Karuwar gida Complete - Chapter 6
Karuwar gida Complete Chapter 6: Karuwar gida Complete Chapter 6. "Ka tsayar da ni malam ina sauri ne"ta faɗa cikin dadaɗar murya wacce Mu'azam yaji duk…
4,470 words
"Ka tsayar da ni malam ina sauri ne"ta faɗa cikin dadaɗar murya wacce Mu'azam yaji duk duniya babu muryar da ta kai ta ta daɗi "dan Allah in ba za ki damu ba ina son ki ban lambar wayar ki"wani kallo tayi mashi irin na tara saura kwabo.
Dr Ibrah yace "please ƴan mata ki taimakawa abokina mana ganin ki kawai ya sa duk ya fita hayyacin shi,in kin ƙi ba shi ƙila ya some min nan"ya ida maganar cikin raha wanda hakan yasa ta yin murmushi haɗi da zayyano mashi numberta.
"Sunan jaruma?"cewar Mu'azam "Rahamatullah"ta bashi amsa..... [02/12 à 12:29] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*29-30*
Tunda Mu'azam ya gamu da Rahma ya ɗauki son duniya ya ɗora mata,gabaɗaya hankalin shi na kanta komi ya samu Rahma dai tsabar son da ya ke yi mata ya sa duk wani abu da ya shafi harafi mai *R* ya ke son shi.
Tuni sunanta ya je gun Hajiya Babba babu kunya haka zai zauna yayi ta bata labarin Rahama,Munawara kuwa kullum cikin tsokanar shi ta ke ta kan ce duk ranar da Rahama tace ba ta son shi daga ranar gidan mahaukata za su kai shi.
Ɓangaren Rahama kuwa ba wani sosai ta ke son Mu'azam ba dan ita tafi son namiji kalar fatar ta wato fari,sai irin yadda ya ke yi mata hidima yasa ta bashi wani gurbi a zuciyar ta .
Cikin masifa Ishalle ta ɗaga labulen ɗakin tace "ke Rahamu uwar mi kike yi da har yanzu ba ki fito ba?ko ba ki ji tun ɗazu aka aiko Mu'azu na waje ya na kiran ki ba?"
"Kimtsawa ne ni ke yi tashina daga barci kenan,amman tsabar jaraba har ya ƙumo sammako ya zo mtsw"ta ja tsaki "to zauna nan dan ubanki garin kallon ruwa kwaɗo yayi maki ƙafa kaf samarin ki akwai tamkar shi?ina ce katifar da ta ke sa ki ranar barci shi ya saya maki ita ko?"Rahama ta turo baki tace "kai anty abun kuma har da gori dan ya saya min katifa?"tsuki Ishalle tayi ta saki labulen direct ƙofar gida ta leƙa ta cewa Mu'azam "Bismillah shigo mana ka tsaya waje kamar wani baƙo"kai Mu'azam ya sosa yace "antyn mu ina kwana?"tace "lafiya lau wuce mana ta na cikin ɗaki"babu muso Mu'azam ya nufi ɗakin Rahama.
Ta na ƙoƙarin saka riga ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,da sauri Rahama ta wawuri hijab ta saka a birkice ma ya ke. Murmushi Mu'azam yayi ya na kokowa da numfashin shi saboda rabin breast ɗin ta da ya gani ta sama farar bra ɗin jikin ta.
Cikin masifa tace "Mu'az miye haka sabida Allah in fah ka tarar da ni ciki mugun hali?amman ai ka ma riga ka gani"ta faɗa ta na turo baki haɗi da juya mashi baya.
"Kiyi haƙuri babyna anty tace na shigo ai"ya faɗa cikin kalar tausayi,"shine dan tace ka shigo sai ka biye mata ko?"ta faɗa tare da juyowa ta watsa mashi harara.
Murmushi yayi yace "baby ni kike harare kuma?" Ta bashi amsa da "eh ɗin ai kai ne minene na zowa tun da safe ?"
"Baby sabuwar waya na saya maki shiyasa nace bari na biyo na kawo maki tun jiya na saye ta amman nace bari har na gani in ba ta dawata matsala sai na kawo maki"Mu'azam ya faɗa tare da miƙo mata waya sabuwa dal a kwali.
Har ƙasan zuciyar ta taji daɗin haka sai dai ta ƙi nunawa a fuska sai ma kumbure-kumbure da ta ke yi,cikin rashin jin daɗin sauyin na ta yace "dan Allah baby kiyi haƙuri Allah ba zan sake ba,karɓi ki duba ki gani Allah sa za ta burge ki"ya ida maganar da ɗan murmurshi.
Karɓa tayi ta fiddo ta,tecno ce Spark 5,tsabar daɗi ba ta san lokacin da murmurshi ya suɓuce mata ba. Mu'azam kuwa bawan Allah wata irin ajiyar zuciya ya sauke ganin murmurshi kan fuskar Rahama.
Tsayawa tayi ta na kallon shi "mi kake ma murmurshi?"amsa ya bata "saboda ganin ki cikin walwala"wani tausayin shi ne ta ji yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da ɗan ƙarfi "tabbas Mu'azam shine masoyin gaskiya"ta faɗa a zuci idonta na cika da ƙwalla.
"Ina son ka Mu'az"ta faɗa hawaye na zubowa a kumcinta,wani girrrr ya ji haɗi da yarrr a take kuma tsikar jikinsa ta miƙe yau ne karon farko da ta taɓa faɗa mashi kalmar so.
Shi ma bai san lokacin da hawayen suka zubo mashi ba,ya duƙa yayi sujada shukur ita kuwa dariyar shi ta shiga yi ganin yadda ya ke ta yiwa Allah godiya da ya gwada mashi wannan rana.
Ishalle da ke bakin ƙofa laɓe duk ta na jin komi ta murmursa ta na mai barin gun,sallama Mu'azam yayi mata ya wuce shago.
Ya na zuwa ya tarar da Dr Ibrah zaune shi da wani yaron da suke gudanar da sana'ar tare "sai yanzu ka tawo?"cewar Ibrah ya na mai kallon Mu'azam wanda ke tangale babur.
"Eh wlh ka ga na daɗe ko?gidan su baby na biya ya ne da fatan ka tashi lafiya?"cewar Mu'azam ya na mai baiwa Ibrah hannu wanda yayi kicin-kicin da fuska jin ya ambaci sunan Rahama.
"Lafiya kake wani cin magani?"Mu'azam ya tambaye shi "ban sani ba,kai shikenan wannan yarinyar ta maida ka ɗan ƙaramin mahaukaci komi Rahama sai kace wata autar mata mtws ni ban ga ma abinda ka gani a jikin ta ba da har kake rawar jiki a kanta"Ibrah ke magana cikin tsantsar fushi da kishi.
"To ni dai ina son ta a haka kai ma ya kamata ka so duk abinda ni ke so"Mu'azam ya faɗa cikin rashin jin daɗin abinda abokin nashi ya faɗa a kan Rahama.
Baki Ibrah ya taɓe yace "can ku ƙarata kai da kaji za ka iya,ni tsohuwar wayar ka na zo karɓa tun da jiya ka sayi sabuwa" sosai ƙeya Mu'azam yayi yace "ai Rahama na saya ma ita shiyasa ma ka ga na daɗe ban zo shago ba can na tafi na kai mata"waro ido Ibrah yayi yace "la'ilah illallah wayar 95.000f ɗin ce ka baiwa wata ƙatuwar banza Mu'azam kan ka ɗaya kuw..."hannu ya ɗaga mashi yace "Ibrah ya isa haka kar ka ƙara cewa Rahama ƙatuwa saboda duk fafutuka da neman ni ke yi domin ita ni ke yin su dan haka zan iya mallakawa Rahama duk abinda na mallaka"cike da fushi Ibrah ya bar gun.
Wunin ranar haka Mu'azam yayi shi a jagule dan sosai ya ke son abokinsa amman ko kaɗan bai kamo ƙafar Rahama ba, murmurshi yayi tuna manyan breast ɗin ta yammm haka jikinsa yayi tare da jin son yin aure ya taso mashi.
Sai marice ya koma gida inda ya tarar ana ta shirye-shiryen bikin Munawara wanda ya rage kwana biyu kacal,ɗakin shi ya buɗe ya aje kayan da ya shigo sannan ya shiga banɗaki yayi wanka. A tsanake ya ke shirinsa inda ya saka wasu fararen kaya uwanda suka yi masifar karɓar sa,in ka ga Mu'azam za ka ɗauka ya kai 25years. Turare ya saka ya buɗe ledar da ya shigo ita ya fitar da na shi sannan ya ƙulle,ya na ƙoƙarin fita yaji muryar Hajiya Babba "ina zuwa kuma yanzu daga shigowar ka,?"waigowa yayi ya gaishe ta sannan yace "zan kaiwa Rahama kayan shigar biki ne"Hajiya Babba ba tace komi ba.
***GIDAN ALHAJI
"Alhaji aure-auren nan ya isa haka,yawan auren nan ba shi zai sa ka samu abinda Allah bai nufa za ka samu ba"wata ƴar datijuwa ke faɗar haka yayinda shi kuma Alhajin da ta ke yiwa magana ya rabka uban tagumi. Can ya ɗago ya dube ta yace "ki bar wannan zancen dan tuni an ɗaura yanzu haka yau bayan sallah isha'i amarya za ta shigo"ya na gama faɗar haka ya miƙe tsaye ya fito babban falo yayinda Hajiya ke take masa baya.
Samari ne a ƙalla sun kai ashirin da wani abu,duk rusunawa su ka yi su na gaishe da mahaifinsu bai amsa ba sai da ya zauna kan wata farar kujera wacce ta banbanta da ta cikin falon sannan yace "lafiya lau na ke,na sa an tara ku ne a nan dan na shaida maku yau za'a kawo sabuwar tantin ku ina son ku buɗe kunnuwan ku da kyau duk wanda yayi mata rashin kunya akan auren uwar sa"duk sunne kai suka yi Ma'aruf wanda shine babban su kuma ba zai wuce 34years ba yace "auren kuma again?ina roƙon Allah ya sa alkhairi ya sa kuma wannan shine na ƙarshe ya cika ma burin ka"murmurshi kan fuskar Alhaji yace "amen ɗan arziki"Hajiya kuwa ji tayi kamar taje ta maƙure Ɗan na ta dan kuwa kaf cikin yaran shi kawai ke son abinda Alhaji ke so.
Dare na yi kuwa ƴan kan amarya suka zo tun daga Agadez suka kawota,yarinya ce sharaf ƴar duma-duma mai jini a jiki kallo ɗaya za ka yi mata ka san taji Addini duba da yanayin shigarta ba irin yadda amaren zamani suke caɓa kwalliya ba,a goshinta kuma ƙaton tabo ne baƙi ƙirin na sallah.
Alhaji cike da zumuɗi ya gabatar da duk abinda Shari'a ta gindiya tambayoyin da yayi mata na hukunce-hukuncen sallah da sauran su ras ta bashi amsar su. A slow ya dinga binta har ya mayar da ita cikakkar mace,azaba kam ta sha ta, Alhaji da kan shi ya gasa ta ita kuma sai noƙewa ta ke yi....
**
Cike da murna Rahama ke buɗa kayan da Mu'azam ya kawo mata har kala uku,farar shadda ta shigar safe, lèche na shigar rana sai lafaya ta kan amarya. Ishalle sai yaba kayan ta ke can tace "ya kamata azo kuma ayi bikin ku kafin ƴan baƙin ciki su kutso kai,kawai ki ce mashi ya turo magabatan shi"dariya Rahama tayi tace "toh ai sai gobe ne zai gabatar da Ni ga danginsa sannan kuma ai sai mun tafi ƙauye ya gaido su Inna"(Ishalle ba ta haihuwa shiyasa ta ɗauko ƙanwarta Rahama daga ƙauye wajen iyayenta,kishiyarta ɗaya sai dai ba gida guda suke ba wannan kenan)
Ranar biki Rahama ta tsantsara ado suka tafi ita da Ishalle,sosai kuwa suka samu tarba mai kyau gun Hajiya Babba sai nan-nan ta ke yi da su. Dangin Abban su ma sosai suka yaba da Rahama ita kuwa sai sunne kai ta ke,Gift ɗin da ta kawowa Munawara sai kowa yayi san Barka dan kuwa sai da ta danne zuciyar ta tayi mata sayayya irin ta amare.
Da dadare a ka kai amarya gidan surukanta wanda ya ke nan cikin unguwa,Mu'azam kuwa sosai ya ke murna dan kawu Tanimi yace in shaa Allah shi ma in ya shirya za su je nema masa auren Rahama..... [03/12 à 09:18] Cham~rose💞: *KARUWAR GIDA*
*LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Après chaque prière*
(1)أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ(2)اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ، وَمِنْكَ السَّلَامُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالإِكْرَامِ
Je demande pardon à Allah [trois fois]. Ô Seigneur ! Tu es la Paix et la paix vient de Toi. Béni sois-Tu, ô Digne de glorification et de munificence. »
Muslim 1/414.
*JUMMA'A MUBARAK MES FANS*🕌
*PAGE 31-32*
Cikin ikon Allah an kai lefe gidan su Rahamatullah bayan Mu'azam ya je har ƙauyen su ya gaishe da iyayen ta. Ba wani saka dogon lokaci ba wata biyu ne kacal,tuni Mu'azam ya fara shirye-shirye ɗakin Hajiya Babba aka gyara wanda ya ke cikin da falo ita kuma ta koma ɗakin shi mai ciki ɗaya.
Abotar su Mu'azam kuwa ta ɗan rage ƙarfi shi da Ibrah duk da sun shirya amman tuni ya gane da Ibrah ya na hassadar shi ne da ƙyashin abun hannun shi. Munawara babu yadda ba ta yi da Kamal su tsaya har ayi bikin Mu'azam ba amman ya ƙiya a ƙarshe da ya ga za ta kawo mashi cikas yayi mata gami da Hajiya Babba ita kuwa ta shiga yi mata faɗa a ƙarshe ta ɗirka mata ɗan karan duka da ciwon jiki da birdin tsamanga Munawara ta isa Saudiyya tare da ƙudirin ita da zuwa Niger sai kuwa in gawarta za'a kawo tunda ba ƙaunarta Hajiya Babba ke yi ba😆
***Bayan wata biyu
Tuni su Rahama an zama amare,zalama gun Mu'azam kuwa ba'a magana ɗaya rana sai ya nemeta fiye da biyar tun ta na kuka har ta saba sai ya zamana har ta fi mai kora shafawa dan wani sa'in ya na shago za ta kiran shi ta aza mashi kuka sai ya dawo gida ya yi mata abun😆
Cikin zumɓurar baki Rahama ta shiga tuƙa tuwon ta na gunguni tare da zagin Hajiya Babba ƙasa-ƙasa ita da ta sa a yi tuwon laushi,cikin yanayin rashin jin daɗin rashin kunyar da Rahama ta tsiro Hajiya Babba ta dube ta tace "Rahamu yanzu haka ake tuƙa tuwo garin ku?duk kin bi kin ɓata madafa da gari kuma tuwon ki na ganin ya na ƙulalai shine kike zuba gari dayawa?to bani in yi kaya na tun farko sai da nace ku yi girkin ku in yi nawa"
Miƙewa Rahama tayi ta baiwa Hajiya Babba wuri,bakin pampo taje ta wanke hannunta ta shige ɗaki zaunawa tayi ta kalli baƙuwarta wato ƙawarta Rahama mai irin sunanta tace "wlh na gaji waccan baƙar tsohuwar ta sa ni yi mata ƙaddararen tuwo kiji fah da rana tsaka a saka ni girgizar jiki" "Innalillahi yanzu takwara uwar mijin ta ki ce tsohuwar banza?"to kiyi saurin tuba ga Allah domin duk wacce ta haifa maka miji ta gama maka komi a duniya "wani uban tsuki ta ja tace "dallah kar ki kawo min ƙabli da ba'adi ke a ko ina sai kin nuna ke ustaziya ce tai can ki zauna ke uwar mijin na ki tayi ta juya ki,shi kuma mijin ki riƙa goya shi iyakar biyayya wai na ga kwanaki har wani duƙawa kike dan za ki miƙa mashi makuli mota kawai salon ya raina ki"
Ita dai ba ta ce komi ba dan ta riga da ta san namsake ɗinta babu abinda ta saka a gaba sai duniya,sallama tayi mata ta yi tafiyarta.
Dare nayi Mu'azam ya dawo,kunkume fuska Rahama tayi shi kuwa bawan Allah duk ya susuce ya shiga tambayarta lafiya buɗar bakinta sai cewa tayi "ai Hajiyar ka ce ta zage ni wai ƴar ƙauye ban iya girki ba,kuma fah ina tsaka da girki ta karɓe wai ai Ɗanta ya yo cefanen shiyasa ma ban yi girkin dare ba kuma ni yanzu yunwa ni ke ji"
Shiru Mu'azam yayi ya na ta juya zancen can dai yace "ina zuwa"ya faɗa tare da fita ya ja babur. Gasasun kaji da frite ya sawo,sai da ya kaiwa Hajiya Babba na ta sannan ya wuce part ɗin su. Cike da murna Rahama ta fara cin kajin a zuci kuma ta na kitsa yadda za'a yi ta haɗa tugun da zai sa su bar gidan.
***2years later
Arzikin Mu'azam ya buƙansa sosai dan har yayi na shi jarin yanzu kan ƙafafun shi ya ke tsaye daram,matsalar shi ɗaya ita ce rigimar Rahama kullum da sabuwar fitinar da ta ke kawo mashi yanzu ita kuma Hajiya Babba ta matsa doli sai ya ƙara aure saboda har yanzu Rahama ko ɓatan wata ba tayi ba.
Ɓangaren karatu kuma BEPC kawai Mu'azam ya ke da daga nan kuma ya tattara su ya maida gefe,yayinda Ibrah tuni ya fara karantar karatun likitanci yanzu haka ya na cikin shekara ta biyu.
Kuka Rahama ke yi wiwi kamar ranta zai fita jin wai kishiya za a yi mata,cikin ɗaukar shawarar da takwararta ta bata ta dubi Mu'azam tace "kafin kayi auren sai ka shirya mu fara zuwa asibiti tukunna a san daga ina ne matsalar ta ke"bai wani damu ba ya amince.
Da zuwan su aka gwada su likita ya tabbatar da duka lafiyar su lau matsala ɗaya ce shine kamar ƙwan haihuwar Mu'azam ya fi ƙarfin ƙwan hallitar Rahama maimakon in sun gamu suyi fécondé sai ya ƙona shi.Cikin dubaru na likitoci ya shiga kwantar masu da hankali sannan yace su dage da addu'a duk da su na da 1% na chance amman lamarin Allah sai shi.
Wannan batu sam bai kwantawa Hajiya Babba ba hakan yasa ta fara neman masu maganin gargajiya a ƙarshe dai sai ta gayyato wani malami kwanan shi bakwai a gidan su ya na aikin shi. Jungum suka yi suna sauraren malam wanda ya ke ta yin murmushi can yace "tabbas akwai arzikin ƴaƴa amman da alamu duk mata sannan hakan za ta faru ne in kun dage da roƙon Allah ku yawaita yin saraka sannan mabuɗin arzikin ku shine ɗaukar Maraya ku ingata rayuwar shi"
"Maraya?ina za mu samu Maraya kuma malam?"cewar Mu'azam "gidan marayu za ku je ku yi adopter ɗin sabuwar haihuwa saboda ita ɗin haske ce tamkar tauraruwa yayin ɗaukar ta za ta canyara kuka ne tamkar lokacin ne aka fiddota daga cikin cikin mahaifiyar ta"malam ya faɗa ya na murmurshi "malam kuma doli sai mace?"Mu'azam ya faɗa dan ya fara ganin abun kamar an kaucewa hanya.
Tsawa Hajiya Babba ta daka mashi tace "ka fi shi sanin aikin shi ne?" Malam yace "istakhara nayi in kuma ka na so kai ma za ka iya yi,tabbas a mafarkina mace na gani haske ya luluɓeta"
Da sauri Mu'azam yace "malam bani karatun istahara ɗin"
Malam yace to ga addu'ar kamar haka: اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيـرُكَ بِعِلْمَكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الَأمْرَ (وَيُسَمِّي حَاجَتَه) خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ
Godiya Mu'azam yayi sannan Hajiya Babba ta sallami malam. Dare na yi Mu'azam yayi raka'a biyu sannan ya karanto addu'a da malam ya bashi yayi tawasli da Allah tare da miƙa dukan yarda shi.
***GIDAN ALHAJI
Dr Ma'aruf ne sanye da kayan likitoci,idon shi manne da farin glass hankali tashe ya shigo gidan. Kallon Abban nasa yayi yace "Abba doli sai an tafi asibiti ka yarda da ni dan Allah wlh ba za'a samu matsalar komi ba"cikin yarda da Ɗan na shi ya tallabo Agaishat wacce ta jigata saboda zafin naƙuda mota ya sakata tare da ɗaukar kayan haihuwa suka wuce asibiti.
Allurar naƙuda Dr Ma'aruf yayi mata sai addu'a ya ke yi Allah sa matan biyu su haifu lokaci ɗaya,waccan ɗayar ta fara nishi da sauri ya tafi ya karɓi haihuwar ta cikin ikon Allah ko minti biyu ba'a yi Agaishat ma ta haihu. Bisa gado ya ɗora jariran wanda suka kasance duk mata ne,sai da ya rumtse ido sosai sannan yayi masaye wato ya canza su ya baiwa Agaishat ƴar wacan matar ita kuma ya bata ta Agaishat.
Cike da murna Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin ya na mata huɗuba,tuni kuwa alhalin shi suka cika asibitin amman ƙememe ya hana kowa ya taɓa yarinyar.
A hankali Dr Ma'aruf ke shafa kan ƴar ƙanwar ta sa lokacin da Marâtre uwar marayun ta karɓe ta daga hannun shi "a kula da ita sosai ita ɗin marainiya ce mahaifiyata ta mutu wajen haihuwar ta sannan dama ta ce ko ta haife ta jefar da ita za tayi saboda ba ta hanyar aure aka haife ta ba"Dr Ma'aruf ke faɗar haka kafin ya tafi ya na jin son yarinyar cikin ɓargon zuciyar shi.
***
Cike da murna Rahama ta shirya saboda mafarkin da Mu'azam yace yayi,cikin ƴar ƙaramar motar shi suka shiga su dukan su har da Hajiya Babba ba su zarce ko ina ba sai gidan marayu.
Babu ɓata lokaci shugan gidan marayun ya kai su ɗakin da ake aje sabin haihuwa,marâtre ita ta rinƙa ɗauko jariran ta na miƙawa Mu'azam da ɗaya-ɗaya duk in an bashi sai ya aje. "Inyaaa !inyaaa"haka jaririyar ke cancara kuka murmurshi dukansu ukun suka yi Mu'azam yace "alhamdullah na ɗauki wannan"marâtre tayi murmurshi tace "Allah sarki ko minti goma ba'a yi ba da wani likita ya kawo mana ita mahaifiyar yarinya rasuwa tayi"nan da suka cika takardu komi da komi Mu'azam yayi mata huɗuba ya juyo ya kalli Hajiya Babba yace "wane suna za'a saka mata?" "Fadimatu"ta bashi amsa ta na murmurshi shi ma murmurshin yayi yace "takwara kika yiwa kan ki kenan?to ni kuma zan rinƙa kiranta da *Mimi*".....
```JUMMA'A RANAR HUTUNA CE BAN POSTING``` [04/12 à 14:10] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 33-34*
Kiran Dr Ma'aruf marâtre tayi kamar yadda ya buƙata cewa duk ranar da aka samu wanda zai ɗaukar jaririyar ayi mashi magana. Babu ɓata lokaci kuwa ya zo adresse ɗin Mu'azam ya karɓa sannan ya bi su har gidan su ya ga muhallin su kafin ya koma. Wanka Hajiya Babba ta yiwa takwarar ta na ruwan zafi sai kuka ta ke canyarawa,mai ta shafa mata ta saka mata kaya masu kyau cikin wanda Mu'azam ya sawo mata.
Karɓar ta Rahama tayi ta shiga bata madara cikin biberon ai kuwa ta fara sha, Mu'azam ya shigo cike da murna yace "Hajiya Babba albishirin ki?"tace "goro"takardun gida ya ajiye a gabanta sannan ya zauna bisa tabarmar ya tanƙwashe ƙafafun shi yace "Dr nan ne ya bani kyautar gida mai kyau ɗan madaidaici sannan kuma har da kaya ya zuba cikin su,babban abun farin ciki da ya tambaye ni nayi karatu ko yaya ne nace mashi eh kawai sai ya bani shuwagabancin compagnie ɗin shi yanzu haka gobe zan fara aiki"wata irin buɗa Hajiya Babba tayi tace "madallah dama malam yace ita ɗin rahama ce gare mu ga shi kuwa tun ba'a yi nisa ba mun fara samun canjin ratuwa,kai masha Allah bari mu tashi mu fara shirin komawa can in ya so nan ɗin sai mu saka ƴan haya"ta na gama faɗar haka ta miƙe tare da shigewa ɗaki ta fara haɗa kayanta😹
Mu'azam ya kalli Rahama yace "ya na ga ba kya farin ciki?"murmurshin ƙarfin hali tayi dan ita sam ba ta so Hajiya Babba ta bi su can sabon gida🙄 Kwanci ta gyarawa Mimi sannan tace "ai abun murna ne sosai ga Ɗiyar nan sai kace kai ka haifeta dan har kama kuke yi"hannu ya sa ya ɗauki Mimi yace "kai haba bari na gani"Rahama tace "Allah kuwa kawai dai dan ta fi ka hasken fata ne"murmurshi yayi yace "farin mahaifiyarta ne tayi,kin ga an raba biyu ni na ɗau kama ke kuma kin ɗau farin fata"
Ranar nan su Mu'azam ba su kwana a ko ina ba sai a sabon gidan da Dr Ma'aruf ya basu wanda ke ADS can wajen masallacin jingile,Hajiya Babba sai zaga gida ta ke ta na kwararawa Dr Ma'aruf albarka.
***GIDAN ALHAJI
Cike da murnar yau Allah ya azurta shi da samun ƙaruwa ta Ƴa mace ya haɗa ƴar ƙaramar walima iya ahalin shi,zuwa yanzu duk yaran shi murna suke su ma sun samu little sis dama can su yawan aure-auren ne ba sa so. Duk wanda ka gani fuskar shi a sake ta ke ya mai nuni da farin ciki amman banda Ma'aruf da ya koma gefe ya na tunanin ya rayuwar ƙanwarsa za ta kasance duk da dai ya fara ingantata ta hanyar canza masu muhalli mai kyau.
Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin sannan yayi gyaran murya yace "alhamdullah gida yayi ƙamshi,ya haskaka,ya girmama da zuwan Raihan"duk taɓi ɗiyan shi suka shiga yi Agaishat ta ɗan murmusa yayinda sauran matan Alhajin suka cicije.
Hidimar da ake ta shagaltar da mutane hakan yasa Hajiya ta zuba wani garin magani farin fal a cikin biberon 🍼 ɗin da ake baiwa Raihan ruwan zam-zam. Cikin rashin sani kuma Agaishat ta ɗauka ta baiwa Raihan ruwan,ashe duk abinda ke faruwa a kan idon Ma'aruf
***
Mimi na cika kwana bakwai aka yanka mata ragon sunanta Fadimatu, gagarumin biki aka yi dan kuwa kusan dama Mu'azam mutumen jama'a ne.
Soyayya ƙauna suka haɗe gu ɗaya suka yiwa zuciyar Mu'azam ƙawanya sosai ya ke son Mimi fiye da komi na shi,a haka har Mimi ta fara girma ta fara ce mashi Daddy Rahama kuma Mami.
Mimi na cikin shekara ta biyu Allah ya yiwa Daddy wani irin buɗi na arziki,nan fah Mami ta aza masifa a doli suka tashi suka koma sabon gidan da ya gina yayinda Hajiya Babba kuma ta zauna wancan.
***Bayan 4years
Daddy ne da Mami zaune gaban Dr Ibrah wanda yanzu ya zama cikaken likita,bayani dai ya sake yi masu kan dukan su lafiyar su lau kawai su jira lokaci. Su na shirin miƙewa yace "am tsaya na ɗibi jinin ku sai na kaiwa wani abokina mu ga shi mai result ɗin shi za ta bada"babu muso kuwa suka tsaya ya ɗiba sannan suka dawo gida.
Washegari tun da safe Daddy zai tafi aiki ya ja hannun Mimi suka fita tare ya biya ya aje ta gidan Hajiya Babba. Fitar Daddy babu wuya Dr Ibrah ya shigo gidan,sai da ya shigo falon ya ƙwala sallame.Mami ta fito daga ita sai kayan barci jigida nayi mata kacau-kacau cak ta tsaya ganin ashe ba Daddy ba ne,har za ta juya sai taji muryar Dr Ibrah "masha Allah a nan Allah yayi babba ƙaddara wacce ba ta dace da baƙar fata ba"da sauri ta juyo ta na kallon shi .
Gira ya ɗaga ya ajiye takardun hannun shi ya fara takawa zuwa gare ta,wuyanta ya sunsuna yace "Hummm komi ma na Gimbiya haɗaɗe ne"lumshe ido Mami tayi ta na jin tsikar jikinta na tashi.
Wuyanta Dr Ibrah ya fara yiwa kissing kafin ya koma ga lips ɗin ta,cikin ƙanƙanan lokaci ya birkita mata lissafi.Ɗaukarta yayi cak ya nufi ɗaki da ita,abinda Mami ba ta taɓa tunani ba shine ya faru wai ita ce tayi zina da wayon ta. Kuka ta shiga yi sosai Dr Ibrah na bata haƙuri,ganin ta ƙi barin kukan yasa ya kimtsa ya bar mata gidan kafin a rutsa shi.
Da marice Daddy ya shigo gidan amman sai yaji shi tsit, ɓangaren Mami ya nufa yaji ƙofar a ƙage fitowa yayi ya nufi kitchen dan ya ga babu komi a dining nan ma wayam . Falo ya dawo ya zauna idon shi ya sauka da farar takarda,ya ɗauka ya karanta sai ya miƙe murmurshi kan fuskar shi ya nufi ɗakin shi wanka yayi sannan ya kira Dr Ibrah amman har ta gama ringing bai ɗauka ba.