Karuwar gida Complete - Chapter 8
Karuwar gida Complete Chapter 8: Karuwar gida Complete Chapter 8. Tuni aka kawo lefena akwatina dozin kowane cike da kaya,tuni kuma Momy ke ta min gyaran…
4,267 words
Tuni aka kawo lefena akwatina dozin kowane cike da kaya,tuni kuma Momy ke ta min gyaran jiki da na km.Cikin ƙanƙanan lokaci na canja na ciko sai sheƙi ni ke yayinda kuma ko muryar Daddy naji sai na wanke pant😹 ban san dalili ba,sosai mu ka shaƙu da Daddy na ɓangaren soyayya sam bai nuna wata kunya dan zai aure ni balle ni da dama na mutu cikin ƙaunarsa da son shi. In muna waya da Daddy za ka ɗauka da wani ƙaramin yaro ne ɗan 27years yadda ya ke tsayawa ya saurare ni ya biye min wajen shirme da sangarta haɗi da shagwaɓa.
A yanzu na saba da gidan mu ga kuma Fatima da ta dawo gidan mu wacce kusan sa'ata ce sai dai na girme ta,duk da ta na zaman ɗiyata amman ni a abokiya na ɗauketa.Ita ke min rakiya in zan je wani gun sai Daddy ya zo ya kai mu in mun gama abinda muke ya je ya ɗauko mu.
Abu guda ne ya tsaya min a rai yadda kwata-kwata Daddy bai son nayi mashi maganar Ameera balle uwa uba Mami,yanzu ma mu na zaune a mota mu na hira bayan ya maido ni daga gyaran gashi. Wayar shi na karɓa ina kallon hotuna cikin gallerie yayinda shi kuma ya ke kallona lokaci zuwa lokaci ya na sauke ajiyar zuciya wacce tuni na gane ta bege na ce dan ni ba yarinya ba ce na san da Daddy ya na fama da sha'awa haƙuri kawai ya ke yi.
Hoton wata mage na gani na ɗago ina cewa "ina son irin wannan magen Daddy please ka sa a nemo min"laɓana ya tsurawa ido,babu zato babu tsammani naji saukar bakin shi kan lips ɗina da sauri na rumtse ido ina jin zuciyata na bugawa yayinda jikina ya ɗauki kyarma.
An ɗauki tsawon min biyar kafin ya janye daga jikina,sunkuyar da kai nayi ina jin wata kunya. Kan shi ya ɗora saman volant ya rumtse ido ya na sauke ajiyar zuciya "bani gorar ruwa "ya faɗa cikin kasala duƙawa nayi kusan ƙafafuna na zaro ɗaya na miƙa mashi ya ɓalle murfin ya fara shan ruwan.
"Mimi dan Allah ki fara shirin tarbata tun ranar farko kin dai ga halin da ni ke ciki"Daddy ya faɗa ya na mai jingina da kujerar mota, rau-rau idona ya kawo ruwa dan tsoro da jajayen idon shi ya tsare ni..... [10/12 à 16:05] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 41-42*
"Ni dai a'a sai na gama karatu"na faɗa ina matsar ƙwalla,shiru Daddy yayi ya na kallona can ya nisa yace "sam hakan ba zai yiyu ba Mimi kuma maganar karatu ki mayar da shi gefe sai wata shekara kuma,yanzu time ɗin kula da ni ne"ɗagowa nayi ina kallon shi jin abinda ya ke faɗa kai na girgiza nace "please Daddy"kawar da kai yayi gefe dan kuwa sam bai ji zai iya cutar da kan shi ba alhalin Mimi ta isa ɗaukar nauyin namiji.
Jiki na min rawa na kamo tafin hannun shi wanda ya ke masifar sanyi ba kamar nawa ba da ya ke rau da zafi,dan kuwa kullumin jikina cikin ɗumi ya ke. "Daddyna please ko yi za kayi ka bari har mu saba"cike da mamaki ya juyo yace "Mimi wane sabo kuma bayan wanda mu ka yi?"na turo baki nace "ni dai ban saba da kai ba"lips ɗin ta ya ƙurawa ido kafin kuma ya kawar da kai gefe dan ya na tabbacin in ya cigaba da kallonta to tabbas sai ya sake kai bakin shi ga laɓanta.
"Ki shiga ciki Mimi in na isa gida zan kira ki"Daddy ya faɗa ya na kunna mota,cikin ƙin jin daɗin rabuwar da za mu yi na fita bayan nayi mashi kiss ga kumatu. Wajen da sanyin laɓanta ya sauka ya shafa ya na murmurshi kafin ya fara tuƙa motar mai gadi ya buɗe mashi gate.
***
"Wayyo Allah Anna zan mutu,wai wai Allah Innalillahi Allah na tuba ka yafe min wayyo na shiga uku na lalace"Fadila ke faɗa ta durƙushe tsakar ɗaki farin ruwa gami da jini na zuba ta ƙasanta yayinda Anna ke gefe ta na kallonta sai da kan ɗa ya sawo kai sannan Anna ta matso ta fara taimaka mata. "Inyaaa"jariri ya canyara kuka yayin shaƙar iskan duniya,reza ta sa ta yanke cibi kafin ta aje babyn gefe ta kimtsa Fadila wacce ke fitar da gumin wahala.
Duk muƙu-muƙun Anna na kar ƴan unguwa su san da Fadila na da ciki ya tashi a banza,domin kuwa Lami ta fita ta gayyato matan unguwa suka kusa cika gidan a kunnen su kukan farko na yaro ya sauka ai suka shiga taɓa hannuwa kowa na faɗin albarkacin bakin sa.
A harzuƙe Anna ta fito ta na masifa ta na cewa "to ƴan gulma miye sabo a duniya?ina ce dai ba gare ta farau ba balle ya ƙare kanta kuma mutum bai san mi zai faru gobe ba sannan mai baya dayawa(zuri'a)bai faɗin aibun Ɗan wani"ai fah kuwa da sannu suka fara sulalewa.
A ɓangaren Nabee kuwa duniyar ta bisa tsinke ta ke ci musamman da ta samu wani Alhaji Waleed,duk da dai ya na da halin banza na bin mata amman shi tsakani da Allah ya ke son Nabee. Cikin sigar roƙo yace "my Nabee kiyi haƙuri na turo manya su sa baki ayi auren nan da wuri wlh a matuƙar matse na ke na gan ki a gidana"kallon ƙaton tumbinsa Nabee tayi sannan ta ƙirƙiro murmushin ƙarya tace "haba dai duka-duka nawa na ke da zan yi aure yanzu?a'a ka bari duk ranar da na shirya ni zan faɗa ma lokacin da za ka turo kayan auren "ta ida maganar ta na sunne kai wai ita ala doli kunya.
Wani daɗi ya luluɓe zuciyar Alhaji Waleed ya samu mace ta gari mai kunya,cikin nuna ƴar damuwa ya kuma cewa "to bbna Allah matso lokacin da wuri ungo ga wannan kin sayi hoda"ya miƙa mata kuɗi amman Nabee ƙememe taƙi karɓa kamar kullum. Hannunta ya jawo ya saka mata kuɗin, tsabar jaraba sai da yaji wani abu daga haɗuwar hannunsu.
A kunyace ta jimƙe kuɗin ta na godiya "Allah saka da alkhairi ya biya ka da gidan aljanna mafi ƙololuwa"Alhaji yayi murmurshi haɗi da jin daɗin addu'arta yace "haba ai babu godiya a tsakanin mu"ta ƴar dariya gami da fari da ido kafin ta gyara dogon hijab ɗinta ta fita daga mota.
Turus tayi tsakar gida ganin Iyani ta saka Nasir a gaba ta na zagi shi kuwa ya sunne kai "ai yanzu sai ka tashi ka sawo rago dan ni kuwa ko ƙwandala ta a to😏 a bar ni da baƙin cikin wacan asararar kawai ina dalili kai kaje ka ɗirkawa ƴar mutane ciki ni ma an zo an yiwa tawa Ƴar masifar ka ce ka zoza mata"shi dai Nasir bai ce komi ba har sai da ta gama sannan ya miƙe ya bar gun.
Can tsakar dare ciwon mara da azaba iri-iri suka ishi Fauziya ta miƙe zaune ta na sharar hawaye. Kallon Nabeela ta tsaya yi wacce ke sharar barcinta hankali kwance,wani irin da na sani ne ya wanzu a zuxiyarta kawai sai ta fashe da kuka.
Cike da masifa Nabee ta tashi daga barcin da ke,ba tayi wata-wata ta ɗauke Fauziya da mari ta na cewa "minene?uwar miye ki kewa kuka yanzu tsakar dare?"cikinta Fauziya ta nuna wanda sai ƙara yin ƙasa ya ke.
Tsuki Nabee tayi tace "uban wa ya aike ki mtws wawuya kawai"tayi kwanci babu jimawa kuma wani barcin ya ƙara ɗauke ta.
Wata irin azaba ce Fauziya ke ji ta ko ina sai dai ba ta da iko ko halin yin wani abu,ko kafin gari ya waye ta jigata tuni ruwan waya sun fashe su na ta zuba amman babu mai kula da ita. Nabee na sauke ƙafarta da asubah taji danshi waro ido tayi da sauri ta cire sakata ta nufi ɗakin Iyani ta na kiranta.
Nasir ya nemo mai taxi suka wuce asibiti,ba su jima ba kuma aka tura su babban gida wato likita babba. Da isar su Mère et enfant aka wuce da ita Bloc saboda matsalar da suka hango,tayi doguwar naƙuda ga kuma ƙarancin shekarunta. Ko da aka ciro yaron bai zo da rai ba,ɗakin hutu aka kai Fauziya. Hamdallah Iyani tayi da aka ce jaririn ya mutu sai dai kuma result ta biyu ta tayar mata da hankali na kamuwar yoyon fitsari da Fauziya ta samu.
***
Sharkaf na haɗa zufa saboda turaren hayaƙin da Momy ta sa ni ala doli sai nayi,ina buɗe bargon wani ƙamshi ya game ɗakin yayinda fatar jikina ta ƙara yin wani haske gami da kwantawa da taushi. Toilet na wuce,ruwan da aka haɗa min cikin bawon wanka na shiga ina mai lumshe ido jin ɗuminsu ya ratsa ni ga wani ƙamshi da suke fitarwa.
Humra na shafa a duk wani lungu na jikina kafin na saka kaya,Momy ta shigo hannunta ɗauke da tray yayinda Yayunta mata biyu ke take mata baya uwanda sun zo ne saboda bikina da kuma taya murnar dawowata.
Baki na kwaɓe dan har ga Allah na fara gajiya da shaye-shayen nan, murmushi Momy tayi ta fara miƙo min ina shanyewa ina bata kofin Allah ya so ni wannan karon duk maganin zaƙi ne da su.
Wayata ta ɗauki ringing ƙin zuwa nayi kusa da wayar balle na ɗauka domin ringing ɗin Daddy ne kuma yanzu da na ɗauka zai fara shagwaɓe min ya na min zantukan da sun girmi lissafina.
"Ba ki jin ana kiran ki ne?"cewar Momy turo baki nayi nace "Daddy ne" "to ki ɗauka mana ki koma can falo"ta faɗa ta na mai nunawa Yayun nata wasu kaya su kuma suna dubawa.
Wayar na cire daga caji na fita sannan na ɗaga ina mai karawa a kunne wani irin numfashi ya sauke wanda yasa zuciyata yin wani yarrr kamar an tsagata "jj-2 jours dai na matsu"shine abinda Daddy ya faɗa "wai yanzu banda gobe ne auren?"na tambaya ina waro ido "ƙwaran gaske nan da jibi kin zama tawa yauwa faɗa min abinda kika tanadar min".... [12/12 à 10:37] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 43-44*
"Ni ban san mi na tanada ba"na faɗa cike da ƙurciya murmushi yayi mai sauti yace "to naji wane Gift kike na baki a matsayin tukuici?"ba tare da wani tunani ba nace"mota ni ke so fara sol mai kyau irin ta mata sai kuma Teddy da kuma farar mage"dariya Daddy ya kece da ita ni kuwa na turo baki nace "Allah su ni ke so Daddy ko ba za ka saya min ba?" "Haba Mimi mi za kiyi da mage?sannan ni ina zan ga farar mage?"Daddy ya tambaya. "Nemowa za ka yi mana,kuma fah na ga hoton wata mage cikin wayar mai kyau"Daddy yace "to ko ciro hoton ake sai a maki cadre ɗin sa?"na waro ido waje tamkar ina gabansa nace "hoto?hoto kuma Daddy?to miye banbancin da na cikin wayar tunda shi ma ba motsi zai yi ba ?ni dai ta ƙwarai ni ke so"na fara bubuga ƙafafu ina kukan shagwaɓa. "Ya Salam!"Daddy ya furta jin wata kasala na zubo masa tamkar yayi ihu saboda abinda ya ke ji duk jikinsa.
"Shuuut!"ya faɗa a kasalance kafaɗa na maƙe kamar wacce ya ke gani nace "ni dai a'a sai kayi alƙawalin za ka samo min" "naji shikenan ko?"Daddy ya faɗa ya na furzar da huci.
Murmushi nayi mai sauti nace "yauwa Daddyna na gode,ina Hajiyar mu?" Ya bani amsa da "ta na can falo" "kai kuma fah ka na ina?"na tambaye sa ina lumshe ido saboda a yadda ya ke sauke numfashi ya jefa ni cikin wani yanayi "ɗakina"ya bani amsa na kuma tambayar shi "ka na mi?" "Kwance mana"shiru nayi jin yadda numshinsa ke sarƙewa "to kaima Hajiya Babba wayar ina son mu gaisa"na faɗa a Shagwaɓe dan naji kamar barci ya ke son yi. "Ban iya fita a wannan halin"ya bani amsa,na turo baki nace "wane hali kuma?"kai ya girgiza a zuci kuma yace "oh Mimi yanzu ba ki gane halin da na ke ciki ba sai kace yarinyar goye?"kukan shagwaɓa na saka mashi jin ya ƙyale bai ce komi ba.
"Babynaaa"Daddy ya furta cikin wata irin murya wacce ta sa doli na nutsu "uhum" "Minene ?"na kwaɓe fuska kamar zan yi kuka nace "komi ni cikina mai ke ciwo"Daddy ya gyara kwanciya yace "daidai ina?"na bashi amsa "ga ciki mana" "Na sani ga ciki,amman saman ciki ko ƙasan shi?"wata kunya ce naji ta kama ni wlh kawai sai nayi ƙasa da murya nace "a'a ba daga sama ba"
Ya sauke ajiyar zuciya yace "to naji Allah baki lafiya"nace "amen!ina Hajiya Babba ɗin?"Daddy ya dafe kai yace "Mimi sai yaushe za ki barin rigima ?a wannan halin zan fita kaiwa Hajiya waya?"cikin rashin sanin manufa nace "to mi ya ke yi?" "Bai komi bari ranar da kika zo za ki gane" "naji to sai an jima zan ci abinci" "ok ki ci dayawa" "Toh"na bashi amsa shi kuma ya kashe wayar.
***
Cikin kuka Mami tace "Dr Ibrah sam wannan ba halin ƴaƴan musulmi ne ba,ta yaya babu igiyar auren ka ko ɗaya a kaina amman kullum sai ka zo min?haba ka bar ni na sarara mana da wane zan ji da wannan ƙaddararren cikin koko da jarabar ka?"kwasheta yayi da mari ya nunata da yatsa yace "ki iya bakin ki in ba haka ba zan yi maki shegen dukan da duk wanda ya gan ki sai ya tausaya maki"shiru Mami tayi ta kasa cewa komi yayinda shi kuma Dr Ibrah ya fara yamutsata. Kafin wani lokaci kukan da Mami ke yi ya sauya zuwa ihu🙊 Ameera wacce ke falo zaune ta tashi ta leƙa su ta ƴar hudar ƙofa ( *KE DUNIYA* next book ɗina in shaa Allah wanda zai magana akan sakacin iyaye masu sex ƴaƴan su na ji)
Da sauri ta ja da baya ta na waro ido tabbas irin abinda ta ke kallo a waya ne su Mami ke yi,tunani ta fara inda za ta samu mafitar abinda ta ke ji. Hijab ta saka ta fita waje mai adaidaita ta tara ta kwatanta mashi inda zai kaita,suna tafe mai adaidaita na sauraren wa'azin Malam Bashir Ghana inda ya ke cewa ```«Yarinya budurwa ki tsare kan ki saboda a ranar lahira gangar jikin ki zai bada shaida da irin abubuwan da kika yi,farjin ki zai bada shaida iya adadin mazajen da suka yi zina da ke,ƙirjin ki zai yi magana iya adadin samarukan da suka taɓa shi,laɓan ki za su bada shaida akan duk namijin da ba mijin ki ba da ya taɓa kissing naki,ƙafa za ta bada shaida ce a ranar ni na taka ta je wajen,Saurayi ma haka a gaban ka za kaji azakarin ka na baiwa Allah report iya adadin matan da kayi zina da su,bakin ka zai ce ni nayi kissing nata hannu yace Ni na taɓa.Dan haka samari da ƴan mata kuyi hattara kuyi taka tsantsan da zangon ƙurciyar ku zango ne da babu sauƙi saboda a lokacin ne kuke da ƙarfi kuke ganiyar samartaka ku saboda rayuwa ta kasu zango uku ne,YARINTA,SAMARTA,TSUFA babu zangon da ake tsananta bincike kamar na tsakiya saboda wannan lokacin Allah ya baka ƙarfi fiye da zangon biyu wanda suke tattare da rauni»``` a daidai nan Ameera wacce jikin ta duk yayi sanyi ta sauka tare da biyan mai adaidaita.
Kallon gidan saurayin nata tayi wanda shine ke tura mata blue Film,kawai kuma sai ta fashe da kuka ta na girgiza kai a fili tace "ai babu babban tonon asiri kamar Allah ya tsare ka gaban bainar nas ana bincikar ka tare da bankaɗo mugan halayen ka, Allah na tuba ka yafe min nayi alƙawarin ba zan taɓa barin idona ya kalli haram ba sannan zan zama mutumniyar kirki ta yadda Manzon Allah SAW zai yi alfahari da ni a ranar alƙiyama"ta na tafe ta na jaddada tuban ta gun shugaban talikai babu zato kawai sai ji tayi an kwasheta ta faɗi ƙasa daga nan kuma ba ta sake sanin abinda ya faru ba.
A ruɗe ABU MALEEK(Nimcyluv)ya fito daga mota ya na mai furta "Innalillahi wa'inna iley raji'un"sungumarta yayi ya saka bayan mota ya na mai tambaya inda zai samu asibiti nan kusa,nan wani ya kwatanta mashi.
Da isar sa Clinic Khasum Moctar aka shiga dubata,ashe suma ne tayi saboda furgici sai kuma kanta da ya bugu an wanke gun a naɗe sa da bandeji. Shiga yayi ɗakin da aka shimfiɗe ta,tsayawa yayi ya na kallon ƙyaƙyawar fuskarta da hawaye ke shatata daga cikin manyan idonta masu dogayen gashi. Ƙarasawa yayi ya saka hannunsa mai dogayen yatsu ya fara goge mata hawayen sai dai wasu kuma ke sake zubowa,"ya Allah!"ya furta a hankali cikin muryar shi mai sanyi buɗe idonta tayi suka sauka kan chocolat face ɗin shi mai ɗauke da jan leɓo.
Maida idon tayi ta rufe ta na tunanin abinda ya faru da ita,"buɗe idon ki petite beauté"ya faɗa ya na mai ɗaga fatar idonta wanda yasa doli ta buɗe su "ya jikin ki?"ya tambaye ta,samun kanta tayi da murmusawa kawai shi ma sai yayi murmushin yace "mi sunan ki?" "Ameera"ta bashi amsa "Meera,ni sunana Abu Maleek yau ɗin nan na shigo garin Maradi cike da zumuɗin zan je na ga ƴar little sis ɗina da aka gani ga shi kuma gobe za'a ɗaura aurenta sai kuma Allah ya katse min hanzarin na banke petite beauté"ya na maganar ne ya na murmurshi mai nuni ya na cikin farin ciki sai kuma da ya zo ƙarshe ya kwaɓe fuska.
Murmushi Ameera tayi ta yunƙura za ta tashi da sauri ya taimaka mata "yi a hankali,bani number wani ɗan gidan ku sai na shaida masa ki na asibiti kar aje ayi ta neman ki"ai tamkar ya caka mata wuƙa haka Ameera ta shiga rera masa kuka.
"Oh my god!"ya faɗa ya na mai dafe goshi, Dr ya shigo ya na tambayar lafiya ko jikin Abu Maleek yace a'a nan ya basu takarda sallama gami da ordonnance ta maganin da zai saya. Hijab ɗinta da fille de salle ta wanke aka ɗauko mata ta saka,hannunta Abu Maleek ya kama da sauri ta fuzge saboda wa'azin Malam Bashir Ghana ya ratsata kuma ya na zaune cikin zuciyarta daram.
"Yi haƙuri petite beauté"ya faɗa ya na murmurshi yayi gaba ta na bin sa a baya har mota,ko da suka shiga ya yiwa mota key bai zarce ko ina ba sai gidan su saboda kiran Alhaji da ke ta shigowa wayarsa ita kuwa Ameera kamar wacce aka rufewa baki ta kasa tambayar sa.
Cike da zumuɗin zuwan Yayana wanda duka-duka jiya ne kawai mu ka yi waya da shi amman yanayin barkwancin shi da yadda ya nuna ya na sona ya sa ni jin ƙagu. Sai shagwaɓa ni ke zubawa Abba na har yanzu bai shigo ba alhalin yace ya na cikin garin Maradi wannan dalili yasa Alhaji ke ta kiran Abu Maleek.
Motar na tsayawa na rugo da gudu waje daidai nan Ameera ta fito daga mota goshinta naɗe da bandeji cak na tsaya ina ƙare masu kallo yadda suka yi wani masifar dacewa shi ya buɗe mata ƙofa.... [14/12 à 15:50] Cham~rose💞: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 45-46*
Da gudu mu ka ƙaraso muna masu rungume juna,wani marayan kuka Ameera ta saki ta na mai ƙanƙame ni kamar za ta huda jikina ta shiga. "Ya isa haka mu je ciki"na faɗa ina mai cireta daga jikina,Abu Maleek ya ƙaraso murmurshi kan fuskarsa ya kama kumatuna duka biyun ya lotsa ƴan yatsunsa ya na jujuya su kamar wata baby haka ya ke min wasa "my rigimamar sis"nayi dariya ina mai ɗora tafukan hannuna kan hannuwansa nace "Ni dai ba rigimama ba, welcome my Bros" "Merci bcp ma belle"ya faɗa ya na mai sakina ya kalli Ameera ya ɗan ɗaga gira "kin san ta ne?"ta gyaɗa kai alamun eh ni kuwa nace "she is my little sis fah"da mamaki yace "au ita ma nan gidan ta ke?" "A'a can gidan da aka raine ni dai"Na faɗi haka a daidai lokacin da mu ka ƙaraso ciki inda ahalin gidan ke zaman jiran mu.
Rungume Abba yayi yace "nayi kewar ka sosai Abbana"shafa kan shi Abba yayi yace "nima haka ya Mamar ka ya hanya kuma?" "Lafiyarta lau tace na gaishe ka ha..."tsukin da Hajiya uwar gidan Abba ta ja ne yasa shi juyowa da sauri ya sauke idonsa kan fuskar da har gaban abada ba zai taɓa manta ba domin ita tayi sanadiyar korar mahaifiyarsa daga gidan ubansa.
"Ina kwana Hajiya ?"ya faɗa murmurshi kan fuskarsa mai cike da ma'anoni,kawar da kai gefe tayi ta ƙi amsa gaisuwar shi kuwa ya gaishe da sauran matan Alhaji da Yanunsa. Momy tace "Al Maleek mi ya tsayar da kai tun ɗazu mu ke jiran ka"ya sosa ƙeya dan shi sam ya manta da Ameera "wlh accident nayi ga yarinyar da na banke nan amman alhamdullah da sauƙi" "Innalillahi to Allah ƙara kiyayewa"cewar Momy ni kuwa nace "amen,Momy ƴar Daddy ce fah "da sauri Abba ya ɗago kai yace "Mu'azam?"murmurshi kan fuskata nace "eh Abba"fuskokin Abba da na Momy ne suka canza yayinda Ameera ta sunne kai ta fara hawaye ganin haka na ruɗe na shiga tambayarta amman ta kasa bani amsa. Hannunta na ja zuwa part ɗin Momy,nan fah Ameera ta faɗa min abinda yasa zuciyata daina bugawa na wani lokaci. Hawaye ne sharrr suka shiga zubo min a fili na furta "why Mami? miyasa kika zaɓi tozarta mu a duniya da auren ki kin mayar da kan ki *KARUWAR GIDA* babban baƙin ciki har da haihuwar ƴaƴa Innalillahi wa'inna iley raji..."kasa idawa nayi saboda wani abu da naji ya tokare min zuciya idona suka kakafe yayinda ciwona na huka ya tashi zubewa nayi kan capet ina fidda numfashi dakyar da sauri Ameera ta fita waje ta na kuka wanda yayi daidai da shigowar Dr Ma'aruf "Mimi ciwonta ya tashi"ta faɗa cikin kuka da sauri Momy wacce ke zubawa Abba abinci ta aje ludayi yayinda shi kuma yayi zumbur ya miƙe Abu Maleek da Dr Ma'aruf suka rufa masu baya.
Taimako Dr ya fara baiwa Mimi wacce ba ta san halin da ta ke ciki ba,"ina ga fah doli sai mun je asibiti"cewar Dr Ma'aruf,Momy tuni ta fara hawaye nan suka ciciɓi Mimi suka fita da ita zuwa mota. Ameera da Abu Maleek suka bi motar su Abba a baya,yayinda Hajiya ke addu'ar Allah sa Mimi mutuwa ce tayi.
Fitowar Daddy daga wanka kenan kiran Abba ya shigo mashi,da tsananin tashin hankali ya shirya ko mai bai shafa ba ya fice ba tare da ya baiwa Hajiya Babba amsar tambayar da ta ke mashi ba,mutanen da suka zo biki kuwa kallon shi suke suna addu'ar Allah sa dai lafiya.
Ikon Allah ne kawai ya kai Daddy lafiya,idon shi sun kaɗa sun yi jajur sabada tashin hankali. Tamkar wani ƙaramin yaro haka ya bi ya ruɗe dan ma Dr Ma'aruf na kwantar mashi da hankali,ɗaukar lokacin da aka yi ba'a fiddo Mimi ba shi ya haifarwa Daddy kwanciya kan gadon asibiti aka sa mashi ƙarin ruwa. Ameera ta zauna kusa da shi saboda in sérum ɗin ta ida ta je ta faɗawa Dr sai ya zo ya cire,hawaye ta goge ta kalli Daddy wanda idon shi ke lumshe ya na sharar barci "Mami kin cuce mu da kika ruguza rayuwar familyn mu ga shi sanadin ki Mimi da Daddy na kwance babu lafiya,ta yaya ne ma kike tunanin Daddy zai tsaya kusa da ke bayan kin zaluncesa zalunci mafi muni a duniya..."ta tsaya da zancen da ta ke ganin Abu Maleek ya shigo ya na kallonta,kallo mai cike da tausayi Allah ya gani tun farko yaji son Ameera ya ɗarsu a zuciyarsa yanzu kuma da yaji ainahin tarihin rayuwarta sai ya ƙara lunkuwa abu guda ya ke tsoro kar Abba ya hana shi auren ta.
Gabanta ya zo ya tsugunna ya share mata hawayen fuskar ya na girgiza kan shi "ki bar kuka ban so"tace "Daddy bai sona yanzu ya tsane ni akan laifin da ba ni na aikata ba"Abu Maleek yace "kar ki damu zan yi mashi magana in ya farka ai laifin wani bai shafar na wani"kai Ameera ta jinjina tace "Allah sa ya yarda" "Zai yarda mana in amarya shi ta sa baki" "Wace amarya?"Ameera ta tambaya "Mimi mana"ya bata amsa "shine wanda za ta aure dama?"kai ya ɗaga, murmushi ya suɓucewa Ameera tace "Allah sarki wlh lokuta da dama in na kalli yadda Mimi ke shagwaɓewa Daddy sai nace da uba na auren ƴa da tabbas za su dace da junansu"Abu Maleek yace "kai haba?"Ameera tace "wlh kuwa ɗan ba ka san yadda Daddy ke sonta ba ne ko mi ya samu Mimi dai har kishi ni ke yi da ita"dariya Abu Maleek yayi yace "yanzu dai taso mu tafi waje in an jima kaɗan sai na zo na duba ƙarin ruwan"ba tare da ta musa ba ta miƙe suka fita.