Kenza eBookz

Karuwar gida Complete - Chapter 7

Karuwar gida Complete - Chapter 7

Karuwar gida Complete Chapter 7: Karuwar gida Complete Chapter 7. Motsin da ya ji yasa shi waiwayo Mami ce kallonta ya tsaya yi ganin tayi wani irin…

4,454 words

Motsin da ya ji yasa shi waiwayo Mami ce kallonta ya tsaya yi ganin tayi wani irin sanyi"ashe har ka shigo ?barka da zuwa ina Mimi" "Yauwa!ta na gun Hajiya Babba yau amarci ni ke son mu sha sosai"ya ɗaga mata gira gabanta ne ya faɗi sai ta ke ganin tamkar zai gane ne in ya kusanceta.

"Ayya Daddyn Mimi banda lafiya kuma"da sauri ya kai hannun shi kan wuyanta ai kuwa yaji kamar da alamar zazzaɓi,magani ya bata sannan ya fita ya nemo masu abinda za su ci su da masu gadi.

Sai da aka kwashe wata ɗaya cur sannan Mami ta fara sakin jikinta ta koma kamar da,Mimi kuwa na gidan Hajiya Babba zamanin ta. Tun da safiya ta waye ta ke zabga amai,babu ɓata lokaci Daddy ya kaita asibiti awon farko Dr Ibrah yace mashi "congratulations kai ma ka kusa zama baba"da murna Daddy ya rungume shi can kuma ya sake shi yayi sujada shukur.

Gira Dr Ibrah ya ɗagawa Mami ya mata nuni da cikin jikinta sannan ya nuna kan shi ma'ana dai ciki na shi ne ba na Daddy ba,kawar da kai tayi gefe dan dama tun farko ba tayi wata murna ba. Murmushi ta saki tare da ambaliya hawayen baƙin ciki na da aurenta za ta haifi shege a zuci tace "lalle na tabbata *KARUWAR GIDA* tunda har zan haifi ɗan da ba na mijina ba"Daddy kuwa a tunanin shi kukan murna Mami ta ke a haka ya kwasheta suka wuce gidan Hajiya Babba..... [05/12 à 14:08] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 35-36*

Haka Mami tayi rainon cikinta har ta haifi ƴarta mace aka saka mata suna Ameera,sosai Daddy ke nunawa ƴaƴan nashi so amman ya fi ƙaunar Mimi. Sam ba za ka ce Mimi ba ƴar su ba ce yadda suke ririta ta da nuna kulawar su fiye da Ameera,lokaci zuwa lokaci Dr Ibrah ya na kawowa Mami farmaki a duk lokacin da Daddy ya fita tun ta na kaucewa har suka ɗinke kullum sai sun yi RDV.

Ameera na da 3years Mami ta kuma samun wani cikin,sosai Daddy ya nuna murnar shi.Ita kuwa Mami masifa ta rinƙa yiwa Dr Ibrah na ya munafinceta bai yi mata allura hana haihuwa ba,to daga nan ne suka yi baran-baran suka rabu Mami ta tuba. Cikinta na shiga watan haihuwa ta haifo Twins duk mata aka sa masu Imane da Ihsane to tun shi ba ta sake haihuwa ba.

***Cigaban labari

Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Daddy,sam bai tsammaci haka ba tunanin shi ma bai taɓa kawowa da rainon ƴaƴan wani ya ke ba.

Ana cikin haka wayar shi ta ɗauki ringing *Dr Ma'aruf* ya gani cike da mamakin kiran Daddy ya ke kallon screen ɗin wayar dan an fi shekarar da tafi goma rabon shi da Dr Ma'aruf ɗin,zai iya cewa ma tun tashin su daga gidan da ya basu saboda ya sha gwada lambar amman ba ta shiga.

