi ƙiba sosai zallar kyawun su ya fito,cikin shirin fita na fito na goya ɗaya Daddy ma ya ɗauki ɗaya sai na rungume ɗaya mu ka nufi mota inda drever ke jiran mu. Asibiti mu ka je aka yi mana ayo,cikin shagwaɓa nace "please Daddy ka bari na ɗauki ko na shekara biyu ne"hannu ya aza min a baki yace "shuuut!kar naji kar na gani babu wani magani da za ki ɗauka,haihuwa duk shekara na ke sonta so na ke ki tara min yara dayawa"buba ƙafafu na fara ina shirin magana naji muryar da har abada ba zan taɓa manta ta ba.

Cikin kuka da damuwa ta ke cewa "wlh likita ni ban taɓa yin iskanci ba ta yaya zan samu HIV?ka sake dubawa dai"da sauri na ƙaraso Daddy na bi na daga baya. Iyani ta goge hawayenta tace "likita ta yaya za ta samu cutar ƙanjamau bayan ka tabbatar min ta na ɗauke da budurcinta har yanzu?koko result ɗin wata ce ka ɗauko?"Dr ya girgiza yace "ku yi haƙuri abinda sakamako ya bada kenan ta na ɗauke da cuta mai karya gangar jiki kuma tuni ta yi tsanani rashin zuwa kan lokaci ta na traitement a gida" "Na shiga uku ni Nabee wacce irin baƙar rana na ke gani?"Iyani tace "Nabeela na zata ciki ne kika kwaso shiyasa har na kawo ki asibiti a min gwaji amman kika ce sai dai a maki na budurci ashe ga banza ne,to gidan ubanwa SIDA ta shiga jikin ki?" "Haba ba haka ya kamata ki yi ba,rarrashi ta cancanta a wannan lokacin dan kuwa har da cutar Hanta gare ta ga kuma infections wacce duk ana ɗauka ne ta hanyar zina ko kuma biye-biyen maza na soyayyar shan minti "

Wani kuka ne ya kubce min ban san lokacin da na furta "Innalillahi wa'inna iley raji'un Nabee ke ce a haka?ke ce kika yi baƙi kika rame kika yakuce haka?Nabee kin ga illar zama *KARUWAR GIDA* ko?mi kuɗaɗen da kika tara suka amfana maki?minene amfanin budurcin da kika yi ta tattali ki na cin duniyar ki da tsinke?" "Mimi ki yafe min na san ƙarshe na ya zo,na so cutar da ke da mahaifin ki amman Allah bai so ba.Yau gani a wulaƙance babu daraja babu kyawun surar da ke ruɗar maza suna biyata..." "Na yafe maki duniya da lahira Allah baki lafiya,dan Allah Nabeela kiyi traitement yadda likita yace da sannu za ki samu sauƙi"banda gyaɗa kai babu abinda Nabee ta ke ta rairafo za ta zo wajen Daddy yayi saurin cewa ya yafe mata ya na mai jan hannuna mu ka koma can cikin room ɗin da triples suke mu ka ɗauko su mu ka dawo gida.

Wuni ranar nan haka nayi shi babu daɗi,sosai na ƙara tsorata da lamarin duniya yadda ya ke juyawa kamar juyin waina.Daddy kasa fita yayi doli ya zauna kusa da ni ya na min nasiha sannan ya ƙara da cewa "ki kula min da yara na ki basu tarbiyya ta ƙwarai ta yadda Ubangiji zai yi alfahari da mu na tsare amanar da ya ba mu"rungumesa nayi nace "in shaa Allah mijina kuma ka yafe min zargin da nayi ma na ka kasance da Nabee"ƙirjina ya shafo yace "bai komi my Life"ya faɗa ya na mai kai bakinsa kan nawa.

***Bayan wasu shekaru Abubuwa dayawa sun faru,ciki kuwa har da samun lafiyar Fauziya na yoyon fitsari tuni tayi aure ,Fadila ma masha Allah ta jerawa Nasir yara sannan tuni ta fara aikin gwamnati mai tsoka ta canza rayuwar Anna wacce ta aza buri akan ta Nabeela ma ana ta ɗaukar magani a ƙarshe kuma ta auri Alhaji Tanimu wanda yayi sanadiyar laƙa mata ƙanjamau cike da baƙin ciki ta baiwa tsohon kyautar budurcin da samari da dama sun so karɓar sa ta hana.Iyani kuwa tuni tayi saranda daga shegen kwaɗayi na son kuɗi tare da nadamar rayuwa.

Ameera ma ta na zaune ƙalau da mijinta Abu Maleek,haihuwar su biyu duk maza. Twins kuwa sosai suka girma ana ta karatu,Mami da Dr Ibrah ma an buɗe babin soyayya zahiri bayan ta ɓoye da aka yi.

A ɓangaren Daddy kuwa tuni na cika mashi gida da ƴan mata har shidda bayan haihuwar ƴan uku na haifi Agaishat mu na kiranta da Ummi sai Twins Nabeela da Nadeera sosai mu ke gudanar da soyayyar mu ni da ƴaƴana da mijina. Har yanzu Daddy na ke kiransa duk da yayi bakin ƙoƙarin sa na ganin ya hana ni, wannan yasa yarana ma suke kiran sa da Daddy.

Ina zaune ina koyar da yarana karatu alƙur'ani Daddy ya shigo,duk suka fara yi mashi sannu da zuwa murmurshi kan fuskata na ke kallon su yadda ya ke rarraba masu abinda ya shigo da shi duk wanda aka ba sai yayi ihu koma gefe ya na murna. Kusa da ni ya ƙaraso bayan ya gama da yaran ya jawo ni jikin sa ya zura min zoben gold da yatsana ya na mai furta "i love You so mush my farin cikin rayuwa"ƙanƙamesa nayi ina mai ɗora hannuna saman ƙirjinsa nace "na gode miji na gari"maganga ya raɗa min a kunne nayi murmushi na saci inda yara suke sai na hankalinsu bai kan mu,hannun shi na ja mu ka fara taka step.....

*ALHAMDULLAH !!!!*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull