Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 13

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 13

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 13: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 13. Lokaci ya ja, shekaru sun matsa Haysam ya kammala js3 ɗinsa…

4,313 words

Lokaci ya ja, shekaru sun matsa Haysam ya kammala js3 ɗinsa ya shiga ss1, a ranar su ta farko a aji wani al'amari ya faru tsakanin malaminsu dasu su Haysam ɗalibai. Suna zaune cikin natsuwa, kowanne da littafinsa a gaban tebur. Malam Sulaiman, wanda ake kira da Mallam Su a kamarantar ya shigo da murmushi yana ɗauke da takarda da kwalkwalinsa kan nan sai ƙyalli yake, bayan ya gama ƙare musu kallo ya basu izinin zama daga gaisuwar da sukai masa ya ce, "Kafin na fara darasi ina da tambaya mai sauƙi ga ɗalibai na sabbi fil a sabon ajin fara girma wato ss", ya ƙare maganar yana kallon ɗaliban ajin ɗaya bayan ɗaya. Cike da girmamawa suka amsa da, "Okay Sir!!". "Ku gaya min, idan kun girma me kuke son zama?". Yara suka fara ɗaya bayan ɗaya. "Ni likita!" "Ni injiniya!" "Ni matuƙin jirgi!" Wasu ko sun kasa faɗa dan basu san mi zasuce ba. Sai idon malam ya sauka kan Haysam dake zaune a tsakiyar kujerar farko yay shiru idonsa akan bangon littafin Iliya ɗan Mai ƙarfi dake gabansa. "Haysam ibn Abdul-rasheed Shehu!". Ya kira sunansa cike da tsokana dan shi mutum ne mai barkwanci. ya cigaba da faɗin, "kai fa? Me kake so ka zama idan ka girma?" Haysam ya ɗago kai a hankali. Idonsa ya ɗan bushe kamar wanda ke da tunani mai nauyi. Ya ɗan ja numfashi kafin ya ce cikin nutsuwa: "Ni… so nake in zama SOJA Mallam." Aji ya ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai wasu yara suka yi ƙaramar dariya, amma Mallam Su ya ɗaga hannu yana nuna musu su yi shiru. Ya ce, "Soja fa? Haysam! Mi yasa soja?" ya maimaita cikin mamaki matuƙa dan a lokacin ba kowa ke son soja ba. Haysam ya maida idonsa ƙasa kamar bazai ce komai ba, sai kuma a hankali muryarsa na canjawa da alamar rauni ya ce, "Abiy na ne... mahaifina. Yana so in zama soja kafin ya rasu shiyasa ma yake kirana da ZAKINSA, nima kuma tunda ya fara bani labarin su waye soja naji ina so, ina son na zama jarumi, kozan iya kwatantawa daga jarumtar magabatan da suka shuɗe a zamanin MANZON ALLAH da wanda suka biyo baya irin su Iliya ɗan mai ƙarfi". Ya ɗan yi shiru kaɗan, yana wasa da yatsun sa. "Ban san ko zan iya ba, amma kullum ina jin kamar idan nayi hakan Abiy zai yi alfahari idan na cika burin nan nasa, dan shi yaso zama soja amma gida baza'a barshi ba, shiyasa yay fatan ni na zama na cika masa burinsa." Malam Su ya ɗan ɗaga kai yana kallonsa da murmushi mai cike da birgewa, dan harga ALLAH yaron ya ƙara ƙayatar da shi. Cike da son ƙarfafawa ya ce, "Zaka iya Zaki mazan fama, in sha ALLAHU sai ka iya, sai ka zama abin alfahari ga babanka damu al'ummar ƙasa. Na maka alƙawarin zan taimaka maka in ALLAH Ya yarda." Abinda ya bama kowa mamaki sai akaga Haysam yayi murumushi, abinda kuma bai cika yi ba, cike da farin ciki ya ce, "Malam kayi alƙawari?". "In sha ALLAHU Zakin babansa in dai ina rayuwa nayi alƙawari. Dan ina da ɗan uwa soja daga yau ɗin nan ma zan bashi labarinka". A wannan lokacin babu wanda ya sake dariya. Kowa ya kalli Haysam da wani sabon kallo na girmamawa da tausayi. Shiko ya koma gida da farin ciki ya sanarma Mammah da Inna. A kuma dalilin wannan alƙawari shaƙuwa ta shiga tsakanin Malam Sulaiman da Haysam, har ofishinsa yake zuwa suyita hira da labarin aikin soja. A haka rayuwa ta shuɗa yau da gobe kayan ALLAH. Ranar da Haysam ya kammala Secondary School, Aisha ta kasa boye hawayenta na farin ciki da na tsoron duk a lokaci ɗaya. Domin tana ganin ɗanta zai tashi neman hanyar rayuwa ta girma da gwagwarmayar da tafi ta shekarun ƙuruciyarsa girma da haɗari. Domin zuwa yanzu Haysam ya gama yanke shawarar shiga aikin soja kamar yanda yasha faɗa mata tun bayan alƙawarin da malaminsu yay masa. A duk lokacin da ya faɗa mata haka, sai ta yi shiru na dogon lokaci kafin ta ce: "Ka tafi idan hakan ne ka ga daidai, amma ka tuna da addu'a. Rayuwar soja ba wasa bace Muhammad, sai dai bazan hana ka ba, ba kuma zan tunɓuke maka burin mahaifinka a zuciyarka ba saboda ina jin tsoro, zan cigaba da maka addu'a da karfafawata ALLAH ya fimu sanin abinda ke ɓoye ai, sannan kowane bawa yana rayuwa ne da ƙaddararsa, kwazonsa a cin jarabawarsa ne ke bashi makoma bisa ga rahamar mahaliccinmu." To a yau ma aka kammala bikin gama Secondary ɗinsu daya tuna mata cewar lokacin zama soja yayi amsar data bashi kenan. Sai kawai ya durƙusa ya rungumeta tare da faɗin, "Mammah na gode da ƙarfafawarki a gareni a koda yaushe, amma ki sani ni bana zuwa neman suna, amma zanje neman ƙarfi da adalci. Na ga yadda rashin adalci ke cinye mutane, zan so in tashi da takobin gaskiya, ko da zai zama ƙarshena, daga karshen dai na cika burin Abiy na kuma cika nawa burin, na kuma maida sunanki UWAR GWANI ko UWAR MAYAƘI." Murmushi Aisha tayi da share hawaye, ta ɗagosa daga jikinta tana mai ɗan dungure masa kai. Murmushi yayi yana mai risinar da idanunsa ƙasa, dama idan kaga sakewa ta musamman ga Haysam to yana a gaban Mammah ne. A'isha dake hawaye itama ta kamo hannayensa cikin nata ta runtse tana addu'a kamar haka, "ALLAH ya taimake ka Muhammad. Ka zama zaki mai adalci kamar yanda mahaifinku ke fata ba wanda ke cin mutane ba. Ka zama ZAKI mai amsa sunan SARKI a rundunar adalci ba Sarkin dabbobi mai mulkinsu ta ƙarfi yana halakasu matsayin abincinsa ba. Ka zama ZAKI mai kassara maƙiya da karya mugayen burunsu da manufofin su. ina fatan wannan jarumin na Abiy da Umman-Haysam (Yakura) ya zama Zaki wanda rayuwarsa ta samo asali daga haske da nagarta, daga hawaye da fata, daga ƙaunar iyaye da ƴan uwa da nauyin al'umma. Kaje soja da fatana da addu'ata Muhammad, kaje soja da amincewata da farin cikina Muhammad Haysam. Amma ina mai gargaɗinka da shaye-shaye, bana so! Bana so! Bana so Muhammad. Ka kiyaye Zina, tana ruguza bawa da zuri'arsa, bana so! Bana so! Bana so Haysam. Ka yaɗa ilimi ka cigaba da neman ilimi musamman na bautama UBANGIJI, kaga dai zuwa yanzu kayi saukar Alkur'ani, ka samu ilimin hadisi mai yawan gaske, ka haddace litattafai da yawa na addini da koni mahaifiyarku kana koyar dani a yanzu. Ka tuna yan uwanka suna kiranka da suna (DADA) a yanzu saboda kai suke gani madadin mahaifinsu, idan ka ɓata ɗan wani kaima za'aci nasarar ɓata maka su Haysam. Yau babu Innata a duniya shekararta ɗaya kenan da rasuwa, tunda Tasi'u yabar ƙasar nan bamu sake jin labarinsa ba shekara huɗu kenan, an kashe mana Bashir a aikin soja, wanda labarin rasuwarsa yasa Inna yanke jiki ta faɗi bata sake lafiya ba sai da ta koma ga UBANGIJI. Haysam banda kowa sai ALLAH NA, sai ku ƴaƴana guda takwas, kune uwata kune ubana, kune dangina. Babu kalar zagin da bana sha saboda naƙi yin aure, ni kuma bana son nayi aure ne wani yazo ya ƙuntata min rayuwarku koda da harara. A kowace rayuwa zaka tsinta kanka ka tuna kai wanene dan ALLAH Haysam ka tuna". Kuka ya sarƙeta, shima sai ya kwantar da kansa a cinyarta yana hawaye. Sun jima a haka kafin ta koma lallashinsu, sai kuma ta koma bashi labarai masu daɗi na rayuwarta da mahaifinsu Abdul-rasheed. A haka su Ma'aruff da a yanzu suma suke js 1 Secondary suka shigo, ba jimawa Ummi da Bilal da Momy suma suka dawo. Ammar da Mimi kuwa ba'a sakasu a makaranta ba har yanzu dai. Aiko zama sukai suka zagaye Haysam da a yanzu suka maida sunansa Dada suna taya shi murnar gama Secondary. Idan ka gansu dole su burgeka su kuma baka tausayi. Akwai zuminci mai ƙarfi a tsakaninsu, akwai ginanniyar soyayyar juna mai tsafta a zukatansu, akwai shaƙuwa mai rahama a tsakaninsu, akwai tausayi mai yalwa a tsakaninsu. Su ba masu arziƙi bane, amma ALLAH ya basu arziƙin farin ciki da so da ƙaunar junansu, ALLAH ya basu arziƙin JARUMAR UWA mai sadaukar da farin cikinta domin gina nasu. Sun rasa uba amma suna kallon babban yayansu madadin uba a wannan lokacin. Dan kuwa shine ke musu ɗawainiya irin ta uba. A dalilin gwagwarmayar talla daya sha ta kayan koli da kayan karatu dama wasu wahalhalu, da aikatau na mahaifiya da wankau, dama wasu abubuwa da tayi bayan nan, dan akwai gaɓar da aka koreta a aikatau ɗin ma, wankin ya daina yiwuwa saboda ciwo daya kwantar da ita, ɗan abinda suka samu ta koma yin abincin sayarwa safe da rana wani lokacin har tuwo da dare ta fita da shi bakin kasuwa. Kai har dakau A'isha tayi domin iyalanta, haka zatayi surfe ta maida dakan gari hannunta na baroro da fashewa amma bazata kula ba, aikin gona tasha yi ta tasa yaranta gaba suyi a biyasu, sussukar hatsi na gona ta ɗure a buhu a biyata. Ga jiyyar Innarta da ciwo ya kayar, da al'amarin ya ƙwaɓe har itace A'isha tayo a daji ta sayar dan samun abinci da kuɗin maganin Inna dan abinda Haysam ke samowa a kasuwa bawai zai wadacesu bane duka amma yana rage musu sosai dan dashi ake biyan komai na karatunsa dana ƙannensa. Da kuma ALLAH ya sakama abin albarka har ya kafa jarin kansa sai yazama har anan gida ana zuwa nema a saya kayan kolin, daga haka ya barma Mammahnsa wannan sanar kolin har ma da kayan karatu na yara ya maida hankali a zana jarabawar ƙarshe da sukayi yau suka kammala. Sai kuma Alhmdllh yaga a gida ma kamar ALLAH yafi sanyama sanar kayan kolin ma albarka, wannan ƙwarin gwiwa ne ya ƙarfafashi a yau ya sake tabbatar ma Mammah zai je aikin sojan da yake ji da kamar zai fasa saboda kar ya barta da nauyi, amma yanzu yana fata wannan sanar tasa data dawo gida zata taimaka musu sosai.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 26_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Addu'ar mahaifiya ba wasa ba, dan kuwa dai Haysam ya tsallaka ajin jarabawa ko muce ƙaddararsa ta uku bayan rayuwar jin daɗi da iyaye, data maraici da uwa ɗaya tilo, zuwa soja a yanzu, sojan ƙasa mai girma irin ƙasarsa. Matakin ƙaddarar soja dake tafiya da fara shekarun hankali da mallakar kai da kai matsayin cikakken mutum, dan kuwa ya ɗauki hanyar tsallake shekaru ashirin ɗin farko zuwa matakin rayuwa ta biyu a masomin cikar hankali da fara sanin ainahin micece ma duniyar, dan a wancan matakin an san duniyar ne a gaɓar banbance iya abinda ƙwaƙwalwa da zuciya kawai ke iya fuskanta da karamin nisan tunani da hange. Matakin farko na samun gurbi a NDA (Nigerian Defence Academy), Haysam Abdul-rasheed Shehu ya samu wannan gurbin Karatu da taimakon Malamin nan nasu da yay alƙawari tun shekaru uku da suka shuɗe wato Malam Su. Bayan Haysam ya gama Secondary School da ƙwazo da halin kirki ya samu result ɗinsa na SSCE yayi ƙyau sosai. Cike da zumuɗi ya nufi ofishin Malam Su ya kai masa, ai ko ya tayashi murna ya kuma ce yaje ya shirya a gobe zasuje Kaduna wajen ƙaninsa wanda yake Major a Nigerian Army, wanda kuma yake da alaƙa da masu duba takardun shiga NDA (Nigerian Defence Academy). Haka kuwa akayi, Mammah tai ɗan cuku-cukunta ta samawa Haysam kuɗin mota da ɗan na guzirin cin abinci, washe gari suka ɗauki hanyar Kaduna. Sun samu tarba ta muntatawa kuwa, bayan sunci sun sha Malam Sulaiman ya gana da ƙaninsa. Bayan ya ƙara tisa masa wanene Haysam, da kwazon yaron da halin manya ya ce, "Wannan yaron bai da uba kamar yanda na gaya maka tun shekarun baya, amma yana da hali irin wanda ya fi zinariya daraja. Ka taimaka a duba takardunsa ba don alfarma ba, sai don cancanta da tabbatarwa irinsu ƙasarmu ke buƙata, dan an gina wannan burin a zuciyarsa tun kwakwalwar sa na jinjira ita da zuciyarsa. Kai da kanka zaka tabbatar da hakan kuma kayi alfahari da gina rayuwar wannan yaron akan wannan aikin watarana in sha ALLAHU". Cikin jinjina kai Major Abdullahi ya ce, "In sha ALLAHU Yaya, nama alƙawarin baza'a samu kowace irin matsala ba. Dan a takardun yaron kawai na tabbatar shi ɗin mai ƙwazo ne. Sannan a wannan zaman awannin da nayi da shi na fahimci abubuwa da yawa atare da shi masu girma da daraja. Kaje in ALLAH ya yarda zakaji labari mai daɗi". "Alhamdullahi Na gode Abdullahi, idan kaimin hakan bazan gushe ba ina mai maka addu'a, domin kuwa ka taimakeni wajen cika alƙawarin dana ɗaukama marayan ALLAH." Aranar suka koma kano akan za'a neme su...

><><><><><

Bayan bincike da gwaji, an sake kiran Haysam zuwa interview a Kaduna, inda ya nuna basira, nutsuwa, da ilimi mai zurfi har ma jami'an da sukai interviewn ya basu mamaki suka kuma yabama kwazonsa kwarai da gaske. Kamar wasa, sai sakamakon shigar NDA ya fito, sunan Haysam Abdul-rasheed Shehu ya fito cikin jerin waɗanda aka ɗauka. Kwatanta muku irin farin cikin da A'isha da Haysam da ƴan uwansa harma da Malam Sulaiman sukayi ɓata lokaci ne a wannan gaɓar, amma dan musamu mu wuce kowa ya ƙiyarsa a tashi zuciyar kawai..

^^^^^^^^^^^^^

3/12/1992 shirin tafiyar Haysam ya kammala zuwa NDA, inda A'isha tai ƙoƙari matuƙa ta haɗa masa dukkan abinda aka buƙata daga iyaye. Ta ƙara tisa masa nasihar da a kullum bata gajiya dayi masa shi da ƴan uwansa. Ranar farin ciki ga Haysam ga ahalinsa, ranar kuma kuka da alfahari. Haysam ya shirya cikin shigar kamala, ya goya jakarsa a baya. Cikin nutsuwarsa yazo gaban Mammah ya durƙusa, gefe A'isha ta kauda kanta kaɗan tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata idanu, kafin ta dawo da fuskarta garesa tana kallonsa zuciyarta cike da ƙauna da fargabar rabuwa da shi, tunda ta haifesa bai taɓa yin nesa da ita na abinda ya wuce sati biyu ba. Dama dai Mama Yakura ce kan ɗaukeshi suje Maiduguri suyi kwanaki sannan tana raye. Tunda kuma mutuwa ta ɗauke mata ita ta ɗauke mata mahaifinsu kuma bata taɓa nesa da su ba, shine abokinta a yanzu, shene babban ɗa, shine ƙani, shine yaya, shine uba ga ƙannensa, shine ƙawa, dole taji raɗaɗin nesantarsu da zai yi, sai dai bazata iya daƙile hakan ba dan tana matuƙar son shima ya samu cikar burinsa ya kuma cika burin mahaifinsu. Addu'a ta sake masa mai ratsa zuciya cikin danne kuka. "ALLAH ya sa wannan tafiya ta zama alheri a garemu baki ɗaya. Ka tuna da addu'a, ka tuna da asalinka. Idan ka zama soja, ka zama soja mai gaskiya." Karo na farko Haysam ya kalleta da idanunsa da sukai jaa, murmushi yay mata irin na kwantar da hankali da ƙarfafawa. "Mammah in sha ALLAHU zan yi kamar yadda kike so koma fiye da hakan. Zan zama soja don na kare ƙasata da al'ummar kamar yanda kika zame mana garkuwa bayan rasa iyaye guda biyu, zanyi haƙuri koda banci ba domin wasu suci, zan sadaukar da farin ciki na dan wasu suyi, zanyi komai da ƙarfin zuciya da ƙarfin addu'arki. Zan kiyaye dokin UBANGIJI da biyayya ga umarnin MANZONSA." "ALLAH yay maka albarka". Ta faɗa kuka na ƙwace mata. Shima idanunsa sun sake yin jazur sai dai babu hawayen. Ƙannensa ma duk sun masa addu'a. Cikin share hawaye Bilal ya ce Dada kada ka daɗe fa... ka dawo da wuri!" "In sha ALLAHU Bilalu na zan dawo da wuri, kai dai kaimin addu'a". Yay maganar cike da kulawa yana rungume yaron. Suma sauran duk sai suka matso suka rungume juna, "Ku kula da Mammah, kada ku barta tayi tunani ko damuwa. Kada ku sakata yawan magana ko ɓacin rai. Duk wanda ya dinga mata laifin da zai ɓata ranta babu ruwana da shi kona dawo, sannan bazan masa tsarabar komai ba". Kawuna suka shiga ɗaga masa. Ya ɗan jajja musu hanci cikin so da jin kewarsu. Sai suka shiga yin dariya ga hawaye. Shima murmushi yay musu mai sanyi, kafin ya miƙe, kallo ɗaya yay Mammah yaga yanda ta duƙar da kai yasan kuka take, sai ya fice da sauri shima nashi idon na tara hawaye...

>>>>>>•<<<<<<<

*_NIGERIAN DEFENCE ACADEMY, KADUNA_*

Haysam ya fito daga motar da jakarsa a kafaɗa, jakar da Mammah ta zuba masa kayan da duk ta tanadar masa, bakinsa da addu'a ya shiga bin tarin sabin ɗaliban dake cike tam da ƙofar gate ɗin tamkar ba safiya ba da kallo. Yaron da aka saba gani cikin damuwar maraici da wahalhalun rayuwa da yawan shiru, yau zuciyarsa cike take da jin daɗin samun cikar buri, da alfahari. Jinsa yake a yau tamkar ya fara wata sabuwar rayuwa, inama Abiy na raye ya gansa a wannan mataki, inama idan ya ɗaga kai ya faɗa domin shi ace kunnensa zasu iya jinsa... A bakin ƙofar gate ɗin akwai jami'an soja dake tsaye. Kowanne sabon ɗalibi sai an bincika jakarsa, an duba sunansa a cikin jerin waɗanda suka samu shiga. Haysam kuwa na cikin ƴan farko-farko da aka fara kira. Dan dai-dai yana tunaninsa akan Abiy aka ambaci cikakken sunan nasa Haysam Abdul-rasheed Shehu. A karo na farko sai zuciyarsa ta buga da ƙarfi, goshinsa ya ɗan tara zufa, amma cikin dakewarsa ya ɗaga kai da girmamawa ya amsa da nufar inda ake buƙatar ganinsa yana ɗaukar matakin soja na farko a rayuwarsa, shekarar farkon balaga dan yanzu yana da 17years a duniya da wasu watanni. A dai-dai nan kuma yay sallama da Malam Sulaiman da yay masa rakkiya. Hannunsa Malam Su ya riƙe cike da so da ƙauna da jin alfaharin cika masa alƙawari, fuskarsa da murmurshi ya furta, "ALLAH ya tsare ka ɗana, banda wasa, banda biyema abokan banza, ka zama jarumin da ƙasa zatai alfahari da kai ba kuka ba". Kan Haysam a ƙasa cike da girmamawa ya ce, "In sha ALLAHU Malam zakayi alfahari dani kai da su Mammah.." "ALLAH ya tabbatar da hakan Haysam". Malam Sulaiman ya faɗa yana sakar masa hannu da shafa kansa.....

Haysam na shiga ciki sai duniya ta canza. Cikin nutsuwarsa ya shiga layin ƴan uwansa da wasu sojoji suketa duba su, suna karɓar takardu, suna aika su wurin medical check-up. Ana duba nauyinsu, tsayinsu, tare da basu lambar cadet. Sannan suka bi jerin sabon layin da ake rabawa sababbin ɗalibai uniform da kayan horo. Sai amsar uniform ɗin suke kuwa cike da farin ciki da zumuɗi, sai manyan takalma da sauran abubuwan buƙata na kwanakin farko. Sai da aka kammala musu komai daya dace a wannan lokacin Sannan aka tafi mataki na gaba. Bayan karɓar kaya, an kai su wani babban hall mai ɗauke da gadaje da yawa da zasu iya kai 200 ma. Kowane gado akwai katifa sabuwa fil. Nanfa bakunan wasunsu suka shiga washewar farin ciki. Wasu suna dariya, wasu suna kallon juna da murmushi. Shaƙiyan ciki masu rawar kai suka fara rawa suna ɗaga hannuwa cikin nishaɗi, yayinda wasu suka fara kiɗa da ƙarfen gado wasu cokula da plate da aka raba musu. Dariya suka bama Sojojin da ke kula da su, dan haka suka tsaya suna kallon suna murmushi kawai. Dan basu da zaɓin daya wuce su bar su suyi farin cikin farko kafin a fara horo na gaskiya, a wannan gaɓar idan ma ance suyi wannan nanayen bazasu yin ba. Duk wannan abin da ake Haysam na zaune ne kawai a gefe bakin wani gado yana kallonsu, bai yi waka ba balle rawa, amma murmushin da ke gefen fuskarsa ya tabbatar da shima yana jin irin farin cikin da suke ji. Kai da ka kalla idanunsa kasan akwai tsananin buri amma a zuciyarsa akwai tambayoyi da yawa. Sai faman ayyanawa yake a zuciyarsa (Zan iya jure wannan sabuwar rayuwar kuwa? Yanzu ko mi Mammah take yi da su Ja'afar. Ƙilama Ammar da Mimi sunyi kukan rashin ganin yau bani zan kaisu makarantar allo ba, bani zan musu wankan dare ba, bazamu ci abinci tare ba. Ƙilama suna can sunama Mammah rigimar kuka). Haka dai ya zurfafa a tunani shaƙiyancin ƴan uwansa ɗalibai na yin nesa da kunensa.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 27_

__________________

LADY'S BEAUTY PALACE

SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE

ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻

Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Lace Hijabs Supplements Kayan yara Saloon Kunshi na salatap Dana zane Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari

Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma

Address bayan gidan drugs katsina State

Kayan mu masu inganci ne sosae

Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯

Whatsapp or call 08169307477

Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)

Instagram Hajara Rabiu

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........A wannan dare na farko Haysam bai iya bacci ba saboda tunanin gida. Ga hayaniyar sabbin abokai, ko gajiya basayi sukam duk sun cika hall ɗin da ɗumi, kaida ka gansu kasan ƙuruciya da farin cikin samun cikar buri ya baibaiye rayuwarsu gaba ɗaya. A hankali Haysam dake kallonsu kawai ya lumshe idanunsa, zuciyarsa na ayyana masa, "Rayuwa ta ta fara daga yau. Farin ciki a Bauchi tare da Abiy, Umma da Mammah, rayuwar ƙunci da kukan rasa Abiy da Umma. Fuskantar ainahin rayuwa da fara gwagwarmaya a Kano tare da Mammah da Inna, kukan rasa Inna, samun cikar burin ɗakko hanyar zama soja a yau. Ko mi gobe zata zo da shi idan da rayuwa? Wane sakamako zamu kalla a jibinmu ta duniya da lahira. Ya ALLAH kasa inyi nasara, nasara mai albarka ta duniya da lahira". Ganin dai barci yaƙi zuwa masa sai kawai ya tashi ya fita tare da ɗaukar sallaya a cikin jakarsa. Alwala yayo ya dawo barandar hall ɗin ya shimfiɗa abin sallar ya kabbara salla. Wannan horo ne da Abiy yay masa tun bai kai haka ba, bayan rasuwarsa kuma Mammah ta ɗora daga inda ya tsaya, shiyyasa sallar dare ta zamar masa jiki sosai, idan ma baiyi ba har jinsa yake kamar mara lafiya. Sai gab da asuba yaji barci na ɗibarsa, sannan ya tattara ya koma ciki, zuwa yanzu hall ɗin ya koma shiru, duk sunyi barci, sai tashin minshari kawai kake ji. A gadon da ya ajiye jakarsa yaje ya kwanta, baima kammala addu'a ba barci yay awon gaba da shi....

_________★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull