Kenza eBookz

Karuwar gida Complete - Chapter 5

Karuwar gida Complete - Chapter 5

Karuwar gida Complete Chapter 5: Karuwar gida Complete Chapter 5. Taimakon gaggawa aka shiga baiwa Daddy aka cire glass ɗin da ya cake shi ga wuya aka naɗe…

4,466 words

Taimakon gaggawa aka shiga baiwa Daddy aka cire glass ɗin da ya cake shi ga wuya aka naɗe gun da bandeji،awani huɗu cur sannan ya farka rumtse ido yayi ganin shi kwance a gadon asibiti a take duk abinda ya faru ya dawo mashi a kai a zuci yace "kenan accident nayi?"

Ya na nan kwance likita ya shigo ya duba shi haɗi da ƙara yi mashi wasu allurai babu jimawa barci ya ɗauke shi,yayinda a cikin barcin ya ke ta mafarkin Mimi.

Ganin Daddy bai dawo ba sam bai tadawa Mami hankali ba,hasali ma Dr Ibrah ta kira suka sha hirar su tamkar wasu masoya.Ba wata hira ba ce sai ta batsa da nunawa junansu sun yi kewar juna nan fah ne Mami ke sanar da shi Daddy bai dawo ba,shiru yayi can yace "kar ace dai shine yayi accident dan ɗazu a wani group na ga an turo wata mota kalar ta shi"da sauri Mami ta dafe ƙirji ko kafin tace wani abu Dr Ibrah ya kashe kiran haɗi da bin didigin ainahin labarin a ƙarshe ya tabbatar da Daddy ne.

Ameera da twins suna falo su na kallo Dr Ibrah ya shigo,cike da ladabi Ameera ta gaishe shi ya amsa tare da cewa "ina Rahman ta ke ?jikin nata da sauƙi?"

"Ta na ɗakin ta kenan ba ta lafiya?"cewar Ameera "eh wlh tun da ta samu labarin baban ku yayi haɗari shikenan ciwonta ya motsa shine na zo na dubata".

Cike da tashin hankali Ameera tace "accident ?yanzu ya na ina?" "Ya na Clinic Hamdallah ungo kuɗin adaidaita sai kuje ke da su Twins ku tsaya can kafin mu zo"Ameera na sharar hawaye ta amshi kuɗin haɗi da jan ƙannanta suka fice .

Murmushi Dr Ibrah yayi ya haura ɗakin Mami ,a zaune ya tarar da ita tayi tagumi hawaye na zuba a kumcinta,wani irin fincikota yayi ta faɗa jikin shi.Halshe ya sa ya na shanye hawayen yace "a kan waccan banza ne kike min asarar hawayen ki?"ta buɗa baki da niyyar magana yayi saurin saka nashi.

Sumba ya ke bata ta fita hankali tuni suka fita hayyacin su ,tamkar wasu ma'aurata haka ya tuɓeta ya fara sex da ita sai ihu suke. Sai da suka yi suka gaji dan kan su kafin su yi wanka,Mami ta shiga kitchen ta samo masu abinci suka ci suka nar kafin su buge da barci.

Da isar Ameera asibiti ba ta wani sha wuya ba suka samu ganin Daddy wanda ke ta sharar barci,har wajen awa biyu da zuwan su amman bai tashi ba. "Ku zauna nan in tafi gida in ɗauko mana abinci kar ku fita ko da bakin ƙofa ne kun ji ko?"cewar Ameera kai suka jinjina mata ita kuwa ta fito bakin hanya ta samu adaidaita.

Cike da mamakin ganin motar Dr Ibrah har yanzu bai bar gidan ba komi?ta shiga ciki. Part ɗin Mami ta nufa har ta ɗora hannunta kan handle ɗin ƙofa sai taji muryar Dr Ibrah ya na cewa "ya ya kika ji kayan aiki ba kamar na mijin ki ba ko?"dariyar duniyanci Mami tayi tace "ai Mu'azam ya fi ka komi kan tsawon kan kauri kawai shi matsalar shi bai san yadda zai sarrafa mace ba ne sannan sai matsalar saurin kawowa"cike da jin haushi Dr Ibrah ɗin yace "kuma kike ihu babu ruwana da munafurci bari ki ga na tashi na tafi wancan mai gadin na ku sai baƙin sa idon tsiya wai fah har da ce min yayi ai mai gidan bai nan,ni kuwa na ƙi kula shi"da sauri Ameera ta bar gun ta shiga kitchen jikinta na karkarwa dan kuwa ita ba yarinya ba ce balle ta ƙi fahimtar inda kalaman Dr Ibrah suka nufa.

Abincin ta zuba haɗi da ɗaukar exotic sannan ta fito,kiciɓus suka yi da su Mami wacce ta rako Dr Ibrah. A ɗan daburce Mami ta kalleta tace "yo ba ki je asibitin ba?"dan dama Dr Ibrah ya gaya mata yadda suka yi,kai Ameera ta girgiza tace "na tafi dawowa nayi ɗaukar abinci" Mami ta ce "toh lafiya kike kuka ko wani abun ne?"kallon mahaifiyarta ta tayi sannan tace "Daddy ne tun zuwan mu bai tashi ba kuma an naɗe mashi wuya"ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka wata ajiyar zuciya Mami ta saki dan ita azaton ta ko tun ɗazu Ameera ta dawo ta ganta ita da Dr Ibrah.

"Allah baku lafiya ga baki ɗaya ke ma ya kamata ki kula da kan ki sosai ni zan wuce"cewar Dr Ibrah,godiya Mami tayi kafin tace "ni zan koma ɗaki na kwanta ki gaishe shi da jiki"bayan Mami Ameera ta bi da kallo kafin ta fita ta na yiwa Mamin addu'ar shirya tare da alƙawarin ita ma sai ta zama *KARUWAR GIDA* ko dan ta ramawa Daddyn ta😳

***Niamey

Mu na sauka babban birnin Niamey na sake kiran wayar Daddy a karo na barkatai wannan karon kuma a kashe najita,cikin sanyin jiki na kira lambar da ya bani yace in mun sauka na neme shi.

Ashe tuni ma ya na cikin gidan EMA,gaishe shi nayi ina mai nuna mashi Hajiya Babba wacce ke ta masifa an ƙi fiddo mata kayan su daga cikin Boot😂kai ya girgiza a zuci yace "su Hajiya Babba manya ashe har yanzu ta na nan dai yadda na santa"ƙarasawa yayi gun ta ya gaishe ta amsawa tayi ta na mai cigaba da mita .

Har mota ya kai su sannan ya dawo ya fara ɗaukar masu kayan da suka raɓe,sai da ya gama sannan ya zagaya ya zauna seat ɗin drever.

A hanya ya ke ɗan jan mu da hira har mu ka kawo gidan da Daddy yasa aka kama mana haya,a gajiye duk mu ka shiga ciki Alhaji Kamal ya fita nemo mana abinci. Ko da ya dawo har mun yi wanka mun canza kaya haɗi da yin Sallah Asar,gasasun kaji ne haɗi da frite ya sawo mana sai lemun kwalba.

Hajiya Babba ta baje sai ci ta ke ni kuwa shiru nayi na koma gefe ina tunanin Daddyna ko lafiya bai ɗaukar kira ita kuwa Mami fushi ni ke da ita dan a mota Hajiya Babba tayi ta faɗa min mugayen halayenta lokacin da suka zauna gida guda haka ba ta tausayin Daddyna.

"Mimi lafiya ?ke ba za ki ci abincin ba?"cewar Alhaji Kamal,Hajiya Babba ta ja baki tace "ta ya za ta ci ta tsaya tunanin Abbanta sai kace wani ɗan yaro duk ta wani damu dan bai kira ba"dariya Alhaji yayi ni kuwa na turo baki gaba cike da jin haushi na nufi ɗakin da mu ka ajiye kaya wanda ya ke ɗauke da matala 3places ta sha shimfiɗa ta alfarma.

A can Maradi kuwa sai wajen sallah magrib ya farka,sannu Ameera ta shiga yi mashi bai amsa ba kawai dai ya sakar mata murmurshi. Likita ta fita ta kira ya zo ya duba shi "gobe zuwa safe in shaa Allah za'a sallame ka bayan ka biya kuɗin da aka yi ma aiki"cewar Dr ɗin ya na kallon Daddy.

"Na gode sosai da kulawa"cewar Daddy, toilet ya nufa yayi wanka haɗi da alwala.Saloli ya shiga yi tun asubah har magrib ya na nan zaune har aka kira isha'i,bayan ya gama ya juyo ya kalli Ameera yace "Ameera samo min exotic"da toh ta miƙe ta fita zuwa frigon asibitin lemun da ta aje ta ɗauko mashi ya karɓa ya yi Bismillah ya sha. Bayan yayi Hamdallah da Ubangiji ya ke tambayarta ya aka yi ta sani?babu abinda da ta ɓoye mashi tun daga zuwan Dr Ibrah maganar da taji su na yi ne da Mami kawai a ba ta gaya mashi ba. Shiru Daddy yayi ya na saurarenta tabbas zargin shi ya zama gaskiya,ta yaya Dr Ibrah zai zo gidan shi bayan duk abinda ya faru tsakanin su?bai ce komi ba sai Twins da ya ƙurawa ido suna sharar barci saboda gajiyar da suka yi.

Washegari tun da safe Dr Ibrah ya sake zowa wai ya zo dubiya ne Amman a zahiri cashe ayar su suke shi da Mami a falo,sai masha'ar su suke. Daddy kuwa sai da aka sa wayar shi da aka ɗauko daga mota caji yayi masu transfer kafin ya nufo gida Ameera na addu'ar Allah ya toni asirin mahaifiyarta. Mai gadi na buɗe gate Daddy ya cinno hancin motar shi cikin gidan.... [28/11 à 06:29] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 25-26*

Cak Ameera ta tsaya ganin Mami kwance Dr Ibrah na ƙoƙarin saka mata ƙarin ruwa a hannu,bungulin hijabin da ta sanya ya fi komi baiwa Ameera mamaki "yaushe Mami ta fara saka hijab?wai ma miye ya ƙara kawo wannan mutumen..."Daddy ne ya katse mata tunani da cewa "Ameera ja daga bakin ƙofa mana kin tare hanya"cikin ɗakin ta ida shigewa yayinda Twins suka danno kai sannan Daddy.

Kawar da kai gefe yayi kai kace bai gan su a falon ba haka ya wuce part ɗin shi,wanka yayi ya shafa da turare mai ƙamshi sannan ya saka kayan shan iska. Ko da ya dawo falo Dr Ibrah ya bar gidan "ashe accident aka yi?"cewar Mami ta na ɓata fuska ita ila doli fushi ta ke har yanzu bai tankata ba sai wayar shi da ya ke latsawa ya na karanta text murmurshi kan fuskar shi ```nayi kewar ka ji na ke kamar nayi tsuntsuwa na dawo```😩 ```Daddyna shine ko ka kula ni babu kira babu saƙo sai kace wacce aka yi kyauta da ita```😰 ```dan Allah kayi min magana da zarar ka kunna waya sannan ka faɗa min dalilin ƙin kula ni har da kashe waya```🥺

Duk text ɗin Mimi ne wasu bai ma samu damar karanta su ba ya danna mata kira,a Shagwaɓe ta ɗaga gami da sallama wata sanyayar ajiyar zuciya Daddy ya sauke jin muryar ta.A zahirin gaskiya tabbas shi ma yayi kewar ta sosai bai taɓa wuni ɗaya bai ji motsinta ba wannan ne karon farko,"Daddyna nayi kewar ka"na faɗa kamar zan yi kuka lumshe ido yayi yace "Mimi da fatan kun sauka lafiya?"da sauri nace "a'a Daddy ni dai tun zuwan mu ban ci komi ba tea ne kawai ni ke sha sai wata ƴar busassar kaza da na ci yanzu"murmurshi mai sauti Daddy yayi wanda har sai da naji shi "kai Mimi kazar ce busassa?to tayi daɗi kuwa?"dariya nayi nace "to ɗan kaɗan dai,wai miyasa ka ƙi nema na koko har ka fara mancewa da ni ?"Daddy yace "wayar ce ta ɓata sai yanzu wanda ya tsinceta ya kawo min"ajiyar zuciya na sauke nace "alhamdullah dama Hajiya Babba tace lafiyar ka lau in bar damuwa da ke ai ba ƙaramin yaro ba n..."dundun da Hajiya Babba ta kai min ne yasa nace "Washhh Daddy😩 Allah wannan tsohuwar so ta ke ta karya maka ni,wani irin duka ta yi min kamar ta bugan guduma" Daddy bai ce komi ba sai ji yayi Hajiya Babba na magana "ni dai ka turon kuɗin mota na koma wannan sangartatar ƴar ta ka ta hana ni shaƙat sai shegen son jiki ba ta moruwa ga ƴar karen sakuwa sai kace autar mata"dariya Daddy yayi yace "ina kwana Hajiya ?"

"Au !ni ke kiɗina ni ke rawata ko?yanzu ina faɗa maka laifin ƴar ka shine kake wani gaishe ni?"ƙeya Daddy ya ɗan sosa yace "afuwan Hajiyar mu kin san halin Mimi sarai ba ta son wahala ne,kuma please kar a cutar min da ita zan turo kuɗi sai a nema maku ƴar aiki" "da dai ya fi"cewar Hajiya Babba ta na mai miƙo min wayar.

"Daddy ina Mami na?"shiru yayi ya kalli gefen da Mami ta ke kwance ta na barci tuni kuma sérum ɗin ya ƙare,tashi yayi ya cire mata haɗi da gyara mata hijab ɗin ta fuskarta ya ɗan tsurawa ido.

Allah ya sani irin son da ya ke yi mata kawai ƴar canzawarta ne bai kwanta mashi a rai ba ga kuma zarginta da ya fara "hello"na faɗa ɗan ƙarfi,lumshe ido yayi yace "umhum!"na turo baki cikin shagwaɓa nace "Daddy shine ka ƙyale ni ?ina Mami?" "Ta na barci"ya bank amsa a takaice,shiru nayi ina tunani dan wannan ba ɗabi'ar Mami ce ba yawan barci a ko wane lokaci ta na ƙoƙarin faranta ran iyalenta shiyasa ta ƙauracewa duk abinda yayi kama da raggonci. "Mimina zan kira ki an jima"ya na gama faɗa ya kashe ya na sauke wani irin numfashi saboda canjin yanayi da ya fara ji,Ameera wacce ta yiwa Twins wanka ta canza masu kaya ta fito tare da cewa "Daddy mi za'a dafawa tunda Mami na kwance?""ki dafa shinkafa dafa duka sai ki gasa kifi"da "toh"ta amsa ta nufi kitchen Daddy kuwa fita yayi izuwa farfajiyar gidan.

***Bayan 2week

Fadila ce zaune tsakiyar gado ta na danna waya da alamu shart suke ita da Nasir sai Shagwaɓa ta ke zuba mashi,shi kuwa bawan Allah bai cikin nutsuwar shi saboda yayi nadamar kusantar ta tunda har ya ga sakamakon yin haka gun ƙanwar sa. A ɓangaren su Iyani kuwa doli ta ɗauki ƙaddara ba tare da tayi yunƙurin zubarwa da Fauziya ciki ba,ita kuwa ba ta so haka ba dan a cewarta abun kunya ne ƴan unguwa su ganta da ciki. Tsangwama kuwa ta na shanta duk in ta gifta Iyani sai ta harareta tamkar idonta za su faɗo,Nabee kuwa ganin ƴar uwarta tayi cikin shege yasa ta ƙara ɗaukar matan tsaro har da zuwa gun wani malami yayi mata laya ta ɗaura ga ƙugu saboda zuwan ɓacin rana kar atai ta samu namijin da zai yi mata ta ƙarfi,amman wannan layar ba za ta taɓa barin namiji kusantar ta ba muddin ta na ga jikinta.

A tsinake ta ke shiryawa cikin wasu fitananun riga da wando wanda suka ɗame mata jiki,wani bungulin hijab ta saka kafin ta rataya bag. "Iyani zan tafi school sai na dawo"ta na gama faɗa ba ta jira cewar Iyanin ba ta fice, adaidaita sahu ta tsayar da ya ɗauke ta ba su zame ko ina ba sai ƙaton compagnie.

Cike da yauƙi ta nufi office ɗin ba tare da neman izini ba ta buɗe ƙofar tare da kutsa kai ciki,da sauri Daddy ya miƙe tsaye ya zagayo sai da ya ƙanƙance ido sannan yace "mi ya ƙara maido ki office ɗina ?"murmurshi tayi tare da cire hijab tace "Washhh Allah na gaji masoyi ka ban ruwan sanyi man"ba ta kai ga ida maganar ba ya ɗauke ta da wani gigitacen mari. Ihu ta buga tare da yin cikin shi za ta rungume shi yayi wani irin taɗe ta sannan yayi ball da ita,wayar rallonge ya ɗauka ya shiga zuba mata Nabee sai kuka ta ke haɗi da ƙoƙarin tashi amman Daddy na mayar da ita ihunta duk ya karaɗe gun.

PA ne ya shigo ya ceceta,da sauri ta saɓi hijabinta da hannu ta ari na kare😹 "Suraj ka dubi tantiriyar yarinyar nan wai ta zo har office ɗina neman ra'ayina kwanakin baya ma ta zo na koreta,ban san inda ta samu lambata ba haka ta ke aiko min hotunan ta da mugunyar shiga.Amman da yake ƴar iska ce shine ta sake dawowa"haƙuri PA ya shiga baiwa Daddy ya na mai cewa "uwannan su ne ɓata gari barin su cikin gari ba ƙaramar illa za su yiwa mutane ba"Daddy yace "shiyasa fah na mayar da Mimi Niamey ka san classe ɗin su ɗaya ban san ko miyasa ta ke bibiya ta ba"PA yace "sir wannan da ka ganta ai ka ga *KARUWAR GIDA* saboda idonta a tsatsaye suke"cike da ɓacin rai Daddy ya rufe office ya nufi hanyar gida.

Tun da ya karyo kwanar ya ke jin zuciyar shi na wani matsiyacin bugawa,da mai gadi ya buɗe mashi get ya shiga yayi parking sai murmurshi mai gadi ya ke wanda Daddy bai san na minene ba.

Wani irin sarawa kan Daddy yayi ya na maimaita kalmar "yi da ƙarfi Dr na yauwa da ƙarfi"numfashin shi ne ya tsaya cak na wuccin gadi kafin ya samu zuciyar shi ta fara halbawa da ƙarfi da ƙarfi. Zaune yayi a falo dafe da zuciya dan ba zai iya ƙarasawa ciki ba,kar ya tai ya ga abinda zai sa zuciyar shi yin bindiga.Ya na nan zaune ya ke jin sautin su tun suna yi da ƙarfi har suka ƙyale,can kamar minti biyar Dr Ibrah ya saɓo Mami zuwa falo babu kaya a jikinsu. Wani irin sakin Mami Dr Ibrah yayi ya ta faɗi timmm lokacin da idon shi suka sauka kan Mu'azam babban aminin shi,"my lovely kan ka ɗaya da za ka sak...."ragowar maganar ce ta tsaya a maƙoshi sakamakon haɗa ido da suka da Daddy ya zuba mata idon shi da suka yi jawur tsabar ɓacin rai.... [29/11 à 15:22] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 27-28*

Tsananin furgice,tashin hankali,rashin zaton faruwar haka ya haifarwa da Mami zubar jini tamkar wacce aka buɗewa pampo kafin wani lokaci tuni lumfashinta ya tsaya cak lokacin da tayi ƙoƙarin tashi tsaye ne juwa ta kayar da ita. Duk tashin hankalin da Daddy ke ciki ganin Mami cikin wannan halin yasa ya mayar da shi gefe ya nufota ya na kiran sunanta da wannan damar Dr Ibrah ya koma ɗaki ya saka kayan shi tare da ficewa daga gidan.

Duk ruwan da Daddy ke malaya mata bai sa ta farfaɗo ba,ɗakinta ya shiga ya ɗauko mata kayan jikinta bayan ya saka mata ya ciciɓeta zuwa asibiti.

An ɗauki lokaci kafin likita ya fito "masha Allah mun yi nasarar daidaita numfashinta sai da kamar wuya cikin jikinta ya tsaya duba da irin shock da attaque ɗin da suka kawo mata farmaki,zuciyarta ma kingin kaɗan ta buga tsabar tsoro"banda ido babu abinda Daddy ya iya sarrafawa su ma likitan ne ya zubawa wasu,sai da zuciyar shi ta dawo daga suman wucen gadi sannan ya fara jujuya maganar likita bisa lizamin hankali a fili yace "ciki?ciki ne da ita?"cikin tausayi Dr yace "kayi haƙuri bawan Allah nima na so ace ya tsaya duba da shekarun da kuka ɗauka ba ku taɓa samun haihuwa ba,nayi mamaki ma sosai yadda ƙwan halittar ka har iya zama a cikin mahaifarta dan kuwa a wancan karon da na auna ku na ga kamar ma impossible ne saboda ƙarfin ƙwayar hallitar ka amman duba da lamarin na Allah ne shiyasa ban yi décourager ɗin ku ba"

Idon Daddy ne suka rikiɗa suka jawur kamar garwashin wuta,shi sam ya ma manta da ya taɓa zuwa wannan asibitin tun shekarun baya da suka wuce to wai mi ma ke faruwa?

Cikin ruɗani yace "Dr wannan shine ciki na wajen huɗu da ta samu amman uwancan duk da ta haife su"ido Dr ya zaro yace "kuma da kai?"kallon ban gane ba Daddy yayi masjid sai yayi saurin cewa "ina nufin kuma kai ne uban cikin na gaske?"

"Daram!dam!dimmm"haka zuciyar Daddy ta buga,yayinda yawun bakin shi suka kafe ƙwaƙwalwar shi ta daina tunani kafin wani lokaci zuciyar shi ta tsaya cak samakon hasaso abinda ya ke fatan ko a mafarki ne ba zai so ace hakan ta faru ba.

*Wasu shekarun baya da suka shuɗe...*

CEG3 makaranta ce da ke jamhuriyar Niger a garin Maradi,makarantar ta kasance ta ɗaya fannin ƙoƙari da hazaƙa a duk makarantun gwamnati da ke Maradi. Ɗalibai ne zaune matasa ƴan 4em duk kowanensu sanye ya ke da uniforme,a tsarin classe ɗin 4em mafi akasari matasa ne sabbin balaga saboda a ƙiyasi ƴan 13 zuwa 15years ne. Gungun students kawai kake gani kowa da abinda ya dame shi,wasu na cin abinci wasu na danna wayar hannu yayinda wasu ke hira.

"Yauwa yanzu abinda za'a yi kowa ya zo ya faɗa mana ra'ayinsa idan ya girma aikin mi zai yi"cewar wani ɗan matashin yaro mai suna Hafiz,nan fah kowa ya shiga faɗin ra'ayinsa haɗi da hujja wasu sun zaɓi koyarwa,wasu aikin soja,masu son kuɗi sun zaɓi aikin ɗan sanda dan karɓar cin hanci.

Hafiz ya dubi Mu'azam yace "ku biyu ya rage ku faɗi ra'ayin ku kai mi kake son zama?"murmurshi Mu'azam yayi yace "ina son na zama ɗan kasuwa nayi kuɗi na gina manyan gidaje,na sayi motoci dayawa ta yadda zan auri mata huɗu tsalatsala masu kyau "dukansu dariya suka yi dan kuwa kusan kowa ya san yadda Mu'azam ke son yin aure tun da ƙananun shekarunsa saboda ya na da yawan sha'awa. Ibrahim shine kawai bai faɗi ra'ayinsa ba hakan yasa yace "ku tsaya-ku tsaya dariyar ta isa haka nan a bari na faɗi nawa nima"duk ƙyalewa suka yi suka zuba mashi ido.

Sai da ya gyara zama sannan yace "ni kuma likitan mata ni ke son zama,saboda na rinƙa kallon mata yadda ni ke so in yau na ga baƙa gobe fara zan gani daga nan nima sai nayi profiter eh yane"ihu suka kwashe da shi wasu na sake zuzuta shi yayinda Mu'azam ya kai mashi dukan wasa dan sun fi kusa duk a cikin délégation ɗin.

"Ɗan iska in mutane suka gane ai sai a kore ka"cewar Mu'azam, Ibrahim yayi dariya yace "ai shi Dr Ibrah ya na da ilimi da wayo ba zai yi yadda za'a gano shi ba ƴan ƙauye kawai zan rinƙa eh yane" Mu'azam yace "ku na ji fah wai Dr Ibrah hhh shi har ya ga ya zama likitan hhh"nan aka shiga yiwa Ibrahim dariya ana ce mashi Dr Ibrah ashe wannan abu yayi mashi ciwo sai ya ga kamar da gayya Mu'azam ɗin yasa yin haka collègues sun dare shi.

Cikin fushi ya miƙe ya fice ya bar class ɗin,da sauri Mu'azam ya bi bayansa ya na kiran sunan shi amman ya ƙi ko da juyowa ne balle ya tsaya.Da gudu ya sha gaban shi tunkuɗe shi Ibrahim yayi ya wuce ya bar Mu'azam da mamaki.

Washegari da suka dawo école sai students suke kiran Ibrahim da Dr Ibrah to fah shikenan sunan ya bi shi tun ya na faɗa da jin haushi har ya haƙura amman har yanzu ba su shirya da Mu'azam ba.

A gajiye ya shiga gidan ya na dab da shiga ɗakin shi ya ji muryar Hajiya Babba na cewa "yau kuma lafiya na ga sai ɓata fuska kake kuma ko gaishe ni ba za'a yi ba?"ƙeya ya ɗan sosa yace "a gajiye ni ke wlh ina sauri naje na kwanta ne"cewar Mu'azam Hajiya Babba ba ta ce komi ba sai kayan Munawara da ta ke kwashewa kan igiyar shanya.

Mu'azam na shiga ɗaki ya haye ƴar sofar shi,tunanin canzawar Ibrahim ya ke son yi tare da nemo mafita amman abu ya sauya salo sakamakon ƙugi da marar shi ta ke. Dafe marar yayi ya furta "ya Allah!"a zuci kuwa cewa ya ke "ƙila wannan shine silar mutuwata ta yaya zan jure wannan muguwar sha'awar a ƴan ƙanƙanan shekaruna?banda kuɗi balle in ce zan yi aure,to wace ce ma za ta aure ni ?"huci ya furzar tare yunƙurawa ya tashi.

Dala biyar ya lalabo a aljihu tare da fita waje ya leƙa ya aiki wani yaro ya sawo mashi ƙanƙara,yaron na miƙo mashi ya buga ƙanƙarar ga bango sannan ya shige ɗaki. Cikin wani ƙyale ya saka ƙanƙarar ya fara dannawa ga mararsa,a hankali ya ke fitar da numfashin wahala a sannu ciwon ya ke ragewa can barci ya ɗauke shi.

Sai wuraren ƙarfe biyun rana ya farka wandon shi duk ya ɓace da sperm saboda mafarkin da yayi,bokiti ya cika ya je yayi wankan tsarki haɗi da yin na sabulu a ƙarshe ya wanke wandon.

Doguwar riga ya saka ya fito daga banɗaki,alwala ya ɗaura kafin ya wuce masallaci. Ya na dawowa ya tarar da Munawara zaune a ɗakin shi ta na jiran sa,cikin sangarta tace "ya Mu'az tun ɗazu ni ke jiran ka kazo mu ci abinci"bai ce komi ba ya zauna haɗi da buɗe abincin da ta kawo masu. Bismillah yayi ya fara ci ita ma sai ta saka hannunta,"Ya Mu'az albishirin ka"ɗagowa yayi kalleta ganin sai murmurshi ta ke zubawa "ya aka yi ne?"sai da ta ɓoye fuskarta tace "dama ɗan gidan Alhaji Abubakar ne yace ya na sona zai aure ni sai mu tafi Makka "shiru yayi ya na kallonta yarinyar duka ba za ta wuce 12year ba amman murna ta ke za ta yi aure.

"Yaushe ya gaya maki haka?kuma kin tabbata dagaske ya ke?"cewar Mu'azam kafin Munawara tayi magana suka jiyo muryar Alhaji Abubakar da sauri Mu'azam ya fita ya na amsa sallamar saboda duk unguwar Alhaji Abubakar ya fi su kuɗi sannan mutumen kirki ne tun rasuwar mahaifin su shi ya ke aiko masu da abinci duk wata.

Cikin girmamawa ya gaishe shi haɗi da yi mashi iso gun Hajiya Babba,har Mu'azam zai fita Alhaji yace "dawo ka zauna yaron kirki "zaunawa Mu'azam yayi.

Nan Alhaji yayi gyaran murya tare da gaya masu abinda ya ke tafe da shi dangane da auren Munawara da yaron wajen shi Kamal ke so, Hajiya Babba tayi murmurshi tace "ai Alhaji duk ƴaƴan ka ne duk yadda kayi daidai ne,ko yau kace za'a ɗaura ni ban ga wata matsala ba tunda da kai da kaya duk mallakar wuya ne".

Sosai Alhaji yayi godiya ya dubi Mu'azam yace "ya karatun har yanzu ka na nan kan bakar ka na son karantar business ko yaya ?"kai Mu'azam ya ɗaga yace "eh in shaa Allah" "ok babu matsala gobe ka zo ka same ni tun da ba'a makaranta sai mu tattauna ka ga za ka iya farawa tun yanzu ta yadda a gaba ba za ka ji wahalar shi ba"godiya Mu'azam yayi.

***Bayan 1week

Hajiya Babba ta gayyato dangin mahaifin su Mu'azam suka tarbi lefen Munawara,dukan su sun yaba inda kuma a nan take aka ɗaura aure biki kuma sai zuwa gaba. Ɓangaren Mu'azam kuwa tuni ya fara kasuwanci wanda Alhaji ya ɗora shi a kai,a kullum in ya taso daga school shago ya ke wucewa yayinda kuma weekend ya ke zuwa da safe tuni cikin ƙanƙanan lokaci Mu'azam ya fara canzawa yayinda shagon da Alhaji ya bashi ya ƙara bunƙasa.

Ganin Mu'azam ya sayi babur shine yasa Ibrahim saukowa daga dokin gaba,nan fah suka shirya inda a kullum Mu'azam sai ya je gidan su Ibrahim ɗaukar shi sannan su wuce school.

Tafe ta ke ta na yauƙi irin na ƴan matan zamani sai wani karairaya take ta na juya ƙugu,cak Mu'azam ya tsaya daga tuƙin da ya ke ya ƙura mata ido ta miror har ta kawo daf da su.

"Am ƴan mata sannu"ya samu bakin shi da furtawa,tsayawa Rahama tayi tare da dafe ƙugu tayi wani fari da ido wanda ya sa zuciyar Mu'azam da gangar jikinsa amsawa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull