Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 12
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 12: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 12. A hankali Haysam dake tsaye ta jikin window yana saurarensu…
3,506 words
A hankali Haysam dake tsaye ta jikin window yana saurarensu ya zame jikinsa yabar wajen. Cikin soro ya koma ya zauna, tattaunawar mahaifiyar tasa da kakarsa na dawo masa dalla-dalla. Yasan abubuwa kaɗan da suka faru a Bauchi, amma ba duka gaba ɗaya ba, domin Mammah bata bari su fahimci komai dake faruwa, dama shine mai shekarun fahimtar, koya ga wani abu idan ya tambaya sai ta nuna masa ba haka yake ba, idan ya matsa ma saita fara masa faɗa, dole yake yin shiru ya bata haƙuri. Daga nan kuma ya saki zancen kawai saboda gudun ɓacin ranta. Hawaye masu zafi suka sakko masa a karo na farko, batare daya gogesu ba ya duƙar da kansa ƙasa kawai suka cigaba da ɗiga cikin ƙasa. Ya jima a wajen yana tunani da iya abinda ƙwaƙwalwarsa zata iya cuɗawa da kwancewa, sai kuma ya miƙe ya fita a gidan. Ba yau ya fara zuwa Kano ba, sai dai idan sun zo ba yawo Mammah ke barinsu sunayi ba, idan ma zasu fita sai da ita, idan ko da Baba sukazo kwana ɗaya ne kuma duk inda zaije tare suke tafiya shima ko Uncle Nasiru, Mammah kuma ta sanar masa yanzu Uncle Nasiru baya Nigeria ya tafi ƙaro karatu ƙasar waje. Ya ɗan san wasu wajaje a anguwar, dan haka ya shiga zagayawa musamman inda kasuwa take ana ɗan harkokin saidawa da sayarwa. Haysam akwai hankali da wayo da nutsuwa, shiyyasa Babansa ke kiransa yaro da hankalin manya. Sai da ya gama zagaye-zagayensa ya dawo gida, ya samu Mammah da Inna a tsakar gida suna hira, su Momy nacin abinci. A'isha dake kallonsa kallo irin na tuhuma ta ce, "Daga ina kake Muhammad?". Bai iya ƙarya ba, amma baya son sanar mata abinda ke a cikin zuciyarsa, dan haka ya bata amsa kansa a ƙasa. "Mammah nan baya naje cikin kasuwa". "Cikin kasuwa kuma? Yin me to? Tun la'asar nake nemanka a gidan nan jiba har magrib ta kusa." "Kiyi haƙuri, nazo na faɗa miki na samu kuna magana da Inna shiyasa na fita kawai". Shiru tai bata sake cewa komai ba, dan bata masa faɗa a gaban ƙannensa koda ace ya mata kuskure, balle ma akan daɗe kafin Haysam yay mata wani laifi da zata tuhumesa, yaro ne mai tsantsani da kiyaye ɓacin ran iyaye. Kiran sallar da akai ce ta sashi tattara su Ja'afar suka wuce massalaci bayan sunyi alwala....
><><><><><><
Tun daga wannan rana, rayuwarta ta canza gaba ɗaya, A'isha ba uwa bace kawai, ta zama har uba, mai ciyarwa, mai kariya, mai ɗora ƴaƴa akan tafarkin gaskiya. Domin kuwa a ɓoye ta samu aikin aikatau a wani gidan masu kuɗi ta hanyar wata mata Iya Tabawa. Zata dinga zuwa da safe tayi ta dawo gida, da yamma ta koma ta ƙara yi ta dawo gida, ta zaɓi wannan yawon ne saboda tarbiyyar ƴaƴanta, ta fison koyaushe su dinga ganinta tare da su. Inna kawai ta san inda take zuwa, su Haysam kuwa sai tace musu makaranta ta samu ta manya a inda take zuwa ɗin, Haysam yasan ba hakan bane ba, dan tun randa yaji hirarta da Inna yake biye da duk motsinta, hatta gidan Iya Tabawa da taje domin ta nemar mata wajen aikatau ɗin ya sani, ranar yasha kuka da daddare sosai, tausayin mahaifiyarsu da ƙaunarta suka sake cika masa zuciya, dan haka ya ƙara ƙarfafa kansa akan nasa ƙudirin shima dake ɓoye a zuciyarsa game da taimakonta. A'isha bata tsaya a wannan aikatau kawai ba, a ɗan lokacin da take dawowa gida bayan kammala aikin safe a gidan aikinta sai ta fara amsar wankau ɗin mutane tanayi, bata damu da ƙananun maganar da mutane suka fara a anguwar ba, ta toshe kunnenta ta fuskanci rayuwarta. To babu mai taimakonsu sai gidan su Nasiru, da yayansa Zubairu daya koyama Abdul-rasheed ɗinki, shima kuma zuwa yanzu iyalai sun fara masa nauyi dan matansa har uku, sai kawunta da tsufa ya fara kamawa, dan mi zata damu kanta da maganar fatar baki daga wanda basa taimakonta da komai. Da kuɗin wankau ɗin nan take saya musu abinci da ɗan cefanen yau da kullum, dan duk wuya bata barin gida babu abincin da zai kai kwana biyu, ga yara har biyu tana shayarwa, dan ma Ammar ya isa yaye dan suna zuwa Kano babu jimawa ma ta yayeshi sai Mimi data rage. Albashinta na farko da aka biyata a gidan aikinta ta maida Haysam makaranta da shi, da roƙo da neman alfarma harda kukanta ta samu aka sakashi js2 ɗinsa kamar yanda yake a Bauchi basu maida shi baya ba, suma su Ma'aruff da Ja'afar ta ɗinka musu Uniform suka koma, sai dai su an sake maidasu primary 2 maimakon 3 da suke, bata damu ba. Ga makarantar allo da tayi dama suna zuwa suma. A tsakanin Tasi'u yazo daga makaranta neman kuɗi shima dan ABU Zaria suke shi da Bashir ɗin duka, suna gama Secondary Abdul-rasheed ya kaisu can, shine komai nasu gashi kuma yanzu baya raye, sai komai ya koma kan Inna, dan ma sunma kansu faɗa sun nema ƴan abubuwanyi acan suna taimakon kansu ganin Inna bashi ne da ita ba, ƴar uwarsu A'isha ɗaya tilo nauyin iyalanta ma ya ishe ta. ALLAH sarki, a hakan bata da shi ɗan sauran abinda ya rage mata ta bama Tasi'u ya juya ya koma shima, ita kuma ta cigaba da gwagwarmayarta ta wankau da zuwa gidan aiki, Inna na sana'ar kokon safe, badan ana cin wata riba ba sai dan marayun nan su samu abin kari da safe..........✍🏼
😂😂Wanda suka karanta wancan sai kusha ruwa kawai kukam kun koshi 🤣🙏
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 24_
__________________
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Lace Hijabs Supplements Kayan yara Saloon Kunshi na salatap Dana zane Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari
Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........Haysam na samun damar cigaba da zuwa makaranta a rana ta farko bayan an tashesu maimakon gida bakin kasuwa ya nufa, inda ya jima yana zuwa zagaye batare da sanin kowa ba, kai tsaye rumfar wani dattijo da ake kira Malam Zakiyyu ya nufa, malam Zakiyyu kuwa ya kwana biyu yana ganin Haysam, dan in zai wuce yakan gaisheshi, wani lokacin kuma yakan gansa tsaye can nesa yana kallonsa, a farko ma ya dinga tsarguwa ko aiko yaron ake ya cutar da shi, sai daga baya ya fahimci sam ba haka bane, hasalima ba rumfarsa Haysam kaɗai ke laɓewa yana kallon abubuwa ba harda wasu rumfunan na abokan kasuwanci. Yau koda Haysam yazo ya gaida shi sai ya dubesa da murmushi. "A'a ɗan baba dama kai ɗan makaranta ne amma kullum kake zuwa kaita yawo a kasuwa?". Haysam baida yawan magana, amma akwai ladabi da girmama manya, gashi yaro akwai na tsuwa. Cike da ladabi ya ce, "Baba yau ne na cigaba da zuwa makarantar dai, da ba'a nan nakeyi ba". Malam Zakiyyu ya ce, "Oho to ALLAH ya bada sa'a, sai a dage da karatu kaji, ALLAH yayi maka albarka. Kaga ga wannan maza kaje gida kar Innarka ta nemeka ko". Kallon kuɗin Haysam yayi, maimakon ya amsa duk da yasan suna da buƙatarsu, amma sai ya girgiza kansa da faɗin, "A'a baba na gode ba kuɗi nake so ba, da dai zaka min wani taimako". Cikin mamaki Malam Zakiyyu ke kallonsa, amma sai ya danne ya ce, "Wane irin taimako ɗan Baba?". Kai tsaye Haysam ya ce, "Idan na dawo makaranta ka dinga kasa min kayan nan ina talla cikin kasuwa, idan na sayar na kawo maka kuɗin sai ka bani hakkina". Ba Malam Zakiyyu ba hatta maƙwafcinsa Malam Datti sai da ya tsaya yana kallon Haysam, gashi yaro ƙarami da bai wuce shekara sha huɗu ba amma a nutse yake, ga magana kuma irin ta masu dattako a tare da shi. Malam Zakiyyu yayi murmushi, tare da shafa kan Haysam ya ce, "ALLAH yay maka albarka, amma yaro ina iyayen ka? Sannan miya baka sha'awa da yin hakan? Bayan kai ɗan boko ne?". Shiru kamar Haysam bazai ce komai ba, da alama baya son faɗar abinda ke zuciyarsa, amma kuma baya son yima Malam Zakiyyu ƙarya, bayan ya jinjina abinda zai faɗar a zuciyarsa ya ɗago ya kalla Malam Zakiyyu. "Baba ni mai neman ilimi ne, iyayena kuma Mammah ta ce kawai, Babanmu ya rasu. Ina son nayi wannan sana'ar dan na taimaki Mammah ne da ƙannena suma su dinga zuwa makaranta kamar yanda nake zuwa". Sosai Malam Zakiyyu ke kallonsa, idanunsa kuwa na cika da ƙwallar tausayi, sai kuma ƙaunar yaron ta kamashi. "ALLAH yay maka albarka yaro ya sunanka?". "Haysam! Mammah na kirana Muhammad, Babana yace dani Zakinsa". "Tabbas gaskiya mahaifinka ya faɗa kai zaki ne Muhammad Haysam. A ina gidan naku yake?". "Anan bakin kasuwa ne baya kaɗan, gidan kakarmu ne Inna mai Koko". Malam Zayyanu daya ɗan shiga nazari ya ce, "Ko gidan su Bashir? Dan ana kiran mahaifiyarsu da Inna mai-koko". "Eh nan, kawuna ne". "ALLAH yay maka albarka Haysam, kaje gida yanzu, gobe idan ALLAH ya kaimu kazo zan fara kasa maka kaya". Wannan kalma taima Haysam daɗi, dan kuwa a karo na farko su Malam Zayyanu suka ga murmushin sa, cike da farin ciki ya nufi gida, ya iske Mammah ta kammala wanki tana saurin shirin tafiya gidan aiki dan ta isa da wuri saboda a ƙafa take zuwa sai ta dawo a abin hawa, wata rana ma idan babu kuɗin a ƙasan take zuwa ta dawo a ƙasa, ƙafafunta duk sunyi fashewar faso, haka hannunta duk yaja ruwa saboda azabar wanki, amma bata damuba, yaranta dai suyi farin ciki shine matsalarta.. Kayan makaranta kawai Haysam ya cire yayi wanka ya zauna cin abinci batare daya gayama kowa ba, Inna na masa hira shi dai nashi saurare, idan kuma yaso ya bata amsa, amma amsar tafi yawa a uhhmm ko eh ko a'a. Kwatsam bayan sallar magriba saiga mahaifin su Nasiru ya shigo gidan yake sanar da Inna cewar wani baƙone keson yin magana da su iya da A'isha. Abin bai ba Inna mamaki ba, dan kwana biyun nan mutane keta aikowa akan suna son A'isha da aure amma tace ita ba aure ne a gabanta ba yanzu yaranta ne. Itama Inna kuma batace mata komai ba dan tasan gaskiya ta faɗa, ina zata tabar waɗan nan ƴaƴa har takwas duk ƙananu?, waye kuma zai yarda taje masa da su gidansa?. Har A'isha taso ƙin zuwa dan tasan irin masu zuwa neman auren nata ne Inna dai ta matsa mata suka fito soron. Sai dai kuma bayan sun gaisa da baƙo daya kira kansa Malam Zayyanu ya buƙaci a kira Haysam. A'isha da kanta ta leƙa ta kirashi yana tsakar gida yana sakama su Ummi da yayma wanka da kansa kaya. Koda ya fito yaga malam Zayyanu sai tsoro ya bayyana a fuskarsa, ya saci kallon A'isha ya saci kallon malam Zayyanu. Malam Zayyanu na lure da shi, sai yaron ya bashi tausayi ya kuma sake birgesa dan ya fahimci yana tsoron ɓacin ran mahaifiyarsa. Cikin hikima ta manya sai bai fito fili ya sanar dasu yanda sukai da Haysam ba, ya nuna musu hankalinsa da nutsuwarsa ne yasa shi da kansa yake son Haysam ya dinga zuwa yana koya masa sana'ar da yake ta kayan koli da gyaran agogo. Haysam ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, yana tsammanin Mammah zatai farin ciki sai yaji tace a'a sun gode sosai, amma Haysam karatu yake yi kuma tana son ya nutsu a karatun kawai. A firgice Haysam ya kalleta, sai kawai suka ga yazo gabanta ya durƙusa yana roƙon ta barshi shi dai yana so. Koda ta masa tsawa bai fasa roƙon nata ba, amma A'isha taƙi. Daga ƙarshe zata tashi tabar soron ma Baban su Nasiru ya dakatar da ita. Shine yay mata nasiha da nuna mata illar abinda take son yi, ya kuma tabbatar mata yasan Malam Zayyanu shekaru da yawa, sai a lokacin Inna itama tasa baki, da ƙyar sukaci kan A'isha ta amince. Sai dai Haysam yasha harara dan ta fahimci koma minene da saninsa. Aiko bayan wucewar Malam Zayyanu ta tirke Haysam a ɗaki, bai iya ƙarya ba, dan haka ya sanar da ita komai. Sai kawai ta kamashi ta rungume tana hawaye. Wannan shine mafarin fara gwagwarmayar rayuwa ga Haysam Abdul-rasheed Shehu, ko da yake ƙarami ne, ya ɗauki nauyi fiye da shekarunsa. Yakan tashi da asuba ya ɗebo ruwa ya cika ko'ina da ruwan saboda yasan Mammah zata nema na wanki, sannan yay shiri ya tafi makaranta. Dama da kayansa na gida a jaka, da'an taso daga can zai wuce kasuwa wajen Malam Zayyanu, ya canja kayansa ya ɗauki tallar ƴan kunne na mata da ɗan kayan koli irin su jambaki, masilla, allura, ƴan kunne, hoda, kwalli, madubi da sauransu. Tausayinsa kesa Malam Zayyanu saya masa fura ko abinci, amma sai yaƙi ci sai ya matsa masa zai tsakuri kaɗan ya tashi ya wuce tallarsa. Haysam da ƙoƙari, cikin ikon ALLAH kafin la'asar sai dai ya dawo da tiren, ko da kaya kaɗan, ayi lissafi a bashi haƙƙinsa ya ɗauki jakarsa da kuɗin sai gida. Idan ya tarar da Mammah ya bata, idan ta tafi wajen aiki ya bama Inna yayi shirin tafiya makarantar allo shida ƙannensa. Ba'a nan Haysam ya tsaya ba, wani lokacin sai dare yayi su Inna sun kwanta da wuri musamman A'isha da ba doguwar hira take ba saboda wahalar kai-kawo sai ya kwaso wankin da ake kawo mata wankau ya hau yi, sai dai kawai su tashi da safe suga kaya fululu a shanye a igiya abin mamaki. Ranar farko da A'isha tai masa faɗa sai Inna ta kwaɓeta, dole tai shiru, Ganin haka sai ya cigaba, sai dai idan Mammah ta ɓoye kayan ne babu yanda zai yi dole ya haƙura, ita kuma tana masa haka ne saboda tasan aikin yafi ƙarfinsa balle ma wanki, dan ma yaro ne mai juriya da ƙoƙari. Ganin ga yanda ALLAH ya saka albarka a tallar tasa sai ya fara ɗan asusu, a cikin sallamar da Malam Zayyanu ke bashi ya dinga ajiye wani abu, da suka ɗan taru ya sai Rula, fensil, biro da ire-iren su kayan karatu ya zuba a jakar makaranta, idan yaje sai ga dinga yima yara talla a ɓoye yace musu yana sayarwa, tun ba'a gane shi ba har aka gane yaran suna saye. Wani mugun malamin su yayi ƙoƙarin hanashi amma headmaster yace a barshi hakan abu ne mai ƙyau, balle kowa yasan Haysam da ƙwazo baya wasa da karatu. Ga ƙoƙarin zuwa makaranta akan lokaci, da wahala ka kamashi da latti ko wani laifin faɗa da wani. In dai kaga yana faɗa an ƙureshi ne gaskiya. A duk lokacin da Aisha ta kalle shi, sai ta tuna da mijinta. Tana ganin ƙarfinsa, nutsuwarsa, da hakurinsa a cikin ɗanta. A lokacin da wasu yara ke wasa da keke ko tsere, shi kuma yana zaune a ƙarƙashin bishiya yana karatu cikin shiru ko kasuwa cikin zafin rana ko ruwan sama ko sanyi yana yawon talla, a makaranta ma bai huta ba, yazo gida kuma ya tadda hidima, dare lokacin barci amma shi ƙoƙarin rage mata wahalhalu yake dan ita ta huta. Sai dai babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya, domin kuwa da wannan neman na Haysam take hidimar karatunsa data ƴan uwansa, na aikinta da wankau kuwa suci abinci. Ana haka su Bashir suka kammala karatunsu suma suka dawo gida, tana murna mataimaka sun ƙaru sai labarin ya canja, dan kuwa kai tsaye Bashir yace shi aikin soja yake so, shi ko Tasi'u da batun auren wata yarinya da sukai karatu tare yazo musu. Hankalin Inna ya tashi matuƙa da wannan batu nasu, suka dinga lallashin su ita da A'isha amma babu wanda ya saurare su. Burin Bashir bai damesu ba, dan kuwa aikin soja ta daɗe tana jin labarinsa a bakin Abdul-rasheed da yanda yake burin shima Haysam ya zama soja, dan yaso ma daga primary military school kawai Haysam zai yi Secondary ɗinsa, amma burinsa bai cika ba, amma ya barshi gine a zuciyar ɗansa dan har yanzu babu abinda Haysam keso kamar aikin soja, na Tasi'u mai aure yafi ɗaga hankalinsu, dan kuwa wadda yake so ɗin ƴar masu kuɗi ce, suko ina suka ga kuɗin auro masa yar talaka ma balle ta masu kuɗi. Amma sun kaɗa dambu taliya yaƙi fahimta.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 25_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.......A haka Bashir ya nema shiga soja, shiko Tasi'u ya fara shirye-shiryen aure dan gidansu yarinyar sunce zasu masa komai. Hakan kuwa akayi, sun masa komai sun aura masa ƴarsu sun kuma biya musu kuɗin karatu zuwa ƙasar waje, sai dai abin takaici da tausayi ko saka su A'isha a hidimar bikin baiyi ba wai suna masa baƙin ciki ita da Inna, haka akai shagali daga shi sai abokansa sai dangin matar ya tare, bayan sati ɗaya yazo yay musu sallama shi ya wuce ƙasar waje karatu da amaryarsa. A'isha da Inna suka masa addu'a kawai ya buga ƙeyarsa yay gaba abinsa. Bayan tafiyar Tasi'u shima Bashir ya samu aikin soja, dan haka ya wuce ya barsu, sai dai shi da sanya albarkar Inna da ƴar uwarsa A'isha....
<<•>><<•>><<•>>