Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 11

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 11

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 11: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 11. ALLAH sarki rayuwa kenan, taron biki ya koma taron makoki, da…

4,222 words

ALLAH sarki rayuwa kenan, taron biki ya koma taron makoki, da ƙyar aka samu A'isha ta iya sallama da gawar Abdul-rasheed. Yakura kam ma anata ƙoƙarin ceto rayuwar ta ne da abinda ke cikinta. Hakama matar Ayuba. Sauran ƴan uwansu makusanta sunyi sallama da gawar Ayuba da Abdul-rasheed kafin a fita da su ƙofar gida inda aka haɗe da sauran abokansa akai musu salla, sannan aka wuce da su makwancinsu na gaskiya. Makwancin da yake jiranmu ni dake, yanzu ko anjima ko gobe, koma yaushe ne dai sai tazo😭. Babu wanda hankalinsa ya koma kan batun Haysam sai washe gari. A'isha ta ɗan dawo hankalinta duk da a jiyan ma ba wani kukan shirme take ba. Yaran suna zagaye da su ita da Yakura da aka samu nasarar tsaida jinin daya ɓalle mata tun a jiya da dare. Sai Yakura ta ce, "Yaya ni naga kowa amma banga ɗan albarka na ba tunda gari ya waye". A karo na farko A'isha tabi yaran da kallo itama. Su duka biyar suna nan, wanda take goye yana bayan Alawiyya. Cikin girgiza kai ta ce, Mama (dan haka take kiranta kamar yanda yaran ke faɗi) bana jin tun jiya ma ni naga ɗan nan naki ai". A ɗan rikice Yakura ta tashi a zaune jikinta na rawa, idonta cike da hawaye ta ce, "Yaya tun jiya fa? Mun shiga uku ni Yakura, dan ALLAH ku nemo min cikin kawun nan ku, Haysam fa tare suke da Babansu Yaya. Kai Ma'aruff tashi maza kira min Kawu Nuhu". Ba Yakura dake magana jikinta na rawa ba, itama A'isha rawar jikinta keyi, sai dai kamar wadda aka dokema ƙafafu ta gagara koda tashi balle cewa komai daga inda take. Har ita Yakuran ma tai ƙoƙarin daddafawa ta sauka a gadon tasa Ummi ta taimaka mata. Dai-dai nan Khadijah ta shigo, itama ido luhu-luhu alamar ansha kukan rasa ƴan uwa. Ganin halin da Yakura take ya sata saurin ajiye kwanon fura dake hannunta, dan ganin A'isha bataci komai ba tun jiya gashi yanzu har an kusa sallar azhar shine ta nema fura ta damo ta kawo mata nan ɗakin Yakura da taga ta shigo tare da yara duba ta. "Yi a hankali Maman Haysam (da yake haka suke ma Yakura alkunya, ita kuma A'isha suce Maman Ma'aruff) kin san da halin da kike ciki, inama zaki ke da akace ba'a son kina dogon motsi". Muryar Fauziyya na rawa tace, "Yaya Khadijah Haysam, kin san fa tare suka tafi da Babansu, amma babu wanda yay batunsa tun jiya". Sosai gaban Khadijah ya faɗi itama, dai-dai nan Ma'aruff ya shigo tare da kawunsu Nuhu, shima yana jin batun da suke tattaunawar hankalinsa ya tashi, sai lokacin ya tuna cewa lallai tare da Haysam aka wuce da Babansa asibiti, duk da shima babu wani alamu daya nuna yana a raye, amma yaji sanda ake sakashi a ambulance likitan na faɗin zuciyarsa na harbawa kaɗan-kaɗan, shiyasa ma ba'a sakashi cikin gawar su Ayuba ba. Ai babu zama ya fita da gaggawa, kai tsaye asibiti suka wuce shi da su Nasiru. Cikin amincin ALLAH suka samu Haysam ya farfaɗo tun da safe, likitoci nata cigiyar ƴan uwansa an duba kaf sun wuce tun juya kasancewar a rikice kowa yake. Tunda suka shiga ɗakin da Haysam yake kalma ta farko daya fara jeho musu shine "Kawu ina Babana?". Babu wanda a cikinsu gabansa bai faɗi ba, amma suka dake cike da mazantaka suka zagaye shi suna lallashi da tambayar jikinsa. Shi ko yaro ne mai wayo, duk da shekarun nashi duka 11 ne a duniya ALLAH ya bashi basira sosai, sai ya ƙi amsa musu ya zuba musu ido kawai. Tausayinsa mai tsanani ya kama Nasiru, dama ga alhinin rasa aboki, kuma amini zagaye da ruhinsa. Sai hawaye sharr suka shiga rige-rigen zubo masa. Kafin ya kauda fuska Haysam ya ganshi. Kawai sai ji sukai ya ce, "Baban Kano kuka kake yi?". Da sauri Nasiru ya shiga girgiza masa kai yana share hawaye. Amma sai Haysam ɗin ya ƙara faɗin, "Babanmu ya rasu ko? Irin rasuwar Baba da Inna da Gwaggon Maiduguri. Dama ranar nayi mafarki ai, dana gaya masa yace nai shiru kada na gayawa kowa mafarki ba gaskiya bane, gashi kuma ya zama gask...." Ya kasa ƙarasawa sai haɗiyar zuciya. Sai suka ga ya rufe idanunsa kawai. Gaba ɗayansu hawaye suke sosai, amma abin mamaki Haysam ko ɗigon hawaye babu a idanunsa, tunda ya rufe idanun nan shike nan, bai kuma sake magana ba har suka baro asibitin. Koda suka dawo gida mutane nata hamdala da ganin Haysam ɗin yana lafiya sai ƙananun raunuka. Kowa kuma na ƙara jinjina hukuncin UBANGIJI, dan duk wanda ya kalla motar su Abdul-rasheed da yanda su suka kasance, dan su dukansu likafaninsu sharkaf da jini aka bizne su a kabari amma ga Haysam ko babban ciwo babu a jikinsa. Babu wanda zai tunanin za'a samu wani mai sauran rai a motar nan. Rungume Haysam Yakura tayi tana kuka, amma A'isha ido kawai ta zuba musu. Koda Haysam ɗin yazo gabanta ya zauna bata iya ce masa komai ba, shima kuma bai iya yama kowa magana ba har lokacin. Duk wanda yace kuma yaga kukan Haysam a zahiri game da wannan rashi yayi ƙarya. Sai da dare A'isha ta kama shi a wani ɗan lungu cikin ɗakin Abdul-rasheed yana kuka shi kaɗai a cikin duhu. Hakan na nufin yazo ya ɓuya ne anan baya son kowa yaga yana kuka. A karo na farko taje kusa da shi ta zauna, tare da kamoshi jikinta ta kwantar da kansa a saman kafaɗarta, sai ya sake fashewa da kuka shima ya rungumeta. Itama kukan take yi sosai. Ranar a ɗakin nan suka kwana ita da shi, tana zaune dangan-gan, shi kuma tun yana a kafaɗarta har tai masa dabara ya zame ya kwanta kansa a cinyarta, a haka gabannin asuba barci ya sacesu su duka. Sai kiran salla ne ya farkar da su........✍🏼

Matan da suka rasa mazajensu ALLAH ya gafarta musu, ALLAH ya baku haƙuri bayin ALLAH, ALLAH ya raya muku zuri'arku ya albarkacesu, yasa su zama masu jinƙai a gareku😭😭🙏🏼.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 22_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau'in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006

TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Anyi addu'ar uku, ranar addu'a mutane sun cika fal harma da wanda ba'a sani ba abokan aiki dana kasuwanci na Abdul-rasheed daga gari-gari. A washe garin cikon kwana na huɗu mutane suka fara raguwa. Sai ƴan uwa na jiki kawai da danginsu na Maiduguri sai su Innar A'isha ƴan kano. Bayan addu'ar bakwai ma kowa ya wuce sai su A'isha kawai da Innarta da zata zauna da su. Sai wata ana kiranta Gwaggo Laraba ƴar Maiduguri dake matsayin kamar kaka a wajen su Abdul-rasheed ɗin. Zasu zauna da su har su kammala takaba, koda yake A'isha ce mai gama takaban a kusa. Yakura kam sai in ALLAH ya sauketa lafiya kuma. Gashi cikin ƙarami ne zubar jinin da tayi kuma zai iya sakawa ma ya koma baya. A yanzu kam Alhamdullah, basu da matsalar abinci da abubuwan buƙatu na rayuwa, dan suna samun ɗauki daga ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman ma Nasiru dake yin iya bakin ƙoƙarinsa. Bai gajiya da yawo tsakanin Kano da Bauchi. A haka A'isha ta kammala takaba, sai Yakura dake jan ciki, tana kuma samun kulawa sosai daga Inna da Gwaggo Laraba har ma da A'isha kanta. A tsakanin Haysam ya kammala primary ɗinsa, sai su Ma'aruff kuma daya kamata ace anyi haramar sakasu, amma a ƴan uwan na Abdul-rasheed babu wanda yayi magana. Sai da Nasiru yazo yaga shirun yayi yawa shi ya ɗaukesu ya sakasu, ya kuma ce saura a jira takardar Haysam ta fito shima ya wuce Secondary, ƙananun kuwa Ummi, Mommy, Bilal. Aka sakasu ta allo kamar yanda Haysam ke zuwa. Daga haka ya juya ya koma Kano. Watan Abdul-rasheed bakwai a cikin ƙasa ALLAH ya sauki Yakura lafiya. Sai dai kuma haihuwa tazo da tangarɗa da tashin hankali, dan tunda dama cikin ya tsufa gata nan ne dai babu isashiyar lafiya. Yau kuma data haihu sai jini ya ɓalle mata. Abu kamar wasa Inna Salame anguwar zoma zata iya tsaida shi, ga su Innar A'isha da Gwaggo Laraba na taimaka mata har abu yaci ƙarfi akace a wuce asibiti. Amma mi babu isasshen kuɗin zuwa asibitin, A'isha ta fita hankali a tashe zuwa gidan babban Yayan su Abdul-rasheed sanar masa, amma sai ya nuna shi wlhy baida kuɗi, hasalima yau haka ya tashi baida ko sisi, sai dai taje wajen ƙaninsa mai bi masa. Shima koda ta shiga ma sai matarsa tace baya nan. Hankalinta ya tashi ta dawo gida, bama ta iya sanar ma su Inna yanda akai ba ta sake fitowa, abinka da babu waya balle ta kira Nasiru dake tsaye akan al'amarin su. Wajen makwafcinsu dake saida dabbobi ta nufa, tace ya taimaketa ya bata kuɗi zasu kai Yakura asibiti idan sun dawo yazo ya kama akuyarta da take kiyo. Bai musa ba ya bata kuɗin, cikin farin ciki ta juya zuwa gida, tana isa aka ɗauki Yakura aka nufi asibiti. Likitoci sunyi faɗa sosai, daga ƙarshe dai suka amsheta. To ashe wasa farin girki, dan kuwa dai Yakura jiyya ce mai girma a tare da ita. Dan abu tun ana ɗaukarsa na marmari har ya wuce gaban kwatance. Tun ƴan uwa na zarya da bada ɗan taimako har kowa ya naɗe hannunsa ya bar A'isha da Nasiru kawai da Innar A'isha akan al'amarin Yakura. Sai Khadijah da autan su Abdul-rasheed angon da sukai haɗari ran aurensa da suma suke nasu ƙoƙarin duk da ba masu ƙarfi bane, dama dai ƴaƴansu Abdul-rasheed ɗin ne taƙamarsu, yanzu kuma ya tafi abubuwa duk sun tsaya musu. Shima Nasiru ƙarfin hali ne kawai ba wani ƙarfi ne da shi ba, gashi yana shirin tafiya ƙara karatu daya samu scholarship a ƙasar waje. Ana cikin wannan kai-kawo maganar tafiyar tashi kuma ta tashi, da farko yace ya haƙura A'isha taita roƙonsa akan yaje dan ALLAH kada ya fasa. Nan dai su Inna ma suka saka baki haka ya tafi bayan ya ajiye musu ɗan abinda zai iya na iya ƙarfinsa, bayan tafiyarsa matarsa da ƴarsa ɗaya Raihana da bata wuce shekara biyu ba sukabi bayansa. Tun ana zaman asibiti da Yakura har rashin kuɗi yasa suka tattaro suka dawo da ita gida, Gwaggo Laraba ma ta sulale ta tafi abinta, sai A'isha kawai da Innarta, ga yara har takwas dan yarinyar da Fauziyya ta haifa ma sai A'isha ke shayar da ita. A wannan halin A'isha ta ƙuƙuta ta saka Abdul-rasheed a Secondary school, ta fara sana'ar masa da safe. Sai kuma ƙananun tsogumin ya fara tashi akan zaman Inna, wai ya kamata ya tattara ta koma Kano, rasuwa shekara ɗaya da rabi amma ta tare a gidan ƴarta. ALLAH sarki Inna uwa mai dattaku, haka ta tattara ta wuce A'isha na kuka Yakura dake kwance komai sai an mata da yara nayi ta wuce. Tafiyar Inna baifi da wata guda ba Babban yayan su Abdul-rasheed ya lallaɓo yazo wa A'isha da batun wai yana son ya aureta, dan su haɗu su riƙe ziri'ar Abdul-rasheed. Takaici ya saka A'isha rufe ido tai masa tass, wannan abu da tayi kuma babu bincike mutane da dangin Abdul-rasheed suka sakata gaba saboda shi ya juya maganar a baibai. Haka aka dinga zuwa har gida ana cin mutuncin A'isha, sai dai su haɗe kai da Yakura da bata ɓoye ma komai ba suyita kuka. Ana tsaka da wannan rikicin jikin Yakuran ya rikice matuƙa, A'isha ta dinga bin dangi tana neman taimakonsu amma kowa ya nuna bazai iya ba bai da shi. Sai kawai ta yanke shawarar saida gidan da suke domin takai Yakura asibiti. Abinda ya bata mamaki sai ga ƴan uwan Abdul-rasheed sunyi uwa sunyi maɗaukiya, ƙarshe ma Yayan nan nashi da suke kira da Yayan gandu daya ce yana son aurenta ne ya sai gidan. Haka ta share bata nuna ta damu ba takai Yakura asibiti, ta biya kuɗi za'a mata aiki da tun farko likitoci suka faɗa rashin kuɗi ya hana. Sai dai UBANGIJI mai hikima bayan yin aikin da kwana biyu ALLAH ya ɗauki ran Yakura😭. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wato gigita da magagin tashin hankalin da A'isha ta shiga da Haysam mai ɗan wayo a cikin ƴaƴan ɓata lokaci ne ma wajen zana shi. Dan Yakura haihuwar Haysam ne kawai batai ba. Amma komai da uwa take ma ɗa ta masa. Haka tsakanin Yakura da A'isha zamane na amana da ba'a batun wani kishi. A ranar da Yakura zata koma ga ALLAH ta kama hannun A'isha dana Haysam ta jaddada musu ta bar musu amanar ƴaƴanta. Bata yarda A'isha ta bama wani su Ma'aruff ba a duniya koda ƴan uwanta ne da suke uwa ɗaya. Tace ta baiwa A'isha har abada, ta kuma bama Haysam dake matsayin Babban yaya ya koma Uba a yanzu. A haka ALLAH ya ɗauki rayuwarta hannayensu riƙe a hannunta. A wannan rasuwa A'isha ta sake tabbatar da lallai suna cikin halin shiga uku ita da waɗan nan yara har takwas, dan kuwa Yakura batai wata biyu da rasuwa ba Yayan gandu ya sake zuwama A'isha da batun auren da yay mata a wancan karon, da tace bata yarda ba yace to ta tattara yara ta bar masa gidansa, ya bata sati ɗaya kacal. Hankalinta ya tashi, ta kira Jamilu autan su Abdul-rasheed ta sanar masa komai dake faruwa, harna sharrin farko da Yayan gandu yay mata, shima hankalinsa ya tashi, dan basu taɓa sanin gaskiyar zancen ba sai yanzu, amma sai yace su koma gidansa dan babu yanda zai yi tunda yayansa ne. Dan haka suka shiga tattare kayansu, abinda zai zama kaya A'isha ta saida shi, sai kayan sakawarsu da abubuwa masu muhimmanci kawai suka koma gidan Jamilu da zama. Sai dai ko wata basu cikaba sabon kalubale ya ɓullo daga matar Jamilu, dan ƙiri-ƙiri ta nuna ita bata yarda da wannan zama ba. Taya tana amaryarya haihuwa ɗaya (dan zuwa yanzu itama ta haihu) ace azo a cika mata gida da ƴaƴa. Rikici ita da mijinta A'isha taga aurensu na neman mutuwa ta shiga tsakani da roƙon Jamilu ya barta ta wuce Kano. Zai tada hankalinsa ta lallaɓasa da nuna masa muhimmancin yin hakan. Badan yaso ba haka A'isha ta hau shiri, da taimakonsa da rakiyarsa A'isha da ƴaƴanta takwas tai bankwana da garin Bauchi ta koma garinta na haihuwa Kanon dabo....

Babu zato babu tsammani Inna ta wayi gari da baƙin Bauchi. Al'amarin ya girgiza mata zuciya, duk da kuwa kullum dama addu'arta ALLAH ya kawo ma A'isha mafita, dan tunda taje rasuwar Yakura ta sake tabbatar da Bauchi bazata zaunu ga ƴar tata ba. ALLAH sarki rayuwa, bayan shekaru goma sha shida A'isha ta dawo gidansu babu Abdul-rasheed a duniya. Tayi aure tana da shekara sha huɗu. Shekararsu goma sha huɗu da Abdul-rasheed, yanzu yana shekara biyu da wasu wattani da rasuwa. Haysam nada shekara goma sha uku da wasu watanni a duniya. Ja'afar da Ma'aruff nada shekara takwas, Bilal nada shida, Ummi nada biyar. Mommy nada huɗu da wata takwas, Ammar nada uku da wata huɗu, sai ƴar da Yakura ta haifa a ƙarshe da taci sunan A'isha suna kiranta MiMi nada ɗaya da rabi. A yanzu A'isha nada shekara talatin da ɗaya ne cif a duniya. Inna ma ba mai ƙarfi bace, dama Abdul-rasheed ne ke mata komai a yanzu, hatta da karatun su Bashir, dan tunda ya rasu suma su Bashir ɗin karatun ma ya nema taɓarɓarewa sai da Nasiru ya shiga ya fita ya samar musu wani taimako sannan. Ƴar sana'ar koko Inna keyi da safe yanzu, sai daddawa, da itace take ruƙe su ita da su Tasi'u da yake ba zama suke ba a gida koyaushe suna ma makaranta ne a Zaria, yanzu ga A'isha da iyalanta sun ƙaru. Lissafin ya canja ƙwarai da gaske. Ita kanta A'isha tunda ta shigo gidan take tattauna abubuwa a zuciyarta, da yanda rayuwa zata sake kasancewa. Amma dai tasan zama bashi yiyuwa, babban tashin hankalinta karatun yaran, duk rintsi bata fatan karatun yaran ya tsaya musamman Haysam dake jss 2 zai tafi jss 3 ne nan da ƴan watanni. Haka taita lissafi tun a daren da suka iso Kano ko rintsawa batayi ba. Washe gari karatun ya fara mata maimaicin kansa a cikin ƙwaƙwalwa. Ga Haysam tunda suka zo ya tsangwami kansa sai dai ka gansa zaune gefe shiru. Koda yake tunda Yakura ta rasu rashin maganarsa ta sake girmama fiye da bayan rasa mahaifinsu. Ya sake zama mara fara'a da yawan walwala.........✍🏼

_Rayuwa kenan, akowane motsi bawa baya rabo da jarabawa da sabbin ƙaddariri, ALLAH ya baki wuyan ɗauka A'isha🥲._

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 23_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Ta shin farko kuɗaɗen da A'isha tazo da su na abubuwan data sayar a Bauchi ta ɗauka ta saya musu abinci. Dan ta fahimci abincin dake a gidan ko cikakken kwana uku bazai musu ba a wannan yawan nasu. Ɗan sauran abinda ya rage kuma ta shiga lissafi da tunane-tunane, babbar damuwarta karatun Haysam, sam bata so karatun yaron ya tsaya koya koma baya. Duk da suma su Ja'afar sun fara a Bauchi, amma a ganinta nasu mai sauƙi ne tunda primary ne. Inna da taga shirun nata yayi yawa ta taɓata tana tambayarta "Mike faruwa kuma? Ni bana son ganinki a wannan yanayin tayar min da hankali yake yi matuƙa". Ajiyar zuciya A'isha ta saki, tare da ɗan murmushin ƙarfin hali. "Inna ba komai ALLAH kamar yanda na faɗa miki tun jiya. Shin Inna idan na saka kaina a damuwa maganin mi hakan zai min, ita dai damuwar bazata canja komai ba, ba kuma zata dawo min da Yakura da Babansu ba wannan duniyar ba, kafin su na rasa mahaifi fa". "Haka ne A'isha ki cigaba da addu'a kinji, komai na rayuwa ƙaddara ce daga UBANGIJI, bawa bai isa gujema ƙaddararsa ba, na ɗan ɗana rayuwar rashin miji data riƙon marayu nasan ƙalubalensa duk da basu kai naki yawa ba, sai dai tabbas nawa mai sauƙi ne dan ban rasa tallafi daga dangin mahaifinku ba, Bilyamin yayi ƙoƙari na ganin kun samu duk abinda ɗa mai rayyayen mahaifi ke samu. Shiyyasa al'amarin dangin uban ƴaƴanki yay matuƙar ban mamaki da tsoro, ya kuma tabbatar min da zamani ya fara canja salon da muka sanshi, ace bawan ALLAHn nan ya ƙare rayuwar samunsa akan hidimarsu amma yanzu ƙasa ta rufe idonsa a gaɓar da sukafi kowa morarsa su juyama zuri'arsa baya, wannan wane irin rashin tausayi ne, wane irin zumunci ne? Musamman yayan nan nashi yafi bani mamaki fiye da kowa. Ko kunya baya ji yazo kuma yace zai aureki kamar dama yana jiran ya mutu ɗin ne". Hannu A'isha ta kai ta share hawayen da suke ziraro mata, fuskata da murmurshi mai ciwo tace, "Babu komai Inna, kansu sukamawa ba shi ba, shi dai dan ALLAH yay musu da zuminci, amma tunda sun nuna su bazasu riƙi bayansa ba ai babu komai. Suma kuma ai sun haifa, kuma mutuwar tasan gidan kowa. Shiyyasa al'amarin mutumin nan ya bani mamaki, kana yaya dan ƙaninka ya rasu kazo kace wai matarsa ta aureka, har sai na auresa ne zai taimaki abinda Abdul-rasheed ya bari a duniya. Inna a zatona ai ana barin halak dan kunya, ai bashi yayansa ba ko Sufyan dake ƙaninsa wlhy bazan iya aure balle shi". "Kibar sheɗani, tunda yanzu kin bar musu garin sai yaci kansa shi da matan nashi masu zaginki su mahaukata masu kishin banza. Ƴaƴa kuma mu ALLAH ya bamu yanda zamuyi mu riƙesu mu basu tarbiyya, ALLAH ya raya miki su ya baki tsahon rayuwar da zaku mori juna ke da su gaba ɗaya". "Amin Inna na gode. Sai dai Inna makarantar yaron Muhammad nan ita ke damuna yanzu, nasu Ma'aruff mai sauƙi ne. Shi ko kinga Secondary yake aji biyu, nan da wasu watanni zai wuce aji uku, bana son ko baya ace ya komai balle karatun ya tsaya. Ga kuɗin da suka rage min bazasu isa ai batun canja masa uniform ɗin sabuwar makarantar da litattafai ba. Shiyyasa nake tunanin ko zan fara wankau ne Inna? Ko kuma naje gidan Iya Tabawa ta sama min gidan aiki?". "Wannan tunani ne mai ƙyau A'isha, duk da harga ALLAH bana son irin wannan sana'o'in tunda duk na jigata jiki ne, wasu ma na kallonsu kamar ƙasƙanci ne, amma idan na hanaki banda hanyar wani abun bayan su, in ma ance sana'a sai da kuɗi, mu kuma bamu da su". "Inna nima baso nake yi ba, amma babu yanda zanyi. Dama dabarata anan idan na ɗan yi kona watanni ne zuwa shekara in sha ALLAHU abinda aka ɗan samu sai a fara sana'ar zai fi zaman shirun da jira a wajen mutane. Ni dai fatana duk su koma makarantar, na kuma share hawayensu kada suyi kukan rasa mahaifi kwata-kwata". "To ALLAH yasa mu dace, yasa haka shine mafi alkairi, yay riƙo da hannayenki, ya zama garkuwarki. Amma kafin a samu mafitar ita bokon zan kaisu wajen Malam su cigaba da makarantar allo tunda kinga acan Bauchin ma suna zuwa". "Eh Inna suna zuwa, hakan kuma yayi, dan nima bana son zamansu a gidan. ALLAH ya ƙara lafiya da tsohon rai mai albarka da amfani. Tabbas yau da bani dake Inna dana shiga uku". "Bazaki shiga uku ba ƴar nan, domin kuwa UBANGIJIN daya hallicemu bai manta da kowa ba, fatanmu dai ya bamu dama da ikon sauke haƙƙin marayun nan da mahaifinsu ya hidimta mana da dukiyarsa da lafiyarsa sanda yana raye, muma ALLAH ka bamu ikon kwatantawa". "Amin Inna."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull