Kawar zuciya Book 2 by takori - Chapter 6
Kawar zuciya Book 2 by takori Chapter 6: Kawar zuciya Book 2 by takori Chapter 6. Suna shiga falon Mama tayi arba dasu, ta kalli kayan dake jikinsu, nan da…
4,492 words
Suna shiga falon Mama tayi arba dasu, ta kalli kayan dake jikinsu, nan da nan annurin fuskarta ya dauke kaman an aiko mata da saqon mutuwa. Tana tozali da kayan jikinsu Sabah ta danna ashar a zuciyarta, tace a ranta lallai ma Safiyyah da take rainawa ta bari tayi kauri da yawa, ta samu Baffa da yawa, me Safiyyah ke nufi na sakawa kauyawan kannenta kaya irin nasu Hatoon?
Haka suka karaso suka gaishe da Mama da kawayenta Mama na zabga musu harara daga su har Safiyyah din. Hajiya Yabi kawar Mama ta lura da irin kallon da Mama ke musu sai kawai ta bude baki tace.
“Wai ni kam Haj. Fatu, Safiyyah har yanzu bata haihu ba ko?”
A gaban kawayenta Mama tace “tayani tambaya, shiru, har yanzu, tamkar Malam yaci shirwa”. Haj. Yabi ta ce “kuma kuke zaune haka baku tashi tsaye akai ba? A can kan tudu layin gidan iyaye na akwai wani mai bada maganin haihuwa, maganinshi kaifiyyan, in kunaso zan karbo mata”.
Sai ta kalli Safiyyah wadda hankalinta ya soma tashi ranta kuma ya soma baci da jin zancen da suke yi a kanta, ai har abada ba ita ba sake neman haihuwa tawata hanyar balle ta hanyar malaman tsubbu, ta riga ta tuba wa Allah da Habibiy dinta, tace bazata sake ba. Haj. Yabi tace.
“Diyata Safiyyah ina fatan zaki sha maganin in an amso, don magani ne me tsada. Kar na karba kizo baki sha ba”.
Safiyya ta gyada kai kawai amma ko motsi da bakinta ta kasa. Mama ta zucciya da banzan data yi musu, ta daka mata tsawa a cikin mutane tace “baki ji ne ana miki magana kinyi shiru, kar ta kashe kudinta a banza a wofi ta karbo miki maganin baki sha ba.
Ni ban ma cika son harkar maganin gargajiya ba Haj. Yabi, nafi yarda da asibiti, amma tunda na matsu na ga diyan Baffa gara a jarraba can din, ba’a san inda za’a dace ba, tunda anyi na asibitin duk ba nasara”.
Duk sauran matan suka ce “exactly, gara a jarraba na gargajiya”.
Baki daya falon sai ya karade da zancen rashin haihuwar Safiyyah har tsayin shekara goma da aure, kannen sa daga mai biyu sai mai uku, kowacce na tofa abinda take tunanin shi ya hana Safiyyah haihuwa, har da masu cewa ko PCOS gareta, don mafi akasari shi yake hana mata haihuwa yanzu.
Safiyyah da kannenta duk sai sukayi jigum-jigum a zaune, suka rasa abinda ke musu dadi, ba zaginta ake ba amma hakan fallasa ne da gori a fakaice, suka rasa abunda zasu ce, duk Safiyya ta tsargu da kanta, taji kamar tayi wani gagarumin laifi ko abun kunya, wanda al’umma ta kasa yi mata uzurinsa, wani irin kuka na takaici ya taso mata.
Sabah ta fahimci hakan, tayi maza ta kama hannunta suka mike suka bar falon, uffan basu ce ba.
Suna fita Hajiya Yabi ta dubi Mama cikin damuwa tace,
“ina fatan dai ba maganar da nayi bace ta bata ran surukar tamu?”
Mama tace “oho mata, ita ta sani, daga abun kirki? Yarinya sai kafirin zurfin ciki da nuku-nuku, gata da sumumu-kasau irin nasu na ‘ya’yan Alarammomi da ka kan rasa gane zuciyarsu”.
Fitarsu harabar gidan suka ci karo da shi yana kokarin shigowa da hancin motarsa bakar ‘Ford Mustang,’ Arch. Zayyan ya sha adon sallah masha Allah dashi cikin farar shaddah bugaggiyar Wagambari babbar, bugun hannu, ba karamin kyau da kwarjini da kamala shigar yau ta kara masa ba. ta kuma kara fiddo zahirin kuruciyarsa ainun.
Da annuri sosai ya shigo gidan, amma yana ganin fuskarta ya gano akwai abunda ya faru da ya canza mood dinta. Suna tsaye a kofar shiga babban falon gidan itada Sabah. Ya adana motar a parking lot na gidansu a nitse, bai fito ba ya sauke glass na barin da yake zaune, sai ya yafitota da hannunsa, yace.
“Sabah, ku ara min Yaya Safiyyah mana, ku shiga gida zan ganta, gata nan zuwa yanzu”.
Sabah da Rayyah har suna hada baki wajen cewa “Toh! Uncle Zayyan”. Suka juya zuwa cikin gida.
Ganin Safiyyah taki motsawa daga inda take tsaye bayan wucewar su Sabah ciki, sai ya fito ya kama hannunta, dole ta bishi kamar rakumi da akala zuwa motar, ya bude suka shiga gidan gaban motar ya rufe, dama glassanta duka masu duhu ne (tinted), motar tana kunne, don haka AC na aiki. Ga kamshin ‘Car fresh’ din motar mai dadin kamshi da ya hade da kamshin turaren jikin Zayyan na mazan da suka amsa sunansu (Ultraviolet), su suka hadu suka dawo da nutsuwa da salama a zuciyar matarsa Safiyyah, ta jingina kanta a jikin kujerar bayanta, ta hau sauke ajiyar zuciya a jejjere, ba tareda ta ko san tana yi ba.
A hankali Zayyan ya mika hannayenshi biyu ya rungomota jikinsa, bakinshi a kasan wuyanta ya sumbaceta lightly, yace.
“Sophie yaya akayi ne? Wani abu ya faru da bana nan ne? Na ganki moody”.
Safiyyah tayi shiru, haka kawai taji kwalla na kara ciko mata, tace “Habiby, ina so in haihu ne, kuma da wuri!” Yace “Yaa Subhanallah! Ita haihuwar nan ba’a hutawa da yin ta? Tukunnama yaushe aka gama jegonta? Kuma shin me ya kawo zancenta?”
Daga Safiyyah babu amsa, sai ma idonta daya karasa cikowa taf! Da hawaye. Kiris suke jira su sauka kan kuncinta.
Zayyan yayi-yayi ta gaya masa abinda ya kawo zancen haihuwa amma Safiyyah ta ki. Kada ya zama cewa ko ta kai karar Mama da kawayenta wajensa ne.
A karshema da ya dameta da tambaya sai ta kifa kai a kirjinsa ta fashe da kuka mai cin rai.
Bai iya yin komai ba ko hanata kukan a wannan lokacin, banda ya rungumeta cikin kirjinsa tsam-tsam, yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi. Ya kuma barta tayi kukanta ma’ishi, yana magana cikin lallashi, kauna da soyayyah masu yawan gaske, wadda ta bayyana kanta a zuciya da tone din furucinsa, Zayyan yace.
“Ki kara hakuri kinji Safiyyah, haihuwa da samun ‘ya’ya duka lokaci ne, in kuma Allah bai ga damar bamu ba…. inaso ki sawa ranki WANI HANIN GA ALLAH BAIWA ne”.
Ya fahimci an mata gorin haihuwa ne as usual. Amma kowanene bai kyauta masa ba suna cikin farin cikin ranar sallah, ranar celebration din musulmi. Sai ya kira Sabah a waya yace “ta robar, me ya faru ne da Sophie da bana nan? Kunje wani wuri ne an bata mata rai?”
Yasan Rayyah ko kusa bazata fada masa ba, don zurfin cikinta irinna Safiyyah ne, kuma bata da yawan magana, amma Sabah tsaf zai ji komai, har abinda bai tambaya ba, don tasu tazo daya sosai.
Sabah tace, “kawai-kawai, daga munzo falon Mama mun sameta da kawayenta mukayi musu gaisuwar sallah, shine wata mata tayi mata zancen haihuwa, nan aka fara zancen rashin haihuwarta, hadda cewa za’a karbo mata maganin gargajiya wajen mai bada maganin haihuwa”.
Baki daya Zayyan ya rikice, ransa kuma ya baci, don ya tsani a kuma zancen zuwa gun malamai karbo maganin haihuwa, yace “wanene da wannan maganar?” Sabah tace “oho bansanta ba, amma tana zaune a gefen Mama, wata fara mai jiki haka”. Yace “Maman, me tace toh?”
Da yake Sabah bata da tsoro sai tace “ba abunda Mama tace, illa ma cewa tayi ta tabbata ta sha maganin da matar zata karbo mata don kudi me yawa za’a saka a karbo. Tace kuma itama bata yarda da maganin gargajiya ba, kawai don ta matsu taga diyoyinka ne”.
Zayyan sai ya rasa me zai ce ma. Amma ransa yafi na Sophie baci. Karshe ya kashe wayar bayan ya gama sauraron Sabah, yace “toh Sophie don Allah banda bakin baki hakuri, bani da kalmar baki hakuri, amma kiyi hakuri ki kuma kara akan naki”.
Washegari da wuri ya daukesu zuwa Dandume, don kada a kara bata mata rai a gidansu.
Ya kaisu har cikin gida ya shiga ya gaida Ammi da Malam. Yayi musu godiyar aron ‘yammatan gidan da aka basu na lokaci mai tsaho.
Bai jima sosai ba ya fito yace ma Safiyyah ta kwana da Ammi, sai gobe zai dawo ya dauketa su wuce Abuja.
Ammi kam ta san halin yaranta ta iya karantarsu su duka, da ganinsu kuma ta san wani abu ya faru a Rafindadi, amma dai bata ce komai ba, ta barsu a hakan. Suma basu tada zancen ba sai wanda ya shafesu.
Yana komawa gida ya tarar da Mama tana zaune ita kadai, mai aikinta Ankudi nata tattare mata falon da bakinta suka bata.
Ya shigo ya zauna a gajiye, yana ta kumburi, ya gaisheta, sai ya koma gefe yayi shiru, Mama tace “a kawo maka abinci ne?” Ya ce “a koshe nake Mama”. Mai aikin na fita yace,
“Please Mama me ya faru tsakanin Safiyyah da mutanenki a gidannan?” Mama tayi salati ta sallame tace.
“Koda naji! Ai dama na san za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
Toh Sannu ubana, nace sannu ubana da ya haifi uwata, matse bakina sai in gaya maka tunda tuhumar abinda ya bata ran matarka ne ya kawo ka ba gaisheni ba.
Sallamamme kawai, kaje kauye an wanke ka a minjaye an baka ka shanye, an aikoka ka mun rashin kunya ko, toh ba zan fadi me ya faru ba duk yadda tace maka hakan akayi, akwai abunda zakayi ne? Ko karya ake mata ta haihu dinne?
Da ta haihu za’a yi mata zancen amso magani? Ka amsa ni mana, rasa kunya beran tanka?
Ai wallahi Baffa mu zuba ni da kai, in dai jimirinka matar ka ta fada maka abu kazo ka tuhumeni to tayi kadan, ko uwarta bata isa ba. Baffa anya kuwa lafiyarka kalau?”
Sai Mama ta hau matse ido tana fadin, “Safiyyah ta kai Babanta Makkah da kudinka, addu’arsa taci akanka Baffa, an janye min kai bakidaya”.
Kawai yayi shiru, ranshi na kuna, yace “Mama haihuwar nan fa Allah ke bayarwa ba mutum ba, ba dabararshi ba.
Babu wanda ya janye miki ni Mama, amma Mama ki dinga yi wa Sophie uzuri akan lamarin haihuwarnan, tunda dai ba dabararta ce zata bata ba.
Kuma wallahi Mama ta fi ki son ta haifa miki jika, amma Mama ace bama ke ba wasu daban suna shiga cikin maganar haihuwarta saboda kin basu fuska ai bai dace ba, ina dai ce Safiyyah tayi haihuwar nan ba jimawa kowa ya shaida tana haihuwar? Allah ne yayi hukuncinsa a kai dagabaya?
Shin Mama wannan bai isa wanke mata zargin rashin haihuwa da gorin ta ba?”.
Mama salatinta da sallaminta ya karu, tace “yau Baffa dani kake sa’insa akan matarka, don ance za’a taimaka mata da maganin haihuwa?
Ai kuwa baku so zaman lafiya dani ba. Nabi haihuwar da ta yin da gudu mai kama da babu na tattake ba takalmi a kafa ta!”.
Ganin Mama ta taso gabadaya kamar zata rufe shi da duka sai ya kwantar da kai ya koma baiwa Mama hakuri, don yaga ta hassala sosai irin yadda bai taba gani ba. Da kyar ya samu ya lallasheta amma tace masa daga yau in ya kara zuwa ya tuhumeta akan an batawa matarsa rai, sai ta yi masa bacin ran da zai dade bai manta ba.
Zayyan yau da kyar ya samu Mama ta hakura da fadan suka koma hirar sallama da juna, don gobe in sha Allah da safe zasu kama hanyar komawa Abuja shi da Safiyyah, kuma ya san zai jima bai zo Katsina ba.
***** ***** ****
Tunda suka dawo Abuja yake tattalin Safiyyah da farin cikinta. Duk abinda ya san yana faranta mata shi yake yi, duk abinda ya san yana bata mata rai ya nesantata da shi.
Har wani dan outing ya tsirar musu fita yanzu kullum da daddare suje eateries ko shawarma joint daban-daban, girki kuwa Safiyyah iya cikinsu take yi su biyu ma’aikatan gidan su suke yin nasu. Ni dai mai rubutu! Nan kusa ban ga mace ‘yar gatan miji wadda miji ya gatanta ya ke tattali don ya mantar da ita matsalar rashin haihuwa, sannan ya girmama matsayinta a zuciyarshi duk da haka, wato duk da rashin haihuwar, irin Mrs. Safiyyah Rafindadi ba.
Yammacin wata Lahadi ya dawo gidansa bayan motarsa shaqare da cefane da provision dinsu yadda ya saba duk karshen wata, Safiyyah ya samu tayi daidai da takardun zanenshi akan gado wai tana zane, ko sallamarshi kanta a duke ta amsa ba tareda ta dago ba, wai kada tayi kuskure cikin zanen da take yi, don a lokacin idea din zanen ke tuttudowa a cikin kanta.
Ya cire bakar babbar rigarshi ta bakin yadin voile din filtex ya ajiye a gefenta, yayi mata duban rahma yace.
“Lallai ma Sophie, wato zane kike shiyasa ko kallo ban isheki ba, balle in saka ran zaki mike kiyi welcoming dina?”
Still bata dago ba sai ‘yar dariya data yi, ta cigaba da Zanenta bilhaqqi, don IDEA da hikimar zane sun cika kwakwalwarta a daidai wannan lokacin, so kawai take ta juyesu akan takarda don kada su gudu.
“Afuwan Habiby, Afuwan kaji? Amma don Allah kada ka katseni”.
Zayyan ya rasa me take zanawa haka da har ta kasa bashi attention dinta ko yaya, ya karaso gabanta ya tsugunna yana leka zanen, ya dora hannu saman bayanta cikin wata irin siga ta kulawar miji zuwa ga matar da yake matukar so.
“To ko zan iya sanin me kike zanawa haka? Arch. Safiyyah Rafindadi? Na ga kamar ba gida ba, ba kuma Estate ba”.
Sa a lokacin ta dago da murmushi tana kallon sassanyar fuskarshi, da kwantaccen sajensa ya kara ma fuskar kwarjini, fuskar da bata taba gajiya da kalla da sajenda bata gajiya da shafowa da hannunta koyaushe. Yanzunma haka ta kai hannu ta shafi sajen nasa with so much love, tace.
“Habiby yau tsegumi kakeso? To ba wani abu bane nake zanawa irin naka ba, ko irin wanda ka sani, ni yau “Ultra-Modern Market” ce nake zanawa irin ta turawa.
Ka tuna sanda muka yi tafiyar nan zuwa conference din “Ranar Masu Zane ta Duniya (World Architecture Day) da aka gayyace ka a birnin Berlin?” Muka ga kasuwar nan ta zamani harka ce min ta burge ka? Da zaka iya da ka zana ta?
To tun lokacin abun na raina, ina jiran ranar da zan samu nutsuwa in kwaikwayeta in zana.
To tsarin ta na dauka yanzu nake nawa zanen a kansa”.
Da admiration sosai yake kallon zanen nata yana mamaki, kodayake in dai Sophiensa ce ai bai kamata yayi mamaki ba, in dai akan hikimar zane ne, in bata fishi ba, to zasu yi kunnen Doki, duk da yana gaba da ita a kwalin karatu.
Ya shiga tattara takardun wuri guda yana turesu gefe yana fadin.
“Ko kina sane da cewa kuma yau ce ranar cin abincin Zayyan ta duniya? It’s my lunch time! Yanzu dai ayi hakuri da zanennan a kawomin abinci, yunwa sosai nake ji a duniya, in na gama kuma a dumama min shimfida irin dumamawar da aka dade ba’a yi min ba.
Baby, na rasa gane kan ki tun last week kike avoiding dina cikin dabara”.
Murmushi tayi, don ta gane me yake nufi, ta dauki kayan zanen da takardun ta kai daya dakin ta adana su ta dawo. Kuma daga lokacin ta manta da zancen sabgar zanen kasuwa ta shiga hidimar hadawa Habibinta abinci, mai rai da lafiya wanda ta tabbatar zai gamsar da shi.
Lafiya kalau suka ci abincin dare tare, tana shiga toilet da zummar tayi wanka, sai taga isowar bakon watanta.
Tsaki tayi, daga haka ta soma kuncin rai ita kadai, sau tari hakan ce take kasancewa da ita duk sanda taga isowar period dinta, ta shiga kunci kenan, tunda alama ce ta cewa ciki dai bai samu ba har yanzu.
Haka tayi wankan cikin dacin rai da bacin rai mai tsanani, domin ta saka rai, dama kuma in period dinta ya kusa, sau da dama behaviour dinta ya kan dan canza, ta zama ‘moody’. Shi bai san dalili ba amma a satinnan ya lura ta rage shige masa, kuma tana kakkauce ma haduwarsu a shimfida. Ashe dalilin duk wannan ne, period ne ya kusa yin sallama.
Ta fito daga wankan kenan ta ganshi kwance a gadonsu daga shi sai shorts, yayi dai-dai a tsakiyar gado irinna jiran isowar uwargida yana waya, sai kawai taji ranta n abaci, aikin Habiby kenan soyayya da iya romance amma bai damu da haihuwa ba, Safiyyah ta fada a ranta. Daga yadda yake wayar (with respect) ta fahimci shi da Baba Murtala ne.
Sai ta zauna akan stool din mudubi tana shafa lotion a jikinta a hankali, cikin son bata masa lokaci da rashin kuzari a tare da ita. Me ke damun Sophie ne?
Idonsa ya kai ga saman kirjinta wanda ya ciko sosai saboda haihuwar data yi duk jikinta ya zama danye (fresh) dashi.
Sha’awar matar tashi da baya taba gundura da ita (duk da baya samun yadda yakeso daga gareta saboda alkunyarta) nan take tazo mashi. Gashi yanada tafiya Lagos a washegari, kan wani muhimmin project na ginin flyover da Baba Murtala ya samo masa kwangilar yinsa.
Hasali Baba Murtala aka baiwa kwangilar, amma ya barwa dan nasa, yace shi yayi madadinsa, don yana son ya shigar dashi harkar ginin bridges da flyovers bayan harkarsu da yafi sabawa da ita ta ‘Real Estate’.
Ya gama wayar ya ajiyeta a gefensa, a lokacin ita kuma Safiyyah ta gama laqailaqan shafa man nata, ta sanya kayan barcinta masu dan kauri, tazo ta haye can kuryar gado ta kwanta, ta ja lallausar duvet ta rufe rabin jikinta.
Zayyan ba haka yaken son ganinta ba, don alamu ne na bazata marabceshi ba, shikuma gaskiya yau din wata sabuwar samartaka ce ta bakunceshi, jin kansa yake at the zenith of his thirties. Ga tafiyar da zaiyi a washegari wadda zata daukeshi kusan sati biyu babu dumin Safiyyah a gefe.
Yayi maza ya daga duvet din nata shima ya shige, ya mika hannu yayi musu light up. Amma da ya kai hannunshi gareta janyewa tayi kamar yasaka mata shocking, ta koma can karshen gado ta lafe abinta, tana faman kuncin rai.
Da matukar lallashi a cikin sautinsa da taushin muryar da ba koyaushe yake mata amfani dashi ba, Zayyan yace “kada ki mun haka Sophie. I’m thirsty. Na lura fa tun shekaranjiya kike avoiding haduwarmu a gadon nan, kike min wannan ciccijewar dana kasa gane ta mecece. Ko meye dalilin wannan kuncin ran da kikeyi yanzu?”
Murya can kasa Safiyyah tace,
“Nifa babu komai”.
Zayyan ya mirgina ya shige cikin jikin Safiyyah da azama, sosai yabi ya kanainayeta ta ko’ina ya like mata, ya ninketa bakidaya a cikin kirjinsa, yana gaya mata cikin radar jan hankalin masoyi da iya lallashin mace.
“Idan kika juya min baya a daren yau, komai zai iya faruwa dani Sophie, kin san ke ce kadai maganin damuwar nan tawa, daga ke banida wata.
Babu wani uzurinki da zan iya karba yau, sati guda kenan kina doje min, alhalin ban yi miki laifin komai ba”.
Ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa da ita cikin rada “hakurina ya kare Safiyyah, ki dubi girman Allah ki dubi darajar aure ki karbeni ko one round ne, haba Sophie me kike so inyi ne?”
Maganarsa ta karshen nan har kunya ta bata. Amma Safiyyah ko gezau, don yau wani miskilanci ne ya sameta babu gaira babu dalili, tayi kememe tayi kemadagas ta ki yarda da shi da lallashinsa. Ta kuma kasa bude baki tayi masa bayanin cewa period dinta ya zo, ya canza mood dinta, don ta san kota fada din, in dai Zayyan ne ba hakura zai yi ba, bazai fasa cewa (she should try and find another way to comfort him) ba, ita kam ta fara gajiya da nacin Zayyan, tun bayan data haihu abin nasa karuwa yake, mutum ne very romantic sosai.
Ita bata san cewa yanzu ne ta zama mace sosai a wurinsa ba, yafi samun nutsuwa da gamsuwa da ita a yanzu, fiyeda kafin ta haihu, tunda ta yada jego ya koma sabon ango shikuma, ya laqe mata kamar kaska, don tafi masa gardi da zaqi yanzun.
Wannan ya biyo bayan kayan gyaran da Yaya Zubaina ta aiko mata na “Manzil Alwafir” dake Kaduna.
(Duk wasu matsaloli na aphrodisiac ko gyaran aure “Manzil Alwafir” sunada maganinsu, including treatment na cutar PCOS da sauran matsalolin da suka shafi mata don gyara matantaka da inganta rayuwar aure.
Manzil na aika kayansu ko’ina cikin Najeriya, za’a iya tuntubarsu ta wannan layin waya 09045065562).
Safiyyah kam ta karba ne gun karamar uwarta Anti Dije bayan haihuwarta tayi amfani da kayan Manzil yadda ya kamata, bata ko san amfaninsu ba, bata kuma san abinda zasu jawo mata kenan ba.
Yayi lallashin, yayi ban bakin, yayi ban hakurin in ma laifi yayi mata bai sani ba, amma Safiyyah ko a jikinta, ta ki bashi access din komai, koda kuwa na ya samu damar da zai sumbaceta ne. A karshe ma da ya fitineta da lallashin sai ta bara baki ta abinda ke cin ranta.
“Ni kam wai don Allah Habiby, na dauka don samun haihuwa ake wahalar yin abinnan?
To ni gara a daina kwata-kwata, tunda ba haihuwa zai ke sa in yi ba…..”.
Ta fada masa hakan cikin kuncin rai, tareda kankame jikinta waje daya, har da kyallin hawaye cikin idonta da yake iya gani ta dan hasken fitilar dim light.
Wannan maganar data fada ne tasa ya fusata, ransa ya baci, komai ya fita kansa, saiya janye jikinsa ya juya mata baya, yayi rub da ciki bisa cikinsa ya rungume hannuwansa a kirjinsa, domin Sophie ta gama kular dashi. Zayyan ya rufe idanunsa yana yaki da zuciyarsa mai cewa ya saka karfinsa na da namiji yau a kan Sophie kawai, ta haka ne zai goge rainin da ya fahimci ya fara samun muhalli a tsakaninsu, wato ya kwaci hakkinsa kota wane hali jikin Safiyyah tunda dai Allah shaida ne kan bashi da wata matar sai ita, baida inda zai je ya sauke wannan bukatan sai gurinta. Ga tafiya ta sati har biyu a gabansa.
Wata zuciyar na tankwarashi da cewa “Sophie ce, His alter ego! Matsayinta ya wuce (marital rape) a gareshi, kada Allah ya nuna masa ranar da zai sakama Safiyyah karfi, don biyan bukatar ransa ko saboda hutun gangar jikinsa, yace a ransa wato lamarin mace babu abinda ya kaishi ban takaici da ban haushi wani lokacin, musamman idan kayi saken da ta san karfin soyayyarta a ranka.
To daga sannan ka gama shiga uku, ka gama yawo a hannunta.
Yace a ransa to ita Safiyyah bayan sanin weak point dinsa data riga tayi, cikin lamarinta na yanzu harda rashin godiya, tunda ta ina ya rage ta ko ya kuskure ma nata bukatun data kasa haihuwar, har da zata gaya masa bakar magana haka, wai tarayyar su ta auratayya kullum bata sakawa ta haihu?
Wannan maganar ce tasa ya hakura, ya juya mata baya shima amma ya kasa ko runtsawa a daren har goshin asubahi.
A takaice Zayyan shi kadai yasan irin azabar da ya dandana shi da zuciyarsa a daren yau.
Amma Safiyyah ko a jikinta, tace banda sawa da yake tayi tana jika gashinta yana kakkaryewa kullum saboda yawan wanka, ita wahala abin yake bata yanzu, saboda bata yin komai cikin dadin rai kamar can baya. Hankalin ta ya bar kan soyayyar miji, kacokam ya koma na soyayyar samun Dan kanta.
Abin ya fita kanta kwatakwata tunda bai sawa ta samu cikin haihuwa. Kamar akan dole take bashi hakkin nasa yanzu, tun bayan haihuwarta.
Wanda hakan ya jefa shi a damuwa da rashin samun satisfaction da ita yanzu, idan ma ta kyale shi din kenan, baya samun yadda yake so daga gareta, don ta dauke zuciyarta daga kan sexual life dinsu, ta mayar kacokam kan son haihuwa.
Da safe ta hada masa breakfast amma ko kallonta bai yi ba itada tebirin breakfast din nata, ya dau wanka da karin guga, ya murza hadaddiyar hular ‘Tonak’ a saman goshinsa, kai sai ka rantse da Allah ba shine ya kwana begging matarshi yana matse ciki tana jansa a kasa ba sabida yadda yabi ya daure fuskar nan tam. Ta gaisheshi, karo na farko da yaki amsa gaisuwar Sophie ta safe, a tsayin shekarunsu goma da aure.
Bata damu ba, ta hau gyaran dakin da suka kwana tana fadi a ranta Zayyan sai da haka, in ba haka ba tsofeta zaiyi da kwarzaba irin tasa don baya gajiya, tun bata ajiye masu yi mata addu’a ba.
Ya dauki ‘brief case’ din shi ya fice, sai ta ‘text messege’ ya gaya mata ya kama hanyar Lagos, a takaice ya gaya mata zasu fara project din da ya gaya mata shi da Baba Murtala.
Bata ga text din nasa ba sai bayan ya jima da barin gidan, har ya shiga jirgi lokacin, jikinta kuma sai yayi sanyi lokacin data karanta, bata san tafiya ce dashi ba, ta kuma ga rashin kyautawarta ga Habiby dinta koda ace ba tafiya zaiyi ba, wannan ne karo na farko daya taba yi mata sallamar tafiya wani gari a waya.
Ta ji babu dadi har ranta, anya Zayyan ya cancanci unfavourable treatment din da take masa a satinnan, don kawai bata jin dadin zuciyarta kan rashin haihuwa sai ta huce komai a kansa?
Kada dai ya kasance shaidan ne yake yi mata ingiza mai kantu, don ta zama butulu, ungrateful ga ni’imomin Ubangiji a gareta, ta zama mara godiyar Allah da rashin gode masa bias alfarmar mijin kwarai daya bata?
A take jikinta ya kara yin la’asar, ta yi maza ta shiga kiran layukan wayarsa, amma cikin rashin sa’a a lokacin Zayyan ya shigar da wayarsa ‘flight mode’ don ya shiga jirgi ha ra zarga belt, ya kashe dukkan wayoyinsa.
Bai kunna ba har saida ya sauka a filin jirgin Murtala Mohammed, inda ya tarar da “Seyi”, direban gidan Baba Murtala kenan ya na jiran saukarshi.
Seyi ya dauke shi da trolly dinsa zuwa gidan Arch. Murtala Babangida dake Ikoyi, da bacin ran Safiyyah fal ransa.
**** **** ****
Kasancewar gidan Arch. Murtala babban gida ne na zamani ginin (Bungalow) a shiyyar Ikoyi har da tankasheshen sassan baki, anan Baba Murtala yasa aka saukeshi.
Saida yayi sallahr azuhur yayi wanka ya huta, sannan Baba Murtala ya turo Seyi, don yayi masa jagora zuwa cikin gida wajensa.
Har falon da iyalin sa kadai ke shiga Baba Murtala yayi umarni ga Seyi ya kai shi.
Baba Murtala dai kamar ya hadiye dan nasa saboda kulawa da maraba, ya rasa ina yaka saka ina yaka aje da shi, duk sanda yazo gidan haka yake nan-nan da shi, Zayyan na shirin zama akan kilishi Baba Murtala yace “zo zauna nan a gefena kaji Zayyan, Da na na kaina, kullum na ganka ji nake kamar da Bello nake tare.
Ka jima ba ka zo gidan naku ba, yaushe rabon ma ka zo har na manta, bana jin duk kannenka ka san su gabadaya”.
Ya dauki waya ya kira maidakinsa Haj. Nana Aisha, wadda ita kadai ce matarsa tun ta lalle, yace da ita “Da na Zayyan ya iso. Maza a Shiryo abincin rana a kawo mana nida shi, muna karamin falona”.