Sai da ta tsinke Daddy bai ɗaga ba,wani kiran ya shigo danne zuciya yayi ya ɗaga kiran ba tare da yace komi ba "Assalamu alaikum Alhaji na zo gida ne sai na gan shi a rufe" "Ina Clinic Agaji ne Madam babu lafiya"ba'a ƙara cewa komi ba daga ɗayan ɓangaren aka kashe wayar.

Can kamar minti ashirin sai ga wata dalleliyar mota tayi parking a harabar asibitin,su uku ne duk sukafito Alhaji ne,sai Agaishat da kuma Ma'aruf wanda shi ya tuƙo motar.

Dialing number Daddy yayi ya na ɗagawa yace "am ka fito mu na harabar asibitin"da "toh"Daddy ya amsa ya miƙe a kasalance ya fito. Gaban shi ne ya faɗi lokacin da yayi tozali da Agaishat wacce ta ƙurawa hanya ido,ƙarasowa yayi amman ya kasa ɗauke idon shi kanta saboda tsantsar kama da Mimin shi da ya ga ta na yi. Hannu ya basu suka yi musabaha yayinda suka fara tambayar shi mai jiki,jin murya Agaishat kuma ya sa zuciyar shi yin rauni tabbas ko makawo ya laluba ya san wannan jinin Mimi ce.

Murmushi Dr Ma'aruf yayi haɗi da sosa ƙeya yace "in ba za ka damu ba ina son mu ɗan zauna za mu yi magana"ya faɗa ya na mai ɗan waige-waige.

Murmushi Daddy yayi yace "maganar mi kuma Dr ?bayan tun kafin ka faɗa na san kun zo nan ne dan ku raba ni da Mimina"ya yi maganar cikin tausayi yayinda idon shi da suka yi ja tun ɗazu suka cika da ƙwalla.

Alhaji yace "Ma'aruf kenan dai dagaske ɗin ne Allahu Akbar"ya faɗa ya na mai zubewa ƙasa ya na sujidah shukur kafin ya ɗago ya fashe da kuka kuma😹 Agaishat ma kukan ta taya shi.

Waje suka samu can ƙarƙashin innuwar mangwaro suka zauna Dr Ma'aruf ya shiga baiwa Daddy labarin komi dangane da haihuwar ƴaƴa Mazan da Allah ke azurta Abban shi sai Mimi ce kaɗai mace.

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke yace "to miyasa ba ka barta cikin gantan ta ba?"Dr Ma'aruf yace "saboda kar a cutar da ita,na san in na barta za'a kasheta ne saboda su sauran matan ba sa so ace an fifita ƴar kishiyar su fiye da nasu ƴaƴan kuma maganar da ni ke yi maka yarinyar da na masayan tuni suka kasheta duk da ƙoƙarin kariyar da nayi ta bata"

Cikin son kawar da zancen tashin hankali nan Daddy yace "yanzu dai Mimi ta na Niamey in shaa Allah gobe zan sa su dawo"

Mimiƙewa suka yi sun so shiga duba Mami amman Daddy ya hana ta hanyar ce masu barci ta ke,su na tafiya Daddy ya kira Alhaji Kamal yace ya yiwa su Hajiya Babba réservation ta dawowa gobe ya na gama faɗa ya kashe wayar shi kwata-kwata. Takarda ya samu gun Dr ya yi rubutu ya aje ta kusan kan Mami kafin ya fice,bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Babba . Toilet ya shige ya sakarwa kan shi shower,a sannu ruwan ke dukan fatar jikin shi lumshe ido yayi ya na tunanin rayuwa hawaye idon shi suka shiga fitarwa.

***

Arerewa haɗi da shewa Lami tayi tace "wuuu *KARUWAR GIDA* an kusa saukewa,a toh dama ƴan jami'a ai duk ƴan iska sun fi yawa yanzu ba sai ayi mu gani ba in tusa ta hura wuta sai mu ga yadda za'a yi karatun hhh"ta ɓaɓake da wata dariya mugunta.

Shiru Anna tayi ta na nazartar kalaman Lami kafin ta maido duban ta ga Fadila wacce tayi fari fyarau ta ƙara ƙiba,kallon da Anna ke yi mata ne yasa ta tsargu kawai sai ta miƙe ta nufi ɗaki.

Tafiyarta Anna ta bi da kallo ta na sake tantance ta,ko minti ɗaya Fadila ba ta yi ba Anna ta shigo.Da sauri ta juyo ta na kallon mahaifiyarta ta haɗi da zare ido kamar wacce ta yiwa sarki ƙarya. "Cire min hijabin jikin ki baƙar munafuka"cewar Anna ta na harar Fadila,kasa cire hijab ɗin tayi hakan yasa Anna ta ja hijabin da ƙarfi ta cire. Taɓa hannuwa ta shiga yi ta na salalami sakamakon cikin Fadila da ta gani kamar ƴar ƙwarya ya fito yayi mata wani cercle ai Anna ba ta san lokacin da ta ɗauke ta da mari ba ta shiga dukanta haɗi da tambayarta uban wa yayi mata ciki amman ta ƙi faɗa.

Sai da taji wuya sosai sannan tace "Nasir ne Anna"wata uwar gwabza ta kaiwa bakinta nan take jini ya ɓalle,ƙetare ta Anna tayi ta shiga ɗakinta ta ɗauki hijabi ba ta zarce ko ina ba sai gidan su Nasir .

"Uban da ya ɗaura auren uwarka da uban ka Allah ɗebe masu albarka,asarare haihuwar asara da yarda Allah ba za ka gama da duniya lafiya ba"wannan shine abinda Anna ta faɗa lokacin da ta shigo gidan su Nasir madadin sallama.

Duk fitowa suka yi suna kallon ikon Allah, Iyani ta fito daga banɗaki kallon kwabo saura takwas ta yiwa Anna kafin tace "baiwar Allah daga gidan mahaukata kika gudo da za ki shigo mana gida ki na zage-zage?"

"Kutumar uban can!ba ki ma gane ni ba?to uwar Fadila ce wanda tanbaɗaɗen yaron ki ya ɗirkawa ciki"dariya Iyani ta fashe da shi tace "to sai mi dan yayi mata cikin?ai haka duniya ta ke dama abinda aka yiwa naka wata rana na ka ɗin ne zai yi ma wata dubi can ƴata ce nima wanin ne ya mayar da ita haka"ta ida maganar ta na mai nuna mata Fauziya wacce ke tsaye da ƙaton cikinta duk ya mayar da ita wata kala.

"Ina ruwana da ƴar ki ni tawa na sani dan haka ki shaida mashi da zarar ya dawo,gobe kotu za ta raba mu"ta na gama faɗa ta fice,tsuki Nabee tayi ta koma ɗaki a zuciyarta ta na mamakin yadda har ƴan mata suke sakacin baiwa namiji kansu kamar shashashu koko dan ba su ƙwarai a barikin ba ne ?oho

***

Cike da masifa Hajiya Babba ta shiga balbale Alhaji Kamal da faɗa sai kace ba sirikin ta ba,a haka dai ta tattare kayan su ni kuwa sai murna ni ke zan koma gida gun Daddy.

Washegari 16h tuni motar mu ta dira a Maradi, drever Daddy ya aiko ya ɗauke mu. Gidan Hajiya Babba aka kai mu,da murnata na buɗe mota na fito na shiga da gudu ina "Daddynaaa "cak na tsaya gani baƙin fuska duk miƙewa suka yi suna kallona nima haka sai dai na tsayar da dubana ne ga mai irin fuskata.

Murmushin da yafi kuka ciwo Daddy yayi yace "Mimina "a Shagwaɓe na je na faɗa jikinsa ina turo baki nace "i miss You Daddyna shine ka ƙi tafiya ka tarbo ni ai da kai na so idona su fara gani sai kawai ka turo min drever"laƙace min hanci yayi yace "ba ki ga baƙi ba ne?"juyawa nayi gun su sai na ga ashe mu su ke kallo.

"Yau na ga ragguwa yarinya dan rashin tausayi kika bar ni da dakon ƙaton aljanin ki,ina dalili yarinya kamar wata..."maganar ce ta maƙalewa Hajiya Babba ganin ashe da mutane falon gaisheta suka shiga yi ta na amsawa tare da yi masu kallon ko ina ta san su.

Teddyna ta jefo min ta na hararena nayi dariya ina kakaɓe shi dan ya faɗi, Hajiya Babba na zaunawa Daddy yayi gyaran murya ya fara bada labari tiryan-tiryan tun daga ranar da aka ɗauko ni daga gidan marayu.

Hawaye shararaaa haka suke zuba a idona na ƙurawa Daddy su ƙyaftawa ban yi,hutu na wucen gadi kwanyata ta tafi ba ta dawo ba sai da naji Daddy na cewa "Mimi ga biologique parents ɗin ki nan"..... [07/12 à 07:45] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 37-38*

Banda kallo babu abinda nayi saboda sam zuciyata ta kasa yin aikinta daidai ya da ya kamata, Agaishat ta taso daga inda ta ke ta zo ta rungume ni wani yammm naji da sauri na sauke ajiyar zuciya ita kuwa kuka ta ke. Samun bakina nayi da furta "Momyyy"cire ni tayi daga jikinta ta ƙurawa fuskata ido ta na murmurshi tace "dauther ina son ki sosai na godewa Allah da gwada min wannan rana,ta so ki je gun Abban ki saura kaɗan zuciyarsa ta buga saboda ke"ta faɗi haka ta na mai miƙar da ni tsaye mu ka nufi gun dattijon arziki wanda ya ƙura min ido tun shigowa ta.

Duƙawa nayi zan gaishe da sauri ya jawo ni na faɗa jikinsa,wasu sanyayun hawaye suka shiga malala a idon shi "Fadimatu na? Allah raya ki a kan sunnah ya tsare min ke daga sharrin ƴan hassada da baƙin ciki..."kuka ne yaci ƙarfinsa sai ya ƙyale.

Hajiya Babba wacce tayi suman zaune tace "oh Allah duniya babu kyau an raba tsoka da jini gudun mugayen ɓoye,ina ta Rahamun ta ke ta san da maganar ?baiwar Allah ta so Mimi kamar ranta"ɗagowa Daddy yayi da jajayen idonsa yace "na saketa ai"da sauri duk mu ka kalle shi dafe zuciyar shi yayi sannan yace "laifi ta yi min mafi muni wanda duk mai ƙaunata ba zai bari na cigaba da zama da ita ba,Rahama ta cuce ni Hajir mu ta rasa da wanda za ta ci amanata sai da babban abokina"

"Mine?cin amana kuma?"cewar Hajiya Babba shiru Daddy yayi dan sai yanzu ya gane da bai kamata ya faɗi haka ba "Mimi tashi kije ki yi wanka"cewar Hajiya Babba ,jiki ba ƙwari na miƙe tare da nufar part ɗin ta.

Sai bayan Mimi ta tafi ne sannan Daddy ya fayyace masu komi Hajiya Babba kuka ta saka Momy na bata haƙuri,Abba kuwa nasiha ya shiga yiwa Daddy dan ya ɗauke shi tamkar ɗan cikinsa. Dr Ma'aruf ya gyara zama yace "gobe ka same ni a asibitin mu zan duba na hauda ka kan magani, sannan ka kawo min result ɗin da sauran suka yi ma gwaji" Daddy yace "in shaa Allah na gode".

Dakyar suka daidaita nutsuwar su suka fara shan fruits,ni kuwa ko da na gama wanka na shafa mai da turare kayan da Hajiya Babba ke tara min na ciro riga t-shirt fara da buje blue na jeans. Tunda na fito mu ka haɗa ido da Daddy wanda ke saiti da ƙofar ɗakin, murmurshi na sakar mashi shi kuwa Daddy zuciyarsa ce ta shiga bugawa ganin na shanun Mimi sun yi tsiriri a tsaye suna zagin sa😹kawai haka yaji haushi ko bra ba ta saka ba za ta fito haka alhalin akwai mutane falon.

A shagwaɓe na faɗa jikin Daddy daga zuwana "shine ka fara ci ka manta da ni"na faɗi haka ina mai amshe apple🍏 ɗin hannunsa, murmurshi yayi yace "Mimi uwar rigima ai na zata ma kin kwanta saboda gajiya,yanzu yaya kike ji komi normal ?"Kai na gyaɗa na guntsiri apple ɗin daidai shatin haƙoran sa sannan nace "Daddy wai sai yaushe Tantie Munawara za ta sauka daga dokin kafiya? ni dai na matsu na gan ta mijinta na da kirki"Daddy yace "sai ranar da kasuwar apple ta tashi"ya faɗi haka ya na kimtse dariya,ƙafafu na shiga bugawa ina kukan shagwaɓa nace "Allah ba santi nayi ba kawai dai na tambaya"

"To Sarkin surutu sai ki sauko ki ci abinci dan na san in an biye ta taki ba za ki ci ba"cewar Hajiya Babba ta na juye dafafun zabi wanda suka sha jar miya kallon Daddy nayi nace "ni ba zan ci ba kar na ɓata hannu na"murmurshi yayi dan ya san mi ni ke nufi a duk lokacin da nayi sha'awar ya ciyar da ni da hannunsa haka ni ke faɗa.

Hajiya Babba ta taɓe baki tace "na ga yaushe za ka barin sangarta ƙatuwa har haka wai fah sai dai ya bata a baki kamar jaririya "cikin shagwaɓar da ta zame min jiki nace "ni dai ba ƙatuwa ba wai duka-duka ma nawa ni ke da ake sa min ido?haka fah jiya ta ƙi ban abinci a baki alhalin Daddy cewa kayi ta je ta kula da ni"duk dariya aka yi Hajiya Babba tace "ah to ni ban iya gantali ba ƙatuwar budurwar da ko yau sai a ɗaura mata aure zan baiwa abinci a baki dan dai duniya ta zo ƙarshe can shi da ya sangartar da ke ya baki"

Baki na turo nace "to na ma fasa ci ban so"na faɗa ina shirin tashi Daddy ya mayar da ni na zauna "miye haka Mimi ki nutsu mana ko ba ki ganin ba mu ɗaya ba ne akwai baƙi?koko so kike Abba yace na sangartar mashi da yarinya?"Daddy ya raɗa min a kunne,turo baki gaba nayi na juyo ina facing shi har zan yi magana ya aza min yatsansa a baki.

Cikin plate Hajiya Babba ta zuba min Daddy ya karɓa ya na bani shi ma ya na ci,yayinda su kuma suka gewaya suna ci su ma. Ƙurawa Daddy ido nayi ina jin wata irin ƙaunarsa a raina,shi ma jefi-jefi ya ke kallon ƙwayar idona.Sai da mu ka ci mu ka ƙoshi sannan Daddy ya aje plate ya zuba mana jus,miƙewa nayi na fita zuwa harabar gidan. Iskar Ubangiji na shaƙa na lumshe ido,an ɗauki kamar minti goma suka fito Hajiya Babba riƙe da hijabi a hannunta saka min tayi kafin na tambayeta lafiya naji Daddy na cewa "Mimi sai in na zo ki kula da kan ki"idona ne suka yi rau-rau na kalli Daddy nace "zuwa ina?"Hajiya Babba tace "ai kaji sakalci Abban ki za ki bi kuje can gida"wani kukan kura nayi na faɗa jikin Daddy na ririƙe shi ina kuka tare da girgiza kai.

Rumtse ido yayi ya na jin abubuwa na mashi yawo a kwanya,na ɗaya saukar dukiyar Fulaninta a kan ƙirjinsa na biyu sautin kukanta.Dakyal ya aro jarumta ya shiga bubuga bayanta,cikin murya mai taushi gami da kasala yace "yi shiru Mimina ai zan zo zuwa dare "kafaɗa na maƙe ina gyara kwanciya kan ƙirjinsa.

"Ku shiga mota ina zuwa"cewar Daddy,wucewa suka yi Hajiya Babba kuma ta koma ciki saboda karyewa da zuciyarta tayi. Haɓata ya ɗago ya ƙura min ido,ta saman gashin idona da suka jiƙe da hawaye ni ke kallon shi.Iska ya fara hura min a fuska na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, daidai saitin laɓana naji ya sauke na shi kafin ya janye yace "ina son ki,ki kula da kan ki ke ɗaya ce mace a can ƴan uwan ki na can na jiran ki saboda bege"idona na a lumshe nace "Daddy mu je tare"murmurshi yayi mai ɗan sauti ya cire ni daga jikinsa ya ja hannu na zuwa mota ina hawaye ina ji ina gani Daddy ya buɗe seat ɗin baya ya sanya ni ya rufe.Wani kukan ne ya kubce min ina leƙen Daddy ta glass Ma'aruf ya yi mata key mai gadi ya buɗe mana gate.

**Cike da tashin hankali Mami ke duba takardar,ihu tayi ta dire daga bisa gado ta fito daga cikin asibitin.Direct bakin hanya ta nufa ta tari mai adaidaita,ya na sauketa ta shiga ciki a falo ta tarar da Ameera ita da Twins duk sun dawo daga school. Ɗakinta ta shiga ta ɗauko kuɗi ta miƙawa Ameera ba tare da tace komi ba ta nuna mata hanyar waje hakan yasa Ameera fita,Twins kuwa sai sannu da dawowa suke yi mata amman ta ƙi kula su. Dr Ibrah ta kira ta shaida masa komi dariya ya shiga ƙyarƙyatawa kafin ya kashe kiran,ba'a fi minti goma ba ya zo gidan.Da gudu Twins suka rungume shi suna mashi oyoyo,Ameera kuwa yi tayi kamar ba ta san da zuwan shi ba. Mami ta fito ta na kuka,Dr Ibrah ya taɓe baki yace "to miye na kuka dan ya sake ki?kuma fah yaran nan duk kin san ni ne mahaifin su to damuwar ta mi ce?"kai Mami ta girgiza tace "na cutar da Mu'azam na haifa masa shegu cikin gida ya ciyar da su haɗi da ɗawainiya yanzu kuma har gidan ya ce ya bar min ba zai iya sake rayuwa cikin sa ba"ta ida maganar cikin fashewa da kuka. Ameera ta miƙe tsaye ta na jin abun kamar almara "ni ne sabon Daddyn ku kun ji ko?daga yau Daddy za ku kira ni kun ji ko?"Dr Ibrah ya faɗa ya na rungume Twins . Kuka Ameera ta fashe da shi ta fita da gudu da sauri Dr Ibrah ya fito ya na kiran sunanta ganin haka yasa mai gadi liƙe ƙofa. Ƙarasawa Dr Ibrah yayi ya ɗauketa da wani gigitacen mari yace "gidan uban wa za ki je?"cikin kuka da rashin tsoro tace "gidan uban ka zan je shege zakka ɗan asara da ba zai ganin Annabi ba da yarda Allah mutuwa kare za ka..."waro ido yayi ya sake ɗauke ta da mari kafin ya fincikota ya shiga bal da ita a ƙarshe ya jata ƙiii zuwa ɗaki. Banda kuka babu abinda Mami ke yi tare da dana sani maras amfani,ganin bugun da Dr Ibrah ke yiwa ƴarta yasa ta miƙe da sauri Ameera tace "kar ki taɓa ni ban son ki ban ƙaunar duk mai ƙaunar ki sannan sai na shiga duniya na zama shaƙiƙiyar tantiriya sai na kawo maki shegu kin raina tunda rainon su kawai kika iya"tayi maganar ta bubuga hannunta da table. Cak Mami ta tsaya ta na jin zuciyar ta na barazanar faɗowa,tabbas ta san Ameera ta aika yin karuwanci ga ɗiyar *KARUWAR GIDA* ai ƙaramin abu ne amman sam ba za ta lamunta ba.

***GIDAN ALHAJI

Tamkar wata tv haka duk suka sani a gaba su na kallo duk yaran murmurshi kan fuskarsu yayinda matan suka turniƙe fuska kamar tsohon kashi. Momy kuwa ta na zaune kusa da ni ta riƙe hannuna gam,Abba na zaune daga gefe ya na murmurshi Dr Ma'aruf yace "tanti amaya ya kamata a kai little ɗaki ta huta kin sa da gajiya a jikinta"murmurshi Momy tayi ta ja hannuna zuwa ɗakinta.Lafiyayen gadonta ta nuna min na kwanta bisan shi, hasken ɗakin ta kashe min na rungume pilow ina jin wasu hawaye na ziraro min kewar Daddyna ni ke yi murmushi nayi tuna ba shine biologique parent ɗina ba..... [08/12 à 16:05] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 39-40*

Kamar yadda Daddy yayi alƙawali da dadare sai gashi kuwa,kowa na gidan ya hallara banda Mimi wacce rashin sabo ya sa tayi zamanninta a ɗaki.

```gani a cikin gidan ku amman ban gan ki ba``` shine text ɗin da na karanta wanda ya fito kuma daga Daddyna,zumbur na miƙe ko kallabi ban saka ba balle wani hijab da ɗan guduna haɗi da murna na nufe shi na faɗa jikinsa duk da kuwa ƙoƙarin hana ni da ya so yi.

"Daddy ka zo ka tafi da ni ne?dama ni na gaji ni ɗaya babu su Twins kuma Teddyna ya na can gun Hajiya Babba"na faɗa ina mai kwantar da kaina bisa kafaɗarsa,sumar kaina ya shafa yace "Mimi ai kin zo gida kuma ke da can sai in kin zo ganin mu"da sauri na girgiza kai nace "a'a Daddy dan Allah kar ka bar ni nan wlh ban san kowa ba kuma fah su nan babu mace ƴar yarinya to da wa zan yi hira?"dariya kusan rabin mutanen suka yi kafin Dr Ma'aruf yace "ai shiyasa Abba ke son ki dawo nan ɗin amman kar ki damu zan cewa Fatima (cewa da Ɗiyar shi)ta dawo nan da zama"kafaɗa na maƙe na jimƙe hannun Daddy.

Mutanen falon duk Alhaji ya sallama ya bar Momy da Ma'aruf kawai wanda tun ɗazu suka yanke shawara duk da ba su san ko Mu'azam zai karɓeta ba ni kuwa ina jikin Daddy na lafe kamar mage. Gyaran murya Abba yayi yace "Mu'azam banda bakin gode maka sai dai in ce Allah saka maka da alkhairi ya biya maka buƙatunka duniya da lahira,sannan a ƙarshe ina neman wata alfarma dan Allah amman sai ka min alƙawari za ka amince"ɗagowa Daddy yayi kalli Abba murmurshi kan fuskar shi yace "to Abba ina jin ka in shaa Allah "

Sai da Abba ya sake nutsuwa sannan yace "ina son ka cigaba da riƙe min Fadimatu a gun ka na san za ka fi kula da ita sai dai wannan karon ba'a matsayin Ƴa za ka riƙe ta ba a matsayin mata"da sauri Daddy ya zabura yace "Mata?mata dai?aure? Mimi? Abba..."hannu Abba ya ɗaga yace "kar ka manta ka min alƙawali"Daddy yace "ita fah Mimi yarinya ce har yanzu kuma kamar an cuce ta an gama ta da tsoho"dariya Ma'aruf yayi yace "haba Mu'azam duka-duka nawa kake ba fa za ka wuce 45years ba amman bari mu tambayi Mimin Daddy ko ta amince"ya ida maganar cikin barkwanci.

Ƙara ɓoye fuskata nayi cikin ƙirjin Daddy dan duk abinda su ke ina jin su magana ce kawai ban yi,yadda Daddy ke shafa gashin kaina yasa barci ɗauke ni ban ma san abinda suka yanke ba akai.

Washegari da asubah Momy ta tashe ni nayi sallah,ina gamawa na zumɓuro baki ganin ashe wayo Daddy ya yi min bai tafi da ni ba. Momy da ke daga gefe ta na lura da Mimi kai kawai ta girgiza ta na jin son ƴarta har ƙasanƙasan zuciyarta,zuma ta miƙo min wacce ta sha haɗi ni kuwa Uwar son zaƙi na shiga sha. Wayata na ɗauka na danna kiran Daddy sai turo baki ni ke yi ina tsara yadda zance mashi amman har ta gama ruri bai ɗauka ba. Daddy kuwa da ke can kwance cikin ɗakin shi tun na farko kafin su tashi daga gidan Hajiya Babba kwanci ya gyara ya na mai cigaba da kallon hotunan Mimi,sam ya kasa daina kallon ƙirjinta tunda aka bashi ita aurenta ya samu kan shi da kalle surar jikinta.

Kiran ya maida mata,ni kuwa ganin appel ɗin shi yasa na ɗauka cikin sanyin murya nace "Daddyna ina kwana?shine jiya ka tafi ka bar ni a nan haba dai"na ida maganar cikin shagwaɓa.

Numfashi ya fesar kafin yace "Mimina?"a yadda yayi maganar yasa ni yin shiru ina jin zuciyata na bugawa "Mimina?"ya sake faɗa "uhum!"murmurshi yayi mai sauti yace "rigima ko?"ido na rufe na turo baki gaba nace "ba kai ne ka bar ni ba"Daddy yace "yaushe kike son dawowa nan ɗin ?"cikin zaƙuwa nace "yau ni ko yanzu ma"Daddy yace "kenan na faɗawa Abba a ɗaura auren yau?"kai na girgiza kamar ya na gani na dan wani tsoro ne ya zo shige ni nan take.

"Kin yi shiru ko ba ki shirya zuwa gidan ba?"ya tambaye ni,a sanyaye nace "na shirya mana amman gun Hajiya Babba zan zauna"dariya Daddy yayi yace "naji kar a kawo ki guna kenan?"da sauri nace "eh" "tsorona kike Mimi?"yayi tambayar cikin kalar tausayi nace "a'a Daddyna"ya sauke ajiyar zuciya yace "kin ci abinci ne ?"na bashi amsa da "a'a Momy dai ta bani zuma ga kuma madara ta kawo min jira ni ke ta wuce in sha"shiru Daddy yayi ya na jin tausayinta a ran shi dan kuwa tuni ya gane an fara gyaran amarya ne.

"Ok to ɗauki ki sha da zafin ta sannan in kin yi wanka ki saka kayan da na kawo maki jiya Please kar kice ba za ki saka bra ɗin ba"Daddy ya faɗa ya na yanke kiran. Ajiyar zuciya na sauke na ɗauki madarar da Momy ta aje na fara sha ina yamutsa fuska saboda goût ɗin hulba da naji.

***Bayan 1week

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull